Showing 1 words to 3000 words out of 114964 words

Chapter 1 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

11336


Documented by muhammad kabeer
Whatsapp number
+2348160112181
[5/6, 9:16 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah* 🌹🌹🌹
01

A guje suka shigo cikin parlorn sai faman haki suke, Inna dake cikin daki ta fito tana gyara daurin zani tana tambayansu lafia, cikinsu babu wacce ta iya amsa mata saima kokarin fadawa bedroom dinta sukayi hade da kullo kofan,
"Danmasani ne ya shigo cikin parlorn yana fadin "wllhi Inna gwarama ki fito dasu don yaukam wllhi bazan hakura ba, "Inna ta gyra daurin kwalinta tace haba 'Danmasani wai kai bakada hakuri ne, yaran nn fa kannenka ne, ko me suka maka ai hakuri zakana yi inyi, waima me suka maka yau kuma, ta tambaya tana kokarin karya goro,
"Tayan keken abokina suka huda haka kawai don sun rainani,
"Kai ni na daukama wani babban abun sukayi, ta jawo drawer din dake jikin center table ta ciro dari biyar ta mika mishi, maza wuce ka kai mishi ya gyara dan nasan dagaji dan gidan matsiyata ne,

"Inaga ya tafi kuzo mu fita, Shema'u ta fadi haka
"Lallaima mu fita ya cafke mu, kinsan shi da shegen la6el kaman 6aro, cewan Sumayya,
"Barin dubo mana toh, Sadiya ta fadi tana kokarin isa bakin kofa,
"Ke dalla wace irin banzace kawai zaki 6ata mana plan, Haneefa ta fadi cikin tsaurin da ta saba,
"Cikin kuluwa Sadiya tace ke wllhi yarinyan nn kin faye raini saikace ba kece karaman mu ba,
"Hehehe su karama manya, mammy tace shekara daya ne tsakaninmu, shekara daya bayan an mata CS an cireku 'yan uku ta haifo ni, Shema tace kunzo mu fita Inna ta sallame shi, a tare suka nufi kofa suna sanda kaman 6arayi

"Toh ja'irai ai sai ku fice mun daga daki koh tunda ya tafi, Haneefa ta turo baki tace ke Kakus dinnan kin faye mita, you talk too much wllhi,
"Rufe mun baki da karyan turancinki, sai tsiwa da tsaurin ido kika iya, ga dan karen tsoro, ku wuce ku fice kar wacce ta kuma dawo mun, har sun fice Sumy ta leko tace kakus muna nn dawowa don't shut your door kinji, ku kuka sani jarabbabu inna ta fadi tana kokarin kunna Tv....

Misalin karfe biyar da rabi suna zaune suna kallo Mamy ta shigo fuskanta babu walwala,
"Sannu da shigowa Mamy, suka fadi gaba dayansu,
"A takaice ta amsa kaman bazata ce komai ba sai kuma tace wato ku baza a muku magana kuji ba ko, sau nawa zan raba ku da shiga hidiman 'Danmasani, yanzu abun naku ya fada har kan abokansa ko, wllhi ina raba ku da rashin jin maga, haka jiya aka kawo karanku kunyi duka ma wata yarinya a islamiya, ga malam Habu ma kun takura masa bayada kata6us a gidan nn, kune fasa mishi buta kune karya mishi benci, toh wllhi tun wuri gwara ku shiga hankalinku, sai kunyi laifi ku gudu wajen Inna koh ko kuma Abban ku ya hana a dake ku, toh bari kuji yayanku na hanya gobe duk wani rashin jin da kukeyi sai sanar dashi, Sady dake kokarin kai cokali baki tayi saurin ajiyewa ta shiga magiya tana rokon mamy kar ta fadawa wa Ya Haydar,
"Shema ta daura hanu a ka tana fadin shiknn yanzu gidan nn zai zama mana like Hell, mun shiga uku, Mamy dan Allah kice Ya Haydar yayi zamansa a can Lagos din,
"Hany ta turo baki ba tare da tace komai ba,
"Sumy ta mike tana fadin uhm barinje nayi assignment din Chemistry na,

Sanye yake cikin Kaki na Nigerian Navy, Fari ne kal kakin, sai hulan mai ratsin baki, wanda yake kaman facing cap, gaban rigan an rubuta *Captain A.A,*, wato Aliyu Abubakar, kayakyawan saurayi dan kimanin shekaru ishirin da shida, very young Navy, farine sol dogo, bashida kiba snn bashi layin sirara, gashin kanshi bakine sosai saidai bai bar gemu ba, kasancewarshi soja amma na ruwa, Tafe yake a babban filin saman Lagos wato *Murtala Muhammed International Airport* tafiyan nashi yafi kama da sarsarfa irin dai yanda sojoji ke tafiya, mintuna kadan aka fara kiran sunayen garuruwa, ana kiran garin Kano Captain AA naga ya nufi jirgin, nan da nn aka kar6i luggage dinshi aka ajiye don basai anyi checking dinshi saboda uniform dake jikin shi, shigan su da mintoci jirginsu ta tashi zuwa jihar na dabo.

👸🏻 Queen Samy😍💄💋.....
[5/6, 9:16 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah* 🌹🌹🌹
02

"Misalin karfe 2pm jirgin su Captain A A tayi landing a babban filin jirgin saman *Malam Aminu Kano International Airport* bai 6ata lokaci ba ya dauki drop zuwa gida,
"Malam Habu mai gadi na ganin shi ya karaso da sauri yana fadin ah ah maraba da sojan ruwa, ya mika hanu zai kar6i luggage din shi, da fari'an Haidar suka gaisa da Malam Habu, cikin girmamawa Haidar yaki mika jakan kayan shi wa malam Habu, ya karasa ciki fuskan shi dauke da murmushi.
"Wani indian film suke kalla mai suna *mad about dance*sun kure volume suna sauraren wakan, Haneefa ta mike tana kwaikwayan rawan da suke a wakan, su shema kuma sai dariya suke mata wai bata iya ba.
"Daga bakin kofa ya tsaya ya hade rai kaman bai ta6a murmushi ba, Shema'u ne ta fara ganinshi cak ta daina dariyan da take, Sumayya ma ta shiru sakamakon ganin shi da tayi ta shiga ta6a Sadiya a hankali,
"Ke dalla ki kyaleni.... muryan Sadiya ya sarke sakamakon tozali da tayi da shi.
"Meye duk kuka wani yi shiru ko ban iya rawan bane.... juyowan dazatayi taga Ya Haidar tsaye bakin kofa, da sauri Shema taje ta kashe tv din cikin inn inna take fadin sann... sannu da zuwa yaya, shiru yayi baice komai ba har ya karasa shigowa cikin parlorn, a tare suka shiga gaishe shi, ya amsa a dake snn yace kuzo nan,
"Ba musu suka karasa gaban shi, suka tsaya cirko cirko, tsawa ya daka musu basu san sanda suka zuba gwiwoyinsu a kasa ba,
"Saboda bakuda hankali kun mayar da gida kaman club, waima yaushe kuka fara kallan irin wadannan films din, ya nuna Haneefa yace wato kece tantiriya har kwaikwayan rawan da suke kike ko, shiru Haneefa tayi ta kasa cewa komai,
"cikin tsawa yace ko wacce ta riqe kunnenta, snn yaci gaba da cewa
"This should be the first and the last warning, idan na kuma ganin kuna kallon such film a gidan nn sai na karya yarinya, ku 6ace mun da gani useless kawai,
"Gaba daya suka mike har suna tuntu6e, Haneefa ta turo baki a zuciyanta tace the devil is back dan ita tsaurin ido ne da ita, dai dai stirs sukayi karo da mamy ko waccensu tana kunkuni,
"Meye haka kuma, kuda wa, mamy ta tambaya, Sady tace ya Haidar yadawo, nan da nn fari'an mamy ya karu cikin sauri ta karasa downstairs,
"Haidar na ganinta ya mike da sauri ya tareta da fari'an shi, rungumeshi mamy tayi tana mishi sannu da hanya.

"Suna shiga daki Haneefa tace wai yanzu shiknn wnn mugun ya dawo knn,
"Sadiya tace ke Hany watch your tongue, he's still your brother, bai kamata ki fadi haka ba,
"Toh ai saiki mun wa'azi, karya na fadi, ba mugun bane cewan Haneefah
"Sadiya tace oho dai you can't change the fact that he's your brother, kuma dole kiyi respecting dinshi idan ba haka ba jiki yayi tsami,
"Whatever, Haneefah ta fadi yayinda take kokarin kwanciya bisa gado,
"Heheehe you guys are funny walla, baku zama inuwa daya sai kun kasa hali,cewan Shema dake zaune hanun kujera
"Sumy 'yar salihan cikinsu tace gaskiya muyi avoiding duk wani rashinji yanzu, if not a banza ya Haidar zai rinka jibganmu, kun san soja ba imani ne dasu ba,
"Ke dalla sarkin tsoro wllhi babu abunda zamu fasa tunda munada Inna da Abba, Haneefah ta fadi haka cikin tsiwa...

"Inna na zaune saman dardumanta ta idar da sllan la'asar Haidar yayi sallama,
"Lale lale da soja, sannu da zuwa Ali, ya karaso yana murmushi ya nemi gefenta ya zauna, bayan sun gaisa Haidar dubi Inna yace matar ashe dai baki karasa tafiya ba, ai na dauka bazaki ganeni ba sai an dauko miki tocila kin haska,
"Inna ta kai mishi dukan wasa tace ja'iri wann ido nawa da kake gani ras yake don yafi nakama, ta mike tana fadin barin kawo maka wani abu ka ta6a,
"Haidar yace Inna da kin barshi na riga naci abinci,
"Bazan bari ba dole kaci nawa, shegen iyayi naku na 'yan boko, yanzu sai kace baza kaci abincin tsohuwa ba, toh ai naga daga wajen Mariyan aka kawo ko, kai ko Habubakar bai isa na bashi abinci yaki ci ba,
"Haidar dai yayi shiru yana sauraren ban bamin Inna, a hankali yace God mutum ya dawo knn, wnn tsohuwa will never change,
'Daga can tace magana ne kake Ali?,
"A'a bance komai ba ya fadi yana kokarin ciro wayan shi a aljihu.

👸🏻Queen Sumy😍💄💋.....
[5/6, 9:16 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
03 to 05

Misalin karfe 9:pm Abba ne zaune a falon shi yana kallon network news, Haidar yayi sallama cikin muryan shi mai dadin saurare,
"Abba ya amsa yayinda yamaida kallon shi ga Haidar
"Haidar ya nemi waje ya zauna hade da gaida Abba,
"Cikeda fari'a Abba ya amsa yana mai jindadin yanda 'dan nasa ya zama babban mutum, nan suka soma hira, Abba na tambayan shi wajen aiki, don Haidar yakan shafe wata biyar baizo ba, sallaman da mamy tayi ne ya katse masu hiran nasu, nan suka ci gaba da hiran dukansu gaba daya harda mamyn.
"Kaman yanda suka saba da gudu suka shigo falon, basu kula da Haidar dake zaune kasa gefen mamy ba, suka shiga 6uya a bayan Abba suna fadin Abba, Abba, Abba...
"Tsawa Haidar ya daka masu wanda yasu nutsuwa babu shiri, baku da hankali ko,
"Ya isa Haidar, ka daina tsawa wa yaran nan zaka sa su dinga jin tsoronka, they are just kids, cewan Abba kenan
"Mamy kuwa cewa tayi ai gwara ya ringa tsawatar musu ko zasu nutsu, kwata kwata basa jin magana, especially you Haneefah, gashi kece karamarsu amma kinfi kowa rashin ji,
"Haneefah ta langa6e kai hade da turo baki, nan Abba ya riko ta ya zaunarta kan cinyar shi yace ya isa Angel, gaba daya sauran ma suka rungume Abba suna fadin, Abba what took you so long, yau baka dawo gida da wuri ba, Abba yace I had to do something at the Office that's why,
"Mikewa Haidar yayi hade da yin saida safe masu Abba ya bar falon, hakan ba karamin da'di yayi masu Shema ba, sun jima suna zuba shagwa'ba wa mahaifin nasu kafin daga bisani suka bar falon suka nufi falon Mamy,
"Mamy ta dubi mai gidan nata tace, a gaskiya sakalta yaran nan da kake yi yayi yawa, su mata ne gidan wani zasu tafi, ba ko wane na miji bane zai tolerating wanan hali nasu ba, ya kamata by now su san sun girma, amma har yanzu dakan kansu 'kanana suke,..... ya isa haka Mariya, Abba ya katseta, kinfi so kiga yaran nan cikin rashin walwala ko, toh ni ba irin iyaye masu takurawa 'ya'yan su bane, beside har yanzu ni kallon yara nake masu, ''yan uku they're just fifteen and Haneefah is just fourteen, so kinga har yanzu babu wacce ta mallaki hankali a cikinsu, don haka ni bana so a rinqa takura musu kin gane,
"Shiru Mamy tayi tana sauraren mijinta wanda a ganinta sakalta yaran shi yawa dukda itama tana tsananin son yaran amma na Abba ya dama nata ya shanye.

"Zaune suka sami 'danmasani yana kallon wani film *Aliens* a mbc2, dukansu suka zauna suka hau zuba surutu, idan akwai abunda 'danmasani ya tsana bai wuce idan yana kallo a cika shi da surutu ba.
"Kai duk yarinyan da bazata yi shiru ba ta tashi ta shige ta kwanta, duk suka yi shiru don sun fara jin 'dadin kallon, suna a haka Haidar ya shigo fuskan nan nashi a murtuqe,
"Bakuda schl gobe ne, ya jeho musu wanna tambayan, 'danmasani yace munada,
"What are you still doing da bazakuje ku kwanta ba, gaba daya suka mike ransu baiso ba, har zasu wuce ya dubi su Haneefa yace kai kuzo nan, ba musu suka karas gabanshi, 'danmasani kuwa ya la'be yana musu dariyn mugunta a hankali.
"Haidar ya dubesu daya bayan daya yace kuna jina ko labari na kuma ji kun shiga waje babu sallama sai na karya yarinya, idiots kawai, ku wuce kuje kwanta, saura kuma naji hayaniyanku na taka yarinya, daga haka ya wuce suma suka shige simsim....

"Bayan sun shiga daki Shema ta dube su tace guys I can't believe this is happening, yayaza'ace our own brother hate us like this, kwata kwata yaHaidar baya sonmu, in banda kama da yakeyi da Abba wallhi da sainace ba 'dan gidan nan bane.
"Kamannin Abba ya 'dauka but ko kadan baiyi kirkin Abba ba, cewan Sadiya knn
"Nifa kunsan Allah na tsane yaHaidar like hell, if it was my choice I don't wanna be with him in the same house, Haneefah ta fadi haka yayinda take ciro pyjamas dinta daga wardrobe.
"What's wrong with you guys, yaHaidar is still our brother no matter what, I want you to understand that we cannot change this fact, jininmu ne yayanmu ne, and I knw he does love us, kawai dai so yake mu zama good girls, Sumayya ta fadi haka.
"Oh my gosh, why are always negative. Haneefah ta fadi haka yayinda take kallon Sumayya, snannan taci gaba da fadin, he's always like that since ever we were kids, always yelling at us, as a matter of fact yaHaidar baiki ya bar ganinmu a gidan nan ba, ku duba fa ku gani yau ya dawo dukda ya shafe kusan wattani shida bai ganmu ba amma da masifa ya fara mana, ta juyo tana kallonsu dukansu tace ban ta'ba kallon yaHaidar a matsayin 'dan uwa ba saidai makiyi, tana kaiwa nan ta haye gado ta kwanta,
"Sumy ta ta'be baki tace Allah ya kyauta snn ta shige bathroom, Sady da Shema kuwa wardrobe suka shiga bude don daukan nitynsu, su kansu abun Haneefah ya fara damunsu, saidai suna tsana nin son 'yar uwan nasu don haka suka sha shantar da zancen....

Karfe 7:30am 'yan uku suna zaune bisa dinning suna jiran gambonsu ta sauko suyi breakfast mamy ta shigo tana fadin har yanzu baku gama ba, kunsan yau yayanku ne zai kai ku gwara ku karasa da wuri,
"Sady tace Haneefah muke jira mamy, har yanzu bata sauko ba, mamy tace oya go and call her, you're going to be late.
"Da sauri Sady ta haye kiran Hany, kwance ta tarar da Haneefah ko tashi batayi ba balle wanka, baki Sady ta rike tace "what am I seeing, ta karasa hade da 'daka ma Haneefah duka a cinya tace, what the hell you think you're doing, ki tashi kiyi wanka jor, we gonna be late, and yaHaidar ne zai kaimu, jin sunan da Sady ta kira yasa Hany mikewa babu shiri tana mutsuka ido, da sauri ta zara towel ta fada bathroom tana fadin, let me take the shower first, dan Allah ki tsayani mu sauka downstairs tare kafin ya karya ni,
"Then you've to be fast, cewan Sady da ta harde hannaye tana kallon Hany da tuni ta shige bathroom,.
Mintuna ka'dan Hany ta dauka ta shirya tsaf cikin Uniform dinta, ta dubi Sady dake tsaye tana jiranta tace "shall we, Sady ta 'dan ta'be baki tace naughty girl, dariya Hany tayi tace naughty girls zakice, a tare suka sauko downstairs....
[5/9, 6:09 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
06

Yau ta kama alhamis su Hanifa basuda islamiya dan haka gaba 'dayansu suna field din gidan suna buga basketball. Team din Haneefa da Shema daya sai Sady da Sumy team dinsu daya, cikin jin dadi da kwanciyan hankali suke gudanar da game dinsu....

"Ya fito cikin shiga ta 'kanan kaya, blue shirt da black jeans gashin kan shi as usual sai sheki yake hannunsa na hagu 'daure da agogon Gshock yayi matu'kar yin kyau, kai tsaye parking lot ya nufa yanda Benz dinshi GLK ba'ka ke pake. Yana zura key da niyyan budewa mota taki buduwa ya sake gwada nanma shiru. Hissing yayi a hankali gamida bugan tayan motan wanda hakan yaja hankalin malam Habu, da sauri malam Habu ya karaso yana tambayan Haidar lafia soja...
"A ba komai malam Habu inaga wani abin ya sami key din ne dn taki recognizing key din, har ya juya ya tsinkayi muryan malm Habu yna fadin "aff amma yaran nan dazu sunyi wasa wajen nan ko sun ta'ba maka wani abin.... Da mugun mamaki Haidar ke duban malam Habu sannan ya sake duba key point din to his greatest surprised 'karfe aka saka a lan'kwasa wajen da 'krfin tsiya.... idan ranshi yayi dubu ya 'baci yau babu abunda zai hanashi karya yaran nan, kai tsaye side dinsa ya nufa a hanya ya ha'du da 'Danmasani yace ya kira masa su Shema'u cikin zagwa'di 'Danmasani ya tafi kiransu dama yanaji da haushin sun 'bata masa PS5 dinsa.

"Yeeeey we're the winners shokyyy cewan Hany da Shema knn cikin murna gamida gwalo wasu Sady suna fadin sorry looser, 'danmasani ya 'karaso yana tafa hannu " huuh bravo welldon. Su Shema da Hany sai murna suke yayinda Sady da sumy haushi ya 'kulesu,
"Let's go in and celebrate cewan 'danmasani, gaba 'daya suka sh jinin jikinsu dan sun san halin 'danmasani wani abin ya shirya masu... muje mana ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login