Showing 21001 words to 24000 words out of 87071 words
allura, guda biyu ya mata daya na bacci daya na ciwon ciki
Ahankali ciwon ya fara sauqa, har tadawo hayyacinta
Ganin ta tsura masa idanu tana kallonsa, yace kinsamu sauqi, daga kanta tayi
Yace ok to ga pad nan ki tashi kishirya jikinki ko
Yunquri tayi zata tashi amma sai takasa dan dik jikinta ciwo yake mata
Kare mata kallo yake sai anan ya lura d kayan jikinta, wani tunanine yazo masa, nan yayi saurin kawardashi
Hannunsa ya miqo mata yace riqeni kitashi dan baqaramin tausayi ta basaba
Daganinta ba tambaya, taji jiki lokaci 1 dik tayi wani iri
Ganin zata bata masa tym kawai ya d'agota, kiris ya hana ya saketa ta fad'i sabida wani shork da yaji tin daga yatsan qafarsa har kansa
Cikin sauri ya matseta ajikinsa dan kada ta fad'i, itama sabida batada qarfi sai takuma lafewa ajikinsa
Hanyar toilet ya nufa, ahankali tace zan dau abu acan ta nuna sif da hannunta
Baiyi maganaba sai juyawa da yayi, budewa tayi cikin kunya ta dauki pants
Shima baice komaiba ya wuce toilet da ita, ajiyeta yayi yace ina zuwa
Daki ya dawo sannan ya miqo mata pad din,oya kishirya kizo kisha magani yace da ita
Ganin idanunta sai lumshewa suke alamun bacci yasa yadanja wani siririn tsaki, taimaka mata yayi tayi wanka, sannan ya fice yana cewa 3mins nabaki kishirya
Yana tsaye abakin toilet yaji alamun bude qofar, tana bud'ewa kamar anhankad'o ta, ta taho zata fad'i
Cikin sauri ya riqota ta fad'o jikinsa, lumshe idanunsa yayi kafin ya dagota har kan bed ya kwantar da ita
Nan ya lura ashema bacci tayi, girgiza kansa kawai yayi yace rikicecceciya daga allura sai bacci ashema jininki bayada qarfi, rikici ne kawai
Qare mata kallo yake daga ita sai towel iyaka cinyanta, dik ya jiqe da ruwan jikinta
Ahankali ya miqe ya nufi sif dinta inda ta bude shima nan ya bude cikin saa yaga sleeping dress dinta
Wata coffee doguwar riga marar nauyi, ya dakko yadawo, warware towel din yayi zai samata rigan nan idanunsa suka sauqa akan qirjinta dasuke atsaye cak
Qura idanu yayi dikda qanqantarsu amma fa sai yaga sun burgeshi
Baisan lokacin daya kai hannunsa kaiba wani yanayi yaji sabo da baisan yadda zai fassaraba
Nan take idanuwansa suka canja launi, jikinsa ya mutu, wani abu yaji yana fizgarsa, lokaci guda yakai bakinsa
Nanfa yafara birkicewa, ga lallausan fatarta data sha gyara, ga wannan fitannanen qamshi dake fita daga jikinta, su suka qara shagaltar dashi har yamanta wacece akusa dashi
Lokaci guda ya matsa kamar an tsunkuleshi, da kyar ya saka mata rigar ya miqe
Ahankali yake takawa sabida illahirin jikinsa amace yake, wani kasala yaji ya saqqo masa da baisan dalili ba ga wani irin feeling dake taso masa ahaka ya fice ya nufi d'akinsa.......
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
2β£1β£
Yana shiga falonsa, zama yayi akan cussion, hannunsa ya nutsa acikin lallausan gashin kansa
Cikin jin haushin kansa yake magana, yanzun mene na aikata ma kaina, meyasa zanyi haka why why
Wani irin zogi da zuciyarsa kemasa ga kuma wani irin mugun feeling dayake ji su suka saka idanunsa sukayi jazur kaman gauta
Tunani yake yanzun shikenan yagama jama kansa raini kenan, gashin dama tagama rainashi kuma haka ya faru ya Kenan
Wani abune yaji ya taso ya tokare masa qirji, ji yake inama yana da halin da zai dawo da lokaci baya da bai bari har zuciyarsa ta rinjayesaba
Shiru yayi kawai dan baida mafita, amma ya yanke ma kansa kawai bazai kuma shiga inda takeba baran tamasa abinda zai sakashi ya aikata abinda zaiyi dana sani dan bazai dauki rainiba
Wata zuciyar tace kawai ka rabu da ita amma kada kad'aga mata qafa dan kada ta rainaka, tinda bata cikin hankalinta batasan maiya faruba so kada ka nuna mata wani abu ya faru
Sai anan yaji hankalinsa ya d'an kwanta amma bai daina jin tsanar kansaba
Ya jima azaune awajen har bacci yayi gaba dashi
Bayan yayi sallar magriba ya sauqo down stairs, kiran wayar abdu yayi yace ya shigo ya aikesa
Dan yau baya cikin mood mai dad'i shiyasa ko son fita baiyi
Kud'in abincinsu ya bashi as usual, harya juya zai fice sai ya tuna da waccar yarinyan dake kwance
Kuma ga sauran alluranta da baa mata ba, ya kamata sai taci abinci da amaata
Tsaki yadanyi ganin tazame masa damuwa, kamar baiso yace Abdu
Dawowa yayi cikin sauri gani oga, kudi ya sake miqo masa ga wannan kabiya ta bauchi club ka karbo gas meat da kaza
Karb'a yayi yace to oga sannan ya fice
Sai da yayi sallan ishai ya danci wani dan gaba 1 bai shaawan Komai sannan ya fara tunanin yazai da waccar yarinyan ya mata nocking ne ya wurga mata abincin ita ta sani
Maganintafa wata zuciyar ta tambayesa, tsaki yaja sannan ya dauki ledar ya fice
********
Fauziyyah kuwa tinda tafara bacci ba ita ta farkaba sai da akayi sallan ishai, ahankali tafara bud'e idanunta har ta wartsake tass
Yunqurawa tayi ta tashi zaune amma sai taga wata riga ajikinta wadda bata tab'a sawaba
Tinani take taya tasaka wannan rigar, shiru tayi takasa tuno Komai tace toh wazai samun kawai nina saka mana abina
Yunqurawa tayi ta tashi tsaye haba nan taji cikinta yayi wani murd'awan yunwa
Daurewa tayi ta nufi toilet tasake wanka, sannan ta canza kaya izuwa riga da zani na courtdivoir mai kalan ruwan zuma
Dikda ba kwalliya tayiba amma tayi kyau tunani take taje tasha koda tea nema Inyaso sai tadafa indomie taci
Ahankali ta riqe handle d'in qofar zata bud'e kawai taji gau an turo qofar anbige mata kai
Cikin sauri ta dafe kanta tana cewa wash Allah na
Qarasa shigowa yayi ya maida qofar ya rufe, ko kulata baiba ya wuce kan resting chair ya zauna, cikin had'e rai yace keh zonan
Ko kulasa bataiba sabida haushi taya ya buge mutum ko Sannu bazai iya fad'a masa ba sannan ya hau wani kiran gadara
Cikin d'aga murya yace keh wlh idan nafice bazankuma bi takanki tinda ciwon ajikin kine ba nawaba
Turo baki tayi tana qunquni to ni sunana keh ne, ai dai bansan dani kake ba, ahaka har taqaraso gabansa
Dubanta yayi yace me kikace, sarai yaji abinda tace kawai so yake yaji mai zatace agabansa zata mai2 ta ko zata doje
Sake turo baki tayi, tace ni bance komaiba fa
Bata ankara ba taji ya kai hannu ya buge bakin da qarfi, yace marar kunyan qarya kisake mun rashin kunya kigani sai na fasa wannan bakin wawiya kawai yaja tsuka
Allah ya isa tafad'a amma acikin zuciyarta, kaman ya jita yace me kikace
Ni bance wani abuba, yace ai sai dai kifad'a acikin zuciyarki
Ledan hannunsa ya turo mata gashi only 10mins nabaki kici ki karb'i maganinki dan inada abinyi
Tsurama Ledan idanu tayi kuma bata d'auka ba, afusace yace ke kinsan Allah ko bakiciba dole ki karbi maganin nan dan bazaki mun asarar kudi ba, gara ma kici inkinqi kece zaki wahala ni baruwana
Ayatsine tajawo ledar dan kada yace ta damu, amma azahiri taji dad'i sabida dama wata baqar yunwa takeji
Bud'e ledar tayi, wata gashashsheyar kaza tagani tasha gashin oven nan yawunta ya tsinke, dan Fauziyyah ba bayaba wajen kwad'ayi, sai data yago zata kai baki ya buge hannun
Dago da idanunta tayi tana masa kallon meye haka
Yace to kwad'ayayya kin sauqe idanun kosaina tsokanesu, ba wannan yakamata kiciba, ki bud'e d'ayan Ledan
Wani haushinsamne ya kamata, haka ta bud'e dayan ledar, gas meat tagani, saima taji tafi shaawarsa sabida d'an romon dake jiki
Nan tafaraci abinta hankali kwance tama manta dayana wajen
Wayarsa yake dannawa, amma hankalinsa na akanta yadda yaga takecin naman tana lasan romon shiya basa dariya a zuciyarsa
A zuciyarsa yace au ashe kwad'ayayyace dubeta sai kace kura
Dago kanta tayi dan taji ajikinta kamar ana kallonta, suna had'a idanu ya wani tsuke fuska yace ke idan kin qoshi ne kitashi ki karbi alluranki dan inada abinyi kada kib'atamun lokaci
Zaro idanu tayi tace me kace, miqewa yayi yana cewa abinda kikaji nace
Cikin tsoro tace sai kanemo wadda zakama allura badai niba
Sai kiyi kuma dan sisi na bazaiyi ciwon kaiba garama kitsaya if not kezaki sha wahala idan tabaci
Cikin tsiwa na qarya dan tsoron gaske ya rufeta sabida aduniya ba abinda ta tsana take kuma tsoro kamar allura
Tace to nina saka ka kashe kud'innaka, kawaifa ni ba alluran dazaka mun mugu kawai
Yace haka kikace to banga abinda zai hana namaki alluran nan ba, ko sauraronta baiba ya d'au ledar maganin
Sirinji ya d'auko ya fara jan ruwan alluran
Ganin dagaske yake yasa tafara tunanin taya zata kwaci kanta dan wannan mugun ba tantama sai ya zurkud'amun wannan shegiyar alluran.........
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
*Wannan shafin nakine Sis Nussaiba ('yar mutanen Nijer), Nagode da kulawarki gareni da kuma yadda kike qaunar littafi na, Mmn Faty luvs u too ππ*
2β£2β£
Yana gama jan ruwan alluran, ya nufota gadan2
Aifa nan ido ya raina fata, cikin muryan tausayi tace dan Allah ya Alamin kayi haquri wlh tsoron allura nake, kuma ko agida baa mun
Cikin tsukewar fuska yace to ainan ba gidanku bane, so kada kijama kanki dogon ciwo dan wlh sai anyi alluran
Jin abinda ya fad'a kawai sai hawaye shar suka fara zuba afiskanta
Ko ajikinsa saima Matsowa daya sakeyi, cikin rawar murya tace pls mana ya Alamin ka kyaleni wlh gara kamun duka akan kamun allura
Yace au kinfison dukan, cikin sauri tace eh nafiso
Wani Murmushin mugunta ya sakeyi yace eyyerh sai kuma abinda bakison zanmaki ba
Oyah juya, ko motsawa taqiyi baran ta juya yace wlh idan na caunting 3 baki juyaba matseki zanyi da qarfi
Ek(1), doo(2), yana cewa tin(3), kawai ya riqo hanneyenta, aiko da iyaka qarfinta tafara fizge2, ko sauraranta baiba ya riqe hannayenta da hannu 1, amma sai mutsu2 take
Hannunta tasamu ta fizge, ta shiga jikinsa ta cukuikuyesa, gagam ta maqalesa tana cewa nika kyaleni ko dole ne tinda nace banso
Wannan shegen shork d'in yaji ta ko ina yana ratsashi, gashi sai qara maqalesa take dik ta dabaibayesa da shegen qamshin jikinta mai matuqar kashe masa jiki da haifar masa da kasala
Jin tana neman tayar masa da hankali yasa iya karfinsa ya b'anb'areta daga jikinsa, ya d'auketa cak ya d'aura akan gado
Danneta yayi yadda ko motsi takasa, batayi auneba taji ya zurkud'a mata allura
Wata uwar qara ta danna lokacin dataji shigar alluran, shiko yana gama mata ya miqe ya d'au wayarsa yayi hanyar fita
Wani kuka tafashe dashi tanajin zafin wajen, sai daya kai bakin qofar fita sannan ya juyo yace ga maganin nan inkin gadama kisha inkinaso kibari damuwarki
Cikin kuka tace eh d'in kuma bazanshaba mugu azzulumi, Allah ya isah banyafeba
D'aga kafd'arsa yayi irin idon't care nan yayi waje abinsa
Itakuma tana nan tana kukanta har bacci yayi gaba da ita
******
Papa kuwa bedroom nasa ya wuce, toilet ya shiga ya watsa ruwa, boxer kawai yasaka ya fito falo
Amma dik atakure yakejinsa tinda waccar fitinanniyar yarinyan ta rugumesa dik yakejin wani yana yi, shi yarasa wannan wace irin damuwace tazamar masa
Ta shigo rayuwarsa ta takuresa, ga wani yana yi datake haifar masa adik lokacin da suka kusanci juna
Tabarsa ya jawo ya kunna, nan danan ya zuqe kara 1, lokaci qanqani ya turniqe wajen da hayaki wane anhura wutar damina
Amma dik da irin shan daya mata baiji hankalinsa ya kwanta ba, sam sabida haka ya balle murfin wine nasa ya kafa kai, lokaci guda yafara jin natsuwa
Kwanciya yayi awajen, yanajin dik samywarsa ta yaye, yana nan awajen har 11 shiba bacci ba, bakuma ido biyuba
Nidai mmn Faty nace Allah ya shirya
******
Kwanan Fauziyyah hudu period nata ya d'auke amma tin ranan farko cikin bai sake ciwo ba, haka bata sake saka papa a idanunta ba
Ranan da aurensu ya cika sati biyu, kuma monday mai zuwa papa zai resuming office, aranan da safe Daddy ya kirasa awaya
Hello Daddy ya gida, yacema Daddy Bayan ya picking call d'in
Lfy lau son, ya daugther inlaw na
Sai daya ya tsine fuska sannan yace fine Daddy
Daddy yace haba son saina roqi a kawomun yar tawace naganta
Toh Daddy nikuma nahanata zuwane, ka turo driver ya kaita mana
Daddy yace driver kuma kai me kake da bazaka kawota ba
Haba Daddy nadaukota amota ta, amatsayinta nawaye kenan har tashigarmun mota kawai to zansa akawota tinda ka matsa
Daddy yace Alamin wai yaushe zakayi hankaline, kodai baka cikin hankalinkane, toh koma yaya ne zuwa yamma ka kawomun ita kuma da kanka that's all, yana fad'in haka ya kashe
Itakuma tana tashi tayi wanka tayi breakfast, sannan ta sauqo down stairs dan tad'an gyara wajen
Sai data gama ayyukanta tsaf, har data wuce sai kuma ta kalli falon papa tace dan Allah badan halinkaba barin gyara maka
Tana shiga kuwa da wannan kyakykyawan photon nasa taci karo, murmushi tayi dan haka kawai wannan photon yake birgeta
Tagama gyarawa ko ina sai sheqi da qamshi yake, tana fitowa taci karo da papa y saqqo kuma ita yake nema dan yayi ta norcking qofar ta baiji motsin ta b
Qaremata kallo yayi, tana sanye da wani swiss army green colour da milk ya mata kyau sosai, amma shi haushima ta basa azuciyarsa yace dubeta kamar yar baby
Yi tayi kamar bata gansaba tazo data wuce shi, hakan ya qara b'ata masa rai, cikin sauri ya saka hannunsa ya riqo mopper dake hannunta ya dawo d ita baya
Tace lfy malam meye haka
Duban walaqanci yamata yace bansaniba kuma ubanme ya kaiki falona
Tace oho nima bansan niba inhar bakasan me ake da wannan ba, ta nuna masa moppern hannunta
Yace ni kike fad'a ma haka ina tambayarki, wani wawan rankwashi ya zuba mata akanta
Tace me Namaka zaka rankwasheni, yace d more bazaki daina mun fitsaraba d more bazan daina dukankiba yar qauye kawai mai kamada mayu
Tace nicema kai, bata qarasaba ya doke bakin ya kuma qara mata rankwashi, sannan yace kikuma shirya da yamma muje gida amma wlh kitabbatar kinyi wanka dan bazakishiga mun mota da qazanta ba qazama kawai yana kaiwa nan ya wuce ta abinsa
Shiru tayi tana tunanin mai ya Alamin yakeji da shine kam yake mata irin wannan walaqancin......
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
Augusf, 2017
2β£3β£
Shiru tayi awajen tanajin wani d'aci aranta
wasu hawayene masu zafi suka zubo mata
gogewa tayi da bayan hannnunta cikin sauri ta haura side nata
tana shiga falonta tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi wadda itama batasan dalilin yinsaba
sai datayi mai isarta sannan ta lallami kanta tayi shiru
dikda damuwanta yananan maqale a ranta amma kashi hamsin cikin darii ya ragu
Bayan tayi sallan laasar tayi wanka, ta tsantsara kwalliya,cikin wata jar super,mai ratsin fari da baqi
kwalliya tayi sosai wadda tinda tazo gidan batai irinsa ba
Wani danqareren gwal tasaka na cikin kayan aurenta,sannan ta feshe ko ina na jikinta da turaruka mmasu qamshi
baqin takalmi tasaka hadi da baqar jakarsa,sannan ta yafa wani black veil ,habawa sai wadda yagani ko maqiyi sai dai yayi shiru badai yace bataiba
Down stairs ta saqqo tazauna gudun yace ta bata masa lokaci
tana zaune fiye da 20mins kafin ya fito,tinda taji takunsa tasunkuyar da kanta dan tin abinda yamata dazuma bata huce ba,kuma bata qaunar ganinsa kawai ba yadda ta iyane
Sanye yake cikin qananun kaya as usual, black troser n white shirt mai layin baqi ,idanunsa sanye cikin wani baqin glass ,wasu baqaqen covers ne aqafarsa masu tsadar gaske, suman kansannan sai sheqi yake alamun yasha gyara,sai wani uban qamshi dayake zubawa ,gaskiya papa qarshene dan haduwa ya hadu ,shikansa shiyasa yakeji da kansa
qare mata kallo yayi tsaf ta cikin glass ,yana nazarin ta,amma sai ya tabe baki ,yace jibeta yadda tayi kamar gaske
qarasowa yayi wajen datake ,amma ko magana bai mataba ya wuce hanyar fita
ganin baikulataba yasa itama tai kamar bata gansaba
sai daya kai baqin qofa ,sannan ya juyo fiska ahade yace keh idan bazakiba nayi tafiyata,ko kina tunanin zanfita na jiraki ne
cikin rashin kula tace ayyah ai banga wucewarka ba baran maganarka
hakan yasake shaqarshi waima bataga wucewarsaba, toh kiqara 2mins kiga wlh barin jiraki ba yanafadin haka ya wuce
wani wawan tsaki taja ,afili tace aifa dan wajen momcy zamuje aida ba inda zani
haka ta fito ,lokacin yana qoqarin shiga mota,gidan baya ta bude zata shiga
wani mugun kallo ya bita dashi ,yace cemaki akayi ni driver ne mai daukar mutane
tace nibanceba,yace toh ki rufemun mota kidawo gaba ko kikona gida ,yafi maki sauqi
turo baki tayi ,tace komai sai anyima mutum masifa mtss,yana kallon bakinta amma baidaiji abinda taceba
ko kulata baiba ,yatada mota,ganin dagaske tafiya zaiyi ta bude motar tashigo
haba wani sanyi da qamshi suka daki hancinta ,lumshe idanunta tayi tana jinjina haduwa irinta papa,moatarsa ma abin shaawa komai nasa unique abinsa
shiyasa yake walaqanta mutane son ransa,dubi yadda masu gadi kemasa adawo lfy kamar su kwant masa amma ko yasan sunayi Allah ya shirye da wannana halayen nasa
yana fitowa layinsu zai sha kwana nan sukayi clashing da TJ ,gefen hanya ya sauqa yayi parking,fitowa yayi ya barta aciki
TJ ma parking yayi ,yana fitowa papa na qarasowa,abinda suka saba da sun hadu shi suka fara suka kashe hannu
TJ yace man kabuya kawai abinka ,meye duniyarma
Papa yace kaidai bari wlh naso naleqaka so bansami damaba
TJ yace ina zaka sami dama tinda yanzu kasamu duniya
bata fiska papa yayi dan ya fahimci inda maganar ta dosa,kaifa baa maganar arziqi dakai sai kabatawa mutum rai
TJ yace nikuma anyi walqiya tahaska ba ,nifa ba abinda zaka fadamun yanzu tunda ashe ni kake mayarwa dan iska
papa yace bazaka ganebane , TJ yace nayarda bazan ganeba ashe shegen kaya kanaso kanaiwa kasuwa,kuma banda iskanci harnima saika rainamun hankali
cikin takaicii papa yace to anrainmaka