Showing 81001 words to 84000 words out of 87071 words

Chapter 28 - Budurwar Kauye Hausa Novel

07 Oct 2024

13126

amma nace mata zandawo

To miye aciki tunda tana dakinta kika wani tada hankalinki

Da shagwababbiyar murya tace bafa nata da hankalina bane ko ruwa ban bata bafa gashin har dare yayi baran abinci

Haba babyna kada kidamu aidai tasan kina tare da mijinkine ko yanzun muje ki kai mata juice da akwai nama a kitchen wanda nasa aka sayomun banciba inyaso saina fita na samo mana abinci

Toh shikenan muje tafada tana tashi daga jikinsa

Riqeta ya kumayi yace me babyna zataci

Shiru tadanyi tace umm QUNDUN Bauchi Club zanci da graves

Dadi yaji sosai jin tafadi abinda zataci ba gardama

Amma kuma tabasa dariya yadda tace wai qundu, dan qaramin bakinta yaja yace oh baby kwadayi kenan

Bata rai tayi tace nikam bana kwadayi kuma tunda kace haka nama fasa barin ciba

Cikin sauri yace am so sorry bafa dake nakeba nida little babynanefa

Cikin sangarta tace aidai nadauka dani kake

Yace waneni nace maki mai kwadayi muje yanzun nakawo maki ko shalelena

Atare suka fito kitchen ya riqo mata abinda zata kawoma hannatu har bakin qofarta sannan ya miqa mata tare da manna mata kiss a forehead nata ya fice

Washe gari da kyar ya fita office sai wani nan nan yake da ita har bata gajiya da kallon yadda yake mata hidima

Bayan yafita ma ajima kadan ya kirata awaya yana tambayar ya suke ita da little babynsa

Ita kuwa tai ta zuba masa shagwaba tana narke masa

Adaddafe yakai 4pm a hospital sannan ya nufo gida

Ita kuwa tana bararraje afalon qasa hannatu ta mata danmalele ta baza mata a plate, yasha manja da yaji ga kuma robar yajin agefenta

Tafaraci kenan ya dawo

Hannatu tana gaishesa ta wuce dakinta

Shikuma zama yayi agefenta aqasan carpet yana cewa babyna nayi missing naki sosai

Ita murmushi tayi tace me too only, munyi kewarka muma

Tana maganar tana kaiwa loma abakinta

Kallon abinda takeci yakeyi da kyau sannan ya dubeta baby mene ne wannan

Itakuwa tsabar dadi har wani lumshe idanu takeyi tace danmalele zakacine

Kai baby a ina kika koyi cin wadannan abubuwan amma dai dafatan bazaima little babyna illah badaiko

Bata fiska tayi tace nifa wato yamun komaima badamuwarka baneba saita babynka kake ko

No bahaka bane baby ke ai babbace amma babynmu baiyi kwaribafa kike wannan ciye ciye

Tace to nidai inzakacine muci inka qoshi kuma shikenan

Tafada tana qara gumbuda yaji

Kutt baby irin wannan cin yajin haka fa yafada yana daukar roban yajin

Marairaice murya tayi tace pls kabani yajina inbakason yajin barin saka maka agabankaba

Yace nikam barinciba kici dadi lfy amma dai yajin nan ya isheki haka nan

Tace nikam kaban kayana tunda baci zakayiba

Yace ko baxan ciba bazan bakiba

Ganin dagaske yakeyi yasa tace toh naji dan qaramun kadan tai maganar tana langabe kai

Yadda tai maganar yabasa dariya yace shikenan debi kadan to tana diba ya rufe yamayar kitchen

Baby barinje na watsa ruwa kafin kigama ko

Toh afito lfy tafada tana cigaba da cin kayanta

Girgiza kansa yayi kawai yana murmushi yadda tabada hankalinta wajen cin wannan abin

*****
Haka rayuwa yaci gaba tafiya masu cikin kwanciyar hankali da natsuwa

Dan yanzun fauziyyah ta murmure sosai daga laulayin datake ba abinda ke daminta

Sai dai kwadayi kam kamar kullum qara mata akeyi

Hannatu kuwa mutumiyar kirki bata gajiya da yimata wannan da wancan

Hankalin papa ya kwanta tunda tasamu lfy batada matsala yanzun

Rainon cikinsu sukeyi cikin tattali da kulawa

Sannu ahankali cikinta yake girma har yakai yanzu watanni shida

Ya fito yayi mata das dan gaskiya cikin ya qarbeta sosai yaqara mata kyau idan tayi kwalliya sai cikin ya fito yamata gwadas ajikinta

Wani sontane kullum ya ke qaruwa acikin zuciyar papa yadda kullum itama take tattalinsa ta take bashi kulawa dikda cikin dake jikinta bai hanata ta bashi haqqinsa yadda yakamata

Yanzun har girki tana masa hakan yasa hankalinsa ya kwanta sosai yayi wani haske harda wata yar qiba yayi wadda tamasa kyau sosai

Kullum adduar su momcy dasu Abba bai wuce Allah ya sauqeta lfy ba

*****
Yaukuma da shagwaba ta tashi

Kwance tasamesa a bedroom nasa yana nade acikin wani milk blanket mai laushin gaske

Doguwar rigace ajikinta ta atampa mai laushi

Tamata kyau sosai sai qamshi takeyi

Bakin bed din tazauna tana kallon kyakykyawan fiskansa mai matuqar annuri

Wani kyau taga ya sake mata dikda baccinsa yakesha peacefully

Sannu ahankaki takai dan yatsanta kan bakinsa tana shafawa ahankali

Dan motsi kadan yayi alamun yanajin ana tabasa

Jikin kunnensa takai dan qaramin yatsanta tana sosawa

Bude idanunsa yayi ahankali yana kallonta da alamu bai gaji da baccinba

Cikin muryar bacci yace yadai akayi babyna

Ashagwabe tace nidai katashi hakannan

Pls baby kibarni sai anjima kadan ko kema kizo muyi baccin atare

Nidai nidai banjin bacci Allah kuma kaima katashi

Oh baby pls fa nace
, tace umum fa nace tana janye bargon nasa

Toh naji zantashi amma saikin bani .....yaqarashe maganar ahankali

Cikin sauri ta waro idanunta tace aa wasa nake maka yi kwanciyarka

Bude idanunsa yayi yace ai tunda kikasani natashi saifa kinbani

Miqewa tazoyi yayi saurin riqe hannunta ya daura hannunsa akan cikinta yanajin yadda yake motsi

Baby kinji little babyna yanason gaisawa da daddynsa, nima kuma inasonjin ya babyna ya kwana

Kwantawa tayi ajikinsa da murya mai sanyin shagwaba tace ba jiyama kaji lfyrsaba nidai bayanzunba

Aa baby jiya ai good night namasa yanzun kuma zan masa good morning yafada yana shafan cikin nata

Narkewa takumayi ajikinsa tana cewa nidai katashi kayi wanka kayi break

Aa baby wani break kuma bayan kinzo kin tayarmun da hankali jifa yadda kike qara kashemun jiki da salon shagwabarki, kuma kemafa kinaso kina kaiwa kasuwa jibi yadda jikinki yayi...


Bai qarasaba takai hannunta tana dukan qirjinsa cikin wasa nidai kasakeni intashi

Aifa nafada ba inda zakije baiqarasaba tace wash cikina tana riqe cikin

Ai baisan ya akayiba yagansa azaune cikin rudewa yake cewa mai yasameki baby mene ne

Cikina kadagani zaune tafada kamar zatayi kuka

Ok ok yafada yana miqar da ita zaune

Kafin ya zame blanket din jikinsa ta tashi da sauri tayi hanyar fita tana cewa saika fito kuma 20mins nabaka

Baby au dama bagaske kikeyiba kika tsoratani ko

Tana bakin qofa tace bakaki katashiba

Good kinmun 1-0 ko bakomai zamu hadu yafada yana miqewa

Ita kuma ta fice....




✍🏻Faty Mmn Faty





🌾🌾🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾



Budurwar Qauye🤷🏼‍♀🤷🏼‍♀🤷🏼‍♀

Written by Faty Mmn Faty

October, 2017



7⃣5⃣
Bayan dawowarsa da kwana biyu,dasafe bayan sun karya zai fita office,saida yagama dik abinda yakeyi sannan yadawo bakin bed inda fauziyyah kezaune,yana zama ta kauda kanta gefe fiskanta babu walwala da alamun fushi takeyi dashi, ganin yadda taci magani tawani juyarda kanta gefe guda saita basa dariya,aifa tanajin yadda yake mata dariya saita qara qulewa,hannunsa yasa ya juyo da face nata yana kallonta kuma baibar dariyar ba,cikin fushi tace nikakema dariya ko saboda ganan mental agabanka, sai anan yayi magana yace no nibadake nakeba baby,to inbadani kakeba kaidawa tunda dagani sai kai ne adakinannan,yadda tai maganar tana murguda mai baki shiyasake basa dariya,haushine yasake kamata ta rarumo pillow tana kwada masa,riqe pillow din yayi yana cewa nadaina baby nadaina barinsakeba kuma bafa dake nakeba,kamar zatayi kuka tace nidai kakyaleni naji da guda daya bakawai kazauna kanamun dariyaba baicin ka hanani fita, baby kece kikasakani dariya da kike fushin rashin gaskiya,tace naji banada gaskiyan katashi katafi abinka ba ruwanka dani sai hawaye sharr,ahankali yace ya salam babyna akan nace kizauna agidane kike fushi hadda kuka?,ita dai bata kulasaba saima cigaba da hawayenta datakeyi,hannunsa yasaka yana goge mata hawayen da murya mai taushi yake cewa ya isa hakanan badai unguwaba zamu tafi tare amma kigane badagangan ne nahanaki zuwaba aa saidan yanayin da kike ayanzun,da kinfita qafafunki sufara ciwo shiyasa amma kinsan ai inda badan haka taya zan hanaki zuwa gidan TJ,tunda kinason zuwa barin hanakiba amma on one condition,dasauri tace nayarda fadi naji,bazaki yini azaune waje dayaba kitakuramun babyna yaqarashe maganar yanajan dogon hancinta,eh nayarda nayarda,yace toh muje kisaka mayafinki muje nasauqeqi kada na makara,cikin zumudi ta miqe ta fice zuwa bedroom nata,murmushi yayi yana kallon yadda tafita da murnanta sai ya tsinci kansa cikin nishadi dan dik abinda takeyi birgesa takeyi har cikin ransa kuma bai qaunar bacin ranta



Aqofar gida ya sauqeta yace kigaida mmn mubeen saina dawo da yamma zanshigo mugaisa,tace toh Allah ya tsare tamasa kiss a chiks nasa har data fita yace emm baby jimana,juyowa tayi tana kallonsa,cikin kallon soyayyah mai narka zuciyar wadda akema yace tum apna kayalakna(kikularmun da kanki),cikin murmushi tace i will insha Allah,good my princess yafada ,itakuma tace bye sannan ta fice shikuma yaja motarsa ya wuce,tana shiga khairy da murna ta tareta tana zolayarta barka da zuw mai sarauta,uwargida kuma amarya agidan likita,cikin dariya tace fadi kanki tsaye wannan haka yake,bayan sungaisa sukayita hiransu na yan uwa abin shaawah,haka suka wuni tate har TJ yadawo sai wajen4:30pm sannan papa yadawo amma haka TJ ya hanasu tafiya wai sai sunyi dinner tukun sutafi,haka suka haqura sai bayan ishai sannan sukafi amma kaginnan fauziyyah ta matuqar gajiya sabida yadda qafafunta ke mata ciwo, kawai sotake su isah gida dan tagaji da zaman motanma, tun amotan tafara kuka tana wayyo qafarta,haka yadinga lallaminta har suka iso gida,tundaga ranan fita inba yazama doleba ko antinatal bata zuwa ko ina

Haka suka cigaba da rainon cikinsu, inda papa yake matuqar bata kulawa na musamman irin wadda mai ciki take buqata,cikin yana rayuwa.cikin halin lfy har Alah yasa ta cika EDD nata sai dai haihuwa shiru,ganin ta wuce EDD nata kuma haihuwa shiru yasa tafara damuwa dan batada damuwar data wuce ganin tarabu da cikin jikinta cos tagaji dashi sai baqar wahala datake sha,ga ciwon qafafu idan tazauna dakyar zata rarrafa ta tashi,ganin yadda hankalinta ya tashi sosai yasaka papa damuwa amma bai nuna mataba sai lallaminta dayake hadi da rarrashi,yanzunma suna kwance har wajen 12 nadare taqiyin bacci,babyna yakira sunanta ahankali cikin natsuwa,umm kawai ta amsa, meya hanaki bacci har wannan lokacin umm yana shafan gashin kanta,cikin damuwa tace nibanasonyin bacci dawurine saina farka cikin dare nagagara bacci idanuna su bushe,baby damuwar da kikasama rankinefa yasa har baki iya bacci,tace aiba dole nadamuba khairyfa lokacin data haihu batama cika EDD nataba ammma ni harna wuce da kwana biyu sai kuma tafara kuka,haba baby ya kike abu kamar wacce bakisan cewar shifa EDD dama 2weeks before or 2weeks after bane,pls naroqeqi ki kwantar da hankalinki kda kije BP naki ya hau baicin bakidashi,haka yasamu hartayi shiru da haka har bacci ya dauketa, washe gari bayan yadawo daga office suna zaune yace baby yadai jikin bakinjin komai,tace babu abinda nakenakeji nikam,yace shikenan Allah ya kawo haihuwan cikin sauqi,tace amin ya Allah


Bayan sallan ishah suna zaune suna cin abinci sai ya lura bataci sai juya spoon din takeyi ,cikin kulawa yace babyna yadai bakicin abincin koba kyason asamomaki wani, aa kawai maratane ta kulle,marakuma baby, tace eh Allah kuwa yace to kidaure kici abincin,tace sai anjima idan tasakeni amma yanzun barin iyaciba,hankalinsane yaji ya tashi amma bai nuna mataba dan tunda yamma daya dawo yaga alamun haihuwa ajikinta yadda cikin yayi qasa sosai fiye dana kullum,shima abincin da bai qarasa ciba kenan


Wasa farin girki tun tanajin abu kamar wasa har yazama gaskiya dan wani matsanancin ciwon mara da qafafu takeji kuma batsan taya zata misaltashiba bama,12am abunfa yaci tura bashiri yadauketa sai hospital akanhanya yakira momcy yafda mata sunkusa isa asibiti fauziyyah tana labour ,aifa nan itada da daddy suka taho asibiti ba shiri,papa suna isowa sibiti aka wuce da ita labour room,shima bayansu yabi ya shiga ciki,sai dai tashin farko ana gwada BP nata akasamu yahau sosai har 160,nanfa hankalinsa ya tashi dik yasan cewan hakan tana faruwa amma dai yadamu sosai sabida tsoron kada eclemsia ya shigeta


Har akayi sallan asuba shiru bata haihuba sai dan karen azaba datake shafawa,nanfa papa yasake inda yakama ya birkice shima lallashi hadi da nasiha su momcy sukai tamasa haryasamu natsuwa,amma ya gagara komawa labour room din cos bazai iya ganinta awannan halinba,suna zaune saiaddua dasuke mata amma babu wanda akafadama around6:30am ta haiho qaton danta namiji,wani saeedah taji lokaci guda,jin kukan jariri yasa papa miqewa cikin sauri yashige labour room din,kanta ya nufa ya riqe hannunta yana mata sannu tare da adduoi,sai daime anasake gwada BP nata akaga yasake hawa sosai180,aifa nan hankalin papa ya kuma tashi take ashiga bata taimakon gaggawa gudun abinda zaije yazo.....



✍🏻Faty Mmn Faty




🌾🌾🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾



Budurwar Qauye🤷🏼‍♀🤷🏼‍♀🤷🏼‍♀

Written by Faty Mmn Faty

October, 2017


7⃣6⃣
Hannunsa sarqe cikin nata ya riqe gagam kamar za'a kwace masa ita,bakinsa yakai saitin kunnenta yana kiran sunanta cikin natsuwa da sanyi,babyna kina jina babyna,da kai ta amsa masa alamun eh tana jinsa, ajiyar zuciyah mai qarfi ya sauqe jin tana cikin hayyacinta,wasu allurai Dr Zainab tamata sabida BP nata kafin tasa aka miqo babyn saitin fiskanta tace mata madam ganan babynki mene kika samu?, kallonta takai kan babyn nata fari sol dashi kuma qato nan take wani qaunarsa taji yaratsa dikkannin jiki da bargo nata, cikin sanyin murya tace baby boy ne,murmushi Dr tayi tace good,sannan aka wuce da babyn dan agyarashi,haka papama sai alokacin yaqarema abinda ta haifa kallo sabida hnkalinsa na akan matarsa da lfyrta,murmushi kawai yake yana dad'a hamdala ma ubangiji abisa kyautar daya masa,yana rungume da ita har aka gyarata aka d'inketa dan ta qaru sosai kasan cewar girman yaron,dikda anmata alluran rage zafi amma baihana papa lallaminta yana shafar knta cikin salon soyayya da kwantar mata da hankali har aka gama mata komai,dakansa ya shigar da ita toilet dake cikin labour room din yamata wanka tsaf sannan ya fito wajen su momcy ya dan karb'an kayanta
momcy tana ganinsa tace yadai papa su fauziyyah suke,da murmushi sosai afiskansa yace momcy lfynsu qalau kayanta ma zaki bani dan zaa maidata obstatric room,cikin murna tace masha Allah shikuma angonnawafa dan nurse tacemun namijine,sake fad'ad'a fara'arsa yayi sannan yace shima lfyrsa qalau suna shiryashine amma saikinganshi farisol dashi kyakykyawa kuma qato shiyasa ya bata wahala,momcy takama baki tace oh papa babu ko kunya kake jero wad'anannan bayanai haka,d'an sosa qeyarsa yayi yace kai momcy yawanefa yanzun wane kunya kuma ai gara mutum ya nuna jin dad'insa tunda kud'i baxai saya masaba,kayan tamiqo masa tace Allahu ya shiryeka papa kaikam kunyarka da sauqi tafada tana cewa kafin kufito barinje office d'in daddy toh nasanar masa lfynsu qalau sannan ta wuce, shima ya koma ciki





Dakansa ya shiryata tsaf,sannan ya sunkuyo da kansa dai2 face nata yace my princess sannuko, murmushi tamasa kawai sabida batajin qarfin jikinta,ina kemaki ciwo? ya tambayeta yana shafan kanta, babu tafad'a, sai dai banjin qarfin jikina ne kawai, Alhamdulillah idan kin huta zakiji kinware kinjiko my life, gyad'a masa kanta tayi dai2 da nurse ta qaraso wajensu hannunta d'aukeda babyn, cikin girmamawa tace Dr ganan babyn tana miqo masa,hannu biyu yasa ya karb'i d'ansa kuma gudan jininsa,cikin so da qauna marar misaltuwa yake kallonsa ga yalwatatticiyar fara'a kwance kan fiskansa,lokaci guda yasakejin qaunar yaron kamar ya maidashi cikin cikinsa,yaro qato kyakykyawa mai kama da babansa dan babu ko tantama kamanninsa sak papa,sai qamshi mayukan jarirai yakeyi,an saka masa kayan sanyi farare sol masu sirkin light blue,ankuma nadesa cikin light blue showel sai qamshi yakeyi,nan take ya tofa masa adduo'i tareda sumbatarsa ta ko ina,fauziyyah kuwa kallonsu take cike da zallar qauna dan sun matuqar birgeta,kallonta yayi yace madam ganan babynmu karb'esa kisa masa albarka ya miqo matashi,karbansa tayi tana murmushi sannan itama ta tofa masa adduo'i
nurse ce tadawo tace yallaba'ai za'a maidata dkin hutu sabida ta huta sosai, is ok yafada yana karba'an babyn, itakuma tadawo kan wilchair aka turata,abakin qofa sukaci karo da momcy dawowarta kenan sai suka wuce room da aka kai fauziyyahn,papane ya jawo plask ya had'a mata tea mai kauri ya tallafota yana bata inda momcy ke riqeda yaron tanata kan buga waya tanasanar da haihuwan,bayan tasha tea sai anan bacci yafara fisgarta sabida alluran da aka mata,bada jimawaba bacci ya d'auketa,sai anan papa yaji natsuwarsa yadawo jikinsa,daddyne ya shigo momcy ta miqo masa babyn tana cewa ganan abokinka sai bacci yake da alamu zaiyi haquri ba irinsu ooba,tafad'a tana kallon papa,dariya kawai yayi ya fice dan yagane dashi momcy take,yana fita yafara buga waya yana sanarda qaruwan da yasamu, haka ma'aikatan asibitin wad'anda suka sami labari sukaita masa murna,shikuwa bakinnan bai rufuwa tsabaragen farin ciki



Kwananta d'aya da haihuwa suka koma gida inda yan uwa da abokan arziqi suka dinga zuwa asibiti gaisheta,hakanan dik wata kulawa da maijego da yaronta ke buqata momcy tana basu,hakan yasa basuda matsala,cikin ikon Allah BP nata ya sauqa sosai dikda bai dawo normal ba
Kwanansu Abba da mama da qanwar maman umma hajja wadda itake binta amma bata da aure mijinta rasuwa yayi suka zo bh kuma ita zata zaunama fauziyyah zuwa arba'in,fauziyyah taji dad'in zuwansu sosai haka suka yini lis sai yamma suka tafi,bayan magriba ya maida momcyma gida tunda ganan umma hajja,suna shiga falo zaune suka sami daddy yana kallon Aljazeerah news, momcy tace barita watsa ruwa tukun data zauna sannan ta wuce,bayan papa sun gaisa da daddy nan yake tambayarsa umm daddy dama inason tambayarka wanne suna za'a sanyawa yaron,murmushi daddy yayi had'i da gyara zamansa yace kaji kafa Alamin dawani zance,aikai zaka zabi sunan daka yadace saika masa hud'uba dashi,shiru yad'anyi yace shikenan daddy zanmasa hud'uban da sunanka,kallonsa daddy yayi yace anyakuwa bakaso kankaba banason kazamo cikin mutane masu son kansufa,kallon daddy yake cikin rashin fahimta yace menayi daddy?, daddy yace inhar dacewane to sunan Abbanku shiya dace da yaronnan sabida haka nina yafe asanyawa masa sunan Abban fauziyyah dan aminina ya cancanci fiye da haka,papa yace insha Allahu sunan Abba zaa saka masa ,cikin jin dad'i daddy yace masha Allah, Allah ya muku albarka,ya amsa da amin, nan sukaita hira har momcy ta fito kafin yamusu sallama ya tafi



*****
Washegari dasafe kamar kullum ya shiga ya dubasu yaga yadda suka kwana,cikin sa'a yau yasamu fauziyyah idanunta biyu harma tayi wanka, dan yau jikinta da sauqi sosai takeji,shima babyn an masa wanka ana saka masa kaya kenan ya shigo, har qasa ya duqa yagaida umma hajjah,bayan sungaisa ta miqo masa yaron dan tagama shiryashi sannan zata fice, cikin girmamawa yace umma nifa fita zanyi nashigo mugaisane dama, tace lah bakomai zanhado mata abin karine kayi zamanka sannan tafice, tana fita ya maida kallonsa kan fauzynsa wanda shigowarsa yakejin wani shauqinta na d'ibarsa amma ya matse sabida idanun umma hajja, wani kyau yaga tamasa tayi wani bulbul da ita irin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login