Showing 18001 words to 21000 words out of 87071 words
tunanin ta wuce kota koma, nan take tayi wani murmushi tace yau saina nuna maka tsiyar dan qauye
Sad'af2 ta juya, d'aki takoma ta sake kwalliya, wata doguwar riga fitedgown tasaka ta shadda, dark ash, anmata aikin surfani daga sama har qasa
Rigan tad'an kamata, idan kaganta tayi kyau sai dai kamar yar baby dan Fauziyyah ba jiki ko kadan ga girjinnan kamar yayan goruba, yarinta zalla kawai daka ganta zaka gani dan babu wani abu mai auki ajikinta
Daurin dan kwalinnan yamata kyau dan Fauziyyah kyakykyawace sosai, fitowa tayi zuciyarta sai bugawa take, tana zuwa bakin steps sai data dai dai ta natsuwarta sannan tafara saqqowa dasdas kake jin qarar takalmin ta
Falon papa ta wuce direct, tana yaye curtain d'in da sallama ta shiga dik suka juyo TJ da kb suka amsa sallaman
Inda papa ya tsaya ganin mai yakawo yarinyannan yana tare da baqi Bayan dik kashedin daya mata
Gunsa yaga ta nufo kadan2, idanu ya zuba mata dan ganin iyaka gudun ruwanta........
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
*This page goes to my swt sis Aunty Hadiza, thanks 4 ur luv n support ππ*
1β£8β£
Cikin taku mai natsuwa harta iso wajen dayake zaune
Kan hannun kujeran dayake ta zauna, hannayenta dik biyu tasa tasaqalo wuyansa
Fiskanta ta kwanta jikin nasa, cikin wata murya dabai san tana dashiba mai tattare da shagwab'a tace
Dear, ashe sun qaraso nikam inacan sai yanzun nagama
Papa nan yayi mutuwar zaune, abu uku su suka hanashi magana
Nafarko wannan shegen shork dayaji jiya lokacin da ta tab'a jikinsa, dik da yana huld'a da mata amma bai tab'a jin irin wannan abinba dan ya tab'a mace, amma karo na biyu kenan da Jikinsu ya had'u amma sai yaji wannan abin
Na biyu kuma wani fitinannen qamshi dake fita daga dikkannin jikinta su suka kashe masa jiki
Na uku shine haushi da baqin ciki yarfashi da tayi agaban su TJ, shi TJ baima damesa kamar kb ba
Sanin bazai yi maganaba yasa ta juyo tana kallon su kb, da murmushi afiskanta tace sannunku da malam TJ, wlh kunzo ina ciki
TJ da mamakin ashe shi Ameen yake, zagayawa soyayya suke sha da amarya fal zuciyarsa amma sai ya share
Yace haba bakomai ai amarya bakya laifi ko da kinkashe d'an masu gida
Dariya tayi ta sake maqale papa, tana kallon idanunsa, cikin shagwab'a tace wai haka ne swt
Wani qululun baqin cikine ya sashi lumshe idanunsa yana tunanin mai zaima yarinyar nan ya huce abinda tamasa
Hakan da yayi sai ya bada kamar amsa mata yayi
TJ azuciyarsa yace shere Dr ashe kawai harka ya bud'e sabuwa yasamu yar shila yana morewa, sai wani pretending yake
Ina yini tace da kb, lfy lau amarya ya amarci?
Wani shuumin murmushi tayi wadda yasake qawata face nata tace sai dai katambayi swt
TJ yace tabbas Ameen keda wannan amasan, aikaga yayi shiru baiko magana
TJ yasake cewa wannan abokinmune yana nuna kb sunansa
Malam kb ko tayi saurin fad'i
Au kinsan sunansama ashe TJ ya fad'a
Dear yacemun zakuzo tareda kb ko namanta sunan, alhalin lokacin data lab'e taga suwayene a lokacin taji TJ ya kira sunansa yace kb
Nan TJ yasake tabbatar da lalle shi Alamin yake rainawa hankali
Miqewa tayi barin kawo maku ruwa, bata jira amsan suba ta wuce abinta
Kitchen ta shiga, tana shiga ta dafe qirji tace hmm lalle yau nayi jarumta irin wannan rashin kunyan bantab'a yin irintaba
Wani dariya kuma tayi dan tasan tabbas yau ta qonawa ya Alamin zuciya
Cikin sauri takama bud'e2 dan taga mene damene akwai dan wannan shine shiganta na farko
Aiko nan taga ba abinda babu, freezer ma shaqare yake da nama, kifi, kaji
Wata qofa tagani, tana bud'ewa taga store ne nanma ba abinda babu, dankali, doya, kwai ma ga wasu banda wadda tagani acikin fridge
Aifa nan tafara jido tana kaiwa falon ta tana ajiyewa, sai da ta d'ebi dik abinda take buqata sannan ta d'auki tire ta cikashi da drinks kala daban2, cups ta wanke sannan ta d'auko ta nufi falon papa
Yanda ta barshi haka tadawo tasamesa fiskarnan babu annuri
Ko d'agowa baiyiba baran ya kalleta, lokacin data fita kamar ya bita amma sai yafasa tinda ai zasu tafi su barsu agidan
Kuma idan har ya bita, tabbas wani tunani nadaban zasu sake tinda tagama zubarmasa da class agaban kb, shi bayajin ta TJ ma
Zubawa tayi ta ajiye masu tace bismilla kusha ruwa
Kb yace godia muke amarya thanks so much
Bakomai ta fad'a, wajen papa ta koma ta zauna, sai dataga sunsha ruwa sannan
Ta matso jikin papa tace swt nikam barin shiga ciki, na daura mana dinner
Maida kallonta wajen su TJ tayi sannan tace toh nikam barin shiga ciki
Saina fito
TJ yace mukam ma tfy zamuyi
Tace haba dai bazaku tsaya kuci abinciba
TJ yace inaa kinaga yadda ango ya had'e fiska alamun mumtakuresa, gara mu wuce tin bai koramuba
Suka kashe hannu shida kb, kb yace gaskiya kam
Mungode madam sai wani lokaci kawai
Tace to mungode Allah yasaka ya bada ladan ziyara
Dik suka amsa da amin
wani hot kiss ta danna masa a chicks dinsa tace Dear sai ka shigo
Cikin sauri ta wuce kada cafkota, aiko tana zuwa bakin steps da gudu ta haura ta nufi side d'inta
Tana shiga ta saka key, ta kulle dik wata maqata najikin qofar sannan ta zauna tana Maida numfashi
Papa kuwa jiyake kamar ya fashe da kuka dan baqin cikin abinda yarinyar nan tamasa
TJ ne yace ango mu zamu wuce sai munhad'u kawai
Da kyar ya iya furta ok man sai munhad'u, thanks kb sai n shigo
TJ ne ya ce wai mutumin har kafara kawo wutane daga zama akusa dakai sai idanu su canza
Kb yace ai kasan yanzu tahau network, suka kashe hannu suna dariya
Papa yace wlh zanci ubanku, cikin fushi yayi maganar
TJ ya matso saitin kunnensa yace ayi dai ahankali kasan yarinyace, dannaga kadau saiti tin baaje ko inava, dftn yanzu kafahimci abinda nake fad'a maka abaya
Na kaiwa nan ya wuce, suna fita shikuma yayi hanyar side d'in Fauziyyah
Tsabar bacin rai har baya gani sosai, sai dai me yana zuwa yaji qofa gam akulle
Wani mahaukacin bugu yake ma qofar
Cikin tsiwa tace wai wayene kam
Kibud'e qofar, maganane ta fad'a irin ko inkula amma azahiri atsorace take
Open the door I Said, wlh don't let me repeat my self
To wai na bud'e akan me, ko d'akinkane
Ok, toh wlh tinda haka kikace yau saina karyaki agidannan, ina nizaki walaqanta, zan nuna maki iyakarki
Tace ah haba kaji haushine, toh idan ka kamani kada kabarni d rai mtss taja dogon tsaki
Ina fad'a maki Kibud'e qofannan tin dawuri fa
Wai kaikam wani irin qauyanci ne yake daminki
Kutt, nikike cema dan qauye ni, ni
Toh inba qauyanciba har kadage na bud'e qofa baicin kana iqirarin saika karyani, aiko inkaga qofannan a bud'e sai dai inkai ka bud'e dan nikam bazan bud'eba gara kadaina b'atama kanka lokaci
Tunawa yayi Da ko wacce qofa tana da extra key, d'akinsa ya wuce ya bud'e drawer dan ya d'auko extra keys d'in dan yau saiya koya mata hankali...........
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
*Wannan shafin nakune masoyan Budurwar Qauye (Fauziyyah), Mmn Faty ta gaisheku all ππ*
1β£9β£
Bincike yake amma wasa gaske ko abu mai kamada makulli babu, bai kuma ganiba
Dik wata drawer dake cikin d'akin sai daya bincika but ba Komai sai takardu da wasu abubuwansa
Zama yayi abakin bed, ya dafe kansa da hannu biyu yana tunanin ina keys d'inanan kam suka shiga
Hannunsa ya dunqula ya naushi d'ayan hannunsa, da qarfi yace dmm it!
Cos ya tuna lokacin da Daddy ya basa keys d'in gidan tare da extra din yace shi baison extra dan baiga mai zai dasuba
Yanzun ga ranan su, safa da marwa kawai yake acikin d'akin yarasa abinyi
Tinani yake idan yabar yarinyan nan taci bulus kenan, n wayasan abinda zata masa agaba tinda ya fahimci kunne qashi ke greta
******
Jin shiru2 har fiye da 20mins batasake jin motsinsa ba, hakan ya tabbatar mata ya bar wajen
Hakan yasa hankalinta ya d'an kwanta, bedroom nata ta shige ta canza kaya, wata simple gown tasaka marar nauyi
Falo ta dawo tafara kwashe kayan data zuba, tana kaiwa kitchen
Sai data ajiye Komai a muhallinsa sannan, ta daura abinci indomie da kwai ta dafa, bata ko juyeba ta wuce daki dan anata kiran sallah amasallaci
Saidata idar da sallah, kafin ta dakko abincinta had'i da gwangwanin sidene
Zama tayi hankali kwance taci tayi nak abinta, ta kora da juice
Wajen kayan kallo taje dan tagaji da zaman shiru, tana kunna socket Komai ya kawo dama ashe an saita Komai
Kallo ta zauna tanayi tama manta da wani wai ya Alamin
Sai da 8 tayi sannan taje tayi sallan ishai, daga tasake dawowa falo abinta sai wajen 11 sannan takashe Komai tayi d'aki dan bacci takeji sosai
Asuba ta gari matar Dr
******
Ganin baya da mafi ta hakan yasa ya haqura amma da niyyar dik sanda suka had'u sai ya hukun tata
Bathroom ya shige ya watsa ruwa, sannan ya fito
Farar rigace mai gajeren hannu yasaka ta shan iska, sai farin wando 3quater
Cikin jin kai ya fito sai wani b'ata rai yake kamar yaga abin kyama
Farfajiyan gidan ya fito yana kiran Abdu mai masa hidima
Cikin sauri ya qaraso, tsugunawa yayi yace gani oga
Cikin isa ya saka hannunsa a aljihu, Kudi kawai ya miqo masa, kasayo maku abinci kamar kullum take away hudu naku
Sai kasayomun rosted fish, da roba 1 na shaka
Toh oga, ya amshi kudin sannan ya wuce, haka ya tako ya dawo ciki
Kwanciya yayi afalo yana jiran dawowar Abdu, tsulum ya tashi daga kwancen ya zauna sabida wannan mayataccen qamshin jikin yarinyarnan ya damesa
Abin mamaki hakan bai masaba nanma bai daina jiba, mtss yaja tsaki ya miqe
Falonsa ya shiga, tab nasa ya d'auka dan awajen ya batta tsabar b'acin rai baima tunaba
Nanma dai falon wannan qamshin yake, ahankali yace kin cuceni amma shiru yayi yana cizan lips nasa
Waje ya fito ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun da aka jera qarqashin wata rumfa mai domin hutawa
Chat yakeyi hankali kwance amma wannan qamshin yanajinsa kuma yarasa daga ina ne
Basarwa yayi yace May b ma hancinane tinda baso nakeba
Yana nan zaune Abdu ya dawo, sai daya tsugunna yace gashi yallab'ai
Ko d'ago da kansa baiba, ya masa nuni da hannu alamun ya ajiye akan table din gabansa
Cikin girmamawa Abdu ya ajiye, sannan yace atashi lfy oga sannan ya wuce
Ko amsashi baiba, amma inda sabo yasaba da halin ogansa, dan indai jin kaine da yarfa mutane to papa no 1 ne, shiyasa ko a office ma special mutane yake gani dan shi consultant ne
Sai da aka fara kiran sallah sannan ya miqe ya shige ciki, direct side nasa ya nufa baiko kalli side na Fauziyyah ba dan yasan bata bud'eba
Alwala yayi, sannan yayi sallah, fitowa falo yayi ya kunna sport tv yana kallo, sai dai me wannan qamshi yakumaji ya damesa
Oh Allah, wannan wani irin damuwane kam, shidai yasan kullum dakinsa a kulle ne baran yace ko kawo masa turaren tayi, n yasan batama tab'a shigo masa d'akiba
How comes to haka ya faru, sharewa yayi kawai ya faracin kifinsa, sai daya gama sannan yaje ya wanko hannunsa, ya sunkuya yana brush sai yaji kamar awuyansane qamshin
Aiko tabbas ajikinsane, nan ya tuna lokacin data riqesa ne wato ta shafa masa
Cire kayan jikinsa yayi ya zuba su a cikin laundry basket
Cika jacuzzi yayi da ruwa, ya shiga yaringa dirzan jikinsa kamar mai canza fata
Yakai 30mins kafin ya fito, Farar singlet da white boxer yasaka, kwanciiya yayi akan 3sitter, remote ya d'auka yana canza channel
Amma kuma dik irin yadda yasake wanka ya canza kaya baidaina jin wannan qamshinba
Rai b'ace ya jawo kwalbar wine nasa, yafara sha , amma tsabar ransa ajagule ne yasa ko dad'inta baiji
Tunani yake waikam mene ne yasa, da jikin yarinyannan ya tab'a sa sai yaji wani irin shork ajikinsa, n gawani mayataccen qamshi da jikinta keyi harta shafa masa
Bawai qamshin badad'i bane kawai baison dik wani abu daya shafetane
Lumshe idanuwansa yayi yana tunanin tin randa ya fara ganinta, har zuwa yau da tamasa abinda ya kasa mantawa
Tsaki yaja ahankali ya furta pagal, gyara kwanciyarsa yayi kawai yana shaqan wannan qamshin lokaci guda yaji wani kasala ya lullub'eshi
Ga wani baqon abu dayakeji, ya kuma kasa gane kome ne ne, kawai abinda yasani yana buqatar mace akusa dashi
Wannan shine rana ta farko a rayuwarsa dayaji shaawan kusantar mace kuma baisan daliliba
Yana nan kwance ahaka har bacci yayi gaba dashi, ranan ko abun sabon baishaba dan jiyayi Komai ya fice masa arai
*****
Wasa gaske yau kwanan Fauziyyah biyu bata fitoba
Hakan yasa basu had'uba, shima baikuma bi takanta ba
Idan gari ya waye yayi wanka ya fice gidansa dake sokoto road, yamma nayi ya dawo gida, bai yarda su had'u da TJ
Fauziyyah kuwa tinda gano tsayuwa asaman barandan falon ta nan take ganin dik wani abinda ake awaje
Yanzun tana sanin fitansa da dawowarsa, dataga ya fita zata sakko tayi abinda take sonyi ta koma abinta
Yau satinsu guda da aure, kuma tun jiya takejin alamun kamar period dinta zaizo
Damuwarta 1 yadda yake wahalar da ita shiyasa ta bud'e qofarta tace ko kasheni zaiyi gara nabar qofarnan a bud'e
Falon taga yayi qura, tace barin gyara falon nan ko shara bai tab'a ganiba
Wani wando d'an qarami wadda ko guiwanta bai kaiba da yar qaramar riga tasaka
Mopper da tsintsiya ta d'auko tafara gyara wajen
Sai taji cikinta ya murd'e nan ta durqusa awajen
Tayi2 ta miqe amma ina fir ta gagara, ga wani irin murd'ewa da mararta takeyi
Qanqame stick d'in Mopper na hannunta tasake dan azaban datakeji
Papa kuwa yau dawuri ya dawo gida dan akwai inda zashi
Yana shigowa falo ya hangota adurqushe da Mopper a hannunta
Wani Murmushin mugunta yayi yace idan kere na yawo zabo na yawo wataran zasu gamu
Kingama boyen naki, yau sai kin gane shayi ruwane
Nufota yayi yana tunanin wani kalan mugunta zai mata.........
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
2β£0β£
Tsayauwa yayi akanta, cikin gadara da isa yace kingama boyen naki marar kunyan qarya
Tana jinsa amma bazata iya masa maganaba, dan wani irin ciwo takeji tin daga kafafunta har kanta
Ganin bata kulashiba, yace oh nizaki rainama hankali kinaji ina maki magana bazaki amsaba
Nanma bata kulashiba, azuciye ya fincikota, aiko datasa wata uwar qara , take ta sanqame awajen
Yace waw that's good, lalle kin iya dramer to gara ki tashi inba haka ba funishment naki ninkuwa zaiyi
Dan atunaninsa likimo tamasa
Hannuunta ya damqe cikin mugunta yace zaki gane bakida wayyo... Maganarsa ce ta maqale jin hannun asake
Tsuramata idanu yayi Da kyau, nanfa abin ya bashi tsoro dan inba kuskure yayi ba kamar bata numfashi
Subhanallah shine abinda ya furta, a rud'e yace ke, ke tashi niba abinda zan maki
Nan ya kama jijiyar hannunta nan ya fahimci suma tayi
Ai baisan sanda ya saka hannunsa biyu ya d'agota cid'ak ya nufi d'akinta
Cikin sauri ya kwantar da ita akan bed ya dawo kitchen, ruwa mai sanyi ya dauka sannan ya dawo dakin
Yanda ya barta amiqe haka yadawo ya sameta
Balle murfin bottle d'in yayi ya yayyafa mata ruwan, amma bako alamun ruwan ya shige ta
Ya salam shine abinda ya furta, tsoronsa kada wani abu ya sameta yasan Daddy bazai yafe masaba
Hankalinta ya matuqar tashi sosai, sauran ruwan ya juye mata akanta nan taja wani dogon numfashi
Alhamdulillah shine abinda ya furta, amma kuma sai yaga sai murd'e2 da shure2 takeyi, tana kuma riqe da cikinta
Matsowa yayi kusa da ita cikin husky voice nasa yace meye haka kikeyi, ko wani abu na daminki ne
Sai anan ta bud'e idanunta ahankali jin muryarsa, nan tafahimci ad'aki take, mai makon ta amsa masa sai ma hawaye dakebin fiskanta
Cikin takaici yace ana maki magana bazaki amsaba sai kifara mun kuka, idan bazaki mun maganaba ke kika sani ni tafiyata zanyi
Ganin sai wani miqewa take hannunta akan mararta kuma batai maganaba sai uban hawaye dake ambaliya afiskanta
Sanin taurin kanta, zaiyi wuya tayi magana inhar ahakane, zuciyarsa ta bashi shawara ya tambayeta cikin sigan lallashi ko zata fad'i damuwanta dan tabbas akwai abinda ke daminta
Kada wani abu yasami yar mutane
Cikin sigan lallashi, ya tausasa murya, umm pls talk to me mana, mene ke damunki, ina ke maki ciwo?
Da kyar ta iya cewa cikina, qafana kaina sai takuma fashewa da kuka
Is ok, ya isa haka umm, kiyi shiru zai bari, shiru yayi yana nazarin ta ahankali yace dama yana maki haka ne ko wannan time dinne yamaki haka
Girgiza kanta tayi, yace yana maki kenan
Nanma nodding kanta tasake masa
Ok to barin muga sai nasamo maki magani ko, hannunsa yasa aqasan marar ta yadan danna, dayan gefen yasake dannanwa
Nan tasa qara, is ok nabari dazafi ko
Barin zo, kiyi haquri yanzun dan dawo ko
Cikin sauri ya fice, da mugun gudu ya figi motarsa, wani babban phermacy ya shiga nan ya had'o mata magani da allurai
Har yazo zai fita, sai kuma ya dawo baya yana tunanin yasaya mata pad
Wata zuciya tace masa, ba girmanka bane ka tsaya sayan pad, pad d'inma ma wata qaramar yarinya
Juyawa yayi ya sayi dika roll din dan yanzu baida lokacin tunani sabida halin daya barta
Dasauri ya shiga mota, ya nufi gida, cikin sauri ya zari ledan maganin ya shiga cikin gida
Direct d'akinta ya nufa, agalabaice yasameta har ta fita ahankalinta
Baiwata wataba yaja ruwan