Showing 42001 words to 45000 words out of 87071 words

Chapter 15 - Budurwar Kauye Hausa Novel

07 Oct 2024

13121

ya wanke sannan ya fito

Yana zama ta matso shi sosai tace yanaga kajima yace umm na dan gyara wajen ne shiyaa

Tabe baki tayi tace ok

Nan yadan fara matsa mata qafa ammafa ina juhaina saita canza layi dan ita bata gajiya da wannan lamarin nan suka tattara sukayi bedroom nasa acan suka gama shaaninsu kuma balaifi papa yana samun natsuwa dan baqaramin gyara tasha ba kawai dai waccan abinne da bai taba gyaruwa amma balaifi tana da niima


Sai bayan azahar suka tashi nanma ya aika akamusu take away

Da dare ma haka take away ya masu

Haka haka har kwanansu uku da aure kullum dare da rana sai dai take away kuma idan sunci bazata iya gyara wajenva baran ta wanke abinda suka bata

Daya mata magana sai tace itafa gara dik abinda suka bata asashi a shara inyaso asai wasu amma ita bazata iya wanke wanke ba


Yace toh zai dauko mata mai aiki harta amince amma daga baya datayi tunani saita ce bataso ba yanxu ba


Afannin munir kuwa tace ranan friday ya shigo bh ya kwana a hotel inyaso ranan saturday sai ya qaraso gidanta kafinnan dr yana gida

Nan ta shirya masa plan nata

Kwanan su shida da aure amma gaba daya papa ya kasa gane juhaina wacce irin mata ce

Komai ba ruwanta bata shara bata wankewanke bata girki ko daidai da rana daya bata taba tunanin ta shiga kitchen tamasu girki ba

Haka baruwanta da gyaran daki abinta sai dai toilet kam zata wanke tsaf ta fesa wanka da kwalliya koyaushe tana qamshi abinta

Ga danbanzan son yawo kullum itakam sufita suje nan suje can

Amma bata taba zuwa gidan momcy ba koda yamata zancen sai tace bayanzu ba

Washegari saturday wajen 12 bayan sun karya suna zaune afalo sai juhaina ta dubi papa tace my king anjima kadan wani cousin nawa zai zo fa


Yace ok wane kenan

Tace sunansa munnir yasamu admission anan ATBU

Papa yace ok amma baki taba ban labarinsa ba


Tace umm mamarsa qanwar daddy ce


Yace toh badamuwa sai ya shigo

Bada jiwaba kuwa aka norcking qofa


Papa ya tashi ya bude ganin saurayi matashi amma bazai kai papa ahaifeba yasa papa yagane shine munnir

Hannu ya miqa masa da murmushi yace barka da zuwa

Yawwa barka dai ya fada suna shigowa cikin falon


Da murmushi afuskarta tace yau malam munnir ne agidana

Shima da murmushi afiskansa yace nine dai amarya ba kya laifi


Tashi tayi ta kawo masa ruwa da juice harda snacks da papa yasaya masu sabida baqi

Ganin yadda take wani rawar qafa da baqon daga zuwansa harta kawo masa ruwa ya fahimci lalle baqon yana da muhimmanci awajenta

Nan suka rinqa hira inda takecewa yaushe zaku fara lectures ne

Tabe baki yayi yace wlh nifa kamarma na haqura da school dinnan

Juhaina tace mai yasa kake yin hakane munnir yanzu wannan shekara na uku fa kenan kanasamun admission amma sai kayi wasa tomeye dalilin daxaka bar school din


Yatsina fiska yayi yace nifa kinsan barin iya zama acikin school ba


So inda zamu samu renting din kuma wai lokaci ya qure dik ankama


Sai wani waje da aka nuna mun shikuma gaskiya bai munba so kawai gara na haqura

Juhaina tace lalle ma akan wajen zama sai ka haqura da karatu dama dai bakason ATBU

Yace ahto ba sunqi sukai mutum wajeba sharp2 yaqare ya dawo


Juhaina tace aikaine baka nuna kanason karatun da gaskeba shiyasa amma badamuwa indai wajen zamane zamuyi magana da my king

Anan sukaci abinci rana sannan ya tafi wajen laasar


Da daddre juhaina tana kwance ajikin papa sunyi shirin bacci

Ahankali tace my king


Naam baby na akwai damuwane

Daga kanta tayi alamar eh


Cikin sauri yace damuwa kuma wacce irice baki fadamunba


Marairaice murya tayi tace wlh kaga munnir shine babba agidansu kannensa mata ne acikin su daga wacce yanzu take service sai wacce take shirin gama skull amma shi yaqi yadda da karatu sai yanzun nema aka samu ya yarda


Gashi shine namiji babba kuma shine hope din daddynsu


Pls ka taimaka kabarmasa BQ mana yazauna kona wannan semester mana


Shiru yadanyi kamar mai nazari


Jin yayi shiru yasa juhaina tace pls mana my king kataimaka


Yace ok badamuwa inyaso saiki fada masa gobe yayi parking ba matsala dik abinda kikeso nima inaso


Cikin jindadi ta qanqameshi tace nagode nagode my king

Daga nan suka lula duniyar maji dadi....


Wai wanene *MUNNIR*?
Kubiyoni a next page dan jin wanene munnir kuma meye hadinsa da *JUHAINA*



โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

August, 2017


4โƒฃ3โƒฃ
Washegari da safe juhaina ta kira munnir a waya tasanar masa saqon papa

Da yamma kuwa lis sai gashi nan da kayansa ya dawo inda yasamu ansaka halliru mai wanki da guga ya gyara masa ko ina


*WANENE MUNNIR*
Mnnir shuaibu shine ainahin sunansa, iyayensa sun jima da rasuwa tun yana dan qarami

Ahannun baffansa ya taso wato qanin mahaifin sa

Tun tasowan munnir ya taso da rigima ba ta kadanba

Gashi da son karyan kudi sai dai Allah bai bashi ba

Tunda ya kammala makarantar sakandire bai cigaba ba sabida halin rashin kudi

Daganan bashida aiki sai bin yaran masu kudi sune party sune biki ahaka ya tabe

Watara sunje birthday party na wata budurwar abokin abokinsa anan ya hadu da juhaina lokacin tazo hutun qarshe wadda daga shi ta kammala karatunta

Lokacin da juhaina ta kyalla idanu taga munnir sai taji ya birgeta har tana sonyin alaqa dashi

Daga nan tazo tasameshi inda yake zaune nan ta nuna masa cewar tana sonsa

Shikuma tunda yaganta ya fahimci akwai yayan banki atare da ita nan ya bada kai bori ya hau

Tundaga ranan juhaina suka dinke da munnir itace kemasa komai na hidimar rayuwa

Tasaya masa waya mai tsada

Ta saya masa kayan sawa ta bashi kudin kashewa

Har lokacin komawarta singapore yayi

Bayan ta komane ashe tana da shigar ciki na wata daya, acan ta zubar dashi bayan tafadawa munnir abinsa ya farru


Juhaina sosai takeson munnir dan araayinta idan ta tashiyin aure shidata aura haka shima ya amince da batun aurenta tinda shikam ya samu tana masa komai

Bayan ta qare karatunta ta dawo nan suka dora daga inda suka tsaya itada munnir

Lokacin da papa yazo mata da maganar aure bata boyewa munnir ba

Amma shi saiya ce sam baisan zancen ba kuma ba auren da zatayi ta barshi

Nan tace masa wane shi harya isa ya hanata aure dama itace tace data aureshi kuma tafasa sai yaya

Duban bakida wayo yamata yace wlh intayi aure sai da yardarsa dan zaije ya samu saurayin nata yafada masa gaskiyar abinda ke takaninsu inyaso yaga yanda zatayi

Sanin munnir zai iya bin diddigi ya samu inda papa yake yasa ta lallaba shi dan tana matuqar son papa sosai

Dakyar tashawo kan munnir ya amince amma da sharadin suna tare koda tayi aure

Haka ta amince akan bayan bikinta zata sama masa koda gidane inda zai zauna saiya dawo bh da zama harma ya fara karatu
Wannan kenan

*****
Bayan sallar magribah papa da juhaina suka fita basu jimaba suka dawo dama abinci sukaje sayowa

Bayan sunyi parking Abdu yazo dasauri ko da akwai abinda zai shiga dashi ciki

Cikin girmamawa yace barka da dawowa oga

Aha Abdu shine abinda yafada yana miqo masa abincinsu adaqike yace gashi na hutar dakai fita

Juhaina ta fito da leda guda uku ahannunta yayinda uban gayyar shima ya fito

Har zata wuce sai papa yace my queen

Juyowa tayi ta amsa da yess my king

Inaga mu miqama munnir abincinsa idan munshiga ciki basai munfitoba ko

Ok muje to tashi dashi

Munnir kuwa tunda suka shigo yake tsaye ajikin window yana kallonsu cikin baqin ciki

Dan wani haushin papa yakeji cos y rage masa jin dadi ganin sun nufo wajensa yasa cikin sauri yasauqe curtain ya koma kan cussion ya zauna yana latsa wayarsa

Norcking suka masa

Daga ciki yace yess come in

Suna shigowa dasauri ya tashi cikin murmushin dole yace barkanku da shigowa

Papa yace yawwa amma yana tsaye cos baxama zaiyiba

Miqomasa take away nasa tayi tace bross ga abincinka sai da safe

Allah ya kaimu yafada yana bin bayanta da kallo

Nace sai kayi ai matar wani ce๐Ÿ™„

Bayan sun ci abinci papa ya dubi juhaina amma bada wasa ba yace my queen yakamata kifara dafa mana abinci tunda kinga yanzu ga munnir ma bai dace kullum muriqa bashi abincin wajeba

Ganin yadda yayi maganar bada wasa ba ya kuma sha murr yasa tace shikenan Allah ya kaimu

Washegari da safe ta dafa masu indomie

Sai dai satisfactory haka sukaci dan bai wani test ba

Da rana kuma haka aka kwaba white rice da stew dikda kajin dake ciki amma sam kasa ci sukayi dagashi har ita

Sauran mutanen gidan kuwa banbi takansuba

Ai daga kan dinning yace mata kada tamasu dinner tabari kawai dan yafahimci bata iya girkiba

Haka sukaci gaba da zama ahaka inda azuwa yanzu yafara gajiya da halayenta sam

Gashi bata kunyar idan yace tamasa abu tace bayanzuba

Satin bikinsu biyu TJ ya kwanta rashin lfy fever mai tsanani har saida papa yaje ya saka masa ruwa agida da allurai

Amma abinda ya birgeshi da gidan TJ shine tsaftar matarsa ko ina kyalkyal kamar baa takawa sai qamshi kawai dake tashi ta ko ina

Gashi ya lura da tana son TJ sosai ba irin sonda juhaina kemasa ba tinda dik abinda yakeso shi take masa

Agidan ya wuni ranan bayan tagama abinci ta kawo masu amma TJ sai ya gagara ci

Papa kuwa haka yaci yaqoshi yana santi aransa har yana inama ace matarsa haka take

Ganin yakasa cin abinci dik ta damu sai tambayarsa take mezaici adafa masa

Yace tamasa faten irish potatoe da hanta da alayyahu

Nan da nan ta daho ta kawo masa balaifi yadanci kuwa sai anan hankalinta ya kwanta

Sai gab da magriba ya tafi yana fitowa wayar juhaina ta shigowa

Doguwar tsuka yaja kafin yadau wayar dan

Tun bayan laasar juhaina take kiransa awaya yaushe zai dawo

Cikin jin haushi yace wai meyene kika dameni aidai zandawo ko ko ancemaki bata zanyi yana fadin haka ya kashe wayar dan wani haushinta yakeji yanzu dayaga yarinya qarama yadda ta iya komai da kula da miji

Ita kuwa banda abiya mata buqta batada aiki

Yana tafiya yana tunanin gaskiya dole dasake inma makarantar koyan girki da gyaran gida zata shiga sai dai tashiga dan zamansu ahaka bazai yiyuba

Itakuwa tasamu dama suna sheqe ayarsu da munnir shiyasa ajima kadan ta kira taji koya kusa dawowa kada ya dawo yasamesu atare


Amurtuqe ya shigo gida direct room nasa ya shige sai bayan yayi wanka sannan ya fito

Juhaina ta dubeshi tana zaune afalo tana kallo tace wai lfy kuwa hooney kaketa bata rai

Nakira ka awaya kana wasu magana gashi kadawo kuma ranka abace

Yace eh kawai zamanmu ne yakamata mu gyara

Gyara zama tayi tace toh kamar me kenan

Yace yanxu ace ko girki baza ki iya yimana ba komai idan inason nagani da kyau sai dai inni nayi haba

Kawai nayanke shawara zan maki register a school na koyan girki da kula da gida

Dubansa tayi nan taji ranta ya baci wato raini ne yasa zai zo yana fada mata haka

So kawai gobe zanje na mak........


Hannu ta daga masa tace heeyheey ya isa haka Alamin kul karkasoma wannan maganar

Da mamaki ya dubeta yace ni kikecema hey har kina dagamun hannu

Tace anfada maka din so what

Kuma ko cemaka akayi mai aikice ni da zaka fara tsiro da wani abu aidai ciyar dani dolenkane

Ko ance maka agidanmu inayin girkine har zakazo kanamun wasu surutai da shouting

Cikin bacin rai ya dubeta yace lalle juhaina nikike fadama haka ba kunya

Tace nice ma kai kajiko

Hannu ya daga zai mareta sai yafasa

Wata dariya ta sheqe dashi tace ya kafasa lalle da kamari mai tsada dan wlh ramawa zanyi tsaf ni banza bazata shani ba

Ko ashaye kazo kada ka taba kwatanta dukana dan ni bazan tolarating nonsense ba


Dubanta yatsaya yi dan baitaba tunanin tasan yana shan wani abu ba tunda boye mata yake

Itama dubansa tayi ido cikin ido tace yess ko ka dauka bansan kana shayeshaye bane kawai kallonka nake so kada kafara abinda zai dameka kaji nafada maka tana fadin haka ta wuce shi tabarshi awajen

Tsabar mamaki da bacin rai yakasa koda motsi kamar wadda aka dasa......


Wai ina labarin mutan Abujane kam๐Ÿค”

Kubiyoni a next page domin jin labarin *Swt Fauzy*



โœ๐ŸปFaty Mmn Faty






๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

August, 2017



4โƒฃ4โƒฃ
Ahankali ya wuce ya nufi room nasa yama rasa wanne irin tunani zaiyi guda daya

Tun daga ranan ya shareta ya fita aharkarta shi atunaninsa zatazo ta basa haquri

Amma har sukayi 5days ahaka itama bata kulashi kamar yadda bai kulata

Abincima sai dai ta tura asayo mata

Papa kuwa abin ya masa yawa wai suna yana da mata amma babu abu daya dayake amfanuwa dashi ata bangarenta

Dan abinda yake samunma yanzu baisamu tunda sun kancake

Gajiya yayi yaje yasameta ya lallaba ta suka shirya

2weeks later
Yanzu hutun daya dauka awajen aiki ya qare hakan yasa juhaina ta bude sabon babin walawanta

Sassafe kafin papa ya tafi aiki munnir yake fita amma yana fita zata kirashi awaya ya dawo

Ta back door yake shiga wajenta yadda bawanda yake sanin shigarsa

Kullum suna shan shagalinsu da munnir hakan yasa yanzu ko papa bako yaushe yake samun biyan buqatarsa

Dan taringa masa hanya2 kenan aa daga tace batajin dadi sai tace bacci takeji

Idan ya matsa mata sai tace toh bata cikin mood din wannan abin

Gashi yanzu tamaidashi kamar ATM mashen sabida kullum acikin ya bata kudi take

Ga yawon tsiya da koyaushe sai dai ta dauki motarta ta shiga gari

Sau da dama haka zai dawo bai sameta ba

Yau dama tun bai fita ba yamata kashedin kada ta fita ko ina idan yadawo office zasuje gida sugaida daddy baiji daddy ba

Bayan ya dawo suka shirya sukaje basu jima ba ta dameshi da sutafi sabida yadda bata samu fuska awajen momcy ba haka aunty niima bata sake mata ba

Bayan sun tafi aunty niima ta dibi momcy tace momcy wlh matar papa ashe bayarinya bace yanzu naqare mata kallo da kyau

Cikin takaici momcy tace wannan ai idan bata girme masa ba toh saidai suzo saanni dan bai isah ya girmetaba

Aunty niima tace wai ya labarin fauziyya ne kam nakai 3days banyi waya dasuba

Momcy lfyrta qalau dazunma munyi waya da mabarukha tacemun tatafi makaranta

Aunty niima tace Allah sarki Allah ya bata miji nagari yarinya mai haquri

Momcy tace insha Allahu Allah zai canza mata da mutumin kirki

Haka sukayita hiransu suna jajanta abinda ya wuce

*****
Juhaina ce tsaye gaban papa ta riqe qugu ranta abace

Fiska a tsuke tace wai Alamin maeke damunka ne dannace kabani kudi shikenan sai kafaramun kididdiga kuma kana dashi bawai baka dashiba

Shima cikin fada yace ai banace bazan bakiba but i just want to know mezakiyi da kudinne ke kullum cikin abaki kudi kuma banga me kikeyi dasuba

Ahasale tace idan bazaka bani bane kawai kafadamum bawai kana wani kwana ba

Kallonta yayi dakyau sannan yace toh bazan bayarba ki kwata

Ok is that what u said tace dashi tana wani turo qirji

Yeah haka nace kin wani tsareni kamar wani danki kina turomun tsumma

Kutt qirjinawa ne tsumma ta fada cike da bacin rai

Adaqile yace toh meye acikin ido banda ruwa ni bani hanya kiga ina da abinyi

Naqi nabaka hanyan marar mutunchi kawai kuma ahakan kake kwantar da kwadayinka ba

Ya tsina fiska yayi yace eh arashin uwa ba

Nan sukayi tsiya tsiya kamar zasu daki junansu

Da kyar yasamu ya shige dakinsa ya kulle dan shakkar juhaina yake kuma ya tabbata idan ya daketa zata iya ramawa shiyasa bayi attempting dukanta

Kwanaki na tafiya, watanni sun shude

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya tsakanin papa da juhaina

Zaman lfy da kwanciyar hankali sun qauracem papa kullum yana yawon wajen cin abinci kuma itama dole ya kawo mata nata inba haka ba bayi da kwanciyar hankali

Kudi kuwa ko yaso ko yaqi dolensa ya bata

Abunda yafi daminsa yanzu yawo da ta qara couse akai yakuma rasa inda take zuwa tunda bata da yan uwa bauchi amma kusan kullum bata yini agida

Munnir kuwa yanzu yayi sabuwar budurwa

Dazaran juhaina ta bashi kudi ita yaje zuwa ya kashewa shiyasa kullum acikin tambayarta kudi yake

Time to time kuwa yana zuwa kd yayi two weeks harma fiye da haka

Yanzu haka mota juhaina tamasa alqawarin zata canza masa

Itama can wajen yawonta tayi sabon kwarto shiyasa yanzu bata damu da mumnir ba

Ita yanzu hanyar da zata samu ta koreshi take nema shiyasa takeson tacanza masa mota ta lallaba shi ya koma kd

Wasa gaske yanzu aurensu ya doshi shekara amma shiru ko batan wata bata tabayiba sabida kwayoyin hana daukar ciki datakesha

Dan bata shirya haihuwa yanzuba acewarta zata tsufa da wuri kuma ma ita bata shaawar yara dan wai takura garesu

Ya zuwa yanzu dik wadda yake tare da papa zai fahimci akwai abinda ke daminsa kawai dai bai fito ya fada bane

Amma acikin zuciyarsa yafara danasanin auren juhaina tunda bai qareshi d komaiba

*****
Aunty mabarukha nagani tsaye ajikin mota da alamu fita zatayi unguwa sai dai kamar jiran wani abu take

Fauziyyah ce ta fito cikin shiga ta alfarma wadda sai danayi da gaske naganeta

Taqara haske taqara girma

Wata arabian gown ce pusher pink wacce ta matuqar shan adon duwarwatsu masu kyallin gaske

Ta rolling veil din rigan akanta hannunta riqe da wata waya mai dan banzan kyau

Cikin sauri ta qaraso wajen aunty
Tana cewa am sorry aunty nabarki kina jirana

Aunty tayi murmushi tace no badai kin gamaba muje bazama mujima ba zamu dawo sabida kada su daddy sudawo daga islamiyya

Ok ta fada tana shiga mota

Gidan wata qawar aunty sukaje suka karbo wasu kaya tadawo daga dubai

Bayan sundawo yara ma sundawo daga islamiyya suna hira afalo

Aunty ta dubi fauziyyah tace Fauziyyah inaga tinda yanzu kina SS2 kawai kizana SSCE inyaso bazaki fasa zuwa school ba

Idan paper yayi kyau sai munemi admission kawai

Fauziyyah tace toh Allah ya kaimu

Aunty tace inyaso idan anyi hutu bazuwa dambam sabida kisamu kiyi karatu sosai

Cikin ikon Allah fauziyyah tana cikin shekaranta na biyu da komawa makaranta ta zana SSCE

Kuma da ikon Allah papers nata sukayi kyau dan fauziyyah dagaske take karatu idan kuna magana da ita zaka dauka tagama university sabida yadda takware a turanci

Kuma tana daukar shawara da nasihar da aunty take mata akan karatu

Takan cemata kiqara maida hankali akan karatunki sabida kizama wani abu kema arayuwa kinga dai abinda namiji yamaki akan rashin karatu

Hakan yasa ita kuma tayi alwashin sai tayi karatu mai zurfi

Lokacin da paper suka fito dikkansu suka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login