Showing 33001 words to 36000 words out of 87071 words
kaya acikin sannan ta duba kitchen din falonta,wayam ba komai,sakowa downstairs tayi ta shiga kitchen da store ,rai bace ta fito suka nufi asibiti
Office din daddy ta shiga nan ta labarta masa komai cikin takaici tace Alamin yaci amanar yarinyannan ,bakomai banda shinkafa da mai da maggi kuma INA zaton tun garan bikinsu nema
Daddy yayi shiru yace balaifi ya kyauta muje wajenta kada ta farka ba kowa
Dakinda aka kaita suka shiga,basufi minti goma ba tafarka ,tana bude idanunta sai kuma ta fashe da kuka
Momcy tamatso kusa da ita tana shafa kanta,cikin lallashi tace kiyi shiru daughter gani nan kusa dake ba abinda zai sameki
Asabe mai aikin momcy ce tashigo,da basket na abinci da flask ahannunta, ajiyewa tayi tana tambayar ya mai jikin
Momcy tace dasauqi ,kikoma gida saimun dawo kawai inaga nan zamu kwana
Tace toh Allah ya sauwaqa sannan ta tafi
Tea mai kauri momcy ta hada sannan tace daughter muje kiyi brush kiyi wanka saiki sha ko
Ba musu ta tashi,saida ta kaita har toilet sannan ta a fito ta barta
Tana fitowa ta bata kaya taje tacanza, bayan tacanza kayan tafito zama tayi a bakin gado tayi shiru
Daddy ya ce ya jikin,ahankali tace dasauqi
Miqo mata tea momcy tayi amma maimako takarba sai tafashe da kuka
Rarrashin duniya sunyi amma taqiyin shiru, cikin lallami daddy yace mekikeso daugther nah fadamun amma kibar kuka kinji
Cikin kuka tace nikam wajen Abba da Mama zanje
Daddy yace toh kiyi shiru zan kira maki Abba awaya amma fa sai kinyi shiru kuma kinsha tea kinci abinci kin yarda
Cikin sauri tace na yadda
Daddy yashafa kanta yace good girl
Momcy ta matso tafara bata tea aiko nan da nan tashanye tass dan yamata dad'i, rabon data sha mai dad'i haka ai harta manta
Plate momcy ta dauka ta zuba mata fried rice wadda tasha kayan lambu da papper chicken
Nan tahauci hannu baka hannu kwarya,daddy juyawa kawai yayi dan takaici ace kamar fauziyyah dan tasamu abinci takeci kamar almajira
Momcy ma haka shiru kawai tayi amma baqin ciki ne fal ranta
Tass tacinye ta kora juice mai sanyi, haba sai wani natsuwa yaxo mata,har wani lumshe idanu tayi tanajin wani natsuwa ajikinta
Daddy ne ya kira Abba awaya bayan sungaisa yace masa ga fauziyya zasuyi magana, Abba yace lfy dai ko
Daddy yace lfy ba lfy ba itance bata da lfy amma dasauqima shine take rigima wai sai dai akawota gida shine nakira taji muryarka ko hankalinta zai kwanta
Ok toh bani ita, tana karban wayar tace ina yini Abba
Lfy lau mama na ya jikin dai,
Tace dasauqi,yace to kuma sai rigima kice sai kinzo gida
Cikin shagwaba tace ai inason ganinku ne
Abba yace toh ai basai kinzoba gobe insha Allahu zamuzo mudubaki
Cikin jin dadi tace dagaske Abba
Yace insha Allah ga mama kugaisa
Nanma cikin murna suka gaisa da mama , mama tace harda khairy zamuxo dan tazomun hutu
Cikin doki tace Allah ya kawoku lfy
Mama tace amin sannan sukayi sallama
Daddy yayi murmushi yace rigima ta qare ko
Sunkuyar da kanta tayi sai taji kunya kuma
Daddy yace momcy inaga muwuce gida kawai tunda tasami sauqi
Momcy tace to bakomai nan tafara hada kayayyakin su
Daddy ne ya dubi fauziyyah cikin kulawa yace daugther na zaki bimu ko zaki koma gida
Dasauri tace aa zanbiku
Nan yadada tabbstarwa lalle abunda papa yayiwa yarinyan nan bakadanba ne tunda har take gudun gidansa
Driver ya kira yazo ya saka musu kayansu a mota sannan suka wuce gida
Ranan fauziyyah tayi kwanan natsuwa dan kafinta ta kwanta sai da momcy tasa aka dafa mata farfesun zabuwa wadda yaji kayan qamshi nn taci tayi nak dama fauziyyah badai son dadi ba๐
Momcy ce ta shigo dakin daddy cikin shirin bacci nan tasameshi yayi shiru
Zama tayi agefensa ta dafashi tace daddy lfy kuwa kayi shiru tunanin me kake
Saida ya sauqe numfashi sannan yace tunanin wanne irin hukunci zanma Alamin nake tunda baida mutunci har yana neman kashe yar mutane saboda son zuciya
Momcy tace nima tunanin danake kenan amma kabarni dashi fauziyyah kuma baxata koma ba harsai ya gane kurensa
Daddy yace hakan zaayi amma ahankali kitambayeta medame ya ke mata
Momcy tace badamuwa bari ta warware
Washegari su Abba sukaxo murna awajen fauziyya ba magana
Tare sukazo da khairy
Nan suka shiga dakinta inda momcy da su mama suna falon daddy
*****
Papa kuwa ganin sunqi sauraronsa gashi baifito da wayaba da yakira TJ yazo ya maidashi gida
Drivern daddy yasa ya maidashi gida
Washegari bayan yayi wanka yafara tunanin yaje ne ko kar yaje
Sai yace gara yaje kada yasake laifi amma bari ya kira TJ yazo suje
TJ ya kira awaya yace yaxo rakashi wani wajemana
Tj yace badamuwa in d next 30mins yana zuwa
Bada jimawaba sai gashi agidan papa yayi parking motarsa suka shigata ta papa suka fice
Suna tafe ahanya amma papa hankalinsa yana can tunanin ko momcy data saurareshi
Tj ne ya katse masa tunani yana cewa man kadakkoni rakiya bakafadamun inda zamujeba sannan kayi shiru baka ko magana lfy kam
Baibashi amsa ba saima yaga sun dau hanyar asibitin daddy
TJ yace man kamun bayani mana kuma gashi mundau hanyar asibiti
Papa yace kaidai bari wlh waccar yarinyan ce batada lfy kawai shikenan su momcy suka fara fushi dani suna nuna kamar nina saka mata rashin lfyr
TJ yace wai wace badai fauziyyah ba
Papa yace ita mana ni wlh yarinyannan tazamamun liability
TJ yace i know u very well friend anya kuwa ba wani abu kamata ba
Cikin fushi yace toh mezan mata nikuma
Tj yace Allah yasa dagaskene kake kuma indai da hannunka nima ba ruwana
Daidai da shigowarsu cikin asibiti nan ya hango wata nurse kiranta yayi ya tambayeta tace ai tunjiya suka tafi gida
Shiru yayi TJ yace ai saimuje gidan to
Nan suka wuce gida, Falon daddy suka fara shiga nan suka samu su Abba
Cikin girmamawa papa yagaida Abba da mama
Sannan ya gaida daddy da momcy haka dai suka amsa ba yabo ba fallasa sabida gabansu Abba nema yasa suka amsa
Wucewa cikin gida sukayi ganin ba kowa a falo yasa suka nufi dakin da yasan zai samu fauziyyah......
โ๐ปFaty Mmn Faty
[3:53PM, 8/19/2017] โช+234 803 341 6395โฌ: ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
3โฃ4โฃ
Bako sallama haka ya hankada qofar dakin ya shige ciki
TJ ne dake bayansa yayi sallama
Khairy dake zaune afalo tana danna wayarta tadago tana amsa sallamar
TJ ko yana ganin khairy yagane ta da faraa yace manyan bakine haka
Itama da faraarta tace sannu da zuwa dan taganesa
Amutunce ta gaidasu, TJ yace ya maijiki
Dasauqi ta amsa ,yace Allah ya qara sauqi tace amin
Ina fauziyyah Tj ya tambaya
Tace tana bacci amma barin tasota
Cikin sauri papa yace aa kibarta kawai sai anan yayi magana tun shigowarsa
Samun waje TJ yayi ya zauna dan shifa ya kyasa baran yau saiyaga taqara masa girma da kyau
Amma kuma bansan sunan malamarba yafada yana kallon khairy
Murmushi tayi cikin kunya tace khairy
Yace waw nice name khairy ya maimaita
Papa da haushi ya kasheshi yace oya man muje idan ta tashi madawo yafadi hakan dan sutafi
TJ yace ok muje amma malama khairy kozan sami no wayarki dan muringa gaisawa
Shiru tadanyi , qasa da murya yayi yace ko zaamun rowa ne
Tace aa sannan ta bashi
Godia nake sosai yafada sannan ya fice lokacin papa har yakai qofa
Suna fita papa yace kaidai Allah ya shiryaka mai zakayi da no wayar wannan yarinyar
TJ yace abinda kake da taka yarinyar dan ubanka
Papa yace lalle nayarda kanka aduhu yake kuma bakasan me duniya take cikiba
TJ cikin rashin fahimta yace toh wayar mun dakai mana
Baikuma cewa komaiba sai da suka shiga mota ya dago tab dinsa yace kallo nan
Karba yayi adakile yace wannan mai idon yan chines dinfa?wace ce ita harda samun matsayin hawa wallpaper
Papa yace buu, dan iska marar mutunci aifa nasan kai dan adawane shiyasa ban shafa maka ba amma tunda kafito fili da rashin mutuncinka to matar da zan aura ce kuma kada ka gwada gigin aibatata
TJ da ya daskare yanajin papa yace man me kake fada aure akan wani dalili
Yes aure ko haram ne ko kamanta ni mijin mace hudu ne
TJ yace nasani but inasonjin dalilinka na neman aure
Cikin rashin damuwa yace sabida nasamu test dita kuma ta dace da kalar matar da nakeso
Jinjina kai yayi yace ah lalle Alamin yakamata ka farka idan bacci kake
Amma mezakayi da wannan yarinyar wlh gara ka natsu ka rungumi matarka yafimaka,ni har ina maka murna nadauka komai ya wuce kundaidaita kanku sai ka tsiro da wani zance kuma haba
Papa yace to ubana barin qarqare maka sabida banason dogon magana
Kasan Allah wannan auren babu fashi idan bazakasa albarka ba just chup(kawai kayi shiru)
TJ yafahimci wanda yayi nisa baijin kira sai yace hakane toh Allah ya sanya albarka yasa ayi damu
Papa yace ahaa yanzun naji magana tunda kabi hanya next week tare zamuje
TJ yace a ina take da zama?
Yace sunanta Juhaina kuma a kd take da zama
Nan suka wuce gidasu TJ suna tattunawa ahanya
Cikin sati biyu TJ yagama shigarda kansa awajen khairy kuma yasamu karbuwa awajenta
Dan yafada mata bada wasa yakeba zai turo iyayensa
Amma taqi amincewa sabida karatunta
Yace indai maganar karatune ya amince taci gaba agidansa
Cikin qanqane lokaci ya samu soyayyar ta dan TJ badai iya zanceba kuma yagaji da gararamba da mata sabida haka yaga gara ya rufawama kansa asiri yayi aure gashi agidama sun dameshi har mmansa tana cewa zata samo masa mata inhar bazai natsu ya fidda mata ba
Hakan yasa dayaga khairy ta masa baxaiyi wasa ba gara kawai ya lallaba ya aureta
*****
Wasawa watan fauziyyah 1 agidan momcy harta maida kibanta ta murmure sabida kula na musamman datake samu daga wajen momcy da daddy
Kuma har yau ba labarin komarta gidan papa,sabida haryanzu papa bai samun fuska awajensu daddy danko gaisuwarsa basa amsawa
Idanma zuwa gidan yayi haka zai qaraci zamansa ya tafi bamai cemasa cikanka
Tin abin baidamunsa har yafara daminsa,ga gidan yamasa shiru idan yadawo office sai dai ya wuce wani wajen dan ya debe masa kewa
Yauma kamar kullum ya taso office gida ya dawo amma sam sai yaji bai shaawar zama acikin gidan danko bakomai wannanar villager tana debe masa kewa ko masifan da walaqancin daya ke mata ma amma yau ba wanda zaima
Cikin sauri yayi wanka ya shirya ya nufi gidan momcy dan ya basu haquri cos ya gaji da shareshi da suke akan abinda baima san dalili ba
Cikin saa kuwa yasamesu dik afalon momcy suna ta hira harda fauziyyah
Tana ganinsa ta miqe zata bar wajen ,daddy yace da ita ina zuwa daugther na
Tace zan shiga dakine
Daddy yace aa muna hiranmu ba inda zakije dawo kiyi xamanki
Cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna
Shima qarasowa yayi ya zauna kusa da momcy yace ina yini momcy
Yitayi kamar batajisaba,ganin bazata amsa ba yasa ya juya wajen daddy shima haka bai amsaba
Nanfa yaji zuciyarsa tana masa zafi
Cikin damuwa yace wai mena makune kukemun irin wannan punishment din, baku kulani baku amsa koda gaisuwata akan abinda bansan dalili ba
Momcyne ta harziqo tace au bakamasan mekayiba lalle dasauranka toh kaje rananda kasan laifinka sai ka dawo
Cikin fushi daddy yace lalle Alamin dasauranka yanzu dik abinda ka aikta bkasani ba wlh ka kiyayi duniya kabita ahankali
Ka cuci yarinya ka zalunceta dik kace bakasan laifinka ba toh kashiga taitayinka kuma wlh kaguji sakayyah ranan da zata....
Kuyi manage da wannan
โ๐ปFaty Mmn faty๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
3โฃ5โฃ
Kamaka dan wlh dik wadda ya dau hakkin wani Allah bazai barshiba
Amma kai ko ajikinka sabida bakasan wannan ba
Momcy tace kuma duk abinda ka aikata kaje kanka kayiwa bamuba tunda ka nuna bamu isa dakai ba
Cikin tsukewar fuska yace wane irin baku isa dani ba kuma ,dan ransa ya soma baci agaban yarinya qarama zasu ajiyeshi suna masa shouting abanza
Daddy yace to inba ka nuna mana cewar bamu isa dakai ba taya zaka ajiye matarka cikin yunwa wanda abanza da wofi na shaye2nka kake kashe kudi fiye da misali
Au cewa tayi ina barinta da yunwa yayi maganar fiskarsa a murtuqe alamun bacin rai
Momcy tace qaniyanka nace qaniyanka dake bamu muka gani da idanunba ko wlh papa ka kiyayeni zanci mutuncinka akan maganar nan dama na zuba maka idanu ne inga gudun ruwanka
Cikin fushi shima yace dama akan wannan munafukan yarinyan tafada maku qarya d gaskiya yasa ko gaisuwata baku amsawa, dama nasan kunfi sonta akan ni shiyasa akan ta akemun abunda aka dama
Bayan antauyemun haqqina an hadani da ita na haqura ina zaune da ita hakan baiyiba sai kuma anxo anacewa nayi laifi
Daddy ne ya taso akansa yace kai har ka isa ka ajiyemu kana fadan magana san ranka
Sabida ka kafi karfin kayi laifi ka amsa laifinka ko toh kayi kadan to
ta inda yake shiga ba tanan yake fita nan ya wankeshi tass
Ganin dagaske ran daddy ya baci yasa ya sassauta murya sa
Yace toh yanzu me kukeso nayi muku
Momcy tace ka amsa laifinka kuma ka gyara gaba dan bazamu lamunci tozarciba, yanzu idan iyayen yarinyannan sukaji wani irin kallo zasu mana
Danma Fauziyyah yar albarka ce bata taba fada masu halinda take cikiba
Sake qasa da murya yayi yace toh naji nayi laifi kuma bazan sakeba kuyi haquri Allah ya huci zuciyarku
Daddy yace nadai fadamaka da gigin wasa kada ka kuma mafarkin maimaita abinda kayi
Yana fadin haka ya miqe ya wuce side nasa rai bace
Fauziyyah kuwa tunda suka fara magana take kuka
Momcy tace kiyi shiru daugther share hawayenki bamai cimaki mutunci mu kyalesa tashi kije kiyi alwala ankusa kiran sallah
Tana tashi momcy ta dubi papa tace son wannan yazama na qarshe kada ka kuma gangancin yin abinda ka aikata kaji nafada maka tunda aure ba hauka bane
Naji shine binda ya fada ya miqe yace nawuce gida
Allah ya kiyaye tace dashi kamun itama ta wuce dakinta ta kuma qudira azuciyarta fauziyyah bazata komaba har sai ranan da yazo da kansa yace ta koma
*1month later*
Papa nazaune a office yana duba xray da akayima wata yarinya a cinyanyanta,watanni uku kenan da yin accident dinta ta karye amma kashin yaqi hadewa shine aka turota wajen Dr Alamin
Wayarsa ce ta fara rurin neman agaji
Tsaki yayi kamar bazai dagaba dan yana aiki amma sai ya daure ya jawo wayar
Ganin sunan mai kiran yasa ya ajiye file din hannunsa ya picking call din
Hello yane toh shine abinda yafada
Daga dayan bangaren akace normal fa ya aiki
Yace aiki ba dadi wlh namagaji ga wani case da aka turomun mtss yaja wani guntun tsaki
TJ yace eyyer sowwie shaanin aikine niyau tun 1 na gudu cos bama da wani aiki shiyasa
Yanzun muka gama magana d popsy nace bara nafara maka albishir kafin muhadu
Cikin kulawa yace inajinka mutumin
Saida yayi wata dariya sannan yace next week fa su popsy zasujemun dambam tambayan aure
Papa yace waw what a great news nayi murna sosai abokina dole nazo gida idan nataso office amma kuma natausaya maka zubewar girmanka
TJ yace toh nagode sai dai kafin nawa ya zube nakane yafara zubewa tunda kaika fara
Papa yace hhh dakenan aini yanzu free nake tunda nasamu su momcy suka riqeta awajensu tunda tayi rashin lfy ni yanzu ai banada matsala
TJ yace kai wlh mutumina bakada kyau dama ashe bata dawo ba tun wancan lokacin toh wlh gara kaje kayi qaramar murya abaka matarka yafi maka
Papa yace wucenan wlh tayi ta zamanta acan har qarshen rayuwarta danni this week ms kd zanje nafada ma queen zanturo dan aure nake buqataryi nan da 3months masu zuwa kafin wannan stomach pain din yamun illah
TJ ya sheqe da dariya yace kaidai kajama kanka tunda da matarka kake daurama kanka ciwo
Kai haba god forbid nahada jiki da wannan villager kuma mai zansamu kawai saina shigo bayan magrib
TJ yace Allahu yahdika abonkina sai kashigo din
Nan sukayi sallama inda TJ yake jiyema abokinsa kokarin barin damarsa dayake shirin aikatawa
Ranan saturday papa ya shirya ya tafi kd wajen sarauniyarsa
Kamar kullum haka suka sha hirar soyayyarsu nan yake fada mata zai turo iyayensa so ya tagani
Murna wajen juhaina baa magana amma sai ta boye tace bakomai ta amince
Yace toh idan ya koma dik yanda yayi dasu daddy zai sanar mata sai tafadama dad dinta ya basu ranan zuwa
Washegari ya dawo bayan ya huta yamma lis yayi wankansa ya chaka ado cikin blue jins da red shirt sun masa kyau sosai
Qafarsa sanye da red bufalinos
Motarsa camry LE ya shiga kalar navy blue ya nufi gida
Falon daddy ya wuce nan ya samu momcy sunashan fruit ita da daddy suna hiransu abin shaawa
Zama yayi ya gaidasu sannan yasa hannu ya dauki grabes guda daya yasa abakinsa
Shiru yayi sai yayi kamar zaiyi magana saiya fasa
Momcy tana lura dashi sai tayi wani murmushi atunaninta yanason tambayar abashi fauziyyah ne kuma yakasa fada
Daddy ma ashe yana lura dashi dubansa yayi da kyau sannan yace yadai babana bakin kannan kamar akwai magana amma kayi shiru
Dan murmushi yayi yace umm daddy wajenka nazo
Daddy yace toh lfy dai ko
Sai da ya dan sosa kansa yace umm lfy lau daddy dama sai kuma yayi shiru
Uhum go on inajinka daddy yace dashi
Dama daddy akwai yarinyar da muka daidaita da ita ne shine nakeson ajemun tambayar aurenta
Cikin sauri momcy ta dubeshi dan maganar yazo mata abazata kuma bata taba tunaniba
Daddy ma haka yaji maganar watairi shiru yayi kawai yana kallonsa cos he is totatly speechless dan yarasa ma mai zaice masa nan take yaji wani irin baqin ciki ya lullubeshi
Dubansa kawai yake cikin takaichi kafin.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
[6:13AM, 8/19/2017] โช+234 705 319 5189โฌ: ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
3โฃ6โฃ
Cikin takaici yace Alamin kana cikin hankalinka kuwa?
Kodai kwakwalwar ka ta tab'u ne?
Momcy tace wanne irin ya tab'u da hankalinsa sarai sai cin mutunci dayakeso ya mana
Daddy yace ok, toh kabud'e kunnenka da kyau kajini idan har nina haifeka ban aminceba ban kuma yarda ba da wannan magana
Idan kuma kaqi toh saidai kanemi wasu iyayen su shige maka gaba kuma bani ba kai that's all
Nan da nan fiskansa ta canza damuwa qarara ya bayyana bude baki yayi zaiyi magana cikin sauri daddy yace i don't want to hear anything from u kawai katashi katafi tunda ba arziqine ya kawoka ba sha3 wadda bai san meke masa ciwoba haryanzun
Rai bace ya mike ya fito motarsa ya fada ya nufi gida ranan kwana yayi cikin damuwa sabida haka ya kashe wayoyinsa baki 1 dan baisan mezaicema juhaina ba idan sukayi waya
*****
Papa yana fita momcy ta dubi daddy tace lalle papa