Showing 51001 words to 54000 words out of 87071 words
naji dadin yadda ka yadda da shawarina da haka harya kwantar masa da hankali kafin yamasa sallama ya wuce
Fauziyyah kuwa cikin qunan rai bayan takashe wayar ta nufi dakinta dan aduniya ta tsani abinda zai tuno mata da papa baran tasashi a idanunta
Washe gari da safe papa baiko tashiba ta wuce hospital abinta sai 3 kafin ta dawo gida
Bayan tayi sallah taci abinci sannan ta tsantsara kwalliya sosai
Wajen qarfe biyar saiga wayar Brr. Nabil kan cewar ya iso fa
Mayafinta ta dauka sannan ta fice
Wani murmushi tasake sabida yadda yamatuqar birgeta
Yana jingine jikin motarsa fara tass , sanye yake cikin wani danyen boyel mai kyau da tsada farare sol wanda sin matuqar amsanshi
Fularsa ta dace da kayan jikinsa haka takalnan qafarsa farare sol, hannunsa daure da agogon azurfa sai kyalli yake
Haka kurum taji ya matuqar birgeta dan harga Allah tana matuqar son mutum mai kamala da shiga ta mutunci
Ahankali cikin takunta mai natsuwa harta qaraso wajensa sallama tamasa cikin siririyar muryarta mai dadin sauraro
Lumshe idanunsa yayi ya bude ahankali dan ta tafi da dikkan tunaninsa kwalliyarta kyan fiskanta uwa uba dirinta sannan daddadan muryanta su suka qara narkar masa da zuciya
Waalaikumussalam barka da fitowa sarauniyar mata
Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta ahankaki tace ina yini
Lfy lau ya gida da aiki
Tace dik lfy lau ya naka
Yace well um gaskiya aikinmu ba dadi sai dai shukrah
Tace ayyah Allah ya taimaka, Amin ya amsa
Gyara tsayuwarsa yayi yana cewa yau gani ga gimbiyata dafatan zan samu mazauni acikin zuciyarki
Murmushi kawai tayi batace komaiba dan nauyinsa takeji sosai
Nan yasake gabatar mata da kansa ya kuma tabbatar mata ba dawasa yakeba kuma bashida mata dan baitaba aureba
Cikin gamsuwa da baya nansa tace bakomai amma yabata time tadanyi nazari
Yace badamuwa ya bata kwana biyu ammafa zai ringa kiranta suna gaisawa awaya tace badamuwa
Papa ne ya shigo gida kamar wadda akace ya duba gefensa kawai yaga fauziyyah da wani mutum atsaye sai faman kallonta yake yana murmushi kamar zai cinyeta
Nan take yaji qirjinsa ya buga wani kishi ya taso masa,jiyake kamar yaje shaqesa
Da kyar ya lallami zuciyarsa yayi parkin motarsa ya fito
Cikin gida ya wuce zuciyarsa adagule
Brr Nabil yace to madam nizan wuce naga kamarma na takureki kinyi shiru bakiyin ko magana
Dubansa tayi aa nibaka takurenba kawai dai nagajine yau awajen aiki
Yace eyyerh kishiga gida kihuta toh inyaso da daddre zankiraki
Tace toh nagode sosai Allah ya kiyaye hanya agaida gida
Insha Allahu zasuji bude mota yayi ya miqo mata wata shopping bag mai kyau baby pink colour yace ga wannan bayawa kisha swt
Aa nikam kabarshi nagode
Bata fiska yayi da sigan lallashi yace haba dai pls kikarba badanniba
Yadda ya tsareta da idanuwansa yasa tasa hannu biyu ta amsa tace nagode
Yawwa dear saikin jini yafada yana tada motar
Itakuma juyawa tayi ta nufi cikin gida tana bude qofar falo zata wuce taji anjawo veil nata hakan yasa tayi saurin juyowa
Papa kuwa tunda ya shigo ya gagara shiga ciki dan gaba daya jiyake kamar yaje shaqe wanda yaganshi yana tsaye da fauzinsa
Ganin papa ne yasa ta tsuke fuska tace lfy malam wani abu kake nema
Dubanta yayi da kyau cikin shan mur yace wayene waccan dana ganku tare
Kallon uku saura kwata ta watsa masa tace mene damuwarka da son sanin wayeshi kumama kaidin wayene dazaka tsareni kanamun wasu silly question
Cikin zafin zuciya yace au bakisan niba kikecewa ma
Tace eh banma taba ganinka tunda kadamu kaji wayeshi mijin dazan aurane ar u satisfied now
Yace lalle kinyaudari kanki barin fada maki bakida miji saini kuma ke matata tace sabida haka da kin daiba yaudarin kanki
Wani murmushi tayi na takaici tace Allah ya sauwaqa ni nazama matarka kuma ma kaga mundace dakai ne
Kadubi yanayin Brr. da shigarsa ta mutunci da kamala shine yadace da mijina ba kai wadda ko shigar mutunci baka iyaba dan shayeshaye kawai mazinaci Allah ya mun katangar qarfe tsakani na da kai kuma ni kadaina iqirarin matarka ce bansankaba bantaba saninkaba arayuwata tana fadin haka ta wucesa abinta .........
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
4โฃ9โฃ
Jikinsane yayi sanyi jin yadda take fadan munanan halayensa wadda ashe tana riqe dasu acikin ranta
Yadan jima kafin ya nufi side nasa cikin tunani kalakala
Zama yayi yana nazarin hanyar da zaibi ya wanke kansa awajen fauziyyah
Yanason ya shafe dik wani tunanin dake akansa na halayen banza ta daukeshi a mutumin kirki
Shiru yayi yana nazarin hanyar da zaibi kuma tabbas dole ya dauki shawaran da TJ yabasa idan yanason gane kanta tinda haryanzu tana riqe dashi da abinda ya mata acikin zuciyarta
Cikin sanyin jiki ya dauko wayarsa ya lalimo layin TJ yafa kira
Bayan sun gaisa papa yace TJ pls gobe irin 10am inason karakani wani waje mana
Ok Allah ya kaimu ya jikin dai
Dasauqi sosai thanks saimun hadun
Yana ajiye wayar yafara tunanin gara yafara shigan mutanen kirki wataqil fauziyyah tacanza tunaninta akansa tunda har take kwatance da wani
******
Itakuwa tana wucewa dakinta ta shige zuciyarta namata zafi cos tunawa da irin azaban da papa ya mata abaya
Allah ya qara ta furta afili dan momcy ta bata labarin matar papa
Tunani take wani irin mataki zata dauka akan katsalandan dayakeson ya mata arayuwarta
Shiru tayi kafin ta miqe ta shige toilet dan kanta harya mata nauyi gashi dama a gajiye take
Washegari bayan papa ya fita office ya dan duba patients nasa ten thirty ya fito ya nufi office din su TJ
A office ya sameshi yace ya zamuje ne ko kana da ayyuka mubari sai da yamma
TJ yace ina zamuje ne kam
Papa yace inda kake sayan kaya daka rakani saimuje wajen tailor naka dinki nakeso amun
TJ yace lalle nayarda abokina kacanza
Papa yace wlh jiya fauziyyah tafadamun abinda ranta yakeso nan yabasa labarin yadda sukayi
TJ yace ainafada maka ajiye fushi zakayi agefe har kasamu kanta dan wlh dama can kasanta yar zafin kaice baran yanzu data san ciwon kanta
Nan suka fito suka nufi shago inda TJ ke sayayya nan yasayi shaddodi da boyel kala ashirin sannan yasayi huluna masu kyau da tsadar gaske
Daganan suka wuce wajen tailor inda suka bashi dinkuna suka biya shi kudin express dan basason ya jima
Office ya maidashi akan sai da yamma zai shigo gida
Fauziyyah kuwa da wuri ta dawo gida yau da yamma ta shirya tsaf cikin wani sari sky blue wadda idan kaganta zaka rantse da Allah kace yar india ce
Nan tacema momcy zataje gidan khairy tinda tadawo batajeba
Momcy tace toh saikin dawo amma kada kiyi dare tinda ke kadaice zaki fita
Cikin ladabi tace toh momcy me abi ayaho (saina dawo)
Momcy tace Allah ya kiyaye hanya adawo lfy
Tana fita gidan khairy ta wuce cikin murna khairy ta tarbeta nan suka zauna afalo suka fara hiran yaushe gamo
TJ ne ya fito dan khairy ta fada masa zuwan fauziyyah
Zama yayi agefen khairy yana cewa hajiya fauziyyah ce agidanmu kodama bata gane mutane amma dai kekam nasan bata mantakiba yafada yana kallon khairy
Murmushi tayi dan tafahimci inda maganarsa ta dosa
Tace habaya Tijjani ni na isa nace banganekaba
Yace ah ranan agidan momcy kikayu kamar bakisanmuba
Tace kasan kazauna kusa da baqon fuska shiyasa kaima sai kabacemun amma yanzun bagashiba nazo har gidanka
Fauzy kenan kinzo dai wajen khairy
Tace dikkanku dai wajen ku nazo
Yace toh ya aiki da haquri damu
Tace aiki mungode Allah saita juta zancen da fadin banga mubeen bafa ko baccin yamma yake
Khairy tace aa baya nanma tun jiya yaje gidan hajiya (gidansu TJ)
Tace ayyah nan sukayi ta hiransu dik akan karatu nema dan khairyma tayi jamb admission take jira
Can wajen magriba fauziyyah tace bari ta tafi
TJ kuwa da tun dazu ya fita ashe suna tare da papa awaje
Nan sukayi sallama ta rakota har bakin mota tana cemata tagaida momcy itama zatazo
TJ kuwa ganin fauziyyah ta fito yasa yayi sallama ma papa ya wuce cikin gida dan dama yafadama papa tazo
Shima cikin sauri ya mufo inda take tana qoqarin bude mota ga hadari ya hadu baqiqirin ashe suna ciki basusan da hadarin ba
Assalamu alaikum yamata sallama juyowa tayi dan bata taba tunanin shibane tinda a iya tsawon zaman da sukayi har zuwa yau bai taba yimata sallama ba
Juyowa tayi dan ganin waye acikin gidan kuma dai ba muryar TJ ba kawai sai taga papa tsaye ya harde hannayensa aqirji
Tana ganin shine ta wani hade rai ta tsuke fiska tayi kamar bada ita yakeba ta bude motarta ta shige
Hannunsa yasaka ya riqe murfin motar yace pls ba danniba ba dan halina ba kiyi haquri kisaurareni
Dagoda manyan idanuwanta tayi ta watsa masa wani kallo batace masa qala ba tasa hannu ta jawo murfin motarta
Saurin janye hannunsa yayi da ta buge masa hannu
Key tayi ma motar zata wuce ta barshi
Shiru yayi yarasa abin ma zaice saiyaji sauqar yayyafa akansa hakan yasa ya juya ya shiga motarsa yabi bayanta
Suna fita ruwa ya kece kamar da bakin kwarya hakan yasa tafiya take ahankali shima yana bin bayanta har suka iso gida
Yana shigowa gate ko cikakken parking baiyiba ya fito ya nufi wajenta
Ita kuma tanayin parking tunani tafara ta fito acikin ruwanne ko ta zauna ya dan ragu
Kura idanu tayi tana ganin yadda ruwan ke sauka sai ta hango papa ya nufota
Cikin sauri ta bude qofar motar ta gwammaci ruwan ya jiqata than ace yazo wajenta
Aiko tana bude qofar motar ta zura qafarta kenan ya qaraso ganin haka yasa tajawo qofar zata kulle
Cikin azama ya saka hannu ya riqe, ganin haka yasa ta maida qafarta ciki batace masa qala ba
Shima baiyi magana ba sai ruwa dake dukansa haryafara diqa
Yakai 5mins ahaka yana tunanin mai zaima fauzy ta saurareshi kawai saiya durqusa awajen cikin ruwa ga kuma tasama ruwa na dukansa
Kallonsa kawai takeyi
Cikin murya mai rauni yace fauziyyah banida bakin da zan baki haquri akan abubuwan dana maki abaya wadda son zuciyata ya jani aikata hakan
Kuma nasani bacin ran abinda namaki ne yasa kike nuna baki sanniba
Amma kiyi haquri badan niba sabida Allah kiyafemun abinda namaki kozan samu salama arayuwata domin alhakinki yayita bibiyana kuma nagane kuskurena
Fauziyyah saima ta juyar da kanta dan bataji alamun zata sauraresa ba kuma ita dama matsa mata yayi ta wuce abinta dan batajin zata iya yafe masa abinda yamata
Ganin bata tankashi ba saima juyarda kanta datayi sake qasa da murya yayi kaman zaiyi kuka yace kefa musulma ce na roqeqi kiyafemun sabida Allah badan niba
Yadda ya marairaice murya saitaji tausayinsa ya kamata amma data tuna irin walaqancin daya mata abaya duka zagi azabtarwa sai taji wani sabon tsanarsa
Jakarta ta jawo afusace ta hankada murfin motar ta wuce tagefensa tayi cikin gida da gudu tana shiga falo wani kuka ya kubce mata direct dakinta ta wuce tana zubda hawaye
Papa kuwa yadda ta barshi awajen yakai minti goma baiko motsa ba yarasa wacce hanya zaibi ya samu yafiyarta wasu hawaye masu zafi yaji suna zuba akan fuskarsa
Kuma hakan datayi ko kadan baiji haushintaba sabida yasan abinda yamata bana kadan bane
Tashi yayi ahankali ya nufi cikin gida yana shiga shima ya wuce dakinsa cikin qunan rai ya dauko sigari ya kunna amma sam ko zuqa daya kasawa yayi haka ya kashe sabida alqawarin da yayima zuciyarsa yabar shan komai
Momcy da daddy suna tsaye jikin window suna kallon dik abinda sukeyi har suka shiga cikin gida
Momcy ta juyo tace daddy kaga papa ko tun bayauba nafahimci taketakensa kawai kallonsa nake naga iyaka gudun ruwansa
Daddy yayi murmushi yace aini tun rananda yafara ganinta nafahimci inda ya dosa sabida yadda lokaci daya ya birkice nan yafada mata yadda sukayi dashi
Momcy tace zaici qaniyarsa ai dan kuwa akwai wadda fauziyyah takeso har jiyama yazo da yamma
Daddy yace good haka nakeso Allah ya daidaita su shikuma zaigane kurensa
*****
Tana shiga daki ta kwanta akan gado tai kuka harta gode Allah kuma tarasa dalilin kukanta
TJ ne ya kirasa dan yaji yadda suka qare cikin damuwa ya zayyanema sa yadda sukayi yace TJ i dont know what to do nayi iyaka qoqarina amma ko saurarana batayi pls TJ help me out
TJ yayi shiru yace shikenan zansan abinyi amma kaci gaba da addua dakuma lallaminta harta amince
Suna gama waya TJ yasamu khairy ya fada mata halin da ake ciki ya roqeta taje gidan momcy gobe ta taushi fauziyyah
Da yamma washegari bayan fauziyyah ta taso aiki sukayi waya da khairy TJ ya kawota
Saida suka shiga daki bayan sun gaisa da momcy nan khairy tafara bawa fauziyyah baki akan ta haura tayafewa papa
Fauziyyah tace dake bake akaciwa mutunciba ko dole mijinki ya dauko yakawo mana saboda abokinsa
Khairy tace wlh ko kadan nibadan haka bane kefa musulmace kuma kada kimanta Allah ma muna masa laifi kuma muroqi yafiyarsa ya yafe mana
Kiyi haquri komai ya wuce wlh Dr yayi danasanin abinda yamaki kuma tunda harya baki haquri saiki hakura kodan albarkacin su daddy
Shiru tayi tana tuna irin walaqancin daya mata sai hawaye
Nan khairy taita lallashinta tace kimanta abinda yafaru abaya matuqar kina tunawa to bazaki taba haquraba
Tabbas kowa yasan abinda papa yamaki bai kyautaba amma ai yaga sakayyah nishawara nabakk ba doleba amma kiyi tunani akai
Fauziyyah tace nagode khairy Allah ya bar zumunci kuma insha Allahu komai ya wuce amma nance kifadama mijinki ba
Khairy tace oh miye laifin Abban mubeen wlh har kullum shi yana bayanki fa
Ya tsina fiska tayi tace tunda abokin ya Alamin ne shiyasa baruwana daku ai
Khairy ta sheqe da dariya tace toh amana afuwa
Dariya sukayi gaba dayansu sai bayan magriba sannan tamata sallama ta tafi.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
5โฃ0โฃ
Aranan bayan tafiyan khairy taita tunani takuma gamsu da shawarin da khairy ta bata kodansu daddy ma ya cancanci ta yafe masa kuma kodan tasamu yarabu da ita zata furta masa kalmar yafiya
Tindaga ranan suka shiga wasan boye, dik hanyar datasan zai hada ta da papa ta kaurace masa
Papa kuwa dik yadda yasan zai hadu da ita yanayi amma abin ya faskara
Har sati biyu rabonda su hadu, a hospital kuwa baiyi gigin zuwa wajenta ba dan kada ta yankwanasa acikin mutane gashi kowa yana ganin girmansa
Amma ya qudiri aniyar kota halin qaqa sai yayi magana da ita sabida haka yau da wuri ya shirya saida ya daidaici lokacin fitanta sannan ya fito
Cikin saa kuwa yasamu momcy da daddy ma dik suna break fast sabida daddy zaifita shima
Assalamu alaikum ya masu sallama yana ajiye jakar system nasa akan kujera a falo
Dik tsayawa kallonsa sukayi
Fauziyyah data debo abinci zata kai bakinta sai ta daga idanunta ta kalloshi itama abin mamaki ya bata
Yau sanye yake da wata dakakkiyar shadda army green tasha aiki mai tsadar gaske
Hularsa kalan kayansa ga wani agogon azurfa dagani ba tambaya kasan kudinsa dayawa
Abinka da farin mutum sai yafito kwarjininsa ya qaru akanna nada dan kayan baqaramun karbansa sukayiba
Abinda ya basu mamaki shine rabonsa da saka manyan kaya haka tun bikinsa da juhaina wadda shine na biyu daya taba saka jumper arayuwarsa
Amma kuwa saiya karbeshi sosai ya fito masa da kamalarsa na cikakken mutum
Qarasowa dinning din yayi yana cewa mornimg daddy morning momcy
Momcy tayi murmushi ganin sauyin da take gani awajen danta tace morning son har anfito yau da wuri haka
Umm inada wani aiki shiyasa na fito da wuri
Daddy yace Dr yaukuma aure zakaje daurowane ba katin gayyata
Murmushi yayi yana sosa keyarsa yace haba daddy kawai dan nasaka saiya zama aure zanyi
Daddy yace ah toh nasani tunda baswa kakeyiba saida dalili
Murmushi yayi yace aa kam kawai nayi shaawar sawane
Daddy yace ko kaifa amma mutum kullum cikin qananun kaya dik jiki atakure amma nasan yau kafi jinka very compotable haina(koba haka ba)
Hakane daddy ya fada yana daukan fork dan shima abincin zaici
Fauziyyah kuwa da tunda ta kallesa sau daya bata qara bin takansa ba bata kuma cemasa kala ba saima ajiye cokalinta tayi ta miqe zata bar wajen
Momcy tace badai kin qoshiba
Cikin shagwaba tace naqoshi momcy zan wuce office
Daddy natafi saina dawo
Momcy tace toh Allah ya tsare hanya daddy ma yamata addua adawo lfy sannan ta fice
Papa kuwa harta fice kallonta yake sabida komai nata birgesa yake baran ya kwan biyu baiganta ba
Haka muryarta baqaramun dadi take masa ba koda masifa take muryarta dadi takeyi baran yanzu dayaji yadda tayi magana ashagwabe sai yaji taqara birgesa
Zama yayi ya break nasa hankali kwance koba komai ganinta da yayi yasami natsuwa
Yau aiki ya riqe masa wuta sosai gashi ranan saturday mai zuwa zaayi bikin sabon asibitin da suka bude mai suna *NAMSA MEDICAL CENTER*
Tinda ya dawo suna tare da daddy har suka fita masallaci tare
Ranan saturday aka bude sabon asibiti hadi da walima
Manyan mutane sun hallarta sosai sannan abin ya qayatar abin birgewa
Da yamma momcy ta shirya walimanta acikin gida inda itama ta gayyaci yan uwa da abokan arziqi
Fauziyyah kuwa tinda aunty mabarukha tazo suna tare har aunty niima tana mata tsiya
Papa kuwa tinda ya dawo yana kwance adakinsa dan yagaji sosai tashi yayi ya wanka ya shirya cikin wani danyan boyel ash colour wanda yamatuqar amsan fatar jikinsa ya kafa hulan nan kamar wani ango
Har ya juya zai fita sai yaje jikin window ya daga curtain dan yagani kozai samu ya fice dan tun daxu yakejin hayaniyar mutane
Kamar wasa ya hangi fauziyyah tasha ado da kwalliyah cikin wani matetial maroon colur dinkin doguwar riga
Ta kafa dauri tayi kyau sosai
Tana tahowa kallonta yake yaga inda ta nufa saiyaga ta shige lambu ta qofar baya inda ake shiga bayin fulawa aiko cikin sauri ya fito ya nufi lambu shikuma ya shiga tacikin falo
Can ya hango ta zaune akan kujera da waya akunnenta
Itakuma wayarta da aka kira yasata shigowa lambun
Qarasowa yayi inda take zaune yaja kujeran gefenta ya zauna
Dagowa tayi ta kallesa sai tayi kamar bata gansaba taci gaba da wayanta ita da Barr.Nabeel
Daure zuciyarsa kawai yayi yanajin yadda take fadan kalaman soyayyah dikda baisan itada wayeba amma yana tunani itada wanda yataba ganinsu tarennan ne
Takai tsawon minti goma tana waya sannan tayi sallama tana sauqe wayar akunnenta ta miqe zata bar wajen
Cikin sauri ya riqo hannunta juyowa tayi afusace ta wurgesa da wani matsiyacin kallo
Saketa yayi da sauri wanda abu biyu yasa yayi saurin sakemata hannun
Nafarko wani