Showing 54001 words to 57000 words out of 87071 words

Chapter 19 - Budurwar Kauye Hausa Novel

07 Oct 2024

13123

danbanzan shorck dayaji kamar wadda wuta ta jashi na biyu wani kallo data watsa masa

Fiska atsuke tace malam wayabaka izinin riqemun hannu

Atausashe yace am sorry pls badagangan bane

Juyawa tayi zata wuce yayi saurin cewa pls Fauziyyah kisaurareni mana tunda nazo wajenki kinsan da magana nazo

Ko kulashi batayiba ta wuce abinta

shan gabanta yayi hakan yasa dole ta tsaya

Pls fauziyyah nasan cewa namaki laifi amma mutum idan yagane kuskure ya roqi yafiya aisai ayafe masa

Kifadi abinda kikeso namaki danki yafemun

Shiru tayi tana sauraronsa yadda yake bata haquri kamar zaiyi kuka tabbas ya Alamin ya sauya fiye da tunaninta

Roqo yake magiya yake haka ya durqusa awajen

Wani iri taji aranta tana tunanin yadda mutum ke sabawa Allah yaroqeshi gafara ya kuma gafarta masa asheko inhakne dole ta yafe masa

Cikin sanyin murya tace ya isa haka ya Alamin yawuce har abada Allah ya yafemu gaba daya amma dan Allah na roqeka daga wannan kada ka kuma shiga harkata koda magana bana buqatar yahadamu

Wani zufane ya yanko masa yace ashe ko inhakane baki haquraba kada kimanta kefa yar uwatace nidan uwankine

Tace yau kenan kasan da wannan yafiyakam nayafemaka har zuciyata kawai alaqa dakaine bana buqata tana fadin haka ta wuce abinta

Jiki asanyaye ya tashi ya wuce dakinsa yaji dadin yadda ta yafe masa amma yadda ta furta wai bata qaunar alaqa dashi shiya damesa gashi riqe hannunta da yayi shiya tuno masa wasu lokuta daya samu kansa acikin zamansu nabaya

Fitan dabaiyiba kenan ya kwanta jikinsa amace.....


*Alhamdulillah anan zandakata sai ALLAH ya kaimu ya nuna mana bayan sallah lafiya sannan mucigaba*

*Inayima dikkannin Al'umman musulman duniya fata da addu'ar yin sallah lafiya*

*Allah yasa muyi hidiman sallah lfy cikin kwanciyar hankali Ameen*



โœ๐ŸปFaty Mmn Faty






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

*Alhamdulillah Taqabalallahu minna wa minkum, dafatan munyi sallah lfy Allah ya maimaita mana, EID-EL KHABIR MUBARAKH*

5โƒฃ1โƒฃ
Soyayyah mai karfice ta shiga tsakanin Barr. Nabil da Fauziyyah

Soyayyah mai tsafta suke gudanarwa atsakaninsu

Kamar wasa son Brr. Nabil ya shiga zuciyar Fauziyyah sabida kyawawan halayensa da son addininsa da kuma yanda yake nuna mata zallar kauna da baya gajiyawa da dik irin abinda take masa na halin ko inkula

Ayanzu ta amince da aurensa kuma tayi naam dahakan har zuciyarta

Afannin Barr. Nabil shima yayi farin cikin amincewarta
Inda yanzu har gidansu sun san yana nemanta

Ummansa tayi farin ciki sosai sabida bata da burin daya wuce ganin dannata yayi aure

Kusan kullum sai yazo gida sunsha hira abinsu dan momcy da daddy ma sunsan da zamansa haryazo ya gaidasu kuma sun amince dashi dan sun yaba da natsuwarsa

Wani lokaci yakanzo asibiti ya sameta sabida yanda yake qaunarta dik lokacinda yaji yana son ganinta saiya taho abinsa

Dik abinda kefaruwa papa yana sane kawai ba yadda ya iyane kuma abinna daminsa kawai baya da mafita ne

Dik lokacin dayayi niyyar yimata magana idan ya tuna kalmar datace wai bata buqatar yin alaqa dashi sai yaji zuciyarsa ta masa zafi

Yauma kamar kullum Brr. Yazo sun hira kasancewar saturday ne dik suna gida

Tun zuwansa papa yake tsaye jikin window yana kallonsu yana jin wani zogi acikin zuciyarsa dan ahar kullum son fauziyyah qaruwa yake axuciyarsa

Yakuma yi niyyar dik abinda zai faru saidai ya faru amma yagaji da wannan walaqancin da cin fuskar da take masa sabida zuciyarsa ta aminta kawai dagangan take masa haka

Itakuwa batamasan yana yiba dan baya gabanta baran tamasa abu da gangan

Yana nan tsaye yanajin zuciyarsa kamar tafashe dan baqin cikin yadda yahango su suna ta dariya abinsu basa da matsalar komai

Tinda yahango Brr. Zai tafi ya fito ya tsaya aqofar falo ya harde hannuwansa aqirji yana jiran isowanta

Kamar wadda akace Brr. Ya juyo aiko ya hangi papa fiskannan ba annuri

Duban fauziyyah yayi yace my life nikam wancan yayan nakin haka yake bai magana ma mutane ne

Cikin ko inkula tace me kagani

Yace sau uku muna haduwa ina masa sallama amma ko ya kulani last zuwana hospital wajenkima mun hadu zan fita shikuma zai shigo ina daga masa hannu amma yayi kamar bai ganniba

Tabe baki tayi tace next time kada kasake kulasa ka rabu dashi kawai

Yazakice haka baicin dan uwankine yafada yana kallonta

Tace to halinsa ne haka idan baiga dama ba kozaka kwana kana masa idan baiga dama ba bazai kulaka ba

Jinjina kai yayi azuciyarsa yace amma ko baida hali afili kuma yace Allah ya kyauta nizan wuce sai munyi waya

Tace toh Allah ya kiyayae hanya agaida umma dasu sis raudah

Toh zasuje sannan ya tafi

Aiko tana nufowa cikin gida tinkafin ta qaraso papa ya taho ganin haka yasa ta kauce ta wucesa

Fauziyyah Fauziyyah Fauziyyah yake kiran sunanta amma ko ta amsa baran ta tsaya

Pls kisaurareni mana ya ina maki magana zaki maidani dan iska

Har takai qofar falo tasa hannu zata bude dan bata da niyyar amsashi

Cikin zafin nama yasa hannu ya fincikota baya

Aiko nan tayo baya kamar zata fadi sabida da iyaka qarfinsa ya janyota dan ransa yagama baci

Cikin sauri ya tarota ta fado akan chest nasa

Wani yarr gaba dayansu sukaji lokaci guda wadda hkan yasa papa sauqe wata wahalalliyar ajiyar zuciya hadi da lumshe idanu

Wani kasalane ya sauqo mata jin yadda ya maqale hannunsa ya zagaye waist nata

Kome ta tuna cikin sauri tasa hannu biyu da iyaka qarfinta ta turesa

Amma kuma takasa barin wajen sabida yadda qafafunta suka mata nauyi

Cikin dakewar murya tace meyasa bazaka rabu dani nasha iska ba abaya kace yafiyata kake buqata kuma na yafe maka to yanzu kuma what else kake buqata ta qarashe maganar cikin fada

Shima da fada fada yafara magana dik da irin yanayin dayake ciki amma dake ta tabomasa indake masa kaikayi yace

Nagaji da irin azabtar dani da zuciyata da kike yi nagaji da ganin walanqancin da kike mun agabana kina tsayawa da wani da wani noo wlh kadana kuma ganinki da wani dan iska agidannan ko awani waje

Da mamaki take kallonsa kawai yadda ya haqiqance yana masifa kamar zai daketa

Cikin jin haushi tace toh miye damuwarka kuma miye hadinka dani dazakazo kanamun wasu magana marasa maana da dadin sauraro

Oh maganan tawace marar maana ya tambayi kansa wani haushi ne yasake kamasa kallonta yake ido cikin ido yace becouse meh tumse pyarr kartahoo( sabida inasonki)

Wani wawan kallo take binsa dashi tagagara cewa komai sai idanu kawai take binsa dashi cos she is totaly speechless

Ahankali bakinta ya furta pyarr(so)

Yess hah kahona pyarr hai(eh inasonki)

Girgiza kanta tayi cikin wani qunan rai dan ji take kamar ya watsa mata dafi

Tace kayi gaggawar fadin istigfari

sabo nayi yafada yana kallonta

Tace aiya wuce saboma inka manta na tuna maka

Kaikuwa mai zakayi da yar qauye qazama wawiya jaka yarinya qarama wadda batada abin shaawa baran na marmari

Wani zufane ya fara tsatsafo masa ta ko ina jin yadda take jero abinda ya dinga fada mata abaya wato bata manta ba

Gagara magana kawai yayi dan baya da tacewa bai kuma san ta ina zai fara ba

Tsabar bacin rai idanunta sunyi qanana da kakkausan murya tace wlh ka cuceni kuma baa taba fadamun baqar magana irin wadda kafadamun ayanzuba wai kana sona bakaji kunyar fadin haka ba

Nace bakaji kunya ba toh koda maza sun qare kaikam nayafe akai kaya masauqi

Sai anan yayi magana yace dik abinda zakifadamun kifada matuqar zaki huce all i know is i luv u with all my hrt

Tace nikuma i hate u n i really hate u ta zuga masa wani wawan tsaki ta wuce tace kana wasting mun time da alama bakada abinyi

Tana wucewa shikuma ya koma da baya ya nufi lambu cikin damuwa kozai samu sauqi da zogim da zuciyarsa takemasa

Tin daga ranan yake binta kullum cikin roqo da ban baki yake akan tasaurareshi amma sam baya samun fiskanta abin duniya yamata zafi yarasa madafa baran taka maimai

Ya rame ya fada sabida ko abinci bai iya ci damuwarsa fauziyyah ta aminta dashi ganin bashida mafita yasa ya yanke shawaran zuwa wajen daddy dik abinda zaayi ayi kawai shidai adawo masa da matarsa....

โœ๐ŸปFaty Mmn Faty




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017



5โƒฃ2โƒฃ
Kwanansa biyu yana shawarin taya zai tinkari su daddy baicin abinda ya faru abaya

Cikin kwanaki biyun nan damuwarsa ta tsananta sosai

Har momcy ta gaza haquri sunayin dinner tace baba na lfyrka kuwa two days dinnan

Dagoda kansa yayi hadi da qaqalo murmushin dole yace mene kika gani swt momcy

Naga dik kacanza irin u look so sad haka kamar bakada walwala

Sake murmushi yayi yace babu komai sai dai stress din aiki kawai

Toh Allah ya taimaka tafada amma badan ta yarda da abinda yace ba

Washegari bayan sallan ishai ya yanke shawarin zuwa wajen daddy

Bayan yayi sallah gami da adduoi akan Allah ya dorasa akan daddy dan yasan idan daddy ya amince zance ya qare

Falon daddy ya nufa zuciyarsa na dukan uku2 da sallama ya shigo yasami waje ya zauna

Daddy ne kadai yana kishingide yana kallon tashar CNN

Dago kansa yayi yana amsa sallamar
Zama yayi yayi shiru yana tunanin ta ina zai soma magana

Daddy ne ya katse masa tunani da fadin yadai Alamin kaxo tayani hira ne

Dan sosa kansa yayi yace um eh daddy naxo taya ka hirane sannan akwai maganar danazo da ita

Ok inajinka ya akayi
Cikin dakewar murya yace umm dama daddy alfarma nazo nema wajenka

Uhum go on name fa daddy yafada yana kallonsa

Cikin sanyin murya yafara magana daddy dan Allah badan niba kataimakamun yadda Allah ya taimakeka kadawomun da matata wlh nayi nadama kuma nagane kuskurena bazan sake aikata makamacin abinda yafaru abaya ba

Kallonsa daddy yake sosai yace Alamin banfahimcekaba explain to me further

Cikin murya mai rauni yace daddy nayi nayi iyaka qoqarina fauziyyah taqi ta saurareni wlh daddy inasonta zan iyah shiga wani hali matuqar fauziyyah ta gujemun

Dan Allah kasa baki daddy kataimakeni tunda tanajin maganarka yaqara maganar kamar zaiyi kuka

Daddy yace kafazomun damagana adunkule kafito straigh forward kayi magana mana

Toh daddy gaskiya matata fauziyyah nakeson adawomun da ita

Wani kallo daddy yake binsa dashi kamun ya tashi daga kishingidar dayake ya zauna dakyau yana dubansa

Yakai minti biyu kafin yace Alamin kana da hankali kuwa kasan me kake fadi kuwa tohma ta ina tazama matarka ko kamanta da ba aure atsakaninku

Daidai shogowar momcy kenan

Zama tayi agefen daddy tace lfy kuwa meya faru daddy?

Daddy yace wai cewa yake adawo masa da matarsa

Cikin takaici momcy ta dubesa tace ashe bakada hankali bansaniba

Ta ina kataba ganin anmaida aure akan saki uku eye?

Nadauka kayi hankali ashe dasaurnka haryanzu daka samu Allah ya taimakeka ya rabaka da raqai dakuma lfyrka shine zaka tono wani abinda baxai yiyuba

Daddy yace baki fahimcesa ba ashe ai gara yace amayar masa da matar da yayima saki uku akan abinda yazo dashi amma gaki gashi ya maki bayani da bakinsa

Duban papa tayi cikin rashin fahimta tace nifa kunasani aduhu wai meke faruwane

Kansa tsaye yace matata fauziyyah nakeso adawomun da ita

What? Shine abinda momcy tafada tana kallonsa kafin tace toh gaka ga daddy wannan ba magana ta bace

Daddy ya kallesa da kyau yace kasaurareni da kyau kaji abinda zanfada maka

Abinda nakeso dakai kada nasakejin wannan maganar abakinka koda kuwa awasane

Daddy dan ....

Daga masa hannu yayi yace banason jin wata magana daga bakinka ingar akan shirmen banzan nanne

Juyawa yayi wajen momcy yace pls momcy kitaimaka mun ki....


Itama katsesa tayi tace papa tashi kafita saida safe dan banason damuwa kajiko

Daddy yace oyah tashi kabani waje stupid kawai

Jiki asabule ya miqe ya fito harjinsa yake kamar bashida nauyi tsabar yarasa tudun dafawa

Ranan haka ya kwana idonsa biyu cur tsabar damuwa da rashin madafa

Tunani iya tunani yayi amma yaga bayada mafita dole wajen daddy zai koma amma bari ya bari sai bayan kwana biyu

Cikin kwana biyun nan dik wanda yagansa yasan yana cikin damuwa matsanan ciya

Idan ya fita aiki acan zai wuni daya dawo ya shige side nasa sai dai sallah ke fito dashi ko cin abinci bai zuwa yadawo shiru abinsa iya da safe ya gaidasu kafin ya fita ko break bai tsayawayi

Bayan kwana uku yauma yasake dawowa wajen daddy


Daddy naganinsa ya bata fiska yace yadai kagama fishin da kake damune?

Girgiza kansa yayi yace wlh ko daya nibana fushi daku taya zanyi fushi daku kuma

Dan Allah daddy kasaurareni kataimakeni kamayar mun da matata kuma ko wanne irin sharadi ka shimfidamun na amince zanbi zanbi

Daddy yace kai banace banason sake jin wannar maganar ba

Idan har aure kake buqata ko a inane ka nemo zan shige maka gaba amma banda fauziyyah

Yarinya mai hankali da natsuwa ba irinkaba ai kaikam da ita kunyi hannun riga dan bata dace dakaiba baka dace da ita sabida haka kwarya tabi kwarya

Kuma aidai kana sane cewar aurenta ma ya kusa ko

Dam yaji gabansa ya buga

Yace yes aurenta ya kusa ko atunaninka zaa maimaita irin abinda ya wucene asake rabata da masoyinta na gaskiya abaka kaje ka wulaqan tata aidai ko kulya mutum ya ajiye zai kula da ita bare mutum dan adam bayan kagama azabtar da ita hakan bai makaba sannan kazo gabana kamata sakin walaqanci ka tozartani ko kana tsammanin na mantane wannan cin mutuncin dakamun haba haba cikin tsawa yace katshi kafita agabana kada kasa nayi abinda banyi niyyaba kafita nace

Durqusawa yayi yana hawaye ya riqe kafar daddy yana cewa nasan nayi kuskure kuma ban kyautawa kainaba daddy nayi danasanin abinda na aika ka taimakeni daddy kada karabani da fauziyyah wlh inasonta kuma itace rayuwata kada karabani da rayuwata

Daddy yace baka sotaba saida kaga tazama mutum ko kuma aikai kanisanta kanka da ita sabida haka kaje kasamo uwar mata ka aura wannan yarinyar ba saarka bace

Riqe daddy yayi yana kuka yana roqonsa amma daddy sam bai saurareshiba saima kwace qafarsa yayi ya wuce abinsa yabarshi durqushe awajen yana kuka .....



โœ๐ŸปFaty Mmn Faty




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

5โƒฃ3โƒฃ
Momcy da ta taho wajen daddy tinkafin taqaraso taji kamar alamun gunjin mutum na kuka

Cikin sauri ta qarasa hankali tashe bako sallama ta fado cikin falo

Turus tayi ganin papa durqushe yana kuka

Dasauri ta qarasa wajensa tana tambayarsa papa meya faru nace meya faru

Bai amsataba sai rungumeta da yayi yana kuka

Cikin tsanin tashin hankali dan batasan meke faruwa ba tace am asking u kya hua(ina tambayarka meke faruwa)

Da kyar ya iya furta momcy pls help me wlh inasonta inasonta bazan iya rayuwa ba ita ba kitaimakeni ki lallashi daddy yayi fushi dani yana magana yana kuka kamar qaramin yaro

Wani iri taji har cikin ranta kuma yadda taga papa ya gigice tabbas yanzu yanason fsuziyyah kuma so mai tsanani sai dai ba yadda zaiyi saidai yayi haquri tunda dama shiya sake damarsa tun farko

Wani irin tausayinsane ya kamata haka takejin kukansa har cikin ranta amma haka ta danne zuciyarta

Tace toh me kakeso namaka papa baicin what ever happens is all ur fault

Yace i know momcy nina janyo ma kaina kuma wlh nayi dana sanin kuma tun fauziyyah bata dawo nagantaba nake fama da matsanancin sonta bawai yanzune nafara sonta ba kiyi wani abu momcy

Ganin yadda ya birkice yaketa surutai yasa ta saka hannunta tana patting bayansa smoothly hadi da lallshi

Haba papa ya kana abu kamar qaramun yaro uum
Ya isa haka nan ka kwantar da hankalinka ko so kake wani ciwon ya kamaka

Look at ur self ya kacanza just in two days haba

Nidai kawai kitayani bama daddy haquri sannan hankalina ya kwanta

Naji amma saika kwantar da hankalinka tukunna

Shiru yayi ya kwantar da kansa akan cinyanta yana sauqe numfashi

Miqewa tayi tariqe hannunsa suka nufi side nasa

Fauziyyah dataji maganar momcy cikin firgici baicin tare suke zaune ta wuce wajen daddy ta barta hakan yasa tabi bayanta da sauri
Tana zuwa bakin qofa ta tsaya jin maganar dasukeyi akantane
Cikin damuwa itama ta fara hawaye kuma jin yadda alamu momcy zatabi bayan danta tunda gashi ta nuna damuwarta akansa

Wani iri taji har ranta yadda momcy ta dauketa tamkar yarda ta haifa acikinta amma ace tasanadinta ta janyo mata tashin hankali
Sai dai duk da haka batajin zata iya komawa gidan papa gara ta sanarma Brr. Ya turo kawai tinda dama ya matsanta mata itace take dan jan abin

Jin takun fitowansu yasa tayi saurin barin wajen ta nufi dakinta tana hawayen da batasan dalilin yinsa ba

Dakinsa sukaje tace maza jekayi wanka barinzo ko

Abinci ta kawo masa ta lallabashi yaci sosai sannan tace ya bari zuwa kwana biyu zata lallami daddy amma sai inhar ya kwantar da hankalinsa

Bayan kwana biyu da faruwan haka suna zaune da daddare dikkansu afalo daddy yace ma fauziyyah daugther dama inason sanar dake kifadama Nabeel ya turo iyayensa maganar aurenku amma kafinnan zanyi magana da Abba muji wacce rana ya dace asaka zuwannasu

Wani irin tsinkewar zuciya taji wadda batasan dalilin hakanba

Papa kuwa da kyar yasamu ya lalimo numfashinsa wadda yayi barazanar daukewa

Ahankali ta furta toh daddy

Momcy kuwa shiru tayi harga Allah tanason papa da fauziyyah tunda yagane kurensa amma kuma tunda ita fauziyyah bata sonsa bawani mafita ya haqura shine kawai
Saidai tana tunanin irin halinda dannata zai shiga kallonsa kawai take tana nazarin yanayin dayake ciki

Fauziyyah ma dakinta tawuce tafada gado tana kuka tabbas tasan tanason Brr. Amma kuma batajinsa aranta kamar yadda taso Yasir
Nan tasakejin tabbas tayin rashin masoyinda takeso har abada

Papa ma haka ya miqe ya nufi dakinsa ya sanya makulli ranan kwana yayi acikin wani yanayi marar dadi

Washegari kasancewar saturday yasa har yamma bai fitoba

Zazzabi mai zafine ya rufesa shiyasa ya wuni a kwance

Gashi daddy yahana momcy zuwa ta duba lfy bai fitoba

Sai da yamma tukun ya lallaba ya fito
Fita yayi ya nemo magani awani pharmacy dake kusa dasu

Bayan yadawo da kyar ya sha dan ruwan tea yasha maganin namma saida momcy ta matsa masa afalonta ya kwanta

Daddy ya shigo momcy tace yanzu zanshiga wajenka dama Alamin ne baida lfy

Cikin ko inkula yace Allah ya sauwaqa kicema fauziyyah tafada ma nabil ranan saturday suna iyah zuwa dazu munyi magana da Abba

Yana fadin haka ya juya

Nan papa yasake birkicewa zazzabi ciwon qirji momcy harta tsorata


Amma cikin ikon Allah washegari yadan samu sauqi dan yasha magani

Kullum cikin lissafa kwanaki yake har anci kwana uku
Tunani badare ba rana yakeyi ta ina zaisamu mafita

Yanzu hanya dayace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login