Showing 60001 words to 63000 words out of 87071 words

Chapter 21 - Budurwar Kauye Hausa Novel

07 Oct 2024

13109

katse sake kira yayi akaro na biyu sannan ya dauka

Hello man how far

Papa yace cool ya khairy n mubeen

All ar fine ya amarya

Wani murmushi yayi mai natsuwa kafin yace tana gida amma dai lfyrta lau

Kaikuma kana ina kenan at this tym

Ina sokoto road daxu nayi parking wlh daddy ya matsamun wai sai dai na qaura


Hhh Tj ya sheqe da dariya yace aikam daddy ya birgeni dan wlh nasan takurin fauziyyah zakanayi

Tsaki ya danyi yace aikaiba nasan iya abinda zakace kenan tokoma mene ne dai nikasamun no wayarta now now

TJ yace toh nikuma a ina zansamomaka kuma yanzu adaren nan

Tsuke fuska yayi kamar yana kallonsa yace banason iskancifa kawai inajira tinda komai saika maida shi wasa

Toh naji naji barin karba awajen madam saina turo maka shikenan

Eh shikenan thanks

Nyt saika ganito

Ok nyt yafada yana sauqe wayar amma bai ajiyeba jira kawai yake yaga message ya shigo

Aiko bada jimawaba saiga message cikin sauri ya bude ya dauko dayar wayarsa ya shigarda no din

Dialling no yafara saidai yaji user busy

Sake kira yayi nanma yaji user busy

Nanfa ransa ya fara baci todawa take waya awannan daren haka

Itakuwa fauziyyah Brr nabil ne ya kirata awaya harda kukansa akan maiyasa ta yaudaresa tasan ba aurensa datayiba gidan mijinta data koma

Daddy ya kirasa ya masa bayani akan yayi haquri shinefa ya shiga cikin damuwa zuciyarsa take ganin yaudaransa kawai fauziyyah take shiyasa bata daukar wayarsa

Dik iya bayani da rantsuwa data masa yaqi ya yarda sabida kishi ya rife masa idanu kawai gani yake dagangan tamasa haka

Shinefa suka dauki time suna magana har ya kira yaji busy

Ya kira yafi sau ashirin cikin saa yaji wayar ta shiga

Harta kusa katsewa sannan yaji ta dauka cikin sanyin murya tace pls ka amince dani wlh wannan auren sabida iyayena zanyi badan so ko wani abuba nifa kaine araina kuma kaina keso bayadda na iyane kawai na amince da auren ya Alamin

Itakuma tadauka Brr ne ya sake kiranta dake da wata no ya kirata shiyasa dataga no ne yanzuma saikawai tadauka shine tafara magana

Wani daci yaji maqoqoronsa ya masa jin yadda take jadda da bata sonsa kuma mawani take fadama haka

Lallai akwai aiki agabansa dole ya danne zuciyarsa haryasamu gurbi acikin zuciyarta

Jin yayi shiru yasa tace pls talk to me mana ka amince da maganata muyi rabuwar mutunci bakadaukeni mayaudariya ba

Cikin sanyin murya papa yace My Fauzy Alamin ne

Abazata taji maganar hakan yasa tayi shiru ta gagara magana

Sharewa yayi yace My Fauzy kina jina

Nanma shiru ba responde

Yace nasan kinajina meyasa bakiyi bacciba har yanzun while dasafe zaki fita aiki

Dama na kirane naji muryanki mai dadi mai sanyani natsuwa kuma gashi kinqi kimin magana amma da kika picking call nawa i appreciate it so ki kwanta kiyi bacci but do not forget kiyi addua kafin ki kwanta

Allah ya tashemu lfy kiyi bacci mai dadi n swt dreamz

Dik yadda yake maganar cikin wani salo mai matuqar dadin sauraro

Hakan yasa tabar dai wayar akunnenta tanajinsa bata kuma kasheba

Yana fadin haka ya zame wayar akunnensa ya kashe yana tunanin ta yadda zai samo hanyar dazai shawo kan fauziyyah dan tabbas yasan akwai ga garumin aiki agabansa

Itakuma jin ya katse wayar ta sauqe daga kunnenta hadi da jan tsakin dabatasan miye dalilin yinsa ba

Message ta rubutawa Brr ta tura masa sannan ta blocking layukansa kafin ta kwanta amma batayi bacciba tana tunanin abubuwa da dama

********
*Waikam ina juhaina ta bace ne???*

Tunda tasamu ya amince mata akan tashiga tacanza kaya amma kada ya sameta agidansa

Suna fita itama taja jikinta cikin wahala taje tahada abubuwanta masu amfani ta canza kaya kafin ta fito

Motatta ta shiga ta fito tana waigen inda zataga munnir sai tahangoshi kwance aqasa baya ko motsi agefen wani lungu bakowa kasancewar yanayi. Layinnasu da bayawan mutane

Fitowa tayi ta koma cikin gidan ta shiga dakinsa ta dauko jakar kayansa ta dawo da kyar tasamu tasaka masa kaya sannan ta koma ta ringa roqon mai gadi har ya amince yazo yasaka matashi a mota ta nufi asibiti dashi

Wani private hospital ta kaishi amma sukaki karbansa saida ta zube masu kudi masu yawa sannan suka amince suka dubashi

Nan itama ta kwana sai washegari ya farfado

Tana samun ya farfado tace dashi toh yanzu alaqansu ya qare tinda yamata sanadin aure kuma ta kawo shi asibitine dan bayida mai taimakonsa sabida haka ita yau zata tafi gida kada ya kuma tunanin yasanta arayuwa idan yaji sauqi yaje yadauki motarsa acan sannan idan yana buqata ya kwashe kayan dakinta yasayar ya san inda dare yamasa kada ya kuma nemanta

Tana fadin haka ta fice ta barshi yana kukan danasani ga jinya ga karaya ga babu haqora guda biyu


Itakuwa tasha taje tasamu fasinjan daya iya mota yajasu zuwa kaduna


Gida ta nufa tana shiga ta ringa kurma ihu dik su mom dinta suka rude gashi duk jikinta shatin duka ya faffashe

Dakyar tafada masu ai papane ya saketa yamata dan banzan duka

Mom dinta tace tabbas saitayi qaransa dan bai isa ya dakar mata ya abanzaba

Dad ne yace aa anemi iyayensa dai aji kanmagana

Nan juhaina tace ai agaban iyayensa yamata haka da saninsu

Mom tace kajiko saina daureshi dan ubansa ta inda take shiga batanan take fitaba

Dad yace indai hakane baiga amfanin wata sharia ba kawai abarsu da Allah su suka sani

Da kyar ya shawo kan mom ta amince inda juhaina taji dadin hakan dan kada asirinta ya tonu.....


โœ๐ŸปFaty Mmn Faty



๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017


5โƒฃ7โƒฃ
The following morning after ya tashi yayi subh prayer baikoma bacciba

Wajen seven ya shiga bathroom ya taking bath

Shirinsa yayi tsaf cikin wata sky blue half jumfer wadda tasha dinkin zirii

Kansa ba hula sai suman nan tayi lufluf which means tasha gyara sosai

Agogon gucci ya daura as usual then yasaka baqaqen half shoes nasa na zallar fata

Designers perfoms ya feshe jikinsa nan da nan ya karade ko ina da qamshi

Breif case nasa ya dauka da woyoyinsa ya fito hannunsa riqe da car key nasa

Babu wadda zai kallesa bai sake ba koda kuwa tare suke kwana daki daya dan papa yayi no lie

Yana fitowa ya tarar anwanke masa mota sai sheqi take

Maaikatansa sukazo one by one suka gaidasa sannan ya bama Abdu kudin Abincinsu yace idan yaqare yayi magana shi ya wuce office idan ya dawo zaije gida ya taho masa da motocinsa

Ya amsa cikin ladabi sannan ya masa adawo lfy

Motarsa ya shiga ya kunna Ac hadi da wani daddan music

Ahankali yake tafiya harya fice direct gidan daddy ya nufa cos he wanna see his darkan(heart beat)

Lokacin daya shiga bakowa afalo sai talatu mai aiki

Bayan sun gaisa yace ina masu gidan

Tace yanzu hajiya ta koma amma bada jimawa ba zasu fito karyawa tunda 8 tawuce

Zama yayi abinsa ya danna wayarsa

Momcy ce ta fito daga side din daddy ganin papa zaune yasa tace papa lfy kuwa kaxo early morning

Dago kansa yayi yana murmushi yace morning momcy

Morning dear baka ansamun tambayar danayi maka ba

Dan shagwabe fiska yayi yace haba momcy mutum da gidansu danyazo sai antambayesa kawai nayimissing naku a lot that's why naxo early morning naganku kafin na tafi office

Dariyama abin ya bata cos ta fahimci abinda yake nufi

Tabe baki tayi tace good saikataso kayi break toh

Yana tashi daddy na fitowa shima cikin mamaki yace Alamin qalau kuwa naganka sassafe

Lfy lau daddy nazoyin breakfast ne fa

Yace yayi kyau to muje

Saida ya gaidashi kafin ya haura dinning ya zauna a permanent seat nasa

Fauziyyah ce ta fito cikin shirinta yau takusa makara dan jiya batasamu bacci da wuri ba

Ganin papa yasa tadan hade rai shikuma sai wani mayetaccen kallo yakebinta dashi

Saida ta gaida daddy da momcy tukun tadanyi kasa da murya kamar dole tace morning ya Alamin hakanma dan su momcy na zaune ne yasa ta gaishesa

Da faraasa yace morning dear kesi ho tum(yaya kike)

Me tikke ta amsa masa(lfyna lau)

That's great ya fada sannan ya cigaba da cin abincinsa

Itama zama tayi tayi break nata kafin ta miqe ta masu daddy sallama wadda dama shi ya koma falo ya zauna

Tsulum papa ya miqe yace shima ya tafi idan ya biyo to idan kuma bai biyoba sai gobe

Suna fita ya nufi motar fauziyyah tana budewa ya shige gefenta ya zauna abinsa

Juyowa tayi tana kallonsa akufule tace yeh he kya karehe tum(meye haka kake aikatawa)

Dubanta yayi yace kyah(kamar yaya)

Tace taya zaka shigomun mota haka baicin kanaga fita zanyi


Oh sorry dear nima ai fitan zanyi shine nakeso kuragemun hanya


Tace pls kafitamun amotana

Yace eyyerh pls kiragemun hanya mana tinda office zani

Tace no i cant pls kafita if not gashi ta miqo masa key namotar tace nisai infita

Qarema hannunta kallo yake wadda yasha lallen rani

Yace aakam keda motarki daman tawance tasami problem amma tinda kinqi shikena

Duban jerin motocin sa takeyi amma yace baya da motar da zaifita tabe baki tayi tace shikenan kafin ta tada motar suka tafi

Ahanya ba yadda baiba kan tayi maganar amma sam taqi



Haka ya haqura ya kyaleta......


โœ๐ŸปFaty Mmn Faty







Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

*I dedicated this page to Rahima Aminu Azare (Ummu Afreen), thanks 4 ur prayers, luv n support, I really appreciate,Mmn Faty ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜*

5โƒฃ8โƒฃ
Har suka iso hospital kallonta kawai yake yana murmushi cos ta matuqar birgesa

D way take driving anatse shiyasake birgesa gashi ta tsuke dan qaramun cute bakinta

Saida tayi parking tana daukan jakarta sannan ya bude ya fita

Zagayowa yayi ta side nata ya sunkuyo sosai lokacin itama ta bude zata fita

Wani killer smile ya mata cikin wani soft voice yace mata shukhriya(nagode)

Yana fadin hka ya wuce abinsa baijira amsarta ba dan yasan abune mai wahala ta kulasa

Kallo ta bisa dashi kafin ta dauke idanunta ahankali

Azuciyarta tace jibesa kamar mutumin kirki baicin dik wata kalar iskanci babu wadda bai iyaba

Tsaki tayi kafin ta fice itama dan kada ta makara

Shikuna yau hankali kwance ya shiga office nasa koba komai yau ya jima kusa da pyarinsa(mosoyiyarsa)

Saida ya kusa tashi kafin ya kira Abdu yazo office ya samesa ya bashi key din motarsa akan yaje ya kawo masa

******
Kwanci tashi babu wuya awajen Allah kwanaki sun shude hakama satittika tareda watanni

Yanzu biki saura sati uku kacal duk wasu shirye shirye babu wadda baa gamaba

Kama daga kan gidan da zasu zauna su lefe komai anshirya masa sai sauran abinda baa raasa ba

Papa kuwa yafi kowa doki da murnan karatowan bikin sai dai haryanzun ya gagara gane kan amarya

Daidai da maganar fatan baki bata hadsu sai yazama dole

Bayadda baibi da itaba taxo suje gidanta tagani amma fir taqi yadda
Haka ya haqura saidai shirye shiryensa bai fasa ba dan biki zaayi na kece raini

Biki saura sati dasu wuce dambam acan zaayi hidimar biki sai bayan biki dasu dawo bh

Aunty mabarukha kuwa yau take hanya yaranta kuma sai saura two days biki zasuzo da babansu sabida exams dasuke a school

Acan dambam ma baa barsu abaya ba dan shiri sosai su Abba suke suma

Momcy kuwa tunba yauba tafara hidimar gyara yarta ta kuma surkarta

Ita dai fauziyyah dik abinda ake bai dametaba hasalima ma da zaa qara lokacin tanaso

Kullum tunaninta ko wanne irin zama dasuyi da ya Alamin

Dik da sosai tana ganin canji atare dashi amma dik da haka zuciyarta taqi aminta da shi sabida sanin halinsa boyayye datayi

Ita tasan kawai jikinta yakeso yadda kullum bai gajiya da fada mata da turo mata messages na soyayyar qarya

Tabarwa Allah zabin alkhairi kawai amma batajin zata yadda tasakeyin zaman qunci agidansa

Da daddare suna zaune afalo tare da aunty mabarukha suna ta hira harda aunty niima itama tazo masu sai anjima mijinta zaizo sutafi

Aunty mabarukha tace mata sis dubamun abinda na daura awuta mana kada ruwan ya qone sosai idan yayi kauri kawai kisauqeshi ya huce

Tace toh sannan ta miqe
Tana shiga kitchen papa nashigowa hangota da yayi saiko yayi saurin wucewa yabi bayanta

Tana sauqe tukunyar yana shigowa

Juyowa tayi taga wane ne ganin shine yasa ta dauke kanta ta kunna famfo tana wanke hannunta

Qarasowa yayi ya tsaya abayanta matsota yayi sosai hartana jin sauqar numfashinsa akan dokin wuyanta

Shiru tayi tanajin wani iri hakanan ajikinta

Murya qasaqasa yace meri darkan(my hrt beat)
Menayi ne kike guduna uumm

Shiru tayi batace komaiba

Sake maimaita mata yayi cikin wata iriyar murya mai kashe jiki yace yakamata ya zuwa yanzun kimfahimci kyakykyawar manufata gamedake

Wlh bantaba tunanin na aureki dan na walaqantaki ko wata manufa ta daban ba

Inason kisan cewar dik wani hali nawa da kika sani ada yanzun munyi hannun riga dashi

Idanma wannan kike tunani toh ki cireshi daga ranki

Jin tayi shiru ganan ruwa na zuba takasa qarisa wanke hannunta yasa ya qara samun courage dan yaga kamar magangannunsa sun shigeta kuma sunyi tasiri akanta

Sake matsota yayi har kirjinsa na gugan bayanta ya saka hannunsa biyu ya riqo nata yafara wanke mata hannayen dashi baiga wani abu ajikiba da harta tsaya wankewa

Santsin hannunta acikin ruwan shiya masa dadi har ya rajaa yana murzawa ahankali

Bakinsa ya kawo daidai kunnenta yana cewa idan kina tunanin wani abu nakeso ajikinki kinyi kuskure

Nafara sonkine tun kina yanda kike abaya tunkuma banganki ayanzuba

Sonki acikin jinina yake pls My Fauzy kibani dama na nuna maki irin kalan sonda nake maki na kuma wanke laifina na baya

Yana fadin haka ya kashe ruwan yace i luv u my pretty sannan ya juya ya fice

Nan ya barta kamar andasata dan gabadaya maganganunsa kemata yawo akwanyarta

Saidai dik da haka bataji wani canjin akan tsanar da tamasa ba

*****
Washegari da safe ya kira aunty mabarukha akan ta lallama masa fauziyyah da yamma zaizo su fita zata rakashi wani waje

Saida aunty ta wanasa kafin ta amince

Haka ta fadama fauziyyah ta shirya 4pm papa zaizo sufita

Batayima ta musu ba dan tana matuqar ganin girmnta

Haka badan ranta yasoba ta shirya cikin wata doguwar rigar material rainbow colour wacce ta matuqar qarbanta

Earing dogi tasaka blue colour sai bangles nata suma passion design ne combination colour

Saita yane kanta da blue veil madaidaici

Waya ya kirata yace pls ta fito yana mota yana jiranta

Takalmanta masu tsini tasaka suma blue colour saita riqe yar qaramar purse nata itama blue colour

Masha Allah nan tafito kamar asaceta agudu dan kyau

Tunda ta fito ya zuba mata idanu yana kallon takunta cikin natsuwa dan tamatuqar birgesa kuma kwalliyar tayimasa 100%

Saida takusa qarasowa ya fito ya bude mata motar

Tana isowa yace bismillah My preety

Shiga tayi ta zauna sannan ya rufe ya zagayo

Ko kallonsa bataiba baran ta gaidashi

Inayini rankishi dade yafada yana kallonta

Shiru tayi kamar bada ita yakeba

Marairaice murya yayi yace haba My Fauzy ko gaisuwan nawama bazaki amsaba

Sai anan ta juyo ta kallesa tace pls idan abinda yasa katakureni nafito kenan toh sai anjima tafada tana kokarin bude motar

Da sauri yace aa am sorry idan ranki ya baci daga haka baikuma cewa komaiba

Ahankali yake tafiya dan yanajin dadin yanayin yau sosai

Saida ya iso wani babban super market yayi parking awajen

Kallonta yayi yace mujeko n pls kidauki abinda kikeso kinji

Rai ahade tace bana buqatar komai

I know baki buqatar komai amma irin kinmin rakiyan nan aibai kamata kikoma empty hand ba

Tace toh bani buqata

Muje to yafada atare suka shiga inda yayima kansa shopping abinda ya kawosa sanna yacigaba jibga kayan ciyeciye da wasu abubuwan amfani na qamshi wannan na fauziyyah ne

Harta gaji tace nafa gaji

Yace ainagama muje sunzo daidai wajen teddy sai wata baby girl wadda shekatunta bazasu fice uku ba tazo tasha gabansu tanata dariya tana cewa daddy ganan teddyna

Daga bayansu sukaji ana cewa fauziyya stop there stop there

Jin an ambaci sunan fauziyyah yasa dik suka juya

Saidai wa fauziyyah zatagani mutuminda ko ta shekara dari rabonta dashi zata ganeshi dikda kuwa canzawar dataga yayi

Shima kallonta ya tsayayi yana tabbatarma kansa itace bawai dikda rabonsa da ita yayi shekaru amma kamanninta bazai bace masa cos her immage is in his heart

Qarasowa sukayi shida matar dake gefensa wata black beauty amma ita saita qarasa ta dauki babyn tana cewa oh My Fauzy meyasa bakijin magana kinason kinasani gudune eh

Kallon babyn papa ya kumayi jin ankirata da sunan dayafi qauna

Murmushi Fauziyyah tayi masa tace uncle yasir dama zansake ganinka arayuwa

Shima murmushi yayi yace Fatima

Papa ne ya juyo yana masa murmushi tare da miqa masa hannu jin yadda fauziyyah ta kira sunan saiya tuno masa da me wannan sunan

Gaisawa sukayi kamar sunsan juna

Bayan sungaisa da fauziyyah ya nuna mata matar dake riqe da baby yace this is my wife Jalila n my dauther Fauziyyah

Kallonsa tayi tace wannan babynkane kuma sunanta fauziyyah

Murmushi yayi sannan yace yeah

Gaisawa tayi da matarsa tana kuma mamakin yadda yasir baimanta da itaba tasan kobai fada mataba takwara ya mata

Ganin tadanyi shiru yasa yace wannan ne maigidannaki yafada yana nuna papa

Gyada masa kanta tayi tace eh nan suka sake gaisawa da papa sannan ya dauki little fauzy

Yace mata babyna kinason teddyne

Eh uncle tafada tana maqalesa yace ok zabi wadda kikeso insaya maki ko

Da fara arta ta dauki manya guda biyu yace sukadai kikeso

Tace eh uncle

Yana riqe da ita ya qarisa wajen biyan kudi katinsa ya bayar nan aka hadamusu kayayyakin

Yariqowa little fauzy nata ya dawo da ita wajen daddynta sannan sukayi sallama suka tafi

Haushin yasir ne ya kama papa ganin yadda mood din fauziyyah ya canza daga ganin yasir saikuma aside guda yanajin son babynsu inama su barmasa ita......

โœ๐Ÿป Faty Mmn Faty




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017



5โƒฃ9โƒฃ
Fitowa sukayi daya daga cikin masu daukan kaya na biye dasu har mota

Saida aka loda kayan a mota sannan ya zagayo side din datake tsaye ta jingina da jikin motar da alamun hankalinta yayi nisa awajen tunani

Bude mata qofar yayi kafin yace shall we
Saida yasake maimaitawa kafin ahankali ta matso ta shiga ya rufe

Zagayowa yayi ya zauna sannan yama motar key yafara tafiya yana tunanin yanayin data shiga one time
Zuciyarsa ce ta aminta kan ya tambayeta mene ne damuwarta

Juyowa kadan yayi ya kalleta kafin ya maida hankalinsa kan titi
Cikin sanyin murya yace My Fauzy kya hua(meke faruwa)naga mood naki ya canza

Shiru tayi kamar bada ita yake ba

Sake maimaita mata tambayar yayi yana cewa lokacin damuka fito ba haka yanayinki yake ba but lokaci guda kincanza kyiu(meyasa)
Pls My Fauzy ki amsamun mana wlh bani qaunar ganinki

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login