Showing 57001 words to 60000 words out of 87071 words
ta rage masa baibiba shine Abba
Kuma gaskiya yanajinjina taya zai kalleshi bayan abinda ya aikata abaya
S
ai dai kuma yaduba yaga baya da wani option gara yaje yasami Abba wataqil yadace acan tunda yasan Abba mutumin kirkine...
βπ»Faty Mmn Faty
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
5β£4β£
Shikadansa ya gama shawarinsa baikuma fada ma kowaba
Gari na wayewa sassafe asuban fari ya dauki hanyar dambam
Cikin ikon Allah qarfe tara ya shiga garin dambam
Gidan Abba ya nufa saidai zuciyarsa tana ta bugawa dan baisan yadda Abba zai karbi maganar ba shinko zai sauraresa ko zaimasa irin abinda daddy yamasa
Da haka harya qaraso qofar gidan yana isowa Abbah yana qoqarin fita
Parkin yayi cikin dauri ya fito dan harya shiga mota
Saida yazo har jikin motar sannan Abba ya ganesa dan yasha jumfer har qasa ga hula hakan yasa Abba baikawo shibane
Da faraarsa ya bude motar yana qoqarin fitowa cikin sauri papa ya tsugunna yana cewa sannu Abba
Aa tashi tashi zaka bata jikinka ai tashi muje cikin gida mana
Tare suka shiga side din Abba dan mama bata gari sunje biki jos
Harqasa ya duqa ya gaisheshi
Shima da faraa ya amsa yace amma dai agarin ka kwana ko
Cikin ladabi yace aa yanzu isowana
Ah lalle kayi sammako yasu daddy dasu hajiya
Dik lfynsu qalau ya amsa
Masha Allahu yayi kyau
Shiru ya danyi kafin yace dama wajenka nazo Abba
Abba ya gyara zama yace toh lfy daikam inasauraronka
Qasa da murya yayi yafara magana cikin nadama yace Abba tabbas nimai laifine awajenku kuma nasan nayi kuskure amma kuyafemun badan halina ba kuyi haquri...
Katseshi Abba yayi da cewa ya isa haka Alamin kaifa danane kum ni bakamun komaiba sabida haka komai ya wuce kuma naji dadin yadda naganka cikin kamala ubangiji Allah ya yafemu gaba daya
Cikin jin dadi yayita godia Abba yace bakomai ya wuce
Sannan yasake qasa da murya yace dama Abba nazo roqon alfarmace awajenka
Abba yace namefa Aminullah
Yace dama Abba fauziyyah ce nakeso tadawo dakinta shikuma daddy yaqi amincewa nan ya zayyane masa yadda sukayi da daddy
Abba dan Allah badan halina ba kutausayamun yanafadin haka yayi shiru dan jinsa yake kamar zaiyi kuka
Abba ya nisa ya dubesa cikin kulawa kafin yafara magana
Yace da darko sai ince Alhamdulillahi daka fahimci kuskurenka kuma naji dadin yadda kaxo kasameni kaitsaye tun abubuwa basu kwabe
Kuma gida bai qoshiba aibazaa bawa dawo ba
Amma alhji bai kyautamunba yana sane da kanason maida matarka ya hana sannan ya shigoda wata magana
Kuma shi wadda yake neman nata aibaasan halinsa ba
Tunda Allah yasa kazo kasanarmun halinda ake ciki to tazo gidan sauqi insha Allahu gobe zanzo bauchin muyi magana da Alhajin
Wani dadine marar misaltuwa yaji yana ratsashi ta ko ina
Sake risinawa yayi yana godia sosai
Abba yace dakaida fauziyyah dik daya kuke awajena sabida haka ka koma abinka kasa aranka fauziyyah matarka ce insha Allahu
Godia sosai haryasa kalmar dazaiyi amfani da ita tsabar murna
Haka yayima Abba sallama ya kamo hanya zuciyarsa wasai
Rabonsa dayaji farin ciki irinna yau harya manta ranan
Gabda laasar ya iso gida wanka yayi ya fito yaci abincinsa hankali kwance
Momcy dai tayi mamakin canzawarsa amma dai tayi shiru batace komaiba
Yana nan zaune afalo tafito ta wucesa tinda yaga fitanta awannan lokacin yasan wannan man dinne yazo ko ajikinsa saida yagadama sannan ya tashi ya dauko car key nasa da wayoyinsa yayi waje
Motarsa ya shiga saida yazo dafda su sannan ya sauqe glass ya nunasa da hannu yace hey kada kabari nadawo nasameka tareda matata kuma zaifi maka sauqi idan katafi kada kasake dawowa
Duban papa yayi da kyau yace matar ka kuma ta ina tazama matarka
Yace bani da tym inada wajen zuwa amma katambayeta ita zata amsa maka ai yana fadin haka ya daga glass din motarsa ya wuce abinsa
Fauziyyah kuwa abu biyu su suka dameta nafarko yadda ta boyema Brr cewar papa shine mijinta na farko sannan yadda papa yake iqirarin wai ita matarsa ce
Brr. Ya kalleta da kyau yace wane ne wannan awajenki
Ahankali tace yaya nane
Yace kada kimaidani bitacan mana inason kifadamun gaskiya miye alaqarki dashi dan najima da fahimtar akwai abinda kika boyemum game dashi
Nan idanunta sukayi raurau tace wlh ba abinda nake boye maka kawai dai banason tuna abinda yafaru abayane
Yace naji amma kada kifadamum shine mijin da kuka rabu
Murya na rawa tace shi shine
Wani baqin kishine ya taso masa cikin fada yace i see shiyasa ashe yakemum abinda ya gadama kekuma kikaqi sanar dani ashe dama tsakaninmu akwai yar boye
Tace bahaka bane
Yace toh ya ne inba haka ba kawai bakida abinda zaki fadamun
Haka taita bashi haquri dan ta lura ransa ya baci shima haka ya tafi yana tunani kalakala
Washegari Abba yazo inda suka zauna da daddy akan maganar su papa
Amma fir daddy yace baisan zancenba idan har papa aure yakeso ya nemo awani waje
Abba yace toh shikuma baiga dalilin da zaa hana papa fauziyyah ba
Nan dai suka ringa muhawara har Abba yayi nasaran shawo kan daddy amma da sharadin sai fauziyyah ta amince
Abba yace batun wannan yaron sai adakar su amma aini har raina ya baci ace taya zaka hana alamin fauziyyah
Daddy yace bawai hanashi nayiba kawai abinda ya aikatawa kansane
Abba yace aiyawuce Allah ya kiyaye nagaba
Abba yace toh shizai tafi amma yanason magana da fauziyyah
Bayan tazo Abba ya dubeta yace mama na ya aiki
Lfy lau Abba ya mama sai gobe zadu dawo tacemun ko
Yace eh sai gobe insha Allahu ai anyi biki kam kuma sunyi ziyra
Tace hakanekan
Abba yace mamana ya maganar yaronda yake zuwa wajennaki kinsanar masa ya turo dinne
Shiru tayi tana tunanin dama akan jiyane zata sanar masa saikuma yatafi cikin bacin rai hakan yasa bata fada masa ba
Abba yace baki amsamunba
Ahankali tace aa banfada masa ba tukunna
Abba yace Alhamdulillah dabaki fada masaba amma kisaurareni kiji abinda zanfada maki
Dafarko nahadaki aure da dan uwanki baason rankiba wadda zan iyacewa dole namaki
Toh yanzun lokaci yayi daya kamata ace kina da aure tunda dik abinda ake nema na rayuwar duniya kinsamu daidai gwargwado
Toh wannan karon bazance ga miji na zaba mikiba amma amatsayina na mahaifinki zanbaki shawara idan har ta miki
Batun maganar Alamin ason raina shine ki amince ki koma dakinki
Cikim sauri ta dago kanta tana kallon Abba
Abba yace bafa nace lallai bane aa shawarace kiduba kiga yanda iyayensa suka daukeki tamkar su suka haifeki
Sannan dik yadda suke tayaki kin Alamin kisani bayadda suka iyane tunda kema kin nuna bakyaso amma suna son dansu kuma sunason farin cikinsa
Kuma nima har zuciyata inasonki da alamin sabida haka kije kiyi tunani da kyau akan maganata
Kuma tunda mutum ya maka laifi ya kuna nemi gafara aisaika yafemasa
Fauziyyah dai nan take tafara hawaye
Abba yace aa nifa banace tilas bane inhar kinfison wancan din shikenan amma ni shawara nake baki kuma kije kiyi tunani mai zurfi
Tsabar kuka gagara magana tayi har Abba ya miqe yace zaitafi shikam
Dakyar ta iya cemasa Allah ya kiyaye hanya
Ranan kasa runtsawa tayi lalle maganar Abba gaskiyane kodan su daddy yakamata ta amince da ya Alamin saidai kuma bata sonsa
Wata zuciyar tace shima Brr. Aiba wani sonsa kikeba
Tunani kawai take taya zata koma zaman aure da ya Alamin tayi kuka har idanunta ya kumbura
Kwana biyu da zuwan Abba abubuwa sun dameta gashi Brr koya kirata awaya bata dauka dan batasan mezata cemasa ba
Shikuma yadauka bata huce bane tun abinda ya faru
Kwanan Abba hudu da zuwa tayanke shawaran amincewa da Alamin amma badan tana sonsa ba saidan farin cikin Abba dan tafahimci yanasonta da Alamin ya boyene sabida kawaici
Haka su daddy ma tasan kawaici kawai suke mata
Ranan tayi kukan rabuwa da Brr hartaji ba dadi
Waya ta kira Abba ta sanar masa ta amince ta zabi ya Alamin
Abba ya ringa samata albarka da mata adduoi sannan yace toh tasanar ma daddynsu shiba ruwansa kada daddy yace shiya tursasata
Suna zaune afalo da daddare tasamu momcy tace tafasa auren Brr. Ita ya alamin zata aura
Momcy tace aa fauziyyah kada kitauyema kanki haqqifa
Tace aa ta amince har zuciyarta
Tashi momcy tayi taje tasamu daddy da maganar
Yace ta kira masa fauziyyah tana fita papa ya shigo bada jimawba suka dawo tare
Bayan ta gaida daddy daddy yace yanzu mom dinku tazomun da wata magana inasonjinta daga bakin
Qasa tayi da kanta sannan tace haa daddy me tayyarki shaadi ya Alamin(hakane daddy na amince da auren ya Alamin)
Wani lamarine mai sanyi papa yaji yana shigarsa tindaga qafarsa kamar anjiqashi da ruwan qanqara
Idanu kawai ya zubawa fauziyyah yanajin wani sabon sonta har cikin ransa....
βπ»Faty Mmn Faty
πΎπΎπΎπΎπΎ?πΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
*Wannan shafin nakune kudanku masoya Budurwar Qauye, Mmn Faty tana godia kuma tana qaunarku adik inda kuke,wadanda banisamun damar mayar masu da reply na messages nasu suyi haquri banmanta dasu ba abinne dayawa amma nagode sosai Allahu ya bar qauna ππ*
5β£5β£
Wani farin cikine ya ziyarci daddy jin abinda fauziyyah tafada da bakinta
Murmushi yayi mai cike da annushuwa yace zonan yar gidan daddy matso kusa dani
Babu musu ta tashi tamatso kusa da qafafunsa ta zauna ta sunkuyar da kanta
Cikin murya mai taushi daddy yace daugther na kifadamun gaskiya dakanki kika amince zaki auri Alamin ko kuma Abbane ya tursasaki
Girgiza kanta tayi cikin natsuwa tace aa bashibane ba baima da masaniya akan hakan
Alhamdulillah Allahu ya hada kanku ya kuma kauda fitina
ALLAH ya maki albarka ya baki yara masu biyayya kamar yadda kika mana
Momcy tace amin ya Allah dan itama wani farin ciki takeji marar misaltuwa tana kuma jin son fauziyyah har ranta
Daddy yace tashi kije abinki Allah ya maki albarka
Asanyaye tace amin sannan ta miqe ta fice dakinta tana shiga tafada kan gado ta bude sabon shafin kuka
Daddy kuwa tana fita ya maida hankalinsa kan papa wadda shikuma yabada full attention nasa akan hanyar waje inda ta fice ya bita da kallo ya kuma gagara dauke idanunsa
Daddy yace toh nadawo kanka yafada yana kallonsa
Jin muryar daddy yasa ya juyo yana kallon daddy
Kasaurareni da kyau kaji abinda zanfada maka
Nafarko kagodewa Allah da mahaifin fauziyyah mutumin kirkine sannan itakuma yarinyace mai biyayya
Toh kagama bin kafa har kasamu burinka ya cika
Amma kasani bazan lamunci kwatankwacin abinda ya faru abaya ba
Matuqar kanason zama inuwa daya da ita saika sake halayenka tass
Cikin ladabi papa yace insha Allahu zankiyaye daddy
Daddy yace Allah yasa sannan tunda burinka ya cika saika tattara kakoma gidanka gobe dan bazaka zauna karinga takura mata ba
Ko ajikinsa yace shikenan daddy Allah ya kaimu
Daga haka ya musu saida safe ya fice zuciyarsa fari qal qal
Yana fitowa ya nufi dakin fauziyyah cikin saa kuwa qofar abude take
Falon shiru sai qaran AC gami da wani sansanyan qamshi wucewa yayi har cikin bedroom nata
Da sallama ya shiga kwance ya hangota tayi rubda ciki akan bed kuma bata amsashiba
Wani kasalane yaji ya sauqo masa ta dalilin abubuwa uku
Nafarko sanyi da qamshin daya doki hancinsa na biyu tsaftan dake tattare da dakin kamar kada ya fita haka yakeji
Na uku yanayin kwanciyar da tayi saiyaji kamar ya qarsa ya kwanta ajikinta dan saiyaji dik hankalinsa ya tashi
Gashi dama wata yaloluwar doguwar rigace ajikinta dazataje wajen daddyne ta daura hijab akai tana shigowa kuwa ta cire
Dik tabi jikinta ta manne sannan ta bayyana illahirin suran jikinta
Wani yawu ya hadiya yana godema Allah daya sanya fauziyyah zata zama mallakinsa
Itakuma tanajin motsin bude qofa da sautin muryarsa taji wani baqin ciki yasake kamata
Banza tayi dashi kamar batasan da shigowarsa ba
Ahankali ya tako har bakin gadon leqa fuskanta yayi nan yagane idanunta biyu kuma kuka mq takeyi dan ganan hawaye shabeshabe akan fiskanta
Nan take yaji ya damu gashi baisan dalilin kukan nata ba
Cikin murya mai tattare da natsuwa da kulawa ya kira sunanta My Fauzy
Wani dam taji zuciyarta ta buga sakamakon tuno mata da yasir da yayi dan shine kadai ke kiranta da wannan
Anatse yasake kiranta My Fauzy sunotoo(kinajina)
Nanma banza tayi dashi kamar da dutse yake magana
Zama yayi agefenta ya riqo hannunta dake gefensa ya sake qasa da murya cikin sanyi yace My Fauzy pls jababdo(ki amsamun)
Bata kulasaba sai yunqurin kwatan hannunta daya riqe takeyi
Saqe riqe hannunta yayi gagam ganin baya da niyyar sakinta saita rabu dashi kawai
Tambayarkifa nake why ar u crying n baki amsaniba yafada atausashe
Ganin batada niyyar yimasa magana yasa ya cigaba da fadin
Koma meke daminki pls kiyi haquri kibar kuka banson kanki yayi ciwo ko idanunki yayi ja
Nazo namaki godia ne akan amincewa da kiyayi zaki aureni
Inkuma qara baki haquri akan abinda namaki abaya
My fauzy inaroqonki kibani dama na nuna maki irin sonda nake maki
Nayi nadamar abinda na aikatamaki abaya
U don't know how much i regret everything that i have done to u
I luv u my fauzy i luv u with all my hrt
Magana yake yana murza dan yatsun hannunta masu laushi da taushi kamar na jarirai
Maimakon taji sanyi aranta sai tasakejin wani zafi aranta nan tasake fashewa da wani sabon kuka mai sauti ahankali
Nam yayita lallami da maganganu masu dadi amma abanza harya fahimci maganarsane batasonji akan dole ya miqe ya fita yanajin kukanta har cikin zuciyarsa
Adaren ya kira TJ ya shafa masa halin da ake ciki
TJ yayi murna sosai ya kuma sake bashi shawara mai kyau akan kada gaba ya kuma gangancin kwatanta abinda ya faru abaya
*******
Washegari daddy ya tafi dambam nan suka zartar da maganar biki sai nan da watanni biyar masu zuwa
Kafinnan angama ginin sabon gidan da zaa kai fauziyyah
Yan uwa kowa yayi murna da samun labarin komawar fauziyyah musamman saida aunty mabarukha tazo bh takuma dauki nauyin gyaran amarya idan lokaci yayi
Haka maman fauziyyah da farko taqi yadda saida Abba yamata nasiha sannan ta amince takuma sanya Albarka
Da aka sanarda papa lokacin auren sai cewa yayi shifa lokacin yamasa tsayi gaskiya
Momcy harta qulu tace tosaika rage tunda ka isa da hakan
Cikin sati daya magana tagama kankama har daddy yabada contract na ginin gidan sabon gidan papa amma wanna karon a kusa dasu nan *Gida Dubu*
Wani filin daddy dake kusa da gidan Aunty naja dambam sukayi shawaran gina masa
Momcy tace gara kusa da auntynsa tunda koba komai yafi shiri da ita kuma zatana leqasu akaiakai taga inda yayi ba daidaiba tasashi ahanya
Dan abinda ya faru abayama harda rashin wani babba akusa wanda yake leqasu
Daddy ya amince da shawarin momcy
Daddy ganin har sati guda papa baida niyar komawa gidansa yasa ya kirasa yace ayau dinnan yayi parking inba so yake ya saba masa ba
Babu musu ya hada kayansa ya loda a mota sai abinda baa rasaba ya bari saidaga baya zaizo ya dauka nan ya
nufi gidansa dake sokoto road wadda rabonsa da gidan tun rabuwarsa da j
uhaina....
*Wai ina labarin juhaina kam[truncated by WhatsApp]
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
*This page goes to Aunty Faty G Dambam, Nagode da qaunar da kike nunama littafina, Insha Allah 2019 Bauchi sai Proffessor, Mmn Faty Luvs u ππ*
5β£6β£
Hankali kwance yake driving har ya qaraso
Amma yana isowa gate sai yaji ransa ya baci cos nan take kwakwalwarsa tafara recalling masa abinsa yafaru lokacin rayuwar da yayi da ex wife nasa juhaina
Horn yafara mai gadi ya bude masa gate dan yasan da zuwan ogan nasa cos ya kirasa awaya kan cewar agyara gidan before ya yazo
Qarasa shiga yayi har parking space yayi parking motarsa
Qarema gidan kallo yake saiyaga ya canza masa kodan ya jima rabonsa da gidanne oho
Koda kudin buqatar maigadi da sauransu saidai suyi waya yazo ya karba
Wani iska mai zafi ya furzar kafin ya bude qofar motan yana tattara wayoyinsa
Yana fitowa daidai da isowar maigadi kenan
Sannu da zuwa yallabai ya fada yana risinawa
Cikin kulawa yace yawwa ya gidan dai hope babu wata damuwa
Aa babu konai yallabai ankuma gyara ko ina kamar yadda ka umarta sai dai daki daya wadda yake akullene da baa gyara ba sabida acikin keys da suke wajena babu nasa aciki
Ok babu damuwa i think key din yana wajena barin qarasa ciki zan fito saika shigar mun da kayana idan kuma Abdu ya iso shikenan
Toh yallabai afito lfy
Wucewa yayi ciki inda yabar maigadi da mamakin canzawar ogan nasu
Tun bayauba ya lura da sauyin idan yaje wajensa but nayau dabanne lura da yadda ya bada time nasa sukayi magana ta fahimta
Falo ya bude ko ina tsaf sai qamshin room freshner da sanyin AC
Ba komai acikin falon sai carpet dake tsakiyar falon
Wucewa yayi falonsa nanma komai agyare yadda yake ba kuma abinda aka taba
Kallon dakin juhaina yayi kamar ya wuce amma sai ya qarasa ya bude nanma bakomai ciki da sauri ya jawo qofar ya rife hadida rintse idanu sabida tuno da abinda ya faru da yayi
Cikin sanyin jiki ya wuce dakinsa key yasa ya bude qofar
Qurakam baa magana ko ina yayi qura kallon dakin yake sosai fridge ya bude nanma da sauri ya kulle ganin kwalaben wine iri da ban daban
Ga wasu kwalabe a zube aqasa ga kuma kwalayen sigari da dai sauran kayan shaye shayensa
Lokaci guda yaji kyaman dakin ya kamasa fitowa yayi ya shiga kiran layin Abdu bada jimawaba ya daga hello oga sir am sorry pls na kusa isowa
Ok am ka tsaya ahanya kasamomin kwalaye manya mana ammafa empty
Ok badamuwa ya fada
Bada jimawaba ya qaraso da manyan kwalaye kamar yadda aka sashi
Karba yayi ya shiga loda tarkacen aciki saida ya kwashe su tas sannan ya manne su tass ya kira Abdu yace yayi waje dasu ya loda su a boot
Falo ya dawo ya zauna ya jira Abdu ya gyara masa dakin nan ko ina ya tsaftatu kamar bashiba
Kayansa suka shigo masa dasu daganan ya wuce toilet ya watsa ruwa hadi da alwala
Agurguje ya shirya ya nufi masallaci
Sai da yayi ishai sannan ya dawo
Yabawa Abdu kudi ya samo masu abinci
Bayan yayi dinner ya jawo system nasa ya kunna ya duba wasu abubuwa sai dai ya gagara samun natsuwa
Jingina yayi da jikin kujera ya lumshe idanunsa ya tuno fiskar luv of his lyf
Jiyake inama yana da no wayarta daya kira yaji muryarta ko zaisami sukuni
Gashi ya na zaune shiru shikadansa dik kadaici ya damesa
Wayarsa ya jawo ya kira TJ
Amma baidaukaba harta