Showing 63001 words to 66000 words out of 87071 words

Chapter 22 - Budurwar Kauye Hausa Novel

07 Oct 2024

13120

cikin damuwa

Ahankali ta kallesa kadan tace ya Alamin dan Allah kadaina kirana da wannan sunan na roqeqa ta karisa maganar kamar zatayi kuka hawaye na ciko idanuwanta

Meye laifi danna kiraki da My Fauzy keba tawa bace uum ko kina manta cewar remain few days kizama mallakina so banga wani damuwaba danna kiraki da My Fa...
Baikaiga qarisawa ba yaji tafashe da kuka sosai

Subhanallahi haba dear danna fada maki wannan sunan shine bakiso harda kuka to kiyi haquri i promissed u barin sakeba

Ganin yanata surutansa ko kulasa bataiba saima cigaba da kukanta da tayi yasa ahankali ya gangara gefen titi yayi parking

Lallaminta yafara hadi da bata haquri kancewar bazai kuma mata abinda batasoba kuma tayafe masa

Amma fir taqi sauraronsa saima kuka datake sosai

Shikuma jin kukan yake har cikin zuciyarsa ganin baya da option kawai saiya dan matso ya jawota jikinsa ya rungume

Cikin muryar lallashi yafara magana yana cewa swt hrt am begging u kiyi haquri kibar kukan nan namaki alqawarin koda wasa barin kuma fada makiba tunda bakiso
Banason jin kukanki yana tabamun zuciya har cikin raina nakeji

Cikin kuka tafara qoqarin janye jikinta tana cewa kadaina bani haquri kabarni nayi kuka shikadaine zai ragemum radadin abinda nakeji

Sake riqeta yayi sosai ajikinsa yana patting bayanta smootly
Yace nasan abinda yasaki kuka n banson tuna maki kuma saidai inason roqonki kibani damar na gwada maki kalar sonda nake maki wlh nayi alqawarin zan kula dake har qarshen rayuwata bazan taba cutardake ba

Kuma da kike kuka sabida ganin yasir bagashiba shima harda matarsa da yarsa

So pls kimanta da baya da abinda yafaru kidauka komai Rubutaccen Alamarine bazai kuma canzuba

Haka yaita lallaminta da kalamai masu dadi harya samu ta tsagaita kukan sai ajiyar zuciya datakeyi

Sunfi 30mins kafin yasamu kanta ahankali ya janye jikinsa daga nata ya tashi motar

Suna isowa gida tafice cikin saa tasamu bakowa acikin falo sabida haka ta wuce dakinta kawai ta kwanta

Shikuma fitowa yayi ya dauki iyaka kayanta ya wuce ciki dasu
Dakinta ya shiga nan yasameta kwance

Baice da ita komaiba ya ya ajiye mata ya fice

*****
Afannin yasirma ganin fauziyyah ya tayar masa da abinda ya jima yana damunsa amma haka ya danne zuciyarsa ya haqura gudun kada matarsa ta fahimta

Kuma baya samum matsala da ita so baison tawajensa asamu rashin jituwa tunda dama tasan da labarin fauziyyah yaukuma taganta ido da ido

Kimanin shekaru hudu kenan da auren yasir

Bayan sundawo daga dambam akan baisamu auren fauziyyah ba lokacin ya shiga matsanancin hali sosai

Saida ya kwanta jinya tun abin yanabawa iyeyensa haushi yafara basu tausayi

Da kyar suka samu kansa yadan warware shinefa baffansa ya bashi yarsa ya aura

Baiyi musuba ya amince dan yanason ya manta fauziyyah aransa tunda yasan tamasa nisa har abada

Itama bataqiba dan dama tajima tanason yasir babanta yana fada mata ta amince

Bayan bikinsu da yadda take kula dashi take nuna masa qauna har ta shiga cikin ransa yafara sonta
Koda ta haihuma baiboye mataba yace sunan yarsa fatima yakeso kuma ana kiranta da fauziyyah

Nanma bataqiba dan burinta ta faranta masa

Wannan kenan


*****
Tunda aunty mabarukha tazo bata zaunaba sai hidimar gyaran amarya take musamman da wadanda ta dakko masu gyara

Dinkunanta ma dik ita ta bada wadda zatayi fitan biki

Kuma tundaga ranan papa baikuna saka fauziyyah a idonsaba

Saidai yaqaraci surutansa awaya nanma text dan bata daukar wayarsa kam

Cikin sati biyu babu abinda ya rage na shirin biki komai ya kankama sai ranan biki kawai ake jira

Fauziyyah kuwa tayi natuqar kyau na birgewa dan baqaramin gyara tashaba ga wani sheqi da da santsi da fatarta tayi

Washe gari suka tattara suka nufi dambam amma gidan Abba aka kaita sabida dagacan zaa dauki amarya

Kuma washegari zaa fara shagalin biki

Papa kuma sai aure saura 3days zai iso sabida wasu abokansu sa zasu taho tare kuma ananne zaayi hidimarda zai halatta.....

โœ๐ŸปFaty Mmn Faty





๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ


๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017


*This page goes to Mmn Faty Novel Fans, Mmn Faty ta ๐Ÿ‘๐Ÿป maku ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜*


6โƒฃ0โƒฃ
Washe hari aka fara hidimar biki amma na gargajiyar aladarsu

Amarya tayi kyau kamar ba gobe,dikkannin wadan da suka halarcin wannan hidima sunyi san barka dayima papa murnan samun mace kam tare damasa adduar Allah yasa yadda yanayinta yake haka halayenta suke

The following day ma haka akasake wani hidimar nanma haka aka watse taro lfy lau

Papa nacan bauchi jiyake wane yayi tsuntsu ya taho yaga gimbiyarsa

Bayadda baiyiba da Aunty Mabarukha kan ta turo masa pics din Fauziyyah na hidimar biki amma fir taqi tace mene kake sauri badai kaima daka xoba kuma gidanka zaakawo maka ita so nothing to worry about

Haka ya dami aunty niima itanma sammaqal dan hada baki sukayi sunfison yaganta azahiri yaga yadda tadawo akwanakin da baiganta ba

Ana gobe papa zasu iso da abokanansa akayi sakun lalle namma guri ya burge dan yan uwa anhadu both side na ango da amarya

Sai wajen 10pm aka tashi daga taro

Jamaar garin dambam sun shaida ana biki afada dan yadda tako ina manyan motoci ke shawagi abinka da bikin manyan mutane maaikata da yan kasuwa

Ga yan uwan Abba dana Mama gari gari dik sonzo saikace shine aurenta na fari

Papa kuwa yayi juyin duniya akan tadau wayarsa koda muryartane yaji kozaiji sauqin abinda yakeji azuciyarsa

Amma sam taqi text kan text daya dametama saita kashe wayartama dan gaba daya bata son damuwa

*****
Tunsafe suka kamo hanya inkagansu kace daukar amarya akatafi yadda sukayi comboy na motoci

Zumudin papa har bai boyuwa burinsa kawai yasaka tauraruwarsa a idanunsa

12:30pm suka shigo dambam
Direct gidan daddy suka wuce inda zasu zauna da friends nasa acan tunda su daddy afada suka sauqa

Bayan sunci abinci suka dan kwanta kafin lokacin tafiya KAMU

Amma sam papa ya gagara kwanciya burinsa kawai 4pm tayi su wuce wajen KAMUN

Ana kiran sallan laasar sunayin sallah suka fara shiri daya daga cikin abokansa guda uku da sukazo daga india yace shikam yau jumper zaisa dan yana shaawar kayan shiyasa yasaka aka dinka masa dan yayi shigar hausawa

Ango ne nagani ya dau wanka cikin wani coppee brown yard mai kyau da sheqi

Kyansa shiya bayyana tsadarsa
Sum matuqar karban fatan jikinsa abinka da farin mutum
Ya kafa wata tsadaddiyar huwa
Brown covvers yasaka aqafarsa sai agogon azurfa dake daure ahannunsa

Ga wani uban qamshi dayake xubawa na musamman

Tabbas ya fito a Ango sak๐Ÿ‘Œ๐Ÿป

Nan fa su Dr khalid suka fara tsokalansa anata barkwanci

TJ ne ya kirasa awaya yana dauka yace yane kuna inane

Papa yace muna gida amma yanzun zamu wuce

TJ yace shine ka azalzalemu ashema baku fitoba to gashinan yanzun haka muna hanya mun dakko amarya

Papa yace to sarkin mita naga dai munfiku kusa dawajen ko kafin ku qaraso mun iso muma

Ok toh saimun hadu

Nan suka fito suka shishshiga motocinsu suka wuce wajen da zaayi KAMUN

Su papa suna isowa su TJ ma suka iso

Sunsamu angama taruwa amarya kawi da ango ake jira

TJ yace basai kunfitoba barin su qaraso naga suna tahowa sannan shima ya fice

Ta cikin glass take hangosa shida abokansa suna tahowa sunkuyarda kanta kawai tayi wadda ita kadai tasan yanayin datake ciki

Suna qarasowa yasa hannu ya bude motar datake ciki

Ya salam shine abinda ya furta ahankali ganin irin kyan datayi

Sanye take cikin wani less pich colour mai toches na coppee brown

Dinkin riqa a siket wadda yamatuqar qarbanta kaman ba gobe

Fiskantannan yasha makeup
Dan qaramin bakinnan anlailayesa da pinks jambaki

Kyaukam baa magana gashin kantannan sai sheqi da qamshi yake andaureshi waje guda da pich ribbon

Sai head na kanta shima coppee brown jeweries natama wasu passion ne dik suma coppee brown masu adon duwarwatsu pich n white

Takalminta da purse nata dik coppee brown

Ahankali yake sakin wani murmushi wadda shikadai yasan maanarsa

Daurewa yayi ya daidaita muryarsa ya kira sunanta cikin wani tattausan murya yace my princess

Dago daradaran idanuwanta masu yarwar lashes tayi ta amsa da muryarta mai dadin gaske naam

Wani lumshe idanu yayi sannan ya bude yana kallon kwayar idonta wadda yasha kajol da maskara tare da siririn line eye liner

Sannan yace meet my friends yana kirga mata sunansu

Dik saida suka gaisa kuma sun yaba da zaben abokin nasu

Daga qarshe ya introducing mata abokansa uku da sukazo daga india yace yeh he Himesh(wannan shine Himesh), Salman aur Imran(da)

Cikin sakin fuska suka gaisa nan TJ ya qaraso yace man kukadai ake jirafa

Papa yace ok muje toh duban Fauziyyah yayi yace my princess muje ko

Cikin natsuwa ta sako qafarta nan yasake shagala wajen kallon lallen da aka qawata qafarta dashi na zallan jan rani

Jerawa sukayi cikin takun qasaita dan jin kansa yake asama qasaisatar ta motsa jinin sarautar ya tsinke

Fauziyyah kuwa dik saita jita atakure dake ita bawasu qawaye ke gareta ba kwakwata su shidane sai

Suna shiga cikin hall din waje ya kaure da tattausan waqa mai dadin gaske

Wajenda aka qawatashi da ado sosai kuma kalan kayansu hatta ballons da aka decourating wajen pich n coppee brown ne

Wasu kujeru ne guda biyu iri daya masu kyan gaske suka qarasa suka zauna sai kuma na abokanai da qawaye da aka ajiye daga bayansu

Kowa ya shashe ranan angwangwaje naira tayi kuka ko motsi tayi saiyace yadai baby kingaji ne sabida yadda yakeji kamar ya maida ciki dan so

Fans na Mmn Faty Novel ma baa bassu abayaba dan sun nuna murnansu sunkuma nunama ma fauziyyah gata

Kodagakan irin liki da sukaringa mata shima abin ajinjina masu ne

Baa tashi ba sai gabda magriba sannan taro ya watse

Ahanyar su ta komawa gidane papa yaga canji yayi juyin duniya fauziyyah tayi magana amma taqi sam shikuma harga Allah baison shirunta shifa ko zaginsane garatayi yasan tayi magana dan baimanta lokacin data kullaci abu aranta tadaina masa magana

Haka suka sauqeta suka dawo gida

Washe gari Thursday akayi Family n Friends day

Nanma sunyi kyau ba qarya

Ranan friday akayi Hafla

Sai washe gari Saturday misalin Qarfe sha daya na safe dubban jamaa manyan mutane maaikata yankasuwa hadda sarakuna da sauran Alumma suka shaida daurin Auren Dr Muhammad Alamin Abubakar n Fatima Usman abisa sadaki 100k lakadan ba ajalanba

Papa dai bakinsa bai rufuwa daka ganshi kasan yana yanayin farin ciki lura daga kayan jikinsa komai fari tass

Sai gaisawa yake da jamaa kawai

Makada da maroka kuwa sai wasashi sukeyi abindai abin birgewa sai muce Allah ya kade fitina kawai

Da yamma akazo daukan amarya

Wata goggonsu papa wadda take yace awajensu daddy ita tabada wata Alkyabba ta musamman tace asawa amarya ita

Fauziyyah tai kuka harta gode Allah sabida nasihan da su Abba suka mata mai ratsa zuciya da dikkan gangan jiki

Da mata adduan Allah yasa sai gawanta zaa fitar agidan Alamin

Haka aka wuce da ita fada su anty papa aka samu a side din da zaa sauqi amarya

Nan suka karbi amarya da murna da farin ciki gami da mutunchi

Nan suka shiga hidima da baki dan Aunty naja(Auntyn Papa ) batada rowa kuma batason harkan qaranta

Dik wadda yazo kawo amarya ya yaba da irin kaunar da yan uwan papa kema Fauziyyah sai fatan alheri suke musu

Bangare guda Aunty papa ta sauqi Fauziyyahs' team


Kuma sun yaba sosai dan Aunty papa bata musu qarantaba ta nuna musu cewar biki ake na dan gata

Har wajen magriba fauziyyah taqi yin shiru sai kuka take
Saida Aunties dinta suka shigo suka lallasheta sannan tayi shiru

Anayin sallan ishai Aunty mabarukha ta kawo mai kwalliya akayima Fauziyyah

Wani mterial ne dinkin doguwar riga milk n golding colour tasaka wadda yasha ado sosai yakuma matuqar yimata kyau

Kwalliya sosai aka mata sai dan veil din rigar wadda shima golding colour ne tayane kanta dashi

Wani danqareren saitin gold Aunty Mabatukha takawo mata tasaka hadda bangkes dinsa manya guda biyu

Takalmin hill ne sosai da purse dinsa suma golding colour

Wasu turaruka na musamman tafesa wadda dik aunty Mabarukha ce takawo mata su

Nan tafito a amaryarta ba qarya

Members na Mmn Faty Group sunsha anko dinsu na material
Fauziyyahs's team sunyi ankon material golding colour

Sai papas' team sukuma ankon material milk colour sukayi

Nan aka fara tafiya dinner kowa ya tafi sai Fauziyyah ita kadai akabari dan wannan umarnin Ango ne

Tana zaune abakin bed shiru itakadai sai taji motsin bude qofa

Bata dago kanta ba amma qamshin turarensa daya gauraye dakin shiya tabbatar mata papa ne

Sanye yake da wani dhegen gezna maih danbanzan kyau da tsada Milk colour

Dikin yamatuqar amsansa ga hularsa da ta dace da kayan hafi da takalminsa

Qaremata kallo kawai ya tsaya yi yana yima ubangiji tasbihi acikin zuciyarsa daya mallaka masa ita amatsayin mata

Ahankali ya tako har bakin gadon datake zaune

Maganama ya kasa kawai hannunta ya kamo ya riqe gam acikin nasa

Wani taushi dayaji shiya haifar masa da kasala lis ajikinsa

Dayan hannunsa yasaka yana murza bangles din hannunta

Da wata iriyar murya yace my princess pls na roqeki kimun magana kinji

Kallonsa tadanyi ta kasan idanunta ta dan turo baki tace to mai zance maka pls kasakemun hannuna

Cos yadda yake wasa da hannun nata dik sai taji ta takura

Shikuma gyara zamansa yayi yama manta da yabar mutum awaje nan yafara barbada mata maganganun soyayya

Qarar wayarsa yasashi yin dan qaramin tsaki dan yana tsaka da jin dadin yadda yake manne da ita bata kuma turesaba

Ganin TJ ne yasa yace yane akayi

TJ yace lallema toh kawai kace inje insallami mutane tunda kai kasamu waje bazaka fitoba

Papa yace oh yaushema nashigo to naji gamunan fitowa

Baby nah mujeko kinga wannan dan damuwar da takurin yafara mita

Batace dashi komaiba hannunta ya riqo ta miqe suka tako ahankali suka fito....



โœ๐ŸปFaty Mmn Faty





Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

*Banmanta dakeba takwarata Fatima Muhammad(Miyatti Allah), nagode da kulawarki gareni Allahu ya bar qauna, Mmn Faty ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜*

6โƒฃ1โƒฃ
Hannunsa riqe acikin anata har bakin mota

TJ dake tsaye yana jiransu shiya bude mata

Da murmushi afiskansa yace bismillah Amaryanmu

Batace komaiba sai murmushi datayi sannan ta shiga tazauna

Ya rufe kafin ya zagaya ya shiga shima

Papama ta gefenta ya zagaya ya zauna
Tafiya suke suke bamai cewa komai itadai ta sunkuyar dakanta tana wasa da ring din yatsanta

Papa kuwa ya wani matso jikinta kamar wadda zai shige cikinta amma baicewa komai cos hakanma he is totaly satisfied

TJ kuwa katse shurun yayi da kunna wani tattausan music mai dadin sauraro

Da haka har suka iso

Batare da bata lokaciba abokai da qawaye suka rufa musu baya zuwa cikin hall din

Lokacin da suka shigo nan aka fara musu ruwan wasu flowers masu kyan gaske da qamshi mai dadi

DJ kuwa waqar da aka masu ta biki ya kunna nan waje ya birge sosai

Cikin takun natsuwa suka qarasa wajen zamansu kafin kowa ya sami waje ya zauna

Baqarya wajen ya qayatu ya kuma matuqar birgewa dan naira tayi kuka

Nan aka fara gudanar da programs iri da ban da ban

Idan ka kalli Amarya da Ango ka rantse kace wasu couples ne masu mutuwar son junansu

Yadda fauziyyah tasake fiskarta kamar bawani abu aqasa
Shikuma uban gayyar dama sai faraa yake kamar gonan auduga yana wani shige mata ganin yadda ta saki jikinta tamkar ba itaba

Kowa ka gani awajen yasha ado da kwalliya gaskiya bikinsu papa ya matuqar tsaruwa sai fatan zaman lfy

Sai wajen 12 aka tashi

Saida kowa ya watse ya rage su papa aka bari kafin suka taho suma

Ahanya papa yacema TJ man kadaukomin saqona daiko

TJ yace waneni namanta yana gaba nan qasan seat

Papa yace ok thanks

Suna isowa gida TJ ya bude mota ya miqo masa ledan take away sannan ya fice

Itama bude qofar motar take qoqarin zata fice

Riqo hannunta yayi

Juyowa tayi ta sauqe daradaran idanuwanta akansa kafin dan qaramin bakinta ya motsa gami furta lfy daiko

Yadda tai maganar ba walwala afiskanta yasa ya marairaice murya yace pls kiban 15mins acikin lokacinki

Pls mana dear badan niba dan Allah

Komawa tayi tazauna
Thanks yafada sannan yasake mata hannu

Take away din ya bude pepper chikchen ne wadda yasha hadi sosai

Kallonta yayi da kyau kafin yace baby pls bawasa nakeba kici abinci kuma kada kice aa dan nasan wunin yau kaf da wuya idan kinci wani abin

Shiru tayi tana tuna tabbas yau bataci wani abinkirkiba

Bude motar yayi ya balle bottle din ruwa ya dauraye hannunsa

Naman ya kutsiro ya miqo mata saitin bakinta

Ba musu ta karba tafara tauna ahankali

Ganin yadda batai gardama yasa yaci gaba da bata abaki tanaci

Matsowa yayi sosai yana lallabata harta ci sosai kafin ta kauda kanta

Ruwa ya bata tasha sannan ya bude mata roban juice sai anan ta kauda kanta tace umum

Murmushi yayi yace thanks a lot wifey nagode muje narakaki ko

Aa kawai tace dashi tafice abinta

*****
Washe gari sunday akayi walimah dasafe daganan wasu suka fara tafiya garuruwansu

Amma su papa sai gobe dasu koma bh

Abdu yasa ya maida su Himesh bh sabida gobe jirgin safe zasubi zuwa lagos dagacan su wuce

Abokanansu dik sun koma TJ ne bai tafiba sai gobe zasu wuce tare da Ango

Itama qawayenta dasukazo daga bh guda biyu sun koma sauran ukun dama yan uwane

Haka ta yini shiru itakadai su aunty mabarukha ma basu zannaba sabida sallamar baqi

Shima haka ya wuni sallama da baqi gashi sunje gidan Abbama sunjima acan

Sai dare aunty mabarukha ta shigo nan tace tana da magana da ita

Gyara zamanta tana sauraronta

Aunty mabarukha tace abinda zan fada maki kidauka ni yar uwarkice kuma ciki daya kikuma dauka bansan papa banida alaqa dashi

Taci gaba dacewa inason kidauki wannan auren yana cikin kaddaranki arayuwa wanda baki isa kikaucewaba

Kuma tunda har Allah ya rubuta haka inason ki haqura kidauki qaddara ki rungumi mijinki kimasa biyayyar aure

Dik halin da kuke ciki da papa ina sane amma yanzun tunda andaura maku aure zance ya qare

Kuma bama fata abinda zai kuma rabaku sai dai mutuwa

Jikintane yayi sanyi kuma ko itama tunanin datake aranta kenan tunda Allah ya qaddari haka tafaru gara ta dau haquri suzauna lfy

Aunty mabarukha tace sabida haka kidauka dik abinda yafaru abaya kamar bai faruba kuma bama fatan ya kuma faruwa

Kuma ina da tabbacin hakan bazai faruba sabida yanzun papa yana sonki so mai tsananin gaske kuma zai iya komai akanki

Amma bawai ina nufin dakunkoma bh kibada kai bori ya hauba aa ki nuna masa cewar kema mace ce

Saikin dan wanasa tukun saiki saqqo ku zauna lfy Allah ya albarkaceku

Sannan kada ki kuskura kiyadda kunya ta cuceki dan matuqar zakiji kunyan yin wani abin toko zaki kwari kanki

Gobe akwai kayan dazan kawo maki idan kinkoma bh

Su zaki ringa sawa agida kina kwalliya tareda yin qayataccen girki kuma kada kihanasa

Kibashi dik tarkone

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login