Showing 36001 words to 39000 words out of 87071 words
baijin magana ashe bai haquraba yana nan akan bakansa tunda har wani maganar aure zai tsiro
Daddy yace kibarni dashi yanason yaga bacin raina ne fiye da zatonsa
Cikin sati1 dik abun duniya ya dami papa
Baijin zai iya rabuwa da juhaina gashi abinda daddy ya fada yarasa ta inda zai bullo ma lamarin
Ko waya sukayi da juhaina ta tambayesa yatajisa wani iri cemata yayi baijin dadine kawai
Yanzun haka yana zaune a office tunani yake amma yarasa mafita
Qarar wayarsa ita ya dawo dashi daga dogon tunani daya tafi
Murya ahankali yace hello baby
Wani murmushi tayi sannan tace naam likitana, badai jikinba naji voice naka so cool haka
Sake gyarawa yayi ya kwantar da kansa yace kedai bari my queen fever ne yake damina amma yayi sauqi
Tace eyyer Allah ya qara sauqi n pls karage zama cikin AC da kuma shan abu mai sanyi dan nasan su zasu sakamaka fever
Cikin jindadin yadda ta damu dashi yace insha Allah my queen i promised u zan rage
Tace yawwa my king har kasa naji dadi amma kwana biyu ko waya mai dadi bamuyi
Yace no kada kidamu am feeling better fa
Tace toh shikenan sannan tasake qasa da murya cikin yanga tace am my king tinda kazo kacemun idan ka koma zakuyi magana da daddy kuma har yau bakacemun komaiba
Rintse idanuwansa yayi ya bude ahankali gamida danne damuwarsa yace wlh tunda kikaga banfada maki ba akwai dalili
Washegarin dawowana daddy yayi tafiya kuma two weeks zaiyi so idan ya dawo dik yadda mukayi zan sanar maki
Cikin jin dadi da gamsuwa tace Allah ya dawo dashi lfy
Ahankali yace amin
*****
Afannin TJ kuma su dad dinsa sunje masa tambaya inda baffansa da baban khairy suka gane juna dan abokaine sosai
Nan suka gabatar da abinda ya kawosu
Baban khairy yace tabbas da baida niyyar auren khairy nan kusa dan yafison ta kammala karatunta kamar sauran yan uwanta
Amma tunda yanzu abu yazama na gida ya amince amma dan Allah abarta taci gaba da karatunta
Nan suka yi godia sosai har aka tsaida ranan biki nan da wata biyu
Cikin ikon Allah lokaci na tafiya har aka fara hidimar bikin TJ
Inda naira tayi kuka kasancewarsa dan fari agidansu itakuma auta ce a mata
Sati guda ana shagali aka daura aure aka taho da amarya gidanta dake bauchi unguwar sokoto road
Sai muce Allah ya bada zaman lfy Amin
*****
Cikin watanni biyu nan papa hankalinsa ba akwanceba sabida kullum haka yakema juhaina hanya hanya akan maganar turowa gashi har yau baisami mafita ba
Fauziyya kuwa tana gidan momcy har yanxu sai bikin khairy da sukaje dambam sukayi sati 1 harda momcy
Auren TJ da kwana biyu juhaina ta kira papa awaya tana masa kuka akan ashe yaudaranta yakeyi ba sonta yakeba tunda gashi rabonsa da zuwa ma sati hudu kenan kullum yace aiki ya masa yawa idan baisontane ya fada mata yafi akan ya ringa yaudararta
Haka da kyar yasamu ya lallameta ta haqura ya kuma mata alqawarin nan da 2weeks zaa zo maganar bikinsu
Yau ya qudiri aniyar komawa wajen daddy akan maganar aurensa da juhaina dan gaskiya baxai iya haqura da itaba
Yamma lis ya nufi gidansu cikin saa ya samu momcy da daddy afalo suna waya da aunty mabarukha akan tace zatazo nan da 1week dan yara sun sami hutun makaranta
Sai da suka qare wayar sannan ya gaidasu adaqile suka amsa dan tun akan maganar fauziyya baya samun fuska
Shima cikin daurewar fuska yace daddy nadawo akan maganar munefa
Daddy ya dubesa yace wanne magana kenan
Maganar auren danace maka ina sonyi ya fada kai tsaye
daddy yace akan baka haqura ba kenan da abinda nafada maka
Yace gaskiya daddy tana sona inasonta to akan me zaa hanani aurenta bayan halal ne ba haramba
Daddy yace toh ai naga bazaka iya riqe mata biyu bane shiyasa tunda guda 1 ma ta gagareka ka riqe
Cikin bushewar ido yace wannan fa ku kuka riqeta agidannan ba ninace tadawo nan da zama ba kuma koma mene ne dai kawai nifa nafada maku aure nakesonyi
Momcy ta dubeshi cikin takaici da mamaki dan batayi zaton rashin kunyarsa da rashin mutuncinsa sunkai nanba
Tace papa ka maimaita abinda kace
Cikin rashin damuwa yace haba momcy, kumafa kun hada abinnan ne batare da neman shawrina ba
Fisabilillahi ina zankai wannan qazamar qaramar yarinyan yar qauye wlh abin kunya ne innunata amatsayin matata, god forbid
Amma ga juhaina wayayya mai ilmi amma kuce baku yabba ba, to nidai nafada maku waccar zabinkuce ba test dina ba so saikusan yadda zakuyi da ita
Momcy takaici da baqin ciki su suka hanata magana
Daddy ya nisa sannan yace naji batunka, amma saika ban takardan sakin fauziyyah sannan na amince da batunka
Kawai daddy na saketa saki 1, shikenan toh yaushe zaajemun KD tambayar?......
โ๐ปFaty Mmn Faty
[3:01PM, 8/19/2017] โช+98 903 074 3573โฌ: ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August,2017
3โฃ7โฃ & 3โฃ8โฃ
Momcy salati kawai takeyi da jin maganganunsa,cikin kuka tace ashe papa har iskancinka yakai haka
Kaje indai matan mazamanine saikayi dana sani
Daddy cikin fushi yace kaje saina nemeka
Papa yace zuwa yaushe kenan daddy
Daddy cikin tsawa yace nace kaje saina nemeka get out i said
Yana fita momcy tasaka kuka tana cewa ka haifi dan yafiqarfinka
Riqota daddy yayi yace haba saudah, meye hakan
Kirabu dashi badai duniyaba, kuma namaki alqawari watarana sai yayi kuka da hawayensa akan Fauziyyah sabida haka ki kwantar da hankalinki sannan nasan aminina zai fahimceni wannan bazai shiga tsakanina dashiba
Share hawayenta tayi tace shikenan Allah ya kyauta yanzun mezamuce wa fauziyyah da iyayenta
Daddy yayi shiru sannan ya nisa yace yanzu muje musameta mukwantar mata da hankali sai mufada mata inyaso gobe insha Allahu zanbar dik abinda nake natafi dambam nasanar da mahaifanta
Momcy cikin jimami tace toh Allah ya kaimu daganan suka nufi dakin fauziyyah
Zaune take tana shirya kayanta acikin akwati wadda aka wanke aka goge mata
Taji sallamar momcy tana amsawa taga daddy ma ya shigo ,dasauri ta miqe sai taji zuciyarta na bugawa ganin daddy har dakinta
Murmushin dole daddy yayi yace aa daugther kiyi zamanki muma zama zamuyi
Komawa qasa tayi ta zauna tana sauraronsu
Shiru sukayi nadan lokaci kafin daddy yayi gyaran murya yace Fauziyyah
Dagowa kanta tayi tace naam daddy
Yace kinsan cewa yana daga cikin rukunnan imani yarda da kaddara alkhairi ko sharri ko
Qirjintane ya tsananta bugawa dakai ta iya amsawa dan sai taji magana ta gagareta
Yace Alhamdulillah ,toh abinda zanfadamaki kidaukeshi kaddarace kuma mai wucewa
Sannan yaci gaba da fadin kwanakin baya Alamin yazomun da wata magana wai yanason yaqara aure
Cikin sauri ta dago kanta tana maimata aure azuciyarta
Daddy yace toh nan nace banyardaba daganan baikuma tada zancenba sai yau dinnan yasake dawowa da maganar
Fauziyyah dai tunani take aranta itakuwa me tayima ya Alamin ya tsaneta har haka baicin yayi watsi da ita baikuma isheshiba har kuma wani maganar aure zai tsiro
Maganar daddy ce ta dawo da ita daga tunanin dake
Yana cewa nikuma nace inhar bazai gaquraba sai dai ya sakeki inyaso yayi auren amma dake dan yaune shine ya furtamun kalmar ya sakeki
Wani razana da tayi yasa momcy tayi saurin riqota
Momcy tace kiyi haquri Fauziyyah tabbas papa ya cutar dake amma Allah zai saka maki kiyi haquri kinji
Shiru tayi batace komaiba sai take ganin kamar amafarkine ko ido biyune
Cikin dauriya tace sagaske kenan ya Alamin ya sakeni momcy tace kansa ya yima kiyi haquri
Aifa nan taji wasu hawaye masu zafi suna mata zarya afuska
Nan su daddy suka ta rarrashinta har suka samu tayi shiru
Washegari ta tashi da matsanancin zazzabi wanda yasa daddy ya fasa zuwa dambam dan tare yake son sutafi da ita
Kwananta biyu da taimakon Allah da rarrashi har suka samu ta sami natsuwa ta kuma dangana tunda har abinci ta karba taci sosai bakaman kwanaki biyun da suka wuceba
Ranan kwana na uku da faruwar alamarin daddy yace fauziyyah ta shirya sutafi dambam
Hakan ko akayi suna isa direct gidansu fauziyyah suka wuce
Agida yasami Abba dan yamasa awaya akan yana tafe
Afalon Abba dik sunyi shiru shida daddy dan maganar tazoma Abba abazata
Cikin damuwa daddy yace wlh nibansanma wacce kalma zanyi amfani da itaba wajen baku haquri
Abba ya nisa yace kada damu nafahimce komai kuma wlh ni bandauki zafi da maganar nanba bakomai Allah yasa haka shiyafi alkhairi ka kwantar da hankalinka aminina maganar yara bazata raba tsakanina da kaiba
Daddy yace nagode nagode Allaha bar zumunci sai dai kuma ina neman alfarma awajenka
Abba yace tsakaninmu kawuci haka fadi komeneneshi inhar baifi qarfinaba
Daddy yace inason nakoma da fauziyyah amma baxata cigaba da zama awajenaba sai nan da wani lokaci kafinnan nacika alqawarin dana daukarma zuciyata
Nan da kwana hudu mabarukha zata zo kuma sati daya kacal zatayi ta koma dan mijinta zaiyi tafiya zuwa Australia
Toh inso sutafi tare da fauziyyah ta koma makaranta acan wajenta
Shiru Abba yayi kafin yace bakomai Allah ya shige mana gaba damacan ai baa gabana takeba
Cikin farinciki daddy yayi tayiwa Abba godia sannan suka shiga ciki ya gaisa da mama
Sannan yafito ya nufi fada akan bayan sallan laasar zai dawo sutafi
Fauziyyah kuwa tun zuwanta mama take kwakwarta akan anya kuwa lfyrta kalau amma haka taqi fada mama maike faruwa dan har yanzun sai tanaga kamar bahaka bane yayane itama dai batasan yadda zata kwatanta abinba
Abbama daya shigo shiru yayi baice komaiba har daddy ya dawo Abba ya kira fauziyyah ya mata nasiha sosai sannan yace kuma tare zasu koma da daddy
Harga Allah ranta baisoba amma haka ta haqura ta bishi
Bayan suntafi sannan Abba ya mayarma mama abinda ya faru
Nan mama tace batasan zancenba ita atafam saidai adawo mata da yarta tunda abin walaqancine
Ita dama tajima jikinta yana bata ba lafy fauziyyah takeba
Da kyar da nasiha Abba yashawo kanta ta haqura dan yasan zuciyar iyaye mata da rauni take shiyasa bai fada mata ba sai bayan sun tafi ya kuma godema Allah daya bashi ya mai jin maganarsa
Bayan dawowarsu fauziyyah da kwana hudu aunty mabarukha ta zo bauchi ita da yaranta uku dik maza
Ranta ya matuqar baci da taji labarin abinda ya faru
Daddy yace sabida haka nakeso kitafi da fauziyyah wajenki kisama mata makaranta ta koma daga naira 1 zuwa biliyan 1 zan kashe dan fauziyyah tasami ingantaccen ilmi
Aunty mabarukha tace tace insha Allahu daddy namaka alqawarin kula da fauziyyah yadda ko kai idan kaganta sai kasan lalle mace ce mai ilmi
Kuma gashi dama yanzun ne zaa koma first term so kafin hutun ya qare zaa sama mata lesson teacher
Shikuma yaje Allah ya shiryeshi amma saiya ga sakayyah
Cikin jin daddy yace haka nakeso Allah ya taimakemu
Momcy ta shigo nan suka cigaba da tattunawa
Sannan ta kira fauziyyah tafada mata tare da aunty mabarukha zasu tafi
Taji dadin hakan dan gaba daya zaman bauchi ya fita aranta
Ana gobe zasu tafi taroqi momcy tabarta taje gidan aunty niima da kuma gidan khairy
Momcy tace sai dai driver yakaiki gidan khairy amma niima kanma zataxo anjima
Sai dayamma sannan ta shirya ta tafi gidan khairy
Agida tasamu TJ sai taji kamar ta koma dan bata qaunar abinda zai kuma hadata da ya Alamin so dataga TJ sai taga kamar tare data gansu
Bayan sun gaisa TJ yace ashe abinda yafaru kenan Allah yasa haka shiyafi alkhairi amma gaskiya Dr bai kyautaba sam
Murmushi tayi tace lah bakomaifa nihakanma yafimun
TJ yace idan da rabo saiku sasanta kuma shimuke fata
Fauziyyah tace hmmm kaidai mubar maganan nan kawai kada na furta abunda ba kyau
Shiryawa yayi ya fice nan yabarsu da khairy suna tada abinda ya wuce
Sai gab da magriba driver ya dawo daukarta
Sai anan take fadama khairy tazo mata sallama ne amma ta roqeta ko mujinta kada tafadawa gashi gashi
Khairy tamata fatan alkhairy ta rakota har bakin mota sannan ta tafi
Washegari sukabi jirgi sai birnin tarayya Abuja
*****
*2weeks later*
Papa yana kwance yana tunanin sati biyun da yayima juhaina alqawari ya cika kuma har yau daddy bai nemeshiba sai yaji qarar wayarsa
Sai daya tashi zaune ganin sunan maikiransa amma haka ya bude idanunsa da toka ya dau wayar yana cewa
Barka da yamma Abba
Yawwa Alamin ya aiki
Yace lfy lau Abba
Abba yace batun yarinyar da kake so nakira inji awanne gari ko unguwa take dan insha Allahu jibi zamuje maka tambayar
Dik iskancinsa dayaji kunya ta kamashi cikin sanyin murya yace akaduna take
Abba yace toh inyaso kashirya gobe zamu shigo bauchi nida Alhaji Sabo qanin daddyne inyaso jibin sai mu wuce tare dakai harda daddynma
Toh nagode Abba Allah ya qara girma
Abba yace bakomai nan sukayi sallama ya kashe wayar kuma yayi hakane dan jin irin furucin da daddy yayi akan shi baruwansa da wannan auren
Da kyar su Abba suka shawo kan daddy ya amince suka tafi kaduna tare
Atare da papa suka tafi kaduna kuma anmasu tarba ta mutunci nan suka tsaida magana maganar aure nan da wata 1 kacal dan ko wani fanni ashirye suke
Papa da juhaina suna zaune acikin garden din gidansu juhaina ta dubi papa cikin shagwaba tace my king
Naama my queen ya amsa
Tace umm ya maganar dakace kowa gidansa da banne ko inace bakacanzaba
Murmushi yayi ya riqo hannunta yana duban idanunta yace ki kwantar da hankalinki Alamin nakine kekadanki
Cikin rashin fahimta tace kamarya likitana fahimtar dani bakacemun kanada mata ba
Yes amma dakenan yanzu single nake cos na yanka mata red card nata so kinga ni nakine ke kadanki
Nan taji wani dadi ya mamayeta koba komai yanzu aikin dake gabanta ya ragu sai dai tayi qoqarin ganin bai dawo da itaba dan gaskiya batajin zata iya zama da Dr Alamin tana ganinsa da wata mata.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
[3:01PM, 8/19/2017] โช+98 903 074 3573โฌ: ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
3โฃ9โฃ
Washegari dasafe suka biyo jirgi suka dawo bh
Gida papa ya wuce dan Abdu yazo daukarsa
Bayan yayi wanka ya kwanta dan ya huta amma sai da yajima yana waya da queen nasa kafin yayi bacci
Bashi ya tashiba sai wajen5 tukunna
Cikin sauri ya gabatar da sallan laasar sannan kira TJ awaya ya sanar masa yana zuwa gidansa anjima kadan
Sake wanka yayi ya shirya tsaf abinsa ya nufi gidan TJ
Afalo yasamesa shida amarya suna zaune suna kallon wani film a setlite
Fiskannan ba yabo ba fallasa ya qaraso ya zauna
Nan suka kashe hannu
TJ yana cewa ashe kana kusa kenan mutumin
Yace no inafa gida nakira ka kawai dai ban biya ko ina bane
Khairy ce tace ina yini ya Alamin
Lfy lau ya amsa mata
Tashi tayi ta fice kitche ta kawo masa ruwa da juice ,tana ajiyewa ta juya abinta daki dan ita haushi papa yake bata ko yaushe fiska kamar an aiko masa da saqon mutuwa
Ya hanya toh TJ ya tambayesa
Umm normal fa kuma albishirinka
Toh goro fari tass ma kuwa
Papa yace anfa tsaida magana nan da 1 months juhaina tazama mallakina
Kashe hannu sukayi TJ yace shege mutumina kace kawai komai ya kankama
Atare sukayi dariya papa yace kai dai yanzu kawai shiri zamu fara dan kasan dole muyi party kalakala sabida baqin da zasu zo
TJ yace tabbas yanzu dai muje kaci abinci dan nasan kyar inkayi lunch ma inyaso sai muduba muga yadda abin zai kasance dan bama da enough time
Papa yace wlh kuwa kaman zanbiya Eatry sai nace barindai fara zuwa nan sai mufita tare
TJ yace ai zanci abinci saiga wayarka nace toh barin bari saika zo sai muci
Ok muje to,dinning suka qarisa
Ya bubbude masu wamers yace bismillah Dr
Aroma ne yaji ya bugi hancinsa ga kuma ya birgesa a ido nan yadauki plate ya debi white rice wadda taji vegetables da chips sai stew wadda tasha naman dajajatun
Spoon 1 yakai bakinsa yaji abincin yamasa 100๐ฏ
Shiru yayi kawai yanacin abincin dan har yamafi na resturant dayake zuwa cin abinci
Gagara haqura yayi yace man wai a ina kuka sami mai aiki wadda ta iya girki haka
Murmushi TJ yayi yace haba wuce nan nayi aure kuma nazo inacin abincin mai girki never
Papa cikin mamaki yace kana nufin wife nakace tayi wannan girkin
TJ yace yeah itace dan bamuma da mai aiki agidannan komai ita takeyi
Shiru papa yayi yana tunanin wannan yarinyan itace ta iya abinci haka sannan gidan ko ina tsaf sai qamshi kawai , da atunaninsa mai aikice ta gyara gidan dan wannan tayi qanqanta tayi haka sannan kuma yar qauye inama tasan wani gyara haka
Maganar TJ ce ta katse masa tunani yana cewa aikasan Allah nifa kullum sake godema Allah nakeyi
Dan wlh bani da matsalar komai , gata da haquri ga tsafta dik abinda dik abinda nakeso shitakemun
Shiyasa na shafama kaina ruwa na tattara dik wata sabga nafakata a gefe dan wlh yadda yarinyarnan takemun biyayya har kunya nakeji tasan halayena nada kuma kullum inaroqon Allah ya yafemun zunubaina dan da dan hali nane bazan samu ta gariba
Papa yayi shiru yana sauraronsa axuciyarsa yace lalle ashe shima zai more tinda wadda ya auri qaramar yarinya ma gashi dik ya canza sabida kwanciyar hankali baran shida matarsa wayayya wadda ta mallaki hankalin kanta
Nidai Mmn Faty nace lalle dasauranka papa dan abin badaga nan takeba wai andanne ma bodari kai
Suna cikin hiransu wayar daddy ta shigo masa
Hello daddy yafada bayan ya dau wayar
Inaon ganinka yanzun shine abinda daddy yafada masa ya kashecwayarsa
Alamin ya dubi TJ yace man zan wuce yanzun daddyne ya kira kuma yanason ganina
Ok sai gobe insha Allahu zan shigo gida
Harka fara fita kenan
TJ yace no sai nanda two weeks zanje sayama khairy form din school ne
Tabe baki yayi yace ok saika shigo na wuce
Harbakin mota ya rakashi sannan ya tafi
*****
Daddy da momcy suna zaune afalo inda papa yake gefensu azaune yayi shiru yana sauraron daddy
Alamin ya kira sunansa
Naam daddy ya amsa yana kallon daddy
Daddy yace toh nakirakane dan inmaka godia ka kyauta sosai akan abindakayi
Kaci nasara ko ,great ,welldone amma kasani wannan auren tinda kai kaga zaka iya toh kasani ba nairana ko daya da zai shiga ciki
Saika hada masu lefe sannan ka tanadi wajen ajiye matar dan ina buqatar gidana
Papa yace ok daddy wannan bamatsala bace zaayi komai yadda ya dace shikenan zan iya tafiya
Daddy yace eh kana iya tafiya
Bayan ya fita daddy ya dubi momcy yace saudah anya kuwa yaronnan yana cikin hankalinsa
Momcy tace mekagani
Yace gashi baiko damuwa da fushinmu baran yagane abinda yakeyi ba daidai bane
Momcy tace Alhaji nifa abinda yasa kaga nayi shiru bana magana wlh nafiganin laifinmu akan na papa
Daddy yace kamar ya laifinmu kuma
Tace toh icce tun yana qarami ake tankwarashi amma mu dik abinda papa