Showing 69001 words to 72000 words out of 87071 words
yakeyi yana tuna yanayin daya samu kansa aciki
Lalle Allah yayima Fauziyyah baiwa iri da ban da ban
Da tunaninta bacci yayi gaba dashi harda mafarki barkatai
*****
Yana fita tasamu ta miqe da kyar ta shiga cikin bedroom nata
Wanka tayi itam cos taga baqon abu atattare da ita sai anan tadanji qarfin jikinta
Falo tadawo ta zauna bude abinda ya kawo mata
Shawarma ce anade da duminta sai aroma dake tashi
Dayan kuma takeaway na gasmeat ne
Haka taci ta qoshi ta kora ruwa mai sanyi sai bacci nan tashige daki abinta ta kwanta
Sai dai sam bacci ya gagareta sai tunani papa daya addabeta lalle ya alamin ya iya luv abinda tafada aranta kenan
Tundaga ranan tasauya salonta bata taba yadda papa yayi koda qaramin wasa da ita
Daya kusantota zata fara kuka tana cewa idan yana qaunar Allah yarabu da ita tunda ba dole
Shikuma bai kaunar yabata mata rai haka zai kyaleta
Gashi kullum cikin tayar masa da hankali take wajen daukar wanka da kaya masu jan hankali
Kullum burinsa ya kyautata mata aikin gidama kusan 50-50 sukeyi kafin ta tashi zai rigata tashi yayi shara mopping ya kunna burner ko ina ya bule da qamshi
Amma abanza Fauziyyah batada niyyar sauqowama dan yanzu maganama bata cika hadasu ba yayi iyaka yinsa harya haqura ya kyaleta saidai baifasa kyautata mata da fada mata kalamai masu dadi na soyayyah ba
*2months later*
Yanzu kimanin watansu biyu da aure kenan
Kullum papa baida abinda ya fice ganin ya kyautatamata ya sanyata farinciki
Ko office ya fita harya dawo hankalinsa yana gunta
Ya sayo mata wannan wancan dik dan ya birgeta yakeyin hakan
Damuwarsa daya yadda yake fama da shaawarta amma ita batada niyyar saurara masa haka yake danne zuciyarsa
Afannin fauziyyah kuwa tun tanajin wani baqon Alamari gameda papa
Tunbatasan mene neba harta fahimci zuciyarta takamu da sonsa
Ahankali ta fahimci lalle zuciya tana son maisonta kuma mai kyautata mata
Wani irinso takejin tana masa wadda bata taba yima wani mahaluqi ba
Takuma gane ashe yasirma son yarinta tamasa
Saida kuma ta gagara daina quntata masa dikda komai zata masa bai nunawa at last ta realizing cewa lalle papa yanasonta sona haqiqa na gaskiya
Amma ta gagara nuna masa hakan koyaushe saita ringa nuna masa baigabanta sam kuma ta gagara daina hakan dan yanzun dakanta idan tamasa abu saiya dameta taji dama bata aikata hakanba
Amma abubuwa da dama taragemasa tunda idan tamasu abinci komabai kusa data leqa dakinsa dikda iyakarta bakin qofa tace yazo suci abinci sabanin da sai dai insanda yafito dan kansa
Yau dawuri ya taso office itakuma batajeba kasancewar Friday ne
Da yamma lis yasmeta zaune afalo
Barka da hutawa baby yafada fiskansa dauke da qayataccen murmushi
Uhum kawai tafada batareda da ta dago ba daga danna wayarta datake
Barinje gidan aunty naja dagacan zanwuce masjid sai after isha zandawo
Ok kawai tafada shikuma ya wuce dan inda sabo yasaba da halin ko inkula datake nuna masa
Yana wucewa tabi bayansa da kallo harya fice sannan ta zame ta kwanta tana roqon Allah yasa ta sassauta zuciyarta ta kyautatawa mijinta
Yana fita gidan Aunty Naja ya nufa afalo yasameta suna kallo itada da yara kasancewar friday babu islamiyyah
Yana sallama oga ya taso da gudu ya rungumesa yana oyoyo uncle
Papa ya dgashi sama yana cewa oyoyo my boy
Zama yayi ya daura oga akan cinyansa suna gaisawa da aunty
Bayana sun gaisa tacema su sopy oya kuwuce dakinku kuje kuyi kallon acan
Ta dubi oga daya dane cinya tace harkaima dakake wani lafewa tashi kabisu
Papa yace da anbarmin abokuna ai
Tace rabu dashi damunka zaiyi da qiriniya
Bayan sun wucene ta dubi papa tace ya Fauziyyah dai yanzunkam komai normal ko
Dan sosa qeyarsa yayi yana cewa umm ai rikicecciyace ammadai yanzun tarage fitina
Tace banganeba wai haryanzun bakasamo kantaba
Cikin muryar tausayi yace ai aunty rikicinta sai a hankali
Da mamaki ta dubesa tace kada kacemun kaikuma zuba mata idanu kayi kake kallonta
Yace to yazan mata ninafison saita fara sona ta aminta dani
Tace so na biyu ko na nawa ai dik wanda yaje gidanku yazauna daku na awa daya zai fahimci fauziyyaha tana sonka kawai pretending takeyi kaikuma idanunka sun rufe ka kasa fahimtar haka
Yace to nidai kawai ina lallabatane muzauna lfy tinda banida option
Tace kana da option kuma cikin ruwan sanyi zaka samu kanta
Nan tafada masa yadda zaibi
Nidai banji maitaceba dan yadda tayi maganar ahankali
Sai kawai naga yanata dariya dan mganar dariya tabashi
Yace kai aunty bakida dama
Itanma dariya tayi tace kaidai kawai kayi yadda nafada maka
Saida aka kira sallan magriba yatafi
Baikoma gidaba sai bayan da yayi sallan isha tukun
Lokcin daya shigo bata falo yaji dadin haka sai ya wuce dakinsa
Toilet ya shiga yayi wanka da ruwa mai zafin gaske dik da shiba maabocin muamala da ruwa mai zafi bane sosai amma haka ya daure nan jikinsa ya dau dumi
Cikin sauri yasaka kaya ya shige bargo ya rufu
Baifi 5mins ba da kwanciya ta leqo falonsa taga bayanan saita leqo dakinsa taga koya dawo yafito suci abinci
Ahankali ta tura qofar ganin wutan dakin akunne yasa tafahimci ya dawo
Shiga tayi ta tsaya abakin qofa ganinsa akwance akuma qudundune cikin bargo yasa tayi tunanin lfy
Cikin sanyin murya tace kafito muci abinci
Murya na rawa kamar mai zazzabin daya masa mummunan kamu yace kije kici kawai bazan iya ciba
Harya juya saita kasa tafiya dan yadda tai voice nasa tasan ba lfy ba to amma mai yasamesa lokaci guda baicin dazun ya fita lfy lfy ta tambayi kanta
Juyowa tayi ta tako har bakin bed inda yake kwance sai rawar sanyi yake kamar gaske
Nanmada ta tsorata dayanayin data gansa
Hankali tashe tace ya Alamin mene yasa meka
Jin yadda tai maganar adame yasan tarkonsa ya kama bushiya
Sake shaqe murya yayi yace baby am sick banajin dadi fever ke damina
Fever tafada tana zare idanu
Daga kansa yayi irin bai iya amsawannan
Nam take taji wani tausayinsa ya dirar mata dan bata taba ganinsa cikin wannan yanayi hakaba
Sannu Allah ya sauwaqa amma lfy kafita ko dama kanajinsa ajikinka
Tai magnar tana miqa hannunta jikin wuyansa ta taba
Nan taji zafi zau.....
*Gaisuwa mai tarin yawa agareki Auntyn Papa Mmn Faty ta๐๐ป*
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
6โฃ4โฃ
Wani sabon tausayinsane ya dirar mata lokaci guda
Banda shaking ba abinda jikinsa keyi, kansa kawai ya iya gyada mata
Haka kawai taji bazata iya tafiya ta barshi awannan yanayinba
Zama tayi akan bedside drawer tadaura hannunta akan goshinsa
Murya ahankali tace toh kanemi magani kasha kaji tafada tana kallonsa
Murya ashaqe yace nasha bayan nashigo
Cikin tausayi tace toh Allah ya sauwaqa
Ganin yadda gabadaya yanayinta ya sauya ta shiga damuwa sai kawai yadan razana kamar wani abin tsoro yagani
Cikin sauri ta riqosa ta qanqamesa tana cewa subhanalillahi ya Alamin menene?
Sake razana yayi ya qanqameta shima aifa nan tafara kuka hawaye wani nabin wani tana cewa meya sameka kamin magana mana sai kuka take dik tafirgita da yanayinsa
Yadda hankalinta ya tashi sosai saiyaji tausayinta ya kamasa
Ahankali yake cemata relax baby ba abinda zaisameni haka fever na yake so ki kwantar da hankali kinji
Da muryar kuka tace aa kam kodai nakira momcy awayane akaika hospital
Aa baby kada kitayar masu da hankali nafarajin sauqi ma da yardar Allah zansami sauqi
Ganin yafara samun natsuwa ya kuma rungumeta ya lafe ajikinta yana sauqe numfashi yasa tadan tsagaita da kukan amma batabar hawayeba
Sunkai 10mins ahaka kafin ahankali yace baby zafi nakeji sosai
Zafi kakeji ya Alamin tafada tana goge masa zufan goshinsa
Gyada kansa yayi yace sosaima
Yaye masa blanket din tayi ganin dik jikinsa ya jike da zufa irin alamun sauqan zazzabi
Tace Alhamdulillah aizafin nasauqan zazzabin ne sannu ya Alamin Allah ya sauwaqa
Lumshe idanunsa yayi yace Amin baby nagode da kulawarki gareni
Murmushi mai sanyi tamasa tace bakomai kona qaramaka qarfin AC dinne
Yace qaramun baby , toh tafada tadauki remote din taqara masa qarfin AC din
Nan da nan sanyi mai dadi ya karade dakin
Cikin kulawa tace ko zakayi wankane kadan sami qarfin jikinka
Kwantarda kansa yayi akan laps nata yace as u wish baby amma banjin qarfin jikinane yanzun
Ayyah sorry kasan jiki da jini barin hada maka ruwan wankan ko
Amma banson warm water baby
Tace i know but tinda da fever ajikinka kada yakuma dawomaka dashi
Cikin shagwaba kamar qaramin yaro yace pls baby Allah banson ruwan zafi
Tace is ok shikenan barinzo nan tazame kansa ahankali ta daura akan pillow ta fice toilet
Yaune shigarta na farko toilet dinsa nan takuma tabbatar lalle ya Alamin mutum ne mai tsabtar gaske komai tsaf saikace baa amfani dashi
Bathtub ta cika masa da ruwa tasaka masa turaren wankansa sannan ta fito da towel ahannunta
Tsayawa tayi akusa dashi tace ya Alamin shiru bai amsaba sake kiransa tayi akaro nabiyu
Uum yafada yana bude lumsassun idanunsa
Jikinne ta tambayesa
No kawai banjin karfin jikinane yafada
Let me help u tafada tana miqo masa hannunta kan ya riqe
Aiko bai bata lokaciba ya riqe tattausan hannunta ya tashi ahankaki tana riqe da towel din tarakasa har toilet
Miqa masa towel din tayi sannan ta fice cikin sauri
Murmushi yayi ganin haqansa ya kusa cimma ruwa ya kuma gaskata maganar Aunty Naja dan tabbas yanda tanuna damuwarta qarara akansa hakan ya nuna tana sonsane
Baiwani jimaba ya fito daure da towel a waist nasa
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta
Basarwa yayi kamar baisana da itaba ya wuce yadan shafa cream kadan ya fesa spray ajikinsa
Wasu kayan shan iska ya saka kafin ya dawo kusa da ita ya kwanta gamida lumshe idanunsa
Ya Alamin muje kadanci wani abin mana kada ka kwanta da yunwa
No bani shaawan komai baby just black tea nake buqata
Marairaice murya tayi tace aa pls don't say that mana kobayawa kadanci inyaso saina hada maka black tea n inbakason fitane nakawo maka nan inyaso
Dan yamutsa fiska yayi yace shikenan muje toh amma saidai kidan riqemun hannuna cos am feeling dizzy
Allah barin kawo maka nan idan bazaka iya zuwaba
Aa muje kawai yafada yana yunqurin tashi zaune
Tana riqe da hannunsa suka fito har dinning room
Nan tayi serving nasa kafin itama tadan zuba kadan dan batajin cin abincin itama
Kawai dan yadancine yasa itama tadan zuba
Bayan sun kammala wadda dukkanninsu kowa yadan chakulane ya bari
Bayan yasha tea din tace zaka koma dakine
Aa muje falo dai nadan kwanta acan
Ok tafada kafin suka koma falo shiya kwanta itakuma tana zaune agefensa sai faman sannu take masa
Can taji yayi shiru irin bacci yadan daukesa while idanunsa biyu likimo kawai yayi
Xubama kyakykyawar fiskansa idanu tayi tana jin wani sabon sonsa da tausayinsa suna ratsata
Sunjima ahaka hartafara jin bacci shikuma dagangan yaqi ya tashi yafison tagaji danknta
Ganin bacci na neman kwasheta awajen yasa tasa hannunta tadan bubbuga hannunsa
Ya Alamin katshi ka koma daki kada jikinka yayi ciwo
Bude idanunsa yayi ahankali cikin murya kamar mai bacci yace umum kibarni kawai anan zankwana
Anan kuma?ta tambayesa
Umm anan zan kwanta bani shaawan kwana a room nawa har garamun nan
Shiru tadanyi harga Allah ita bacci takeji kuma bazata iya tafiya tabarsa afalo shikadai ba ga ba lfy ce dashi ba
Cikin sigan lallami tace haba ya Alamin taya zaka kwana anan baicin dik yawan dakunan gidan nan
Idan can baimakaba saika canza wani dakin bawai ka kwanta anan ba
Sai dai muje room naki ya fada kansa tsaye
Shiru danyi tana nazarin maganarsa
No kada kisama kanki tunani kije ki kwanta abinki sai da safe yana fadin haka ya juya mata baya
Shiru ta danyi nadan lokaci kafin murya asanyaye tace katashi to muje
Aa barin takureki bafa kije kawai abinki
Umum baka takurenba muje ka kwanta acan din badamuwa
Yunqurawa yayi ya miqe zaune tare da miqo mata hannunsa
Riqesa tayi ya miqe ta kashe komai suka wuce
Har bakin gado takaisa saida ya kwanta sannan ta juya nan ta tsinkayi muryarsa yana cewa inazaki
Batare da tajuyo ba tace zancanza kaya nane ta wuce ta dauki kayan baccinta ta shige toilet
Acan ta canza kayanta sannan ta fito blanket ta dauka ta nufi kan sofa ta kwanta
Dik abinda take yana kallonta
Mene haka kuma zakije can kikwanta
Eh kai ka kwanta akan bed ni nanma ya isheni tafada tana lulluban jikinta
Tashi zaune yayi yace aa kam keda dakinki barinzo intakurekiba, kidawo nan sai ni na koma falo inyaso inkuma ba hakaba kizo kikwanta abinki, inbakuma guduna kikeba
Tace ya Alamin na roqeka ka kwanta abinka ni hakanm yamun
Ganin ya miqe dagaske zaifita yasa tace shikenan zandawo ka kwanta toh
Tasowa tayi tawuce can qarshen gado ta kwanta sannan shima yazo ya kwanta abaki baki
Amma yana tunanin hanyar da zaibi ya jawota jikinsa
Itakuma tana kwanciya bada jimawaba bacci ya dauketa
Kamar amafarki taji nishin mutum kuma bana lfy ba cikin firgita ta tashi zaune ta waiwaya ind yake kwance
Nan taganshi qudundune acikin blanket sai rawan sanyi yake yana nishi samasama
Batasan sanda ta isa gabansaba tana kiran sunansa ya Alamin jikinne ganin ya gagara amsa mata kawai saita fashe da kuka tana cewa saida nace inkira momcy ka hana yanzun gashi dare yafara yazanyi
Murya ashaqe yace sanyi nakeji pls kitaimakamun sanyi
Tace inqara maka bargonne, murya narawa yace koma mene kimun kitaremun sanyin nan
Qara masa bargon tayi amma still baidaina shaking ba
Hankalinta inyayi dubu ya tashi sai hawaye datakeyi wani nabin wani
Cikin kuka tace katashi mutafo asibiti kaji
Girgiza mata kai yayi yace yace aa sanyi kawai nakeji banjin zazzabin
Tace ai shine alamun zazzabin nanan kenan nidai mutafi asbiti adubaka
Yace aa abu daya zakimun nasamu sauqin sanyinnan shine dumin jikinki pls ki kwanta ajikina
Ba musu ta yaye bargon zata kwanta yace saikin cire rigarki sannan nasamu dumin jikinki
Tsabar yadda take adame ganin halin dayake ciki batai musuba ta cire doguwar rigar baccin dake jikinta ta kwanta ajikinsa
Lumshe idanu yayi yana jin sauqan niima har cikin bargonsa
Gyara kwanciyarsa yayi ya matseta sosai akan qirjinsa lokaci guda yaji wani kasala ya dirar masa har idanunsa na rufuwa
Itama wani yanayi ta tsinci kanta aciki amma ganin yadda yake cikin halin rashin lfy saita haqura ta kwanta sosai
Ahankali hankali yadaina rawan sanyin ya kuma daidaita natsuwarsa dan bacci sosai yafaraji
Itama bada jimawaba baccin yasake dauketa
Ranan shima kwanan farin ciki yayi koba komai yanzun yana ganin nesa tazo kusa
Sassanyar iskan sanyin asubane daya karade sararin samaniya wanda ya sanadin sanyaya duniyar baki daya shiya qara sanyaya dakin daya hadu da sanyin AC
Hakan yasa taji sanyi yamata yawa har yayi sanadiyar farkawarta
Sannu ahankali ta bude idanunta nan taganta kwance tayi daidai ajikin papa
Yinquri tayi cikin sauri zata matsa sai taga ya motsa aifa nan tasake lafewa ajikinsa dan batason yafarka yagan ta awannan yanayin
Daga ita sai dan guntun wando ajikinta.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Fat Mmn Faty
September, 2017
6โฃ5โฃ
Batasan cewar ya rigata farkawaba kawai baison jikinsu ya rabune yasa yayi kamar bacci yake
Cikin dabara ahankali ta zame jikinta daga nasa ta jawo rigarta ta saka
Lallabawa tayi ta sauqa ta nufi toilet Alawala tayi tadawo tafara sallolinta kamar yadda tasaba
Shikuma tun data tashi yaqura mata idanu yana kallonta harta shige toilet
Lumshe idanunsa yayi yana yaba surar da Allah yai mata, wani murmushi yasaki daya tuno yanayin qirjinta
Ganin har zai makara sallan asuba yasa shima ya miqe Ahankali ya fice dakinsa
Wanka yayi sannan ya daura alawala ya fito yayi sallansa adaki
Sai wajen 6 sannan ya dawo room nata lokacin ta idar da adduointa tana ninke sallayan
Bakin bed ya qarasa ya zauna saidata maida komai wajen zamansa sannan ta dawo ta zauna aqasa jikin qafafunsa
Murya Ahankali tace ina kwana ya Alamin
Da murmushi afiskansa yace lfy lau babyna
Ya jiki?tafada ahankali
Dasauqi sosai baby dafatan kintashi lfy daiko
Tace lfy Allah ya sauwaqa
Amin yafada yana kallon yadda ta sunkui da kanta irin batason su hada idanun nan
Baby ya kira sunanta da wani salo
Har cikin zuciyarta taji sautin muryarsa,naam ta amsa asansaye
Taso kiji wata magana
Babu musu ta dawo gefensa ta zauna
Zamewa yayi ya kwanta akan laps nata cikin sanyin murya yace baby nagode nagode da kulawar da kika bani Allah yabani ikon kyautata maki nima
Murmushi tayi dan taji dadin kalamansa tace bakomai ai haqqinane na kula da kai lokacin dakake buqatar hakan
Yace toh nagode
Dame zakayi break nadafa maka ta tambayesa
Shiru ya danyi yace nibanjin shaawan komai dan nayi loosing apatatide
Da muryar lallami tana dan shafa kansa tace haba dai daurewa zakayi badan dadiba kadanci wani abin
Aidai bai yiyuwa kazauna da yunwa daiko
Dan yatsina fiska yayi yace shikenan naji
Tace to mezakaci
Anything ya amsa yana lumshe idanunsa dan yanajin dadin yadda take sosa masa kansa
Shikenan barinje nadanyi aiki, aa baby kibari bayanzuba mana
Tace toh shikenan naji
Dahaka har bacci ya daukesa sannan tazameshi ahankali tafice danyin ayyukanta
Sai 10 taqare komai tadawo dan tayi wanka nan ta tarar baya dakinta
Wanka tayi fess tafito ta shirya cikin atampa dinkin doguwar riga wanda tamata matuqar kyau
Dinkin yazauna sosai ajikinta kamar kasaceta ka gudu haka tayi kyau
Fitowa tayi sai qamshin humra ke tashi ajikinta ta nufi dakin papa kan yafito ya karya
Tasaka hannu zata bude qofar falon shikuma ya rigada ya bude aiko saita afko ciki dan tabada qarfinta wajen jingina ajikin qofar
Nan tafada kan faffadan qirjinsa tana sauqe numfashi dan ta tsorata, zatonta aqasa data fadi
Shikuma tana sauqa kan qirjinsa ya shaqi wani niimtaccen kamshinda ya haifarmasa da kasala lokaci guda
Hannunsa ya daura akan bayanta yace am so sorry baby bansan kina wajenba
Kanta ta kwantar sosai ajikinsa kafin tace bakomai nasan bakasaniba ai ammafa na tsorata
Eyyer am sorry my dear kada kitsorata am here kinji
Kanta ta gyada kawai sabida yadda yake wani shafan kunnenta da hannunsa harya gangaro zuwa wuyanta
Cikin wata iriyar murya saitin kunnenta yace baby sarqannan tamiki kyau sosaifa yana shafan jikin wuyanta
Wani yarr taji harcikin jikinta yadda yake maganar yana wani shafanta kasa jurewa tayi cikin qarfin hali tace ur breakfast is ready
Ok thanks a lot mujeko yasake maqaleta ajikinsa
Ahaka suka sauqo sai wani shafata yake yana sunsunan jikinta kaman wani sabon maye itakuma dik jikinta yasake tawani lafe ajikinsa
Kujera ta jawo masa ya zauna sannan itama ta zauna agefensa
Faten irish potatoe tamasa mai dan ruwaruwa yasha alayyahu da hanta irin namarasa lfyn nan
Zuba masa tayi tace bismillah maqe kafada yayi yace umum
Tace why tana kallonsa
Yace saidai muci tare
Murmushi tayi tace toh muci, tare sukaci yana cewa ya qoshi tana lallaminsa ya daure yaci
Batasan cewar dadin abincin yakeji sosaiba kawai yana pretending ne irin patient dinnan lol
Bayan sungama ta tattara wajen suka