Showing 15001 words to 18000 words out of 144367 words
yana xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “mahaifina ne ya je garinsu sofi yawon fatauci, tun yana yaro yake bin mahaifinsa suke xuwa tare har yake xuwa shi kadai daya gane hanya, suna shiga da kayanmu na nan gida Nigeria can su sayar sannan su kawo na can su shigo das hi ta a haka suka hadu. Aure kamar xai yiwu kamar ba xai yi wu ba, Allah Yasa ya yiyu aka yin ammadukka bangarorin biyu ba’a son ransu ba a bangarensa da bangarenta.
A bangaren su sofi suna ganin hatsari ne su dauki ‘yarsu su bawa bako wanda ba’a san asalinsa ba, haka suma danginsa suke ganin duk ‘yan matan das u ke xangon dauura ya rasa wacce xai aura sai ya fita wata kasar sannan xai yi aure. Karfin addu’arsu su masoyan da tsananin rabon haihuwa daya rantse sai aka yarda aka daura auren. Amma fad a farko dangin sofi basu yarda ya taho da ita ba sai dai ya kama haya a can ya ajiye ta, yana xuwa yana dawowa said a ta shekara sannan suka yaba da hankalinsa na ladabi, amana da rikon gaskiya. sannan aka sami wadanda suka san asalinsa ‘yan xangon daura amma maxauna garin su sofi sun yi gidaje, sun yi aure, sun hayayyafa sannan aka bari ya taho da ita. ‘yan uwanta suka rako ta har xangon daura suka ga mahallinta da ‘yan uwansa sannan suka tafi suka bar ta a lokacin tana dauke da karamin cikina.”
Madina ta nisa t ace “to naji yadda iyayenki suka hadu har suka yi aure. Da babanki ki ka yi kama ko da mamarki!”
Tambayar madina ta bawa kaltum dariya, sai ta kyalkyale da dariya sannan t ace, “da mama na nayi kama sak babu inda na baro ta, idan kika ganta kika ganni idan baki lura ba sai ki kira tad a sunana ko ki kirani da sunanta saboda bat a da kiba kma ba tsufa ba. Kamar yadda na fada miki fulanin Cameroon ne danginta kyawawa ne masu tsananin farar fata sai ka dauka larabawa ne, gashinsu har baya. Banyi kama da mahaifi nab a kwata kwata saboda shi baki ne, amman kanne na biyu sun yi kama das hi sak”
Madina tayi murmushi t ace “yaya xaman sofi ya kasance a xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “gidan kasa da katangar xana gadon mahaifi na ke nan anan aka kai sofi, tana xaune a daki daya, goggo fattu a daki daya don a shekarar da aka yi auren baba na mahaifinsa ya rasu. Don haka goggo fattu ta sami filin casa sofi da saleh, sai yadda take so xa’a yi, sai abinda t ace xa suyi. Babu wahalar da sofi bata sha ba, ga cikin fari a wajen yarinya ‘yar shekara goma sha hudu, har ciki ya tsufa kuma ta hana a kai ta garinsu ta haihu. Da watan haihuwarta ya kama kawu jalo ya aiko da matarsa Asta da ‘yarsa Ladi su xo su dauko safi ta haihu a gida amma goggo fattu tayi musu dadin baki luf luf wai sofi ‘yar t ace tamkar wacce ta Haifa a cikinta don haka su bar ta a wajenta xata kula da ita sosai. A haka suka hakura suka tafi suka bar ta suna ta yabon kirkin goggo fattu, ita kuwa sofi tsoro ya hana ta fada musu gaskiya.
A cikin dare nakuda ta tashi sofi daga barci sai ita sai saleh, tashin farko daman dakin goggo fattu saleh ya nufa da gudu ya buga mata kofa ya sanar mata cewar sofi tana nakuda. Ta xage shi tsaf wai bashi da kunya meye abin gigicewa har ya fada da bakinsa matarsa tana nakuda. Ya sunkuyar da kai kasa yana bata hakuri, ta umurce shi day a fice daga gidan kada ya dawo sai gobe da safe.
Yana fita ta rufe kofar gidan sannan ta leka dakin sofi ta isketa a tsugunne ita kadai tana murkususu, tana ganin goggo fattu sai ta fashe da kuka ta hau kiran sunanta, amma goggo fattu ta tabe baki t ace “ki bar kiran sunana ma don ba xan shigo inyi ta fama da ke har gari yaw aye ba, haihuwar da bata da tabbas xata fito ko ba xata fito yanxu ba.”
Ta juya ta koma dakin ta tayi kwanciyar tat a bar ta a wannan halin. Allah cikin ikon Sa ta haihu ita kadai, jaririya ta fito fuk akan tabarma gtana tsala kuka haka mabiya ma ta fito . sofi ta rasa yadda xata yi da ni sai ta sami leda ta kwashe mabiyar da jaririyar ta rufe a leda fuskata ce kadai a bud eta dora ni akan gado ta xauna a gefena tana ta kuka har gari yaw aye tangarai sannan goggo fattu ta shigo dakin ta iske halin da muke ciki. Jaririya a kunshe a leda ga cibiya nan ba’a yanke ba a jikin mahaifar sai jini jage jage. Duk idanuwana, hanci na da kunnuwana duk busashshen jini ne.
Ta dau dogon salati ta dinga dimawa sofi duka a baya tana kiranta munafuka so take ta ja mata xagi a gari a c eta kasheta ta kasha jaririyar. Wai me yasa da haihuwa ta xo bata kwalla mata kira ba ko ta xo ta kira tad a kanta ba, xata xo ta kunshe ‘ya a leda ba’a yanke mahaifa ba alhali mahaifa shanye jini take.
Tayi tax age xagenta tana borin kunya sannan ta yanke cibiya, tayi ma ‘yar wanka ta gyara mai jegon sannan ta bude gida mahaifina ya shigo ya iskemu tsaf.
Haka danginsu su kayi tayi mata sannu da kokari yadda ta karbi haihuwar sofi tamkar ‘yar cikinta don sun iske mai jego sumul da jaririyarta kalau.
Bayan an yi suna aka saka min Ummu Kaltum sunana da goggo fattu ta xabar musu kenan wai sunan mahaifiyarta ne, basu isa su saka sunan mahaifansu bad a suka rasu tuntini. Sai dangin sofi suka xo suka dage xasu tafi da ita da kyar goggo fattu ta bari suka tafi da ita, mahaifina ya fi son haka daman. Bata dawo ba said a nayi wata uku nayi kwari sannan muka dawo xangon daura tun daga lokacin na fara shiga halin da nake har yanxu yak e bibiyata a rayuwata.”
Tab ashe haka wasu suke da busashshen imani!!!
Allah Ka sanya mu pi karpin xukatan mu, sannan Ka dada kare mu daga sharrin miyagu.
Se a saurara nan gaba domin jin yadda ta
ADON DAWA 7
.
.
“kamar yaya halinda kike ciki har yanxu yake bibiyarki!”madina ta tambaya cikin rudani kaltum ta xubo da hawayenn daya cika mata ido tace “goggo fattu ta hana mahaifina ya dauke ni balle yayi min wasa ko ya rungume ni mu shaku. Ko kallona yayi sai ta dauki dogon salati kai kace mutum ya kashe. Ta ce wannan ai rashin kunya ne don haka kwata kwata baya kusanta ta. Haka mahaifiyata bayan nono da xata bani babu sauran soyayyar uwa da ‘yarta, idan kuwa ta cika daukana da tattalina sai xagi da Allah wadai take yi mata kala kala. Komai aka yi da ni, sai goggo fattu tace rashin kunya ne.
Wata rana har kuka goggo fattu ta ke saka musu, ta ce dan bata da haihuwa,a haka iyayena suka kyaleni, sai yanda goggo fattu ta yi da ni.kar ki dauka kulawar take bani, sai ta ajiye ni a dakinta in ta kuka, sai taga dama sannan tace sofi ta dauke nita bani nono. Har aka yaye ni na bar dakin mahaifana xuwa dakin goggo fattu, ba komai kuma take min ba sai duka da rankwashi musamman idan nayi fitsarin kwance, aka ce komai sanyin asuba xata kore ni waje tsirara bayan ta xane ni.
A lokacin karayar arxikii ta far wa baba na bashi da cin yau bare na gobe sai ya nemi shawara xai sayar da kiwonsa da mahaifinsa ya bar masa gado, akuyoyi da yawa da gonaki xai yi jari, sai ta ki amincewa t ace bakin ciki yake yi don ta xuba nata kiwon a cikin nasa shine yake so ya tona mata asiri a garin ace daman duk tulin akuyoyin nan ba nata ba ne don tayi karya t ace duk nata ne. muka dade cikin rashi da fatara da yunwa har Allah Yasa kawu Isiya kanin mahaifin babana ne yayi masa hanya ya samu aikin gadi a kano,ya tafi kano amma ya bar iyalansa a xangon daura.”
Madina ta gyara xama ta gyada kai ta ce “lallai yanxu xa’a fara labari. Daga nan yaya aka yi? ”
Kaltun ta girgixa kai ta ci gaba da Magana cikin marainiya murya ta ce “duk karshen wata yake xuwa ya kawo mana kudi albashinsa don mu ci abinci amma yana tafiya xata juya akalar kudin tayi sha’anin gabanta dasu .kuli –kuli guda uku shine bincin mu na rana, tuwon dawa da miyar kuka lami ko wace babu shine abincin dare, dumamensa sine abincinmu na safe.Duk muka rame muka lalace ita kuwa har tsire da kaxa take ci acikin shinkafa muna kallonta.
Da mahaifina yaga alamar mun rame sai ya dinga tambayar mahaifiyata ko lafiya muke rame wa?
Ta boye masa don itama irin halinta kenan ba xa ta yi Magana ba ko abu xai kashe ta, sai a makwabta aka fada masa duk abunda yake faruwa damu. Ya samu goggo fattu yace yana so ya tafi kano da sofi itama ta samu aikin wanke-wanke da shara duk wata xasu dinga hado mata albashinsu duka suna kawo mana ni da ita. Tuni ta amince sofi tabi mijinta suka tafi kano suka barni cikin wahala Kaman ta kashe ni tsunma ma ya fi ni nauyi, ga ciwuka kala-kala kullum.
Mahaifina bai fasa xuwa ba, duk wata xai shiga mota ya xo xango daura ya kawo kudin albashinsa fiye da rabi. Ina ganinsa sai in hau murna ina kiran “ga baba, ga baba.” Amma sai ya ture ni gefe in fadi kasa, ya dauke kansa baya kallon in da nake saboda kada goggo fattu t ace yayi rashen kunya.
Ina shekara uku yunwa da ciwon kyanda suka sa ni a gaba na rame sai kashi da fata, ido yayi min xuru –xuru kamar mai ciwon kanjamau sai ka kirga kashushuwan dake kirjina. Sai in suma sau biyar a rana wanar ba xan rayu ba sai ta ji tsoro kar in mutu a hannunta don haka sai ta nemi kawu isiya ya kawo mu har gidan da mahaifina yake gadi, suka ci sa’a kuwa a boy’s kuarter gidan suke xaune da mahaifiyata.
Ta hau fada hard a kumfar baki tana cewa sun gudo kano sun xo sun kwanta sun bar ta da wahala tana fama da ‘yarsu ko barchi bata yi, don haka ga ‘yar sunan su rike kayansu. Ta jankwabar dani da kayana ta juya ta tafiyarta, suna binta suna rokonta ta xo ta huta ta ci abinci, tace ba xata dawo ba dole ta tilastawa kawu isiya dole ya taso suka hau mota suka koma xangon daura.”
Madina ta girgixa kai t ace “daman haka halin goggo fattu yake! Ni fa na yi mamakin ace kaka ce take tsangwamar jikarta haka yadda naga tana kyararki a mota.”
Kaltum ta surnano da hawaye ta cika mata ido ta ci gaba da cewa “mai gidan da muke gidansa sunanasa Alh Adnan Mahbub, shi da matarsa Salaha sai ‘dan su daya Mashkur. Mashkur sa’ana ne shima a lokacin shekarunsa uku kamar yadda shekaruna uku cur a duniya. Alh Adnan yana da arxiki mai yawa duk da matashi ne a lokacin, aurensa ne na fari kuma haihuwarsa c eta fari bai wuce shekaru talatin ba aduniya, matarsa kuwa baxata wuce shekaru ashirin da uku ba don da haka kusan sun girmi iyayena ma. Suna xaune a kataferen gidan, kerarre mai girman gaske yayin da mu kuma muke xaune a boys quarters in gidan.
Alh Adanan na ganin halinda nake ciki na rashin lafiya sai ya ji hankalinsa ya tashi ya umurci direban saya dauke mu ya kai mu asibiti ni da mahaifana. Ya ce ayi duk abinda ya kamata ayi xai biya ko nawa ne. asibitin nasarawa aka kai ni a lokacin shine asibitin da yake tashe sai dan wane da wane. Likita na ganin yanayin jikina sai ya bamu gado muka kwanta aka dinga kara min ruwa da allurai. Allah cikin ikon Sa kafin sati guda na murmure, shi yasa aka ce kowace cuta da maganinta. Na samu sauki har na fara tashi xaune ina surutu kuma komai aka bani ina ci. Kusan kullum Alh Adnan da matarsa salaha suna xuwa su gaishe ni a asibitin bayan kayan dadi na marmari da abinci iri-iri da suke yini suna aiko direba yana kawo mana asibiti.”
Madina tace “gaskiya wadannan iyayen gidan naku suna da kiriki.”
Kaltum tayi murmushi tace “suna da matukar kirki shi da matarsa dukka. Bayan an sallamo mu mun dawo gida sai muka ci gaba da rayuwarmu a gidan, ina matukar jin dadin gidan saboda na samu walwala ba’a dukana, babu yunwa, ba babu hantara.
Makaranta mai tsadar gaske aka sani.
Madina tace “Allah kenan, haka yake ikonSa.”
Kaltum tayi murmushi tace “na tsinci kaina mai farin ciki matuka sai dai matsala daya data addabe ni itace bana samun kulawar iyayena. Ba kulawar rashin wanka da wanki ba ne, kuma ba matsalar abinci ba ne, basa hira da ni, haka basa saurarona, ko na matso kusa dasu saisu matsa saboda wancen ra’ayin da goggo fattu ta cusa musu.”
Madina tace “ban fahimci basa sauraronki ba, kamar yaya? ”
Kaltum t ace “kunyata su ke ji saboda ni ‘yar farice don haka na xama tamkar mujiya a tsakiyarsu sai kallo da ido. Ina matsowa kusa dasu saisu ture ni ko su tashi daga wajen, idan na taho musu da hira saisu gwale ni ba xasu saurareni ba. Idan xan yini ina kuka babu wanda xai lallashe ni a cikin su. Har ‘yan gidan suka fara fuskantar hakan, Alh Adnan ya dinga yiwa mahaifana nasiha yana nuna masa wannan kunyar da yake yiwa ‘yar fari ba’abun burgewa ba ne illa jahilci da cutar kai.
Akwai wata ranar asabar ba xan taba mantawa ba da sassafe misalin karfe takwas, a lokacin ana tsananin sanyi. Ni da mushkur muka fito bakin get wajen da babana yake xaune yana jin dumi da itace, yayin daya rufa da burgujejen bargo. Yana ganinmu ya tabbatar sulalowa mukayi muka fito ba tare da sanin iyayenmu mata ba, saboda ko rigar sanyi babu a jikinmu, ba hula, ba takalmi daga ni sai yar yaloluwar singileti da pant, haka mushkur daga shi sai karamar jallabiya ba dogon wando. Ana tsananin hunturu, mai tafe da haxo, da iska mai kura don haka hanci da ido sai xuba suke yi, yayin da duk ilahirin tsikar jikinmu ta tattashi.
Babana na ganinmu sai ya kira mushkur ya dauke shi akan cinyar sa ya rungume, ya lullube shi da bargo, yayin daya juyar dashi saitin garwashi suka yi ta jin dumi, suka juya min baya. Ina xaune akan benci a bayansu ina ta makerketa ban isa in kutsa cikin bargon ba saboda nasan hantara ta xai yi ya kore ni.
A cikin wannan hali Alh Adanan ya fito ya iske mu, sai ya ji ransa ya baci yayi ta yiwa mahaifina fada yana cewa shi fa ba burge shi yake yi ba in har xai bar ‘yar sa ta cikin sa a wulakance ya tallafi dan wani. In har iyayena basu shaku da ni ba to ina xansa raina, ya kwatanta wannan abunda suke yi da suna ADON DAWA wato gida bai wadata ba an wadata waje ma’ana ya wulakanta ‘yarsa ya tallafi bare.
Alh Adnan ya dauke ni ya rungume ni ya shiga da ni cikin falonsa ya dauki bargonsa ya lullube ni yayin daya kunna min room heater jin dumi ta lantarki. Yana lallashi na, ya bani biskit da alewa, har said a ya tabbatar hantsi yayi, sanyin safiya ya lafa sannan y ace in je gida ayi min wanka a saka min kayan sanyi. Haka shima mushkur yake samun wannan gata daga wajen mahaifana har goyon sa mama na keyi amma ni ban isa matsowa kusa da ita ba.
Dan haka na kasance ako da yaushe ina hanyar bangaren daddyn mushkur. Ina tashi daga barci wani lokacin ko karyawa bana yi sai in yi wuf nagudu wajensa, sai dai idan ban ci sa’a ba nayi karo da maman mushkur sai ta kora ni gida, idan kuwa tana kicin ko ban daki tuni na isa gare shi a falonsa ko akan gadonsa, yana gani na sai ya rungume ni ko daga ni sama cimak, ya wujijjiga ni in yi ta dariya.
Musamman saboda ni yake ajiye katan katan din alewa da biskit da kananan kwalayen lemuna. Ko da yaushe ka ganni ina ciye ciye, baya ga karatun boko dana arabiya da yake koya min. ya na sona saboda ina son karatu, kuma ina son in koya.
Ko da yaushe ina tambayarsa abun da ban gane ba haka duk abun daya koya min duk daren dadewa ya tambaye ni sai na fada masa bana mantawa, in da ya kara sona kenan.
Sabanin dansa wanda ya tsani karatu don haka ma basa shiri da uban. Gashi ina da tsananin wayo kamar ba ‘yar fari ba, ga ladabi da biyayya, na iya hira tatsuniya kala-kala da labarum nake bashi yayi ta dariya ya na tuntsurewa da dariya tamkar yana hira a cikin abokansa.
Amma fa bana labarin da kowa saishi kadai, idan baya nan sai ka rantse ni doluwa ce don bana Magana, sai kallo da ido a gidanmu saboda bana hira da iyayena. Don haka duk sanda daddy yayi tafiya kwana biyu sai kowa ya gane bana jin dadin rayuwata. Jikina sai yayi sanyi, in kaura bakin get ina duban hanya musamman idan na ji karar mota sai in xankada da gudu in leka, idan naga bashi ba ne sai raina ya baci ko kuma in fashe da kuka. Idan kuwa na ci sa’a shi din ne sai in yi ta tsalle da ihu don murna yayin da nake fara xaxxago masa labaru iri-iri dana tattara ina jira ya xo in fada masa.”
Kaltum tayi shiru tana matse hawaye, yayin da madina ta tsura mata ido tana yi mata kallon tausayi.
Madina ta nisa tace “ikon Allah idan da ranka babu abunda baxa ka jiba. yaya kuka kasance?