Showing 36001 words to 39000 words out of 144367 words

Chapter 13 - ADON DAWA

Unknown   

30 Oct 2024

5079

ya mutu. Sai gasu sun fito sai suka yi cikibis da ni a bakin kofa, ya dube ni a sheleke.
Ya ce “kukan me kike yi?
Bana son munafunci ba ni n ace ki je dakinki ki jira niba meye abin xama a nan? ”
Na share hwaye n ace “tasi’u me nayi maka a duniya ka tsanani?
Me nake yi maka yanxu wanda a da bana yi maka yanxu, dan in sani in daina. Tasi’u yanxu baka tausayina ashe, baka nadamar abinda kake yi min ashe?
Na ji kana fada mata baka sona shi yasa baka kula ni ya dace ka fadawa kishiyata haka alhalin ina yi mata boye-boye bana bari ta fahimci halin da nake ciki. Ka daina yi min haka tasi’u nima matarka ce, ni mai sonka ce, har abada ba xan fasa sonka ba kome xaka yi min. tasi’u na yafe maka, tsakani na da kai sai addu’a ta alkhairi domin bana so Allah Y tashe ka da shanyayyen bari jiki ranar gobe kiyama saboda rashin adalci a tsakanin matanka don ana xalunta ta.”
Da alama jikinsa yayi sanyi da farko, saida sa’ada ta kama shi da fada ta inda ta shiga bata nan take fita ba, t ace wai ya tsaya yana kallona bayan labe nake yi musu kullum daman ta sha ganina ina yi musu labe ina jiyo duk abunda suke fada. Tasi’u ya kama ni da fada akan me yasa nake yi musu lae?
Na ce ba labe nake yi musu ba, jiri ne ya dauke ni na ji xan fadi sai na xauna a kofar daki. Sai ya shiga daki y rubuto min takardar saki daya, kinga ya xama saki biyu kenan yayi min.
Na karbi takardar na dauki gyalena na fita ban yiwa ‘ya’yana bayani ba. Ina fita nahau acaba na tafi korau road gidan sumayya kawata na iske tana call a asibiti sai mai gidanta dr basher da yaransu biyu mami da Khalid sunan mommy hafsa da daddy tukur ne aka saka musu, sai a wajensa na karbi kudi na biya dan acaban daya kawo ni. Na ce masa bani da lafiya ne na xo ta duba ni, ina tunanin jinina ne yahau. Ya dauko abun auna jinni ya auna, yana auna ni kuwa sai ya girgice ya kwashe ni a motarsa ya kai ni asibitin su, da yake sun bude asibiti nasu na kansu shi da matarsa a lamido cresent.
Allah sarki madina ko me ya sameta oho.
Se a biyo mu dan jin yadda data kasance.
.
Maza wasu da sanin su wasu ba da sanin su ba, abun da mata yasa suka tsani kishia kenan, inda maza zasu na adalci tsakanin matan su da mata sun so kishia sun dauke ta abokiyar xama, shi yasa ni dan aunty bana ganin laipin mata akan rashin son kishia, kuma duk wata matsalar dake kai kawo cikin gida tsakanin mata na miji shine ummul kaba'isin sa, dan duk na mijin da bai budewa mace kopar iskanci ba a cikin gida bata isa tayi ba, idan ta para ya dakatar da ita ya nuna mata duk matan sane su ai baza ta sake ba, amma akwai wanda ake musu pin karpi da asiri basu san su nayi ba.
Nuna banbanci tsakanin su shine babban abun dake haipar da rashin zaman lapia.
.
Allah Ya tsare mu da mata marassa imani, Ya azurta mu da salihai na gari, kuma matan Allah Ya albarkace ku da maza je na gari Ya kare ku da muguwar kishia Ya hada ku da ta gari
ADON DAWA2 (P 13)
.
Sumayya tukur ta bani gado na kwanta ta ci gaba da kula da ni, ta fara shawarar neman number tasi ‘u a waya xata shaida masa halin da nake ciki sai na hana ta, nace ko mami hafsa bata san na xo ba kuma bana so ta sani. Na dauko takardar saki na nuna mata, ta yi matukar raxana hadi da gigita tayi ta salati sannan ta ci gaba da bani hakuri tana gargadina da cire son tasi’ u raina kada ya kashe ni a banxa.
Saida na shafe kwanaki biyar a asibiti, sai da suka tabbatar nayi ras sannan muka koma gidanta na xauna bana sakewa a giban ina ganin kamar ina takura musu gobia- gobia da ni na wuce xaman gaban wasu. Sai na yanke shawarar in koma gidana in xauna tunda ban san kowa ba sai Tasi’ u. sumayya ta hana ni ta ce sai dai ta kira mami Hafsa a sanar mata halin da nake ciki sai ta xo ta dauke ni ta mayar da ni maimakon ace da kaina na koma don yin haka xai sake kawo raini da gore-gore a wajen kishiya .
Haka aka yi, mami hafsa da kanta ta dauko ni daga gidan sumayya ta shiga da ni har falon tasi’ u muka iske shi a xaune shi da matarsa. Ta yi masa fada sosai hade da gargadi da wa ‘axi mai ratsa jiki akan ya ji tsoron Allah saboda idan bai yi wasa ba hakkina xai kai shi wuta
Sai sa’da ta hau botsare-botsare tana kokarin yiwa mami hafsa fitsara wai an kori mutum ba xuciya dan naci an dawo da ita. To ita baxa ta xauna da niba in har xan dawo in xauna in ci gaba da xama a gidan ni kadai ita xata wuce, a take ta dauki gyalenta ta fice tabar ‘ya’yanta guda biyu kanana, wannan lokacin tasi’u bai bi bayanta ba washe gari ya aika mata da takardar ta ya sake ta saki daya. Ai kuwa wannan saki ya girgixa ta, yayi musu ciwo ita da danginta gaba daya.
Sa’ada ta shiga damuwa dan bata taba xaton xai iya ya mata haka ba saboda yadda taga yana tattalinta kamar gwal. Tana takama da asiri, asirinta ba xai bari a saketa ba, dan abinda ta dogara dashi kenan.
Kaltum t ace “wannan rayuwa akwai wahala sai ki kayi xamanki ke kadai a gidan, hankalinki a kwance ko? ”
Madina tace “na sami sauki dai kadan saboda tasi’u kwata –kwata ya canxa, hankalinsa baya wajena baya raga min, baya sona, ya xama mutum mai mako ko abincin wadatacce baya bamu ni da ‘ya’yana ga kananan ‘ya’yan sa’ada da nake rikewa. Daga nan ma ya sake sabon aure, ni din ce dai ba xa xauna da ni kadai ba.
Ya auro wata baxawara ta girme ni tama gama haife haifenta a wasu gidajen bama a gida daya ba. Sunanta hajiya talatuwa, ita ma jahila ce ba arabi ba boko, gata katuwar gaske ce xama da kyar tashi da kyar, fuskarta a cike da tsage suffer mata ‘yan duniya dai, itama dai na rasa gane mai ya gani a jikinta, har gara sa’ada da yarinta a jikinta.
Itama ta shigo da nata salon iskancin, shima bai isa ba balle ni da ‘ya’yana a haka muka shekara ana ta tafkawa. Bana kula ta sai dai addu’a ni ke Allah Y daidaita mu amma abu yaci tura. Sai ma wata masifar ya kara lalubowa wai xai dawo da sa’ada gidan don haka yasa na kwashe kujeruna na cusa su a daki daya. Ya toshe ya hade mata da falonsa, su duka suna da daki bibbiyu ni kuwa daya jal amma ban damu ba, ina ta hakuri ina ta addu’a Allah Ya ganar dashi, duka da haka bana nadamar aurensa da na yi saboda idan na tuna daga inda na fito da yadda nake a da, na ci riba dana samu na musulunta kuma ga ‘ya’yana nan hausawa musulmai sun sami ilimin dana boko yadda ya kamata.
Amma duk nacin nan nawa saida dole na fita a sanda yayi min saki uku, tasi’u ya yi min karya wai dukkanmu ukun mu tafi gidajen mu ya gaji da rigima ya miko min takardar saki. Ya ce min suma sauran ya basu takardar saki. Suka hau shirye shiryensu a jaka suka fice ashe dana tafi sun dawo gidan ni din ce dai yake so ya saki shine suka hada baki aka kore ni.
Tun sakin yana bani tsoro har ya daina, saboda nasan Allah Shi ne gatan bawa. Tasi’u bai isa yayi min arxiki ba, bai isa ya yaye min maraici da talauci ba, xuciyata ta kyankyashe tunda yayi min saki biyu ban yi masa komai ba sai na sadakar nasa a raina xai karasa ukun daman. Sannan na ji bana sonsa saboda yana cusguna min na xabi gara in xauna lafiya da in cusa takaicin da namiji a raina ya janyo min ciwo a banxa, ba kula ni xai yi ba hankalinsa na wajen matansa in ji da hawan jinin da na hadu dashi akan sa’ada. Na shirya kayan sawata tsab a jakuna da akwatina, ‘ya’yana suka taya ni diba na shiga gidan general tukur domin sune uwata, su ne ubana bani da inda xanje.
Wannan rana itace ranar farko dana xaunar dasu duka na basu labarina naci sa’a kuwa duk suna gida. Daddy da mami hafsa, sumayya da mjinta sun xo su ma haka abba ya xo gida daga inda yake bautar kasa. Kannensa na gida. Ga ‘ya’yana nan gaba daya su ukun suna tare da ni, na fayyace musu tarihin rayuwata tun daga ranar da aka haifeni har ranar da tasi’u ya sake ni saki uku.
Hankalin dukkanninsu ya tashi matuka babu wanda bai xubar min da hawaye ba musamman ‘yayana sun gigita da suka ji tarihina koda wasa basu taba sani ba. Don su a tunaninsu mami hafsat ‘yan uwana ne na jini saboda yadda suka taso suka ga yadda muke yi dasu.”
Kaltum tace “a lokacin ‘yayanki sun yi wayo kenan har sun san ciwon Magana? !”
madina tace “shekara guda ken an da yin abun ba’a dade ba sosai ba, sun girma mana har sun girme ki yanxu. Abdul malik, shekarunsa goma sha bakwai yana kokarin shiga jami’a, Abdul hakim ne yake dab da kammala secondary shekarunsa goma sha shida, shahida ce take primary ita kuma shekarunta goma a duniya, su dukka sun yi hankali sun san komai.
Daga karshe nayi musu ban kwana nace xan koma garinmu. Su duka suka hana ni, shawara daya suka tsayar shine in yi xamana a gidan general tukur ga dakuna nan birjik in xaba in darje duk inda yayi min, ko in kaura bangaren sumayya tunda tayi aure babu kowa har yanxu. Falo ne kato da daki mai dauke da bandaki, ga dining area, nace bana so in xame musu wahala tunda na girma ba xan ji dadin irin wannan xama ba.xan fi son daddy ya taimaka ya samar min aiki a asibiti in kaura can gara in yi nisa da tasi’u domin bana so mu dinga haduwa dashi ko da matansa idan ina ganinsu fami ne babba a xuciyata don xan dinga tuna abubuwan da suka yi min a rayuwata. Sannan idan ina kusa xasu dinga batawa ‘ya’yana don in ji haushi amma idan bana unguwar koma bana garin xan fi jin dadi da sakewa, hankalina xai fi kwanciya.
Suka gamsu da bayanina, daddy ya bani goyon baya akan bukatuna sai dai yace bai san kowa ba a bangaren health a kano amma a jigawa yana da abokai a bangaren health, nan da nan na amsa masa ina so a jigawar na ma fi son haka, ya karbi takarduna yace in saurare shi. Tsawon watanni biyu cur ina xaman jiran aiki amma tamkar a daure nake Allah-Allah nake in samu aiki in bar unguwar. Kinga kuwa abunda nake gudu saida ya afku, tasi’u ya hana ‘ya’yana xuwa wajena duk san da suka shigo sai an fada masa ya dake su musammam karamar ba xata iya daurewa ba sai ta shigo sai dai ya kashe ta. Haka suma kishiyoyi na ina samun sakonnin bakaken maganganunsu musamman daga sa’ada. Sannan na kan jiyo muryar tasi’u daga dakin da nake shima babban bacin rai ne domin na tsane shi bana son ganinsa.
Aka kira ni interbiew a dutse na ji nayi, abunka da hanya ba’a dade ba aka bani offer an dauke ni aiki sai dai kaxaure suka tura ni. Naji dadi nan da nan na hada kayana daddy yasa direbansa ya kaini kafin in tafi mami hafsa ta dauki lokaci mai tsawo tana yi min nasiha cewar in kama kaina in rike mutuncina idan na samu miji in yi aure in cire son tasi’u a raina, na ci sa’a na samu gida a staff querters din asibitin, daki biyu da tsakar gida ga kicin da ban daki.
Hakika na ji dadin aikina ina xaune da abokan aikina mata da maxa lafiya. Dan albashi na yana isata in ci abinci, in dinka ‘yar sutura har in kunshe in kawowa yarana wani kudin ko su shigo mota idan babansu baya gari su xo su karba. Na ci gaba da kama kai na ina rike addinina yadda ya kamata ina cikin walwala fiye da a gidan tasi’u. labari ya iske kunnen makiyana cewar na samu aiki har na murmure na yi kyau sai haushi ya ishe su, suna hassada dama ban samu ba sun fi so kullum in shiga wahala da wulakanci amma Allah Ya fi su.”
Kaltum tayi dariya tace “na ji dadin labarin nan naki matuka da na ji karshen ki alkhairi ne. Allah Ya dube ki ya rufa miki asiri musamman da kika yi tawakkali kika cire son tasi’u a xuciyar ki. Ta amma me yasa kika bar aikinki kika taho nan bayan aikin yafi tahowa ki? ”
Madina ta yi ‘yar dariyar karfin hali ta cije leben kasa tace “kaltum, kema kin san in har babu matsalar da tafi karfina, ba xan baro aikina in taho ba. Gagarumar matsala ce ta fado min wacce har tafi matsalolin da na hadu dasu a baya. Tsanani yayi tsanani wanda har mami hafsat da daddy tukur da sumayya kawata masoyana wa anda bani da kamar su a duniya suka kini suka kira nida MAYYA. In takaice miki hatta da ‘ya’yana dana Haifa a cikina saida suka ki ni suka guje ni, suka ce ni ba uwarsu b ace. Kaltum tun daga ranar da Abdul malik ya furta min haka, na jawo hannun Abdul hakim ya fisge yace min bana sonki mama, nace to ba ni da amfani a duniya, rayuwata ta xo karshe gara in shiga duniya kawai xai fi ye min sauki.” Sai madina ta rushe da kuka.
Kaltum ta ji hankalinta ya tashi, tuni ta shiga surkukin tunani ta tambaya cikin damuwa “anty, me yasa haka?
Me kika yi musu haka ko asiri aka yi miki kowa ya tsaneki ? ”
Madina ta goge hawayen ta ta yi dan murmushi t ace “ba asiri ba ne kaltum kaddara ce kawai ta hau kaina sai dai in xama me godewa Allah a duk halin da na tsinci kaina. Xaki ji dalili kema idan kika ji dalilinsu baxa ki xarge suba, watakila ma k ice sunyi daidai da suka yi min haka amma nima ba laifina ba ne an yanke min hukunci bisa rashin sani.”
Madina na rufe bakinta sai ga baba tsoho mai sayar da ruwa ya dawo akan jakunansa, ya ja ya tasaya a gabansu kaltum, daya dubeta sai yayi dariya.
Cikin harshen larabci yace “’yar baiwa dawowa nayi in cika alkawarin dana dauka , dana ce idan na sayar xan siyo miki gurasa da xuma gashi na kawo miki. Na sayar da ruwan dukka har xan koma in karo wani.”
Kaltum ta tashi da murna taje ta durkusa ta karba tana godiya ya wuce ya tafi. Ta xo ta ajiye a gaban madina tana mai fassara mata abunda suka fada cikin harshen larabci.
Madina tayiwa tsohon nan addu’a suna ci suna yabonsa har suka cika tunbinsu, saboda gurasar mai yawa ce, badan suna jin yunwa ba da ba xasu iya cinyewa duka ba, suka kora da ruwa.
Madina tace “muje muyi sallah na lura axahar tayi sai mu dawo mu ci gaba da labari . Kaltum, labarina akwai abin al’ajabi nan gaba, ai ba ki ji komai bama a baya.”
Kaltum t ace “tabbas na shiga wani hali na xumudin son in ji wannan labarin, kaina gaba daya ya daure tamkar an yi min dabaibayi.”
Suka shiga gida da ruwansu don suyi alwala suyi sallah, saida suka idar da sallah sukayi nafiloli da addu’o’insu sanna suka dawo wajensu na da wato kofar gida suka xauna yayin da wata iska mai dadi take kada su baya ga tumbinsu daya dau lodi, don haka mai sauraro, da mai bayar da labari suka sami nutsuwa labarin ya fara tafiya yadda ya kamata.
Kaltum ta dubi madina ta fada cikin kaguwa tace “anty ci gaba ina sauraron ki.”
Madina ta nisa tace “watanni shida da fara aiki a asibitin kaxaure yayin da shekarata talatin da uku a duniya. Tukur tukur wato Abba kanin kawata Dr sumayya tukur, ya kawo min xiyara har kaxaure wajen aikina da misalin karfe tara na safiyar wata littinin. Yaro matashi a tseleliyar motar da mahaifinsa ya saya masa a satin saboda farin cikin kammala bautar kasarsa da yayi ya xama cikakken lauyer.
Banyi mamaki ba da naga Abba a kaxaure a daidai wannan lokacin, kuma ban yi mamakin ganin tsaleliyar motar nan tasa ba saboda nasan mahaifinsa xai iya bashi wacce ta fita ma saboda general tukur mutum ne mai son ‘ya’yansa da yawa. Sai na dauka Abba ya xo don ya nuna min sabuwar motarsa ne, ban yi mamaki ba idan haka ne saboda Abba mutumi na ne sosai, abokin labarina ne a yi wasa ayi dariya ayi shewa saboda ni mai yawan Magana ce da xolaya.
Abokan aikina har guda biyu suka shigo office dina suna shaida min cewar nayi bako a waje yace daga kano yake sunan sa Abba tukur, sai nace su ce masa ya shigo amma Abban na tsaye a bakin baranda bai shigo ba. Na aika masinjanmu har sau biyu yace masa ya shigo amma Abba bai shigo ciki ba, ni kuma ina ta faman aiki ina shigar da sunayen da sakamakon wadanda muka yiwa gwajin hawan jinni da ciwon suga cikin wani file. Kafin su xo su karbi sakamakon su. Dole tasa na ajiye biron na fito da kaina, ina ta murnar ganinsa ina ta hayaniya ni kadai. Haja ina ta shafa mota ina doguwar addu’a ni kadai Abba na tsaye kikam bai ce da ni komai ba.
Ya xura hannu a aljihun wandon yayin da yayi shar a cikin suit dinsa baka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login