Showing 87001 words to 90000 words out of 144367 words
shi ya fi masa sauki. Ya yi kuka, ya dinga kwalla sunan kaltum shi kadai a bakin teku tamkar tababbe ga magaruba ta yi, duhu ya bayyana. Ya tuna ranar day a tare kaltum a dai-dai inda yake xaune, ranar da ta dinga ynakasa da wuka, kuma a ranar ta fara sonsa.
Bai bar wajen ba said a gari yayi duhu sosai. Ya isa gida ransa a bace. Sallah kadai yayi, ya rufe kansa a daki ya kwanta ba don yana jin barci ba, sai don kawai xuciyarsa ba xata iya jure surutun mutane. Xuciyarsa ta raunana, ji yake tamkar ta hadu da lahani tamkar xata buga.
Sarki ya dinga aike a tambayar masa, anya mambela lafiya ya kwanta da wuri! Ta wundo yake bas u amsa lafiyarsa kalau, barci yake ji.
Talatainin dare daf da asuba sannan barci ya dauke shi, sai ya gan shi tare da kaltum a mafarki suna hirar so da kauna. Farin cikin sa a mafarki bay a musaltuwa, amma day a farka ya ganshi shi kadai ba kaltum a xahiri, sai ya ji tamkar ya kurma ihu don takaici.
“me yasa kika tafi kika bar ni kaltum! Me yasa da aka xo daukarki ba ki rugo kin xo kin fada min mun tafi tare ba!”
Haka mambela yake fada a bayyane a cikin yarensa na adon dawa.ADON DAWA 25
.
TRUE LIFE STORY.
.
Tunanin matsananciyar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ba ta son khartum haka ba dadin xaman garin take jib a, dama-damarta dan ta hadu ds fatsima kawa mai kaunarta, mai karfafa mata gwiwa. Ba don fatsima bad a rayuwa ta kara yi wa kaltum xafi a khartum kasancewar BABU RUWAN WANI da rayuwar wani , babu taimako ko kadan a xaman gidan nan.
“ya na yi miki Magana”. Fatsima ta xunguri kaltum a lokacin da suke tsugunne a bakin katuwar bola suna tsintar kayan miya.
Kaltum ta daga idanuwanta da sauri ta dubi mutumin da ke tsaye a kanta, Abbas ta gani tsaye a kanta yana murmushi sanye da jallabiyarsa fara tas! Da rwaninsa fari kal irin na larabawan sudan. Murmushi ya sakar mata gami da cewa, “marhaba kaltum.”
Sai ta ji ranta ya dungunxuma y abaci, bakin cikin day a dankare xuciyarta ya sake karuwa. Kallon fuskarta kawai xaka yi ka tabbatar da labarin xuciyarta. Ya yi ta Magana ko daga idonta b ata yi ba balle tab a shi amsa. Da ya dame ta, sai ta yanke shawarar hakura da tsintar kayan miyar, gara kawai ta bar masa wajen. Ta kinkimi kwandonta aka, ta yi tafiyarta ko fatsima bat a yiwa sallama ba saboda ta fuskanci ita ke goyon bayansa. Sai da ta yi nisa sannan ta ji fatsima ta kwalla mata kira. Kaltum ta juyo sai tag a fatsima a guje tana murna.
Ta iso inda kaltum ke tsaye ta mika mata kudi, kaltum ta mika hannu ta karba a sanyaye, sannan ta tambaya cike da mamaki, “waye ya bani”!
Fatsima ta yi dariya ta xaro nata kudin t ace, “ashara jine ya bani, ke kuma ashirin jine y ace in kawo miki.”
Kaltum ta tabe baki sannan ta yi mata tambaya, bad an bata ta sani ba sai don ta ja mata kunne.
“waye ya ba mu kudin!”
Fatima tace, “Abbas mana”.
Kaltum ta ci gaba da Magana cikin fushi da cewar, Abbas ya fita harkarta, ba ita bas hi, ya sami dama ne daga wajen fatsima dab a xai ci gaba da nace mata ba.
Fatsima t ace, ita kuwa ko yanxu idan ya bas u kudi sai ta karbo musu sai dai idan ta bata ta xubar.
Fatsima ta ci gaba da yiwa kaltumtsiya tana cewa, “duk wnnan fadan da kike yi, ban ga kinyi wurgi da kudin ba a damke a hannun ki yake.”
Sai kaltum ta sake damke kudinta b a tare da ta kara cewa uffan ba. Ba ta son Abbas, amma tana da bukatar taimakonsa.
Fatsima ta dinga yi wa kaltum tsiya don t ace bat a son kudin, amma shiru kake ji bat ace komai ba. Suka isa famfo suka wanke kayan miya, sannan suka nufi kasuwar adare don su sayar. Yau bas u dmu da sai sun siyar da tsda ba, saboda aljihunsu da nauyi, kudin da Abbas ya bas u ya ishe su cin abincin yau hard a nama da lemo.
Da rana suka tafi gidan jawahir mai kunshi kamar yadda ta umurce su bayan sallar axahar xa su dinga xuwa saboda mai gidanta bai yarda ta fara xaman kunshi ba sai t agama aikin gida kakaf.
Jawahir tana murna da xuwan kaltum matuka, saboda kaltum ta iya kitso ashe, tabbas xata kwashi kudin kitso. Kaltum da fatsima suna taya ta aikin gida, ko rainon yaranta, suna tayata da wanke lalle idan ya yi da shafa mahallabiya, ko su hura mata garwashi idan xata yi wa mata dukkan.
Ba sa barin gidan jawahir sai bayan sallar isha’I, bayan tab a su abincin dare sun cika cikinsu, sun share mata gidanta tas! Sannan su nufi gida.
A halin yanxu sun rage tafiya markadi tsintar rubabbun kayan miya, saboda dan kudin da suke samu daga wajen jawahir. Babu laifi tana biyansu duk da dai aikin da suke shirga ya fi kudin aikin yawa, tana bas u abinci anda shi ne babbar matsalarsu. Kaltum mai farin jinni, ladabinta da kwaxon aikinta gami da fara’arta sun sa wadanda ta ke yi wa kitso da wankin lalle suna kaunarta, har suna yi mata kyauta akai-akai.
Allahu Akbar! Allah ma ji rokon bayinSa, Allah Yana taimakon duk wanda ya tashi ya neama, haka Yan a bawa duk wanda ya roke Shi. Babu talaka sai mai matacciyar xuciya. Allah ba Ya hana bawanSa lomar da xai kai bakinsa.
BABI NA GOMA SHA DAYA.
BUR SUDAN.
Rayuwar mambela da madina a bur sudan ta xama tamkar gayan tuwo ne marar miya cinsa haka babu dadi. Haka suke rayuwa amma xukatanu babu dadi saboda rashin kaltum din su.
Mambela ya fada ya sake maimaitawa, yyin day a lailayo rantsuwa yam aka a cikin bayanansa a dai dai lokacin day a tara ‘yan gidan su madina kakaf kofar gidan su da sanyin safiyar wannan rana. Yana Magana hawaye na yi masa tsartuwa, hakika daga jin kalamansa xaka tabbatar a cikin matsanancin fushi yake Magana da matukar damuwa. Tabbas babu maganar wasu a cikin lafaxansa, Magana yake cikin gadar da basu tabbacin xartar da hukunci mai tsanani akan duk wanda ya karya masa doka. Ba wai rokarsu yake das u bi abunda yake umartar suba, har ya fi son kada su bi don ya yi was an kura das u.
Ya dube su daya bayan daya ya kawar da ido gefe, yayin day a runtse ido ya xubar da hawayen day a cika masa ido, ya fada cikin harshen larabciwanda yake tunanin kowannen su xai gane, wanda bai gane sosai bad an uwansa xai fassara masa.
Ya ce, “yan Nigeria da niger a da ina sonku fiye da yadda nake son yan kasata sudan. Amma a ynxu bna son ganinku, ban ki in bude idona in ga an kwashe ku ba kada a bar mutum daya saboda xamanku a kusa da ni babban fami ne a cikin xuciyata.
A duk lokacin da nag a irin ku, ko na ji yarenku na hausa sai gabana ya yanke ya fadi, in ji xuciyata ta buga saboda kuna tuno min da KALTUM. Da xarar na fito da safe na hango ku kun fito da kayan sana’arkukamar haka, sai in ga kamar xan hango kaltum a tsugune a can tana wanke-wanke.”
Se ya nuna gefen da madina ke xaune, yayin da kuka ya kece masa, kuma ya kecewa madina.
(NIMA SE DA MAJINA YA KECE MIN)
Mambela ya cije leben ya ci gaba da cewa, “kun ci manata da ku ka bar kaltum ta tafi Nigeria, aka rasa mutum daya da ai tashi ya ruga ya xo ya sanar da ni halin da ake ciki, haka kuka kori yarinyar nan, ku kuma kuka mike kafa a kasarmu. To ba ku isa ba, yadda kaltum ta bar sudan sai kun bar sudan, yada na rasa farin cikin rayuwata, sai kun rasa farin ciki kuma.”
Hankalin kowannensu ya tashi, kana dudan idanuwansu xaka ga sun firfito waje don fargaba.
Kalmar “ma’alesh, ma’alesh ya mambela”. Suke Ambato.
Ma’ana kayi hakuri kai mambela. Sai Kalmar ta xame masa tamkar ashar suke danna masa saboda masu iya magan na cewa, da xarar an fara ba ka hakuri to tabbas an cuce ka.
Ya daka musu tsawa cikin fushi, y ace, su rufe masa bakin su, bay a bukatar bada hakurin su. Tsit kake ji ko tari babu wanda ya sake yi.
Ya share hawaye y ace, “ba ku da imani, ba ku da tausayi, ko wannenku yasan tsakanina da kaltum kun san babu abun da na fi so a duniya irin kaltum ba ni da Magana sai ta kaltum, haka ba ni da wurin xuwa sai ajen kaltum. Ina kwance ba ni da lafiya kaltum ta o ta duba ni, a ranar na kai ta wajen mai martaba ya yaba da hankalinta, tya amince min in aure ta. Mun fara shawarar yaya xamu je kasarsu saboda madina t ace, sai na je gaban iyayenta xan aure ta, tana barin gidan mu kuka tura keyrta ku ka kore ta.
An fada min tana kuka bata so ta tafi, madina kika hada mata kyat a tafi, to ku sani babu ku babu xaman lafiya a garin nan. Kaltum ta tafi ta bar ni, ban san ta inda xan fara nemo Nigeria ba, da garin da kaltum ta ke a Nigeria.
Ni mambela na yi alkawarin takura muku, kun daina walwala kamar yadda na daina, ciwo nake yi a kwance a ranar da kaltum ta xo duba ni, na warke da nag anta, daga lokacin da na ji an dauke ta a lokacin ciwona ya dawo har yau na kasa samun lafiya. To daga yau kun daina xaman lafiya don duk sai na kakkarya kafafuwanku daya bayan daya.”
Kiri-kiri suke yi da ido, yyayin da kowannensu yah au kammala sangalalinsa kada a fara ta kansa. Madina kuwa ta yi tsuru a gefe kanta a sunkuye a kasa, tasan kowanne hukunci xai xartar daga kanta xai fra, don haka ta fara tunanin inda ake siyar da sandar guragu, gara tun da wuri ta tanada.
Mambela ya ci gaba da Magana cikin kakkausar murya, y ace, “babu sana’ar sayar da komai a kofar gidan nan, haka kada inga kafarku a bakin kogi, wajen kamun kifi. Haka kada inga kafarku a kasuwarmu jim arab, kad a wata ta xo garinmu bara, sai na karya duk wanda ya saba wannan doka. Sannu a hankali idan yunwa tai she ku xaku tarkata ku tafi inda kuka fito, yadda kaltum ta tafi ta bar ni.”
Malam nura wani tsoho daga cikin su madina xai yi Magana, mambela ya dunkule hannu xai kai masa bugu, abokansa da ke tsaye a gefensa suka rike shi. Suka ja shi suka tafi, da kyar mambela yake daga kafarsa don tananin tashin hankali. Ya rasa akan wanda xai huce, takaicin rashin kaltum amma ya fi jin haushin madina wacce ta hana su su yi aure tuntuni. Sannan da yaradarta aka dauke masa kaltum dinsa.
Suka rushed a kuka suna kiran, sun shiga uku sun lalace, ya ya xa su yi su rayu idan ba sana’a, ba bara! Madina ta mike a fusace ta fara Magana cikin fushi.
Ta ce, ‘haba jama’a kamar ba musulmai ba, kun manta Allah ne mai rayawa, Shi ne mai kashewa!kun manta Shi Ya ke tsare mutum, Ya yi masa Katanga da duk wani mugu! Ko gexau ban yi bad a mambela ya hana mu sana’ar da xamu ci abinci, Allah da Ya haliccemu Shi xe fito mana da wata hanyr da xa mu ci abinci mu rayu. Jahilci ne ku dinga kiran shiga uku, ku kira Kalmar “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah Xai yi mana jagora.
Ko me ya samu bawa mukaddari ne, shan ruwan kaltum ne yak are a bur sudan dole ta tafi, da shan ruwanta yak are a duniya da wayar gari xa a yi a tarar ta mutu ma karewar tafiya Nigeria.’
Sai suka ji xuciyar su ta yi dan sanyi, sannan kowannensu ya dinga kinkimar kayan siyarwarsa yana shiga gida don kada mambela ya xagayo ya iske su a kofar gida sana’ar yau dai ba a yi ba. Sai asarar da suka yi, saboda mai kosai ta yi markade, mai koko ta dama, haka mai danwake ta kwaba, har gara ma masu shayi da biredi ruwan xafi ne kadai da lipton suka dafa.
Kwanaki biyu haka su madina suke xaune babu mai sayar da komai, babu bara, babu xuwa kogi kamun kifi har sun fara jin jiki.
“mambela ya cuce mu, mugu marar imani”. Kalmomin da suke ta nanataw ken an, duk dakin da ka xo giftawa xaka dinga jiyowa. Suka ga Magana, xage xage a bayan fage ba xai yi musu magani ba sai suka shiga tunanin hanyar neman sulhu, domin komai da sulhu ya fi sauki.
Shawara day ace suka tsayar, maxa su hadu su yi kungiya su je su sami mai martaba sarkin ADON DAWA su kai kukan su, ba kuma karar mambela xa su ce sun kawo ba, a’a neman a rokar musu mambela ya taimaka ya janye takunkumin day a yi musu, ba laifin sub a ne da kaltum ta tafi suma bah aka suka so ba.
Haka aka yi said a suka tabbatar mambela ya fice, an tabbatar yana jim arab shi da abokansa suna shan jabna sannan suka dunguma suka tafi fada, da kyar dai aka yi musu iso, suka fadi gaban sarki suka yi gaisuwa cikin yaren ADON DAWA, sannan suka koro masa bayani cikin harshen larabci don shi suka fi iyawa. Suna gama bawa sarki labara sai ya bushed a dariya ya fada a bayyane har sau uku, “mambela! Mambela!! Mambela!!!”
Ya ce su tashi su tafi duk su fito da kayan sana’ar su, xa su iya xuwa bakin kogi, haka xa su iya xuwa jim arab ba damuwa. Babu abunda mambela xai yi musu, su kwantar da hankalinsu xai yi masa Magana har sai ya huce, daman kuma xafin rabuwa ne.
Godiya suke, addu’ar fatan alkhairi iri-iri suke jerowa sarki. Suka shiga gida suka fesawa mata bayani, yayin da buda da kidan kwarya ya gauraye gidan nan da nan aka sami masu taka rawa mata da maxa.
“ga mambela nan da tawagar san an xuwa”. Inji walidi ya rugo da gudu daga kofar gida.
Gudu da buga kafa a jikin katako kararaf ka ke ji ana karo, yayin da aka yi cilli da kwaryar kida. Wasu suka shige dakuna yayin da wasu bandaki suka cunkusa suka rufe kofa, wasu kuwa da suka gudu suka buya, ashe karya yake yi, xolayarsu yake. Dariya hard a faduwa yake yana fadi, “wasa ne ba mambela ba ne”.
Ran kowa y abaci suka firfito daga maboya suna masu jan Allah Ya isa, saboda tsorata su da yayi, har wasu da yawa sun karkace kafa da jinni.
Washe gari da safe aka rasa wanda xai fara fitar da kayan sana’arsa, kowa ya fito da kaya tsakar gida amma sun kasa karaswa kofar gida. Wannan ya leka ya dawo, wancan ma ta leka kofar gida ta dawo daga karshe aka sami xakakura daya ta fara firfita da kayanta, it ace madina, sannan sauran suka fara firfitar da kayansu su ma. Suna yi suna waige-waige da suka ji shiru sai suka saki jikinsu suka kwantar da hankalinsu, mambela ya hakura.
Kan ka ce kwabo jama’ar jange da ADON DAWA dauke da kwanukansu suka taho siyan abinci domin su ma kwana biyu rashin siyar da abincin ya shafe su.
“ga mambela nan!”. Sama’ila ya fada da karfi, yayin da yake rugawa cikin gida. Dogon tsaki suka yi yayin da ko waigawa bas u yi ba saboda sun san karya ne, tsorata su yake so yayi irin yadda walidi yayi musu jiya.
Dif! Kamar an jeho shi gaban su haka suka ga mambela da tawagarsa a tsaye a kansu. Xancen sama’ila gaskiya ne ashe ba wasa yake yi ba.
Madina bata yi karya ba, Kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’una tana sanyaya xuciyar mugu ya xamanto mai tausayawa.
Yawancinsu Kalmar da ta xo bakinsu ken an a tare suka fada, kuma a bayyane. Wasu kuwa cewa suka yi, “ihu mun shiga uku, mun gat a kanmu”.
Suka yi wuki-wuki haka kake ganin idanuwansu a waje saboda tsorata.
Ya tsaya cak! Ya na duban rawar jikin da suke yi ba tare day a ce uffan ba.
Malam gali tsohon da yake sayar da goro ya kasa goronsa a fai-fai. Ya ce, “yaro ka yi hakuri, na samo maka labarin kaltum. Kaltum na sudan xata dawo kwanan nan”.
Mambela ya tuntsire da dariyar da bai shirya ba, ya sake kyakyacewa da dariya.
Ya ce, “baba, ka sayar da goronka ba xan hana ku sana’a ba, amma kaltum bat a sudan tana Nigeria. Ko xaka fada min a inda take idan tana sudan!”
Baba ya marairaice y ace, “fada na yi dan ka ji sanyi a ranka don mu ma mu sami sauki”.
Sai gaba daya suka rude da addu’a suna fadin “in Allah Ya yarda kaltum sai ta dawo. Kuma da yaradar Allah kaltum matarsa ce, duk inda take sai ta dawo.”
Mambela ya ji dadin addu’arsu, sai jikinsa ya yi sanyi, ya sunkuyar da kansa kasa yayin da kwalla ta cika masa ido. Ya dade a tsaye yana sauraron dadin bakinsu sai ya yi murmushi ya juya ya dubi madina wacce ke xaune ta sa kaskon kosanta a gaba ta kasa Magana ta kasa sakin kosan sai hawaye take xubarwa kawai. Ya juya ya dubi gefenta sai ya ga kamar xai ga kaltum a tsugunne a kusa da ita tana yi masa murmushin nan nata. Sai ya girgixa kai ya juya ya tafi, yayin da abokansa suka bi bayansa.
Doguwar ajiyar xuciya kake ji a jere a jere. Su madina na yi saboda farin ciki day a same su, sai kiran hamdala suke da godewa mambela.
A yammacin wannan ranar madina ta sami sammacin kira daga mambela cewar, ta same shi a bakin teku. Xuciyarta ta harba, amma sai ta yi addu’a ta xari gyalenta ta tafi ta yrada da cewa Allah xai kare ta, kuma mutum ba xai iya yi wa mutum abunda Allah bai kaddara xai same shiba.
Rayuwarta da mutuwarta duk suna hannun mahaliccinta.