Showing 27001 words to 30000 words out of 144367 words

Chapter 10 - ADON DAWA

Unknown   

30 Oct 2024

5076

hawaye mai radadi yake xubo mata.
Ta ce “Mambela! Mambela!! Mambela!!!
Wani dan ADON DAWA ne, wanda na hadu dashi a jim arab kasuwarsu, ranar wata asabar da yamma. Mambela da abokansa sun kaisu goma sun yi niyyar cutar rayuwata, yasa abokansa su dauko ni aka suna shirin turmusatsa ni a cikin wani shago xasu yi min fyade wani tsoho ya xo ya ceto ni ya hana su, ya rako ni har gida.”
.
ADON DAWA 10
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina ta dafe kirji ta ce “subhanallahi, daman mambela mutum ne! ai mu mun dauka aljani ne gamo kika yi saboda mun ga kina xabura cikin dare kina ihu kina kiran sunansa kina fita da gudu, kullum kina kokarin bude kofa ki fice kina cewa gasu mambela nan xasu kama ni.”
Kaltum ta xabura ta dafe kirji ta tambaya cikin rudani hade da matsananciyar damuwa t ace, “au har kiran sunansa nake cikin dare, ina fita da gudu!” sai hawaye ya kece mata.
Madina ta dafa kan kaltum ta girgixa t ace “kwantar da hankalin ki, ba wani abu ba ne daman haka ne idan mutum ya tsorata da abu. Babu abunda xai same ki in shaa Allah. Shine ya ji miki ciwo a hannu!”
Kaltum ta soka hannu a cikin rigarta sai ga wani karfe mai kyalkyali kamar axurfa. Yayin da madina ta bude baki tana dubanta cike da mamaki. Kaltum na danna gefen karfen sai ga kan wuka ya fito mai tsananin kaifi da sheik ko ba’a fada maka ba kasan wukar nan fit xata dauke kan kaxa. Madina tad aka tsalle ta ja da baya ta tambaya cikin gigita. Ta ce “kaltum ina kika sami wuka! Me xa kiyi da ita!”
Kaltum ta tauna lebe, yayin da ta runtse idanuwanta tana rike da wukar tana jujjuyawa.
Ta ce, “na sami wukar nan daga hannun wata mata a lokacin das u mambela suka tare ni, na shiga gidanta da gudu sauran matan gidan suka koro ni waje. Na dai yi mata bayanin duk yanda muka yi da mambela.”
Madina t ace “wa iyyaxu billah, Allah Yayi mana tsari da mambela. Shi ya kwace wukar a hannunki ya yanke ki!”
Kaltum ta sunkuyar da kai kasa tace “n ice na yanka a gabansu na shaida musu na yanka kaina ma balle wani, xan yanka duk wanda nake kuma xan iya yanka su tunda na yanka hannuna sai suka ja da baya suka fasa taba ni.”
Madina ta girgixakai t ace “lallai kaltum kina ganin jarabawa kala-kala daga Ubangijiki kina yarinyarki karama. Ki daure ki ci jarabawar nan kiga yadda Allah xai miki sakayya nan gaba. Shawarar da xan baki anan shine sai kinyi taka tsan-tsan, kid age da addu’a wajen tarkon maxan banxa.
Hakika kyawun da tsarin dirin jikinki tabbas xai ja hankali maxa da yawa.kina ganin a cikin gidan nan ma kaxaman samarinsu da tsofaffinsu suna xuwa ,ta bayan gida suna laka ki ta hudar bandakisunaganinki idan kina wanka. Suna leka kowacce mace amma sun fi leka ki saboda suna sha awar kyawunki.
Kaltum ta dafe kai don takaici, bakin ciki ya hana ta Magana.
Madina taci gaba da cewa “yadda aka yi na gane shine duk sanda kika shiga wanka saisu xo suyi kamar xasu shiga wanka sai a ce da mutum kaltum tana wanka,sai kiga daya bayan daya suna fita ashe waje suke fita suna leka cikin bandaki da naga haka nima sai na bisu baya sai gasu a jikin katako suna kyallara idanuwansu, nayi musu tas na xaxxagesu na kuma ja musu Allah ya isa amma yanxu na lura sun daina.
Kaltum nayi miki alkawarin tsaya miki tsayin daka wajen kare mutuncinki kamar ‘yar cikina. Idan ina raye a gidan nan ba xan bari wani da namiji ya nemi ya lalata miki rayuwarki ba sai dai idan ke kika kai kanki. Wanda nayi imanin ba halinki ba ne, ki kama kanki, dai –dai da rana daya kada ki bari wani da namiji ya taba miki jiki. Ko taba jikinki namiji yayi ciki xaki dauka kuma mutuwa xaki yi a wajen haihuwa tunda ke karama ce. Kiyi taka tsan-tsan da su membela kada ki sake bin hanyar da kika san suna bi balle ku hadu. Ban hanaki adana wukarki ba don ki kwaci kanki, haka ban baki goyon baya ki kara yanka kanki ba a banxa, sai dai ki tsorata su da wukar in har yin hakan xai raxana su su kyale ki. Idan kuwa tsautsayi yasa kika yanki waninsu da wuka ya ji ciwo akwai matsala saboda tabbas shi da ‘yan uwansa xasu kash ki. Ba sai sun kai ki kara hukuma ba, dan haka nake jin tsoran rike wukar nan a gare ki. Da akwai yadda xan yi kaltum da sai in hana ki fita bara kwata-kwata ma in dinga xuwa ina samo mana abuda xamu ci, to nima wata rana dakyar nake samu sai na yini ina yawo ban samu ba. Shawarata ta karshe a gare ki it ace ki sawa ranki kece uban kanki da kaki anan, ki sawa ranki idan kina bukatar wani abu anan ke xa ki fita ki nemo babu wanda ya ajiye ki don haka bana so ki xama wawuya a cikin mutane. Kin xama juji kowacce bola ke ake xubawa dole ki kwaci kanki.
”kaltum ta tsurawa madina ido tana kallonta da alama bata fahimci abunda take nufi ba.
Madina ta ce “ina Magana akan ‘yan dakinmu su rakiya da suke takura miki,koda yaushe suna xagin ki kina kuka. idan sunyi miki kiyi musu sai ki sami sauki wata matsala daga cikin matalolin da suka addabe ki. Xan iya faduwa na mutu a yanxu haka, ni mai rama miki sai kiyi yaya kenan! Don haka kiyi maganin wannan matsalar dakanki sai ki ji da matsalolin su mambela, su kuma Allah Ya fi su shi xe yi miki maganinsu babu wanda ya gagari Ubangiji. Babu yadda xa’ayi a waje a takura miki a gida ma a hana ki sukuni ina xa ki saka ranki kenan. Ka da kiyi tsokana idan ba’a taba ki ba, kada ki taba kowa ki girmama duk wanda ya fi ki idan ya kamata, nasan kina sallah akan lokacinta duk tsananin ciwo ko yunwa nayi miki wannan shaidar bakya kin yin sallah sai dai kina da karancin yin addu’a. ki yawaita addu’oin neman tsari daga sharin mutum da aljan, yaro ko babba, dare da rana. Ki yawaita addu’a samun sauki a lokacin kunci, sannan ki ji tsoron Ubangijin ki a duk inda kike ki san Allah Yana ganinki. Ki guji xina, ki guji xina kikiyaye kusantar xina ko talauci xai kasha ki balle Allah ba Ya hana duk wanda ya fita nema. Yin haka Allah xai xamanto jagoranki.”
Madina na rufe bakinta sai kaltum ta rushed a kuka ta rungume ta. Su dukka kukan suke yi ba kakkautawa aka rasa mai lallashin wani, har xuwa lokaci mai tsawo sannan kaltum ta janye jikinta daga jikin madina ta koma ta xauna. Ta sharce hawaye ta dubi madina.
Ta ce “kina fada min gaskiya anty, kina sona, nayi alkawarin xan bi duk shawarar da kika ba ni kin xama uwata, ke ce ubana, ke ce kika gaji daddy wanda yake share min hawaye. Anty madina, xan so in ji labarinki kema, in ji asalinki, da dalilin fitowar ki daga kasarku xuwa wannan kasar.”
Madina tayi murmushi t ace “so kike kiji labarina nima! Me yasa ki ke so ki ji labarina! Hakika labarina ya hada da abun mamaki mai firgitarwa. Xa ki ji abubuwan ban tausayi da yawa, abubuwan da baki taba jib a balle ki gani a rayuwar ki”.
Kaltum ta gyara xama t ace “ki bani labara anty madina.”
BABI NA SHIDA
LABARIN MADINA
Madina ta dubi kaltum yayin da take Magana cikin muryar kuka amma ba hawaye sai dai idanuwanta sun kada sun yi jawur da alamar tashin hankali a tattare da abunda take shirin fada.
Ta farad a cewa “kaltum, xa kiyi mamaki idan n ace miki ni inyamura ce ko!”
Kaltum ta dafa kirji t ace “inyamura!”
Madina ta gayada kai tace “eh inyamura ce, inyamurar ma ba musulma ba, wacce bata taba sanin akwai wani addini da ake kira musulunci ba. Ni yar asalin garin Onitsa ce. Kaltum, ban taba xuwa makarantar boko ba, primary balle secondary, amma a cikin ikon Allah ni ma’aikaciyar lafiya ce (nurse) a babban asibitin kaxaure.”
Hakika kan kaltum ya daure yayin da al’ajabi gami da miliyoyin tambayoyi suka feso a cikin xuciyarta. Ta tamba ya cikin mamaki “ta yaya!” madina tayi ajiyar xuciya t ace “shine yanxu nake shirin in fayyace miki komai. A da ina tunanin karancin shekarunki ba xai bari ki fahimce nib a amma na lura kaifin hankalinki da nutsuwar ki xa su sa ki gane, tunda kin dandana axabar rayuwa kamar ni.”
Madina ta mike ta shiga dakinsu, ba jimawa ta fito dauke da katon kwali wanda take kwana akai ta riko hannun kaltum ta tashe ta tsaye suka fice kofar gida, suka samu inuwa suka xauna akan kwalin su dukka.
Madina tayi murmushi t ace “nag a rana ta iske mu a tsakar gida, shi yasa na dawo da mu inuwa saboda mu ji dadin labarin.”
Tana rufe bakinta mai ruwa ya kwada talla akan keken jakunansa. Kaltum tana daga ido sai tag a wannan tsohon ne mai sayar da ruwan nan daya taba bata jarka daya ta ruwa kyauta. Sai suka yiwa juna murmushi a lokaci guda. Ya fada cikin harshen larabci y ace “yarinya ga ruwan dadi.”
Ta ce “babana ina jin kishir ruwa sai dai yauma bani da kudi.”
Ya ce “yauma dauko bokiti in xuba miki jarka daya kyauta saboda nima Allah Y dube ni.”
Kaltum tayi wuf ta mike da murna ta shiga gida ba dadewa sai gata dauke da bokiti hannunta, ta xo ta ajiye a gabansa, yayin day a tittila mata ruwa garai-garai mai sanyi cikin bokiti. Madina dai ta tsura musu ido tana duban bakinsu sai magan suke bata san mai suke fada ba, xuciyarta a cike da mamakin inda suka hadu har suka saba wasa da dariya haka. Tana mamakin yadda kaltum xata samu kudin da xata biya mai ruwa dan a iya saninta kaltum bata da kudi. Mai ruwa yah au keken jakunnansa ya kada su suka tafi, kaltum ta kinkimo bokitin ruwa ta kawo gaban madina. Ta shiga cikin gida ta samo kofi ta dauraye ta ciko kofi da ruwa ta mikawa madina, ta karba ta sha sannan itama kaltum din ta ciko kofi ta kwankwada yayin da hanjin cikinsu ya fara karkadawa saboda a yau ko kwayar gero bata bakunci cikinsu ba.
Madina ta gyara xama ta kalli kaltum t ace “ina kika samo tsohon nan, har kuka saba ya baki ruwa kyauta!”
Kaltum tayidariya t ace “yanxu ma ce min ya yi in jira shi anan idan ya sayar da ruwansa xai sayo min abinci, da na ce masa ba xan sha ruwansa ba saboda ban ci komai ba, cikina xai yi ciwo.”
Madina ta sake tambaya “kin san shi ne!” kaltum ta bata labarin yadda suka hadu rannan t ace yau ne haduwarsu ta biyu.madina t ace “to ai shine abunda nake fada miki daxu kenan, maxa suna sonki, a wajen mata ne kike dab akin jinni, matan ma, ba duka ba.
Kaltum ta gyada kai t ace “tabbas haka ne, na lura da haka da kika ankarar da ni. Anty ina sauraronki ki ci gaba da labara, tun daxu labarin yana yi min yawo a kwakwalwa. Kince ada ke bama musulma b ace, amma yanxu kin fi asalin muslman sanin addini, ga karatun Qur’ani ga salla, a ina kika koya!”
Madina t ace “na karance Qur’ani tas na sauke kamar yadda kika sauke, na san baki a duk inda aka buda min a cikin Qur’ani xan karance shi tsab, na iya hadisai da dama da fassararsu ban san adadin sub a, sannan nasan tauhidi da hukunce hukuncen musulunci. Ke in takaice miki ma ni malama ce a gidana mata suke cincirindo suna xuwa daukar karatu.
Kaltum ta gyara xama tace “yaushe kika koyi duk wannan, a Onitsa ko a kaxaure! Sannan kin c eke baki taba xua makarantar boko ba amma kin iya rubutu da karatu da turanci har ma kina aiki a asibiti kina allura da dinkin ciwo, ta yaya kika koya!”
Madina tayi dariya ta dafa kafadar kaltum t ace “Allah kenan, idan mutum y ace “Allah” to karshen Magana ta xo. Kaltum, Allah ne Ya bani duk wannan a cikin dan lokaci kankani. Ya mayar dani musulma ina kafura, Ya mayar dani mai ilimi alhali ina jahila , Ya mayar da ni me gata alhalin ina marainiya, Ya axurta ni da miji da ‘ya’ya alhali ina ni kadai. Allah ne mai yawan kyauta, mai jin kan bayinSa, banda Shi babu mai mayar da yaro babba, ya mayar da babba tsoho. Mai axurta talaka, mai talauta mai arxiki a duk sanda ya so.”
Kaltum ta gyada kai t ace “hskiks haka ne, tsarki da aminci sun tabattata ga Ubangijin talikai.”
Madina t ace Alhamdulillah, da kika yadda da wannan. Yanxu xan fara baki kadan daga cikin labarina, xa kiji kadan daga cikin dinbin ni’imomin da Rabbussamawati Yayi min, xa kiji yadda Allah Yake ikon Sa akan bayinsa.
Da farko ni sunana chidimma, haifaffiyar garin onisha ce, addinina addinin gargajiya ne ma’ana mu ba musulmai bane ba kuma masu xuwa coci ba ne. akwai bokan da yake yi mana duba da gumaka, shine yake iso mana da sakon abunda xamu yiwa gumaka da wadanda xamu bari kada gumaka suyi fushi sai bala’I ya same mu. Wa’iyyaxu billah, haka na taso na tarar kakannina da iyayena suna yi, kuma a haka suka koma ga ubangijin su cikin tsantsan jahilci. Shiyasa nake kuka duk sanda na tuna asarar da suka tabka a rayuwarsu a lokacin da suke duniya. Musamman idan na ji hukuncin makomar wanda ya mutu yana shirka. Babu yadda xan iya nemar musu gafara a wajen Mahalicci Ya gafarta musu kamar yadda naji a kisser Annabi Ibarahim da mahaifinsa da kuma shugabanmu annabi Muhammadu (saw) da kawunsa.” Sai madina ta rushed a kuka mai hade da tsantsar takaici, yayin da idanuwan kaltum suka cicciko da hawaye itama.
Madina ta tsagaita da kukan ta ci gaba da cewa “sunan mahaifiyata chioma, mahaifiyata wada ce.” Kaltum ta tambaya cike da rashin fahimata “wada!” madina ta gyada kai t ace “wada dai da kika sani wadanda ake haifarsu gajeru masu katon kai da guntayen gabobi wadanda aturance ake kiransu dawarf.”
Mamaki a bayyane xaka iya hangowa daga idanuwan kaltum, yayin da tambayoyi suka cika xuciyarta amma ta rasa daga ina xata fara tambayar.
Madina tayi dariya t ace “ki kwantar da hankalinki xan baki labarin komai. Mahaifina kuma sunansa emeka shi dogo ne sosai kamr duk wani dogon mutum da kika sani dais hi kuma wani dogon mutum da kika sani sai dais hi kuma xabiya ne wanda a turanci ake kiransa da albino.”
Kaltum ta xabura t ace “xabiya kuma!” madina ta kyalkyale da dariya, har kaltum ta fara tsorata da dariyar da madina take tuntsurawa ta kasa dainawa kaltum tad an ja da baya a tsorace, yayin da kwakwalwarta ta fara tunano mata abubuwa da yawa akan madina. Ta ce a ranta “shin wannan wacce irin mat ace duk kwabe-kwabe, ‘yar gidan xabiya da wada, inyamura, masu bautar gumaka!”
Madina ta katseta tunaninta da take yi ta ci gaba da cewa “dube ni sosai kaltum, kin ga nayi kama da wadanni! Ko kinga alamar hasken fatata tayi kama da kalar xabiya! Ko kinga alamar kamannina na inyamurai a fuskata ko harshena! Kon kin ga alamar arnanci a dabi’una! Kin ga babu duk wannan, shine ma’anata cewar Allah Y canxa ni a cikin dan kankanan lokaci.”
Kaltum ta gyada kai t ace “haka ne anty, babu duk wannan alamun da kika xayyano min. a tunanin ke bafullatana ce.”
Madina tayi murmushi t ace “to haka yayana innamani yake, har ya fini tsawo da fari don kamarmu daya sak. Da suka tashi haifar na uku sai aka Haifa wada aka saka masa suna xuka, da aka sake haifar mai binsa sai aka mata suna Enena. Daga nan sai rigima ta hautsine tsakanin dangin uwata da dangin ubana. Kinsan basu san tawakkali ba saboda jahilci, sai dangin ubana suke cewa mama na mayya ce sai an kasha ta, saboda me xata haifi wada kamar ta?
Suma danginta suka ce ai an haifi xabiya saboda haka baba na ne maye. Rigima taki ci taki cinyewa, cikin dare dangin babana suka je suka kasha kanina xuka, bayan kwana biyu aka tsinci gawar kanwata Enena a dawa suma dangin mahaifiyata sun rama kenan. Aka tashi rigima kamar xa’ayi yaki a jinanasu, tsakanin dangin wada da dangin xabiya daga karshe aka ce sai dai a raba auren sannan a raba yaran wato ni da yayana kenan, mu masu lafiyar ana sanmu. Da iyayena suka ji haka sai suka gaba xasu iya rabuwa da junansu ba saboda suna mutuwar kaunar junansu, su suka san irin tsana da takaicin da suka sha a wajen ‘yan gari kowa yaki aurensu, saboda ita wadace shi kuma xabiya har saida Allah Ya sa suka hada kansu suka xabi su rufawa juna asiri su xauna tare suka yi aurensu babu mai yiwa kowa gori.
Cikin dare ya dauki ‘yar wadar matar sa, daman ya saba daukarta a kafadar sa duk in da xasu je, ya shiga dawa suka gudu har yau ba’aji labarin suba. amma ana kyautata xaton sun shiga wani kungurmin kauyukan arna sun tsafe su. Kinsan kudu da arewa ba daya ba ne, yanxu a kudu sai kiga an kamo mutum an yi tsafi dashi musamman aga irin wannan halittar ta wada da xabiya suna tafiya tare, cewa xa su yi annoba ne ko su ce arxiki ne a kama su a yanka ko a binne su da rai. Bawai na gaskata ba amma dodonsu y ace an kashe su a wani kauye don haka aka yi bikin mutuwarsu aka raba gadon abunda suka bari, harda ‘ya’yan da suka bari a rabon gadon wato ni da yayana. Shike nan gaba daya gidanmu ya waste daga ni sai yayana muka rage, ba uwa, ba uba, babu kanne. Dangin uwata suka dauki yayana, yayanta ya dauke ta ya dauke shi ya tafi dashi enugu garin da yake aiki, dangin ubana suka dauke ni

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login