Showing 120001 words to 123000 words out of 144367 words
dira a kunnuwan kaltum,
kaltum ta zabura ta dago kai ta dubi goggo Fattu wacce ke kwance luf kamar ba ita tayi magana ba, matar da a shekaru biyu maba a taba gane abunda tafada ba sai yau,
kaltum ta share hawaye tace goggo me kika ce?
shiru bata sake magana ba amma hawaye yana ta kwaranya daga idanuwanta,
kaltum ta rushe da kuka ta saka gefen zaninta tana gogewa goggo fattu hawayen da yake kwaranya daga idanuwanta,
kafin lokacin makarantar islamiyyah yayi kaltum ta saka kayan makaranta ta dauki Qur'an nta tanufi makaranta saboda kawai kada Abba da alh Adnan su fito su kirawo ta.
Abba yayi shiru yana nazarin akan bayananda alh Adnan yayi masa, saiyaji tunaninsa ya hargitse ya kasa magana har lokaci mai tsawo?
Abba yayi ajiyar zuciya ya dubi alh Adnan yace alhaji meye abunyi yanzu kace kaltum ta bada shawarar lallai a tafi dani sannan Madina zata yarda ta dawo, kace alh saadu yace shizai iya kawo mana ita yaya ka gani ?
Alh adnan yace kabar alh Sa'adu mugani din idan zai iya idan yagagara sai kaje din ta ganka kuma nace idan ya ganta yabata waya zanyi magana da ita nasan abunda zanfada mata.
Abba yace to shikenan amma inhar ta yarda zata taho to kada maka fada mata ina nan ka boye mata bayan ta dawo kun hadu ka roketa ta aureni saboda kai zata iya yarda da maganarka ina fargaba ta bijire ta ki aure na.
alh Adnan yayi murmushi yace yarinta ke nan kana so aki fada mata baka mutuba kana tunanin zata yarda tazo din in baka nan?
Abba yace ina kyautata zaton zata iya yarda da maganarka idan ta dawo zata iya bijirewa taki aurena,
Alh Adnan yace ka bari ta dawo din nayi maka alkawari zanyi iya kokarina ka auri Madina,
Abba yayi murmushi yace Allah Ya taimaka, alhaji nasan Madina tanada alkunya kayita magiya zata yarda, yanzu nawa zaikama dukka harkawota kano da dan rakiyar kuma nawa za a biya mai kawowar?
alh adnan yace karka damu nizan dau nauyin komai saboda Madina ta taimaki kaltum tanada matukar mutunci, naji inaso na taimaka mata nima.
Abba ya langwabe kai yayinda kwallah ta cika
masa ido yace Wallahi alh ba wanda zai zauna da Madina koyaji labarinta baiji ta kwanta masa a rai ba, macece mai matukar kirki da sanin ya kamata, madina ta banbanta da sauran mata don haka duk wanda na tinkara nakeja da baya domin basuda halin Madina, alh ka taimakeni nasamu Madina a rayuwata, inason matar nan idan ban aureta ba nahakura da aure kwata kwata...
kayi addu a Abba, Allah Ya zaba maka abunda yafi maka alkhairi a rayuwar ka, alh Adnan ya fada yayinda ya mike tsaye yana daura agogo,
Abba ma ya mike tsaye yana godiya yace bari natafi naga kana shirin fita ina ta bata maka lokaci ko?
ai idan na sami wajenda za ayi min zancen madina banaso intashi daga wajen na gode
alh Allah Ya kara zumunci Allah Ya taimake ka yadda ka taimakeni.
alh Adnan Ya amsa da amin. suka dunguma suka fito,
saleh ya tako da gudu ya zo ya duka ya gaishe da alh Adnan yana jira yaji hukuncinda aka yanke masa na mummunan laifinda ya tafka dazu, saiyaga alh Adnan cike da fara a ya dube shi yace saleh ga Abba ku gaisa, kaltum na cikine ka kirata su gaisa?
sai malam sale yaji fargabar da yakeji ada ta dadu ya dago ido ya dubi Abba shima ya dubeshi sai Abba ya gaishe shi, malam saleh ya amsa a sanyaye gami da kirkiro busasshen murmushi yace ai kaltum ta tafi islamiyyah dazu,
alh Adnan yace to ai shi kenan dama gaisawa zasuyi da bako yayinda, Abba yake kokarin furta tambayanda ya addabeshi aransa haka ma malam sale yake furta tasa a wannan lokaci sai su dukka suka tsaya suna kallon juna,
alh Adnan kamewa yayi atsaye yana sauraronsu malam saleh yace da Abba yaro fadi maganarka tukunna sai nima inyi tawa.
Abba yace daman tambaya zan yi ince yaya kake da kaltum?
sai malam saleh ya dubi alh Adnan ma'ana yabashi amsa,
alh Adnan yayi dariya yace mahaifin kaltum ne,
Abba yasake duban malam sale da alaman mamaki ya gallabi zuciyarsa amma bai sake cewa komaiba saidai kallo daya zakayimasa kasan ba iyakar tambayarsa kenan ba,
malam saleh kuma yace nikuwa tambayanda zanyi shine waye wannan?
don ko a danginku bantaba ganinsa ba saboda asan juna idan an hadu a wani waje a dinga gaisawa kada ayi abun kunya,
Abba ma alh adnan ya kalla ma'ana yanzuma shizai bada amsa,
alh adnan yayi dariya yace wannan Abba kenan angon Madina ne wacce suka zauna da kaltum a bur sudan.
malam sale yaja dogon numfashi sai a yanzu ya samu nitsuwa.
Abba yayi musu sallama ya fice yayinda alh Adnan ya shiga motarsa malam sale kuwa yahau aikinsa na bude get harsaida alh Adnan ya fice sannan ya rufe get ya koma ya zauna akan benci yayi zugum yana sake-sake da alama ya yarda da zancen kaltum cewar Abba ba saurayinta bane.
labbaika rasulillah sautin dake fita daga wayar alh Adnan kenan wayarsa tayi ta ruri misalin karfe takwas na safiyyar asabar yayinda yake tsakiyar barci akan luntsumemen gadonsa da yake katafaren gidansa na hadaddiyar unguwar nan mai suna asokoro a babban birnin tarayyah Abuja, da kyar ya daga hannunsa ya lalubo wayar a karkashin filon da yake kwance ba tareda ya iya bude ido yakaranta sunan mai kiranba saboda tsananin barcinda yakeji saiya danna yamaka a kunne daga kwance batare da ya iya magana ba haka yakasa amsa sallamar da mutumin yake radawa sauraronsa kawai yake yi hello alh kana jina?
gani abur sudan tareda Madina,
kalmarda tashiga kunnen alh Adnan kenan a take yanemi naunauyan barci nan yarasa sai yaji idonsa ya wartsake garau ya tashi ya zauna daram akan gado yayinda matar sa salaha ta fasa ficewa daga dakin ta dawo ta tsaya akansa tanaso taji waye mai wannan wayar da har ta wartsakar dashi daga barcin da yake,
yace alh sa adu da gaske kake katabbatar itace Madinan Abba?
alh sa adu yace kwarai kuwa itace kadai Madina ma agidan tasan kaltum kaima tace tasanka Allah cikin ikonSa ma ankawo service din waya garin, itama da waya ahannunta don haka gatanan zakuyi magana don naga a tsorace take bata yarda dani ba, alh sa adu ya mikawa Madina waya ta karba atsorace hannunta na kakkarwa gami da yimasa sallama cikin ladabi da girmamawa, ya amsa cike dakulawa yakara da cewa Madina kamar yanda kikeda labarina nima inada labarin ki kakaf banason tone-tone banason maimaita magana banason jin ra layinki na da, magana zamuyi ta yanzu maganar da ya wuce, kaltum tafadamana irin kokari da kikayi ko ince jihadi da kika yi kika ceto rayuwarta a wajenda kowa takansa yakeyi, ta fadamana dalilinki na barin ya'yanki
kikayi gudun hijira da zummar har abada baza ki dawoba a yanzu dai atakaice ni alh Adnan na aiko alh saadu abokinane shine wanda na aika ya dauko kaltum inaso ki biyoshi ku dawo m
ta rushe da kuka mai firgitarwa ta girgiza kai tace alh naji dadin kulawarka agareni Allah Ya saka da alkhairi ammakayi hakuri bazan iya biyo shi ba har abada bazan dawo Nigeria ba.
alh Adnan yaji hankalinsa yatashi yatambaya agigice Madina meyasa?
amatsayinki na musulma kike fadin haka?
bakisan kaddara ba?
kobakya yafiya?
ta girgiza kai ta share hawaye da gefen gyalenta tace bahaka bane alh nafi jin dadin rayuwa anan fiye da can, na yafewa duk wanda ya zalunceni irinsu Tasi'u da matansa nayafewa duk wanda sukayimin Kazafi irin mummy hafsat general Tukur da kawata sumayyah, na yafewa 'yayana dasuka ki min biyayyah amma na hakura da kara cigaba da rayuwa dasu babu mai wankeni a duniya sai Allah, Abba ne yafi kowa sanin gaskiya lamarin shi zai fitarda ni, shikuma baya raye to mezanzo nayi?
sai ta rushe da wani kuka mai daga hakalin mai sauraro,
alh Adnan yayi ajiyar zuciya yace kinaso kigayamin da Abba na raye zaki yarda ki dawo saboda zai wankeki daga zarginda ake miki?
Madina ta gyada kai tace eh da Abba naraye zan dawo saboda nayarda da son da yake min koda ace bazan aure shi ba,
ADON DAWA 41
.
TRUE LIFE STORY.
.
Ko da ace baxan aure shi ba inason Abba har raina.
kinaso kice min da Abba naraye yace har yanzu yanakan bakansa na auranki da yake son yi zaki aure shi?
Madina tace tabbas da matacce na dawowa da zan auri Abba, nayi nadamar abunda nayi masa gashi duk da gudun rigimarda nakeyi naki amincewa saida ta afku har fiye ma da ace na yarda,
alh Adnan yace bakya tunanin 'yayanki musamman karamar mace?
ta sharce hawaye tace alh na rayu ba uwa ba uba babu yayye amma daga baya na hadu da mutanen da suka fiye min iyayena da dangina alkhairi duniya da lahira don haka rashina bazai zama shine karshen gatansu ba Allah shine gatan bawanSa Allah Ya hadasu da abokan zama na gari, ina daganan ina jifansu da kyawawan addu'o'i bazasu tagayyara ba insha Allahu, babbar damuwana daman kaltum ne na matsu ta koma gida ta rayu da iyayenta tayi aure cikin mutunci Allah Ya amsa addu'a ta yanzu hankalina ya kwanta zanji da kaina,
alh Adnan ya shiga yi mata magiya yana hadata da ta duba girman Allah da darajar Manzon Allah (s.a.w)ta dubi matsayin musulmi awajen dan uwan ta musulmi yayi mata alkawarin bazai fadawa su mummy hafsat ta dawo ba bakuma kano zataje ta zauna ba, a Abuja zatazo ta zauna tare kaltum,
tun Madina tana bashi hakuri akan ya daina ma rokarta bazata dawo ba har tayi shiru ta rasa abunda zata fada masa daga karshe ya fada mata wata magana da tayar mata da hankali yace da ita Madina dalilin da yasa nace a nemoki shine Abba bai mutu ba, duk tsawon shekarun nan yana kwance yana jinya a asibiti anan Abuja, bai daina Kiran sunanki ba ki tausaya masa kizo ki ganshi ko Allah zaisa ya warke...
alh Adnan ya katse waya ya barta a zaune kikam rike da waya ahannu tamkar gunki,
Hajia salaha ta dubi maigidan nata ta tsuke fuska yayinda ta rike kugu ta girgiza ko ba a fada masa ba yasan yau akwai rigima ta tambayeshi tamkar danta, dawa kake waya wacece Madina?
daman kai ai komai inda Madina aciki kafi bashi muhimmanci, wato bayan kaltum dinda aka aika aka dauko har kawarta xaka dauko?
kaine bawansu kai zaka dauko ta to bari kaji babu matarda zata dakomin gida don naji kana lallashinta idan batason kano taxo Abuja.
Alh Sa'adu kuwa sai magiya yake mata da nasihohi iri iri yake jero mata akan ta taho su tafi, haka mata da mazan gidan suke shawartarta ta shirya ta tafi tun kafin damar nan ta subuce mata suna masu yi mata albishiri da sune suka sami wannan dama da karshen matsalarsu tazo a dunia, daga karshn Madina ta shirya tayi sallama da yan gidansu aka yi ta kukan rabuwa saboda an saba, sabo turken wawa, bata fito daga bur sudan ba saida ta garzaya jim arab kasuwar yan ADON DAWA ta iske mambela a rumfarshi da abokansa suna shan jubna yana ganin jajayen idanuwan Madina sai ya wurgar da kofin jabna ya zabura ya mike tun bata karaso rumfar ba ya tareta yana tambayar ko lafiya?
agigice ta rushe da kuka cikin yaren ADON DAWA tace mambela nima anzo daukana zan koma Nigeria gidansu kaltum.
ya dade yana dubanta bai iya magana ba cikin sanyin murya yace da ita ki daina kuka ki share hawayenki abun murna ne ki gaishe min da kaltum kice har yanzu ina son ta,
sai hawaye ya kwaranyo daga idanuwansu su dukka ya juya ya koma cikin rumfa ya zauna jikinsa ya mutu ya zurawa Madina ido har ta kure, yaki amsawa abokansa tambayoyinda suke ta jera masa,
daga bur sudan Madina da alh sa adu jirgin kasa suka hau na zuwa Khartoum ya kai ta gidan wasu mata yan Nigeria acan ta zauna har tsawon kwanaki hudu ana cuku-cukun tafiya visa da ticket sannan suka sami tahowa bayan komai ya kamkama,
ranar talata da yamma Madina da alh sa'adu suka dira a birnin tarayyah Abuja, daga filin jirgi suka bugawa alh Adnan waya yace su ba wa mai taxi waya yayi masa kwatancen gidan, tunda dan gari ne nan da nan yagane anguwar gwarumpa gidan alh Mansir babban amininsa na Abuja kenan,
kafin sukaraso har alh Adnan ya bayyana a gidan daman ya shaidawa mai gidan zai kawo musu bakuwa su rike masa har zuwa wani dan lokaci saboda yasan halin matansa bazata bari ta sauka agidansa ba,
hankalin alh Adnan ya tashi dayaga Madina daga ita har jikinta da buhun kayanta da take rike dashi, ya fada aransa daman wannan itace madinar da Abba yake muradin so kamar zai rasa ransa adalilin rashin ta?
to koba haka take ba ada yanzune tazama haka?
Madina ta durgushe agabansu ta gaishesu ba tare da ta matso tsakiyar kafet din da yake tsakiyar falonba balle ma ta hau kan kujera ta zauna,
hajiya zainab matar alh Mansir ta taso da fara'arta ta karbi buhun kayan Madina tana mai yimata sannu da zuwa da bata izinin ta iso cikin daki, Madina ta na biye da ita a baya zuwa cikin daki, katafaren daki mai dauke da
tafkeken gado da madubi da durowar saka Kaya, bandakin acikin daki bayan ta saka buhun kayanta a durowa sai ta nunawa Madina bandakin ta umurceta ta shiga ta yi wanka za a kawo mata abinci yanzu, sai mamaki da farin ciki ya lullube zuciyar Madina yaushe rabon duniya da ayyaraye wai yau ita ake cewa ta shiga kayataccen bandaki tayi wanka ta fito taci abinci?
da irin wadannan tunane tunane ta shiga wankan kafinta fito ta iske mai aiki ta jera mata abinci kala-kala agaban gado, kamshi da tururi ne suka daki hancin ta,
haj zainab ta shigo da fara-arta ta dubi Madina tace ga wata atamfa nan tawace sabuwa ce na dinka ko sakawa banyi ba jiya aka kawomin daga wajen dinki ki saka alh Adnan yace kada abari kisake mayarda kayan
jikinki yace kikawo buhun kayan a zubar zai dinka miki wasu, kin san shi dan gayune ga tsafta baya son tsohon abu, sannan kici abinci mutafi asibiti yanason a duba lafiyanki gaba daya agani ko akwai rashin jini ko wata cutar a baki magani,
madina tayi kasake tana duban hajiya zainab kamar a mafarki take jinta, tayi murmushi yayinda hawayen farin ciki ya cika mata ido tace to ta jawo sabuwar atamfa super holland ta saka kayan kuma daidai jikinta kasancewar itama hajiya zainab din bamai kiba bace saidai kash bazata iya yafa tsalelen gyalenda aka hado mata da atamfarba, hijab kawai take iya sakawa tafita waje saita yiwa hajiya zainab bayani cewa inda hijabi ta bata bata yafa gyale aka kuwa yi sa'a akwaita da hijabai kala kala saita dauko mata ruwan daurawa wanda ya dace da atamfar kalar koriya ce da ruwan daurawa,
Madina ta zauna ta fara bubbude manyan fulasan abinci taga soye soyene na doya da dankali da wainar kwai ga flask din shayi ga biredi da cake duk wanda takeso zataci, tsohuwar yunwa dake jikinta ta taso sai citakeyi batasan inda abincin ke tafiya ba ma, har taci rabin abincin batayi rabin koshiba rabonta da tasami abinci mai dadin wannan harta manta.
alh Adnan alh Mansir dakuma alh sa'adu haryanzu suna zaune a falo suna tattaunawa akan irin wannan matsananciyar rayuwa da mata da yara kanana suke jefa kansu ta tafiya kasashen wasu da zummar neman kudi, daga karshe naira na dukan naira har naira dubu dari biyu da hamsin aka bawa alh sa'adu bayan tikitinsa na komawa sudan kamardai yanda ka bashi dayakawo kaltum sukayi sallama,
alh Sa'adu yana sake nanawa alh Adnan cewar yana nan dai idan aka sake samun irin haka a tuntubeshi a shirye yake daya taimaka sannan ya tafi,
bayan ya sallami alh sa'adu sai Adnan ya caske kudi yabawa haj zainab ya umurce data kai Madina asibiti a kwantar da ita a asibiti ko lafiyarta kalau akwantar da ita ta huta sannan a dinga Saya mata duk wani abinci mai gina jiki domin daga ganin Madina ko ba a fada maka ba kasan babu blance died a jikinta, yasa aka kira masa Madina ya dade yana yimata nasiha akan ta kwantar da hankali a sami lafiyarta kafin ayi maganan Abba...
Sai tayi caraf tace alh zanso nafara ganin Abba tukunna kafin inje asibiti tunda dai ahaka lafiyata Kalau.
ya girgiza kai yace ta Abba mai saukine bani nace Zaki gashi ba?
zankawo mikishi ki ganshi.
ta sunkuyar dakai kasa sai hawaye sharaf sharaf sharaf sharaf tasan wayo yayi mata don ta dawo amma babu Abba, ya mutu
alh Adnan ya lura kuka takeyi sai ya shiga lallashinta yana dada jaddada mata zataga Abba ta kwantar da hankalin ta ita dai ta fito daga asibitin tukunna.
tayi ajiyar zuciya tace Allah Ya kaimu Allah Ya sa muga alkhairi, ina kaltum kuma?
alh Adnan yace kaltum tana nan lafiya itama zaki ganta tare da Abba,
saita kura masa ido tana masa duban rashin
yarda yayinda tashiga kokonton ko ta fada hannun yan damfarane?
saitace aranta Allah na tare da ita Shizai fitar da ita ko a wanne hali ta tsinci kanta,
alh Adnan yayi musu sallama ya tafi,
Haj zainab da mai gidanta suka umurci Madina ta biyo su za'a kaita asibiti tana zaune a bayan moto tana duban gari yayinda hawaye bai daina zuba ba, wata zuciyar nace mata meyasa ta yarda ta dawo gashi ita ta zo ita bada ganin kaltum ba balle Abba, wai shin ina hankalinta da tunaninta yatafine da har akayi mata wayo aka dawo da ita Nigeria?
Sai ta tuna da komai yasami bawa mukaddarine ne daga rabbul samawati abunka da mai ilimi saita share hawayenta taci gaba da kallon gari tana duban manyan gine gine da titina kayatattu a birnin tarayyah Abuja daman bata taba zuwa Abuja ba a rayuwarta tace aranta ashe muma munada kudi a kasarmu. tome sudan zata nuna mana dahar muka je muka makale musu.?
ta gangaro tunanin 'yayan ta taji a ranta babu abunda tafison gani ahalin yanzu irin ta ga ' ya yanta tayi kamar tace musu sukaita tasha su sakata a motar kano ta fasa zuwa asibitin
saita daure tayi shiru tana mai biyayyah da umurnin wanda ya taimaketa alh Adnan,
suka isa kelina hospital dake cikin unguwar gwarumpa, lafiyayyen asibiti mai kunshe da kwararrun likitoci.
ADON DAWA 42
.
TRUE LIFE STORY
.
haj