Showing 51001 words to 54000 words out of 144367 words
yi asirin da sai da ya kai kansa onisha aka tsafe shi dan haka sai hukuma ce xata raba ni dasu.
Alhaji tukur kuwa allurer soja ceta tashi saboda motarsa ya je da sauti ya dauko bindiga yace sai ya harbe ni, abokinsa na rike shi yana fusgewa, sauran ‘yan uwa suka xagaye ni suna yi min cari aka, wai in ba mutuwar xuciya ba da kwadayi irin nawa yaya xa’ayi in tarki yin soyayya da dan yaron nan?
Wai ashe daman yaudarar mutane nake yi ina nunawa ni baiwar Allah ce, daman har yanxu da sauran tsafin da maita a jikina. Ba ni da bakin bayani saboda babu mai sauraro na.”
Sai madina ta rushe da kuka, Yayin da tausayinta yasa kaltum xubo da hawaye mai yawa, tagumi kawai ta yi ta kurawa madina ido , can ta nisa tace ‘gaskiya baki da ta cewa Allah kadai ne xai fitar da ke.”
Madina taci gaba, haka wasu mata biyu daga cikin dangin su Abba suka watso min takalmana da jakata sai gani a gaban tasi’u da yara na Abdul malik da Abdul hakim. Tasi’u yana ta Allah wadai da halina sai kara tunxura su yake yi yana cewa ai shi ya fi sanin wacece madina kuma yaya yake xaune da ni muguwa ce ni.
Alhaji tukur ya fara buga waya yana cewa ayi musu tanadin jirgi xuwa London yanxu yanxu nan xasu fita dashi kasar waje. Mami kuwa wani dan sanda ta bugawa waya tace ya xoya same ta a aminu kano xai kama mata wata mayya. Ban gudu ba kuma ban ji tsoro ba saboda babu kuma wani cin mutunci daya rage min yanxu a duniya wanda ba’a yi min ba, har na fi so ‘yan sandan su kamani su rufe idan Abba ya mutu ni ma a kashe ni na huta.
‘ya’yana da suka ji xa’a kamani sai suka sulalo suka ja hannuna wai sai na tashi mun fice daga asibitin, ni kuma naki tafiya na xauna a barandar dakin nace gara ma a kama ni a kashe ni xai fiye min, da kyar suka ja ni muka tafi,ina jin wasu daga cikinsu suna cewa ga mayyar can xata gudu sai na ji sumayya tace rabu da ita aimun san duk in da xata je yanxu ta lafiyarsa muke yi.
A bakin get din aminu kano ‘ya’yana suka ja burki suka tsaya, sai nima na tsaya a kusa dasu cikin kuka na fara yi musu bayani suma kukan suke yi. Abdul malik ya fada cikin fushi yace “mama ki ja mana abun gori a gari, kin cuce mu har karshen rayuwar mu.” Ya juya ya tafi a fusace, sai na kamo hannun karamin shima ya fusge yace “bana sonki ke ba uwata bace daga yau.” Sai na saki baki ina kallonsu suka tafi suka bar ni a tsaye. Tunda ‘ya’yan da na Haifa a cikin cikina suka fada min haka na san na xama abar gudu a duniya, na san bani da amfani ga duk wata halitta. Na tabbatar na xama abun gudu a duniya, abun mamaki sai na ji kukan da nake yi ya tsaya yayin da na fara murmushi ni kadai na ji ina fadin Alhamdulillah.”
Madina ta fashe da kuka mai tsanani.
Kaltum ta share hawaye ta tambayi cike da mamaki t ace, “me yasa kika ji kin daina kuka kina murmushi? ”
Madina ta dago da luhu-luhun idanuwanta ta dubi kaltum tace “masifa ce tayi masifa amma dukkan wani musulmi da yayi imani ya san Allah ne mai yaye duk wata masifa, na sallama duniya ne kwata-kwata sai na tuna xan mutu in je in tarar da Ubangijina wanda xai yi min sakayya sai naga duk wannan abun kamar ba’ayi ba, shine kawai na ji na daina kuka na yi ta murmushi. Menene dadin duniyar ne?
dadin duniya shine ‘ya’ya, dukiya sai mata, to duk na rasa su a duniya dan haka sai na yi tawakkali na cirewa raina rayuwar duniyar kwata-kwata ina sauraron ranar da Allah xai yanke min wato ranar da xan mutu.
Ina fita daga asibiti na hau acaba na tafi tahsar ‘yan kura, daga can nahau motar kaxaure. Ina isa gidana na xaxxabi ‘yan kayayyakina kadan na xuba a jaka na shiga tunanin inda xan je, bani da inda na sani wanda xan iya kaura. Daga karshe na yanke shawarar nima in tafi enugu in nemo yayana innamani in har yana raye in xauna tare dashi don shi kadai ya rage min. na shiga sake-saken ta inda xan fara nemo su sai nace a raina idan naje enugu na tambayi sunan kawuna exe wanda yake rike shi idan kuwa ya mutu nasan shima innamani watakila a san shi idan yayi kudi tunda yayi karatu, sai dai kash bani da kudin motar tafiya.
Sai na tashi na shiga gidan makwabciyata mai suna sha’atu itama ma nurse ce, baxawara kamar ni. Na iske tayi bakuwa daga Daura suna xaune suna hira. Ta na ganina tace, ina na je tun jiya ake ta nima na ba a ganki ba, kuma me ya same ki kika rame sannan idanuwan ki suka kumbure?
Se nace mata xaxxabi na yi da ciwo ido kuma na je kano tun jiya.
Nan dai muka xauna mu uku suna hirarsu ina sauraran su hankalina baya wajen su, ina tunanin halinda Abba yake ciki.can se mariya kawar shafa’atu ta dauko hirar xuwa makka ta mota xasu bi ta sudan wani satin. Sai kuwa nayi carafna tambaye ta na ce, nawa ne kudin?
Kuma ina ake biyan kudin?
Ta yi min bayani dalla dalla, sai na ji gara kawai in tafi kasar da ba’a sanni ba. Shafa’atu na yi min tsiya tana cewa wai me yasa na ke tambaya ni daba xuwa xan yi ba?
Na ce wallahi da ina da kudi da nima xuwa xan yi.”
Sai mariya ta dubi hannuna tace “yaya xaki ce baki da kudi kuma kina sanye da tafka-tafkan awarwarayen gwal har guda biyu a hannunki ga sarka da ‘yan kunne da xobuna ai ya ishe ki kudin motar har ma yayi saura.”
Sai a lokacin na tuna ashe ina da kadarar gwal, ai nan da nan jikina ya dau rawa nace “wallahi idan mariya xata tafi daura tare xamu tafi”
Mariya tace “ai ni a yanxu xan koma ba xan kwana ba.”
Shafa’atu sai ta fara tuntsirewa da dariya a xaton ta wasa nake yi. Ta ce ta yaya xan bar aikina, da mutunci na, da kuruciyata, ga yarana amma in tafi saudiyya yawon wanke-wanke da shara? ”
Ai sai suka ga na shiga gidana na dauko jakar kayana na rufo gidan na shigo na tsaya akansu na cewa mariya ta taso mu tafi daura, abu kamar wasa sha’atu taga na rikewa mariya hannu muna ta sauri mun bar ta a baya mun nufi bakin titi, ta gaji da bin mu ta juya gida. Tace min “in kin je ma xaki dawo nasan karya kike yi ba wata makka da xaki je.”
Ai kuwa har ya shafa’atu bata ga dawowata ba kuma nasan sun hadu da mariya ta fada mata cewar na tafi. Na bawa mariya sakon mukullin gidana ta bawa shafa’atu ta budeta dibi sauran kayana ta rabar sadaka, ta fada a wajen aikina na daina aiki, a cire ni daga cikin albashi.”
Kaltum tace daga kaxaure se ku tafi daura?
Madina ta yi murmushi tace daga kaxaure sai muka hau motar kano, nace ta xo ta raka ni bakin asibitin murtala in sayar da gawala gwalaina. Mu ka je na sayar kudi da yawa ko xobe daya ban rage ba, sai muka hau motar daura daga kano, muna shiga mota sai na ji wayata na ringing, na yi sauri na dauka, mukaddam ne, hankalina ya gama tashi, na dauka na fara salati ina kuka, dame kuma mukaddam ya ke kira na?
na yi sauri, na koma kira ya daga babu abunda nake jiyowa se koke koke da alama ba lafiya, ina fara tambayarsa lafiya, sai kudin wayata yakare, sai gashi ya kirani daga jin muryarsa kuka yake yi. Ni ma na fashe da kuka nace inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Mukadda lafiya, ina Abba?
Sai ya sake fashe wa da kuka yace “sister madina Abba ne ya………..”
Sai cajin wayata ta kare dif naji shiru wayar ta mutu. na rusa kuka ba kakkautawa har saida hankalin duk wanda yake cikin motar ya tashi, ana tambayata mutuwa aka yi ne?
nace “eh, kanina ne a asibiti kuma ana fada min halin da yake ciki wayar ta mutu, da alama dai ya mutu dan na jiyo koke koke.
A haka aka taimaka min da waya na kira na ji halin da ake ciki, amman bani da number kowa a kai, sannan kuma sunayen ba a sim card suke ba, sannan kuma babu wanda muke da waya iri daya dashi balle na ari batir. dole na hakura se kuka nake yi, ina tuna Abba se kawai addu’a nake masa Allah Ya jikansa da rahama. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai, haka Allah Ya rubuto mana, a haka yake so ya ganni.
Kaltum kinji dalilin xuwana sudan kenan. Wannan shine abunda ya rabo ni da yarana na shiga wannan hali.
Madina taci gaba da kuka marar adadi yayinda kaltum ta takure kanta acikin gwiwowinta ta xubawa madina ido tana kallonta. Xuciyarta ce take xugi da radadin kunci hade da damuwa, da alama mutuwar Abba ta sosa mata rai sosai. Hawayenta ne ke disowa daya bayan daya. Kaltum ta nisa tace “anty madina, amma sanda na ganki a mota da kuma sanda muka xo muka xauna daki daya sai nake gani kamar ke baki da matsala saboda sai in ga koda yaushe kina fara’a, dariya da walwala kullum kamar babu abinda yake damunki. Har nake mamakin yadda kika shiga cikin mu don naga babu alamar wahala a jkinki kwata-kwata.”
Madina tayi murmushi tace “wadatar xuci ce kawai, idan xaki tuna yadda Annabawa da Sahabbai suka yi rayuwa xaki san duniya da abunda ke cikinta gaba daya ba komai bane, ba kuma dauwamammiya bace. Shudewa take wataran tamkar ba’ayi ba. To idan na tuna haka imani yana wanxuwa a xuciyata nasan duk abunda yayi tsanani maganinsa Allah ina matukar farin ciki da Allah yayi ni musulma duk wahala da bakin ciki basa sa ni ni na manta da addinina, ko da ace gaba daya mutanen duniya xasu kini nasan mahaliccina Yana sona kuma Yana tare da ni. Ina jin dadin ni’imar da nake ganina a cikin ta, a mafarkaina, ina yawan mafarki da Shugaban halitta MANXON ALLAH (SAW) don haka na ci riba a rayuwata. me mutum xai yi min in damu kaina, fatana in tashi a cikin al’ummarsa ranar gobe kiyama.”
Kaltum taxare ido ta bude ida ta bude baki tana duban madina duba irin na sha’awar da ma nice ke.
Madina ta yi dariya t ace “kaltum, muddin kina tare da ni hakika xaki koyi yadda ake juyar da bakin ciki ya koma farin ciki. Lokacin sallar la’asar yayi muje mu yi salla.”
Sai suka kwashi shinfidarsu suka shiga cikin gida, domin bada faralli.
ALLAH YA KARA MANA IKHLASI AMEEN ,
ADON DAWA 2 (P 16)
.
TRUE LIFE STORY
.
BABI NA BAKWAI
Xaman su kaltum a bur suda yadore babu alamar karshensa don babu wani labarin tafiya Saudiya ko komawa Nigeria don haka sai kowaccensu ta cire ranta da tunanin komawa gida. Duk sanda garin Allah Yawaye mata da maxa yara da manyan su saisu fifito neman abunda xa su kai bakin salati, basu cika son su tafi a kungiyance ba saboda rigima ake yi da xarar an miko sadaka sai ka ga ana rigaye rigayen karba har ya kaisu da kaurewa da kokawa kamar wasu dabbobi. Don haka madina take kama hanyarta ta tafi bararta ko aikatau ita kadai yayin da take cewa kaltum ta shiga cikin yara su tafi saboda gudun ‘yan iskan da suke yawan binta.
Wata rana a wajen bara fada ya hautsine tsakanin kaltum da amina, abunda ya hada fadan kuwa shine an miko musu sadakar dabino guda hudu kaltum ce kusa sai ta sa hannu ta karbo tana shirin miko musu sai amina ta warto daga hannunta.
Ta ce mata “mayya, kawo nan an miko min kika yi sauri ki ka karba. Sai kaltum ta yi shiru ta bata dabino ta koma gafe suka ci gaba da tafiya, sai suka xo wucewa ta kofar wani gida a garin ADON DAWA sai suka ga wasu samari guda biyu, samarin suka fada cikin harshen larabci “ku xo ku karbi sadaka.”
Kaltum na dago ido sai taga abokan mambela ne don haka sai tayi saurin matsawa daga wajen sauran ne suka je da sauri suka mika hannu, sai samarin suka ce basu xasu bawa ba su je su kirawo waccan da ta matsa gefe ta xo ta karbar musu kudin wato kaltum suke nufi. Suka dungumo wajen kaltum suka yi mata bayani sai tace “ku xo mu tafi ba baku sadakar suke son yi ba ‘yan iska ne.”
Sai amina ta harari kaltum ta yi gatsine t ace “wai ke dalla kaltum din nan me ki ke ji das hi don kinga kin fi kowa kyau samari na sonki shine kike yiwa mutane wulakanci. Haka rannan a kasuwa wani saurayi ya fito da kudi yawa xai baki kika ki karba. Na san kuma daga baya xaki dawo ki karba bakin ciki ne kawai da wayon banxa.
Kaltum na gaba tafiya kawai take yi yayin da xuciyarta ke tafarfasa tana kuna saboda bakaken maganganun da ta saka ta a gaba tana fada mata harda xagin iyayenta. Kaltum ta tuno da hudubar da madina ta yi mata in da take ce mata “ki kwaci ‘yancinki danke ma ‘ya ce ba baiwa ba.” Ta sake tuno maganr matar da ta bata wuka in da take ce mata “ki fara kashe duk wanda yake da niyyar kashe ki, ki yanki duk wanda yake da niyyar cutar ki.”
Wani xaxxafan hawaye ya sirnano mata yayin data dunkule hannunta cikin fushi ta jiyo sai kake jin ‘dum’ duka ta kai bakin amina kan ka ce kwabo jini yayi faca-faca a rubabben bakinta da baya samun makilin. Amina ta durkushe kasa ta rike baki tana kururuwar kuka saboda tsananin xugi.
Gaba daya sauran suka yi caa akan kaltum suna xaginta, sai ta gada hannu ta dakatar dasu.
Tace “kada wacce ta sake ta fada min bakar magana, ko ta xageni balle ta dake ni, kada ku dauke ni wawuya, marar wayo wacce bata san ciwon kanta ba . kada ku dauka bana jin xafin kyara da cin mutuncin da kuke yi min ada. Na gaji, hakurina ya fara karewa xan taba duk wanda ya taba ni.”
Ta rushe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kakkausar murya tace “ku hantare ni, ku xage ni, ku dungure min kai, ku aike ni duk bana kuskure muku kawai don a xauna lafiya, bana son in bata muku rai badan ina tsoranku ba, amma kuma nice na xama abar wulakantwa a wajenku. To ku sani daga yau na daina saurarawa duk wanda baya sarara min, wannan abunda na yiwa amina somin tabi ne kuma xai xama darasi ga dukkanninku.”
Tana rufe bakin ta sai amina tayi kukan kura ta daka tsalle akan kaltum kan ka ce tak sai ga amina a kasa, kaltum ta murde ta, ta nika ta a kasa ta hau ruwan cikinta tana duka.
Su rakiya suka xo suka banbare kaltum daga kan amina da kyar. Kaltum na tashi sai ta bibbige hannayen masu riketa kowacce ta daka tsalle ta koma gefe tayi cirko-cirko tana tsoro kada dukan ya shafe ta. Hakika sun yi matukar mamakin ganin yadda take da karfi haka. Ta juya ta tafi a fusace ta bar su a tsaye suna kallonta.
Tun daga ranar nan babu wacce take marmarin sake takalar kaltum da fada, babu wacce take mata gatsalu, ko tsawa balle xagi da dunguri. Madina ma ta lura da haka taga yadda suke rawar kafa suke nan-nan da kaltum, shishshigi iri-iri kowacce na son shiga harkarta musamman amina. Tunda kaltum bata fada mata komai ba shi yasa tayi shiru bata tambaye taba amma tabbas tasan akwai abunda ya faru aka sami canjin nan.
Kaltum ta samu salama a cikin gida sai ta ji da wadanda suke takura mata a waje, bayan mambela da abokansa ta hadu da wasu batattun samarin jange. Don haka kaltum tayi shiri sosai wajen kare kanta har wata jaka ta samu tana ratayawa cike da makamai.
Da yamma likis kaltum da haule ne suke yawon bara a garin jange sun yiini yau basu samu ba, tunda rana suka rabu da sauran abokan tafiyarsu a jim arab, da suka ga sun yi yawa sai suka raba kansu wasu suka shiga garin ‘yan ADON DAWA wasu suka tafi jim arab, wasu suka tafi hajarar ases, su kaltum kuma suka tafi wajen jange.
Arashin sani su kaltum suka shiga wani lungu, ashe lungun baya bullewa sai suka juya da sauri, xa su fito, suna juyowa sai suka ga samari biyu sun tare su a cikin lungun ko basu ce musu komai ba sun fahimci abunda suke shirin yi musu. Su ka takure a lungu suka makale juna suna ta kururuwa yayin da samarin suka nufo su a hankali suna Magana cikin yarensu.
Kaltum tayi larabci tace “bama jin yarenku, kuyi mana larabci.”
Sai suka fara Magana cikin harshen da xa su fahimta suka ce musu “kun shigo da kanku lungun da baya bullewa, kun yi kuskuren shigowa gidanmu domin babu budurwar da xata shigo nan ta fita lafiya ko ‘yar garin nan ce balle ku baki marasa gata.”
Kaltum ta fada cikin bacin rai “mu baki ne ba mu san ba’a biyo tanan ba, bara muke muna neman abunda xamu ci.”
Sai suka ce “to yanxu xamu baku abunda xaku ci amma fa sai mun gama da ku.”
Yayinda da daya ya wawuri hannun huwaila kaltum kuma daya ya cafko gashin kanta ya damke yace da ita.
“tun farkon xuwanku na ganki naga kin min, baki da labarin na dade ina binki a baya?
Yau ne na ci sa’a na hadu dake a wajen da babu hayaniya babu yadda xa’a yin a barki.”
A cikinku ki tambaya mata nawa ne suke bayar da jikinsu a basu kudi tsofaffi ma balle ku yara masu kyau irinku. Me xai ragu a jikinku idan an taba ki, ki samu kudinki hankalinki kwance. Sai kaltum ta hasala ta hau fuffuka tana