Showing 138001 words to 141000 words out of 144367 words

Chapter 47 - ADON DAWA

Unknown   

30 Oct 2024

5070

ciki ya surnano daga idanuwansu dukka biyun.
madina ta ambaci sunansa cikeda farin ciki sai ya juya da sauri ya dubeta sai yanzu ya shaida Madina ce, itama ta canja ta goge kamar ba ita ba sai mamaki mai dimbin yawa ya rufeshi ya fada cikin yarensa na ADON DAWA a ah yaya naganku kunzama tamkar larabawa dama kunfi jin dadin a kasarku kukaje kasarmu kuke wahala?
dubi yanda kuka zama fa?
kaltum da Madina sai dariya sukeyi kawai donsu kadai sukeji abunda yake fada.
Madina cikin harshen turanci ta gabatar masa da Abba, mambela ya mika masa hannu suka gaisa cikin harshen turanci yace Abba na dade inajin labarinka ashe baka rasu ba?
Madina ta gabatar masa da saleh da sofi cewar ga iyayen kaltum, da taga mambela na kokarin mika masa hannu sai tayi masa larabci tace ya durgusa ya gaishesu al'adarmu ba a hannu da surukai don haka mambela yaje gabansu ya durgusa ya gaishesu da larabci suka amsa da hausa ya dawo ya zauna a kasan kafet kusa da abar kaunarsa kaltum,
alh Adnan yayiwa mambela bayani cewar ya fada musu komai kuma in shaa Allahu babu matsala komai zai dai daita yanzu abunda ya rage shine idan ya koma kasarsu ya taho da iyayensa mata da maza da duk kayanda akeyi na al adarmu ta hausa wajen nemar aure,
mambela ya tambayeshi me ake bukata a auren hausawa?
alh ya nuna kaltum yace ga amarya ka tambayeta ta yadda akeyin komai amma kafin atashi daga wannan zaman inaso inbawa iyayen kaltum dama ko suna da abun fada ko korafi ko suka gameda hukuncinda na yanke saboda kunada hakki akan yarku, wlh duk abunda baiyi muku ba ku fada zan cenza ra ayina kuma bazan damu ba.
saleh ya girgiza kai yace ko da wasa baka taba zartar da hukunci akan kaltum wanda zai zama ba dai dai ba ko wanda zata yi nadama daga baya ba, ka fimu ilmi kafimu tunani kafi mu kula da rayuwar yar nan sunan mun haifeta ne kawai babu wata matsala wallahi fatanmu Allah Ya bada zaman lafiya kaikuma Allah Ya saka maka da alkhairi,
sofi ma irin wannan addu ar ta dinga zazzago masa,
Abba da Madina ma sunyi masa addu'a da godiya a bisa kyakyawar niyyarsa.
kaltum ta durgusa a gabansa tayi masa godiya haka ma mambela sannan ya umurci kowa ya tafi sai da safe kuma,
suka duguma su dukka suka fita daga falon,
alh Adnan kadai aka bari a zaune fuskarsa cike da fara a da alama yafi kowa farin ciki da Allah Ya nuna masa ranar daya cikawa kaltum burinta.
Madina da Abba suka raka har motarsu suka shiga suka tafi sannan sofi da saleh ma suka shiga gida,
mambela da kaltum ne a zaune akan kujera a farfajiyar gidan suna rera hirar yaushe gamo hirar so da kauna suna masu godewa Allah daya sake hadasu badon sunaso ba sai don dare yayi sukayi sallama kaltum ta shiga gida mambela ma ya shiga gida, alh adnan dama ya nuna masa dakinda zai kwana anan ya ajiye akwatinsa tun sanda sukazo yadda bacci ya gagari idanuwan mambela haka ya gagari kaltum juyi kawai sukeyi suna tunanin juna yayinda farin ciki yayi musu katutu a zukatansu kamar wadanda suka hada baki a alokaci guda suka ayyana aransu tunda bacci ya gagara gara su tashi suyi alwala suyi sallah su godewa Allah dayayi musu wannan
babbar kyauta.
Madina ma da Abba suna can a gidansu sun raba dare suna hirar wannan abun al'ajabi ashe sofi ma da saleh farin ciki ne ya hanasu
barci suma suna daga daki suna tattaunawa sai dai duk rabin hirar tasu addu a ce suke jerowa alh Adnan suna yi masa fatan Allah Ya biya shi da gidan aljannah.
daya bangaren kuwa alh Adnan ne kwance kan gadonsa ya takure yayinda kuka ya kece masa yana addu ar Allah Ya kara masa dangana da juriya rabuwa da kaltum domin yana sonta har cikin ransa kuma yayi niyyar auranta saidai ya fuskanci zai tauye mata rayuwa saboda akwai wanda takeso bashi ba don haka ya sadaukar da son da yake mata ya bata wanda takeso donta sami nutsuwa arayuwarta shiya yarda da duk wani tsanani da zai shiga na sanadiyar rabuwa da ita,
juyi kawai yakeyi yayinda zuciyarshi ke tafarfasa don tsananin tashin hankali da yake addabarsa, yana kiran InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah Ka yayemin abunda nakeji kada in dauwama dason kaltum a raina har gara in mutu da in dauwama cikin wannan hali ,
ahankali yaji zuciyarsa na sanyi saiyayi wuf ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala yazo ya kwana yana sallah yana neman hakurin dangana da neman sauyi mafi alkhairi,
washe gari da safe sofi da kaltum suka dinga hidimar dafe dafen abinci kala kala don su bawa bakonsu, sun san halin alh Adnan ba cin abincin safe yakeyi ba kofin shayi dayane zaisha saikuma da rana ko sun kai sunsan bazai ci ba saidai mambela.
kannen kaltum ne suke jerawa kan daning table dinda ke falon alh Adnan yayinda alh Adnan da mambela suke zazzaune a falon suna tattaunawa da alama alh Adnan shiryo tafiya zaiyi harda yar jakar kayansa a gefensa, ya umurci mambela daya cigaba da zama a gidan kamar na sati biyu ko uku Madina ta zayyano masa komai sai ya tafi ya shirya suyi waya su fadi ranar da zasu zo sai a buga katin gayyata anan a rarraba suna zuwa sai a daura aure ayi biki gaba daya.
farin ciki ya rufe mambela ya rumgume alh Adnan yayi godiya suka dungumo suka fito zuwa bangaren su kaltum.
sofi da saleh suka fito da sauri suka durgusa suka gaishe shi, alh har zaka koma Abuja da sassafe haka ko karyawa bakayi ba?
sofi ta tambaya cike da kulawa,
alh adnan yayi dariya yace ai yau akwai aiki saboda mambela nazo amma zan barshi anan ya zauna har sawon sati biyu ku saba sosai kuma ya gana da amaryarsa sannan sai ya tafi daga nan basai yaje Abuja ba idan ya shiryo sai yazo da iyayensa a daura aure ayi biki akai ta dubai shi kenan, yasaka hannu a aljihu ya damko kudi ya ambulowa saleh a hannunsa yace ka rike wannan saboda cefene ya karu adinga dafawa mambela abinci mai kyau kuma kala kala ina kaltum din ne?
kaltum tayi wuf tafito daga daki sanye da hijabi tazo ta durgusa ta gaishe shi yayi dariya yace kin iya abincin zamani kuwa kosai tuwo irin na sofi?
donshi shi tafi kwarewa kullum kaga sofi to muciya ce ahannunta tana tuki ba a yin soye soye mijin kuma dan gayu ne ya saba da snacks da shawarma, kazar kfc, mr biggs, mcbanas, pizza a dubai ba ya cin tuwo idan baki iya ba kije Madina ta koya miki tun wuri nasan ita ta iya.
kaltum da iyayenta suka tunzure da dariya yayinda mambela yake tsaye yana kallon bakinsu ba tare da yasan abunda suke fada ba cikin harshen hausa, yaji yanaso ya koyi yaren hausa domin yanajin dadin sauraronsa tun ba yanzu ba.
daga yadda alh Adnan ya fuskanci mambela yana yawan kallon kaltum ya tabbatar yana sonta matuka har kamar zai hadiyeta, zuciyar sa na ayyane ayyane sai alh Adnan yaji kishi ya turnuke shi babu yadda zai yine kawai yaga kaltum ta kara kyau dariyarta ta zame masa lu'u lu'u a idanunwansa sai ya dinga karanta a'uzubiLlah minal shaidanir rajim kuma ya gaggauta barin wajen, da mambela ya rakashi mota sai alh adnan ya damko kudi ya bashi yace ya sayi duk abunda yake sha'awa, da farko mambela yaki karba yace yana da kudin Nigeria daya canza kuma yana da dalar.
alh Adnan yace saiya karba dole don haka mambela ya karba yayi godiya,
alh adnan yaja mota ya tafi yayinda hawaye mai radadi ya dinga fita daya bayan daya har saida ya ji turnukukin da yake damunsa ya ragu saboda karatun kur'ani daya kure a rediyon motarsa, addu'ace maganin masifa
haka hakuri maganin zaman duniya ya isa gida kuma ya iske matarsa na jiransa domin sai yanzu yan gulma suka kawo mata labarin aurensa da kaltum ta ayyana a ranta tafiyarda ya tarka da tsakar rana zancen auren yaje don haka tace ya zaba ko ita ko kaltum don bazata zauna da kaltum a matsayin kishiyarta ba.
saiyaji ya kasa magana kallonta kawai ya zauna yanayi saboda babu ciwon da yafi aibu irin jahilci ya yarda jahilcine ke damun salaha
kamata yayi ta tambayeshi gaskiyar magana tunda bayayi mata karya ai zai fada mata gaskiya saita yarda da gulmarda yan gari suka fada mata ta zartar da hukunci yasan hankalin mata tunanin su ragagge ne a matsayinsa na namiji sai bai kula ta ba tayi ta fadanta harta gaji ta daina.
kaltum da mambela sun kasance koda yaushe suna zama tare a kan wasu fararen kujeru a farfajiyar gidan sallah da cin abinci ne kadai yake tashinsu hira kawai suke yi cike da farin ciki marar misaltuwa idan dare
yayi kowa ya shiga barci sai su dinga magana a waya har assalatu sannan su tashi suyi wanka suci ado su fito su kafa kujera su zauna hira.
sofi da saleh suna ganin ikon Allah yarinya ta iya hira rairairai duk da larabci suke yi basa fahimtar abunda suke fada amma suna ganin murmushi da kashe ido da muryar da takeyiwa masoyinta ko ba a fada musu ba sun san sai yanzu kaltum ta sami wanda takeso wanda take ganin ya dace da rayuwar ta.
dan ladi direba ya zagaya da kaltum da mambela gidajen yan uwa da kawayenta, sunsha zuwa gidan madina da abba su gaisheta, madina ta taya su murna tayi musu nasihohi masu yawa ta rubutawa mambela duk abubuwanda ake bukata a auren hausawa ta kuwa zabga kudi fiye da yadda aka saba , sadaki ne kawai ta rubuta kadan don neman albarkar auren, dalilinta guda biyu na farko dan tasan suna da kudin sannan tanaso ya kashe kudi yaji ajikinsa zaifi rike aurensa da daraja duk da tasan ya gama shan wahala kafin ya sami kaltum, inda kudin yafi yawa shine wajen kayan lefe akwatuna shida tace ya ciko da tsadaddun Kaya baya ga lifgin gwala gwalai data ce ya zuba, abun mamaki sai taga bai damu ba harma yana ce mata yanzu haka saiya koma dubai don ya kai kudin gwala gwalan kamfani suyi masa disign mai kyau wanda za a rubuta sunan a jiki da sunansa.
satin mambela uku a kano acikin kwanakin daya yi saida sukayi kwana uku a zangon daura kwanaki uku a garinsu sofi saleh da danladi direba suka raka shi yaje ya gaishe da dangi su suka ganshi tabbas sunyi farin ciki da zuwan mambela don dollar ya dinga raba musu nan da nan suka ji kaunarsa a ransu sunyi amannah ya aure yarsu.
ranar dayazo tafiya madina da abba da kaltum ne suka kai shi filin jirgi sai ga kaltum da mambela suna kukan rabuwa, madina tana musu tsiya,
mambela ya tafi yabar kaltum zuciyoyunsu va
dadi amma bayan ya isa dubai sai suka bude shafin yin waya ba dare ba rana bai damu da daruruwan dirham din da yake kashewa ba wajen kiranta ba shi dai shidai burinsa yaji muryarta haka da ya isa sudan tun a Khartoum ya saka layinsa ya fara Kiran ta har saida ya isa bur sudan yanzu service har garin yan ADON DAWA don haka ba dare ba rana waya sukeyi saidai idan sallah zasuyi ko cin abinci da sauran uzururruka suna gamawa kuwa to sai su hau waya ko dayake mambela ne mai kudin kira ita nata sakon wasika ne tafi iya turawo da turanci koda larabci ko da wanne yare ne ma dai yana bata
amsa, kalaman dai naso da kauna ne da tsantsar bege duk wanda yasan kaltum saiya san labarin mambela haka shima sarki ya rasa kansa ba ya zuwa fada ko kadan yana daki a nade yana waya ko yaushe.
iyayensa sun yarda da bayanansa sun amince zasu shirya zuwa Nigeria.
saboda farin cikin an bashi kaltum mambela ya sami yan gidan su kaltum na bur sudan yayi musu albishiri da cewa duk wanda a cikinsu yake so ya koma kasarsu ya dauki nauyin biyan kudin motarsu da guzurinsu har zuwa Nigeria duk ya sadaukar saboda kaltum,
su iya mairo da jikarta su akawa wannan saboda sun matsu su koma Nigeria amma babu kudin mota, kadan daga cikinsu ne sukeson zama a bur sudan da yawansu sun amince zasu tafi ya umurce su suzama cikin shiri sai daf da bikinsa da kaltum a kano bayan biki zai bawa kowa kudin mota ya tafi garinsa, suka hau murna da tsalle suna masu yi masa addu ar fatan alkhairi sai suka hau hada tsummokarai suna wankewa.
kaltum ma bata zauna ba ta amince da shawaran alh Adnan tana zuwa gidan madina akai akai tana koyar abinci kala kala, i dan madina ta koma abuja sai mummy hafsat ta koya mata ko ta tafi gidan dr sumayyah ranarda bata zuwa aiki ta koya ba abinci kawai suke koya mata ba suna koya mata duk yadda ake zama da miji da yadda ake masa biyayyah yadda za arike zuciyar mai gida yaji babu wata a gabansa sai ita.
.
RANAR DAURIN AURE
rana bata karya saidai uwar ya taji kunya watanni shida mambela ya dauka sannan ya
dumgumo yazo da iyayensa tafe suke da kayan aurensa kakaf, abun nayine sarki da matarsa sun hallara haka baban mambela da mamarsa aka zo sai maza biyu tsofaffi da mata biyu tsofaffi suka taho a jirgi.
dandazon yan gudun hijira motoci biyu j5 ne suka iso kofar gidansu kaltum da kayan su mata da maza da 'yayansu kanana su suka fara isowa kafin ma su mambela su iso , da yake ya shaidawa kaltum tun a waya kuma ya turo kudin da za a sauke su don haka tayi tanadin zuwansu an nemi gidaje biyu haya daya mata daya maza, aka dinga dafa abinci
ana cika daruka ana aika musu aka daura auren mambela da kaltum, aranar wannan asabar din alh Adnan ne waliyin amarya manyan mutane daga wuri daban daban sun halacci daurin auren nan, kawun mambela daga dubai da manyan abokansa sunzo yan uwan sofi daga camoroun sunzo matansu da mazansu haka yan zangon daura da yan daura suma ba a barsu a baya ba.
alh adnan bai manta da malam Abdulkadir ba na Khartoum, ya aika masa da kudin jirgi shi da dan rakiyarsa mutum daya suka zo.
madina da yayanta gami da mijinta da surukanta da 'yayanta suma ba a barsu a bayaba dasu aka yi komai a wajen shagalin bikin,
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
.
ADON DAWA 49
.
TRUE LIFE STORY.
.
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
tayi bajintar da babu wanda ya yi saboda dawainiyar data yi da yawa ta buga kalandu da memo da robobi da barguna bayaga abinciccika da ta dauki ma'aikata aka yita dafawa, itace mai yiwa amarya kwalliya da zabar mata kayan da ya dace ta saka, a bangarenta amarya da kawayenta suke hidiman su duniya kenan budurwar wawa wanda ya biye ta saita kaishi ta baro shi, alh Adnan ya tsaya kawai yana duban matarsa yana mamakinta domin a iya sanin da yayi mata ta tsani kaltum tun tana karama ashe a lokacin ma kishi ne sai yanzu ta saki ranta kenan, sai ta shiga kame kame tana bashi hakuri a bisa rashin mutuncinda tayi ta shuka masa a baya a rashin sani.
gaba daya liyafar bikin nan ita ta tsaya ta tsara ta yadda ya kamata, bini-bini ta dafa amarya a dauke su a hoto abu kadan saita kira sofi gefe ayi shawara kanka ce kwabo an kulla kawance ita da Madina da sumayya tukur har da musayan lambobin waya,
danta mashkur ma yazo daurin auren daga London sun sha hotuna da amarya haka alh Adnan da amarya da ango anyi hotuna ba adadi.
sati guda aka kashe ana shagalin biki daga nan sai jama a suka fara watsewa da yake kowa yasan ba anan za'a ajiye amarya ba don haka babu jere, fataken da suka yo kaura daga bur sudan suka kama hanyar garuruwansu bayan mambela ya damka musu kudin motar da zasu karasa garuruwansu, yan Niger suka kama hanya, sakkwatawa suma suka nufi Birnin Shehu, daurawa ma suka nufi Birnin Daurawa suna masu godiya da fatan zaman lafiya tsakanin ma aura ta, yan camaroun ma suka daure kayansu suka nufi gida kanwar sofi ce joda
kadai bata tafi ba saboda sunanta ya fito a yan rakiyar amarya dubai.
malam saleh kuwa shine yace zai raka yarsa da kansa babu wanda zai wakilceshi daga danginsa sai kuma salaha daga bangaren kaltum kenan duk mambela ya dau nauyinsu, yan ADON DAWA ma sun juya zuwa kasarsu sarki ne kawai zai raka jikansa Dubai,
sai kuma Madina da Abba da suka dau nauyin kudin jirginsu daman sunada niyyar zuwa su huta.
maimakon kayan daki sai alh adnan ya kunshe zunzurutun kudi har miliyan daya ya bawa kaltum yace taja jari, jirgin emirate suka hau a legos basu tsaya a ko ina ba sai filin jirgn nan mai tsananin kyauwu da tsari wato
emara airport, kaltum da mambela sunga abunda basu taba gani ba sai suka ware ido suna kallo tunda basu saba fita ba kamar su Abba da mummy salaha ba har gara kaltum ma ta taba ganin wasu abubuwa a makkah amma dai shekarun da yawa babu wanda yakai joda dashi kansa ransa ya dade sarkin ADON DAWA shima bai taba fita ba idan yayi tafiya mai nisa to Khartoum ne sai santi yake yana basu dariya suna kyakyatawa.
acikin dubai gida mambela ya kamawa kaltum haya a wani anguwa da ake kira bur Dubai, dogon gini mai hawa ashirin ne gidaje don haka a hawana ashirin gidan kaltum yake babu wahalar hawa bene saboda akwai wuta ba a daukewa, na'urane zata kai ka cikin lokaci kalilan wato lifta.
tsantsari gidan yayi kyau domin an kara kayata gidan da kaya masu kyau da tsada da kalar da ya dace, dakuna biyune gidan da falo daya dining area da kicin sai bandaki uku hardana baki a falo babu wani abu na jin dadin rayuwa na wannan zamani da mambela bai saka mata ba wannan shi ake kira aljannar duniya, abun dariya harda katon photo yayi enlargement shida kaltum a bur

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login