Showing 75001 words to 78000 words out of 144367 words
ta halakasu ta tsuda kwanon ta kora ruwan sanyi suka kara gaba.
suna shiga sakar gida suka iske damdazon matan gidan kwansu da korkotansu a tsaye suna ta ce ce kuce .
hayaniya tayi yawa har ba zaka iya tsintar kalma daya ba kamar fada akeyi ko mayarda zance ,labari ne suke yi ko kuwa jajanta wani abu sukeyi wajunansu?
Allah shi Ya barwa kanSa sani.
fargaba gami da mummunar bugawar zuciyace ta fado wa kaltum asanda taga gaba daya matan sun yiwo kanta suna fadin ,yauwa ga kaltum din ya
ADON DAWA 22
.
,yauwa ga kaltum din nan yar halak .
ta dafe kirji ta fada cikin,fargaba InnaLillahi wa'inna ilaihi Raji'un .me nayi ,lafiya?
Magajiya tafada cike tausayawa ,tace,sai kikaji abun da ya sami kalah da yar lami?
Kaltum tasake jin mummunar damuwa.tace meyasami kalah da lami?
Sai taga hawaye yana kwaranya daga idanuwan wasu daga cikin su ,saboda
tausayawa .kankace kwabo kaltum tafashe da kuka,yayinda jikinta ya dau karkarwa tana tambayarsu cikin matsananciyar damuwa mai hade da fargaba amsar da zasu bata .wai me yake faruwa ne ?
Ku fada mini.
magajiya ta sharce hawaye tace ,kalah da yarta lami ne suka yi hatsari a kwale kwale a
hanyarsu ta hayewa makkah ta barauniyar hanya jiya da tsakar dare,
kalah na asibiti rai ahannun Allah ,yayinda lami da sauran mata uku Allah Ya a
musu rasuwa kalmar innalillahi wa inna ilaihi
raji un ce ke fitowa daga harshen kaltum ,ta tsulale ta tsugunna yayinda ta hada kai da gwiwa tana rusa kuka .
magajiya tace kowa anan yasan hakkinkine yakama kalah da yarta kowa yasansu kalah suncuceki ,Allah baya Ya fe wa wani laifin
wani,sai kin yafe musu susami rahama kaltum kiyafewa lami wacce ta rigamu gidan gaskiya,kalah kuwa da bakinta take cewa anemo mata ke tanemi gafararki yanzuma daga asibiti muke bata anbaton kowa sai akiraki tanemi gafararki tasan ta cuceki mun duba duk inda zamu samoki tunda safe bamu gankiba
kaltum tafada nan da nan nayafe musu asabebe tace tashi muje asibitin taji da kunnenta ko hankalinta zai kwanta kaltum ta mike da sauri yayinda kowaccensu ta zaro gyalenta tafiya sukeyi fakam-fakam cikin sauri suna tayar da kura kai kace garken shanu aka bude aka korosu kiwo .
kowaccensu ka duba sai ka rantse daga kabari ta fito butu-butu wasu da goyo wasu da yayayyun 'yaya sunrike hannunsu mata fiye da ashirin ne suka taho duba kalah.
nan da nan ma aikatan suka taho da sauri suka tare bakin kofarda kalah ke kwance .
tambayarsu suke lafiya?
Asabe ce ta koro musu bayani ,wannan itace kaltum da kalah kecewa anemo tunda tsafe suka bar asabebe da kaltum suka shiga ragowawar aka tura keyarsu baya .akarkashin wata itaciya suka tarufi, takaici ya ishesu baza arasa tsaki da harare harareba harda yan tsirarun ashariya duk sun kutuntumawa ma'aikatan cikin harshen hausa tunda basaji ,
fargaba da kidimewane suka hadu a zuciyar kaltum dai dai lokacinda tayi ido hudu da kalah yanayin jikin kalah zai tayarwa da duk bil adama hankali musulmi harda wanda ba musulmiba saboda mugayen raunukan da ke jikinta kama daga kanta zuwa kafarta duk bandejine,
karkarwa kawai kaltum keyi yayinda taja burki tayi turus tana duban kalah.itama tana dubanta hawaye masu zafine ke kwaranya daga idanuwansu,
yayin da bakin kowaccensu ke karkarwa. kalah na kwance reran an nadeta da farin bandeji, wanda ya yi nashe-nashe da jini. kafafuwanta dukka biyun, da hannunta data dorin karaya ne. fuskarta luhu-luhu a kumbure idan ba an fada maka ita ba ce babu yadda zaka kalleta sau daya ka gane ta. da kyar kalah ta daga hannun ta fada cikin wata shamulalliyar murya marar kuzari, 'zo nan kaltum, zo wajena, kun ga yadda Allah ya yi da ni. na cuce ki, amma kaina na cuta' kaltum ta matso a hankali ta raba ta zauna a gefen gadon kalah tana mata duban tausayawa,hawayen dai bai tsagaita ba daga idanuwan kowaccensu, su ukun har da asabebe.
kalah ta kara da cewa,
'me za'a yi da halina, me za'a yi da zalunci, cin amana da damfara?
kaltum, na damfari iyayenki ,nacuce ki ,najawo kaina.shin me kudin nan dana cuce ku ya karamin yanzu?
mezamu fada wa Ubangijinmu nida lami ?
kuka me yawa ya ruftowa kalah takasa
cigaba da bayani asabebe nashafa hannunta tana bata hakuri tana cewa daina kuka kalah fuskarki duk dinkine kada ya sake kuburi yihakuri kaltum tariga tayafemuku,
kalah ta fara magana cikin nadama Allah ya yafemin ,kaltuma kiyafe min inkinje gida
kicewa alhaji adnan yayafemini domin naci amanarsa akwai wani Inuwa agent dan Daura ne wanda duk shiyakawomu nan shi alhaji adnan yaje yasamo har Daura ya tambayi inda kike inuwa agent yace ya dade baiyi wannan harkarba ta kawo mutane sudan saidai zaisa a binciko inda kike bansan inda
inuwa yasamo labarin bur sudan ba andai tabbatar masa kina cen saisuka shiga tunani yanda za ayi adaukoki da farko shida alhajinne suka shirya tahowa bur sudan dinsu taho dake sai gani kwasam nabugowa inuwa agent waya inaso yakaiwa 'yaya na wayarsa muyi magana dasu don basuda waya sai kuwa yaji dadi daganin numbata
daganan sai labari ya canja cewar intaikesu in dauko musu ke daga bur sudan in dauraki ajirgi kitafi kano nan da nan na kalallamesu da dadin baki danaji maganan kudin jirgi na
nunamusu ciwon 'ya mace na ' ya mace ne, d'a ai na kowa ne, na daukan musu alkawari zan kawo musu kaltum har gida kada ma su bata lokaci da kudin jirgi har na mutane biyu zuwa da dawowa ga wahalar zuwa bur sudan godiya iri iri da shi albarka suka dinga mini basusan abunda na kudurta azuciyata ba
mukayi lissafin kudin jirgin kasanda zai kaini bur sudan da wanda zamu dawo Khartoum ni dake da kudin abincinda za muci a hanya sannan da kudin jirgin sama nawa da naki daga Khartoum zuwa kano hatta da kudin taxi da zamu hau daga filin jirgi zuwa unguwarku saida ya lissafo ya aiko min .
Inuwa agent yasan inda suke tura kudi daga wapa zuwa nan khartum har gida suka bawa mai canjin adireshina da lambar waya ta saigashi yakawo min makuden kudi nan shaidan ya zugani naji bazan iya kashesu ta hanyarda aka umurceni ba abunda nake
nemane ido rufe shekara da shekaru muna fafutuka a sudan mun kasa hade kudi mu karasa saudiyyah .
da gudumawar shawarar 'yata lami na nade kudi na boye nayi zamana na manta da alkawarinda na dauka .yawan damuna da wayar da alhaji.adnan da inuwa agent ke yi ga wa' azi da gargadin da kawayena wadanda agabansu na karbi kudin ke yi shi yasa na canja shawara inje bur sudan in dauko kaltum insakata amota ta tafi kano ita kadai sauran kudin in rike, inasaka ranar tafiya bur sudan natsami mai tafiya Hauwa saina bata sako ta taho min dake zuwan ki khairtum naji
bazan iya cire zunzurutun wannan kudi ba in biya miki kudin motar zuwa nigeria ba don haka nacire numban wayata na yar yadda su inuwa agent ba za su sake samuna a waya ba balle su dame ni da tambaya, domin duk karairayin da nake shirga musu sun kare, ban san kuma abun da zan dinga fada musu ba.''
kalah ta fashe da kuka mai tsanani, yayin da kaltum ta ji kukan da ta ke yi ya kafe, takaici ya ishe ta, ta tsurawa kalah ido tana dubanta tana tuna irin wannan cin amana da son zuciya irin ta mutanenmu.
asabebe kuwa fadi ta ke,
''cafdijam! duniya ina zaki damu?
kalah, kin yi kuskure a rayuwarki. me kudin nan zai yi miki a rayuwa, ki ka sani idan da
kin kai musu 'yarsu su baki fiye da abun da suka turo miki tun da masu hali ne?''
kalah ta jima tana kuka kafin ta ci gaba da
magana. ta ce 'na yi niyyar yin biza ta kirki mu yanki tikiti mu hau jirgi mu shiga makkah yadda doka ta tsara sai kawayena suka bani shawarar kada in kashe kudina. ni da kawayena guda biyu da tshohuwa daya muka shirya tafiya makkah ta barauniyar hanya''
kaltum ta tambaya cike da neman karin
bayani, 'ta barauniyar hanya kamar ya ya?
kalah ta matse hawaye tace
eh ta barauniyar hanyace domin da tsakar dare ake fara tafiya alokacinda jami' an tsaro ke barci ko ince babu kowa a kogin sai ahaye saboda hatsarinda ke tattare da tafiyan da
rashin tabbas ba ama biyan me kwale kwalen harsai yasallakar da ku saboda adayan biyu kuke ko kuhaye ko akamaku, ba makkah zai tsallakar da ku bafa wasu kauyukane agefen ruwan suma en kauyen sana'ar da suleyi kenan kuna isowa cikin dare sai ku biya me kwale kwale kudinsa yacika aikinsa sukuma en kauyen sai su kwasheku cikin sanda da leke-leke sai su shigar daku cikin gidajensu cikin gidanma a cen kuryar daki karkashin gado zasu boyeku saboda jami'an tsaro na iya zuwa bincika ko akwai irinmu idan bakuyi sa a ba aka kamaku to tabbas daku da matafiya da masu gidan zaku fuskanci fushin hukuma ,
kasancewar akwai wasu daga cikin yan kauyen da suke kaiwa jami'an saro gulma idan ansami labari irin wannan sai suzo
sufara bincike gidajen daya bayan daya dan haka ake tsoron boyemu saidai wadanda suka tari aradu da ka ne basu daina ba
kaltum ta gyara zama taci gaba da kurawa kalah ido tanasonjin karshen labari .meya hada duk wannan labari da mummunan
hatsarinda suka samu harda rasa rayuka ?
takaici ya isheta da takejin hanyoyin karya doka da mutanen mu yan nigeria keyi adole sai sun shiga makkah alhali a makkah dimma a wulakance suke koda yaushe askarawa nabin su da gudu suna kamawa suna dawo dasu kasarsu suba ibadar suke samu suyi
ba sai neman kudi yaki halak yaki haram ana kyararsu ana korarsu, kaltum tafi bukatan ta dauwama a sudan da tashiga makkah saboda tasan azabarda tasha awancan karon
kalah ta katse mata tunani taci gaba da cewa kamar yadda aka mana bayanin yadda akeyi idan kukayi kwanaki kamar biyu a boye agidan kauyawan nan idan suka tabbatar yan saka ido sun daina zargin an boye mutane hankalin kowa baya kansu da tsakar dare sai su fito daku ta bayar gari sununa muku hanya ta inda zakubi ku bulla jidda sannan kubiyasu kudin aikinsu to da dabara da boye boye ga yar karan tafiya mai yawa har ku samu kushiga jidda shikenan hukuma batasan kun shigo ba daganan sai kowacce tayi ta kanta idan ajidda zaku zauna to idan mota zaku hau ku tafi makkah ko Madina to yarage naku,
asabebe tace ni abunda banganeba ku a ina
kakayi hatsari har kuka sami raunuka haka ne asudan ko a saudiyyah ?
Kalah ta girgiza kai yayinda ta zubo da hawaye daya cika mata ido tace a sudan abun ya samemu bamu kaiga hayewa ba bamu dade da fara tafiya ba a cikin kwale-kwalen mu biyar ne dukka matane sai matukin ne kadai na miji kamar yadda na fada muku da tsakar dare ake fara tafiya a lokacin da duk wata halitta ke barci a hankali yake tuka jirgin ko tari bai umurcemu muyi ba balle magana muna cikin tafiya kwasam
saiya hango haske daga nesa an haskemu da alamar babbar jirgine na ma'aikata sai mu kaji magana da lasifika ana umurtanmu
da mu tsaya a inda muke kasancewar yanada labarin irin mummunan hukunci da za ayi masa idan aka kamashi sai ya gigice ya fara azazzalarmu yana daka mana tsawa waimu fice masa daga jirgi ganin ya gigice sai muma muka fishi rudewa don haka mun manta a tsakiyar ruwa muke saisu dukansu harda lami suka daka salle cikin ruwa ba a kara ganinta ba saidai mutsu-mutsunsu tunda basu iya ruwaba suduka suka mutu nice naki fita ina ta ihu na dora hannu a kai kiran yata lami nake shiru lami bata amsa ba ta lume cikin ruwa bankara ganinta ba ashe bazan sake ganin ta ba har abada?
Su dukka ukun suka fashe da kuka a lokaci guda cikin kuka kalah taci gaba da cewa baidaina yimini tsawa infice masa daga jirgin kwale kwalensaba amma naki fita gudu yakeyi yana wuce kima musamman dayaga hasken fitilar nan ya nufo mu aguje arashin sani baisan ta inda ya nufo ba ashe wani gungumemen dutse yanufo a gaban ruwa jirginmu ya daki dutsen mu mu duka muka tarwatse mukayi sama muka fada cikin ruwa damu da jirgin namu ni kadai nayi rai gawarwaki biyar aka fitar daga cikin ruwa har da direban mu nice asume da wadannan raunukan
ina fatan nima zan mutu inje inhadu dasu lami don bani da anfanin zama aduniyannan sai kalah tarushe da kuka yayinda kaltum ta sunkuyar da idanuwanta da sauri kasa hawaye yana kwaranya saboda tausayinsu lokaci me tsawo babu wanda ya iya magana a cikinsu can kaltum ta dago da luhu-luhun
idanunta tadubi kalah tana magana cikin marainiyar murya tace kalah na yafe miki nayafewa lami Allah Ya yafe mana
gabaki dayan mu,
sai kalah ta rushe da kuka me karfi har saida
majinyatanda ke kwance asauran gadajen suka firgita yayinda ma'aikatan jinya suka yi tsawa suna cewa kalah ta rufe musu baki tana damun marasa lafiya tamkar xugata suke ai sai ta bude baki gaba daya tana rusa ihu magana take cikin harshen larabci yadda kowa zaiji tace na zalunci kaltum na zalunci
kaina akan abun duniya idan na mutu mezance wa Allah ?
ban mori kudin ba ko sisi ya watse aruwa na rasa yata lami na rasa lafiyata nibanje makka ba kuma sunana yabace a garin mu saboda inuwa agent zai fada wa dangina abun kunyarda nayi
hankalin kaltum da asabebe a tashe suka dinga rufe mata baki suna danneta don kada taci gaba da tonawa kanta asiri saboda abun ya zame mata tamkar tabin hankali daga karshe su ma su kaltum aka koresu waje yayinda aka dannawa kalah allurar barci a cikin karin ruwan da ake yimata tun tana magana har ta fara lunshe ido,
kaltum da asabebe suka fito wajen yan uwansu kallo daya suka taro su suna jero musu tambayoyi, kaltum ba ta iya magana ba
gefe dasu ta tsugunna ya yinda asabebe take kora musu bayanin abubuwan da basu sani ba muryar daya daga cikin ma'aikan jinya ce tace dasu kuje ku suyowa kalah abinci mai ruwa kamar lemo da shayi tunda aka kawo ta bataci komai ba nanfa aka hau kallo kallon aka rasa wacce zata ce wani abu
sai kowannensu tafara cewa ban fito da jaka ba a'a bubu canji da na bayar,
cikin marainiyar murya kaltum ke rokarsu tace dan Allah ku taimaka mata a suyo mata shayi tasha bakin ta ya bushe babu abinci banida kudi ni kuma,
da kyar uku daga cikin suka fitar da wahid jine dai dai salas jine kenan suka ba wa kaltum ta falfala bakin get ta siyo shayi kofi daya da gutsiren biredi ta shiga ta kai wa kalah. Ta iske ta a kwance barci na fisgarta sama-sama amma tana kokarin bude ido
kadan-kadan magana ta ke yi,amma ba a ji,tabbas ruwa ta ke cewa a bata.
kaltum ta daddage ta dago ta zauna zauna gami dayimata weji da filo a bayanta ta dan kishingide duk da karin ruwa da yake hannun ta ga karaya a daya hannun kaltum ta dinga tarfa mata ruwan shayi da cokali a bakinta duk da ta kasa tauna biredi amma ta shanye ruwan shayin tas,
a bandakin dake ciki kaltum tashiga taryo ruwan fomfo a kofi ta kawo ta dinga tarfa mata abaki sannan kalah taji dama-dama kaltum tana gyara mata kwanciyarta saikuwa
tarufe ido ta fara barci mai, nauyi kaltum ta lullube mata jiki da mayafinda ke gefemta sannan tajuya zata fita yayinda tayi arangama da ma'aikaciyar lafiya mai kula da kalah sai ta miko wa kaltum wata zungureriyan takarda ta magungunanda ake
bukatar da ruwanda za a dinga kara mata tana bukatar karin jini kije kukawo,
hankalin kaltum yatashi dataji batun kudi ko
sekon daya bata karaba tace wa matar wallahi banida kudi matar ta harareta tace daman ina kikaga kudi ?
Ki kaiwa iyayenki manya suje su sayo su kawo yanzu,
kaltum tajima a tsaye tana juya takardannan
sannan ta fara tafiya asanyaye ta isa inda har yanzu yan gidansu suke saye ta dubesu daya bayan daya ta fada cike da fargaba saboda shayin jine uku da kyar suka biya balle a ce an ambato irin wadannan makudan kudi tana ambaton musu jerin magungunan suka tabbatar kudin ne mai yawa sai ko waccensu ta fara hada yanata-yanata ma'ana kowaccensu ta zazzage zaninta ta juya ta kalli get din fita kaltum tayi narai-narai da ido kamar mai shirin yin kuka ta fada cikin damuwa ku taimakawa kalah ance bata da jini a jikinta kar ta mutu,
waye mai jini ajiki ?
ai dukkanmu nan idan aka tsaga mu baza a sami jinin kirki ba, shafa'u tafada dai-dai sanda ta fisgi hannun yayayyiyar yarta ta kara gaba ai sai duk sauran suka bi bayan shafau
magajiya ce ma dai ta dan tsaya tabawa kaltum shawara cewa ta taho suyi tafiyarsu kawai tama daina damun kanta kada ma
ta sake zuwa asibitin balle su ganta su tambayeta kudin magani idan sukaga shiru ba yan uwanta gwamnati ce zata dauki nauyinta koda kuwa anzo gida neman yan uwanta kada ta sake tace ta santa ma ko mutuwa tayi sun san yadda zasuyi su bunne ta,
kaltum ta kame a tsaye tana duban ganin
ikon Allah tana tambayar zuciyarta wai ina soyayyanda sukeyiwa kalah a da?
me dalilin rusa kukanda da su asabebe
keyi na tausayin kalah daman bana gaskiya bane ?
idan tausayin ta sukeji da gaske ai zasu siya mata magani donta warke inhar suna son ta rayu,
magajiya ta juya ta tafi da taga alamar kaltum bata da niyar binta sutafi kaltum tayi zaman ta akasa tana rike da doguwar takarda a hannu sai yanzu ta sake tuna madina wacce ta tsaya tsayindaka wajen kula da ita, da haka za a barta a yashe har sai ta zama mushe babu wacce zata taimaki wata da karfinta ba ma da kudinba?
hawaye ya kwaranyo daga idanuwan kaltum tahada kai da gwiwa tana kuka a bayyene take kiran sunan madina da mambela fadi take meyasa aka kawoni garin da wani baya
taimakon wani?
kaltum kaltum ?
muryar wata mace taji daga
wundon gadon da kalah ke kwance tayi farat ta hango ma'aikaciyar jinya a tsaye nanda nan ta mike aguje yayinda zuciyarta ta hau bugawa tana fargaban abunda zata shiga
ta iske tana karasawa kalah ta duba saitaga tana numfashi duk da idanuwanta arufe suke tayi ajiyar zuciya jin dadi tunda ba mutuwa tayiba AlhamduLillah, ma'aikaciyar jinya tadubi kaltum ta yatsune fuska tace kidubi jikin mahaifiyarki ki