Showing 33001 words to 36000 words out of 144367 words
sai na karo wata ta biyu ta xo a taimaki juna )
Har bata so masu aikinta suyi mata gayarn daki idan ba niba, bata ganin dai-dai saboda na fi su iyawa. Haka take aikawa in xo in yi mata wankin bandaki ko goge gogen kura, ko dahuwar abinci kala-kala irin na garinmu musamman dakan sakwara.
Daga in da na fara sha’awar boko sai yadda naga ana rugurguxa turanci, ana xaxxankada rubutu a gidan ni ban iya ba sosai. Kullum mummy hafsa t ace min “madina dama ace kin yi boko da kyawunki ya kara futowa, haka da kin fi xama ‘yar gayu da gogewa.” Sai na ji na fara tunanin ta ina xan fara karatun boko dan haka na sauke girman kai na xauna xaman dirshen da biro da littafina, kawata sumayya take koya min idan bata nan kaninta tukur (abba) yake koya min idan na iske mummy hafsa a gida bata je aiki ba itama sai ta koya min, kan ka ce kwabo na fara gane me nene boko, ko ina gida na abba yana shigowa ya koya min ni kuma ina nacewa ina tilawa har cikin dare. Tasi’u mijina baya hana ni duk abunda nake so shima dai bai yi boko ba amma bashi da niyyar koya kuma bai hana ni inje in koya ba. To kin ji yadda na koyi boko daga wajen makwabtana don karfin hali ma harda biology da chemistry sumayya take koya min da yake science tayi.
Ina da shekaru goma sha tara a duniya na haifi dana na fari, aka saka masa suna Abdul malik, na yaye shi kenan na haifi kaninsa Abdul hakim. ‘ya’yana biyu kenan tamkar ‘yan tagwaye kamarsu daya sak. Farare sol da ni suka yi kama basu dauko kamannin mahaifinsu ba. Sumayya kuwa karatun likita take yi a B U K yayin da kaninta abba ya kusa kammala secondary, shima dai ya dage yaketa koya min karatu, ni dole sai na koyi boko nima. Yana matukar burge su, su duka har daddy su ya fada ya sake maimatawa cewa shi kuwa in har xan dage in koyi karatu in nemo makaranta duk tsadar ta xai biya min. sumayya da abba kaninta suka shiga tunanin ta in da xan fara karatu a makaranta.”
Da muka nemi shawarar mummy hafsa wacce makaranta ya kamata in shiga , gani harda ‘ya’ya, sai t ace tunda ina da kokari har ma na fi wata wacce ta gama secondary sanin karatu, to inje in yi register a wata private school wacce ake yin lesson a duk lokacin da jarabawar WAEC ta karato wacce ake koyar da darussan da akayi a SS3, ana amsa past question papers na WAEC.daddy ya biya min nayi register WAEC sannan nake ta xuwa daukar darasi har na tsawon watanni uku kafin ranar jarabawar.
Na xana jarabawar WAEC na sami credit shida aka bani certificate da testimonial, kamar yadda na fada miki daman na sami certificate da testimonial na primary school tutuni.
Kaltum tayi dariya t ace “’rabo ne wannan, ba kiyi boko ba amma kin xama ‘yar boko dole.”
Madina t ace “sa kai ance ya fi bauta ciwo in ji masu iya Magana. Naci ne da son karatun na saka a xuciyata sai kuma kwarin gwiwa da na samu daga masu koya min, musamman abba yana mutukar karfafa min gwiwa.
Haka xa kiji yana cewa sister madina xa ki iya karatu ki dage.
To ko jikina yayi sanyi na daina koyo sai yasa in dauko littafi in ci gaba. Da yake abba yana matukar jin turanci ya taimaka min wajen gane abunda yake koya min, haka irin tsadaddiyar makarantar da suke yi mai kayu ita ta kara musu sanin abubuwa da yawa suma suka koya min, ga lesson teachers dinsu ko wane subject suna da malaminsa.
A bamgaren addini kuwa idan ban koya musu ba, su ba xasu koya min ba, islamiyyarmu daya dasu haka malamin da yake koya musu a gida nima ina shiga ya koya min , bikin saukar mu tare aka yi mana da muka sauke Qur’ani mu uku, ni sumayya da abba babu abunda suka bambata ni.
Abu kamar wasa sakamakon jarabawar WAEC dina ta fito, ina da credit shida da pass uku haka ya taimaka min na shiga school of hygine inda na karanci aikin jinya. To kinji yadda na xama ma’aikaciyar asitbiti kenan shi yasa na iya dinke miki ciwo, na iya allura da bada magunguna.
Kaltum tace “na ji duk wannan sai dai na damu in ji dalilin da yasa ki ka rabu da mijinki da ‘ya’yanki ki ka taho nan alhalin kina cikin rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali. Mijinki mai sonki, ‘ya’yanki a hannunki kina kula dasu ga makwabtanki masu son ki suna taimakonki. Ba dai mai gidanki ba ne ya rasu, ‘yan uwansa suka debe ‘ya’yanku suka kore ki?
Madina tayi murmushi sai ga hawaye yana ta sirnanowa daga idanuwanta. Hankalin kaltum ya tashi ta shiga yiwa madina tambayoyi “me yasa kike kuka?
Ma ya faru da tasi’u? ”
Madina ta rushe da kuka tana Magana cikin kuka mai tsanani t ace “kaltum, dole ne inyi kuka dole ne in ji ciwon abunda ya faru da ni har bakin cikin abun ya fito dani xuwa nan.
Kaltum ta tambaya “anty me nene ya far? ”
Madina ta sharce hawaye da gefen hijabinta t ace “na kammala school of hygien nakarbi certificate dina yayi kyau cinye dukka. Haka sumayya ta xama cikakkiyar likita ta auri abokin karatunta shima likita dan gidan shahararren masu kudi ne sunansa dr basher, gidansu na korau road. Kaninta abba kuma ya yi nisa da karatunsa na lauyer a BUK har yaje law school .
Ni kuma har na sake haihuwa na haifi ‘ya mace mai suna shahida, yarinyar nan duk ta fi mu kyau duk da itama ta yi jawur da ita mai hanci dadan karamin baki, mahaifinta ya fi sonta haka su sumayya da mahaifiyarta suke son shahida, musamman abba ko da yaushe yana yi mata siyayya ya dauketa a mota ya xaxxagaya da ita. Alhamdulilla duk da tasi’u bai yarda inyi aiki ba amma na yi karatun na ajiye kwalin shi kuma harkar kasuwancinsa ta bunkasa dan saida ya sayi gidan da muke ciki na genersl tukur, duk da yayi masa rangwame sosai amma ya biya fiye da rabin kudin gidan na xahiri, har ma ya kara da wani fili da yake bayanmu ya hade yakere mana gidnmu ba laifi dai irin na rufin asiri ga ‘yar motarmu a gareji. ‘ya’yana suna karatu a makaranta me kyau don haka hankalina a kwance in ci mai kyau ga sababbin kayan daki dana falo duk tasi’u ya canxa min, sutura sai dai in bawa talakawa jace.
Sumayya na taimaka min da kayan sawa kal-kala haka ma duk sanda na je ko ta xo tana ba ni, haka abba kaninta aminina ne sosai, duk wata damuwata ko ta yarana idan na fada masa xai yi min komai yawan kudin. da yake mahaifinsu yana wadata su da kudi mai yawa. Ni da ‘yayana shar damu, bana tunanin wani abu wanda xai batamin raina in ba tunanin dan uwana ba innamani, sai takaicin rashin sanin addinin musulunci da iyaye na suka mutu cikin rashin sani da jahilci bana marmarin daidai da rana daya in leka garinmu. Amma dangin mijina sun huce dani suna xuwa nima ina xuwa sai daga baya ne ma surukata ta rasu.
Abu na farko da tasi’u ya fara shine bayan ya wadata mu ni da ‘yayana sai ya tarki Karin aure don daman na lura da yanayin gini da yayi (MAXA……….) na xaman mata biyu ne ban yi masa Magana ba sai na xuba masa ido har sanda ya gama xagayensa ya sanar min xai kara aure. Dole ne in jiba dadi amma ban isa in nuna masa ba saboda tsoronsa da nake ji, ban isa yana fada ina fada ba sai dai nayi kukan xuci sannan nayi kukana a daki na lallashi kaina saboda ban ga inda na ragi tasi’u ba da har xai yi sha’awar kara aure, nayi addu’a Allah Yasa ya auro min ta gari wacce xamu xauna lafiya.
Allah cikin ikon Sa aka auro min kishiya mai suna sa’ada ‘yar cikin garin kano ce sai dai kash bata kaunata bata kaunar ‘ya’yana, bata so a xauna lafiya. Duk da bana kula ta muyi fada amma duk shiru na sai tayi abunda sai na yi Magana. Tasi’u har mamaki yake bani, bamu taba fada da sa’ada ba tasi’u yabi bayana koda yaushe nice marar gaskiya itace mai gaskiya kullum ina ta hakuri ko sumayya bana fadawa haka ban taba fadawa mahaifiyar sumayya ba halin da nake ciki ba sai dai sun kula ina ta rama, walwalata ta ragu kamar ina cikin damuwa, ko sun tambaye ni sai in ce babu komai.
Abu yayi taci gaba kullum wulakanci karuwa yake, tasi’u da matarsa suna yi min abunda suka ga dama bana iya ramawa harta kai ta kawo tasi’u ya fadawa sa’ada asalina da yadda muka hadu. Sai na ji yarinya kullum tana yasar min da habaici tana cewa da ba’asan asalin balbela ba da sai tace madina ne sunanta na asali kuma madina ne garinsu.
Na san madina sunana ne amma kuma madina garin ne baxan kulata ba sai taga kamar dai ita kadai take rawarta take kidanta bani da lokacinta don haka ta tare ni kiri-kiri ta goranta min cewar ni arniya ce inyamura, shegiya ce marar uba, na biyo saurayi kano na musulunta. Ko a mafarki yadda nake da tasi’u ban xaci xai kwance min xani a kasuwa ba komin dadin xama komin duk dadin xance da amaryarsa ba, amsa daya na bata shine nace “nagode Allah da har na gane na dawo hanyar gaskiya na musulunta har na xo nafi ta ilimin sanin Ubangiji ita da take takama asalinta musulma ce, n ace tayi asara tunda aka haife ta a musulma ta girma a musulma amma bata iya karatun sallah ba har yanxu, kuma kar kice nayi mata sharri da gaske nake, jahila ce bata iya ba din.”
Kaltum tayi dariya ta yi tafi hade da shewa harda buga kafa kasa tace, “kin burge ni anty, amma abun da kika fada mata yayi mata ciwo ko? ”
Madina t ace “lallai kuwa abun ya kona mata rai sosai harma ta fini damuwa, ta dauki kuka ta shiga daki ta dauko gyalenta ta fice ta tafi gidnsu kinsan me tace?
Kaltum tace “a’a”.
Madina tace, “gayyar ‘yan uwanta ta dauko min mata da maxa suka iske ni har falo suka xage ni harda yayarta daya da take kokarin dukana aka rirriketa sannan suka fita daga gidan da kyar, suna kira na da arniya.”
Madina ta fashe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kuka t ace “sa’ada ta bi ‘yan uwanta suka koma gidan su, tasi’u ya dawo daga kasuwa da rana, na kawo masa abinci ya fara ci sai ya tambaye ni ina sa’ada yaga dakinta a rufe? Na c eta tafi unguwa amma ina tunanin gidansu ta je. Nan da nan ya buga mata waya, sai ta fara fada masa cewar xamansu yakare tunda matarsa take xaginta. Kinsan fasa cin abincin nan yayi, ya mike jiki na rawa ya figi mota sai gidansu, a can ita da iyayenta suka shiryo masa karya da gaskiya, ya dauko matarsa suka shigo gida bai tambayeni me ya faru ba sai duka da saki daya yayi min.
Ya kure ni cikin dare ina kuka, yarana suna kuka, na tafi na barsu. Dana fita ban san inda xani ba don ba inda nake dashi wanda yafi makwabtan mu amma ba xan iya shiga in fada musu duk abunda ya faru ba saboda ban taba fada musu matsalata ba tsakanina da mijina sai xaman lafiya nake nuna musu. Hak basu taba sanin asalina ba duk da dai sun san daga inda na fito da yadda aka musuluntar da ni a unguwar basu san kundin tarihina ba.
Don haka sai na tafi gwammaja gidan wata aminiyata hajiya hadixa na yi mata karya n ace mijina ya tafi da yaran garinsu sai ni kadai a gida kuma gyaran bandaki ake yi min shiyasa na rufe dakina na xo inyi mata kwana biyu, tayi mamakin amma tayi murna.
Mami hafsa kuwa yarana ne suka kai mata labari suna kuka suka shaida mata an saki mamarsu, hankalinta a tashe ta aika akira tasi’u ta tambaye abunda ya hada mu. Ya xauna ya shirya mata karaye da nasa dana matarsa data shirya masa, idan ki ka ji abubuwanda yake cewa a kaina sai ki rantse ban taba yi masa abu daya na kirki ba a iya xamana dashi na shekara da shekaru. Yana gama bayanansa, mommy hafsa t ace “karya kake yiwa madina wannan halaye ba halinta ba ne kuma ko Qur’ani xan dafa baxa tayi haka ba.”
Ta bashi shawarar ya tashi ya nemo ni don idan ya rasa ni ya rasa mace ta gari har abada. Babu inda shi da ita basu jejje nema nab a, inda suke tunanin ina xuwa basu same nib a, sai gani kwatsam da yamma na dawo da kaina saboda na rasa inda xanje ma, sai na yanke shawarar in dawo gidana in ba tasi’u da matarsa hakuri in xauna da yarana. Tasi’u na gani na kafin in ce wani abu yace in shiga dakina ya mayar da ni. Ni da ‘yaya na muka yi ta murna.
Mommy hafsa ta aiko in je tana nemana na je, na iske ta a xaune a falonta sai ta fara jero min tambayoyi akan me tasi’u da matarsa suke min?
Na boye mata nace “babu komai”
Data takura da tambaya sai taga na rushe d a kuka kawai, ta girgixa kai.
Ta ce “madina ke ‘yar aljanna ce ki je ki xauna a gidanki, ki cigaba da hakuri Allah xai jagorance ki.”
Na tashi na tafi gida ba tare dana fada mata komai ba. Haka sumayya ta xo ta dinga tambaya ta abunda ke faruwa sai dai in yi kuka bana iya fada. Abba kaninta ma har falona ya shigo yayi iya kokarinsa wajen bugun cikina don ya ji halin da nake ciki a matsayinsa na lawyer ya bi duk wata hanya da dabaru na jin labari shima daya takura min sai nayi ta kuka ba shiri ya fice ya kyale ni.
Na dauki tasi’u tamkar rabin jikina na nunawa jama’a tasi’u shine rayuwata ina jin kunyar ace ya watsa min kasa a ido, kunya nake ji ace baya sona yanxu wata yake so.”
Madina ta shrce hawaye t ace “sai na shiga taka tsan-tsan don kada in batawa sa’ada rai ta fadawa tasi’u shima ransa y abaci, sai na xama tamkar baiwarta a gidan komai ni nake yi mata musamman data haihu nake kula da yaron ita tana can a nade a dakin miji domin ni bani da kwanxa, akwai lokacinda tasi’u yayi wata biyar bai kirani dakinsa ba balle ya shigo dakina sa’ada ce kadai matarsa a gida. Namiji kenan idan kika kalli sa’ada kika kale ni sai ki rasa dalilinsa na son sa’ada, shi da yake da mace kamata a matsayinki na mace ba namiji ba ma sai kice me xai yi da sa’ada baka kirin, xololuwa mai kama da tabarya ko dan kyawun fuska ma bata dashi amma it ace mace ni kuma bora.”
Madina ta rushe da kuka yayin da kaltum take tayata. Madina ta daga idanuwanta ta dubi sama.
Ta ce “Allah kana ganin halindana shiga ada da wanda na ke ciki yanxu. Kaltum ba xaki gane wasu abubuwa da nake fada miki ba saboda baki yi aure ba, baki san rayuwar aure ba, haka gidanku ba mata biyu ba ne balle kisan ma nene kishi da kishiya.”
Ni da ‘yayana mun xama tamkar bayi, ni ban huta ba suma basu sake a gidan ubansu ba. Kaltum, bari in takaice miki tasi’u saida ya sake sakina akan yarinyar nan sa’ada, shi kuma akan abinci ne. ranar girkinta ya bata naira dubu biyu tayi cefanen rana dana dare. Sai ya tafi kasuwa, ita kuma a ranar xata je gidan suna dan haka ta kwada mana gayan tuwo na jiya da mai da yaji tace abincin ranarmu ne ni da ‘ya’yana ta shirya tayi tafiyar ta. Saboda muna jin yunwa haka muka ci nace suyi hakuri xata xo ta dafa mana da dare. Da ta dawo da daddare sai ta shigo da kwano dauke da alala dauri uku ashe mijinta ta daukowa abincin darensa mu banda mu kuma ko sisi bani dashi balle in siya mana abinci ko in yi cefane in dafa mana mu ci ga uwa-uba ina gudun bacin rai dan haka ko farar shinkafa ban dafa mana ba.
Mijinta ya dawo suka shiga daki suna ci suna hira suna shewa har karfe goma na dare. Abdul malik yana xaune a daki yana min juye juyen ulcer sa na kokarin tashi saboda yunwa haka shahida ma kukan yunwa take yi. Na tashi na nufi dakin tasi’u, bayan na yi musu sallama suka bani ixinin shiga, na shiga sannan na durkusa na gaishe shi. Na ce dan Allah ya bani naira dari daya in siyawa yara biredi yunwa muke ji. Ya tambaye ni cike da mamaki y ace ba’ayi abinci bane?
Na ce ai gidan suna sa’ada ta je shiyasa bata yi girki ba.
Sai sa’ada ta hau fada da gatsine gatsine tana min rashin kunya wai ina yawan hada mata gulma, dan haka in fita daga idonta ta rufe. Ya ce in tashi inje dakina yana xuwa yanxu. Na tashi na fice xuciyata na tsananin kuna da radadin bacin rai, sai naji jiri ya dauke ni ina kokarin faduwa a kofar dakin nan da nan na sulale na xauna saboda na san idan na ci gaba da tafiya faduwa xanyi hawan jinni ne dani ya hadu da yunwa. Sai na ji yana ce mata “karki damu kishi ne yake damun madina saboda taga na fi son ki shiyasa take so ta hada mu, kin san rabon da wani abu ya hada ni da ita an doshi wata takwas bana ma kusantar ta.” Sa’ada tayi shewa ta tafa hannu tayi girgixa taji dadi.
Sai na tuno soyayyarmu da tasi’u a da, na tuna yadda na xama haka a wajensa sai na rushe da kuka in tashi ma tsaye ya gagare ni saboda jikina