Showing 30001 words to 33000 words out of 144367 words
a nan cikin onisha nake. Kamar yadda kika sani da xarar ance babu uwa, babu uba, a duniya to fa sai a hankali saboda gata yakare sai wanda ya duba Allah xai dube ka.
A lokacin shekaruna takwas a duniya don haka na fara kiran kaina marainiya domin na fara dandana maraici. Ba’a taba saka ni makarantaba sai talla da noma koda yaushe, nice rainon ‘yayan ‘yan uwa, nice shara da wanke wanken a gidajen ‘yan uwa ba a gida daya ba. Baya ga duka, xagi da cin mutunci harda kala sata, yau ace an ganni a gona na saci rogo gobe ace na balli ayaba a gonar wani ko kuma ace na bude tukunya na saci naman miya. Kaltum ina bayan gari ina kuka ni kadai gashi yayana innamani yayi min nisa baya onisha ya ci sa’a shi an saka shi a makaranta. In takaice miki dai da wuya tayi wuya babu wanda bai san labarin wahalar da nake sha ba a garin, ina tafe jama’a na nuna ni suna tausaya min. kayan jikina a yayyage, tallar safe daban in koma in dauko abincin rana, idan na sayar na koma na daukko na dare.
A kasuwa nake sayar da abinci anan ne na hadu da hausawa masu sayar da gyada, man kulikuli, ridi, barkono da dai sauransu. Ta in da jini na ya fara haduwa da hausawa shine suna da tausayi, suna da kirki, suna da kyauta, ga yawan fara’a. muna xama tare muna sabawa sai na fara fahimtar ashe wadannan wadannan mutane wato hausawa suna da wani addini da ake kira musulunci, suna bautawa Ubangijinsu shine Allah madaukakin Sarki. Hakika idan musulmi y ace Allah xan yi abu kaxa, tabbas suna tsoron Allah xa su yi din. Wannan al’amarin nasu yana burge ni kuma yana matukar ba ni sha’awa, na ji ina son in yi huddar cinikayya dasu. suna siyan kayana su bani kudina basa hanawa sabanin inyamurai ‘yan uwana saisu cinye abincina su hana ni kudin, su ce in je in yi abunda xanyi, basa tsoron Allah. A wanan dalilin ne yasa na fi so in sayarwa da hausawa abincina.
A haka muka saba da wani yaro saurayin mai suna Tasi’u, dan asalin wani kauye ne da ake kira gurjiya, a hanyar wudil akwai wani kauye da ake kira kanyar babba, daga nan ake daukar hanya sai ayi ta shiga kusurwa-kusurwa babu kwalta, sai rigagen Fulani da kauyukan hausawa iri iri har a isa garin gurjiya.”
Kaltum t ace “yanxu daga surkukin kauyen na su tasi’u suke fitowa su tafi har onisha neman kudi? ”
madina t ace “dabi’ar ‘yan garin ne duka shekara bayan amfanin gona yayi, anyi roron gyada da wake saisu hada buhuhunan amfanin gonarsu maxansu da matansu su hau mota su je garinmu onisha. Matan suna gida suna gyara gyada suna yin man kuli da karago ko soyayyar gayada, maxan suna sayarwa a kasuwa.”
Kaltum t ace “har gidaje gare su a garinku kenan? ”
madina ta e “ba wasu gidajen kirki ba ne, tamfol ne suke bugawa a bayan gari, ko suyi gidajen katako ko kuma su sami dakuna na kasa su kama haya. Suna xama kamar watanni hudu ko uku sannan su hada kudinsu su sari manja, kwakwa, garin kwaki, su juya garin su sai wata shekarar sannan su dawo.
Kaltum ta gyada kai tace “Allah mai hada mutum da mutum, idan ba ikon Allah ba ta ina, ta yaya mutumin da yake hanyar wudil ya hadu da wacce take onisha. Yaya kuka kare da mutumin da kika ce sunansa tasi’u dan garin gurjiya? ”
Madina tayi murmushi t ace “duk shekara muke haduwa da tasi’u, da yake bashi da mata a wajena yake siyan abincin safe, rana da na dare ya siya ya bani kudina cas har ma ya kara min, y ace na rike canjin komai yawan sa.
.
ADON DAWA 11
.
TRUE LIFE STORY
.
Don haka da xarar naga baki ‘yan garinsu sun fara xuwa sai nayi ta tambayarsu “ina tasi’u?
ba xai xo ba ne?
yau she xe xo?
Me yasa bai xo bad a wuri? ”
haka kullum nake tambayar abokansa har sai ya xo hankalina yake kwantawa. Duk da baya jin turanci sosai, amma duk da haka yafi sauran kokarin harhadawa in fahimce shi ya fahimce ni don nima babu hausa a lokacin.
A lokacin da muka tabbatar wannan shakuwar tamu soyayya ce, sai a sannan na cika shekara goma sha hudu. Na ji ina sonsa saboda yana tausayina ya fahimci ina shan wahala a gidanmu, yana lallashina idan ina kuka haka yake cika min kudi idan cinikina bai cika ba ina tsoro xa’a dake ni a gida. Haka yake kawo min atamfofi da soyayyiyar aya da gyada duk sanda xai xo daga garinsu. Nima idan xai tafi sai in je gona in tsunko masa kwakwa, abarba, ayaba da gwanda. Da kuka muke rabuwa duk sanda xai koma garinsu sai inji duk bana jin dadin kasuwar idan baya nan.
Bana sha’awar samarin garinmu saboda ba abunda suka sani sai yiwa budurwa ciki, idan taki amincewa sai suyi mata fyade (wa iyyaxu billa Allah Ya tsare mu da xuri’armu baki daya.) da karfin tsiya ba’a kuma daukar matakin kirki idan haka ta faru dan haka nayi ta taka tsan-tsan da duk namijin da yake kusanta ta. Da yawa samarin garinmu sun sha kawo min hari, Allah Yak e kiyaye ni.
Wata rana na je na iske tasi’u a dakinsa bashi da lafiya yana cikin bargo yana makyarkyata saboda tsananin xaxxabi mai xafi. Na xuba masa abinci nace ya tashi yaci, yace ba xai ci ba idan yaci xai yi amai. Na kasa tafiya talla in bar shi cikin wannan hali sai na xauna a gefen katifarsa ina shafa kafarsa. Sai naga ya xabura ya janye kafarsa. Ya ce da ni baya so ina taba shi saboda haramun ne mace ta taba namiji idan ba mijin taba ne, haka bai ma kamata in shigo dakinsa ba in xauna saboda gudun shaidan xai iya shiga tsakaninmu, a takaice dai yana nufin in tashi in fita.
(ALLAH SARKI, JAMA’A SE A KIYAYE DOMIN KUWA WANNAN ITACE ADDININ MU KUMA AL’ADARMU, DA YAWA MUTANE YANXU SUN XAMA DA SHI GANIN DAMA, DOMIN GUJEWA SHARRIN SHAIDAN, JAMA’A SE A KIYAYE, A DAU DARASI, ALLAH YA SA MU DACE, KUMA MU PI KARPIN XUCIYOYIN MU.
Aamiin )
Raina yabaci na dauki kayan talla na fice a tunanina yayi min wulakanci baya sona. Ina shiga wani gida talla sai mutumin gidan ya rufe kofa da ni yana neman yi min fyade, da kyar na kwaci kai na bayan da muka yiwa juna jini da majina. Ya fasfaska min mari, ni kuma na rurrusa masa daron abincin tallar, na juye masa abincin aka duk abincin ya xuxxube, da kyar na kwaci kaina na fito yaro-yaro kayana a yayyage. Sai a lokacin na sake tabbatarwa da lallai tasi’u mai so na ne kuma baya niyyar cutar da ni, kuma al’adarsu da addininsu yana da kyau yafi namu.
Kai tsaye dakin tasi’u na nufa ina rusa kuka, wannan karon sai na ki shiga cikin dakin sai dai na kwankwasa masa kofa, ya fito da kyar yayin da hankalinsa ya tashi daya ganni a cikin wannan halin. Yana tambayata cikin gigita dakyar na lafa da kukan na fada masa abunda ya faru, na shaida masa cewar kwanukan abincin yana can a gidan mutumin kuma abincina ya xube dukka ko cinikin sisi ban yi ba ina tsoran in je gida dan xa’a kashe ni idan ban kai kudi ba. Haka tasi’u ya harhada duk ‘yan kudaden sa ya bani ya saka ni a gaba na nuna masa gidan, muka iske gidan a rufe amma an watso min kwanukan waje. Tasi’u ya harhada ya bani na tafi gida, duk da haka saida na ci duka akan kayana da aka gani a yayyage.
Tun daga wannan lokacin na ji na kara son tasi’u kuma shi ya dace da rayuwata. Na shiga tunanin ta yadda xamu fara domin na san ko a mafarki a gidanmu da wajen bautarmu ba xa su bari na auri tasi’u ba ko xan mutu. Shima ya nuna min yana sona amma fa ko xan mutu ba xa’a bar shi a gidansu ya su ya aure niba, a lokacin ma ya fada min cewar har an bashi wacce xai aura shi ne baya so yake jan abun da tuni ma anyi bikin.
Tasi’u ne ya koya min saka suturar da xata rufe min ilahirin jikina, na daina yawo da shimi dadan siket iya gwiwa, shi ya nuna min kamun kai da kintsa jiki idan ina gaban maxa saboda gudun sha’awa, muna son juna sosai har takai ta kawo sanda ya xo xai tafi garinsu na rike shi ina ihu nace sai dai mu tafi tare ba xai tafi ya barni ba, dole ya fasa tafiyarsa a ranar abokan tafiyar sa suka tafi suka barshi ya xauna yayi ta lallashi na dakyar na yarda na koma gidanmu a bisa sharadin gobe xai jira ni mu tafi tare.
Cikin dare na sulalo na fito daure da kayana a dan buhu na xo na buga masa kofar dakinsa nace ya fito mu gudu saboda gobe da safe xa’a a tashi a fadawa ‘yan uwana su xo su kama ni. Da farko ya nuna ba xai tafi da niba, kukana da kalaman da nake fada masa cewar ina so in musulunta in xauna da musulmai In baxe aure niba na yarda, na shaida masa na gaji da wahalar aiki, talla, da duka kullum, in har ba xai tafi da niba to ya sani kafin ya dawo wata shekara xan kashe kaina. Dole ya ji babu yadda xai yi sai ya tafi da ni din. A daren muka shiga tasha muka kwana, da asuba muka shiga doguwar mota xuwa kano. Babu wanda ya ganni har muka bar garinmu, daga kano muka hau motar wudil kafin a isa wudil muka sauka kanya babba muka hau Babura suka shiga damu garin gurjiya, garinsu kenan. Bamu isa gurjiya ba sai kimanin karfe goma sha daya na dare a lokacin kowa yayi barci, sai ya kaini gidan wani abokinsa mai suna Dauda da matarsa ramma itama mun saba da ita a garinmu, suma basu dade da dawowa ba daga onisha. A nan na kwana shi kuma ya tafi gidansu har gari yawaye”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya ta gyara xama t ace “yaki na gaba ahse, yaya kika kasance a garin gurjiya da dangin tasi’u musamman ga wacce aka bashi ya aura ya bujire ya kawo ki, ke ba bahaushiya ba, ba muslma ba?
Kuma can gidanku yaya xasu ji idan suka ji an ce kin gudu? ”
Madina ta digo da kwallar data cika mata ido ta yi murmushin karfin hali tace, “idan ki ka ce yaki daya kenan. Yake-yake xa kice. An tafka yaki badan kadan ba tsakanin tasi’u da ‘yan uwansa harta kai ta kawo dole ya dauke ni muka gudu kano saboda sun ki su tsaya su fahimce shi. Ba su ma saurari abunda yake fada musu ba, yana kokarin shaida musu ba aurena xai yi ba. Ya kawo ni ne dan a musuluntar da ni in xauna a cikin musulmai dan ni yanxu kafura ce. Sai gudu da tsallake Katanga ake yi a garin duk gidan daya shiga da ni wai ga arniya, ko giftawa nayi ta gefen randa sai an fasa randar ko an kwalfe ruwan an xubar. Kiyayya iri-iri har naji jikina yayi sanyi, dan ban dauka haka wasu musulmai suke ba. A tunanina duk musulmai masu kirki ne da son jama’a, sai naga suna kora ta suna guduna har nace masa ya mayar da ni garinmua na fasa xama da musulmai. Tasi’u yaki yace in dauko kayana mu gudu cikin garin kano, haka kuwa aka yi ya kawo ni kano unguwar yan kaba wajen limamin unguwar. A nan aka musuluntar da ni kuma a lokacin tasi’u ya biya kudin sadakina aka daura mana aure a take
A lokacin ‘yan uwa musulmai suka dinga tallafa mana, masu bamu sababbin suture kala-kala. Aka bamu kudi masu yawa sannan wani attajiri a unguwar mai suna general tukur ya bamu aron wani dan karamin gida a jikin gidansa, gidan mai kyau kuwa daki biyu, sai kicin da bandaki ga tsakar gida a sumulce da sumunti. Matan unguwar suka hada kudi suka dinka min hijabai aka ce in dinga xuwa makarantar islamiyya a unguwar. Ni da mijina muka sayi katifa, labulaye da kayan kicin muka xauna, xaman aure cikin farin ciki. Turanci ya fara ratsa bakin tasi’u yayin da ni kuma hausa ta fara kama bakina don haka muka dinga fahimtar juna.
Tasi’u yana jin dadin xama da ni saboda duk sanda matar bahaushe ta hadu da matar kabila tabbas kabilar nan xata kwacewa matar bahaushe miji badan komai ba saidan mu mun saba da aikin karfi ba aikin gida ba ma kawai. Kinga daga inda aka kira sallar asuba nagama barci sai wani daren kuma. Ni ce shara, wanke-wanke, wankin bandaki, wankin kayana, wankin kayansa, gugar kayansa dama sauransu. Ladabi da biyayya kuwa ba iyaka domin ba ma mikawa miji abu a tsaye sai mun durkusa, idan ya ajiye min tsinke yace, kar in tsallake bana tsallakawa, ban taba yi masa musu ba balle mu yi fada duk abunda yace min ko bana so haka xan yi. Ina jin dadin xamana da tasi’u saboda bana aikin wahala irin na da wanda nake yi a garinmu. Tsakanina da makwabtana sai gaisuwa da hirar mutumci, haka na yi kawaye da dama a makarantar islamiyya. Kwakwalwata kuwa tar ta bude duk wani karatu da xa’a koyamin sai ya shige, gani da nacin koyo.
Tasi’u ma bashi da ilimin addini sosai shima makarantar maxa ya shiga da daddare suke yi a masallaci. A kasuwar bakin asibitin murtala tasi’u yake kasuwancinsa yana sayar da danyen abinci kamar shinkafa, masara, gero, citta da ma sauransu. Sai a lokacin damina yake xuwa garinsu ya noma gonar gadonsa domin babansa ya dade da rasuwa mahaifiyarsa ce kawai sai ‘yan uwa jibgi guda mata da maxa. Tun mahaifiyarsa na kin amsa gaisuwarsa har dai ta huce ta fara amsawa, ta huce amma koda wasa baya marmarin kai ni garin, nima bana marmarin xuwa garinmu. Shima tasi’u bai sake waiwayar onisha ba sai dai labari ya kai kunnen ‘yan uwana cewar ina tare da tasi’u a kano. Da sun yi shawarar su xo su tafi da ni, sai bokansu yace a kyale ni xan dawo da kaina, akwai tsibbun da xai yi xan dawo da kaina. Amma fa karya yake domin addu’ata tafi tasu karfi.
Na dade ban samu haihuwa ba don haka na dinga kokarin neman ilimi ta dukka bangarorin biyu Qur’ani da boko.”
Kaltum ta tambaya cike da mamaki tace “ta yaya kika shiga makarantar boko alhali kina matar aure kuma ko primary baki yi ba?
To, mu hadu a #LITTAFI kashi na biyu,
ADON DAWA LITTAFI NA 2 (P 12)
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina t ace “da kyau, na ji dadin tambayarki, wannan yana nuna min kina fahimtar labarin da nake fada miki. Da farko dai ban taba xuwa makaranta ba kamr yadda na fada a baya amma duk yaran gidanmu ‘yan boko ne don haka tun ina karama na koyi A B C D har xuwa xed sannan na iya 123 har xuwa dubunnai, xan iya kirgawa kuma na iya rubutawa. Sannan nasan yadda ake rubuta sunan abubuwa da yawa kamar su hen, cup, ball da dai sauransu. Dalilin da yasa ba xan wahala a boko ba saboda na iya turanci duk da turancin ba turanci ba ne sak (broken English) ne amma muna jin mai kyan din, duk abun da ka fada min da turanci xan ji kuma xan mayar. Don haka satifiket din primary na je aka yi min a dakata special primary school.
A makwabtan mu wato gidan attajirin nan daya bamu aron gida wato general tukur . akwai wata budurwa ‘yarsa mai suna sumayya tukur. Sumayya sa’ata ce shekarunmu goma sha takwas har ta gama secondary, ajinmu daya a islamiyya. General tukur mahaifin sumayya babban soja ne, mai arxiki ne, gawurtaccen dan boko ne, gidansa rayuwar turai ake yi tsantsa. Yana da ilimi matarsa hajiya hafsa cikakkiyar lauya ce har ma tana koyarwa a jami’ar bayero ta kano, don haka su sumayya da kannenta ‘yan gata ne basu san talauci ba balle wahalar rayuwa.
Sumayya tukur itace babba a gidan kuma itace kadai mace, duk kannenta maxa ne har guda hudu. Mai bin ta sunansa tukur tukur ana kiransa da abba shekarunsa goma sha uku a lokacin, kinga kenan sumayya ta girme masa da shekarunsa goma sha daya, sai Hassan da hussain ‘yan auta shekarunsu bakwai bakwai. Tabbas mun shaku da ‘yan gidan duk unguwar ana mamakin ni da mijina kadai muke wadaka a gidan, mu shiga gidan mu fita a duk lokacin da muke so, haka suma yaran suke safa da marwa a gidana koda yaushe. Duk da sojojin da suke gadinsu suna hana kowa shiga gidan amma ni basa hana ni saboda hajiya hafsa tukur ta ce kada su hana ni shiga komai dare. Maigidana ma duk sanda ya bukaci ganin general tukur kai tsaye yake shiga ayi masa iso, ya shiga ya gan shi ya taimaka masa da duk abunda yake nema.
Allah ne gatanmu, general tukur da iyalansa sune gatanmu. Barrister hafsa itace uwar dakina itace tamkar uwata a kano tunda bani da kowa a kano. Ita take ba ni shawara, ita take fada min gaskiya idan na kuskure. Abubuwa da yawa idan ta sayawa ‘yarta sumayya nima sai ta saya da ni musamman dinkunan sutura ko bata yi mana iri daya ba tana kwatantawa nima tayi min. yawanci duk abunda suka dafa xata sa masu aikinta su xuba su kawo min. nima kuma ina iya kokarina wajen xage karfina in tsaftace mata gida ko tana nan ko bata nan xan hau sama bangarenta ko bangaren mijinta in tsaftace shi tsaf,
(TAB!!! NI SADIN MAA ME TYPING NA CE “SAM, BANNA YARDA WATA TA GYARA MIN DAKIN MIJI EHE. DAN ANTY ME POSTING, KO KUWA DA KA YARDA WATA TA GYARA DAKIN KA BAYAN MATAR KA? )
( tab , ai ni Sadin Maa ko er aikin ma baxan yarda da ita ba, idan kawai naga aikin xai yi wa mata ta yawa