Showing 45001 words to 48000 words out of 144367 words
akwai kashin daya goce a hakarkarinsa sai gobe xa’ayi wannan aiki sannan xa suyi masa hoton kwakwalwa itama su duba ko ta tabu saboda raunin da yake kansa a haka suka kwantar da mu a amenity dakin mutum daya.
Mukaddam yabiya kudin daki mai tsada lafiyayya mai AC, fanka, firij da kujerun alfarma. Mukaddam ya fita ya sissiyo mana abinci da abin sha , shi ma be iya ci ba balle ni, balle kuma shi marar lafiyar wanda babu abunda yake yi sai suma an sakala masa roba a hanci ana xuko numfashi, sai Karin ruwan da ake yi masa leda leda.
Ina xaune a gabansa a kan kujera yayin da nake rike da hannunsa na gaji da kuka sai addu’a nake tofa masa Allah Ya tashi kafadarsa.
Yayinda mukaddam yake lungu yana ta sa addua’ar hankalinmu a tashe bamu Ankara ba sha biyun dare agogon dakin ya buga ya yin da daidai wannan lokaci wayata da wayar mukaddam tadau ruri. Ina duba tawa naga sunan sumayya tukur yayin da mukaddam na duba tasa lambar mami hafsa tukur ce, maman Abba . sai gaba dayan mu muka mike tsaye muka dafe kirji, muka xaxxare ido muka kalli juna. Na ce sumayya ce, yace, mami ce, sai na yi saurin na karbi wayarsa dan kar ya danna . suka yi ta ringing har suka katse yayin da na murtsika wayoyin na kashe gaba daya, duk na bi na rude, ban san me ya kamata na yi ba.
Mukaddam na kokarin nuna min bai dace na kashe wayoyin ba saisu xaci ba lafiya ba ko mun hada baki mun kashe shi musamman idan suka xo suka iske mu tare dashi a asibiti cikin wannan halin, sai na cakumi kwalar rigarsa na matse shi a jikin bango Magana nake yi cikin fushi da kururuwa ina kuka, nace kai ne duk munafukin da ka janyo mana, saboda me xa ka kaishi tasha yahau mota ya tafi garinmu baka sanar min ba, baka sanarwa iyayensa ba?
Dan haka baxa ka amsa wayarsu ba, in kuwa har Abba ya mutu ka sani gawa biyu xaka kwashe domin ni ma sai na kashe kaina.
Kaltum ta tambaya “kuma ke lokacin da gaske kike xaki kashe kan ki? Duk wanda ya kashe kansa dan wuta ne fa.”
Madina ta share hawaye ta yi dan murmushi tace “ba kashe kaina xan yi ba, bacin rai ne kawai da tsantsar jin haushin mukaddam.”
Kaltum t ace “yaya kuka kare? ” madina t ace “kinsan kasa kwacewa yayi daga shaker da na yi masa yana ta bani hakuri har saida Abba yayi Magana. Nan da nan muka dungumo da gudu wajen gadon da yake kwance muna kiran sunansa idonsa a rufe amma sunan madina ya ambata a hankali nan da nan na rike hannunsa na matso da bakina saitin kunnensa na ambaci sunansa nace “Abba, ka ganni bude idanunka ka ganni. “sai yayi ta kokarin bude idonsa amma ya kasa. Hawaye ne kawai yake tsiyayowa daga idanunsa.
Ya fara Magana cikin sanyin murya wacce take fita a hankali y ace madina, ki yafe min abubuwanda nayi miki sannan ki sani duk abunda ya same ni dominki bana nadamar son da nake miki. Burina da fatana ki yadda da gaskiyar son da nake yi miki don kina xaton yaudararki nake, ina so ki kasance akan gawata yayin da Allah Ya dauki raina tamkar yadda mace ta gari take yiwa mijinta addu’a bayan ya mutu nima ki yi min saboda na lissafa ki dan haka na ci burin na aureki Allah baisa kin fahimta ba.”
Na sulale na durkusa na dora hannuna duka biyu a ka ina rusa kuka gami da salati fadi nake Abba na amince xan aureka, ka tashi kar ka mutu ka bar ni. Ya na cikin magana sai jini ya ambulo daga baki da hancinsa, a guje na xura na kira likita. Ya na xuwa sai yace xa su yi masa wata allura kafin gobe a shigar dashi tiyata idan iyayensa sun xo. Dan mukaddam yace musu iyayensa ne xasu saka hannu, tun daga nan Abba bai sake farfadowa ba barci kawai yake bai san inda kansa yake ba.
Jikina ya dauki karkarwa har saida na bawa mukaddam tausayi ya jawo ni ya xaunar da ni akan kujera yayin daya durkusa a gabana yana xubar da hwaye yace, “sister madina, naga kin rikice kin damu da yawa, na san abunda kike tsoro kada iyayensa su xo su ji a dalilinki haka ta faru da shi kin manta da Allah ne Yake shedar bayinsa a nan duniya da gobe kiyama?
Kin manta iyayen Abba musulmai ne, dole su yadda da kaddara mai kyau da marar kyau?
In har bakya so su ji abunda ya faru na amince ba xan fada ba ki dauki jakarki ki fice daga asibitin nan, kafin gobe su xo su ganki.”
Na girgixa kai na ce “idan na gudu shine xa su fi xargina su ce da sanina hakan ta faru saboda dole sai ka fada musu a inda yayi hatsarin saboda ga motarsa nan daya fita da ita a hannunka bada ita yayi hatsarin ba kuma dole likitoci sun dauki statement din yan sanda da suka kawo shi cewar a hanyar onisha suka dauko shi. Don haka gudu ba nawa ba ne duk daran dadewa gaskiya xata fito. Mukaddam, a ganin ka yaya iyayen Abba xasu ji a ransu idan aka ce musu Abba ni yake so har ma dalilina xai rasa rana?
Me yasa ka bari Abba ya jefa kansa cikin wannan hali nima gashi nan ya jawo min? sai na rusa kuka.
Mukaddam ya gyara xama ya bani labarin yadda abun ya faru daga farko har karshe.
LABARIN ABBA.
Mukaddam yace “tun muna yara idan kika lura Abba na sonki, ba son soyayya ba, yana matuakr son ya xauna dake. Baya gajiya da sauraron labarinki haka baya gajiya da kallonki, baya gajiya da yabon kirkin ki ko a bayan idonkine. Haka kawai kike burge shi yadda ya ga kina da tsafta, kina kula da gidanki, yaranki da mai gidanki, yace baki da kwadayi dan bakya roko sai abunda aka baki ki ke karba, baya ga rikon addininki bakya wasa da sallah. Abba ya shaida min cewa ko ya girma xai yi aure sai ya duba mace me tsafta da ladabi irinki sannan xai aura.
Bayan mun girma ya shaida min yana matukar damuwa da irin wahalhalu da wulakancin da mijin ki da kishiyoyinki ke yi miki, hakan bai sa kin fice ba saboda biyayyar aure. Idan muna xaune muna hira, sai ki ji ya tambaye ni yace, “mukaddam, anya kuwa a xamanin nan xan samu mace kamr Madina? ”
sai n ace masa “rabo ne ai, kai dai kayi addu’a kawai. Abba yayi ‘yan mata da yawa amma tun kafin aje ko ina sai dangantakar ta kwabe saboda bata da hali irin na madina. Kinsan gidansu rayuwar turawa ake yi bai tashi ya ga mahaifiyar sa na yiwa mahaifinsa hidima ba komai sai kuku da masu aiki ke yi, ke kuma ya ga komai ke ki ke yiwa mijin ki hatta tsinke xaki mika sai kin taso da gudu kin durkusa har kasa sannan ki bashi haka idan ya kiraki da gudu xa ki bar abinda kike yi ki je ki durkusa. Ba ki da lokacin kowa sai kin salami mai gidanki ko kadan ba kya bata masa rai baki da kiwar aiki.
‘yan mata da dama sun so Abba sai sun fara sai ya daina yace baya son su, har Allah Ya kawo lokacin rabuwarku ki ka bashi tarihin rayuwarki, ki kayi matukar bashi tausayi musamman daya ji kince kin rasa inda xaki nufa baki da iyaye. Sai yace min yana tausayinki yana matukar son yaga ya tallafawa rayuwarki kin koma cikin farin ciki kamar kowace mace mai miji da iyaye.
Daga nan bai sake cewa komai ba sai da aka dade, sannan na lura yana cikin damuwa na, na yi juyin duniyar nan ya ki fada min abunda yake faruwa sai ranar da muka je kaxaure wajen ki kika kore mu nima ranar ya shaida min halinda yake ciki nayi ta bashi hakuri kafin mu rabu yayi min alkawari xai hakura dake amma sai ya kirani a tsakar dare yace ya kasa hakura dake gashi tunaninki ya hana shi barci. Muna ta addu’a amma abu sai karuwa yake yi.
Ya ce min ya fi so ya auri matar daya ke tausayinta dan ya riketa amana. Burinsa ya raya sunna kamar yadda Manxon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija a baxawara, ta grime shi, burinsa ya haifar miki da farin ciki, fatansa ya sami soyayyarki, ta iyayensa duk mai sauki ne yasan yadda xai bullo musu su amince kin ki sauraransa ma balle ki fahimce shi.
Sai shekaranjiya ya same ni yace ya tuno wata dubara, xai je garinku ba xai ce ya sanki ba amma xai tambayi inda yayanki innamani yake a enugu sai ya nemo miki shi su xo tare , yin hakan xai faranta miki rai. Na ce kada ya je, yace in kyale shi xai je ko da kuwa xai rasa ransa ne a hanya. Ashe ya fada da bakin mala’iku, haka ta same shi.”
Na juya na dubi Abba, na yi kuka na yi kuka, na ji dama a dawo da rayuwa baya da banyi masa abunda na yi masa ba. Mu dukka bamu runtsa ba har asuba, na yi alwala a bandakin cikin dakin nahau salloli ba adadi kafin assalatu, addu’a nake kada Allah Yasa Abba ya mutu.
Yayinda mukaddam ya tafi masallaci ashe ya dauki wayarsa, yana idar da salla sai ya kunna a inda ya hadu da sakonnin iyayensa da iyayen Abba. Hankalinsu a tashe suke tambayar ina suka shiga shi da Abba tun jiya?
Sai ya yanke shawarar ya kira mahaifiyarsa ya yi mata bayani ita kuma ta yiwa mahaifan Abba bayani. Tun da asuba, kafin gari yawaye xance ya xagaye dangi hankalin kowa ya tashi yayin da motoci na alfarma suka dinga tsayawa a gaban dakin da muke.
Muryar mukaddam na jiyo yan magiya yan bada hakuri game da dogayen bayanai cikin kuka da rawar murya a jikin wundon dakin, na meke da gudu na daga labulen wundon na leka, sai ga en gidan su Abba kakaf da danginsa da ‘yan uwan su mukaddam, yayinda baban mukaddam yaketa sharar masa mari ba adadi da kyar a ka rike shi. Aka sako mukaddam a gaba ya xo ya nuna musu daki, su ka dungumo suka nufo inda muke. Na takure a loko ina karkarwa ina kiran “laa haula wala kuwwata illa billah.”
Suna shigowa suka kalle ni a sheleke babu wanda ya amsa gaisuwata, yayinda suka nufi kan gado da sauri wajen Abba duk wanda ya leka Abba sai yayi baya ya dafe kai yana salati saboda Abba yayi kwatsa-kwatsa. Ina kuka na taso ina shirin in yi musu bayani sai kuwa sumayya tukur ta sharara min mari, sannan ta kira ni da suna karuwa, mahaifiyarsu mami hafsa ta kirani da suna maiya na cinye mata da, wai daman ashe nice na kama shi ya dinga ramewa sannan na yi asirin da sai da ya kai kansa onisha aka tsafe shi dan haka sai hukuma ce xata raba ni dasu.
Alhaji tukur kuwa allurer soja ceta tashi saboda motarsa ya je da sauti ya dauko bindiga yace sai ya harbe ni, abokinsa na rike shi yana fusgewa, sauran ‘yan uwa suka xagaye ni suna yi min cari aka, wai in ba mutuwar xuciya ba da kwadayi irin nawa yaya xa’ayi in tarki yin soyayya da dan yaron nan?
Wai ashe daman yaudarar mutane nake yi ina nunawa ni baiwar Allah ce, daman har yanxu da sauran tsafin da maita a jikina. Ba ni da bakin bayani saboda babu mai sauraro na.”
Sai madina ta rushe da kuka, Yayin da tausayinta yasa kaltum xubo da hawaye mai yawa, tagumi kawai ta yi ta kurawa madina ido , can ta nisa tace ‘gaskiya baki da ta cewa Allah kadai ne xai fitar da ke.”
Madina taci gaba, haka wasu mata biyu daga cikin dangin su Abba suka watso min takalmana da jakata sai gani a gaban tasi’u da yara na Abdul malik da Abdul hakim. Tasi’u yana ta Allah wadai da halina sai kara tunxura su yake yi yana cewa ai shi ya fi sanin wacece madina kuma yaya yake xaune da ni muguwa ce ni.
Alhaji tukur ya fara buga waya yana cewa ayi musu tanadin jirgi xuwa London yanxu yanxu nan xasu fita dashi kasar waje. Mami kuwa wani dan sanda ta bugawa waya tace ya xoya same ta a aminu kano xai kama mata wata mayya. Ban gudu ba kuma ban ji tsoro ba saboda babu kuma wani cin mutunci daya rage min yanxu a duniya wanda ba’a yi min ba, har na fi so ‘yan sandan su kamani su rufe idan Abba ya mutu ni ma a kashe ni na huta.
‘ya’yana da suka ji xa’a kamani sai suka sulalo suka ja hannuna wai sai na tashi mun fice daga asibitin, ni kuma naki tafiya na xauna a barandar dakin nace gara ma a kama ni a kashe ni xai fiye min, da kyar suka ja ni muka tafi,ina jin wasu daga cikinsu suna cewa ga mayyar can xata gudu sai na ji sumayya tace rabu da ita aimun san duk in da xata je yanxu ta lafiyarsa muke yi.
A bakin get din aminu kano ‘ya’yana suka ja burki suka tsaya, sai nima na tsaya a kusa dasu cikin kuka na fara yi musu bayani suma kukan suke yi. Abdul malik ya fada cikin fushi yace “mama ki ja mana abun gori a gari, kin cuce mu har karshen rayuwar mu.” Ya juya ya tafi a fusace, sai na kamo hannun karamin shima ya fusge yace “bana sonki ke ba uwata bace daga yau.” Sai na saki baki ina kallonsu suka tafi suka bar ni a tsaye. Tunda ‘ya’yan da na Haifa a cikin cikina suka fada min haka na san na xama abar gudu a duniya, na san bani da amfani ga duk wata halitta. Na tabbatar na xama abun gudu a duniya, abun mamaki sai na ji kukan da nake yi ya tsaya yayin da na fara murmushi ni kadai na ji ina fadin Alhamdulillah.”
Madina ta fashe da kuka mai tsanani.
Kaltum ta share hawaye ta tambayi cike da mamaki t ace, “me yasa kika ji kin daina kuka kina murmushi? ”
Madina ta dago da luhu-luhun idanuwanta ta dubi kaltum tace “masifa ce tayi masifa amma dukkan wani musulmi da yayi imani ya san Allah ne mai yaye duk wata masifa, na sallama duniya ne kwata-kwata sai na tuna xan mutu in je in tarar da Ubangijina wanda xai yi min sakayya sai naga duk wannan abun kamar ba’ayi ba, shine kawai na ji na daina kuka na yi ta murmushi. Menene dadin duniyar ne?
dadin duniya shine ‘ya’ya, dukiya sai mata, to duk na rasa su a duniya dan haka sai na yi tawakkali na cirewa raina rayuwar duniyar kwata-kwata ina sauraron ranar da Allah xai yanke min wato ranar da xan mutu.
Ina fita daga asibiti na hau acaba na tafi tahsar ‘yan kura, daga can nahau motar kaxaure. Ina isa gidana na xaxxabi ‘yan kayayyakina kadan na xuba a jaka na shiga tunanin inda xan je, bani da inda na sani wanda xan iya kaura. Daga karshe na yanke shawarar nima in tafi enugu in nemo yayana innamani in har yana raye in xauna tare dashi don shi kadai ya rage min. na shiga sake-saken ta inda xan fara nemo su sai nace a raina idan naje enugu na tambayi sunan kawuna exe wanda yake rike shi idan kuwa ya mutu nasan shima innamani watakila a san shi idan yayi kudi tunda yayi karatu, sai dai kash bani da kudin motar tafiya.
Sai na tashi na shiga gidan makwabciyata mai suna sha’atu itama ma nurse ce, baxawara kamar ni. Na iske tayi bakuwa daga Daura suna xaune suna hira. Ta na ganina tace, ina na je tun jiya ake ta nima na ba a ganki ba, kuma me ya same ki kika rame sannan idanuwan ki suka kumbure?
Se nace mata xaxxabi na yi da ciwo ido kuma na je kano tun jiya.
Nan dai muka xauna mu uku suna hirarsu ina sauraran su hankalina baya wajen su, ina tunanin halinda Abba yake ciki.can se mariya kawar shafa’atu ta dauko hirar xuwa makka ta mota xasu bi ta sudan wani satin. Sai kuwa nayi carafna tambaye ta na ce, nawa ne kudin?
Kuma ina ake biyan kudin?
Ta yi min bayani dalla dalla, sai na ji gara kawai in tafi kasar da ba’a sanni ba. Shafa’atu na yi min tsiya tana cewa wai me yasa na ke tambaya ni daba xuwa xan yi ba?
Na ce wallahi da ina da kudi da nima xuwa xan yi.”
Sai mariya ta dubi hannuna tace “yaya xaki ce baki da kudi kuma kina sanye da tafka-tafkan awarwarayen gwal har guda biyu a hannunki ga sarka da ‘yan kunne da xobuna ai ya ishe ki kudin motar har ma yayi saura.”
Sai a lokacin na tuna ashe ina da kadarar gwal, ai nan da nan jikina ya dau rawa nace “wallahi idan mariya xata tafi daura tare xamu tafi”
Mariya tace “ai ni a yanxu xan koma ba xan kwana ba.”
Shafa’atu sai ta fara tuntsirewa da dariya a xaton ta wasa nake yi. Ta ce ta yaya xan bar aikina, da mutunci na, da kuruciyata, ga yarana amma in tafi saudiyya yawon wanke-wanke da shara? ”
Ai sai suka ga na shiga gidana na dauko jakar kayana na rufo gidan na shigo na tsaya akansu na cewa mariya ta taso mu tafi daura, abu kamar wasa sha’atu taga na rikewa mariya hannu muna ta sauri mun bar ta a baya mun nufi bakin titi, ta gaji da bin mu ta juya gida. Tace min “in kin je ma xaki dawo nasan karya kike yi ba wata makka da xaki je.”
Ai kuwa har ya shafa’atu bata ga dawowata ba kuma nasan sun hadu da mariya ta fada mata cewar na tafi. Na bawa mariya sakon mukullin gidana ta bawa shafa’atu ta budeta dibi sauran kayana ta rabar sadaka, ta fada a wajen aikina na daina aiki, a cire ni