Showing 39001 words to 42000 words out of 144367 words

Chapter 14 - ADON DAWA

Unknown   

30 Oct 2024

5091

da farar shirt a ciki mai dogon hannu, wuyansa makale da nektie, sai wani bakin takalmi kafa ciki sai sheki ya keyi. Abba ya yi kiba, ya murmure yayin da kalar fatarsa mai hasken duhu (chocolate colour) ta sake haskakawa, dogon hancinsa da habarsa wato (quarter million) sai abun salla baki a goshinsa ya dinga walkiya babu musu kana ganinsa ko ba’a fada maka ba kaga cikakken lauyer ko likita.
Na dube shi tsab sai na kwashe da dariya nace “barrister Abba, nutsuwa ceta xo maka ne, saboda an girma aka daina Magana sai sunkuyar da kai kasa?
Ni yayarka ce fa na san tsarkin kashinka, ni kuma xaka jawa aji?
Wuce cikin office ka taya ni aiki, idan na gama sai mu je gidana ka ci wani abu.”
Na wuce gaba Abba yana biye da ni har cikin office dinmu. Mu biyu ne a offishin kowacce da kujerarta sai na ci sa’a a ranar dayar bata xo aiki ba sai ni kadai. Na jawo masa daya kujerar kusa da ni nace ya xauna, ya xauna a hankali. Idan Abba ya dube ni sau daya sai ya sunkuyar da kai kasa da sauri wanda ada baya yi min haka. Ya gaishe ni cikin siririyar murya mai tafe da tsantsar ladabi da biyayya. Na amsa masa a sanyaye, sai na gyara xama a hankali ina fuskantarsa na dube shi na tambaya cikin fargaba. Na ce “Abba lafiya?
Waye bashi da lafiya ko kuma waye ya rasu, ‘yayana ne ko? ”
ya girgixa kai yace “babu wanda ya rasu kowa lafiyarsa kalau.” Na xungure shi na yi dariyar farin ciki nace “shegantakar banxa, wai meye haka ko yunwa kake ji in je in sayo maka abinci? ”
ya sake girgixa kai a sanyaye alama baya ci.
Na ce “to yanxu xaka warware dole idan na saka ka aiki, karbi biron nan ka fara shigar min da sunayen nan cikin file din nan.” Abun mamaki sai ya karbi biron hannunsa ya hau karkarwa ya kasa rubutun, ina daga nesa na jiyo bugun xuciyar sa ke yi saboda tashin hankalin da yake ciki. Na mike tsaye da sauri na fashe da kuka na tambaye shi cikin kakkausar murya Abba, ka fada min abunda yake faruwa kafin xuciyata ta buga, kasan ina da ciwon xuciya da hawan jini idan ba so kake na mutu ba, ka fada min abunda yake faruwa. Ni musulma ce Abba na san kaddar na yarda da ita kuma ‘ya’yana ne suka mutu ko?
Ko kuwa mami ce ko daddy? ”
Shima sai ya fara hawaye yace wallahi babu wanda ya rasu, xauna in fada miki abunda yake tafe da ni.”
Na xauna da sauri jikina na rawa na xura masa ido hawayena yaki ya tsaya, amma sai naga yahau kame kame, yayin da yana Magana numfashinsa ya na kokarin tafiya gaba daya saboda fargaba. Bana jin abunda yake fadi, sai na tabbatar Abba bashi da lafiya yau har maganarsa na hardewa baya ga bugun da kirjinsa ke yi tamkar xuciyar sa xata fito sarari in ganta. Na dora hannuna a kirjinsa na dafe yayin dana dafa kansa na fara tambayarsa ina ne yake masa ciwo?
Sai na ji ya ja dogon numfashi yayi ajiyar xuciya da karfi tamkar ransa xai fice. Na figa da gudu xanje in kira likita, sai naji ya jawo hannuna ya dakatar da ni yace “lafiyata kalau sister madina, dawo ki xauna xa muyi wata magan.”
Na dauka abin gwada jini na auna dantsensa, hakika jininsa yahau kadan. Na ce “Abba me yake damunka kai kuwa a duniya da har ka hadu da hawan jin kana karamin ka?
Abba me kake nema ka rasa a duniya daya wanda ya dameka a xuciyar ka?
Kada ka kashe kanka a banxa ka tashi iyayenka tsaye bayan iyayenka gaba daya burinsu da tanadin su akan ka, ka gama karatunaka kai na miji ne babban namiji, ka dube ni mana ka dubi irin matsananciyar rayuwar da nake ciki amma na yi hakuri da tawakkali.”
Sai ya sirnano da hawaye yace “ai kuwa sun kusa su rasa ni, shine ma abunda na xo in bayyana miki. Sister madina, ajalina ya xo tabbas na kusa mutuwa.”
Sai na fashe da kuka na dauki dogon salati, shima kukan yake. Na ce “Abba me nene matasalarka inyi maka maganinta in har xan iya? ”
Ya girgixa kai ya yi murmushi yace “ba xaki iya ba sister madina, abu daya nasan xaki iya taya ni dashi shine addu’a, itama sai bayan na mutu xaki tabbatar abun nan da nake fada miki bada wasa nake yi ba. Ba ni ne na jawowa kaina ciwon da gangan ba, sister madina na dade da kamuwa da ciwon nan a kalla xai yi wata shida ina fama da abu daya ni kadai amma daidai da rana daya ban taba samun sassauci ba sai dai ma karuwa da ciwon yake yi. Na rasa yadda xan yi har na tsani kaina da kaina kafin jama’ar gari su ji su tsane ni suma.” Sai kuka ya ci karfinsa, ya rushe da kuka me tsanani..
Ni kuka, shi kuka. Na tambaya cikin kuka “kai kuwa Abba wannan wane irin ciwo ne?
me yayi xafi haka ka fada mini ko mene ne irin ciwon ne, na yi alkawarin xanyi iyaka kokarina wajen taimaka maka, xan yarda da abunda xaka fada min ko da ace duniya gaba daya xasu karyata ka. Me yake damunka kanina ka fada min, Abba ciwon kanjamau ka dauko? ”
Sai yayi murmushi yace “kanin ki? Anya kuwa yau xaki bi bayan kanin nan naki kuwa, alhali ya bi baudaddiyar gada mai Burma wa?
Ke ceta farko da xaki fara karyata kaninnan naki a yau koda ace duniya gaba daya xasu gaskata shi. Ciwon kanjamau sassaukan ciwo ne tunda yana da maganin da xa’a sha a xauna lafiya a ci gaba da rayuwa cikin kwnciyar hankali.”
Sai na fara tsorota da jin irin wannan sababbin lafaxai daga bakin dan uwana Abba. Na koma jikin kujera na jingina na langwabe kai ina dubansa, na ji alamar jini na ya fara hawa.
Ya ga alamar na damu sosai sai ya shiga lallashina yana bani hakuri. Na fada cikin sanyayyar murya nace “Abba bana bukatar hakurinka, laifin me kayi min da xa ka bani hakuri?
Sai dai ina mamakin wannan al’amari naka, idan wasa ne ka daina. Wannan watan September ne ba april ba balle kayi min April full na kasa gane manufarka. Ka xo ne kawai don ka tayar min da hankali tunda baka tausayi na yanxu, bayan kasan tashin hankalin da nake ciki na rabu da mijina, na rabu da ‘’ya’’yana, ba ni da kowa sai Allah , sai kuma ku da iyayenku.” Na fashe da kuka.
Ya girgixa kai yace “ba April full ba ne ba, ba ma irin wannan wasan dake sistr madina. Ki gafarce ni akan abunda nake shirin fada miki domin nasan ba xai yi miki dadi ba ko kadan.”
Sai na ji xuciyata ta sake harbawa na shiga tunanin abunda xai fito daga bakinsa marar dadi da yadda kunnuwana xasu xukowa kwakwalwata. ‘ficik’ na jiyo wata kakkausar mummunar kalamai sun fito daga bakinsa xuwa kunnuwata yayin da xuciyata ta harxuka, kaina ya sara, kan kace kwabo gumi ya keto min, tsigar jikina ya mike tamkar an kwara min ruwan kankara a lokacin hunturu, na ji kamar na shake shi ya mutu, nima idan ya so a kashe ni, har na gwammace mutuwata da wannan mumunar kalaman daya fada min.
‘wukit’ na bude dara-daran iduwannan nawa na dube shi yayin da nasa dara-daran idanuwan suka tsugunna kasa da sauri. Na fada cikin fushi n ace “Abba ban jiba, maimaita min abunda ka fada.”
To pa, ko wace irin mummunar kalma Abba ya padi, bamu sani ba, nima se dubawa nake na kasa sanin me ya padi mata....
.
ADON DAWA 2 ( P 14)
.
TRUE LIFE STORY
.
Me Abba ya padi ne?
Tabbas kunnuwana ba suyi min karya ba Kalaman daxu ce ya maimaita min itace “SISTER MADINA ALLAH YA DORA MIN CUTAR SONKI.”
Na ce “Abba kamar so na ji ta fi fito daga bakinka ixuwa gare ni kunu wata?
Ashe xaka iya duban sumayya ka ce kana sonta so iri na soyayya? ”
Sai ya durkushe a kasa yana neman gafrata, yayinda yake nuna min kuskure yayi ba haka yake so ya fada min ba, kubcewa Kalmar tayi.
Na fuskanci xai raina min hankali don haka na mike a fusace na nuna masa hanyar waje, ma’ana ya tashi ya fita daga office dina. Simi-simi ya mike yana tuntube ya fice, na yi kukan takaici har na gaji a wannan rana. Na ji na tsani Abba har na fi tsanar kai na, ina tunanin Abba yana yi min kallon ‘yar iska don ba ni da miji kuma bani da kudi don haka xai xo ya sauke tashen balagarsa akaina. Na tunano tonan sililin da xa’ayi min idan har maganar na ta fito fili, mutuncina xai xube a idon mutane. A yi min mummunar fahimta da fassara ace yara nake bi kanana sa’annin kanne na ko ‘yayana.
Maganr nan ta dame ni sosai a raina, kwana biyu bana xuwa office ina gida ina xulumi ni kadai babu wacce xan iya fadawa. Abun mamaki sai ga Abba na turo min sakonnin soyayya ta waya, yana bayyana min mummunar halin da yake ciki a sanadiyar rashin amincewata.
Bana bashi amsa sai dai in yi kuka in goge sai takai ta kawo ya daina turo sakonnin saboda bana bashi amsa ya fara kiran lambar. Watarana da daddare misalin karfe goma da rabi ya kira ni, a wannan lokacin ne na fara amsa wayarsa don da rejecting nake yi sai a lokacin na samu daman amayar da duk abundake xuciyata. Na ja masa kunne nace Abba, saboda talauci da rashin gata da rashin asali mai kyau ne har na xama haka a wajen ka?
Ko rashin miji da rashin kudi shine kake tunanin xan xubar da girmana da mutuncina in yi lalata da kai?
Ko dan a gidanku ne ake taimakona shike nan na xama wulakantacciyar baiwa wacce xaka iya daukarta wajen biyan bukatar ka ta banxa? ”
Sai ya rafka salati yayin daya hau rantse-rantse cewar ba haka ba ne. ya shiga yi min bayani wallahi shima ya tsinci kansa ne a cikin wannan hali wanda da farko bai yarda ba sai da abu ya ci tura bayan yayi addu’a da kansa haka yasa abokansa sun taya shi akan Allah Ya yaye masa amma abu sai karuwa yake yi shine ya yanke shawarar bayyana min ko xan taya shi addu’a daman yasan ko da wasa ba xan amince ba.
Na sake jin na tsane shi fiye da da, na shaida masa koda har abada babu wani namiji a doron kasa saishi to wallahi gara in koma ga mahliccina banyi soyayya ba da na yi soyayya dashi. Na fatattake shi na ja masa kunnuwa koda wasa kada ya sake kirana ko ya turo min sako balle ya tako ya xo kaxaure. Nima har abada na daina xuwa gidansu.
Sai na ji ya fashe da kuka yana fadin inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, na murtsuke wayar gaba daya na kashe. Sai da aka yi sati guda sannan na kunna abun mamaki sai ga sakonninsa ba adadi. Hakuri dai yake bani, lallashina yake in saurare shi, wai ya kasa daina sona.
[TAB “SO” BALA’I YA ALLAH KA MANA BAIWAR WANDA XUCIYAR MU TA XABA DA DUKKAN KHAIRI, amen]
(Aamiin thumma Aamiin Sadin Maa)
Wanna al’amari na Abba ya fara tsorata ni sai na shiga tsayuwar dare ina mai neman tsari daga sharrin Abba. Hankalina ya tashi dana ji kiran wayar yayarsa sumayya ta dinga damuna da tambaya wai me yasa bana xuwa week end yanxu sunga na dade ban je ba. Na lura dai bata san abunda yake faruwa ba, haka daga mami hafsa ta kira ni sai kirjina ya harba sai idan naji ba wannan ba ne dalilin kiranta sannan in ji sanyi a xuciyata, ina ta faman yi musu karairaye cewa aiki ne ya yi min yawa amma xan xo.
Wani week end sai ga Abba har cikin gidana ya shigo ya iske ni kadai a xaune atsakar gida, ya yi baki sosai kuma ya rame. Yana shigowa sai ya tsugunna ya gaishe ni, ban amsa ba, sai ya koma gefe ya tsugunna rabe har abin tausayi.
Ban kula shi ba, na tashi na ci gaba da aikace aikace na na tsakar gida, almajiri na ya shigo na mika masa tsintsiya xai yi min shara sai Abba yayi xuruf ya dauki tsintsiyar ya fara shara. Cikin fushi na Harare shi na daka masa tsawa nace ya ajiye min tsintsiyata bana son shararsa, ya ajiye da sauri ya koma gefe ya tsugunna. Almajirin yakare shara sai na dauko kayan miya nace ya gyara min ya kai markade, sai Abba ya taso da sauri yahau tsinke hancin tattasai. Ko kallonsa ban yi ba don na fuskanci takalo abunda xan fara yi masa Magana yake yi. Ya ja alamajiri suka tafi markade a inji.
Takaici ya sana rushe da kuka ni kadai a tsakar gida, na rasa abunda yake yi min dadi suka dawo suka iske ni ina kuka Abba ya xo ya durkusa a gabana yana furta min kalaman sanyaya rai dan hankalina ya kwanta amma sai suka xame min tamkar wuta yake hura min a xuciyata. Na hasala na mike tsaye na dakawa almajiri na tsawa nace ya fice min daga gida, ya fice da gudu saboda yaga yadda raina ya baci kada in kai masa mari duk da yasan bai yi min laifin komai ba. Yayin da na juya na dubi Abba a durkushe a gabana na sake jin haushinsa da tsantsar tsanar sa suka hadu, na fashe da kuka mai tsanani.
Na ce “Abba, idan sha’awa ce ke damunka me xaka yi da tsohuwa er shekaru talatin da uku kana saurayin dan shekara ashirin da takwas?
Me xaka yi da ni wacce na tsufa na gama haife-haifena, wacce ba ni da sauran amfani na wanda har shi kansa mijina yaga bani da amfani ya sake ni, yakore ni, yace baya sona. Me xaka yi da sauran alhali ga sababbin ‘yan mata can a gari wadanda ido rufe irinka suke nema. Na yaye hijabinda yake jikina daga ni sai siket da t-shirt ko eaner wears ban sa ba. Na ce me kake sha’awa a jiki na?
Idan sha’awata ka ke yi mushiga daki in har daga yau xaka rabu da ni in huta.”
Sai Abba ya sa hannu ya rufe idanunsa da sauri yaki dubana, ya girgixa kai ya fada cikin tashin hankali da damuwa y ace “wallahi sister ba wannan ba ne manufata, ban taba sha’awarki ba kuma da xaki yarda ki aure ni ki gindaya min sharadin kada in dangwali hanuna a jikin ki, har karshen rayuwar mu to xan amince, don ni ke nake so kawai.”
Hankalina ya gushe yayin da haushi ya ishe ni, na rufe ido na na yi ta cusa masa ashar babu kakkautawa. Na ce ya tashi ya bar min gida kafin na dauko tabarya in fasa masa kai. Ya tashi sadan sadan ya kama hanyar waje saida ya kai bakin kofa, ya waiwayo ya dube ni yana hawaye yace “madina idan na mutu kece ajalina, nagode da duk abubuwanda kika yi min, ki yafe min, ki yafe min nima ba haka na soba.” Sai ya fice ya bar ni a nan a tsaye kamar gunki.
Bayan sati biyu da faruwar wannan al’amarin a bisa takurawar mami hafsa da sumayya akan na xo week end dan na dade ban je ba, dole tasa na ebo ‘yan kayana kala biyu na taho gidansu Abba. Abba na fara iskewa a falo yana xaune sai gumi yake yi shi kadai duk da AC dake kunne a falo, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar yana cikin matsananciyar rayuwa. yana ganina sai ya xabura ya gyara xama sai dai kash ya kasa hada ido da ni, ni nake yi masa duba irin na tsantsanr tsana da jan kunne ma’ana niba sa’arka bace.
Na wuce shi ba tare da na yi masa Magana ba na isa kofar dakin mahaifiyarsa na kwankwasa mata kofa gami da yi mata sallama.
Kasancewar tasan ina tafe nan ta dau muryarta t ace “madina ki shigo mana.” Na shiga muka gaisa, na tambaya duk ‘ya’yanta sai ban tambayi Abba ba, tace “mutuminki ma Abba ya dawo daga bautar kasa. Bai je ya nuna miki motarsa ba? ”
da xata lura da ni a lokacin da xata ga yadda na raxana yayin da a gigice n ace “be je ba.”
Sai ta dan gatsine fuska tace “Abban ma kamar wanda aka yiwa jifa a kudu nan daya je wajen bautar kasa, daya dawo duk ya susuce kamar bashi ba, baya son shiga mutane haka nan baya walwala da kyar sai da lallashi yake dan cin abinci. Sai daddy ya dauko mai aski da gyaran fuska, sai kaga ya tara kasunba yumu-yumu yana muxurai kamar wani bunsuru, kai gaskiya Abba ba lafiya ba. Shiga dakinsa ki ganshi ko ke da yake mutuniyarsa ce xai yi miki bayani.”
Sai na ji gabana ya yanke ya fadi tabbas al’amarin Abba ya fara bani tsoro ya wuce xolaya kamar yadda nake tunani. Kan kace kwabo hankalina ya tashi na shiga xulumi, abu daya nake tsoro kada Abba ya sake ya furta musu damuwarsa, yana furtawa kuwa mutuncin dake tsakaninmu dasu ya rabu har abada saboda ba abu ne mai yuwa ba, a dukka bangarorin biyu ko da’ace su xasu yarda niba xan yarda da yaron da na girma ba koda wanda ma ban sani ba ne, balle Abba yaron da na sani, na san yarintar sa. Baxan iya ba har abada, da in yi soyayya da Abba gara Allah ya dauki raina shi ma na fada masa haka. A haka na share xancen xuwa dakin Abba, na yi saurin xakulo hira kala-kala daga nan ma ‘yayana suka shigo muka hau murnar ganin juna daga karshe suka rako ni har wajen motoci direba ya kaini gidan sumayya.
Ina xuwa gidan sumayya muna hira sai da ta maimaita min abunda mahaifiyarta ta fada min akan Abba cewar ko an jefe shi ne a wajen bautar kasa, saboda ya susuce. Itama tana so na tambaye shi cikin dabara kasancewar sun san mutumi na ne, na amsa mata amma badan xan yi ba. A daddafe na yi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login