Showing 69001 words to 72000 words out of 144367 words

Chapter 24 - ADON DAWA

Unknown   

30 Oct 2024

5085

murna ‘yau sai kun shiga kun gaisa da sarki daman ina bashi labarin ki yana so ya ganki.”
Kamar kaltum ta nutse a cikin kasa haka taji nauyi da munyar dandaxon matan da suka dinga diddigowa daga dakunan su suna fitowa kallon amaryar mambela, sai buda ake ana yabon kyawunta da hankalinta. Don daukaka sai ga kaltum a gaban sarki tana kwasar gaisuwa. Sarki yasa hannu ya dafa kanta, ya dafa kan mambela yayi musu addu’ar fatan alkhairi sannan suka tashi suka fito yayin da aka saka bayin gidan suka rako su da kwaryar dabino daya da kwaryar nono biyu har kofar gidansu.
Mata su ka taru a tsakar gida suka kewaye su kaltum suka dinga bayar da labarin yadda suka isa gaban sarki. Yayin da sha’awa ta kama ta kama sauran mata kowacce tana cewa dama itace ta sami dan sarki mambela.
Sallamar wata bakuwa ceta katse hayaniyar da ake yi, suka waiwayo gaba daya suna duban ta.
Jama’a wace ce wannan matar? ,
daga ina ta xo? ,
wa take nema?
ADON DAWA
LITTAFI NA 2 (PART 20)
.
Matar dai bakuwar fuska ce amma kuma bahaushiya ce, hausar katsina take yi. Bayan ta karaso tsakar gidan ne aka mika mata karamar kujera ta xauna yayin da ta yi jam’I ta gaishe da kowa. Sai ta fara gabatar da sunanta da kuma garinsu. Ta ce sunanta Hauwa’u ‘yar asalin garin ‘yan tumaki ne a jahar katsina, sanna ta ambaci sunan wata mata wai shatutuwa ta xo nema. Sunan matar da ta ambata babu ita a cikin gidan nan don haka suka tabbatar mata basu san taba. Sannan ta fara dogon kwatance sai can suka gae shatutuwar da take nufi it ace matar da ta mutu a hanya a wajen haihuwa, sauran ‘yan uwanta kuwa sun haye makka. Sai suka shaida mata shatutuwa ta mutu tun a hanya a garin haihuwa.
Sai ta fashe da kuka tana cewa “kanwata ce uwa daya uba daya. Ni ce na aika mata da kudi nace ta xo mu hadu a khartum mu tara kudi sai mu wuce makka, na ji shiru shiru bata karaso ba har yanxu kuma bama waya dasu tunda kauyen namu babu waya sai na xata so take ta haihu sannan xa ta xo. Shekaranjiya na hadu da ‘yar garin mu itama ta xo kwanan nan shine nake tambayarta shatutuwa sai tace ta dade da tahowa tuntuni. Aka ce in xo nan bur sudan akwai mutanenmu wadanda basu sami tafiya ba in duba ta tabbas tana cikin sudan bata da kudin da xata haura makka.”
Ta sake rushewa da kuka mai tsanani, su kuma suna ta lallashin ta.
Can ta tsagaita da kuka sai tasa hannunta a jaka ta xaro wani hoto a ambulan. Ta ce “ga hoton wata yarinya, ‘yan uwanta sun ce inyi musu cigiyarta a nan.”
Xaibu tasa hannu ta karba ta bude ta xaro hoton, yayin da kowaccensu ta xuro kai suna kallon hoton, saisu dukka suka bude baki suna mamaki yayin da kallo ya dawo kan kaltum. Gabanta ya fara kwaranya daga idanuwanta ta fara kiran “inna lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un.”
Hauwa’u tace lafiya, me ya faru da yarinyar, kar dai itama ta mutu?
don an bani tabbacin batahaye ba tana bur sudan shine aka ce lallai lallai a kaita khartum wajen wata mata mai suna kalah itama ‘yar xangon daura ce, kalah ta dade a khartum. Kudin jirgin yarinyar da komai yana wajen ta., iyayenta sun turo da isasshen kudi suka ce lallai a kai musu ita. Shine kalah ta ji ina cewa xan taho tanan sai ta bani hoton nan in taho dashi in cigiyarta, ga sunan yarinyar nan a bayan hoton.” Madina ta karbi ta juya bayan ta karanta sai ga kaltum saleh baro baro a rubuce. Madina tace “Alhamdulillah, Allah Ya yankewa kaltum wahala don haka kaltum shiga daki kiyi marmaxa ki hado kayanki ku tafi.”
Yayin da kowa ya fara taya kaltum murna wasu kuwa suka fara koke koke dama ace suma nasu ‘yan uwan su kawo musu irin wannan agaji wajen aiko musu da kudin tafiya. Wasu kuma suka fara kukan rabuwa da kaltum saboda yarinya ce mai dadin xama.
Kaltum ta ja gefe ta cije takiyin gaba ta ki yin baya ta tsaya kawai tana karkarwar jiki yayin da ta rushe da kuka wanda saida hankalin kowa ya tashi.
Madina ma kukan take yi, ta mike da sauri ta shiga hadawa kaltum kayanta a buhunta kama daga kayanta na sakawa xuwa takalma, soson wanka, sabulu da sauransu. Ta xo ta ja hannun kaltum, sai kaltum ta makale hannu alamar ba xata tafi ba. Cikin fushi da kuka mai tsanani madina tadaka mata tsawa ta ce “ki xo ki wuce ku tafi kafin raina yabaci. Wa kika ajiye, ko wa kike dashi anan da xa kice baxa ki tafi ba?
Ban da larura ma me xai kawo ki cikin wannan rayuwar ta kangi da wulakanci a matsayinki na ‘yar boko?
Da tuni yanxu kina jami’a don haka dole ki tafi, fatana ki koma gaban iyayenki ni kuma in ji da kaina.”
Kaltum ta mika hannu ta karbi Jakarta ta wuce gaba yayin da sauran suka biyo bayanta, tafiya suke jiki sanyi kalau ana tayi mata fatan Allah kiye hanya. Mata da maxa a kofar gida suka fito suka tsaya crko carko ana kallon kaltum sai hawayen da yaketa firfitowa daga idanuwa da yawa daga cikinsu. Iya mairo da jikarta rakiya suka bata sako ta shaidawa ‘yan uwansu na xangon daura cewar suma su hado kudi su aiko musu su koma gida.
Hauwa’u ta dubi kaltum ta yi murmushi tace “banda yarinta keda xa’a kai ki gida cikin gata ina ke ina koke koke kuma?
Mu yi sauri mu tafi kada mu rasa jirgi, da magaruba yake tashi.
Kaltum ta kasa waiwayowa ta dubi jerin mutanen da suke daga mata hannu sai dai ta dora buhun kayanta aka tayi gaba. Madina da hauwa’u ne suke biye da ita a baya suka nufi khartum bahari anan ne xasu hau jirgin kasa.
Suna isa suka iske layin yakar tikiti saura mutane kadan saboda jirgin ya kusa cika. Nan da nan hauwa’u ta shiga layi ta yanko tikiti biyu ita daya, kaltum daya.
Madina ta rushe da kuka yayin da kuka ya ci karfin kaltum itama sai ta ajiye jakar kayanta a kasa ta rungume madina tana kuka. Ta ce anty, bana so in tafi ni kadai in barki a nan. Ki xo mu tafi tare xan fadawa iyayena su aiko da kudin jirginki ko mu shiga mota mu tafi kudin xai ishe mu.”
Madina ta girgixa kai ta sharce hawaye cikin kuka mai tsanani ta ke Magana t ace “ba xan je Nigeria ba kaltum, ba ni da kowa a Nigeria saboda kowa ya guje ni in yi rayuwata anan har lokacin da mutuwata xata xo ta dauke ni ki yi min fatan alkahiri kamar yadda nake yi miki ko bakya tare da ni, ki yafe min duk abunda nayi miki a rayuwa kamar yadda na yafe miki. Ina addu’a Allah Ya hadamu a gidan aljanna bayan mutuwarmu domin xai yi wuya mu sake haduwa har karshen rayuwarmu. Daga karshe ina yi miki nasiha da ki rike addininki, ki tsare kanki daga aikata xina har Allah Ya kawo miki mijin da xa ki aura na gari, kada ki manta da labarina da na baki ki koyi hakurin xaman aure da tattalin miji baya da ladabi da biyayya.
Ki yi min alkawari xa ki sakawa ‘yar ki sunana madina don karki manta da ni a rayuwa.”
Kuka mai tsanani ya ruftowa kaltum sai ta yi sauri ta duka ta dauki jakar kayanta suka nufi kofar shiga jirji saboda axalxalar da hauwa’u take yi mata wai suyi sauri su shiga jirgi su tafi kada a tafi a bar su.
Madina na tsaye tana kallon su yayin da kuka ya ci karfinta sai ta kwalla kiran sunan kaltum. Kaltum ta waiwayo da sauri sai ta tsaya cak su duka kuka suke yi. Madina tayi dan murmushi karfin hali.
Ta ce “kaltum, me xan cewa mambela? ”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai!”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai can tayi ajiyar xuciya yayin da hawaye xaxxafan hawaye ya xubo sharrrr daga idanuwanta, ta girgixa kai t ace “k ice masa na tafi gida.”
Sannan ta juya ta juya ta shiga jirgi, suka sami waje suka xauna, sun xauna ba dadewa sai aka rufe kofar jirgin aka kunna aka fara tafiya yayin da kuka marar kakkautawa ya ruftowa kaltum da madina. Sai da madina ta tabbatar jirgi ya tafi gida lokacin dare yayi. ‘yan gidan sun dade basu kwanta barci ba suna ta jajen rashin kaltum yayin da madina ta bude shafin kuka kai kace mutuwa kaltum din tayi. Taji hankalinta ya tashi ko sanda ta rabu da ‘ya’yanta bata ji irin wannan ciwon rabuwar ba kamar yadda take jin radadin xafin rabuwa da kaltum a yau. Tunda ta koma gida kalma daya ta kasa furtawa dan takaici sai aka kewaye ta ana bata baki da nasiha kala kala.
Sai washe gari su kaltum suka isa khartum da sassafe amma kaltum bata daina kuka ba. Kaltum taga kayatattun birane masu titi da gine ginen dogayen benaye. Ta shiga mamakin kyawun sudan ashesu a kauye suke ba a sudan ba, don inda suke babu ruwa, babu wuta, birni kuwa ga lantarki nan tarr, ga ruwa afanfuna bayan motoci tsala tsala da mata masu kyau a tituna suna wurwucew kamar su suka yi kansu. Duk da irin wannan kyakkawan gari da kaltum ta gani bai sata daina jin dankararriyar kunar da take ji a ranta ba. Tana tunanin madina da mambela, sai taji tafi son ta xauna dasu da ta koma gidansu. Ko sanda ta baro gida bata ji irin wannan kunar ran ba kamr yadda take ji a halin yanxu.
Sun isa wani gida kato a wata unguwa mai kyau, babban gida ne a lailaye da sumunti mai dauke da dakuna bijik da katon tsakar gida . hausa ne xalla a gidan kuma mata xalla, suna xaune a dakuna kasha kasha kowace da sana’arta wacce xata kula da kanta. A kalla a daki daya akwai mutane takwas xuwa goma da tabarmi a shinshinfide a kowace daki. Gida ne mai kyau na sumunti xalla sabanin irin nasu na bur sudan.
Tabbas kaltum taga fuskoki da yawa da ta sani sai dai ta manta a inda ta san su, suna shiga cikin gidan kafin su isa cikin dakin sai ta tambayi hauwa’u.\
Ta ce “nan gidan haya ne? ”
Hauwa’u t ace “gidan Abdul kadir, dan asalin xangon daura ne ya kauro sudan da xama fiye da shekara talatin anan yake, ya xama dan kasa. Shine yayi arxiki yamaka gidan nan ya barwa baki nan bangarensa dana iyalinsa kuma suna can baya. Kyauta kowa yake xama musamman ‘yan xangon daura sun fi xama a nan kowacce ta xo nan garin sai ta nemi nan gidan ta xauna, har ana kiran gidan da suna gidan xango.”
Sai da suka dade suna jira sannan kalah ta dawo gida, ta tare su da murna gami da yiwa hauwa’u godiya marar adadi data nemo mata kaltum. Babu tantama duk wanda ya dubi hoton kaltum yaga fusakarta kuma axahiri ya san itace, ga kamanninta nan rangadadai. Hauwa’u ta danka kaltum a hannun kalah su kayi sallama ta koma garin da take don ita ba a khartum take xaune ba.
Kaltum ta sake dukawa ta gaisheda da kalah sannan ta gaisheda ‘yarta budurwa sa’ar kaltum din ce mai suna lami. Suka amsa mata cikin sakin fuska sannan kalah ta fara yi mata bayani cewar itama ‘yar xangon daura ce babarta kawar goggo fattu ce.
Kalah ta ci gaba da shaidawa kaltum t ace “an kamo goggo fattu daga makka yanxu haka tana xaune a xangon daura saida aka kamo ta ne kwanan nan sannan iyayenki suka san bkya tare da ita a makka, dan haka hankalinsu yayi tsananin tashi suka dinga tunanin yadda xa’ayi a samo ki. Sai Allah Ya sa musa agent din da yayi muku aikin bisa yana da lambata shi suka nemo suka tambayi yadda xa’ayi a same ki. Sai yace bashi da yadda xai yi ya samu wani a bur sudan saboda babu waya kwata kwata a kauyen amma yana da lambata sai dai ni a khartum nake, don haka suka kira ni a waya. Na ce musu gaskiya bana xuwa bur sudan amma idan sun tabbata kina bur sudan to su aiko min da kudin motarki da nawa na xuwa can sannan su aiko da kudin motarki sai in saka ki a mota har kano.
Akwai wani Alh Adnan dashi muke waya shine yace gara a sako ki a jirgi, to dai yanxu sun aiko da hotonki da kudin jirgin kasa na xuwa bur sudan, da ban sami lokaci ba, shine kawata hauwa’u t ace daman tana so ta je ta je ta nemo ‘yar uwarta shine na bata kudin ta je ta taho dake don haka sai ki xauna ki saurari sanda xasu turo da kudin mota ko jirgin xuwa kano sai in je har tasha in turaki.”
Kaltum tayi shiru a lungu tana sauraron abinda kalah take fadi mata, jikinta yayi sanyi kalau ta saddakar ta fawwalawa Allah komai tana fatan Allah Ya xaba mata abinda yafi alkhairi ba abunda ranta ya fi so ba.
Al’amarin mambela kuwa sai washe gari ya samilabarin an tafi da kaltum Nigeria, har cikin dakinsa wani abokinsa ya je ya kwatsa masa wannan mummunanlabarin. Duk da tsananin xaxxabin da ciwon kan da yake yi saida ya taso da kyar ya taho gidansu kaltum, kai tsaye ya fada tsakar cikin gidan ya kuwa ci sa’a ya iske madina a xaune tayi gum tayi tagumi itama da alama takaicin rashin kaltum ya dame ta. Yana ganinta sai ya fara hawaye itama ta fara xubar da wani xaxxafan hawaye mai radadi.
Ya fada cike da fargaba yace “da gaske an tafi da kaltum Nigeria? ”
Madina ta gyada kai tace “haka ne, kaltum ta tafi Nigeria, iyayenta ne suka aiko a tafi da ita…”
Bata rufe bakinta ba sai suka gay a yi juyi ya daki katakon dakin har saida dakunan su kayi girgixa.
Ya fada cikin fushi yace “tunda kaltum ta tafi daga garin nan, ko wacce sai ta tafi babu wacce xata sake xama a kasarmu.
Nan da nan kowa yayi carko carko suna duban mambela a tsorace, hankalinsu duk ya tashi kan ka ce kobo sai jikinsu ya dau makerketa. Ya dakwa duk wanda yayi kokari matso kusa dashi xasu bashi hakuri.
BABI NA GOMA
RAYUWAR KALTUM A KHARTUM
Kwanakin kaltum uku a khartum a lokacin ta ji rayuwa ta fara tsananta a gareta saboda tsananin wulakanci, dabakin halin da kalah da ‘yarta lami suke nuna mata . kalah ma sana’ar sayar da kosai take yi irin na madina. Kaltum taxage tana taya su aiki, itace mai wankin wake, itace ixa wuta da wanke wanke ashe ba’a son ransu take yi musu wannan hidimar ba, suna ciyar da ita ne kawai amma ba’a son ransu ba.
Suna wajen sayar da kosai da safe sai kalah ta dubi kaltum ta tsuke fuska t ace “kaltum ina fatan dai kin san yadda rayuwar sudan take, kowa ta kansa yake kin ma fi kowa sani tunda an ce bara ku ke yi a bur sudan. Dan haka ka’idar ciyar da bako kwanaki uku ne kin cika kwanaki uku yau, don haka ki fita ki nemi naki tunda har yanxu iyayenki basu bugo waya ba balle su turo da kudin jirgi.”
Hankalin kaltum ya tashi ta rasa abinda yake damunta, ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa babu inda ta sani , bata san inda xata fara neman kudi ba don haka sai ta fara kuka ta fada cikin tashin hankali.
Ta ce “kalah, ina xan je in nemo abinci bayan ni bakuwa ce?
Ki taimaka min ki kira iyaye na a waya su turo da kudin jirgi ko mota sai in tafi………”
Kalah ta katse ta tun kafin ta rufe baki. Kin bani kudi ne da xaki ce in kira su a wayata, su baxa su kira niba sai ni, ashe ni na damu suga ‘yar su. Baxan kira ba in daisu ba xasu kira niba.
Lami ta jakunnen kaltum da karfi tace “ki bude kunnuwanki ki ji, ki sani anan khartum ba’a bara ba kamar a bur sudan ba, idan ki ka yi bara a nan kama ki xa’ayi a kai ki dajin mujawara a yarda ke, ke ba a nigeri ba ke ba a sudan ba har sai wahala ta kashe ki.”
Kaltum ta fashe da kuka ta juya ta koma gida ta shiga daki ta xauna akan buhun kayanta, tayi tagumi tayi kuka har kamar idanuwanta xasu fice. Ta yi takaici akan rabo tada aka yi da bur sudan aka kawo ta nan inda bata san kowa ba, babu mai taimakonta. Haka ta yini da yunwa ba abincin safe babu na rana saida daddare tana kallon kalah da ‘yarta suka dafa abincinsu suka juya mata baya suka ci saida suka rage saura suka bata ta ci ta sude kwano sannan ta iya samun dan barci.
Gari na wayewa bayan kaltum ta yi sallah sai ta shiga wankewa kalah wake, a fusace lami ta xo ta fuxge kwaryar da waken yake ciki ta sake maimaita mata cewar ba xasu iya ci gaba da ciyar da ita ba ta je ta nemi sana’arta. Kaltum ta koma gefe ta tsuguna tana kuka tana ganinsu suka dauki kayan suyar kosansu suka tafi wajen sayarwa.
Hantsi yayi cikinta kuwa ya dau rurin yunwa tana tunanin in da xata nufa gashi bata san kowa ba a garin sai taji an dafa kafadarta ta baya tana dagowa sai taga wata matashiyar budurwa ‘yar kusa da dakinsu ce mai suna fatsima.
Ta ce da kaltum”lafiya kike xaune kina kuka ke kadai? ”
Sai kaltum ta fara share hawaye tana murmushin karfin hali tayi sauri ta gyara xancen ta ce wai ciwon kai ne yake damun ta. Fatsima ta girgixa kai tace “babu wani ciwon kai da yake damunki mun san komai tun sanda kika xo muke tausaya miki saboda mun san xaki hadu da wulakanci a wajen kala da ‘yar ta saboda basu da kirki kowa ya san bakin halinsu ko kadan basu da mutunci gasu da rowa. Ki tashi muje kiyi irin sana’ar da muke

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login