Showing 24001 words to 27000 words out of 62773 words
dazasu hau,akwatina na dora a kaina na yanki hanya ina ta gudu burina karsu bacemin bangansuba,ina haki ina komai kaman raina zai fita amma ban dakata da gudunba saida na fara alamaun ganin bakin hanyar dasuka ce na samesu tukun.
A jiye kayana nayi a gefe,lokacin dana isa. Bamu muka samu wata motar ta daukemu ba har wajen karfe 8:00am na dare,saboda lokacinne suke wucewa mu kuma said mu sauka a bakin garin su kuma su wuce garin dazasu je.
Hawa mukayi dukkanmu kowa da kayamsa,nikam samun waje nayi na kwanta tareda yin filo da kayana saboda gudun sata,su kuwa kowa yana bayanin idan an sauka,mai zai farayi,masu lissafin wajen da zasu sauka daban haka masu lissafin irin aikin kudin dazsuyi daban kafin lokacin yah kare mudawo.
Na dade ina bacci saboda lokacin dana tashi duhu yah lullube sararin samaniyah ga kuma duhu hazo da kuma azababben sanyi dayake hurawa kaman an saka mutum a cikin fridge.
Kallon sauran mutanen bayan bodin motar nayi ,suma duk sun takure a wajen daya kaman sardines,hmm neman kudi da wuyah na fada a raina.
Karar salatin da mai motar yah fara yine yah dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi,inda kowa a cikin motar shima yah tashi zaune dan jin mai suka gani,hantar cikin mune da duri ruwa tun kafin mu san abinda yake faruwa,tsofin cikin said salati sukeyi wanda suk da banyi karatuba kuma banason yi nasan ba dadai suke fadaba.
Wani daga cikin yaran dirabannne ya leko ta gefen glass din gaban motar yake cewa,
"Toh jama'a saidai fah kowa yayi ta kansa saboda,yan fashine a gabanmu kadan"
Iyar shehu ce tayi saurin cewa,
"Yan fashion kuma,a wannan hanyar amma bamu taba jin labarin yam fashi a hanyar nan ba duk wushewar mu"
"Hakane I yah muma bamu taba gamuwa dasuba gaskiya akwai abinda yake faruwa,gashi babu damar mukoma da baya ,domin suna dauke da bindigogi a hannunsu kuma basuyi kama da kananan yan fashi ba"
Duk abinda suke fada ina jinsu,saidai bana gane mai suke hasasowa saboda ni ban taba ganin yan fashinba sai labarinsu dana keji a nayi kawai.yaran cikin motar kuwa su iliyah da bazasu wuce shekarunmu ba sai kuka suke suna kiran sunan iyayensu sai kace wani shegenne yace su taho.
Motarmu ce tafara sloww a hankali har muka tsaya cak da tafiyah.
Wata muryah ce marar dadin ji ta doki cikin dodon kunnena daga jin muryar babban mutumne kuma ba yaran hausawa ba,masifa yake yiwa direban akan ya fito daga cikin motar. Fitowa yayi yana gaishesu,saida suka kwala masa wani abu kafin daya daga cikinsu yace,
"Kudi ka bamu kudi koh kuma mu dauka rai"
"Ogah babu kudi yamzu muka debo kayan"
Wani ne daga cikinsu yace kai wannan ka barsu kawai basuyi kama da wanda zamu samu kudi a wajensu ba"
Har sun barshi yakoma cikin motar mu fara tafiyah,wani yaro daga cikin mu yayi atishawa saboda murar dayake yi,hantar cikinmu ce tah kada dan dagani kashinmu yah bushe yau.
Tun kafin na gama Tunani naga sun yaye tampol din da muke ciki sai gamu gasu lokacin da suka dallemu da wata fitila mai haske.
Wani daga cikinsu ne ya duro cikin motar yana daukar mu yana mikawa wanda yake waje shikuma yana diremu a kasa,kallon mu sukeyi da mamaki ganin yara a motar kayah.
"Kai driver kenan sato yara kayi baka fadamana ba"
"Ahah ogah ba sato su nayi ba,zan ajiyesu a babban garine na wuce"
"Taya zamu yarda dakai lallai dole kayi bayani"
Dukansa suka farayi yana ihu tareda rantse musu,nice nayi saurin cewa,
"Ba sato mu yayi ba mu ka ce yarage mana hanya zuwa cikin babban gari"
Tun kafin na rude baki wani daga cikinsu yah yadak'i dan kwalina tareda gashina da karfi,wata kara na sake mai kara saboda azabar danaji,zefarni yayi a gefe tareda cewa,ku kama yarannan dukka ku saka min su a motah.
Su iliyah suna jin haka suka fara ihu,babu abinda na tuno a raina sai yanda dukka yaran iyayensu suke matukar nuna musu soyayya,yah zasuji idan suka ga cewar yaran su sun bata kenan har abada,musamman mahaifiyar iliyah shikadai ta haifa a rayiwarta ,dole na ceci abokaina in ba hakaba zasu illatar dasu,sannan koda na saukar da rayuwata babu komai tumda idan na mutu a sannan babu wamda yake sona bare yah tuna Dani,da haka na samu karfin gwiwar tashi daga wajen nace,
"Bazaku tafi dasuba,saidai ku tafi da ni kadai, in ma tafiyah zakuyi da wani daga cikinmu,sukam dole su koma wajen iyayensu cikin koshin lafiya"
Dariyah ogannasu yah fashe da itah ganin yanda na wani murtuke fuska kaman wadda zata iyah masa wani abu,tahowa yayi wajena yah kamani tareda hade hannuna waje daya yana kallon fuskata,cizo na garya masa a hannunsa na kusa da fuskata,aikuwa cikin sauri yayi min duka mai karfi wanda saida hankalina yah gushe.
Cikin juyawa da kaina yake na ga lokacin da motar yan sanda tah fara tahowa daga nesa,yayinda ogannasu yace su daukoni su sakani a cikin motarsa,ina ganin lokacin da motar dana ke ciki tana ta tafiya cikin jeji hoton motarmu kuma yana karayin nisa a cikin idanuna har wani duhu yah lullube ganina.
Bude idona nayi na ganni a wani daki mai dauke da yara da yawa,dukkansu tsiramin ido sukayi kaman sunga dodo,nima a vangarennawa kallonsu nakeyi da tunanin a wane waje nake haka,babu wanda zai amsamin tambaya ta da alamu saboda yaran dukkansu a tsorace suke taya zasu amsamin wata tambaya.
Daga idona nayi ina kallon wani mutumi wanda shigowarsa dakin kenan,kama yayimin dana daba ganinsa awani waje,saida nayi Tunani kafin na tuna da yana daya daga cikin yan fashin da muka hadu dasu a hanyarmu ta zuwa babban birni,cikin kankanin lokaci hankalina yah fara tunanomin abinda yah faru dallah,saboda hankalina ya gushe lokacin baya saboda dukan da shugabannasu yayimin a kai.
Daga ido yayi yana kareni da kallo sannan yana daga gira,nima kallonsa nayi saidai ban dade ba na dauke ganina daga Kansas ina sunkuyar dakai kasa,wani ne daga bayansa naji yana tambayar sa cikin gurbatacciyar hausa.
"Wace yarinyace wannan kuka kawo jiyah"
"Mutumiyar ogah ce yana bukatar hukuntata ne,idan yah warke,dan yanzu haka yana can daki hannunsa ya shanye saboda cizonsa datayi,nazo yin magana da itah kuma naga kaman da alamun hankalinta yah gushe saboda mummunan duka da ogah yayi mata akai"
"Wai dagaske kanayi shine abinda yah faru"
"Eh babu karyah akan hakan,yanzu bari na kaitah dakin ogah doctor yana nemamnta"
Duk maganar dasuke inajinsu,saidai koh daga kai banyiba,amma batun hannunsa daya shanye nasan dama hakan zata faru dan yadda jinina yake da guba haka ma bakina,nikaina ina Mamakin hakan.
Fizgata yayi ta kayi saidai da alama shidin a tsorace yake dani,domin duk yah daure hannunsa da wani karfe,duk da halin ciwo da nake na rikeni dayayi saida nayi dariyah da abinda yayi din.
Dakin babu nisa daga inda yah fito dani saidai kuma yanayin surkukiyar wajen daga gani anyi ne domin samun damar tserewa idan rana ta baci.
Ni kaina saida abin yah tsoratani ganin yanda hannun nasa yayi wani baki musamman wajen da cizon yah fara,kamar wanda maciji yasareshi,sunkyar da kai nayi har ya sakko daga kan gadon ya iso wajen danake,kama kumatuna yayi kafin yah dago da fuskata dan dole.
Nima kallon mummunar fuskar tasa nake mai,cike da takaici a cikinta,
"Ke me kika saka min acikin jikina mai azabar ciwo wanda inaji yana kone jinin jikina sannan kuma yana rubar da fatar jikina?"
"Ni babu abinda nayi maka,kawai wata cutar ce dakai"
"Ke kewaye da har zakice haka,zaki fuskanci hukuncina dole,ku daureta a cikin cell,sannan ku fara shirye shiyen tafiyarmu,kasar da zamuje ta boyayyiyar hanya"
Komawa sukayi dani daga amma yanzu wani daki ne daban mai matukar duhun gaske.
Tun daga bakin kofar mutum yake jiyo kukan beraye da kuma warin datti dana mushe,tunkudani ciki sukayi tareda maida,kofar suka rufe.
Tafiya nake a hankali a wajen saboda bana ganin gabana har na isa jikin bangon dakin,samun waje nayi na zauna dan ganin mai zai faru kuma yanzu.
Mutanen da suka saba zuwamin ne yauma suka zo,saidai yanzu sun sanja kaya daga jajaye zuwa bakake wuluk,kara mikomin kwaryar sukayi yauma dauke da wani jan ruwa a ciki,har nayi kokarin kawar da kai mutumin yace,
"Karki dam u wannan ba ruwan dawowarki cikinmu bane,wannan na biki ne da mukeyi,kuma yah zama dole shikin sha wannan domin a wannan lokacinne zaki fara taka mataki na gaba"
Sake mikomin yayi bayan ya gama bayani,abinda yah ban mamaki shine na kasa yimasa,musu akan hakan saima karba nayi na kai baki,dandanon gishiri naji dakuma karni daya ziyarci hancina,cikin sauri na sau kwaryar ta fafi kasa ina mai cewa,
"Jini jini kuka bani na sha ,meyasa"
"Saboda shine nasararmu zaki sani daga baya watarana,yanzu zamce yakare tunda kin dandana a bikinki,duk wanda kika dandana jininsa a nan gaba zai kasance namune,ki saka wannan acikin kwakwalwarki"
Tun daga wannan maganar na farka daga baccin danake yi,yau banyi Mamakin ganinsu ba saidai abinda yabani mamaki shine abinda suka bani nasha,kuma tun daga lokacin nakejin kaman ana zigani na ciji mutane.
Bamuyi kwana uku a wajen ba na ga wani yazo wajen kejinnawa amma ba wanda yasava kawomin abinci bane,budewa yayi tareda yimin alama na biyoshi,saboda hasken daya ziyarci idona karo na farko bayan kwana uku,bansan lokacin dana rufe idona ba,saida nasaba da hasken kafin na bude ina kallon sararin samaniyah,da sauri na bishi ganin yanda yamin nisa kafin na isoshi.
Samun su nayi kowa yayi shiri,dukka yaran an saka su acikin mota ,nima ina zuwa suka iza keyata cikin motar muka fara tafiyah.
Tafiyar mai nisa mukayi,tun muna ganin rana har ta fadi mukayi bacci gari yah sake wayewa amma duk muna cikin tafiya,dukkan mu idan ka ganmu mun yi laushi lukwui saboda tsabar gajiya.
Bude ido mukayi kawai sai ganinmu mukayi a bakin wani tafkeken ruwa,sai shiga jirgin ruwa ake ana wucewa.
Mu ma cusamu akayi a wani jirgin ruwan saidai a kasan cikin jirgin ruwan inda babu wanda zai kuladamu.
Nan ma munyi tafiyah mai nisa kafin muka ji ana mana alamar mu fito ,kallon inda muka nake da mamaki.
Toh kuma nan ina ne ???
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤16❤
Da mota aka daukemu zuwa masaukinmu wanda shima cikin lungunne kaman wanda muka fito a ciki,duk da bansan a wani abu ba lokacin amma nasan wajen ba kasarmu bace,saboda duk mutanen da muke wucewa fararene tass kaman zabiyah,kallon hanya mukai tayi har muka isa inda zamu zauna din.
Washarin saukarmu a sabon wajenne muka tashi da cewar ogan su yah mutu,saboda cizon danayi masa sati d'aya daya wuce,zuwa sukayi suka sake daukata zuwa dakin dayake inda likitoci suke ta zirga zirga,
Yaron oganne wanda shine mataimakinsa,tsaye yake akan gawar yana kallon yanda yayi bakikkirin kaman an shafeshi da gawayi,rufeshi yayi da wani farin kyalle idonsa yana zubar da hawaye,juyo da kallonsa yayi i zuwa gateni wanda nima kallon gawar nake.
Tun daga fuskarsa zaka san ransa yah baci matuka saboda hatta naman jiknsa rawa yakeyi.
Wata wukace a hannunsa mai masifar kaifi yake nufoni da itah,wani bugu zuciyata takeyi ina matsawa da baya domin nasa hukuncin ba mai dadi bane,magana yafara cikin dacin harshe,
"Dolene kema ki mutu kuma kisan wulakanci tunda har kikayi sanadiyyar mutuwar dan uwana"
Damkar wuyana yayi yah dagani sama yana kallon cikin idona,har sannan wutar bakin cikin dake huruwa a cikin ransa bata daina ruruwa ba,daga wukar yayi yah shaftata min wuka a makogarona,wani irin zafine ya ziyarci wajen inda nayi sautin saka hannu ina tari,tsorone ya kamani jin yadda iska ke fitowa daga makogarona a maimakon tah hancina ko baki,ina jin yadda iskar ke daina fita har yah zamo ta koma fitowa daga inda dama ya dace da ita wato hanci.
Dauke hannuna nayi daga kan wuyana ina,kallon yanda jinin dake hannuna yake konewa,a lokacin dana kai kallona kan mutanen dake dakin dukkan su kowa ni yake kallo bakinsa bude,ni kuwa ko ta kansu banbi ba saima,fita da nayi daga dakin ,saboda idan Mamakin abinda yah farune ni na dade da gama wannan Mamakin,kawai na mika wuyah da duk ma wace halittace ni shikenan komai yah banjama banjam.
Tun daga lokacin babu wanda yasake tunkarata da wani zancen komai kaffah kaffah sukeyi kowa yana tsoron zuwa kusa dani,tun abin yana min dadi har yafara damuna saboda yanda sukeyimin kallon dodo abin babu dad'i,sai a sannan na tuno illar da ummah take nunamin na gujewa nuna ainihin ni wacece a gaban mutane,musamman ma wanda suke kusa dani,dan saina budi ido na rasa kowa a DUNIYA TA.
Washagari da safe lokacin dana tashi babu kowa a dakinnamu,abinne ya dauremin kai saidai ban ce komaiba,tashi nayi na fito waje nan ma ban hadu da komaiba,
Wasu mutane nagani da alama kaman yan sanda ne danna gansu da kayan tsaro,suna kallona suka iyo wajena tareda sakamin wata sarka a hannu,nidai kawai kallonsu nake har muka dau wata hanya bayan mun shiga wata mota mai budadden baya.
A bakin wani get muka tsaya saida wani mutum yah duba kafin muka shige.
Gidan yana da bangarori da dama,gashi babban ginine wanda tunda nake ban taba ganin irin wannan gininba.
Iza keyata sukayi har wani bangare wanda yake can karshen gidan,muna shiga naganshi kaman gida saidai,da gani wajen da tsaro sosai,a wani daki suka sakani bayan an cire sarkar da take hannuna.
Wasu yarane a dakin guda hudu dukkan su suna sanye da kaya kaman uniform din makarantar garinmu irin wanda,aka bani bayan shigowarmu wajen,biyu daga cikinsu bazasu kaini ba,amma dayar da take gefe ita kam zatayi sa'a ta daga ganinta,dukkansu fararene tass da alama basuyi kama da kalar fatataba,duk da cewa nima farace amma baza'a hada nawa farin danasu ba.
Samun waje nayi na zauna a gefe duk da yanda nakejin fitsari babu damar na tambaya tunda bansan da wane yare zanyi magana ba,saura kiris fitsarin yah zubo kafata har rawa takeyi naga daya daga cikinsu ta tashi ta shiga wani dan daki shima a cikin inda muke dinne. Bayan ta fitone nima na shiga saidai ja nayi na tsaya ganin wani katon baho a bandakin da kuma wani dogon karfe a tsaye sai wani abu kuma mai dan kai shima a kasan dogon karfen,tsugunnawa kawai nayi na tsula fitsarina koma dakin waye shiya sani.
Bayan na gama ne zan tashi sai santsi ya debeni,kama bakin dake jikin dogon karfennayi gam,amma sainaji yah juya ruwa kuma ya fara zuba,tsayawa nayi ina kallon ruwan da mamaki ganin daga inda ruwan yake fita,kunnawa na farayi ina kashewa nayi yafi goma kafin na tsaya dayi,fita nayi da sauri na dauko wannan kayan da suka bani masu kyau kalar ruwan omo,zuwa nayi na wanke jikina kafin nasaka su na fito ina bubbudawa nima na saka irin kayansu.
Yanzu nayi sati daya a wajen,kullum za'a kawo mana abinci mai dadi,su kam na dakin kaman basa son zaman wajen da kullum cikin tagumi suke abincin ma basaci da yawa,nikuwa saina cinye nawa na side kwanon wani lokacin ma saina hada da nasu na cinye tass,ga wanka yanzu nasan yanda ake amfani da komai na bandakin sainayi sau uku ma a rana,sannan idan rana ta dan fito sosai za'a kaimu wajen karatun su larabci da kuma su litattafai na addini.
Cikin lokaci kankani nayi bulbul dani fatata har sheki tajeyi saboda tsabar dadin danake ci,abu daya na tsana wanda yake cimin tuwo a kwaryah,shine duk lokacin sallah sai anzo an tafi damu zuwa cikin masallaci ran juma'a kuma zasu bamu abaya da gyalenta musaka mu tafi masallaci,ga karatun asuba dole sai kowa yayi,wannan shikadai yake hadamu dasu,idan kuma mutum bayyiba ayi masa duka lilis,kuma sai ka wanke dukkan kayan yan dakinku da kuma wankin bandaki.
Yanzu nafara sanin wani abu idan yan dakinmu sun fada ,dan yanzu nasan sunansu suma sunana,khairah da hairah,su yan biyune,matar babansu suka yiwa wankan soyayyan mai shiyasa aka kawosu,ita kuma shaheedah guduwa tayi daga gida tabi yan iska,shiyasa yan uwan babanta suka kawota nan,tambayar su nayi nikuma meyasa aka kawoni wajen,cewa sukayi wai sunji ana cewa an kamani ne da hodar iblis(cocaine)a cikin wani gida da ba'a amfani dashi,da alama wai abokan aikina ne suka gudu saini kadai,cikin kankanin lokaci nayi tunanin cewa,da gangan suka gudu suka barni a kamani saboda tsorona da sukeyi.
Tun daga lokacin muke dan magana da,su shaheedah duk da cewa banajin yaren larabci sosai amma ina gwadawa,har take fadamin sunan kasar su palastine. Abin bai wani ban mamaki ba tunda ba wani sanin mai take nufi nayi ba,kawai dai naji ta ne,ni dai ina rayuwa kawai naci na koshi kuma nayi abinda nakeso idan masu kuladamu basu ganiba,dan yanzu har wajen bangaren maza nake jan shaheedah muje hira dayake itama jar wuyah ce tasan takan rayuwar air,saimunsha hirarmu da su munajin mai sukayi aka kawosu suna fadamana,harda labarin yanda area su take.
Haka kawai idan ba zancen rashin arzikba bana jin raina yanaso don duk lokacin da'aka zo karatu tun daga na turanci har na larabci yi kawai nake badan raina yanaso ba,duk da ina kokari sosai na iyah kowanne amma raina bayaso,kawai dannasan horon dazai biyo baya bazaimin kyau bane,gashi tsoron malamin addinin nan nake kaman raina zai fita,dan koda da kuskure ya zangamin carbinsa ji nakeyi kaman yana kona jinin jikina,shiyasa ni nake fara bada hadda idan yazo karba,sai yaga kaman nafi kowa san karatun ,nan kuwa ba haka abin yake ba sam.
Wata ranar juma'ane aka daukemu zuwa makabarta,munsha abaya bakake dukkanmu matan,su kuma mazan sunsha fararen kayah,bayan mun shiga motane kuma naga wasu matan suma sunsha bakaken kaya amma su da nikaf a idonsu suna shiga wata motar,tabo shaheedah nayi wanda take gefena a zaune,dagowa tayi tareda tambayar menene,nuna mata nayi tunda har sannan ban iya larabcin sosai ba sai kalmomi kadan kadan,ganin ta kallesu ne nace mata suwaye?
Murmushi tayi kafin tace,
"Masu laifine amma sun haura shekara goma sha takwas shiyasa aka kaisu wancan kurkukun,muma da mun yi shekara sha takwas da can za'a kaimu,kuma su suna aiki sosai ga kuma horo ga wanda yah aikata laifi mai yawa"
Jijjiga kaina kawai nayi har muka ja muka tafi idona bai dauke daga kan motar tasu ba.
Mun dade muna tafiyah kafin muka isa zuwa cikin makabartar,ba mu muka dawoba har sai wajen magriba ,naji dadin fitar sosai koba komai nayi kallon waje dayawa.
Bayan munyi sallar isha ne nazo na kwanta ba bacci nayi ba tunani kawai nakeyi na gida ,tareda yiwa kaina tambayoyi yanzu suna can sun manta Dani babu wanda zayyi tunanin an