Showing 9001 words to 12000 words out of 62773 words
yabi wani Soja a anguwarsu.
A can yayi makarantar sojojin a wajensa sannan yah fara aikin sojan,saboda kwarewarsa da kuma zafin nama har yakai matsayin Major da kananun shekaru.
Yanzu shekarar sa biyar da aure,inda yah auri matarsa Saleemah y'ar gidan shugabansu,da d'ansu guda daya mai sunan baba umaru,(farouq),saikuma ciki ta saleemah take dashi dan karami a halin yanzu.
Babu wanda yasan wace wainar ake toyawa a gidan major sameer din saboda sai yayi shekara biyar ma bai zoba,dan tun sanda yayi aure yakawo matarsa bai sake dawowa ba sai wannan zuwan da zaiyi wani sati mai zuwa,suna can a porthacourt shida matarsa da kuma aikinsa.
"Kee salma sinji wai yayah sameer zaizo wani satin shida anty saleemah,"
Zainab ta fad'a tana washe baki,
"Toh miye dan zasuzo din ,ni wlh na tsani matar nan tasa ta wani makaleshi ko zuwa bayayi bare ya samu wata ya aura,sai ita kadai kawai"
"Heeehhehe yarinya kice kishi kike,koh kina cikine a yi y'ar hadi gida keda shi"
Sameerah ta fada tana turo daurin dan kwalinta gaban goshi,wanda tun dazu chatting take a WhatsApp batace komai ba sai yanzu "
"Kee sameerah banason iskanci kishin uban me kuma,mai zanyi dashi "
"Mai zai yi dake dai,kina nan guntun alhajawa sun lakace sun bar saura,kinga dan kyakykyawan matashi mai kudi kinaso ki shiga daga ciki"
"Kutumar Uba lallai sameerah sai yanzu nagane inda kika dosa,kinaso kice kishi kike dani dan kinga bakya kasuwa,babu kowa sai wannan kanjamemmen sameenun mai kama da biri,Wanda koh daura min shi akayi zan cire na zefar ke kuwa nan har durkusawa kike kina rokonsa kar yah tafi"
Wani wawan duka sameerah ta kaiwa salma a kumatu,ai kuwa suka hau kokuwa,zainab ceh ta tashi ta fice dan ganin abin yayi yawa,dama itah tsoron masifah ne da itah kamar farar kura.
Sameemah kuwa tana zaune tana kallonsu saima dauke kai da tayi kaman ba'a haliccesu a dakinba.
Wayar tah ce tayi ring ta zuya ta dauka,saidai batajin mai ake fad'a saboda surutun da su salma sukeyi,wata tsawa ta daka musu cikim bacin rai.Dukkansu shiru sukayi suna kallonta,
"Hello,burgu mai kake cewa waim"
"Had'uwa da BUBA JINI kuma ?"
"Shikenan zamuji da Wacce yazo saidai ka kaishi zuwa gobe dan yanzu akwai abinda nake shirin yi ne"
Saida ta ajiye wayar ta kallesu kafin suka kula da yanda ta basu umarni cikin kankanin lokaci kuma suka bi batare da sun sani ba(sameemah kenan).
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____***GIDAN GANDU***____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤07❤
Tashi sameemah tayi kaman mai kiwuyar tashi a wajen kafin ta nufi kofar da alhaji babban yake.
Yana kwance anyi masa shimfidi a tsakar dakin saidai idonsa yana kallon mai wucewa,kallon sameemah yake da son gano wacece,
"Wannan din wacece?"
"Sameemah ceh "
"Ohj sameematuh ceh,toh yah labarin mahaifiyar taki kuwa an ji labarin itah y'ar inace ?"
"Mahaifiyata kuma ,ita kam ai tah rasu"
"Yaushe amma banida labari. Koh?"
"Ina nasan maka ni zaka tambaya,ya jikinnaka?"
"Lah jiki da sauki yar nan kinsan tsufah ne "
"Eh AI naga alama kam"
Tafada tana kare masa kallo daga inda take zaune,
"Toh nizan tafi allah yasa kurigamu gidan gaskiya,ina haka ake cewa?"
"Ni zaki tambaya,toh kigaida ummartaki idan an ganta"
"Kai ni karka dameni da wani zancen na gaisheta,inaga ma kaine kake kallonta saboda ka kusa jona sahunsu,haka kawai zaka wani dameni da cewa in gaida wanda yah mutu,kai idan kaje kace ina gaisheta "
"Lallai yar nan allah yayi ja'irah"
"Ashe da sauran hankalinka kasan mai kake,to sai anjima allah yah sawwake"
Daga haka ta kade skirt dinta tabar wajen tana buga feduwa,tai hanyar waje,bayan tah gyara gyalen wuyannata(dan itah yanda maza suke ficewa daga gida sanda suka so fita haka take ficewarta sai sanda ta dawo).
Washagari da safe da wuri tabar gida saboda shirye shiryen haduwa da buba jini,dan kaff garin ba kungiyar dabar da ta kai tasa wajen kwarewa da kuma bud'adden ido.
Lokacin da suka isah ainihin inda sansanin yan dabarsa take saida burgu yayi Mamakin irin tsarin da akayiwa wajen kaman na yan boko haram.
A harabar cikin wajen suka samu anyi shimfid'a da kayan marmari duk na tarar seemah jar wuyah da yaranta.
Tun daga nesa kuwa buuba jini yah hangosu itahce a gaba suna biye da itah ,har Mamakin irin biyayyar da yaranta suke mata yake,saboda ko shi daya tara manyan yan daba,basa masa biyyayah yanda yaran seemah suke mata biyyayah.
Tana zuwa saida ta zauna a tsakiyar daddumar suna kallon juna ita da buba jini kafin sauran yaran ta,wato su burgu suka zauna a bayanta.
Murmushi yayi tareda dage girar hagun irinna yan iskannan kafin yace,
"Barkanki da zuwa"
Itama irin yanda yayi mata tayi kafin tace,
"Na amsa gayyatarka ,saika fadamin meyake dauke a bakinka da har ka nemi yin magana dani,kuma har cikin gidanka?"
"Ba komai bane ,inaso ne kawai ki had'e da kungiyata muzama d'ayah"
"Meyasa ka bukaci hakan"
"Saboda keh macece,nasan ba iyah dan kungiyah yan siyasa suke nemanki ba,harda wani kudurinsu na daban,kinga idan muka hade ,karfin izzarki da kuma tsaro zai karu,nikuma kinga saiki kawo mana hankalin yan siyasah su bamu aiki,nasan bazaki ki amincewa ba"
"Idan kuma naki amincewar fah mezakayi?"
Kallon idonta yayi yanda take maida martani kaman ba a gabansa take ba ,babu alamar tsoro a idonta,
"Tunda kika shigo gidannan dole ki amince da bukata ta "
"Idan naki fah mai zai faru"
"Toh bazaki bar gidannan da kafarki b............"
Tin kafin yah karisa maganar,seemah ta yanka jijiyar hannunsa daya rike wukar dayake mata barazana da itah cikin kiftawar ido.
Kururuwa yah fara yana danne wajen da jini yake tah fitah,
"Kai din dama ba babban shege bane ,ya za'ayi wanda yake kiran kansa da suna jini kuma yayi ihu dan jini yah fito daga jikinsa?"
Yan dabar sa ne suka iyo kanta da sauri,sai kuma yah dakatar dasu ,cikin dauriyah da cije baki yace
"Karku yi mata komai,kuyi hanzarin shiryah motah yanzu mu tafi asibiti,banason kowa yayi mata hukunci,ni nan da kaina zan hukuntata,sai tayi dana sanin abinda tah aikata"
"Kai dakata da surutun haka,duk naji su,bana bukatar neman ayimin maimaici,saidai kai din kayi hanzari,domin in bakayi sauriba jininka zai kare a nan wajen,kaga sai muga wa zai baka ransa kazo daukar fansar dashi"
Mikewa yayi idonsa yayi jawur dan azaba,fadawa mota yayi tareda watsawa sameemah wani mugun kallo,na alamar zamu had'u.
Ita kuwa gogar ko a jikinta saima murmushi da tayi masa tareda daga masa hannu tana yimasa bye bye.
Duk abinnan da ake,su burgu mutuwar zaune sukayi lokacin da suka ga abinda sameemah ta aikata,dan sun saddakar yau kam kwanansu yah kare a wajen buba jini,dan duk fadin garin babu wanda bai sanshi wajen yanka ba da kuma aika aika,kowa tsoronsa yake babba da yaro.
Saida ta shuri burgu kafin yayi ajiyar zuciya yace ,
"Ma'am shugaba,sun yanka mu ne"
Zefah masa makullin mashin tayi kawai batare da tace komai bah.
Bayan sun hau mashi dinne suna tafiyah burgu yace,
"Amma shugaba bakya ganin yanzu muna cikin matsala"
"Dallah ni yi shiru ka rufemin baki ,bakuda aiki sai tsoron tsiyah,ni narasa meyasa ma nake tare daku har yanzu"
"Yi hakuri bazan kuma bah"
"Kudin hannuna yayi low,kaini gidan badariyyah,zan karbi bashina da tazo har gida ta karbawa mijinta a wajena,yau zanga mai hanani fitowa da kudina a cikin gidannan,in tareda uwar wani ake samosu"
"Gaskiya kam shugaba kiyimasu rashin mutunci ba shin fah ya kusa wata guda a wajensu,babu ma yah wannan mijinnata kullum yana wajen caca"
"Toh ina ruwanka,kai waye zaka zagi mijin yar uwata,ko cewa nayi ka tayani,kudinka ne koh nawa?"
"Kiyi hakuri shugaba an iso gidan "
Sauka tayi daga kan mashin din kafin tacewa burgu,
"Jirani na Shiga na fito,dan ko bayanan saita fadamin inda yake"
Langa langan kofar gidan tah buga da karfi,saida awakin gidan suka dungura suna d'aure,badariyyah ce ta fito da sauri,suna had'a ido da sameemah ta buda wani uban salati da a'uziyyah tana dafeh kirji.
"Eh zaki kori shedan mana tunda kinga nice,na rantse ko dujal zaki kora saikin fitomin da kudina,koh kuma ki fadamim inda lalataccen mijinnaki yake naje na karba"
"Haba sameemah babu koh Sallama,kuma ai saiki shigo mu gaisa koh?"
"Ba gaisuwa ceh ta kawoni ba,kudina nazo karba,saiki bari sanda nazo zumuncin saiki ce ga wajen zama,ki fitomin da kudina yanzu ,dan babu d'aga kafa yau,koh inna karime zaki sayar bai dameniba,ni kudina nasani,tunda ba da wani shege aka hadu aka tarasu ba"
"Kiyi hakuri sameemah,wlh ko kudin cefane nima bai baniba,kuma ai ni yar uwarkice"
"Hmmm ke kikasan wannan yaren,fad'amim inda yake yanzunnan,ko kuma na tattare y'an awakincan nayi kasuwar dabbobi dasu yanzunnan"
Tafad'a tana nuna awakin Badariyyahn,
"Ahah kiyi hakuri,indai baban iliyah neh,wallahi yana rumfar kofar gidan Ashiru mai shayi"
"Dama nasan ai duk munafurcine,ba sonsa kike na,indai akan kudinkine"
Juyawa tayi ta fice daga gidan bayan tayi boll da langar data gani a tsakar gidan miyar kuka ta bushe a ciki,
"K'azamai kawai,ai dole kuyi ta gudawa"
Bayan ta fitane Badariyyah ta sauke ajiyar zuciyah tareda cewa,
"Na rabu da masifar yau kam,saikuma wata ta gaba"
Ashiru mai shayine ya k'ara gyara zamansa zance yayi dad'i yace,
"Hmm AI baka saniba BALA,shi sha'anin kudi a bishi a hankali kawai"
Audu ne (baban iliyah mijin Badariyyah),wanda shine mai raba cacar yana tah juyata acikin hannunsa kafin yah raba,
"Shiyasa ni da kaganni nan,banason na ci bashi na mayar,dan ji nake kaman ana zarar hanjina"
Bayan angama rabawa ne,aka hau wasa,round din farko baban iliyah yah cinye wasa,tattare kudin yah farayi,yana washe baki tareda zuga kansa,
"Saini baban iliyah mijin Badariyyah,caca tah sanmu mun santa,nasars a jininmu take"
"Eh in ka gama kirarin saika kirgo kudina ka bani koh?"
Yana d'aga kansa sukayi ido hud'u da sameemah wanda take tsaye a kansa,kokarin maida kudin cikin aljihu yake burgu yayi Sauri ya warce kudin a hannunsa,
Haba sameemah ya zakiyimin haka,Wannan kudin............"
"Yimin Shiru Dallah,kai burgu kirgamin kudin kaga nawane"
"Dubu bakwaine shugaba"
Mika masa hannu tayi tareda cewa,
"Miko sauran cikaton kudin?"
"Iyee na'am ni banida wasu kudin,haba ke kuwa,yah ina auren yayar ki dan kawai na ari bashinki ki dungamin irin wannan tijarar"
"An taba yimaka kaciyah tah biyu?"
"Kaciyah kuma?"
"Toh in baka daina nunani da yatsa ba saina yimaka kaciyah ta biyu yanzunnan,maza ka dauko kudia sauran dubu uku ka bani yanzunnan"
"Ni bani dasu kiyi hakuri,dan allah karki sakemin kaciyah,wallahi ta wanzamai akayimin mai kyau ,bana bukatar ta biyu"
"Toh shikenan,kai burgu ku bud'e gadon bayansa kuyi masa balli balli guda talatin,kowace nairah dubu balli balli goma"
Kowa a wajen dayaji mai za'ayiwa audu sai yacika wandonsa da iska yabar wajen,shikuwa haka suka danne shi yana ihu yana komai suka babballe bayansa da aska,
"Wayyyyyo wayyyyyo,dan Allah kiyi hakuri,wallahi zan baki kudinki wayyyoo"
"Mtswww aikiniki banza lokacin biyan kudin ai yah wuce,bari a gama maka kawai saika tafi gida,na yafe sauran dubu ukun ma,kaga yanzu ba zuwa caca sai an warke kuma😄😄😄😄😄".
Nan suka tafi suka barshi yana ihu,saida yaji bayan yafara hucewa kafin yah lallaba yah tafi gida,Yana ihu yara suna binsa suna dariyah har yah shiga gida.
Tun daga bakin kofah da burgu ya sauketa a mashin takejin hayaniyah,amma da alamun ba na fad'a bane kaman yanda aka saba.
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤08❤
Tundaga daga tsakar gidan tayi arba dana miji mai kayan mata,yana ta wani rausaya kaman bishiyah.
Saida ya juyo kafin takula a she DAN LITI ne yayan bashari,wanda yanzu yah koma LITTY,da suna wanda rabonsa da gidan tun lokacin su sameemah suna shekara goma.
"Hay sister ya kike yah hidima"
"Wata harara ta watsa masa,tareda matsawa zata shige"
"Habadai y'ar uwa yah antynki tana miki magana kina wani shigewa kamar baki ganni ba,ni ba seemah bace bane"
Kare masa kallo tayi,yan da yah sha jan baki,ga hoda kaman zatayi magana,sai rausaya yake yana gyara attachment din dayake kansa wanda ya sakko har kafadarsa.
"Hmm kaine antyn nawa?"
"Eh mana kinyi mamaki ne ?"
"Ahah banyi mamaki ba,taya zanyi mamaki,amma kasani koma kai wayeh banason shishshigi ka fita a sabgata ,in kuma ba haka ba,ko kuma kana tantama ka tambayi y'an gidan suyi maka karatun zama dani in kuma ba hakaba,bazaka iyah jure hukuncina ba,in kunne yaji jiki yah tsira"
Tana gama fad'a masa tayi hanyar dakinnasu,dan liti ne (littty)yah juya yana kallon y'an gidan wanda kowa kallonsa yake da mamaki.
Sameemah tana shiga dakin su,taga kayan mata,akwatina da kuma kayan shafe shafe,batayi mamaki ba ,sai ma abinda yakawota da tayi ta fice a dakin.
A hanyar kofah zata tafi tasake haduwa da shi har sannan yana tsaye a wajen,suna ta tad'i shida su matan gidan,dan yanzu kowa yasake dashi saboda kayan daya kawo ya raba musu,masu shaddodi da masu atampopi,kowa sai washe baki yake yana murna(hmmm mutane da san banza).
Dan litine yah kulada fitar sameemah,cikin sauri yah sha gabanta yana tattaro zanin shaddar dayasa,shi a dole ga mace,
"Haba y'ar uwa,yah daga shigowa kuma zaki fice,tun safe fah ban ganiki a gidannan ba,kuma yanzu kice fita zakiyi?,gaskiya hakan bai daceba,ace kina mace kina fitah"
Yah karisa maganar yana shafa fuska da hannunsa sannan kuma yana kifta ido,takaicine yah isheta ta kasa cemasa ma komai,
"Kasan Allah Idan nasake ganin ka shiga lamarina saina b'atamaka rai,sannan kuma kaje dakinmu ka debe kayanka dan dakin matane ba na gardawa ba"
"Tabbb kijimin karamar yarinya,me kike nufi ai naje dakin maza gardawa?,bazan iyah ba,dakin mata zan zauna yan uwana,dole mu zauna daku karkuji komai,ni banason harkar kauyanci da rashin wayewa ehhe"
"Toh shikenan Allah yabaka sa'a,zakuwa ka bawa wani labari"
Fita tayi da sauri dan ta tuna da zasuje ita da burgu wasu yan kato da gorah sun kama yaronta guda d'ayah yasaci akuyarsu a wani k'auyeh.
*Wanene dan liti?*
Ainihin sunansa shine Shu'aibu ana kiransa dan liti.
Tun yana saurayi yabi yan tafiyah neman kudi can kasar kudu onitcha,tun daga can yabi masu tuwo tuwo.
Shima kwanci tashi yanzu yazama mai zaman kansa dan yanzu yana da gidan tuwo tuwo har guda uku,gashi yazamana rikekken dan daudu,mai gidan kansa na karuwai da kawalai.
Sai wannan lokacin yaga damar zuwa gida bayan barinsa gida na tsawon shekaru,sanda yazo sunyi Mamakin yanda yazama,amma daga lokacin daya fara rabon kaya,sai kowa yah sake yana godiyah,inna karime kuwa sai washe baki ake yi,dan ita kadai saida ta tashi da turmin atamfa har guda goma,ka kuma mayuka da sabulai,ba abinda kkeji sai guda da yada habaici.
Da daddare a zaune suke ana ta hira kaman ba su ba,dan liti yabayar an siyo nama an dafa kowa yana ta ci,ana zazzare ido.
Mazan gidanne suka shigo kowa saida yayi turus ganin bakon al'amari a gidan,
"Ku wace macen ce tazo da mangariba haka?"
"Lah baba umaru nice fah litty ,baka ganeni bane"
"Lah ha I'll ah,kai dan liti,dama kana nan,menene wannan din zan gani haka"
Shi ma kawu shehun uban gayyar kama baki yayi,haka sauran mazan gidan ma,
"Meka gani,sabon salone mun tuna gidane shine muka zo,kasan ance duk wanda yabar gida toh gida yan barshi,gwara mudinga tuna gida saboda wataran"
"Eh zaka tuna gida mana,saboda in an tashi kawoka sanda kafara kashin ajali koh?"
"Haba shehu wannan wane irin fata kake wa danka daka haifah,in bazakayi faran alkhairi ba kayi shiru"
Inna karima ta fada tana tafa cinyah ta cuno baki,itah a dole an zagi d'anta mai k'ashin arzik'i,
"Lallai karima idonki yah rufe yanzu wannan ne d'an? Yanzu zai tattara yabar gidannan basai anjima na karya jawo mana abin magana,muji da wadda ta baibayemu ma yanzu"
"Oh Toh bishiyah ka gani?,kana ganin kayan arzikin dayah kawomin ,idan aka tara abinda kamin tun aurenmu bazai kai hakanba,zancen yabar gidannan kuma babu shi,in abun magana ne ai akwai wanda suka fishi abun magana ma,menene bamuda shi a gidannan,tundaga kan yan fashi,da yan daba,harda yan shaye shaye,toh babu inda zaije,kaima ai bana allah bane,ai kawai ayi sha'anine wai na birni ya cuci na kauye"
Kowa shiru yayi jin abinda uwar dan liti tace,wanda yaga dama yayi addu'a allah yah shirya wanda yaga dama kuma yah yi shiru ya bisu da hmmmm.
Baba kamulune yah shiga kofarsa inda yasamu amaryarsa wanda bai dade da aurota ba dan itah d'anta d'aya ,kuma jinjirine,uwar gidance hauwa mai y'ay'a guda goma,
"Baban su mustapha sannu da shigowa"
"Yawwa Sannu,Ina yayartaki ne,kiramin itah"
"Ohh ta zagaya bandaki bari tah fito"
Suna cikin magana kuwa saiga ta ta fito da buta a hannunta,
"Menene yafaru baban mustapha?"
"Hmm Ku bakujiba kenan,wai dan litine yadawo yazama babban dan daudu yan nan yana raba shaddodi da atamfa ,yayah shehu zai koreshi karima ta hanashi"
"Toh wata sabuwa kenan,allah yah shiryah"
"Ameen dan annabi"
"Ina su mustapha kuwa,yayinsu nagani a masallaci shi ban ganshiba"
"Hmm mustapha suna d'aki da fitila ta tunda dare yah farayi,wai malamar makarantar safece ta bada assignment kuma gobe zata karba shine sukeyi,tun yamma suke abu d'aya ,wai ance duka ne da itah sosai,ni gaskiya ma har karatun ya fita a kaina bakaga fah yanda suka tashi hankalinsuba kamar ba suba,aka ma d'an mutum a yita duka kaman jaki"
"Hmm matsalar damuke fama da ita kenan,allah yah kawomu zamanin da y'ay'a suke samun d'aurin gindi daga wajen iyayensu,yanzu mahaifah sun zama agwagi sai yanda d'a yakeso shi zasuyi,yaushe toh za'a gyara tarbiyyahr yara idan kowa yah boye laifinnasa d'an kuma yanaso ya fad'i laifin d'an wani.
Toh ki kiyayeni da zancen hanasu zuwa makaranta,wata rana ai sai labari,kin fison su zauna a gidan su zama irin sauran yaran koh?su da karnuka babu banbanci? Ko bayan raina ban yadda y'ay'a na su tashi sakaka ba babu nunawa yaro dadai kaman goyon gwauro"
"Shikenan malam amma da zuwa kayi kace a rage dukan yayi yawa"
"Ba inda zanje bazaki bar zancen nan ba koh?,maza ni shiga ciki ki dauko min tuwona,yunwa nake ji"
"Allah yah huci zuciyarka malam"
"Ameen"
Sai can wajen goman dare sameemah tah dawo daga yawonta,kowa yah shiga kofarsa bayan an gama shagalin cin Kayan dad'i Wanda litty yah kawo,tun daga baki kofar dakinnasu takejin shewa ana rangad'a gud'a kamar za a kai amaryah,dan liti ta samu a bakin gadonta a zaune ,sauran yan matan kuma wanda suke nan,suna zaune sun bashi duk hanlalinsu yana tsara musu yanda harkar jin dad'i take ,da kuma abubuwan da mace zatayi ta haska a dunga yayinta,sameerah ceh cikin jin dad'in bayanin da dan liti yayi tai caraf tace,
"Banza muke tah bulayi bara a kufai,ashe ga dan uwanmu nan yasan dawar garin koh yah kikace salmah?"
"Hakane kam ,ai zamu faso said dai kiji ana labarinmu"
"Eh Toh naji kuna so ku haska,amma bazamu shiryah ba idan kuna kirana da d'an uwanku,ku kirani da litty koh kuma sister,yanzudai ku gyaramin wajen kwanciyah said gobe muga yanda za'ayi,ke kuma miye kike tsayeh tunda kika shigo"
Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sameemah wanda tayi tsayuwar sojoji ganin abinda yake wanzuwa a dakin,tab'e baki sukayi had'e da cewa,
"babu ruwanka da itah litty,wannan y'ar bakin cikice,bari mu gyara maka shimfid'in