Showing 51001 words to 54000 words out of 62773 words

Chapter 18 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4428

❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤31❤


Tunda suka hada ido da sameemah duk wani motsinsa yah dauke saura kawai rawa da jikinsa yakeyi,musamman daya ganta da kayan da duk masu hali irinnasa suke tsoron su rutsasu.
"Miye katsaya ka tsaya kana kallonna koh so kake nazo na saka maka wandonnaka harda wani rawar jiki,ai na karya kakkeyi zakayi bayani ne yau"
Har sannan bakinta dauke da murmushi dan taan son irin haka dama,Kallon matar tayi wanda ta ja bargo tah rufe jikinta tana sunkuyar da kai.
"Hmm ji munafuka dallah ku tashi ku fito inason ganinku a waje yanzunnan"
Tana gama fadar hakan tah fice daga dakin tareda nufar sauran dakunan.
Babu kowama a cikin su saboda tuni sauran ma'aikatan suka rarrako su zuwa wajen sauran.
Dukkan su maza da mata yara da tsofi kkwa yah Zauna yayi shiru domin yaji abinda zai faru,mai gidan hayar ne ya shigo da sauri wani yaronsa yana biye da shi,da waya hannunsa koh takalmi bai saka ba,daga ido sameemah tayi tana kallonsa domin jin shikuma da me yake tafe,
"Ina gida naji ance gidan hayata ba lafiya,wai masu kamen karuwai sunzo,toh ke kuma wayah aikoki saboda yanzu ma muka gama waya dashi bayuimin cikyakykyen bayani ba,dan idan kudinharaji ne nariga na bayar hada karin danakeyi a shekara,amma waka a bakin mai ita tafi dadi bari kiyi magana dashi.
Yana gama fadar hakan ya mikawa sameemah wayar dake hannunsa,dauka tayi kafin ta saka hands free,
"Hello........hello.sameemah bai kamata daga hawa aikinki har kin fara saba dokaba,kamata yayi idan zakiyi abu toh ki nemi shawara mana,yanzudai komai yah wuce ki baro Gidan zamuyi magana kawai sannan..........."
"Alhaji bala KO nace Bala,kadaiji yanda na kira sunanka koh,toh billahillazi idan na sake jin hannunka a cikin aikina koda dan kadanne,kai ko wani nakama yafada maka kabashi koyon baya,toh wallahi idan muka dunga buga chakwakiyay dakai saina yi maka kaca kaca,hatta zaman garinnan ma kai har cikin yan uwanka ma sai yayi maka wuyah a rayuwarka,idan kuma kana tunanin ban kai nayi hakan ba toh bismillah mu zuba ni dakai"
Daga wayar tayi ta kwankwatsata da kasa tun kafin ma taji mai zaice daga daya bangaren,jiki na rawa mai gidan hayar yaja da baya yana kallonta.
"Kai kuma idan baka bace a wajennan ba ,toh idan na tashi dakai zan hada harda mataimakinnaka"
Tun kafin ta rufe bakinta yah yayi waje da sauri yana baza rigarsa.kallonta ne yah koma kan wanda aka kama din wanda idonsu zuwa yanzu yah raina fata,
"Ku kiramin wanda na aikesu kuma na ce su tsaya a waje yanzunan"
"An gama ranki yah dade"
"Wani dan gajere daga cikin yan vigilantee dinne yah fita da gudu zuwa waje,basu dade ba sai gasu sun dawo da wasu garada guda biyar,kowannensu dauke da dorina mai kai biyu,
"Kubisu KO wanne kuyi masa bulala goma goma,sannan ku saka su a mota zuwa office"
Ihu suka fara da kururuwa saidai babu yanda zasuyi tunda tafada toh fah lallai sai anyi musu.
Bayan angama round Donne kowa sai nishi yake yi wasu kuma suna tah soshe soshe,masu ragwanta kam harda kukansu.
Har an tashi za'a tafi sai sameemah tah dakatar dasu tareda cewa,
"Tun daga ina akeson shugaba yayi adalci idan ya hau kan mulki?"."
Had'a baki sukayi tareda cewa,"daga gidansu"
"Toh Indian hakane a matsayina na shugaba mai adalci sannan mai nuna yakamata,zanyi adalci ta hanyar karawa kawuna dayake wajennan bulala ashirin kacal,kunga tah kama talatin kenan anyi masa ninkin nasu sau uku"
Dama tun lokacin da sameemah tafara wannan maganar muguntar kawu shehu ya fara tara kwallah a idonsa saboda yasan bazata barshi ya tafi haka banza ba.
Tana nuna yatsanta akan sa garsawannan suka tattagoshi dama basu gaji ba,taleshi sukayi aka fara tsula masa sabon wani lissafin.
Saboda tsabar wuyah kasa ihu yayi sai nishi kawai kaman balamar tunkiya tazo haihuwa,kusan za'a kai karshe kawai gani sukayi wandonsa ya rine da fitsari yana zuba.
Duk da zafin dukan da'aka yimusu saida wasu sukayi dariyah ganin yanda kawu shehu yake fitsari.
Kowa tashi yayi yana dingisawa har wajen motar tasu,shikuwa kawu shehu saida aka tattageshi saboda lagabewa da jikinsa yayi.
Suna zuwa office suka samu su surayyah sun dawo,kuma sunyi nasarar kamoshi kaman yanda aka fadamusu,saidai masu sata a kasuwane ba'a kama ko daya ba.
Wajen da'aka kaishi sameemah ta nufah tareda tsugunnawa a gabanta.
Dayake dan duniyah ne kallon cikin idonta yake yana cewa,
"Dama barin zancen nan kikayi yah wuce yan mata,dan babu abinda zaki iyah a kai,dukane na riga na dake shi"
Tashi tayi daga kusa dashi dan bai isheta ma kallo ba a yanda yake,wani na gefe ta bawa umarni akan yayi masa hukunci kafin a kai shi wajen yan sanda yah bada tara.
Marinsa ma'aikacin yayi amma yah zuyah fuskarsa yah tofar da yawu yana Murmushin taurin kai.
"Ashe Baki cika sunan ki ba na jar wuyha sannan baki cancanci gwagwarmaya da irin mu ba,nayi mamaki da aka cemin yanzu macece shugabar yan kato da gora,amma yanzu na gane kawai daurin kafa kika samu har kika hau kan kujerar,kuma kina daga gefe kina saka mutane aiki suna yimiki,kir idan kin isa ki kiyi dealing da mu mana da kanki"
Har sameemah tah taka kafarta zata bar cikin wajen amma ta tsaya cak saboda jin maganar dayake fesa mata,jijiyoyin wuyanta ne suka tashi lokaci daya,damke hannunta tayi da cije baki,ba wanda bayyi mamaki ba ganin yanda takoma gabansa tah tsugunna.
"Bazan ce komaiba akan abinda kace,saidai daga ni har kai zamu buga wani wasa sai aka ya zai in ma dorani akayi akan mulki saboda inada daurin gindi koh kuma matsayina yakai nasamu.
Wasan mai sauki ne idan ka fahimata,zamu bada filin daga tsakaninmu,kowa zai fita babu wanda zai saka hannu,sannan idan har kayi nasarar yimin dukan da bazan iyah tashiba toh zan baka duk abinda ka bukata kuma za'a sallameka anan wajen,kuma babu ruwan shari'a a ciki."
Murmushin jin dadi yayi dayaji abinda tace,shikuwa wanda aka Bashi ajiyarsa kallon sameemah yayi da alamar gargadi na batasan yan iskan zamani ba fah.
Nuna masa tayi ba matsala tareda cewa,
"Karka damu babu abinda zai faru ,kawai ka bamu waje sannan kace ban yadda koh wani abune yah faru wani yah shigo ba"
"Shikenan tunda kince haka amma duk da haka zamu tsaya a kusa saboda tsaro"
Jawo musu kofar yayi tareda nufar su burgu dan yasanar musu abinda yake faruwa saboda yasan su zasu iyha yi mata magana,amma yana gama bayanin yaga kowa yah cigaba da abinda yakeyi.
Kallo akeyi tsakanin sameemah da saurayin,saurin mike wa yayi yana gyara wuyansa wanda ya bada kara kakkkk,dantsensa ya daga yana murdawa domin bata tsoro,ba karyah kam namiji ne majiyin karfi wanda zai iyha firgita duk wanda yaga dantsennasa amma babu alamar hakan daga wajen sameemah,saima kara matsawa da tayi tana bashi waje ya gama motsa jikin.
Cikin sauri yah shammaceta ya kinsa mata naushi a fuska saida ta juya,dago da fuskarta ta tayi tareda yimasa murmushi kaman babu abinda yah faru,wani naushin yakara kawo mata inda tayi saurin rike hannunsa da nata hannun,jijjiga hannunsa yayi da niyyar janyewa amma yayi yayi yakasa kwacewa,mitsitstsikawa tayi sai ji kake kururrs kurus.
Wata kara ya sake yana kallon yanda yatsuna hannusa suke kokarin tashi a aiki,amma duk da haka yah kara kawomata daya hannun,wannan karon ba iyah Yatsun ta karya ba harda tsintsiyar hannun,sannan ta kara masa da wani duka a akan gwiwarsa hakn yasa
Ya zube a gabanta akan gwiwoyinsa,
"Yanzu mai zaka ce game da aikina,koh kana da wani saurin bayanin da kake son isarwa gareni,idan kuma karaya uku bata isheka ba saina kara maka wani ,hadda wani kawo naushi da karfi kuma wai ga mace koh kunyah bakaji ma"
Saboda ranar ba wani bacin rai takeji ba dan ma taji furucin da yayi ne,gashi a aikin banza yah jawo wa kansa duka.
Dakin da aka kai su kawu shehu ta nufah,suna hada ido da shi yayi saurindauke kai,
"Zaku Zauna anan za'a dan yimuku horo kafin kowa yah tafi gidansu,wanda kuma suke a wani garin za'a saka su motar garinsu"
A wajen park din motarta suka hadu da wanda yake kula da saurayin da yah sha dukan,
"Yawwa kaje ka duba shi ayi masa dorin karayarsa zuwa gobe zamu kaishi wajen yan sanda"
"To shikenan sai gobe toh"
Daga haka ta bar office din ta nufi gida.

Tun a bakin kofar shiga gidannasu da hangi sameerah suna fira da ummaruje sai wani sunne kai takeyi itah a dole ga mai kunya,shikuwa har wanj lekata yakeyi yaan dariyah.
Tun kafin ta fito daga cikin motar ta karemusu kallo tass,duk da abin yabata mamaki amma kawai tah watsar abin aranta dan bata ga dalilin sake tunawa dashi bama.
Kashe motarta tayi kafin tazo bin ta kusa dasu zata wuce,hakan bai ishi sameerah ba ko tana tunannin bata gansu bane,?oho
"Lah sameemah kin dawo ne,ga ummaruje ku gaisa mana,tun dazu nake cemasa bari kizo ku gaisa amma yace wai na daina yimasa zancenki amma bari kiji daga bakinsa ma"
"Ahah basai najiba nima ban nemeshi ba ai,dama kece kike neman na hada ki dashi nacemiki idan kika nemeshi kuka gaisama babu abinda ya shafeni gashi kuma kun gaisa din na gani,kuci gaba da gaisawarku kawai"
Har sameemah ta saka kai zata wuce kuma sai sameerah ta sake cewa,
"Naji ummaruje yace wai dama ke kika je har gidansu wajensa koh?"
Abinne yabatawa sameemah rai dan rainin hankalin yakuma fara isarta ga kuma gajiyah da ta kwaso yau din,komawa tayi har wajen, kafin ta kankance ido ta fara cewa,
"Ke sameerah wallah in baki rabu dani ba ranki zai baci,me kike nufi shidin daya fadamiki yana tunanin wajensa najene?toh ki fadamasa duk da naga kaman wannan bashine a gabana ba tunaninsa yana wani wajen daban,wannan gangar jikice,toh idan yadawo hankalinsa kice masa ba wajensa najeba,wajen ubansa naje domin yi masa gargadi,kuma dama koda bai fita a rayuwata ba zan fitarda shi,dan ko a farcen kafar mutum din da zai iyah rayuwa dani bai kaiba,sannan ke kuma ...........hmmmm ban ma yi hakuriba ki shigo gida kisameni kawai idan banyi bacciba.
Kwafah taja babba saida sameerah taja da baya kafin ta bar wajen zuwa cikin gidan.
Yawwa shirin yayi aiki akan ta hankalina ya kwanta tunda yanzu baya ranta kaman yanda bata ransa itama yanzu,shikenan zan wataya saboda nasan nawane ni kad'ai. Fadin sameerah kenan acikin zuciyarta.



*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤32❤


Tana shiga gidan yara suka fara kallonta har da manyan,ganin kayan dayake jikinta wanda basu saba ganinta dashiba,saboda lokacin data fita da safe basu tashiba bare suga fitarta.
Duk da yanda suka kewayeta amma bata kula kowanne daga cikinsu ba,domin abu ne mai wuyah mutum yaganta tana kula wani daga cikin yaran gidan.
D'aki ta shiga ta cire kayan kafin tah kwanta,ta dad'e tana tunanin yanda rayuwa take gara mata,amma kasancewarta mace mai nuna juriya yasa babu wanda yasan halin da take ciki.
Kiran sallah akeyi amma koh a jikinta ,gashi yanayin lokaci na magriba ba'a son kwanciyah,amma baga sameemah ba kam,wanda sallar ma batayiba bare kuma ta kiyaye lokacin kwanciyah.
Fiiiiiiifiiiii kake jin feduwa daga zaure,saida ta bayyano kafin ummah tata ta rike baki,itakuwa zata so taga ranar da surayyah zatayi hankali,da kuwa tafi kowa farinciki.
Duk da kallon da umma take yi mata bai sa taji wani koh dar a ranta ba saima kokarin zama da takeyi zata nada labarin abinda yah fafu a wajen aikinnata zuwan farko.
Dakatar da itah tayi kafin tace,
"Kai mai Sunan manyah,wane zama kuma zakiyi bare bada labari,bakyajin ana ta sallah a masallataine,ki tashi kije kiyi sallah ina yaso koma mainenee zanji daga baya"
Kobare fuskar tayi tana dadare da buga kafah a kasa,sai ka ce ba itah ce ta shiga har gidan wasu tah kamo mai laifiba dazu.
Da haka dai ta wuce badan taso ba ta tafi yin sallah.
Idarwar ta keda wuyah taji wayarta taNa kara,kaman mai kiran kuwa yasan sanda zata sallame sallah.
Duba screen din tayi inda sunan burgu ya bayyana a gaban wayar ,dauka tayi tareda murmushi saboda tuna alkhairi dayake mata a kwanakinnan ba dare ba rana.
"Aslm yar ummah ya kika shiga gida lafiyah"
"Lah lafiyah kalau karamin ogah,yah gajiyar aiki"
"Tabi jiki sosai,ki mikamin godiyh a wajen umma mana"
"Zataji sosai"
Da haka suka cigaba da hirarsu suna ta wasa da dariyah,har zuwa wani lokaci.
Tun kafin kowa yah tashi sameemah yau ma tabar gidan.
Saidai yau babu wani aiki sosai saboda jiyah kusan suka kammala ayyuka da yawa daga zuwansu.
Can wajen rana tana aiki a takardu aka cemata ana sallama da itah,bada izini tayi akan a shigo,bata daga kai tah kalli wanda suka shigo din ba har sai da sukayi gyaran muryah tukunna.
Baba umaru ne da Manu da kuma baba munkaila,dayake bayau ta fara rashin mutumci ba fuskewa tayi tana kara daure fuska tareda kishingida akan kujerarta tana juyawa.
"Uhm ina jinku mai yake tafe daku?"
Baba munkaila ne ya harzuka dayake dama yah fisu zuciyah,
"Ke seematu kinci gidanku,wajen ogah daya kama mana dan uwa mukazo bakeba sannan dan rashin tarbiyyah kina kallonmu ko gaisuwa babu ko,wai tukunna ma uban me kikeyi a cikin wajennan dakuma kayan ma'aikata"
Duk fadan da yake yi bata cemasa komai ba har yayi yah gama,
"Toh malam duk naji bayaninka ,shugaba da kake nema nice shugabar wajen,batun kuma kama dan uwanku da akayi tabbas anyi haka kuma bazan sake shi ba sai yayi kwana uku kaman kowanne masu laifi da muka kama jiyah,ina fatan ka gama jin amsar tambayoyinka,idan kuma basu gamsheka ba zaka iyah tambayar daya daga cikinma'aikatan,"
Tun kafin ta rufe bakinta kuwa saiga wata yah shigo,da sauri yah duka yah gaisheta tareda mika report zai fitah,Sunan sa ta kira tareda cewa,
"Am zo zaka dan yimin wani aiki mana,wannan zaka raka zuwa dakin da muka ajiye yan kamen jiyah"
"Okay ma'am,"
"Ku bishi ku kalleshi na baku wannan alfaramar"
Dan tsabar mamaki duk cikinsu babu wanda yayi magana,sai kawai tashi da sukayi domin bin wanda tace musun.
KO a jikinta kuwa tah cigaba da abinda takeyi ,kaman dama dai duniya bata san suba.
Bayan tafiyarsu da kusan minti talatin mutane da dama zunzo karbar yan uwansu,dan office dinnata yah cika har wasu suna tsaye,duk maganr da sukeyi bata ko dago kai bare basu amsa.
Su baba umarune suma suka dawo office din bayan sunje sunga baba shehu,wanda bayansa yayi burd'i burd'i da dukan bulala,bakincikine kwance a ransu,musamman ma Manu wanda shi ubansa ne,kuma sa'anni suke da sameemah din ,buga table din yayi har saida takardun wajen suka zube,
"Ke Wacce irin halitta ce wai,tum dazu muke magana amma koh amsa mana bakiyiba,wane irin laifi ubana yayi miki kika yimasa wannan hukuncin,kuma dan zabar ke baki imani kika yimasa dukan dayafi na kowa a wajen,magana nake yi nima amatsayin bansanki tunda naga dan kin sami matsayi tun ba'a je ko ina ba kin watsar da yan uwanki,sun zama sune abin farautarki,butulu kawai wanda bata san zafin iyaye da yan uwa ba"
Cikin zafin nama sameemah tah zabga masa mari dama a tsaye yake a bakin table din ta,wanda hakaan yasashi hadiye sauran maganar dayake shirin amayarwa,tashi tayi ta tsaya lokaci guda tah sauyah daga kamannin da take,nuna shi takeyi da yatsa kafin tace,
"Kai waye da har zakazo office dina kana fadamin magana,koh dan kaga kana dan uwana?,toh baka da wannan ikon kuma bazaka samu ba,a ganinka bansan mai nakeyi ba ne,har zaaka fadamin bansan zzafin iyaye ba kasan mai kai ubannaka yayi da kake jin zafinsa"
Rintse idonta tayi tareda kokarin control din jijiyoyin dasuke kwance akan goshinta,
"Ban so fada maka abinda yah faruba har da mutanen gidan ma banso su sani ba amma shiahhsiginka yasa saina fadamaka inayso duk abinda zaka ji ma kai yah shafa,...........a kwance na ganshi akan karuwa a dakinta suna aikata masha'a ,mai kake tunanin zanyi,dadi zanji kenan,iyah fadaamka danayi nasan zaka ji zafi,amma bazaikai nawa ba tunda kai kwantance zan yi maka amma ni zahiri nagani......"
Tun kafin ta gama fada baba munkaila ya daga mata hannu,dan shima ba kdan ba abin ya bugeshi sosai.
Jan Manu sukayi suka bar office din wanda yazama tamkar gunki,kallonta ta mayar kan sauran mutanen office din wanda yawancinsu daga wanda tazo karbar danta sai mai karbar mijinta ,wata yar ta wani kuma kanwarsa koh kuma yar yayanka da sauransu,
"Ku kuma mai kuke jira da bazaku bacemin daga ni ba,babu wanda zan saki saina ganan masa azaba kaman yanda yaganawa zukatan jininsa,da kuma masu sonsa,dan tsabar baku da hankali wai su bijiremuku su tafi shashahnci amma kuzo kuna yar karamar muryah a sakesu,yaushe duniya zata cigaba a samu raguwar yan banza idan har zuciyoyi bazasu tsaya su kawar da so su hukunta masoyinsu ba.
Ban yards da irin wannan son ba ni "
Da sauri kowa yah fita daga office din babu sauran magana tunda aka ga yamda tayiwa dan gidansu ma,wasu suna cewa ta kyauta wasu kuma suna cewa zaluncine,amma duk da haka babu mai magana *wai an ce fadan dayafi karfinka saika mai da shi wasa*.
Kaman yanda tayi alkawari kuwa saida baba shehu da sauran masu laifin suka cika kwana uku kafin ta sake su,office tace akawo mata baba shehu wanda har saida ya rame a iyah kwana ukun,rigar jikinsa duk tayi wani iri,kansa a sukunye aka shigo dashi saboda kunyar da yake ji.
Wasu kaya na maza yadi ta wullah masa tareda nuna masa bandakinta na office din,
"Ka Shiga nan ka yi wanka akwai ruwa sannan ka sanja kayan jikinka"
Ba uhm ba uhm uhm,sanna babu musu yah dauki kayan yah shiga bandakin.
Ya dan dsde da alamun gasa jikinsa kayeji kafin yah fito.
Abinci tah bashi mai rai da lafiyah yah ci yah koshi,tukunna tace,
"Ina fatan kaga yanda ta kasance koh?,idan har kuna cin kasa ku kiyayi tah shuri,yanzu ba da bane an sauya tsarin kungiyar nan,sauran ma nayi musu gargadi,idan har kuka kuskura nasake kama wani a wannaa wajen ba ma iyah nan ba,toh ba iyah bulala zanyiba,wallahi kawu shehu dandakeka zanyi yanda akeyiwa Akuyah,ai ka tara y'ay'a da sun isheka,toh idan baka kama kanka ba zaka mutu babu mazakutah,ni nan ni zan rabaka da itah,idan kaji kayiwa kanka,yanzu idan ka shirya muje na kaika gida,sai a gyara hali kuma".
Shidai har ta gama abinda zatayi bai ce komai ba har ta fita a office din yabi bayanta shima.
Mota tashiga suka tafi,duk da lokacin tashi ba yyiba amma tabar aikin a wajen mataimakinta kawai.
Suna shiga gidan kowa kallo yah bisu dashi,shikuwa baba shehu kofarsu yazo zai shiga,inna larai ce tayi tsallae ta tare bakin kofar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login