Showing 60001 words to 62773 words out of 62773 words

Chapter 21 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4451

saboda masu kawo kayan zainab sun iso,kowa sai san barka yake sakawa ganin akwatinan ta har guda uku.
Wata kawar zainab dince wacce suke zaune a dakinsu tace,
"Gaskiya zeeey kinyi farin jini a wajen yunusa kuma yana sonki,ji fah har akwati guda uku aka mikk"
"Hmm dama an fadamiki so dan karami yake min ai komai yah mallaka ma zai iyah kashemin ga ............."
Katsewa tayi da maganar suka leka waje da gudu jin wata gudar wanda tafi tah farko,
Zare ido sukayi ganin yanda aka kawo akwati har guda shida kuma ainihin designer.
"Kutt wannan duk kayan sameerah ne,tabb to a aiko a auren farko bata samu rabin na zainab ba ma,amma ji akwatinan ta"
Ihu da tsllen sameerah suka jiyo a bayansu da alama itama ta ga kayan da aka kawo gidannasu a matsayin nata.
Haka aka gama hidimar kawowa kayan aka gama kowa yah watse.
Ita kuwa sameemah dama ba ta gidan bare tasan mai akeyi dan da gangan tah tsiri aikin patrol na dare a hanyar masu cin kasuwa dan kawai kar tah dawo gidan,aikuwa ba itah ta dawo gidanba sai shabiyun dare.
Tayi mamaki ganin har sannan su sameerah basuyi bacciba sai tadi sukeyi kaman ba darene yayiba,haushine ya isheta ganin dukkansu babu wamda yayi bacci gashi tana bujatar hutu.
Sameerah ce takallesu cikin ji da kai,harda fada da karfi saboda sameemah da batasan mai yah faruba itama da ji me ake cewa,
"Ai ko yanzu na cire tuta a tarihin gidan gandu,dan tunda ake auren yan mata a gidannan ba'a taba kawo irin kayama ba,har akwati guda shida kuma masu tsada"
Haushine yakama zainab dan duk da uwar su daya amma ba karamin kishine da haushi yah turnuketa ba ganin yamda kayan yar uwar tata ya kere nata.
"Toh nidai anga kayana saikuma muka wane kaya gobe tsoho zai kawo ,shin zai taka rawa ko kuma karyar ce kawai"
Salma tanajinta amma bata ce komaiba saima murmushi kawai da tayi da alamun zan baku mamaki ni kadai na san abinda na tanada.
Duk zancen da suke babu wanda yayi gigin saka sameemah acikin zancen dam tunda kowa yaga yanda sameerah duk da rashin mutuncinta take kaffah kaffah da itah kowa ma fita harakar ta bare yimata abinda ba daidai ba.
Washagari da yamma dadai lokacin da aka kawo kayan su sameerah itama salma aka kawo nata,saidai nata yaci uban nasu sameerah,dan akwati shidan itama aka kawo amma kuma hadda wata jaka ta takalma dackuma jakakkuna,banda kuma uban kudin da aka hado dashi a cikin takrda,kofar kawu shehu babu abinda kakeji sai tashin guda da kuma hayaniya.
Tunda ganin kayan bakin sameerah ya mutu tah daina cewa nata yafi yawa,wanda hakan yabawa salma damar cewa,
"Toh yamzu mai farin jini kayan waye yafi na wani kenan?"
"Eh naji idan kayanki yafi yawa ma amma aikin banzane tunda tsoho zaki aura kuma bai kai dai saurayi ba koh?"
"Eh naji tsoho zan aurah,amma ki sani babu boka babu malam da kissata na kamashi a hannu,ke kuma fah saida aka hada dana gindin tsamiyah tukunna,saboda baza'a iyah ba.
Fada sukayi tayi har saida aka rikesu tukunna suka daina.

Kwanaki sun matso na auren su sameerah,dan dama abinda aka sakawa rana toh fah lallai sai yazo,ko ina na gidan shirye shiye akeyi dan an kula auren na manyam mutanene,babu yadda yan uwan su inna hajara basuyi da sameemah ba amma fur tace koh tsefe kai ma bazatayi a watan ba bare ace na Niki tayi,haka dole suka kyaleta,kowa yana shirin bikii ita kuwa tana tafiyah wajen aikinta.
Ana sauran kwana uku daurin aure ta dawo daga aiki cikim kayanta na damara,dan ranar koh dan karamin hijab dimma bata saba,daga itah sai hular aikim kawai.
A bakin kofar gidan suka hadu da sameer wanda shigowarsa kenan garin,wani aiki aka turoshi yankin toh yah gama shiyasa yah zo idan aka daura aure sai yah wuce,dan dama yah fadawa shugabansa.
Kallon kallo sukayi da itah ta dauke kan ta tana shirin wucewa cikin gidan,
"Ke sameemah zonan"
Tsayawa tayi kaman bazata zoba sai kuma ta taho ta tsaya a gabansa tareda cewa,
"Gani"
"Kina Ganina amma kika saka kai kika wuce koh,wai yaushe zakiyi hankaline kam iye,su inna Rabi(kanwar inna hajara),sunce sunyimiki magana akan kiyi dan shiga irin ta mata saboda yanayin biki amma kika cemusu bazakiyi ba,sannan baba yace dukkanku kowa tah fitar da miji,amma ke kikace bazakiyi aureba,so kike a jikaki a sha,yanzu fadamin wanne Kika fitar a cikin samarinki"
"Ni yah sameer banda saurayi,kuma batun kwalliya indai kainane toh nace banaso dolene,kuma aure ai ba wajibi bane mutum yana iyah cewa bazayyi ba,dan haka karabu dani karka saka daga zuwanka mufara fada da kai akan abinda bai kai ya kawoba"
Tsayawa yayi sororo yana kallonta da mamakin abinda ta fada duk da ba yau yafara jin tijararta ta ba.
"Ke yamzu sameemah abinda kike kinga yana dacewa,kinsan dai bazan ji dadi ganin ki haka ba koh,kalli aikin da kikeyi fah,babu wanda yasani sai gainki sukayi a ciki,kuma dam tsabar ke kin iyah tarar aradu da ka wai kece mai hukunta kawu shehu dan yayi laifi,kina tunanin sunji dadin abinda kikayi ne duk da basu fadamikiba"
"Toh suzo su rama masa mana,ko kuma su turoshi ya rama idan zai iyah koh .......,......."
Tun kafin ta gama surutun sameer yayi buge mata baki da hannunsa yana cewa,
"Rashin kunyarki shiyake hadaki da mutane,kawunna ki da iyayenki kike cewa suzo su rama?"
Saurin rufe bakin tayi tana hade rai itah a dole taji haushi,shikuwa bai kulada yanayin dake ba sai wucewa da yayi yah tafi masallaci jin ana kiran sallah.
Sauke hannunta tayi a wajen tana kallom dan jinin dayake hannunta yana konewa kaman ruwa akan karfe mai zafi,wanda dama dalilin dayasa tah rufe wajen kennan.
Shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ko kallon wanda suka tsura mata ido bata yiba.
*** *** ***
Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA....................SAMEEMAH&.................πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,kujirani zuwa gobe inshaallah,wannan wajen daga kasan ster duk shortcut ne..πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ.


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:πŸ“ž *07038339244*


❀❀SADY-SAKHNACEH❀❀

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❀❀By sadi-sakhana❀❀


Wattpad username:SAKHNA03


❀37❀


Tun wayewar gari na ranar da za'a daura aure kowa yana ta shiri,su sameerah sai rankwada kai akeyi za'a yi aure.
Karfe takwas na rana bakin kofar gida yah fara cika da mutane masu daurin aure.
Yau sameemah bata tashi da safeba saboda rashin bacci jiyah da batayiba saboda yanayin surutu na gidan,dan duk matan da'akayi aurensu nagari da ba na gari ba dukkansu sunzo,wanka tayi kafin tah dauko kayan aikinta zata saka,inna rabi ce tah ganta aikuwa ta hada mata kwaredede,
"Yanzu diyar nan mai kike shirin yi haka?,za'a yi aure a gidanku amma ke kina kokarin fita wannan shegen aikinnaki,toh ko namijima yau kam bazaije ko ina ba".
Hakadai tah rinka yimata fada har saida aka hada da sameer tukunna kafin ta ajiye kayan.
Amma kayan anko kam na daurin aure kin sakaawa tayi,bare kuma lalle da kitso.
Baba umaru yah sha farar shadda sai sheki takeyi ga kuma hula ya kafa,duk inda yazaga murmushi kawai yakeyi kaman gonar auduga.
Motocin su umaruje ne suka fara shigowa kofar gidan da abokannansu,can kuma saiga na alhaji bala ma shida abokansa su alhaji Sama'ila,ummaruje bai tashi mamaki ba sai da yaji abinda mai shela yake fada na daurin auren,baki yasake jin wanda yah auri salma,sai a sannan ya tabbatar ba iya wajen daurin aurensa na ubannasa yazo,shima nasa aurenne yakawoshi ashe.........
Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA.................allah basu zaman lafiyha.
Har bayan an gama daurin auren mutane har sun fara tafiyah saiga kira daga wajen uban amare biyu wato wato baba umaru kan cewar yana kara gayyaar wani sabon daurin auren na y'ay'an sa. Dawowa aka farayi angwaye harda ma abokan angon da kuma yan uwansu,su alhaji bala sai washe baki sukeyi kaman bai san tashin hankalin dayake jiransa a gidaba.
Mamakine yakama mutanen gidan kan cewar wane aure za'a daurah bayan kuma angama,sannan nawa kuma wanda ba'asan dashiba sai yanzu?.
Surutun da'ake a cikin gidanne yatsayah cak,yayinda kwanon dayake hannun sameemah yah fadi a kasa ta koma kaman gunki wanda bashida digo rai a cikinsa sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata a waje daga bakin mai shelar:
Toh jama'a ga wani aurem ma wanda yazo a bazata saidai muyi fatan Allah yasa a samu zaman lafiyah tsakanin amrayah SAMEEMAH dakuma angonta SAMEER.
Kowa ka kalli fuskarsa a cikin gidannan yana cikin firgici saboda abinda yah ji,yam uwan inna hajarane basu ce komai ba dan kaman dama sunsan abinda yake faruwa musamman ma inna rabi.
Ba ga iyah cikin gidanba hatta mutanen dasuke waje saida suka shiga cikin rudu akan abinda yake faruwa.
Shikuwa sameer sunkuyar da gansa kawai yayi dan ji yake kaman kunnuwansa basu jiyo masa dadai ba na auren da ya jiyo sunan sa mahaifinsa yah daura masa da yar kanwarsa kwayah daya tall wacce yake da itah,kuma yake tunanin jininsu yah kusa fiye da kowa a gidan.
Su burgune suka kamashi tareda shiga dashi cikin kidan dan koh kafarsa baya motsawa sosai,banda numfashi babu abinda yake fitarwa da kyar,shidinma barazanar karewa yake a makogaransa,babu abinda yake sakawa a ransa sai tambaya guda dayah.
"Tsakanin nida sameemah shin wanene wanda ba dan gidan gandu ba kenan?"
Gangar jikintane gameda tunanintah suka tsayar da itah a da'irah guda daya,tareda hanata damar sake motsawa tun bayan lokacin dataji BAK'IN SAK'ON,dayah jiyarci cikin dodon kunnwanta,dan ji takeyi da zasuyi arba da manzon sakonnan da sai ta raba kan sa da gangar jikinsa nan take batareda da nadama koh danasaniba.
Idanuwanta ne kawai suka samu karfin gwiwar bijirewa sakon da kwakwalwarta suke basu na su tashi suma a aiki,saidai suna iyha kokarinsu naganin suna dakkomata hoton mutanen dasuke kallonta da ido a zare kaman itah ce wacce ta isar da sakon.
Tafi dakika sittin a wajen bata san inda kanta yakeba,dan ta rasa ma mai yahanata barin wannan duniyah a yanzu mai cike da zallan rudani,
Itama tambaya tayiwa kanta cewa,
"Tsakanin mu wanene wanda ba ummah na ce haifeshi ba, NI KOH SHI???."
Saida tasamu tah yiwa kanta wannan tambayar kafin komai na haske a idonta yadauke ya barta da bakin duhu mai cike da zullumi da rudani.
Ganin tah fadi ragwaf a wajenne bayan sandarewarta na tsawon awa guda yasa akayi kanta tareda daukarta zuwa dakin baba umaru,dan shine kadai dakim da babu kowa a cikinsa a lokacin.
Haka aka cigaba da biki saidai ba kaman da ba,kowa kuzarinsa ya ragu sannan kuma yana dauke da tambaya idam za'a amsa masa amma kowa yasan babu wanda zai zauna yayi masa bayani a lokacin.
Dare yanayi aka zo daukar amare domim kaisu gidan aurensu,kawacce tasha kwalliya dadai yamda jikinta zai iyah dauka.
A wajen daukar amaryah iyaye sunzo daukar salma yayinda su kuma y'ay'a suka zo daukar sameerah,dukkansu gida dayah aka kaisu saidai kowacce da part dinta.
Part din salma a cikin gidane yana kallon na hajiyha mairo,yayinda na sameerah kuma yakewani bangare daban,dan sai an shiga wata kofah ma tukunna,sannan kuma za'a iyah fita ta ainihin get a kofar sameerah iyah karamar kofah ce tah hada ta cikin Gidan.
Tum kafin a kawo salma da sameerah bayan daurin aure wata mata ta shiga dakin hajiyah mairo babu klwa sai su kadai,ta zayyane musu duk wani abu dayake faruwa,kama daga alakar salma sameerah har zuwa yanda rayuwar gidannasu take.
Numfasawa hajiyah mairo tayi kafin kankamce ido tana cewa,
"Lallai wato abin hakane koh,sun auri dana saboda su mallakeshi sannan kuma sun auri mijina saboda nima su gajeni,to kuwa hakan bazai yiyuba dole saina dau mataki da kuma fansa,wato dukkansu a siri sukayi musu bada son ransu suka auresu ba,ni nan ina nan zaune gahotar bansa mai ake cikiba,tabbna ai dole ma na dau mataki"
A can Gidan surukan zainab kuwa wani daki aka kaita guda dayah sai dan wani waje na bandaki,hakanma inna laraba sai surutu takeyi wai an mata giinin bulo da bulo an sakata sauran matam y'ay'an ta da kuma itah kanta suna giinin kasa............hmmm toh fah.

A rigingine yake yana kallon rufin dakin,dan tunda aka gama daurin aurennan aikinsa kenan koh magana mai karfi bayayi sai dauriyah kawai irin na mazajen sojoji,shi da yake zancen ana gama daurin aure zai tafi sai gashi har ana shirin kwana uku da aure amma har yanzu bai tafiba,bashida aiki sai tunani da neman mafita wanda har yanzu ya gaza samowa amsar ma,babu abinda yake ji aransa sai tausayinsu daga shi har sameemah wanda tun ranar yau tana cikin kwana na uku kenna amma koh mosti batayi ba .
Manjone yashigo dakin tareda tsugunnawa a gaban sameer din,karakto da fuskarsa yayi yana kallon manjon.
"Yanzu sameer kana ganin wanannan rayuwar zata kai ka,inaga mafitah shine kaje ka samu baba yah fitar dakai daga cikin zullumin daka ke ciki"
Dan murmushi sameer yayi wanda daga gani na yakene kafin yace,
"Ni bansan ma mai zanyiba a halin yanzu,nakasa samun mafita"
"Dama bakaine zaka samu mafitaba kamata yayi kaje kasamu baban"
Kimanin kwana uku da daurin auren,zuwa lokacin mutum duk san sa da jin abinda yake faruwa na auren su sameer sai da yah hakura yah tafi badan yasoba.
******* *********
Wata irin jan iska tayi mai karfin gaske,saida ta gama gauraye duk ilahirin jikinta kafin tah fesar da itah ta karfi kaman tayar trailer tah fashe.wani mikewa tayi daga kan gadon tana karewa dakim kallo kaman mai son tuno wani abu daya shige mata duhu.
Wani irin huci tayi kwayar idonta tah koma tamkar jini na yan sakanni kafin suka koma yamda suke.
Inuwar mutum ta gani yana shigowa dakim wamda hakan yasata kawar da kanta,dan a halin yanzu bata bukatar kowacce irin halittace tah kusanci inda take,bata dago taga waye ba har gama abinda yah ke shima yah fice,da alamar mai shigowar yah fuskanci yanayin da take ciki na rashin son ganin kowa a tareda itah.
Tun safe tah tashi har wajen la'asar tana zaune bata motsaba,inna rabi ce ta shigo dauke da kwanon abinci a hannunta,
"Yar nan yakamata kici abinci,yau fah kwananki uku bakici komaiba"
Har ta gama surutuntah sameemah batace ko juyo da fuskarta ba bare ta kalleta.
Matsala tayi da niyyar dafa kafadarta,aikuwa da sauri ta ja da baya ganin yanda sameemah ta buga mata wani arnen kallo mai kamada na karashiyah.
Saurin barin dakin tayi jikinta har rawa yakeyi dan tsoro.

Baba umaru ne yashigo dakim tareda cewa,
"Sameemah yakamata zuwa yamzu ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddara,dan shima kansa yayannaki yaui tawakkali ba kaman keba,kashi har kwana uku sunyi da auren ki ya,kamta akaiki dakinki kema kaman sauran yan uwanki"
"Aure ,dakina, yayana, tawakkali,toh duk nabisu da azababben gudu babu wando tsirara dan malafar ubansu,kuma kaima idan baka fita a harkata ba inban hadaka da duk munafukan da akwai hannun su akan danyen aikin dakuka mini ba na saka ku a daki daya na kona ku ba,harda shikansa dan banzan da kake kira da mijinnawa,duk abinda kuka aikata ma dole zaku amayar dashi yai basai gobeba,koda bazai amayuba billahillazi saikun amayo da hanjin da gurbatacciyar garkiyar lamarin yah taba.............."


TAMMAT BIHAMDULLAH!!

Ananne na kawo karshe litaffin gidan gandu,sannan duk wata cakwakiyah da za'ayi a cikin gidan gandu takare,yanzu sai a gidajen yan matan gidan, littafin zai cigaba..................Tambayoyinku dazasu samu damar amsuwa a littafi na gaba sune:

#shin wace irin hargitsatstsiyar gaskiyah ce da su baba umaru suka boye akan rayuwar su sameemah?

#wace irin rayuwa su sameemah zasuyi da sameer har ma saleemah a gida dayah?

#shin saleemah zata yadda ta zauna da sameemah kuwa bayan tana ganin ubantane yake da ikon komai ,gashi bata yi tsammanin kishiyah a rayuwarta ba barekuma irin kishiyah kaman sameemah?

Da farko ma sameemah zata yadda da auren da'aka daura mata kuwa?

#wace irin cakwakiyah za'a buga a gidan alhaji bala da amaryarsa salma sannan da surukarsa sameerah,ga kuma hajiyah mairo?

#ina kuma rayuwar gidan zainab da surikarta inna laraba kuma?

#yah rayuwar sameemah a barikin sojoji na porthacourt?

#ina kuma halittarta wanda har yanzu ba'asan menene ba?

******~~~~~~~*********~~~~~~

DUK WANNAN AMSOSHIN TAMBAYOYINNAKU SAI A CIKIN LITTAFIN...........

*WASA FARIN GIRKI* *(cigaban gidan gandu)*

Wanda zaizo nan da sabuwar shekara akan farashin Naira dari biyu kacal (200).

..........AFUWAN........

Nasan wasu zasuga na ce musu littafin kyautane amma kuma na shiga na kudi ta cikinsa.
To dan Allah kuyi hakuri wallahi ina bukatar kudin dazan dunga saka data ne,saboda kudina duk ya kare a saka data na littafin gidan gandu,dan haka nasaka dari biyune domin samun kudin data,idan kuma baka fajimceni ba to shikennan.

Domin neman karin bayani ku tuntubeni a numaber wayata kamar haka:
09035784150.

Ina yiwa kowa fatan alkhairi sannan kuma ina godiyah Sosai ga duk wanda suka bani goyon baya a littafinnan tah hanyar bani support da ku nuna soyayyar su ga littafin.
Uwa uba kuma wanda suka taka rawar gani wajen yimin cover.
ABIN YABO BOOKSHOP &KING AIIMAR GRAPHIC.
Ina godiyah sosai.

..........JINJINA ........

Ga mahaifiyata allah yakara yiwa rayuwa albarka.

.........GODIYA......
Ga daukaci masoyana ina godiyah sosai,Allah yah biyawa kowa bukatarsa tah alkhairi. Musamman yan group din WhatsApp kun fi taka rawar gani wajen comment,sannan Facebook,sai wattpad sai kuma telegram.
Dukkanku ina godiyah.

Wasallalallahu ala muhammadin wa ala ali Muhammadin,wasallama tasliman kasserah.




Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login