Showing 33001 words to 36000 words out of 62773 words

Chapter 12 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4433

karisa wata goman,tafiyah zanyi kawai"
Kallona suke da mamaki,musamman yanda na hade rai sun san da gaske nake,tsallakesu nayi na wuce,har nayi nisa na juyo na kallesu,
"Kowa yah me yah kwanta kafin gone mu tafi,zanje wani waje sai na dawo"
Ina fita ta fence ban same KO ina ba sai gidan DPO,dayake police quarter da wuta,haske ya garwaye ko ina,wata sanda na fara cikin kwarewa kamar mage na shiga cikin gidan.
A falo na tsaya babu kowa a wajen amma ina jin hayaniyarsu shida matarsa a cikin daki,wasu kuloli na gani a akan dining table,ai kuwa idona yayimin tozali da wasu kaji a ciki sun sha farfesu,zama nayi na fara ci hankali kwance kaman ina cikin gidanmu.
Ban kai ga cinyewa ba DPO yah fito daga cin shida matarsa suna min kallon mamaki,nuna ni yakeyi da yatsa yana kokarin fito da waya a aljihunsa,dagatar dashi nayi tah hanyar daukar wuka na yanka hannuna na hagun,
Jikinsa ne yah fara karkarwa ganin yanda wajen yake komawa yanda yake,komawa nayi na zauna bayan na maida wukar inda take,
"Karka daga hankali nka ka dagawa matarka ma,naga kaman kudin sabin aurene,koda ka kira wannan karnikannaka (yan sanda) babu abinda zasuyimin,dan haka ka saurareni da kyau,..........inaso gobe idan kaje aiki,abinda zaka farayi shine bugamin takardar sallama nida yarana guda goma,idan kuma ka barshi sai gobe,toh wallahi daga kai har matarka a duk fadin Nigeria banga mai hanani juya rayuwarku zuwa yanda bakwa tsammaniba,hmmmmmm kai karma kayi mana"
"Zanyi wallahi zanyi,ni daman daga ganinki nasan ba mutum bace ke"
"Nidai na fadamaka"har na fita daga gidan na dawo nace wa matar tasa,
"Abincin ki yayi dadi sosai,kiyi hakuri na raguza miki miji,nagode sosai"
Da safe kuwa tun kafin na karya saiga yan sanda guda biyu sunzo kirana,tashi nayi na bisu muka tafi office din.
Tun daga shigowa ta da muka hada ido da DPO,yah dauke fuskarsa da sauri,nima bance komai ba har yah mikomin takarda ta,sunayen dana bashine su "burgu"naga an buga tasu sallamr ma.
A ranar bamu kwana ba a garin abuja sai garinmu kuma gidan mu wato "GIDAN GANDU".
Tun daga shigowata garin nake ganin sanji da dama,saboda tsawon shekarata goma bana garin sai gashi na dawo. Da wata yarinya muka fara haduwa a bakin kofah,bansanta ba amma daga gani yar gidan inna larai ce saboda yanda suke kama sosai,itam kallona take da mamaki kafin ta ruga kofarsu da sauri,mutanen gidanne suka fara fitowa ciki harda inna ramatu,wanda ta dan fara manyanta saboda shekaru.
"Kuttt sameemah dama kina raye baki mutuba?".
"Ga shi kuwa kin ganni,inso kike na mutu sai ki kasheni yanzu ma lokaci ai bai kuremikiba"
Kowa shiru yayi yana bina da mamaki,gashi na wuce duka bare su dakeni su huce,dakin mahaifiyata na tafi wanda nasan shine yan matan gidan suke,matsar da kayan wata nayi a wajen danaga yafimin kafin na ajiye jakata a wajen.
Tunda nafita bani na dawoba sai dare dauke da kayan amfani,wanda na siyo da kudina,su burgune suka shigomin dasu dayake shima dan garinne,biyar ne a cikinsu ba yan garinmu ba kawai.
Sannu a sannu na fara kafa kungiyata harda su iliyah wanda suma suka zama yan iskan kansu,mika wuyah sukayi ga kungiyata saboda basu manta ceton rayuwarsu danayi ba shekara goma da suka wuce,hakanne yasa yan kungiyata suke bani daraja,saboda babu wanda na jawoshi da kudi saidai sadaukarwar daanyi masa ko kuma wani taimako.

**** ****** *****""
DAWOWA CIKIN LABARI.

Kowa tsayawa yayi yana kallon sameemah,ciki harda wanda yawu yah bushe a bakinsa saboda mamaki.
Ta shi sameemah tayi daga kan kujerar da take tana kade rigarta,
"Toh yanzu kunji labarina,kuma saura naji zancen a bakin wani,ban yadda wani ya fitar zancennanba,sannan munyi magana da alhaji labiru zan hau kan kujerar shigabar vigilantee ta garinnan,dukkanku za'a debeku aiki,kuma banason shashanci ku kiyaye,ku kuma (tafada tana nuna yaran da suka ganta lokacin da sukayi fada da yaron bubu jini da kuma dukkan yarannasa),tunda kun ji labarina toh kun dawo yan kungiyar nan,daku za'a fara aikin vigilantee,musamman matan kune masu kamomin wani idan yah shiga Gidan su,daga wani satin za'a fara koyar da horo wanda zan dauki nauyi a gidan horona dayake cikin jeji"
Dukkansu amsawa sukayi da cewar,
"Mun ji shugaba kuma mun mika wuyah"
"Yadai fi muku,sauran naji wani yayi abinda ban saka shiba kuma"
"Babu wanda zayyi ma ranki ya dade"
Motarta ta nufa tana kakkada key,saida ta zauna na dan wani lokaci kafin ta ja motar tabar wajen,sai kurar tashinta me kawai yah saura.
Wata bakar motace tah faka a gaban gidan gandun,baka mai sheki amma ba wacce sameemah ta iyo kwacenta a wajen alhaji bala bace.
Saleemah ceh takalli major sameer ganin ya faka a wani waje kaman gwalalo,shima kallonta yayi amma baice komai ba,
"Honey naga ka tsaya koh motar ce ta baci kai?"
"Ahah ba motace tah baci ba anzo gidanne"
"Gida kuma honey wannan fah kaman ba gida bane,baka ganin yanda yaje ne"
"Saleemah ya fah isheki haka,tun kafin mu taho kike wani bata rai,miye nufinki,bazaki zo gidanmu ba kenan,saidai ni nayi ta zuwa gidanku,toh bazai yiyu ba wannan shine gidan mu kuma sai munyi sati guda kafin mu tafi,dan haka kima shirya zaman cikin gidannan"
Hawayene yafara zubowa a cikin idonta tana wani cuna baki,
"Nikam bazan iyah zama a cikin gidannan ba,mai laifin ka kaimu hotel sai mu dunga zuwa,gaskiya d'ana zayyi gudawa a cikin gidannan"
"Eh Kat d'anki yayi gudawa ko?,toh ni na mutu mana kafin ki ganni,kuma sai yanzu kike son dan"
"Eh KO ma menene ni bazan zauna ba"
Ganin abinnata bazai kareba ne yasa yah fito daga cikin motar yah barta itah kadai tana ta mita da shagwabarta,tsayawa tayi da mitar da take ganin wata mota mai irin tasu bak'a ta shawo hanyar layin da suke,saleemah ceh ta fito daga cikin motar tareda tsayawa a kusa da sameer din,tambayar sa take saboda tsabar gulma tana cinta,
"Honey dama akwai irin wannan motar acikin garinnan ne,tunda muka shigo ko karamar mota ban ganiba amma ji wannan motar kuma a hanyar gidanannan?"
"Kin isheni da surutu ki tsaya ki gani mana"
A bangaren sameemah kuwa tunda ta shawo hanyar gidannasu tah kulada motar kofar gidan ,kuma ta gane sarai suwaye a cikin motar,tana zuwa fakawa tayi a gefensu tareda fitowa daga cikin motar tana feduwa.
Dukkansu kallon ta sukayi da Mamaki harda saleemah wanda bata santa ba,ina kuma ga uwar gayyah yayannata.
Tahowa tayi tah gabansu zata wuce sameer din yayi saurin shan gabanta tareda cewa,
"Ke ubanwa ya baki wannan motar haka"
"Uban wani ne yabani itah mana"
"Akan wane dalilin,wane irin aiki kike masa haka"
"Akan dalilin na bashi budurcina ne,batun aikin danake masa kuma,irin aikin da matarka take maka duk dare shi nake yi masa nima,har yah bani itah"
............,.😲😲😲😲


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤21❤

Baki yasake yana bin sameemah da kallon mamaki,wanda ta shige gidan tana feduwa da karfi.
Sun fi minti goma a,tsaye kafin yayi karfin halin jan hannun saleema suka shiga gidan.
Tun daga bakin kofa ake tah muranar isowarsu,yayinda saleemah take tah makewa a jikin sameer kaman taga kashi,lura da hakan da yayi ne yasa shi tureta daga jikinsa yana aika mata kallon tah shiga hankalinta,itama wayancewa tayi tana aika musu murmushin.
Cikin kankanin lokaci aka shimfida musu tabarma a tsakar gidan suna gaisawa,shima baba umaru yana gida saboda yasan da zuwan dannasa bare kuma su baba shehu kodan gulmama ai,kowa shiru yayi da zancen sa ganin shirga shirgan karnuka sun shigo gidan suna d'aga jela,saleemah ceh tayi tsalle ta haye kan sameer tana kikkifta ido,dan dama kaman akan kaya haka take ji,wucewa sukayi tareda nufar dakin da sameemah take ciki,sameer ne yayi karfin halin cewa,
"Karnukan fah,kuma a cikin gida haka"
"Uhmmmm"
Shinen abinda kowa yace tareda kawar da zancen.Sameemah ceh tah fito daga dakinsu daga itah sai wata vest da dogon wando,ledar nama ce a hannun ta karnukan sai binta sukeyi har suka je wajen kejinsu.
Ganin koh kallon inda suke sameemah batayi bane bare kuma gaisuwa tah hada su,yasa Baaba umaru cewa,
"Keh sameemah baki ga dan uwanki da matarsa bane,kika tsaya baki zo kun gaisaba"
"Mun gaisa mana dashi a waje,wace gaisuwar kuma yakeson kara ji daga wannan"
Sameer ne ya mike tsaye cikin zuciyah irinta sojoji yace,
"Ke anya kuwa hankalinki daya dazu kin yimin rashin kunyah yanzu kuma kina yiwa harda yan gida,ana miki magana hankalinki yana kan karnuka,wai tukunnama menene na ajiye karnuka a cikin gida,in kinyi wasa yanzu zansa a fita dasu kuma bazaki kara ganinsu ba"
Inna larai ce tah tashi cikin jin dadi tace,
"Yawwa gwanda da kazo ko zakayi maganin ta,wlh ta addabemu matuka"
Kowa fara fadan albarkacin bakinsa yayi.
Duk abinda suke sameemah bata koh motsaba ,saida kowa yagama fadan abinda yake bakinsa kafin ta tafa hannunta raffffff,tsitt kakeji kaman anyi ruwa an dauke,takawa take a hankali har ta kai gaban sameer numfashin su yana bugar na juna,
"Wace rashin kinyar na maka,fadamin itah naji,amsar dana baka dazu bayan ka tambayenine rashin kunya ko kuma dan naki zuwa na gaisheku kaida matarka,wanne ne daga ciki?,sannan kuma da kake cewa zaka batar da karnukana bazan sake ganinsu ba koh?,dan allah bismillah kada ka fasa,kaima kuwa kai kadai zaka koma inda ka fito batareda danka da matarka ba,dan nima saina batar dasu"
Kowa zaro ido yayi tareda shan jinin jikinsa jin abinda sameemah tace,musamman ma saleemah da taji ana cewa za'a batar da itah,cikin kankanin lokaci tah tsure.
Kallon kallo aka fara tsakanin sameemah da sameer,shi yana mata kallon Mamakin yanda ta zama ita kuma tana masa kallon zaka san koni wacece.
Katse kallon da suke ita da yannata tayi sanadiyyar karar da wayar ta tayi a cikin aljihun wandonta,saida ta danyi yar karamar tsuka kafin tah daga kiran tana hade girar kasa da sama,
"Kai miyene wai kuka dameni,naga yanzunnan na dawo gida ko hutawa banyiba"
Dayake wayar tana handsfree kanajin abinda ake fada a daya bangaren,
"Ogah Ranki ya Dade wallahi duk bayanin da mukayi masa akan kece kika turomu yaki bada hadin kai,yanzu haka muna wajensa ma"
"Okay inason information gameda komai nasa nan da dare,sannan ina sabin yan kungiya suke,dafatan kun fara nuna musu aiki kaman yanda nace"
"Eh shugaba,matan sun bi su uban dawa wajen campaign din alhaji Sama'ila,sauran kuma har yanzu jikinsu a mace yake tunda sukaga abinda kikayiwa ogahnsu wanda yake asibiti"
"Karka dam u dasu zasu ware ,ka kawo min information kafin dare ina jiranka"
"Shikenan ogah allah yaja da ranki"
Sauke wayar tayi tareda yah mutsa fuska ganin yanayin reaction din fuskar su ya nuna duk sunji abinda aka fada a cikin wayar.
Barin wajen tayi ,ko a jikinta maganar da tayi.
Su sameerah ne suka dauki kayan saleemah wanda suke kira da anty saleemah zuwa dakinsu,binsu takeyi a baya kaman anyi mata dole,su kuwa sai shige mata sukeyi ganin yanda tasha kaya na girma da alfarma.
Shikuwa sameer dakin mazan gidan yah tafi da kayansa.yah ajiye jakarsa kenan yana kallon dakin saiga manjo yah shigo yana kirga kudi a hannunsa,sai wuriwuri yake da ido da alama baya son wani yah ganshi,sameer ne ya katseshi daga diridirin dayake ta hanyar cewa,
"Ah MUSA dama kana nan ,na shigo ban ganka ba tun dazu"
"Lah wa nake gani kaman sameer,shege kace kaine dai nake gani,wallahi daka ganni nan wani abun arzikine yasameni,da banso na fadamaka ba amma tunda kaima babban yayantane,toh bari a yi zancen dakai"
"Menene yah faru Musa(manjo)?"
"Ai in fadamaka abokina ne sule maye yake son seemah jar wuyah kaman ya maida ta cikinsa,toh shine nace yah kawo nairah dubu talatin casss ba ragi ba kari na bashi itah,ni zan shige masa a daura aure,kagansu nan ya bani su cifff,ai ni kam yau kakata ta yanke saka,irin wannan kudi haka inba sata nayi ba har saina kai ga filo da kasa ban sami kamarsu ba"
Mamakine yakama sameer jin abinda manjo yake fada,
"Amma Musa Kaman naji kace na neman aurenta ne,kuma yanda naga fuskarka kaman so kake ka rike kudin,kuma kana tunanin yanda nima iyah yau na hadu da itah zata bari ka aurarta a haka kuwa?"
"Kaga tsaya sameer shiyasa fah dama nake tah buyah kar a ganni,toh gashi kaima kana cikin yan bakin cikin ashe,kudi babu mai hanani cinsu ,batun kuma karta yarda ai dolenta ma ,ina yayanta ta kawomin iyah shege"
Daga haka sameer bai sake cewa komai ba sai jijjiga kai kawai da yayi.
A dakin su sameemah kuwa,iyah sameerah ce sai zainab a zaune suna ta zubawa saleemah labari,wani ta amsa wani ta gwalesu ko kuma ta tayi shiru,amma da yake basuda zuciyah kkh a jikinsu,suna cikin hirar ne salma ta shigo itama tana wani yatsina fuska dan kana ganinta kasan haushin saleemah takeji ,koh miye dalilinta oho.
Sameerah ce ta washe baki bayan saleemah tah yabawa zainaba wata magana ta rashin mutumci,
"Amma anty saleemah gaskiya kina burgeni dazan samu dama ai da nabiku porthacourt koba komai zan tayaki ayyuka acan,tunda a nan din na rasa miji kinga acan din watakil saina samu mai dan romo nima,nasan yah sameer din ma bazai hanaba"
Saida saleemah tayi mata kallon mamaki kafin tace,
"Lallai kam ki bimu,waya ce miki ina bujatar yar aiki,nida nake sanja yan aiki sau kusan goma ma a sati daya,sannan sashe guda aka warewa masu yimin hidima,kinga kuwa bana bukatar yar aiki,sannan dakike cewa yaynki bazai hanaba,dama bashi keda ikon wannan ba nice nan,sai wanda na yadda kafin yah zauna a cikin gida"
Dariyah sameerah tayi cikin jin kunyar maganar ta da kuma irin amsar da aka bata,saidai bata da ikon nuna cewa taji haushi.
Duk maganar dasuke sameemah tana jinsu dan shigowarta kenan daga waje.
Tsayawa tayi akan katifarta ganin jaka da kuma gyalen saleemah akan gadonnata,daukarsu tayi ta wurgawa saleemah akan fuskarta kafin ta zauna a bakin katifar.
Binta sukayi da kallo ganin abinda tayiwa saleeman,sameerah ce tayi karfin halin cewa,
"Kefah sameemah bakida mutunci,yanzu a gaban bakon ma saikin nuna halinki,toh akan gadonnaki zata kwanta in yaso saiki kwana a shimfidin wata,haka inna ramatu tace"
"Saboda ubanta ne yasiyamin katifar kome,ko kuma itah inna ramatun ce ta saya mun iye?"
Cikin bacin rai saleemah ta fara yiwa sameemah magana,
"Ke na kula tun sanda na shigo garinnan bakida mutunci kina ji da tashen rashin mutunci,toh bari kiji na fadamiki ke baki kai ki ganni ba ina dan dalilin nazo gidanku ba,bare har kiyi misayar miyau dani,ke kinsa inda nake rayuwa kuwa da har kike takama da wata katifa"
"Hmm lallai kina bukatar na koya miki hankali,da farko uban me yakawoki gidan namu da har naganki,koh nice na take Naje inda kike,sannan idan harkin isa yanda kikace da sai kice bazaki zo garin ba mana,kodai kina tsoron mijinnaki ne kar ya sakeki?,toh ki bude kunnenki kiji,daga ke har shi a tafin hannuna kuke,ke inkinyi wasa saina shiga har Gidan ubannaki na saka masa wuka a wuyah ,kuma idan kina musu ki bani lokaci da kuma address ki gani"
Tsayawa tayi da maganar ta furzar da iska idonta yayi ja,dan daga gani dama a cikin fushi take,wiwi ta,dakko a cikin kwarkwaro ta banka mata wuta ta fara zuga tana fesarwa ta hanci da baki.
Karkade tokar tayi kafin ta zawo wata leda da ta shigo da itah,kaza ce a ciki taji jar suyah da dakuma lemo mai sanyi.
Saida taci tayi nak kafin tah koma kan katifar ta zauna tana daddanna waya. Duk abinda take suna kallonta amma babu wanda yayi tunanin magana saboda abin yafi karfinsu sosai.
Kirane ya shigo wayar tata inda ta daga tana cewa,
"Eh yah kawomin information din dazu sannan nagani sosai,kah saurari abinda zan fadamaka,inaso ku satomin kanwarsa a gida ku kaimin itah gidan horo ,amma ban yadda kuyi mata komai ba ,har abinci ku bata kafin naje wajenta,ba lallai naje da wuri ba saboda zanje karbar kudina a wajen alhaji Sama'ila gobe"
Gyara shimfidin tayi taja bargo sai bacci,abinda ta iyah kenan.
Sameerah ceh ta kalli su Salma lokacin da sameemah taja numfashi bacci na farko tace,
"Tabbbb yanzu ku gani,toh ni ko a tarihi ban taba ganin mai irin halin Sameemah wlh ba karamin tsoro take baniba"
Basuja hirar da yawa ba suma suka kwanta dan kar tsautsayi yasa ta jisu su shiga uku.
Fitowa tayi daga dakinnasu cikin shiri zata je wani waje,babu kowa a kofar tasu saboda yanayin lokaci daya tafi sosai.
Baba umarune ya tsayar da itah har takai bakin kofa ,juyowa tayi kafin kuma yam hankalin suka ce ta dawo da baya,
"Ina kwana "shine kawai abinda tace daga nan kuma tayi shiru,
"Lafiyah kalau saidai ba dan gaisuwa na tsayar dake ba,wani waje zakuje dake da yayanki da kuma iyalansa,saiki shiryah tunda ba yau zaku dawoba"
"Wani waje kuma ina kenan"
"Dangin mahaifiyar ki ko shima bazaki jeba ne"
"Ahah zanje amma ba yanzu ba,akwai abinda nake idan na gama saina je daga baya ai nasan garin sosai,kuma nafison tafiyah ni kadai"
"Hungo naki(yafada yana bata yatsu biyar),dasu zaku tafi kuma a mota daya saura kuma naji kince bazaki jeba kumadu,kije maza ki dauko kayanki koh guda biyu kizo ku tafi"
Daga ido tayi tana kallon sameer wanda yake ta zabga mata harara shikadai,itama ramawa tayi tareda mutstsika baki kafin kuma tah cije lebe alamar zasu kwala.
Komawa dakin tayi da dauko wani dan karamin trolly,na irin tafiyah kwana biyu,ficewa tayi zuwa wajen ko sake kallon baba umaru batayi ba,tun a hanya take hango saleemah a gaban motar sameer din,itama itah take kallo ido cikin ido.

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤22❤


Budewa motar tayi ta shiga tareda maida kofar da karfi kaman zata cireta,itah dai saleemah bata kuta ba,dan abinda ya isheta yah isheta na zuwa kauyen da za'ayi na su inna hajara,tana ganin an kawota lungunan cikin zariyah a she ga kauye can za'aje.
Shigowa yayi cikin motar suka fara tafiyha a cikin motah,sunyi tafiyah mai nisa amma babu wanda yace wani abu,saleemah ce ma ta kalli sameer da alamun shagwaba tace,
"Honey fushi kake da ni?"
"Haka nace miki,abinda kike yi ne banaso bawai fushi dakeba,bai kamata ki dunga kushe gidanmu a gabana ba"
"Toh na DA in a"
Takaicine ya isheta tana bayan mota,ga an katse mata aikinta na rana guda an hada ta da wayannan shashsashun waje daya a cikin motah,ganin abin yayi waya ne yasata daka wata uwar tsuka kafin ta fuske ta kalli window,dukkansu juyiwa sukayi suna kallonta amma babu dama sanin mai ya sameta tunda ba magana zata musu ba.
Tin daga bakin kofar shiga garin yara suke ta shafa motar saboda yanayin kauyene sosai.
Wani gida suka shiga wanda aka zagayeshi da dangar kara,tun daga cikin gidan suke jiyo murnar yara

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login