Showing 27001 words to 30000 words out of 62773 words
saceni kowa zai dauka na tafi babban birni neman kudi kaman yanda na fadamusu,hawsyene ya fito a idona dansn tuna da ummah na,lallai mutuwa mai yanke kauna ce,nasan da tana.nan da yanzu ina gefenta a kwance tana yimin tatsuniya,saidai wani bangare na zuciyah ta yana cewa,gwanda da bata nan,domin da tana nan da hankalinta sai ya tashi matuka da haka na gama tunanina har bacci ya dauke ni.
Kwanci tashi shakuwa ta shiga tsakanin mu ba iyah yan dakinmu ba hatta bangaren maza babu wanda bai sanniba musamman ma shaheedah wadda kullum tare muke da itah,dan ni da itah har wiwi mike sha wanda mazan suke bamu suna siyah a wajen amintattun mutanensu masu gadi,saidai duk abinda mukeyi babu wanda yasani hatta yan dakinmu ma basu saniba,gashi babu inda na fita naje amma zallar rashin mutunci koh shaheedah bazata gayaminba duk da ita ta dade a cikin yan iska amma saida na nuna mata iyakarta wajen rashin tsoro da kuma aikata abinda nayi niyyah,saboda ni bayan rashin mutuncin danakeyi har jinake ana,zugani a cikin kaina idan kuma nakiyi sainaji kaman ana son azabtar dani,gashi duk sanda mukayi fada da wani sainaji babu abinda nakeso sai shan jininsa,tun kafin aje ko ina na kula cewa wannan abinda zuciyata takeso yana da matukar hatsari,shiyasa idan hakan ta faru saina shiga bandaki na rufe,saina huce kafin na dawo,yanzu kuma in ba wiwi na zukaba banajin dadai kwata kwata.
Muna cikin tsaka da shuka tsiyamu nida shaheedah kwatsam saiga iyayenta sunzo tafiyah da itah,a da lokacin baya kafin zuwana babu abinda takeso sai tabar wajen amma yanzu bata kaunar abinda zai rabata da wajen,dan yanzu ta gane tsiyar danake jan ragama anayi a cikin wajen koh inda take ba'a irinta.
Tun safe take kuka nake rarrashinta akan wata rana zamu hadu,sai can wajen rana kafin motar kawunta yazo,wata takarda ta mikomin da number a jiki,kafin tace.
"Ni zan tafi amma ki tabbatar kin kirani duk lokacin da kika dawo,zanyi kokarin na gyara number kuma ina jiran kiranki duk ranar da kika fito,bazan taba mantawa dakeba,yimata alama nayi da karta damu,dan ni a yamzu tunda na rabu da mahaifiyata to kowa ma zan iyah rabuwa dashi ko waye shi kuwa.
Bayan naga kulewar motarsu ne na kade rigata tareda shigewa dakinmu ko a jikina ,wasan ma yanzu aka fara bugawa.
Toh fahh.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤17❤
Ina Shiga naji su nairah sunyi tsit da alama gulmata ma sukeyi,dan kwanannan naga wuyahnsu nema yake ya isa yanka,kallon kowaccensu nakeyi cikin kankanin lokaci suka shiga taitayinsu,shigewa nayi bandaki nayi wanka kafin na fito na kwanta sannan ana ta kiran sallah,gyara filona nayi na kwanta,khairah na kalla wadda take saitina a zaune itama daga idon tayi tana kallona tareda cewa ,
"Menene anty sameemah?"
Murmushin jin dadi nayi yanda ta kiranin kafin nace,
"Idan muallim yace ina nake a wajen sallah kuce bana sallah ne"
"Ahh amma fah yau kwananki uku da yin tsarki,kuma muce masa bakya sallah a cikin mutane"
"To Karku fada ku hadu dani,ina ruwanan dan kowa yaji bana sallah iye,dolene said nayi sallah ni ya takuramin dan yaci sa'a babu wanda nake tsoro duk duniyah sama dashi da wallahi saina koya masa hankali,kuma saura karku fada ku gani,hmmm"
Komawa nayi na kwanta,dan wannan shine period dina na farko a duniyah,tinda yanzu naji a kwai excuse din rashin sallah ai kuma shikenan ta zo gidan sauki kuma,na samu abin cewa har sai yaganoni da Kansa.
Komawa nayi na kwanta su kuma suka fita suna tura baki jin irin aikan danayi musu,gashi dole said dun fada ,dan yanzu ba karamin tsorona suke jiba,tun lokacin dana danna kan khairah a cikin ruwan toilet na ploshing dan ta zageni suka mungun tsorona kaman mala'ika,gashi kuma shaheedah bata nan dama itace take taremusu hukuncina idan suka shoga gonata.
Ban ta shi a bacci ba sai wajen magriba,ina tashi na dauki abincina na ci,nasake wani wankan kafin kuma nafara shirye shiryen bin barauniyar hanya zuwa cell din maza,ban samu su hairah a dakinba sun tafi sallah dan haka har na bar dakin basu dawoba,
Wajen babu nisa da inda muke dan haka dama sun san da zuwana kawai kofah suka budemin na shige,zama nayi a tsakar dakin ina kallon kareem wanda zaikai shekara sha biyar a duniyah,yarone amma shegen kansa ne,murdaddiyar wiwi yah mikomin na karba ina busawa,take wani sanyi yah ziyarci zuciyata naji duk duniyah babu wanda yafi burgeni sama dashi,hira aka shiga yi ta labarin duniyah da kuma yanayin yanda kasar take.
Bani na dawo dakinmu ba said sha biyun dare,aikuwa ina dab da shiga dakin na hadu da nannyn mu mai kulada wajen,saurin juyar da fuskata nayi ina kallon kasa,
"Ke seemah me kike a wajen"
Shine abinda tace da Mamakin ganina a wannan lokacin,dayake nidin shigaba ce Cikin sauri nace mata cikina ne yah baci shine na fito domin nayi tusa a waje kar na damu su hairah,alamar kin kyauta tamin tareda yimin addu'a allah yah kara shiryamu,ni kuwa a raina nace,aida zanyi tusa dari wallahi duk sai sun sheka dan banga shegiyar dazan fito waje dan kartaji tusa ba,saidai ta mutu a kaita da safe.
Bugo kofar nayi bayan nashiga wanda yasa dukkan su suka tashi a razane suna kallona,nima kallonsu nayi batare da nayi musu magana ba na koma na kwanta.
Bayan shekara daya da tafiyar shaheedah mukayi sauka a makarantar mu'allim nafi kowa kokari da kuma kaifin hadda,kuma dama duk wanda yafi kowa ilimi toh za'a tambayi wanda yake zaune dasu shaidar halinsa idan an ga yah shiryu sai a sallameshi.
Da sassafe muka shiryah domin zuwa wajen walimar,cikin kaya iri daya,na maza daban na mata daban,mu'allim na zaune akan kujera duk sanda muka hada ido said yayimin Murmushi,nikuwa kallonsa kawai nake,wai fah yanace danna shiryune na ke bada haddar,baisan carbinsa nake tsoro ba,dan duk sanda ya dakeni dashi kwana nake ina jin azaba,kaman ana kwaramin wuta,shiyasa nake binsa kawai a rabu lafiyah.
Tunanin na katse lokacin dana ji ankira sunana,SAMEEMAH UMAR,tashi nayi zuwa wajen karatun na fara.
Da karfi nake cikin kwarewa,saboda burina shine su sallameni a wajen nima naje naga me akeyi a cikin garin.
Kabbara naji yah dauka lokacin dana gama wajen da aka bani,da ni watace dadi zanji amma maimakon haka saima gani nake bata lokacin su sukeyi.
Da haka aka gama walimar da kuma karatun kowa yah kama gabansa,da niyyar gobe za'a ji wanda yayi na daya a bashi kyautukansa da kuma sallamarsa zuwa gidansu.
Bamu muka dawoba sai tab ana kiran magriba,bayan munci abinci mun yi komaine,na kira,sunan su khairah ina gyara zama akan katifa ta,dukkan su nutsuwa sukayi,dan sunsan hankalinsu nake bukata a lokacin,
"Yawwa inaso na gargadeku,idan aka tambayeku ni wacece naji wata tayi zancen abinda nake aikatawa,har kukasa aka ce bazan tafiba hmmmmmm,basai na fadaba kawai"
Khairah ce ta cuna baki kafin tace,
"Toh dama ko kin hanamu ai shaidar karyah zamu bayar a kanki dan ki tafi muma mu huta"
Hairah ce tayi saurin gwabe bakinta tareda yimata kallon ta shiga hankalinta,
Nikuwa tunda naji abinda tace nasan banida matsala tanan bangaren sai kuma a ji da gobe kuma.
Da sassafe na tashi yau saboda zumudi mai zai faru,cikin sauri muka shiryah domin zuwa jin sakamako.
Bayan anyi taro kowa yayi shiru yana sauraran mai gabatarwa can naji sunana yana amsa kuwwa kaman a cikin mafarki,dagaske fah ni aka kira wai na lashe gasar karatun qur'ani da kuma litattafan addini,tab lallai sunyi kuskure,tsinke tunanin nayi na tashi ina tafiyha cikin nutsuwa har naje gaban mu'allim,Murmushi yayi min tareda mikamin kyautata yana cewa,
"Hakika nay I miki murna sameemah ke yarinyace mai hazaka da kuma dagewa,allah yah albarkaci rayuwarki sannan ina muki albishir da cewa a yau an sallameki daga gidan horo na yara zakije wajen danginki ki cigaba da rayuwa kaman ko wane da mai yanci"
Banyi murnar karatun ba da kuma addu'a abinda na sani shine fita waje domin neman shaheedah shine kawai a raina,amma a fuskata murmushi kawai nayi tareda nuna masa na ji dadi sosai.
Haka taro yah Kare kowa yah karbi kyautukansa mukuma nida sauran guda ukun da aka sallamemu kaya masu kyau suka bamu ba uniform dinmu ba.
Tun kafin na shigo dakinmu su nanny sun hada min kayana uniform kuma sun dauke abinsu,su hairah nagani a,zaune ko kallon inda nake basuyiba,nima ban kallesuba,lokacin danazo fitane nace musu sai wataran,su ma toh suka bini dashi, na kama hanyata nayi hanyar waje inda za'a daukeni a mota.
Bayan mungama sallama da kowa muka dauki hanyar tafiya,sauran mazane suna ta murna zasu je gida. Daya daga cikinsu aka sauke sai shima dayan da akayi tafiya mai nisa dashi aka saukeshi.
Ni kuwa tafiya muke tun suna hakuri har suka gaji sukayi magana ganin nayi shiru bana da alamar nuna musu hanyar gidanmu,
"Keh sameemah a ina zamu saukeki ne?"
"A gidan dayake farkon hanyar dazaku shiga"
Toh kawai sukace,a bakin wani gida mai baki get suka saukeni,kayana na dauka na shige cikin gidan kaina tsaye ina daga musu hannu,saida naga wucewarsu da wasu mintina kafin nafito daga cikin gidan ina lellekawa ko wani yah ganni a cikin gidan,saidai cikin sa'a babu wanda yaganni harna fito na tari taxi.
A cikin taxi dinne na rokeshi yabani aran wayarsa, da farko bai niyyar baniba amma dana marairaicemasa akan gidanmu zan kira sai yah bani.
Number wayar shaheedah na saka,cikin sa'a kuwa sai ta dauka,da farko tayi Mamakin ganina saidai ban barta ta cikani da surutuba na tambayeta address din gidansu,tana fadamin in fadawa driver da haka har muka isa kofar gidansu kafin nabashi kudinsa ina yimasa Godiya.
Da murna ta rungumeni tana tsalle kaman zata cinyeni,cikin gidan muka shiga gashi mai kyau saboda babanta yana da kudi sosai.
Mahaifiyar tace ta tarbeni cikin mutunci da ta fadamata ni kawarta ce ta makaranta.
Satina daya a gidan su shaheedah komai yana tafiyah normal amma kuma matsalar daya shine yayanta yah takuramin waishi sona yakeyi ,saidai abinka da dan iska ina ganinsa nasan jirgi daya ne mudashi amma da alama ita shaheedah bata fahimci hakan ba,kuma duk matsalar daga wajen mamarsu ne domin itah ce take sangartasu batareda sanin mahaifinsu ba.
Yau ma a zaune muke a falo nida shaheedah mamarsu batanan ta tafi shopping,sai shaheedah ta shiga wanka nikuma ina zaune da waya a hannuna,banzata na kawai naji hannu yana bin cinyata ina daga ido naga yah shaheed ne,abinne yaban mamaki ganin abinnasa har ya kai haka. Matsawa nayi gefe batareda nace komaiba,shima sake matsowa yayi yana wani bina da mayen kallo,fuskarsa ya matso domin yah sumbaceni bansan lokacin dana zuba masa wani gigitaccen mari ba akan fuskarsa,wanda yayi dadai da shigowar mahaifiyar su ta dawo daga kasuwa.
Zubar da kayan siyayyar tayi tana bina da kallon mamaki,dan a duniya babu abinda takeso yah yayannata guda biyu ,shiyasa ta tsani jinin abinda zai tabasu ko miyeshi.
Lokacin da aka kai shaheedah gidan horo ma itace tayi kutun kutun aka dauko mata yar ta.
Matsowa tayi inda nake har sannan idonta bai dauke a kaina ba,ganin haka ne yasa shaheed yayi saurin cewa,
"Ummeeh dama ban fadamikiba wai fa dan kawai ina yimata wa'azine saboda itace take hurewa shaheedah kunne lokacin da suna gidan horo"
"Gidan horo kuma,amma naga shaheedah tacemin kawarta ce daga makaranta"
"Karyane it's ce shugabar tantirai a gidan"
Kallon su kawai nake batareda nace komai ba,dan ko mamaki banyiba tunda hakan ba bakon abu bane a wajena.
Bayan sun gama zancen sune ummeeh ta kalleni tareda cewa na bar mata gidanta ,daga kai kawai nayi alamar naji,juyawa nayi domin komawa dakin shaheedah domin tattaro kayana,kicibis mukayi ta idah a bakin kofa da alama taji duk abinda mukace,bance mata komai ba sai rabewa danayi na wuce dakin ina tattara kayana.
Rike hannuna tayi tana jijjiga kai alamar karna tafi,dafa kafadarta nayi ina cewa,
"Ahah shaheedah dole na tafi amma ba rabuwar kenan ba,nima tunda akayi haka yanzu nafison nayi zaman kaina ba nawani ba"
"Amma sameemah.........."
"Karkice komai dan kinsan ba sauraronki zanyi ba"
"Shikenan amma zan baki number BINLAD,saiki nemeshi nasan zai baki inada zaki zauna dan suna neman irinki,nima ina zuwa cikin satinnan dan akwai wani patrol da zasu je"
"Shikenan hakan yayi ni bari na tafi saikin shigo,kuma sannan ki fadawa yayanki kar ya bari na hadu dashi a hanya ko kadan,ke kinsan mai zai faru dan haka ki sanar dashi"
"Zan fadamasa ogah seemah"
Bansami kowa a farlon ba da alama ummeeh da shige dakinta shikuma gogan yah fita,shaheedah ce ke biye a bayana fuskarta tayi narai narai da alama bata son tafiyahta,saidai ni kuma a nawa bangaren tunda naga abinda yah faru naji banason zama a karkashin wani ba iyah gidannasu ba ma,address din wajen na karba da kuma numaber wayarsa kafin na tari taxi.
Bayan na shiga ne na juya naga shaheedah tana matse Kwallah,hakika nima banso mu rabuba saboda ita kadaice kawa mace dana tava yi a rayuwata,amma ni nafita juriyah badai mutum yaga raunina ba kama,ta inda muka banbanta da itah kenan,duk da ta iyah tsiyah amma tanada rauni gakuma shagwaba.ni kuwa wa yaga dutsi.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤18❤
Tafiyah mukeyi a cikin birnin har muka shiga wajen da babu gidaje sosai sai jeji,ga kuma garin yayi duhu sosai da alama cikin kowanne lokaci ruwa zai iyah kwacewa.
Driver ne yakalleni ganin muna ta shiga cikin jeji har munzo inda babu wani gida amma bance mun iso ba,
"Gaskiya kiyi hakuri amma daganan zan ajiyeki duniyah babu yarda karnaje ke mai cutarwa ce ki cutar dani,kiyi hakuri bazan sake yin gaba ba gashi kuma hadiri ya hadu inason komawa wajen iyalai na ni.............."
"Yah is a haka zaka iyah saukeni,banason dogon zance"
Bayyi musu ba kuwa yah fara fitomin da kayana daga cikin motarsa saida yagama kafin na bashi kudinsa yayi gaba.
Samun wani wajen kiran waya nayi na zauna saboda wayata babu charge.
Tun daga nesa nake ganin hasken fitilar har yah fara isowa inda nake,ban matsa daga inda nake ba bare na tashi saidai kallon mai tahowa danake duk da bansan wayeba.
Lokacin da suka iso wajena ne nakula ashe mazane guda uku sun saka rain coat bakake,zagayeni sukayi da bindiga kafin daya,daga cikinsu yasa,
"Ke wacece,sannan kuma waya aikoki"
"Bai shafeka da sanin ni wacece ba,saboda ba matsalarka bace"
Kallon na raina musu hankali suka faramin saboda jin amsar dana basu,
"Dolene ki amsa tambaya a wajen ogah binlad,ku daureta yanzunnan,sannan ku rufemata ido,sai iyayenta sun kawo kudi tukun"
Tashi nayi daga zaunen danake ina kallon su,kayana na dauka na rike kafin nace,
"Wanene wanda zan hau mashin din nasa,yazo mu tafi kar dare yayi ga kuma ruwan sai karuwa yakeyi"
Nafada ina kallon hadarin a sama,ko ban kalli fuskokinsu ba amma yanda nayi magana nasan sunyi Mamakin action dinane,hakan a jinina yake bawa mutane mamaki da halina.
Dukkansu tada mashin dinsu sukayi,ni kuwa saida naje gaban ogannasu mai barazanar kafin na dale mashin dinsa ina gyara zaman jakata.
Kara nausawa cikin dajin muka kara yi,munyi tafiyah mai nisa kafin muka iso wani gida da aka yi katangarsa da karfe,masu tsaron bakin wajenne suka bude mana,dukkansu kowa yana rike da manyan bindiga a rataye,kana ganin su kaga manyan yan iska.
A bakin wani babban d'aki muka tsaya,wanda yafi dukkan dakunan wajen girma,shiga sukayi nima nabi Bayan su.
Wani farin balarabene a zaune yasha askin tankwal sai uban gemu kaman zayyi magana,bakar jallabiyace a jikinsa ga idonsa yasha kwalli,a takaice dai jan wuyane kawai.
Sallama yamin na amsa kafin yace,
"Sunana Binlad"
"Nasani basai ka fadaminba"
Yayi Mamakin yanda nayi masa magana babu tsoro amma kuma sai yah basar,
"Baki fadamin sunanki ba"
"Kaima baka tambaya ba"
"Miye sunanki karamar yarinya"
"Sunana sameemah "
"Yayi barkanki da zuwa"
"Toh"
Daga nan na katse maganar tamu ta hanyar zuyawa ina kallon wajen,shima bai sake cewa komai ba sai kareni da kallo kawai dayake wanda inajin yanayin kallonsa a jikina,maganar sa na jiyo yana cewa,
Akwai dokoki a wajennan sannan kuma saboda ke macece akwai matsayin dazaki tsaya bakomai zamu sakaki ba kar shirinmu yah wargaje",
juyowa nayi Nima ina kallonsa kafin nace,
"Ka barni a tsaye haka ake taryar sabon member ,toh ina jin bacci kuma sannan nagaji dayawa,inayaso koma mai za'a cemin sai gobe kuma"
Daga haka na kalli wanda mukazo tare ina tambayar sa inda zan zauna,binlad ne yayi masa alamar ya kaini kawai inayso sai goben.
Da safe kuwa wata tsohuwa ta shigo hannunta dauke da tea da kuma gurasa,karba nayi na ajiye kafin naje gyara jikina tukunna,saida na shiryah na karyah tukun naji dan aike na shaidamin kiran Ogah,wani dan gyale nasaka, a kaina bayan dogon wandon dayake jikina da kuma riga iyah gwiwa.
Ya u ma kaman jiya yana zaune saidai yasaka rawani,samun kujera nayi na zauna tun baice na zaunaba,
"Ke Baki iyah gaisuwa bane"
"Na iyah amma banayi,kayi hakuri"
"Keee,..........."
"Kana Bata lokacin ka,bayan na fada maka ra'ayina,muwuce wannan shafin kawai,kafadamin menene abinda zanyi kawai"
Buga bencin dake gabansa yayi idonsa yayi jaa,da alama furucina yah bata masa rai,
"Tabbas ke baki sanniba kina bukatar a horar dake,inaso yanzunnan,samad kuyi mata bulala hamsin da dorina"
Matsowa sukayi da niyyar kama hannayena ciki harda wata mata jikinta a murde,dakatar dasu nayi kafin na wuce inda mai bulalar yake,kwanciyah nayi akan table din hankalina kwance.
Saida naji yah irga hamsin tukunna na tashi daga wajen na dawo na zauna akan kujerar danake zaune dazu,
"Yanzu shugaba zaka iyah cigaba da bayaninka tunda hankalinka ya kwanta ka horani din"
Bude baki yayi yana kallona,duk da yana kokarin boyewa amma alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa,komawa yayi yah zauna tareda cewa,
"Zaki fara koyon sand'a ko wuce waje batareda wani yah gankiba,sannan nagaba kuma harbi da bindiga saikuma koyon fada"
"Saikuma me?"
"Banson musu ki koyi wannan din tukunna"
"Shikenan and gama ogah"
Tun daga ranar na fara koyon harbi da kuma fada babi dare babu rana,nikadaice mai koyon saboda babu sabon shiga a lokacin shiyasa masu horon ni kadai suke yiwa.
Cikin sati daya na kware wajen harbin bindiga da kuma fada,hatta wanda suke koyamindin sai sunyi dagaske su yi abinda zan aiwatar,labarine ya isa kunnen ogah binlad na himmata da kuma rashin tsoro.
Saboda yanayin nasarar dana taka a cikin wata daya sunana yah fito a cikin wanda zasu je fashi,da farko su Samad sunyi bakin ciki ganin yanda nake taka matakin da saida sukayi shekaru kafin su taka,nikuwa harka ta nake ni kadai ,saidai idan aikine yasamu muke zuwa in group,shima wani lokacin Samad ya jagoranci shirin wani lokacin kuma ni,kuma duk aikin dana jagoranta ba a samun cikas,saboda koda harbi