Showing 42001 words to 45000 words out of 62773 words

Chapter 15 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4440

kenan kullum tana cikin aiki,ko an saka ta ko ba a sakata na zata tashi tayi,tunda ta dawo daga hannun sameemah kaman an sanjata haka ta zama,ummanta sai murna takeyi.
Yauma zaune hajiyah Sa'aden take bayan sun gama aiki dan d'anta dayake aiki da sojoji yau zai dawo garin,Kwallah mata kira takeyi amma babu itah babu labarinta sam,abu tun safe har wajen yamma,lokacin yayannata har ya iso yah huta,shima daya tambaya cewa akayi bata nan.
Shigowa tayi tana sanda hanyah,bata ankaraba saijin maganar mutum tayi a bayanta,
Juyawa tayi taga ashe yayantane da zaizo yau,
"Daga ina kike haka tun safe,kuma ke ba makaranta kike zuwaba,yansu surayyah kina nan da halinki na yawo da rashin kamun kai koh?"
"Iyah Gidan kawata fah naje,ni ba wajen wasu najeba yau din"
Jijjiga kai yayi kawai ya wuce shima cikin gidan,itama binsa tayi a baya har ta wuce dakinta,tanajin kowa yana fadar abinda takeyi ita kuwa tura dan kwali tayi tana bubble din chewing gum.
Sallamar yah Mahmoud ce ta fito da itah daga cikin dakin tana lekawa ta window,
"Miye kike lekoni kizo ki karba abinda kikace na baki"
Fitowa tayi kanta a sunkuye kamar wata wanda kwai yah fashe mata a ciki.
Mahmoud ne ya mikawa kaninnasa takardar tareda cewa gashi kaima kayi sign tunda kazo,
Har zai tambayi ta mecece amma Mahmoud ya hanshi,hakan yasa yah karba shima yayi sign din.
Mikawa surayyah takardar yayi kafin yace,
"Abinda kika tambayeni sati daya daya wuce ne,wanda nace miki saikinyi hankali shine kika dauki yin aiki na karyah ga ummah,ganin ban baki ba kika tafi wayo inda zan ganki koh?wato koma menene nayi din,shikenan na cika miki sharadinki,gashinan mun amince kiyi aiki da sameemah jar wuyah komai yah faru da amincewarmu"
Ba iyah surayyah ba har su ummah su da suke wajen saida sukayi Mamakin abinda yake faruwa,itah kuwa karbar takrdar tayi tareda komawa dakinta tana Murmushin jin dadi,kaman anyi mata albishir da kujerar makkah.
Uwar ce takasa hakuri tace,
"Amma mahmuda wannan wane irin danyen hujunci kayi,yarinyar da ake nema ta shiryu"
Saida yayi murmushi da alamun shi ya hango mai yah faru tukunna yace,
"Ummah karki damu babu abinda zai faru sai shiriyah,dan ina mai tabbatar miki kwananna surayyah zata shiryu a wajen seemah,dan nayi bincike nagano cewa duk yaranta yanzu ta hanasu shaye shaye da kuma aikin banza,dalilim da yasa tayi kidnap din surayyah dan na yi mata sign din takrdar neman izinine na zama shugabar yan vigilantee,kuma duk yaranta tace zata sakasu aiki,wanda zasuyimata iyah itah kadai,kaman yamda kuke ganinta ba haka takeba,tana kula da duk wanda yake karkashinta sannan yanda kikasan uwa akan yayanta haka take akan duk wanda ya yadda yah zama acikin kungiyarta,zata iyah bada ranta akansu.
Yamzu haka idan wani abu yasamu surayyah,ko bamuyi komaiba zatasan yadda zatayi ta tabbatar ta kubutar da itah,kuma ina mai tabbatar miki zata hanata yawon dare da kuma shaye shayen da take ganin tanayi,kuma dole ta daina dan dole,saboda zataji maganarta fiye da yanda takejin taku.
Kudai kuzuba idon ku gani,itah bata san yah sameemah takeba shiyasa take rawar kafar shiga kungiyarta ai,kudai ku zama yan kallo,sannan ku kwantar da hankalinku kaman kun kaitah gidan horo................mai zakuje zai faru tsakanin surayyah da seemah😂😂😂😂😂😂.


*Please wanda basayin comment sai dai thank koh liking,ku dunga yin comment mai kyau,musamman Facebook da telegram,naga yan wattpad sun dan fara dagewa.
Amma WhatsApp kune akan gama ina ji daku sosai*


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤26❤

Kwanaki sunja sameemah ana ta shiryen zama yar damara,duk wani abinda take bukata ta gama hadawa,dan yanzu koh lokacin yan gidannasu bata da shi bare kuma akai ga tsayawa ana saida dan hali.
Suma yan gidan nasu bidirin sukeyi an kawo goron tambayar auren Zainab,wannan jarabbabbeb saurayinnata da suke kaiwa dare a wake,sukuwa manyan gidan wato sameerah salma da su sameemah kaman anyimusu asiri babu wacce tayi aure har yanzu,dan gwara ma sameerah ta tabayi ta fito.
Su inna ramatu sai kafafa akeyi y'a zatayi aure,su guzuma ana zaune wato su salma.
Babu laifi yayi mata kaya masu kyau dadai karfin sa,inda aka saka bikin nan da wata biyu.
Duk abinda akeyi sameemah batasan anayi ba dan idan ta fita bata dawowa sai dare,sai shirye shiye sukeyI.
Yau ma da sassafe tah tashi kaman abin arziki akayi su wanka da shigar mutunci tafito,babu kowa a tsakar gidan dayake safiyah ce amma rana ta fito,manjo ta samu yana alwala a bakin kofarsa ko kuma nace wanke ido,hada ido sukayi koh eh bata cemasa ba haka shima bai kulata ba,yan miskilancin suna kusa.
Gidan su burgu ta fara zuwa tah daukeshi suka tafi ainihin babban office din dayake birini,dauke da takaddar da Mahmoud yayi mata sign da kuma ta Alhaji bala.
Saida ta dauki lawyer tah saboda tsaro kafin suka dauki hanyar tafiyar.
Zainab ce a zaune tana shafa kurkur a fuskarta tana wakar habaici saboda taga yayan kawu shehu mata a wajen da kuma sauran yan matan gidan,
"Lokacinki ne yayi amarya yar amana sai kize ki zauna da miji aure ibada ne............"
"Hee amaryah manya,amaryah da yin kurkur,kir ayi mai na kanti mana,kuma a wane shegen saurayin kowa yasan halinsa da bin yaran mutane"
Wata ce itama ta sake cafkewa bayan salma ta yi shiru,
"Ke ma kya fada,dan dai an rasa wani ne sai shi,in ba hakaba mai za'ayi da Uzairu a rayuwa"
"Eh haushin rashine makaho yace ido da wari,inma mai danne iyayene wata ta fito da nata mana,aurene nima zanyi na bar gidan gandu nafara girka nawa abinci wanda nakeso na barku da tuwon masara miyar lami"
"Dan ma tuwon masara kikaci kika girma ,kuma shi uwarki zata shigaba da ci har kasa ta binne idonta"
Salmace cikin yatsina fuska tace,
"Ke zainab ya isheki haka kuma,bamuson raini,a wane shegen saurayinaki naga saida nace bana sonsa kafin yah dawo wajenki,kuma shi banzan bazarane a cikin masoyana wallahi"
"Eh naji banzan bazarane shiyasa naga baki auri wannan tula tulan alhazan nakiba ai kika makale da soyayyar yah sameer har kike zagin matarsa,kuma duk jarabarki ma zaki barshi ki auri daya daga cikin tsofinnaki,dan anty saleemah ba sa'arki bace ehhe"
Cikin rashin daurewa da zancen salma tah kaiwa zainab wani uban naushi a bakinta,abinka da brush bai ishi bakinba sai jini yace yah samu wajen fita shikuwa.
Kururuwa ta hada itama ta kamata suka fara fada sai ga sameerah ta shigo da leda a hannunta da alama daga wani waje take,wajen su tayi tana rabasu tareda cewa,
"Ku hakan menene mai kuma yah faru kuke wannan kokuwar,ke salma bakiga aure zatayiba kike dukan ta a fuska?"
"Ke sameerah kema banason iskanci,auren yaci kundun ubansa,haukane auren dan zatayi ta dunga yadawa mutane magana,toh gobema ta kara saina zubar mata dukkan hakoranta,saidai inna ramatu ta akaita a saka mata na roba"
Tana gama fadan hakan ta bar dakin tana huci,sukuwa binta sukayi kawai da kallo.
Ita kuwa sameemah tun safe suke bakin kofar shugaban amma basu samu shiga ba schedule dinsu bai zoba har dare yafarayi,tun suna saka rai har suka hakura suka dawo,gashi sai wani satin su koma kuma.
In ran sameemah yayi dubu toh yah baci a wajen dan ko magana batayi sosai,haka ga gajiyah ga komai tah tuko motar suka taho.
Saida ta fara sauke barr.Kamal kafin ta sauke burgu shima a gidansu,yana mata godiyah da huta gajiyah ko kulashi batayi ba saima kara hade fuska da tayi.
Tun da ta shigo layin gidansu takejin muryar yan gidannasu gashi darene dan 9:30pm ta kusa,takaicine ya isheta tasan ba lallai ta shige Kalau na.
Ai kuwa hakance tah faru dan inna karimane da inna larai suke fada akan marar tuwo guda biyu.
Babu wanda yah kulada da itah a wajen dan manya da yara an tsatstsaya kowa wasuma hadda torchlight a hannunsu saboda su gani da kayau dayake an dauke nepa.
Baba umarune ya dawo ana tsaramasa yanda akayi,tun kafin su gama tsarawa sameemah tah fisge kwanon tuwon ta wullawa su bingo wanda suke biye da itah sunga ta shigo.
Kowa mamaki yayi tareda yin shiru amma banda inna larai dan masifah ta farayi kaman makogaranta zai fashe,
"Kinsan allah inna larai ko kiyiwa mutane shiru da darennan ko kuma na tura karennan yah ciromin mamanki na hagun idan kina bacci,kinsan sarai zan aikata yanda kofar dakinki kuwa ta baci babu sakata,dan haka saiki zaba yanzunan"
Kowa inna larai yake kallo da jin wanne zata zaba maganar sameemah,aikuwa cikin sauri tayi kofarsu tsitt kakeji kaman ruwa ya cinyeta.
Kowama dayaga hakan kofarsu ya nufa yana dariyah da tsoron inna larai,ga tsokana ga fada dakuma rashin gaskiya, aka bar filin wajen,sai gobe kuma.😂
Yanzu dakinnasu iyahsu kadaine babu zainab saboda tah koma dakin iyah mai kalwa(kakarsu da ta rasu )ana mata al'ada na aure,kaman su tsimi na tsugunne da sauransu,hakanma sai yafi musu,domin indai zasu zauna da itah da salma toh fadane zai biyo baya tsakninsu da itah,ita kuwa dama sameemah babu wanda take shiga shirginsa saidai idan ka shiga nata shirgin ku kwashi yan kallo.
Misalin karfe 12;00pm rana tayi ga kuma zafin rana saboda yanayin lokaci na rani,surayyah ce ta shigo gida da sauri sai hada gumi takeyi,babu ko sallama bare ta kula mutanen gidan ta dau buta tayi bandaki da gudu,saida ta fito ta sha ruwa kafin ta zube a tabarma a tsakar gidan nasu wanda take karkashin bishiyah.
Saida ta gama hakin da fifita kafin ummansu ta tambayeta,
"Mai Sunan uwata ya na ganki haka kaman wanda aka zefoki daga sama"
"Hmm ai bari kawai ummah,muna kan tsallaka siradi ne,da yawanmu shugaba ta saka a training kuma duk wanda bai fito da matakin nasara ba sallamarsa zatayi,gashi bata afuwa,idan tana yimana training dinannan kaman fah soja haka takeyi,gwanda ma ogah burgu yana mana da sauki.
"Ahh kikce aiki kukeyi babu kama hannun yaro"
"Hmm ni ummah kuwa anya kungiyar yan daba ce kuwa?"
"Me kika gani?"
"Naga an Hana shaye shaye,an hana yawon dare sannan ba'a yin shagali,kullum ana cikin training da kuma fita aiki,ni gaskiya gani nakeyi kaman ba kungiyar dana ke jin labari bace"
Dariyah ce ta kama ummah amma haka ta kunsheta kar surayyah ta gane,kwata kwata satinta daya tana zuwa wajen sameemah amma har ta fara sanjawa,babu shegen wayon club,babu shigar rashin mutumnci sannan babu wannan baccin safen har zuwa azahar.
"Uhm ummah bani abinci naci,nayi wanka dan in anjima shugaba tana neman mu akwai abinda za'ayi,naji tace wai zata sakamu a wajen koyon computer wasu kuma a turasu wajen training na police da yan sojoji,nikam kungiyar tamu har ta fara bani tsoro,yanzu ko samarina nagani tsoton kulani sukeyi wai tunda na shiga kungiyar seemah"
Narai narai tayi da ido kaman zatayi kuka,amma tunanin abinda zai faru idan bata koma ba yasa ta mike tana wani lankwashewa kaman wanda ta fito daga labor room,itadai ummah bata kara cewa komaiba sai dariyah da takeyi ciki ciki tareda fadin madallah.
Aikuwa la'asar nayi tun kafin tagama cin abinci saiga kiran burgu,da sauri ta tura sauran lomar da cokali ta mike zuwatt,badan tsoron burgu ba saidan tsoron wanda tasa burgu ya kirasu.
Da gudu gudu tayiwa ummah bye bey ta fita,sai a wajema ta karisa saka gyalen a wuyanta.
Tun da sameemah ta dawo gida sanda su inna larai suke fada da daddarenan take ta bacci har bayan azahar,su kansu yan gidan su zata ta mike ta can zuwa makwancinta na gaskiya,wanda da hakan yah faru da sunfi kowa farin ciki,saidai kash!!! Daidai wani lokaci ta bude idonta tareda yin wata mika irin ta wanda babu abinda yah dameshi.
Fitowa tayi tsakar gidan tana rarraba idon neman yaro dan ya debo mata ruwa,ita wannan rashin ruwa da suke fama dashi yana ci mata tuwo a kwaryah ba kadan ba.
Dan Gidan manjo ne yah yazo wucewa zai fita waje,sai sameemah ta kirashi,da sauri yah taho wanda koh uwarsa ce albarka,saboda yasan bata wasa dasu ko kadan.
Bayan ya tafi debo ruwanne tah koma dakin jin wayarta tana ta ringing,gashi dama bata saka volume kadan,kuma da saninta takeyin hakan.
Ganin number ummaruje saida tayi jimm kafin ta dauka,
"Allah ya taimaki gimbiya sameemah,yah gida da kuma jin dadi"
"Lafiyah kalau yah hajiya"
"Lafiyar ta Kalau,dama inaso naji in kina gida yau zan zo miki mu gaisa baby"
"Kaman wane lokaci"
"Kowane lokaci kika saka duk dayane"
"Ka Bari sai anjima zanyi wani aikine"
Ajiye wayar tayi tah shiga wanka domin zuwa wajen yarannata.
Bayan surayyah tayi wannan gudunne gashi bata samu abin hawa da wuri ba hantar cikinta sai kadawa takeyi kaman zata fito waje,abin haushi kuma har saida ta yi kusan wata awar kafin sameemah ta zefo hancin motarta wajen cikin takama.
Dukkansu tashi sukayi duk da ba itah ta saka masu dokar hakanba su suka sakawa kansu.
Ajiyar zuciyah ta sake bayan taga dukkansu hankalinsu ya dan koma jikinsu.
"Yawwa nasan kowannenku Yaga yanda ake saka ku aiki sosai,wasun ku sunsan dalili wasu kuma basu sani ba,toh kaman dai yanda kuka sani,daga rana i ta yau,wato wani satin ina so sunan kunhiyar nan ya tashi daga marar lasisi zuwa mai lasisi,wato zan mayar ta zuwa karkashin gamnati ta hanyar shiga kungiyar vigilantee.
Duk abinda zamuyi zai zama babu mai kaimu kara bare kuma ya dau mataki,walau tah hanya mai sauki koh ta hanya marar sauki ina so mu saki ruwan rashin mutunci a garinnan ban daukeba har cikin gidan gandu domin kawo sauyi a cikin garianan sannan kuma muma mu kafa namu tarihin da wanda za'a dunga tuna mu dashi"
Surayyah ce ta daga hannu tace,
"Amma shugaba muma aikin vigilantee zamu dungayi mata damu,baza'a dunga aikin daba ba kenan"
"Ke surayyah ke fah dama nakula duk da horon da aka baki har yanzu kina cin kasa,toh ki kiyayeni in dan auta kike ji nima nan itace,dan haka banson harkar lalaci duk wanda kika ganshi anan wajen walau mace koh na miji sonake ya zage dantsensa wajen nuna kwazo,banason abinda zai kawomin nakasu gameda burin danake son ai watarwa sam.


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤27❤

"Ina su Lubna da Kubrah"
Dukkansu daga hannun su sukayi dan dama duk cikin su babu wanda tayi magana amma daga ganinsu kaga mata masu kirar karfi da kuma zarrah(ina baku mantaba sune wanda suka kira sameemah lokacin da yaron buba jinI yakeson zanta cikin jeji).
"Yawwa ina so aikinku yahada da surayyah,duk wani wanda yayi Rashin mutunci yashiga dakin uwarsa toh ku nakeson ku shiga ku daukoshi sannan ku mikashi ga mazan su kawomin shi,saboda bai kamata muna gyara kuma mu bar maza su dunga shiga gidan mutane ba any how,jibi zanje mu sake zama da shugaban tsaro a cikin babban birini,idan abu yah tafi normal za'ayi bikin saka ni akan kujera,ku kuma za'a baku uniform bayan lokacin.
Kowa zai iyah tafiyah,akwai training daga karfe bakwai na safe,sauran kuma burgu ya cemin wani bai zo da wuri ba hmmm"
Ta shi tayi ta fita saboda ta gama isar da sakon da tazo isarwa dama.
Inna ramatu ce zaune a daki itah da yayanta sameerah da zainab,wanda babu wanda ya kaita rawar kai itah a dole zatayi aure,sai wani rangwada takeyi tana cuna baki,
"Yawwa ummah kikace zaki kaini wajen malaminki ta yanda zan mallakeshi kk uwarsa bata isa ta fada masa yajiba koh?"
"Hmm ke harki na ganin zan manta da wannan zancen nne,ai kwantar da hankalinki ni kaina malam shine dogarona shine dalikin dayasa na kai yanzu a wajen ubanku,da badan haka ba da yanzu nasan inda dare yamin"
Sameerah ce ta yah tsina fuska kafin tace,
"Nikam da ina baki shawara karki bi ummah wajen wannan mutumin,idan ta kama taimakone ta karbo miki basai kinje ba kawai"
Saurin katseta inna ramatu tayi tareda cewa,
"Ke sameemah banason shashancin banza,dan ubanki ba shine dalilin dsyasa kikayi auren farin ba,sannan kuma shine yabaki sa'a kika Rike bazawarinki a hannunki kinsan da haka"
"Eh ni dama bance ba shine yake bani sa'a ba ,kawai tun sanda yah turmusheni bana sha'awar komawa wajensa da dadin rai"
"Kiji sameerannan wallahi ke yar bukulu ce,kina zagewa yana baki sa'a amma ni kice bazanyi ba koh,bana san shawarar taki toh,idan ba da neman taimako ba ai mazan sai a slow"
Haka suka cigaba da zancensu har daga karshe aka yanke lokacin da za'aje wajen bokan(malami in jisu da fada).
Yauma sameemah da wuri ta tashi saboda tafiyar dazasuyi tana cikin ranta sosai.
Duk da sammakon su saida suka samu mutane a wajen sun rigasu wanda hakan ya bata mata rai sosai,akan layi suke amma hankalinta baya kan wajen kwata kwata,bata ankaraba sai jin hannun wani tayi akan bayanta wani Yana shafawa,zuyawa tayi da niyyar magana sai ta hada ido da wani saurayi ya sha askin wizaye da kuma sabullalen wando,lashe baki yakeyi yana binta da wani dan iskan kallo,
"Yadai yan mata kinaso a cigaba ne ko yah?"
Karisa juyawa tayi sosai tana kallonsa,dauke da dan iskan Murmushi,
"Eh mana ina so a cigaba amma yanzu kamata yayi ya zama layina ne,nice zanyi koh"
Wani washe baki yayi jin abinda tace tana wani kashe muryah.
Cikin lokaci kadan sameemah ta rike ta rike kaciyar sa ta cikin wando da karfi kaman zata cireta,ihu yasaka iyah karfinsa amma hakan bai sa ko motsi tayi ba,saima wani daskarewa da tayi duk kuwa da dukan da kuma kokarin zanyeta da akeyi.
Wani ne yah shiga da gudu ya fadawa shugaba abinda ake ciki,saboda yaron da ta rike dan sane,dama haka yake yi idan mata suka zo wajen neman wani abu,idan kika ki yin abinda yake so sai yasa a koreki,wai ana cewa yana da ciwon zuciyah da kuma dan dabin hankali,idan ba'a barshi yayi abinda yakesoba zuciyarsa zata buga.
Security ne suka rike hannunta ta kowanne bangare kafin cikin saka karfi suka cire hannunta daga inda ta rike,sannan har ya galabaita koh ihu baya iyawa da kyau sai haki.
Duk da hakan idonta yana kansa saima kokarin nufarsa da tskeyi tana huci,shikuwa ganin hakan da gudu yayi bayan wani security na miji kaman yaga aljani.
Ganin tsaida itah zai musu wuyah ne yasa secretary yi mata magana akan ta shiga da bujatarta duk da lokacinta bai yiba,saboda a samu ta rabu dashi da ransa.
Su burgune suka bi bayanta shida lawyer ta wanda idonsa yayi tsuru tsuru.
A office din secretary suka tsaya itah kuma ta shiga office din da takardu a hannunta.
A zaune yake yana zuyawa akan kujerarsa duk da yadan manyanta saidai zama a cikin AC,bazai bawa mutum damar ganin hakan ba.
Itah ma zama tayi a kujerar guess wanda take fuskantarta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login