Showing 45001 words to 48000 words out of 62773 words

Chapter 16 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4470

tun kafin ya bata izini,karemata kallo yake na kurullah kafin ya karbi takardun hannun nata.
Saida yagama dubawa tass kafin yah sauke dan glass dinsa yana kallonta,
"Mekike nufin,cewar bansan labarinki ba,da irin abinda Kika yiwa alhaji bala,saboda ki karbi kujerar aiki daga hannun yaronsa,ko kuma dan kin ga kina juya wasu yan yara a yankinku shi zai sa na yimiki sign sannan na doraki akan kujerar tsaro.
Sannan kuma kin daki yarona a waje,duk da nasan akwai abinda yayi miki amma baki da shaidar hakan,saboda yana da takardar asibiti na cewa bashida cikekken hankali,kinga yanzu dole ki amsa kiran kotu"
Karishe maganar yayi yana shafa gemunsa tareda tsira mata ido dan yaji mai zata ce.
Murmushi tayi mai kayatarwa kafin tace,
"Dama inada wannan halin na barin mutane su gama fadar abinda yake bakinsu,kace kasan labarina,amma bayaninka ya nuna baka sani ba,saboda da kasani da bazakayi furucin da kayi yanzu ba"
Fitowa tayi da dan kunnenta wanda yake yin yar danjar wuta ta ajiyemasa a gabansa,ido ya zaro yana kara karewa abin kallo,tabbas Camera mai recorder yake gani.
Kasheta tayi kafin ta gyara zama,wasu takardu ta mika masa tareda bashi damar dubawa.
Gumine ya yanko masa lokacin daya gama karantawa,(ba komai bane sai taksrdun ban girma da aka bata a kasar Brazil lokacin da suka je horo).
"KO baka fada ba na karanta abinda yaje kan fuskarka,kuma nasan kasan labarin Raudah da take jikin paper,idan naga dama zan iyah neman kujerarka da takardun kuma na samu.
Yaronka kuwa karamin alhakine,dan zan iyah kutse cikin yanar gizon asibitin na sanja information dinsa kaf,zuwa abinda naga dama,kuma babu wanda zai gane.
Dan haka umarnine kasa ka hannu a takardun nan,ka taho dasu gobe zuwa garin mu ka dorani akan kujerar dana ce maka ina so,idan kuma ka kiyin hakan,.............hmmmm toh zaka sauka akan taka kujerar ka bani,sai ka zabi abinda kaga yafi maka"
Tana gama fadar hakan ta fice a office din ta barshi yana goge gumi da handkerchief .
Bata yiwa su burgu wata doguwar magana ba,sai kawai alama da ta musu akan su zo su tafi.
Da gajiyah amma dauke da farincikin samun nasara ta isa gida,sabani wancan zuwan da bata samu abinda takeso ba.
Yau tayi akan zata hadu da ummaruje dan haka tun yamma yake shiri kafin ma rana ta danyi sanyi,dayake ya fadawa mahaifiyar sa inda zaije wato hajiyah mairo,itama sai murna takeyi dan haka kawai take some sameemah din.
Itama sameemah a bangarenta shiryawa tayi,duk da bata arziki bace dan kwalliyar wandunan nata tayi amma tayi kyau sosai.
A motarsa yazo dan haka tana zuwa gaban motar ta shige.
Kowa zai wuce sai yah kalli motar saboda kyanta,kuma ga hasken allah dan kowa yana kallonsu a gaban motar kasancewa ba mai tinted bace.
Tunda ta shigo motar ummaruje yaje murmushi wanda ita kuma hakan ne yasa taji ta takura,dan ta tsani taga mutum yana ta murmushi ko dariyah,shiyasa zama da mata yake mata wuyah,saboda basu da aiki daga gulma sai dariyah da shewa.
"Barka da fitowa baby"
"Wacece babyn wai ni?"
Mamakin tambayar da tsyi masa yayi amma sai daure yah cigaba da magana,
"Gaskiya nayi farinciki da har kamarki wannan kyaky kyawar ta bani izinin nazo ganinta"
Surutunsa yake tayi amma bata sake cemar komai ba saima cewa da tayi,
"Uhm Idan ka gama nizan shiga ciki a gajiye nake sosai,ka gaidamin hajiya "
Baiji dadin abinda tace ba amma haka yah daure tareda mikamata wata bakar leda a kusan cike da kaya.
Kallon ledar take taredashi kafin tah yunkura zata ba motar,saidai tsyawa tayi jin abinda yace,
"Dan allah karkiyi haka,wannan kyautar ba daga hannuna bane ummah ce tace na kawomiki,idan na koma dashi bazata ji dadiba,koda bazakiyi amfani dashi ba at least ki tafi dashi.
Fizgar ledar tayi ko sallama batayi masa ba,shima a nasa bangaren Murmushi kawai yayi tareda cwwa,
"Farkon farawa ne" a ransa.
A can gida kuwa tun kafin sameemah ta shigo har zance ya baza cikin gidan har da makwantai cewa sameemah tana hira da dan gidan alhaji bala a mota,bakin ciki idan yayi dubu toh ya taru a cikin ran matan gidan gandu,dan tsohuwar gaba ce tsakaninsu da jinin inna hajara wanda suna ganin babu ranar dazata gushe a cikin ransu.
Musamman ma uwar gayyar wato innna ramatu,cikin hade fuska taja su sameerah daki daomin taji ainihin tushen zancen,duk da tah leka amma hakan bai isheta ba.
Zama tayi akan gadonta mai rumfa yayinda su sameerah suka zauna a kan kujerar dakin kwallo dayah kaman rai.
"Wai ummah mai kike fadane ban ganeba"
"Bazaki ganeba sameerah amma indai har asirin dayake kan sameemah yah karye toh akwai matsala,dan haka basai gobe ba a yau komin dare zamuje wajen malam domin yimana sabon shiri,tsugunne bata kama mu ba,ba iyah ni kadai ba har da sauran matan gidannan"
"Toh Wai ummah ina ta magana amma kin saKa mu a cikin duhu"
Masifah ta darara musu tareda cewa,
"Dallah ni kuyimin shiru,maza kowa taje ta dauko mayafinta mu tafi,har ke sameerah dake,saboda akwai tsumin danake so ayimiki,dan babu shakkah ina jiyo tashin hankali yana tunkatowa"
Duk su ukun tare suka fito daga dakin,inda sukayi kisibiss da sameemah tah dawo daga waje da leda a hannunta,wanda kowa yah gani yasan ba abune na harkar karanta a cikiba.
Wucesu tayi tana waka ta shige dakinsu,inda sai a lokacin dukkan su suka dauke idonsu daga kanta suna jijjiga kai tareda cewa........uhmm!


Toh nima uhmmmm.........😀😀😀😀


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤28❤


Duk da dare yayi amma haka inna ramatu ta dage akan dole sai sun tafi waje malami,dakyar suka shawo kanta aka bari akan sai gobe da hantsi sai suje.
Can Bayan isha kowa yana kofarsa saiga inna larai da dan mayafi ta shige dakin inna ramatu.
Sun Dade suna dan kuskus dinsu kafin ta fito ta koma kofarta.
Kaman hadin baki kuwa tana komawa itama inna karima ta shiga kofar,itah kam sai can wajen dare kafin ta tafi.
Gabadaya gidan shiru yah koma banda munafurci babu abinda yake zagayawa a gidan,ko na menene oho.......
Da safe gidan da wani yanayi daban yah tashi,
Sameemah tah shiryah ta tafi wajen shirye shiryen hawa kujerar ta
Sukuwa su sameerah sunyi hanyar zuwa wajen malamin sa'ar su.
Yayinda innna larai kuma tace tah tafi gidan su in jita da fada.
Itah kuwa inna karima dayake gidan su babu nisa tun a jiyan taje gida,dawowarta ne ta shiga kofar inna ramatun.
Sauran kofofin kuwa kowa yana fama da tasa matsalar,musamman ma kulu habibiyar manjo🤣🤣🤣🤣.
Shigowa yayi daga wajen mai shayi yana daga wata babbar riga ko waye yah bashi ita oho,kulu ce ta kalleshi da kallo mai kama da harara kafin tace,
"Kai manjo sai ka cemin wai ka tafi shan shayi saina ce ka kawo kidin sabulu da abinci rana kacemin kai baka dashi,wai a ina kake samun kudinne,dan nasan mai shayi ba kanin ubanka bane da zai dunga baak kullum a kyauta ai"
"Ke kulu wallahi ki shiga hankali ki,na hana ki yimin magana kaman dan ki bakyaji koh,toh ba kudina bane ,kudin sadakin sameemah ne nake dan tabawa a matsayina na yayanta"
Tsayawa tayi da hurar wutar da takeyi tana kallonsa da alamar neman karin bayani,ganin bazai sake magana ba gashi kuma ta matsu ta ji mai yake faruwane yasata sake tambayar sa,
"Manjo wace sameemah kake nufi"
"Sameemah dai ta gidannan akwai wata sameemah a garinnan ne bayan itah,shegiya mai suna mai wahalar samu,anayin kwatance mutum yasan ita ce"
"Amma waye yabaka sadakinnata ne"
"Waye kuwa banda amininna sule maye,kinsan irin kaunar da yake mata kuwa"
"Ahah bansaniba amma daga ganinka baka da labarin abinda yah faru a kofar gidannan koh?"
Matsowa yayi kusa da kulu yana baza kunne kaman wata mace a wajen son gulma,
"Ke fa dam in mai yake faruwa kinsan daga ni har sule bama gida mun tafi karkashin gada"
"Ohh dama karkashin gada kaje,shine kacemin wai kana wajen abokanka,toh bari kaji na fada maka dan gidan alhaji bala ne yake son seemah,dan jiya ma yini sukayi suna hira a cikin wata dan kareriyar motarsa,baka ga yanda innarku ta dau fushiba saboda basu sameerah yakeso ba,Nima da zai soni tun yaushe na fige wannan auren masifar ga.........."
Bata kare maganar ba manjoya zabga mata mari tareda cewa,
"Shegiyar yar kundun uba kai,ina tsaye kike cewa zaki je wajen wani saboda kinga yanzu na fara girma bana dukanki kullum"
Bata bari yah karisa fadanba ta ture kujerar da take kai tayi dakinsu da gudu.
Daga rigarsa yayi ya share gumin da yake tsatstsafo masa,dan yasan idan sule yaji labarinanna bai san yanda zasu kare ba sam,da haka ya samu kwarin gwiwar fita wajen, saidai zuciyarsa bata daiNa dukan tara tara ba,dan kudi kam ya cinyesu babu dalikinsu a wajensa.
Saida su sameerah suka hau mashin kusan sau uku kafiin aka kawosu dadai inda saidai su isa da kafarsu saboda duhuwa da kuma matsin wajen,zainab sai ware ido takeyi dan dama ita kadai ce bata san wajen ba su sunsani.
Wata hanyar suka nufa wanda zata kaisu wajen bokan da suka zo dominsa.
A wajen wata bishiyah suka tsaya saiga dariyar sa ta na amsa kuwwa a wajen.
Lokacin daya bayyana a gabansu saida zainab da saka wata uwar kururuwa dakyar inna ramatu ta riketa tana mata alamar gargadi da ido.
Kara rikicewa tasake yi jin muryar sa mai kama da aradu tana dukan kasar wajen (hmmmm sumayyah kiji ta fah,amma take raina kawarki dan tana kallonta kullum).
"Ki Shiga hankalinki ba a yimana yarinta a nan wajen,kinzo karbar sa'a ne ba nuna tsoroba,madubinmu ya nuna mana cewa idan akayi aiki zaki mallakeshi yanda kikeso har sai abinda kikace shi zaiyi,uwarsa data kawoshi duniya ma bata isa ba"
Ai zainab daga jin haka ta gyara zama tana washe baki,zuyawa yayi yana kallon inna ramatu kafin yace,
"Ke kuma ki tashi tsaye,domin aikin da mukayi akanta lokacin ta dake yarinya ba mai karfi bane,domin uwarta duk da mun nakasata tana kokarin yin ibada akan yayanta,toh sihirin dayake saka ta rashin mutunci da kuma jin batason kowa yah matso inda take da sunan yana sonta toh ya karye"
Inna ramatu kaman zatayi kuka tace,
"Malam kayi wani abu akai,naga alamar har tafara yin samari masu kudi,dan ina zaton morar nan ma yaronne yabata"
"Bashine yabata na mahaifinsane ya bata ,dukkansu sonta sukeyi,saidai akwai aikin da za'ayi idan kun amince"
Cikin sauri suka fara jijjiga kansu a tare,
"Zamu maida soyayyar yaron zuwa kan babbar yarki sameerah,duk da bazawara ce amma haka zai nace yace duk duniyah itah yakeso,saboda soyayyar da iyayensa suke yimasa haka zasu amince da hakan,ita kuma zamu kara yin wani aikin a jikinta wanda zai kara saka kiyayyarta a cikin zuciyar mutane kaman yanda kuka fada"
Sameerah wanda tunda aka fara magana tayi shiru,amma jin ummaruje da ko kallonsa bata san zatayiba ance zai sota har ya aureta ai tuni ta jita a wata duniyar daban.
"Yawwa boka dama inaso idan da hali,a rabata da duk abinda ya shafi gidan alhaji bala,saboda kar idan nayi auren ta kawomin cikas,saboda naji kace uban ma yanasonta"
"Eh kin fad'i wani abu,za'a nesanta ta da duk wata kaunar namiji a zuciyar ta indai da niyyar aurene,saidai ke anan zaki zauna akwai turaren da za'ayimiki wanda zai sa shi kwarewa cikin kogin sonki"
Duk da bata son zama a wajen bokan tunda ta san halinsa,amma yau kam bata damuba saboda babban shirin da za'ayi mata,itama zata faso cikin manyan mata.
Wani dauri yabawa inna ramatu wanda za'a saka wa mijin zainab din,sannan da wanda zatayi matsi dashi idan aka zo auren.
Haka inna ramatu ta karba tana godiya suka taho itada zainab din,babu alamar damuwar barin yar ta da tayi wajen bokan
*kai wa iyah zubillahi duniyah ina zaki damu,allah yakara tsare mana zuri'a,ya hana mu dogaro da wani bayan shi*.
Kaman yanda sameemah ta fadawa shugaban yan vigilantee kuwa,karfe tara ma a garin nnsu tayi masa tareda shi da tawagarsa,duk da a fuskarsa kasan baya farinciki da abinda zai aiwatar saidai babu yamda zaiyi,*farillah ne tusa ga mai bacci*.
A wani babban hall akayi taron wanda sameemah ta dauki nauyin komai,kama daga tarar baki har zuwa shirya waje da sauransu.
Sai wajen karfe goma kafin ta shigo da kayanta na damara anyi masu dinki mata sun amshi jikinta sosai,dayake dama ta iya tafiyar sojoji sai hakan yabada wani style mai zaman kansa.
Su kansu manyan bakin basu san sanda suka lume a kallonta ba har ta ison kan presentation floor din.
Rigane da wando irin na kayan vigilantee sai wani babban belt daya zagaye hips dinta,ga kuma takalmi mai kaman na sojoji amma na mata,kitsone a kanta amma ta sau jelar ta kasan hular da take kanta.
Babu kwalliyah a fuskarta banda dan lip gloss din da ta shafa,saidai fuskar nan babu alamar fara'a,dan dama bata dariya,a ganinta zubar da girma ne.
Shikansa speaker saida yayi dan gyaran muryah har sannan yana satar kallomta kafin yafara abinda ya kawoshi wajen.
Ba wani bayani sosai yayi ba saina yamda take gwagwarmayah a garin,sannan kuma yah kara da nasa aji moton irin na yanayin aikinsa,wato da abinda tayi da wanda batayiba,sannan da dalilinta na karbar aikin dan san kawo cigaba a garin.
Tafine ya dauka raff raff a wajen musamman ma yaranta wanda suke cikin audience.
Shugannne ya fito shima da kayan aikimsa a jikinsa saidai akwai yana yi tazarar ster tsakanin nasa da na sameemah.
Godiyah yah fara mikawa kafin kuma yayi nasa dan takaitaccen bayanin.
Yaransane ya miko masa takardu da kuma file wanda suke dauke da cewa ya yarda da zaman sameemah akan kujerar aikin,wanda zata zagoramci garin karkashin ikonsa.
Mika mata fike din yayi da hannu daya itama ta miko hannun da niyyar karba,wani kallo yake binta dashi na allamar kinyi kuskure,yayinda itama take aikamasa kallon ina daidai da kai.
Mutanen da basu san mai yake faruwa na gani suke kaman tausaya mata yake akan aikin.
Alhaji bala da kuma Mahmoud dukka sun halarci taron,saidia alhaji bala ko kallon inda take bayyi ba,saboda shi kadai yasan takaicin da ta kunsa mar.
Alhaji Sama'ila kam har taya murna yayi mata,yana wani cusa kai saboda idan bukatar alfarma ta zo,su samu da rangwamemi.
Mic aka bawa sameemah domin tayi bayanin nuna godiyar ta gameda irin nasarar da ta samu.
Karba tayi tana gyara tsayuwa,inda gun yayi tsitt kowa yana jiran yaji mai zatace,
"Da farko dai ina godiyah da duk wanda yah halarci wannan taron,sannan ina yiwa kowa fatan komawa gidan lafiyah,gameda nasarar dana samu kuwa tabbas nayi farinciki,saboda ni kadai nasan dagewar danayi akan hakan,dan haka aiki sai inda karfina yakare.
Sannan bazan yadda da shigowar wani gabana ba ba tahanyar da ta daceba,kowaye shi koda kuwa uba nanne sai na dau mataki akai,Shirina akan aikin nan kuwa nikadai na santa sai kuma idan wanda yayi abin da bai daceba zai gani,da kuma lokaci idan yah ara mana.
Nagode sai anjima"
Dukkan maganar cikin tsare gida da gargadi tayi ta gama,hakan yasa ko tari babu wanda yayi har ta gama maganar tayi shiru.
Sallamatr kowa akayi saboda taro yah kare an bar wanda yah sauka da cizon yatsa shida mutanensa da kuma kudirin daukar fansa.
Yayinda aka bar kuma yan kungiyar sabuwar tawaga da murna da kuma kudirin yin aikin su cikin nasu tsarin.
Dadai lokacin sallah azahar ne manjo ya fito daga masallacin unguwarsu,har sannan wannna rigar gadon ce a jikinsa bai cireba.
Yah karyo kwanar gidan kenna yayi turus ganin sule maye a kofar gidansu yana jiransa,kokarin komawa yakeyi amma babu dama saboda sun riga sunyi ido hudu shi da shi.
Ga shi ba dama yakawo masa wani uxirin dan da alama bai yi shaye shayenba idonsa tar yake,maitar karban kudinsa tah motasa.
Cikin sanda manjo yah isa har gaban sule mayen yana wani sunne kai,tun kafin yayi magana sule maye yace,
"Karkace komai manjo billahillazi kudina zaka bani,dan nima daka gsnni nan ba kudina bane sato su nayi,kuma masu kudi sun ganoni dasu ma muke tare,dan haka ka bani na basu ,ko kuma na nuna ka nace kudi yana wajenka ehe"


Toh manjo ka shiga uku,za'a manjeka kenan😀😀😀😀.




*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤29❤


Wuri wuri da ido manjo yayi jin abinda sule maye yake fada.
Gabadaya jikin sa rawa yakeyi,ganin yamda wasu mutane suka zagayesu da alamar sun fi su manjo iyah shege.
Bakin manjo sai motsi yakeyi amma ya gagara fidda ko kalma daya,wani daga cikinsu ne yah kinsa masa duka a ciki,aikuwa ya hada kururuwa yana neman taimako.
Ganin da sukayi manjo babu kudin a wajen sa cikin kankanin lokaci suka fara dukansu kaman sun samu kayan wanki.
Tun manjo da sule suna ihu har sukayi shiru suna karbar ruwan dukan dayake Ziyartarsu.
Karar motace da hayaniya ta tsayar da su daga jibgar su manjon suna kallon waye yake tahowa.
Motar sameemah ceh a gaba sai wata mai bodi an cikota da mutane kuma anyi mata paint irin na uniform din jikinta.
Fitowa tayi daga motar ta mutane suna binta a baya harda yan kungiyarta,a wajen su manjo ta tsaya wanda sukayi futu futu da rairayin wajen,saboda burburwar da sui tayi.
Kallon masu dukannasu tayi tareda tambayar su abinda yah faru,
D'aya ne daga cikinsu ya zayyane mata abinda yah faru,kuma ta yadda da hakan dan sunyi maganar kudin kuwa ita da manjo,sannan tasan ko za'a kashe sule maye bashida inda zai samo dubu biyar ma bare har dubu talatin,dan matarsa ma da shi kansa innarsu ce take ciyar dasu.
Hakuri ta basu inda suka ce,dama tafiyah zasuyi tunda sun daki na kudinsu,saida suka bace daga layin kafin Sule ya karkace baki yace,
Dama nasan har yanzu kina sona kawai zancen mutanene,gashi kin cece............."
"Kai Dallah yimin shiru marar hankali kawai,duk da dukan daka sha hankalin ka bai dawo ba koh?,kasake magana a wajennan in ban kirasu sun karisa ka ba yanzunnan"
"Kai kuma (tafada tana nuna manjo wanda fuskarsa tayi buleliya koh magana bayayi),kasake karbar kudi ka kashe kai a dole ga mai son banza,kaga yamzu sai kulu tayi jinyarka koh?"
Tana gama fadar hakan ta yiwa wasu gardawa guda biyu magana akan su kinkimi sule zuwa gidansu,yayinda wasu guda biyun kuma suka shiga da manjo shima gida,sai nishi yakeyi saboda tsamin jiki.
Tsitt kakejin gidan babu hayaniyah saboda kofar kawu shehu innna karima ce kawai a ciki,abokiyar fadannata wato inna larai bata nan bare a jisu ,ita kuma inna ramatu har yanzu itama bata dawoba.
Kofar kulu tah nuna musu akan su kaishi,dan bazata iya da kuma hayaniyar kulu ba a lokacin,idan ta huta koma menene sai ayi,dan dama an saba ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login