Showing 12001 words to 15000 words out of 62773 words

Chapter 5 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4436

shema'u tunda bata nan satinta d'aya da tafiya har yanzu bata dawoba"
Har suka gyarawa dan liti wajen kwana sameemah tana zaune batace musu komai ba saima waya da take yi,kuma a wajen shema'un shine a kusada da itah,dan duk dakin tafi kowa saukin kai da daukar komai ba komai ba,yanzuma ta tafi garin su mamartane wanda bata gidan saboda an basu hutun makaranta,itah kad'ai ceh sameemah take yiwa maganar arziki itah ma kuma ta d'au sameemah tamkar y'ar uwarta ta jini,babu ruwanta da su salma wanda suke uba d'ayah.
Saida sameemah tah bari dare yayi sosai,tah gama abinda take,tana wajen tsakar gidan tana jan wiwi a kwarkwaro,saida ta tabbatar tah dau caji mai kyau,tana jinta a can kololuwar sama,inda babu wani shegen daya kaita kafin tah koma d'akinnasu.
Saida tah kare musu kallo,kowa ta kula da irin kwanciyar da yayi,kafin tah fito da wata zambad'ed'iyar bulala wanda tah bawa burgu aike yah kawo mata daga gidan horo.
Kakkad'ata tayi tak'ara juyata,kafin tayi wani Murmushin gefen baki na mugunta,

D'agawa tayi iyah karfinta kafin tah shek'awa dan liti wannan bulalar a gadon bayansa,wata irin mika yayi tareda mikewa tsaye yana k'andarewa,
" Shshshs, yimin shiru kuma kayi kneel down,idan kuma ba hakaba wallahi zansa karnukan nan suyi tah yagar naman jikinka"
Dan liti yana had'a ido da karnukan masu jajayen idanu wanda duhun dare yasa yake ganinsu kamar kurayeh.
Yawu yah hadiye mukut kafin yayi yanda tace,
Kara d'agawa tayi tah zambad'a masa iyah karfinta,lokacin data sauke masa tah uku kasa zama yayi ,dan azaba bai san sanda yah dungura ba yana kikkifta ido😂😂😂,(ga mari ga tsinka jaka,@rahama zo ki cece shi keda @chuchu,uhm irin su umma najma kam bazata iyah zuwaba).
Jambad'a masa bulalar take tayi gashi ta hanashi kuka ko kad'an ,ganin zata kasheshi kwanansa bai kareba ne,yasa shi takarkara ya zunduma wani uban ihu tun daga mak'oshinsa irin na ainihin gardawan nan (shege ashe yasan shidin na mijine).
Su sameerah ne suka tashi a firgice wanda ba iyah su ba ma duk yan gidan ma babu wanda baiji ihun dan liti ba saboda yanayin dare.
Samunsa sukayi a zaune sai karkarwa yake ya had'a gumi shirkif kaman anyi masa wanka da ruwa.
Ta shi sameerah tayi zata bar dakin domin kiran wani a cikin gidan,saidai cak ta tsayah daga dorah kafafunta a bakin fita daga d'akin,saboda wani mugun gargad'i da sameemah tah antaya mata,
"Kina fita daga dakinnan zaki zo kema ko jone dashi ,dan duk wanda ta min shshshigi da itah zan had'a"
Tofahhhh

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤09❤

Dukan tsiyah sameemah tayi wa dan liti,tun yana kuka a cikin d'aki har suka fito waje amma bata bar dukansa ba,kowa fitowa yayi dan ganin mai yake faruwa kaman ba dareba,
"Zaka sake Shiga dakin mata ka kwanta?"
"Ahah bazan sake ba kiyimin rai na tuba"
Tsayawa tayi da dukan ,wanda cikin daga muryah inna karima ta fara magana,
"Ehhh lallai yau kam abin yayi yawa,dan tsabar rashin mutunci daga shiga daki saiki masa wannan aika aikar,dan kawai kinga kashin arzikin da uwarki har ta mutu bata samuba koh?,toh bazan yadda da wannan rashin mutuncin ba kuma..........."
Tun bata rufe bakiba sameemah tasake zabga masa bulalar,tana sake magana ta kara sake zuba masa ita,ganin hakanne yasa inna karima tsuke bakinta tayi shiru,saidai takaici na duniya yah isheta,
"Keh karima kike ko ma waye?har yanzu bakisan halina ba koh?,a gabanki dazu da yamma nayi masa kashedin ya dauke kayansa a d'akinmu amma yayi kunnen uwar shegu da ni,ke kuma da kikasan abinda zan iya aikatawa idan na tarar bai d'aukeba kika kasa jamasa kunne.
Sannan na dawo nasameshi a dakinmu kuma ma saboda tsabar raini a kusa da gadona wa'ennan shashashan mutanennan suka yi masa shimfidi koh,ba laifinku bane ,laifina ne da na ke daga muku kafa.
Toh bari kuji billahillazi daga yau idan nasake kafa doka wani yah karyah ta a gidannan hmmmm,yayi kuka da Kansa koda kuwa bak'one idan yazo a sanar dashi.
Kai kuma"
Tafad'a tana kallon dan liti,
"Iye na'am ina jikinki madam"
"Idan nasake kamaka a hanyar dakinmu saina cire maka kafa guda d'ayah,kai koh a cikin gidannan na shigo naganka da kayan mata kana zaune a cikin mata ,saina yi maka hukuncin dayafi wannan,ku kuma zamu hadu daku ,zakusan kun sauke gardi a dakin danake kwana"
"Naji Ranki ya Dade kuma inshaallah bazan sake ba ,nidai karki sakemin irin wannan hukuncin,ni gobema zan bi motar sassafe na bar garin bazaki sake ganina ba"
"Yadai fi maka"
Kowa juyawa yayi ya nufi wajen kwanciyasa aka bar dan liti a wajen yana kakkarwa ,karshe dai a wajen yah kwana.
Da safe kuwa kaman yanda dan liti yafada gari yana wayewa ya kama hanyar tasha bayan yayiwa kowa sallama,dan baya fatan sake gamuwa da irin wannan hukuncin da tunda uwarsa ta haifeshi ba'a taba masa yau gashi seemah jar wuyah tayi masa.
Saida aka shafe kusan kwana biyu wata fitinar bata sake kunno kai ba tun wacce akayi da daddare tsakanin dan liti da sameemah.

PORTHACOURT:SOLDIER'S BARRACK.


SALEEMAH ceh a zaune akan kujera tana chatting ta nad'e k'afa d'ayah kan daya kaman wata yar basarake.
Kyakykyawace ajin farko ga tana ji da ilimi da kuma matsayi,kowa a cikin barikin shayin wani abu ya had'ata dashi yake,dan ko fita zatayi sojojin da suke rakata sun ninka wanda suke raka mijinnata idan zata fitah.
Itah kadaice a wajen mahaifinta wanda shine General a duk gabad'ayah barikin,yataka matsayi da dama Sannan allah ya jarrabe shi da son yar tasa wanda yake jinta a cikin ransa,baya kaunar duk wani abu dazai tab'a farincikinta bare kuma lafiyar tah.
Tun lokacin da tah dawo daga karatunta a Germany,suka hadu da sameer yah kawo wasu document wajen mahaifinta,tun daga wannan ganin taji duk duniyah babu Wanda takeso saishi.
Har daki tasami mahaifinnata ta fad'amishi ,cikin kankanin lokaci General Musa Funtuwa,yah amince dan shima yah yaba da hankalin sameer din,saidai yanada zuciyah da kuma tsayayyan ra'ayi,amma indai kyan haline yasamu lambar yabo kaf barrack din akan haka.
Cikin kankanin lokaci yah kirah sameer yasanar dashi bukatarsa,da farko yace yah bashi d'an lokaci,amma daga baya yah amince saboda mutuncin general din a idonsa,sannan kuma duk da saleemah bata had'a dukkan abinda yakeso ba,tana da wasu abubuwan,dan itah din macece da bakowa zai kalleta ba baiji ta burgeshiba.
Bayan yah amincene soyayya ta fara kulluwa tsakanin saleemah da sameer duk da ba wasu cikakkun masoyah bane ,saidai kowa yana daraja lokacin kowa. Saidai soyayyar da saleemah takeyiwa sameer din a gaban kowa take nunawa har da kuwa iyayenta.
Saboda soyayyar daya ga tana yiwa sameer ne ya sashi d'aga matsayinsa zuwa major general sannan yah aura masa itah.
Lokacin da aka daurah aure,gida guda yah basu tareda colony na sojoji guda akasa a area gidannasu saboda tsaronta da kuma yi mata hidima.
Masu aikin cikin gida ma part guda aka waremusu,saidai duk wadda tazo aiki saleemah tah nuna batayimata ba ,a ranar ake sanja ta a dauko wata.
Masu kulada kayanta daban,masu kulada abinci daban,masu kula da sashenta daban haka masu kulada sashen mijinta su ma daban.
D'anta kuwa suna ta haifeshi ne,dan said tayi kwana uku bata ganshiba yana wajen nanny,ita kuma tana harkar gabanta.
Duk inda ka wuce ba sunan dayake tashi sai madam,shi kansa sameer bai isa yasaka ta abinda batayi niyyah ba,sai idan taga ransa yana baci kafin tah aikata abinda yah ce.
Mai shara ce ta zo goge palourn amma tana tsoron yiwa madam din magana saboda kar a koreta kaman yanda ake yiwa sauran.
Kulada itah saleemah tayi a tsaye kafin tace mata,
"Ke kuma miye kika wani make a can lumgu,kafin kifara sharar jeki waje duk sojan da kika gani kice ina san ganinsa yanzunan"
Cikin sauri kaman ana turata da iska tafita domin cika umarnin nata,koh minti uku batayiba said gata da wani soja sun shigo.
Saida ta gama abinda take a wayar kafin tace,"
"kuje kaida driver gidan kawata Surayyah zata baka sak'o ka kawomin,yanzunnan"
Saida yah sankame ta sara mata kafin yace,
"Yes madam"
Ta shi tayi ta koma daki dan bawa mai sharar daman gyara wajen.
Tana cikin sharar ne sameer yah shigo daga wajen aiki,babu kowa sai kawai mai sharar tana ta aikinta,
"Saleemah tana nan"
"Eh ranka yah dade yanzu tah shiga ciki"
Bai amsa mata ba said wucewa da yayi d'akin saleeman,nan ma saida yah jera sallama uku bata jishiba.
Samunta yayi tah kure wakar Alan walker,ga kuma chat tanayi.
Jin an fisge wayar tane,yasa ta saurin d'agowa tana kallon sameer din,cuna baki tayi kafin tace,
"Honey ka dawo neh?"
"Ba zancen honey bah,ki amsa gaisuwar danayi tukunna,koh kina so ki cemin bakiji sallamar ba?"
"Ahah ni banjiba"
"Toh yanzudai ba wannan ba ina abbana yake? Nasan sun dawo daga school tun d'azu"
"Nima ban ganshiba,amma ai sun dawo yana wajen su nanny d'insa"
"Wai saleemah anyah kuwa ke uwace ta gari,yanzu haka iyayenki suka miki,d'an ki haifeshi a cikinki amma kuna gida d'aya yah dawo a makaranta koh bai dawo ba ke baki saniba,sai chat da friend shi kika iyah kawai"
"Kai honey fad'anka yayi yawa kwana uku baka gida,kana dawowa babu hug din kayi missing dina ,sai fad'a"
Ficewa yayi yah tafi d'akinsa bayan yah mata kashedin ta d'auko masa yaronsa kafin yah fito.
A haka badan taso ba tah nufi sashen da nanny din farouq din suke.
A zaune tasameshi yana cin abinci har sunyi masa wanka,yana kallonta kuwa yah taho da gudu yana kiran mommy.
Tsugunnawa tayi ta rungumeshi itah kanta tana son d'annata saidai rashin halin kulawa irin nata kawai,
"Mommy tun d'azu na dawo daga school,kuma anty tace wai gobe zamu koma sabon clash"
"Eh hakane ya kk,ka gama cin abincinne?"
"Eh mommy ni bana son abin abincin tsami yake yi(mayonnaise) "
"Shikenan muje abbanka yadawo yana nemanka"
"Hee I mish abba"
"Okay toh muje"
Sanda ta koma sashennasu har yah fito daga bandaki da towel a kansa yah watsa ruwa,yana kallon yaronnasa yah mika masa hannu yana dariyah,
"Oyoyo abbana ya kake yah makaranta?"
"Fine abba,na dad'e ban ganka ba abba,sai yanzu"
"Eh my boy Abba yah tafi aikine,amma yanzu yah dawo,zamuyi wasa koh"
"Eh Abba "
"Yawwa Toh yanzu kaci abinci sosai"
Saida yah yatsina fuska irin ta yara kafin yace,
"Ni Abba bana son mayonnaise indomie zanci"
"Shikenan kije mommy ta baka koh"
Har suka gama firar saleemah na tsaye ta nad'e hannayenta tana kallonsa,saida ta ji an sakota a zancen tukun tah mikawa farouq hannu akan yazo su tafi,had'e fuska tayi kaman mai shirin fashewa itah a dole yana magana da farouq banda itah.
Bayan ta gama hidima da farouq dinne tah sake turashi sashen su nanny din,sai tsuka take itah a dole ta gaji da yi masa aiki.
Fitowa yayi daga dakin yasha kananan kaya amma na kakin sojoji,sosai ainihin yarintar sa yah ,tundaga fitowarsa saleemah tah kafeshi da ido ganin yanda kullum kaman kara kyau yake,shima yah kulada irin kallon da take masa saidai yasan inda kallon nata zai nufah wanda in akaje shi zata bari a ruwa.
Kujera yah ja ya zauna a wajen cin abincin,kafin ta tashi tah zuba masa abincin,bai yi wani murna dashi ba saboda yasan ba itah ce ta dafa masa ba da hamnunta,duk da yah dade bai dawo ba bazata iyah yi masa girkiba ko d'okin zuwansa saidai tayi ta masa korafin baya yimata soyayya yanda ya kamata.
Bai fi loma biyar yayi ba ,yah rufe abincin tareda cewa yah koshi,
"Haba honey Har ka koshi mai ma kaci toh"
"Shine cin,bari na fitah akwai dan aikin dazanyi saina dawo"
Rike rigarsa tayi tana masa shagwaba irin ta sakalan yarannan,dan dama ta kware tah wannan fannin,
"Uhm uhm shikenan daga dawowa sai kace zaka fitah,gaskiya yau gabadaya lokacina ne ,kuma kasan nafi bukatarka fiye da kowa yanzu"
"Saleemah ba dadewa zanyi ba ,in anjima zan dawo daga nan koma miye kisaka ni a gaba kiyi dani har zuwa gobe"
"Shikenan promise karka dade"
"Yeah I am sure"
"Okay bye "
Toh nima bye😍😍😍

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤10❤

Sai can wajen karfe 9:00pm,kafin sameer yadawo daga inda yacewa saleemah zaije,batare da tambayeshi mai ya faru ba kawai tah fara zazzaga masifa dama tah cika tayi famm ,dan tun dazu take jiransa a falo bayan tayi sallah.
Takaicin halinnata ne yasashi wucewa daki kawai batare da yabata karin bayani ba,itama bata huceba binsa dakin,sanda tah shigo yajuyah bayansa yana fitarda wani huci mai cike da bacin rai,saleemah bata kulada yanayin dayake cikiba tah cigaba da ta cigaba da mitar da take,
"Amma abban farouq dakai fah nake magana shine ka shareni ka shigo daki bayan kasan..........."
Katseta yayi daga karisa maganar sanadiyyar had'e bakinsu dayayi waje d'ayah,yah dad'e kafin yabata damar jan numfashi.
Fatar bakinta har saida tayi ja saboda farmakin daya kai mata cikin zafin nama,kallon idonta yake kafin ya fara magana kasa kasa,
"Dama ina abinda yasa kika damu na zauna a gidan kenan,sannan dana shigo ma kika fara fad'an na dad'e?,ba damuwarki rashin dawowa tah ba ko halin danake ciki,burin ki shine wannan,toh zo na baki"
Cikin halin ko inkula da maganar da yayi mata cikin salon maganar halinka mai sanda kuwa tah cafke bakinsa tareda maida martanin kiss din.
Sun dad'e a tsaye kafin suka isa ga kan gadon,saidai gogan cikin zafin nama daya kuma had'u da halin dayake ciki na baci rai yake kaiwa duk wani sassan jikinta farmaki.
Tun tana jurewa har tah matsa daga inda yake tah koma gefe tana sheshshsekar kuka,(dama su saleemah sakalai).
Shikuwa kansa yasaka acikin filo yana cije lebe tareda sauke ajiyar zuciyah,yah dad'e a haka shikadai yasan halin dayake ciki. Itah kuwa saleemah tun yana jin ajiyar zuciyarta har yah fara jin numfashinta yayi nauyi da alamun tayi bacci.
Tausayinta ne yakamashi,danshi kansa a sanin dayayi mata yasan bazata jure yanayin daya zo mata dashibagashi kuma tana dauke da yaran ciki,saidai shikansa yana tausayin kansa domin yasan koh kusa zaman su da saleemah bazai dore da haka ba,dole yah nema wa kansa mafita ,duk da yasan fitina yake shirin kunnowa,dan saleemah da d'anta ma kishi take ina kuma ga wata matar idan yah auro?(tabb hmmm).
Yah dad'e yana tah Tunani kafin yah tashi ya shiga bandaki.
Saida yah yi sallahr dare da addu'o'i kafin shima yah koma ya kwanta.
Da safe har sameer yah tashi yah gama shiryawa amma saleemah bata tashiba,kare mata kallo yayi da takaici kafin yace bayan ya bubbuka gefen filonta ta tashi,
"Wai kinyi sallahr dana tasheki kiyi da asuba kuwa"
"Eh nay I"
"Toh shikenan ni na tafi,sannan na manta ban fad'amiki ba,ki shiryah a cikin satinnan zamuyi tafiyah,zanje na gaida iyayena sannan kuma kakanmu alhaji babba bashida lafiyah"
Mitstsikewa idonta tayi tareda tashi zaune kaman ba itah ce take muryar bacci ba,
"Gidanku kuma?"
"Eh gidanmu menene a ciki?"
"Amma bazaka tafi kai kadai ba,kasan fah ni ba lafiyah ce dani ba"
"Tareda Ku zamu tafi dan nagama yanke hukunci,saboda tunda na aureki baki taba zuwa garinmu ba ka kuma farouq basu sanshiba yakamata na kaishi gidan kakanninsa yagansu"
Bai jira amsar dazata bashiba ya yi ficewarsa yabarta a kan gado baki a sake,
Tabdijan garinsu kuma,toh wata sabuwa(😂 yarinya zakije gidan gandu ki more).

GIDAN GANDU PALACE(na su princess sameemah😂)

Koh kwana biyu ba'ayi da tafiyar dan liti ba saiga shugaba MANJO yah diro garin.
Koh sallama babu said ganinsa sukayi a tsakar gidan yana zazzare ido kamar anyi masa kwalli da barkwano,kowa idan yah kalleshi sai yah karewa dress din jikinsa kallo.
Saboda wata biri da wando yasamu yah mamuk'a hantsar da matseshi ,kafafun rigar kuma a iyah gwiwarsa suke,ga kuma hular sanyi daya tabka,sannan ya goyi wata uwar jaka a baya.
A takaice dai kana kallonsa kaga mahaukaci sabon kamu,yaranne suka tafi da gudu suka kirah kulu a kofarta,da sauri ta fito jin ance manjo ya dawo har tana tuntube da gyara zaninta,turus tayi ganin irin shigar dayayi ga kowa sai dariyah yake kasa kasa,haushine yakamata ita da inna ramatu saboda daga gani babu wani abin arziki daya kawo,saida yah juyo ne kafin yah kulada kulun,
"Lah kulunkulun din manjo bakya ganin na dawo ne,babu wani dan tarba ta irin miji da matar nanne?"
Duk maganar cikin shakyakykyiyar muryah yake yin ta,ga bakinnan jawur dashi kaman bakin tsoho mai cin goro,tab'e baki tayi kafin tace'
'Wannan shigar fah daga iyo ta me cece?"
"Lah wannan suwaga ce,suwaga ba ,ai irinta ake yayi"
"Mtswww Toh naji,saika shigo ai muji dame kuma ka dawo"
Binta yayi kaman rakumi da akala suka yi kofar tata,dan idan suna dad'i itah dashi tana juyashi yanda taga dama,saidai idan kwayar tagaya masa ba daidai ba kokuma tayi masa laifi ,toh ba iyah ita ba ko yan gidan sai sunsan an tab'oshi ,dan manjo shima number one ne wajen rashin mutunci,gashi bayan manta tsiyar da akayi masa a sauki.
Suna isa kofarsu manjo yah akiye jakarsa yah shiga bandaki ,kulu ta dau jakar tareda zazzageta a tsakar dakin,zare ido tayi gsnin abinda yake dauke a cikin jakar,ba komai bane sai wasu shafta shaftan silifas da kuma wani tsohon bargo sai kuma kayansa guda uku,har sun sanja kama dan daud'a.
Manjo yana shigowa dakin kulu tace,
"Wai uban me toh ka kawo duk tsawon dad'ewa dakayi da tafiya ranin iyee?"
"Uban me nakawo kaman yah?,tsaya wai kema uban me yasa kika zazzagemin jakata,har zaki wani sakani a gaba mai na kawo,uwarki na kawo,kulu billahillazi ki kiyayeni ,tunda na dawo kikemin masifa kaman wani d'anki,dan kinga ina muss(missing) dinki,toh wallahi zan ajiye muss din nayi miki duka,kinga saiki tunoni mu zauna lafiya"
"Eh zakace zaka dakeni mana saboda ga jaka,karyah nayi uban me ka kawo,naga jiya dan liti daya zo rabon shaddodi ya dungayi da atamfofi nima har turmi biyu aka bani "
"Ke dan yah rasulu,sheege toh ina tawa shaddar nasan yah bayar a ajiyemin kinga saina dunka in za'ayi daurin aure a gidan mudunga sakawa muna fitowa a manyan yayu,kuma baki isa kicemin an baki ki ajiyemin kice kin sayar ba,dan saikin fito da itah yanzunnan"
"Kutt lallai ma manjo wai wannan wane irin zance kake ne haka,toh ko yah baka ma bazan ajiyeba sayarwa zanyi barema babu wanda yah tuna da wata halitta wai itah manjo,dan koni saida akacemin ka shigo kafin na tuno da kai,saidai bansaniba koh inna ramatu ta tuna dakai"
"Kulu kulu tam"
"Menene? Dukana zakayi yanda ka saba?"
"Ahah bazan dakeki yau ba saidai inaga gobe kam saina yimiki lilis yanzudai debomim abinci tukunna,idan naci kuma saina zaga gari domin asan na dawo garin"
"Ni ban dafa komai ba,saika jira in an gama na dare na karbo maka"
"Ke Wai ina wancan shedaniyar yar wiwi dinne,tunda na dawo ban ganta ba"
"Me kake ci nabaka na zuba zaka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login