Showing 36001 words to 39000 words out of 62773 words

Chapter 13 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4442

suna fadan isowarsu.
Irin tabarmar karauno aka shimfida ga kuma kindirmo(nonon shanu)da kuma kaji da aka dafa saboda taryarsu,dan kowa yasan mutunci irin na inna hajara shiyasa komai idan daga wajenta ne toh yan uwanta basa kyashin nuna tasu bajintar,saidai marar nuna godiyah ya kushe musu,irin su saleemah dan fafur kin saka wani abu a cikinta tayi,itah a dole wai jagwalgwalone,sukuwa su sameer zama sukayi suka ci abincin sosai.
Dan duk duniya sameemah babu wanda take ganin mutuncinsa badan yah tursasata ba ya mahaifin ummah ta wato Malam Mansur,saboda ya nuna mata soyayya matuka,musamman idan suka zo da inna hajara a wajensa take zama har su tafi yana mata labarai da kuma jan kunne,duk da bata so amma tana kokarin ce masa zata gyara.
Mahaifiyar su inna hajarance ta zauna ana gaisawa Sannan wani lokacin idan ana tadi sai a dunga sako irin abubuwan da inna hajaran tayi a baya,sameemah ce tayi kuncin da fuska can kuma da taga abin bazai yiyu ba said tace,
"Nikam iyah in san samu ne kidaina sako ummah in kina yin zanjenki kiyi zancenki kawai,bai kamata zance marar amfani a dunga saka ta ba gaskiya"
Baki ta sake tana kallon sameemah wanda ta hade fuska tana wani bada umarnin a daina zancen ummahn tah,
"Iyeee lallaima yarinyar nan toh kinci gidanku,bazan daina zancennata ba idan yar kice ke kika haifeta"
"Toh ina ummah tace koh,to nace a daina haka kawai sai a dunga zancenta a kan abu marar amfani,ko kuma a dunga bada labarinta ga mutum marar amfani,hakan bai daceba"
Sameer ne ya kalli sameemah wanda ta wani hade rai tana zuba tijara,sai a sannan ya gano meyasa take fadan,dan kawai an fadawa saleemah labarinta ne yasa take wannan tsiyar,jijjiga kai yayi yana Mamakin yanda yarinyar ta zama bayan tafiyarsa,kwata kwata ta koma kaman an sanja ta.
Malam mansur ne ya shigo daga gona da fartanya a rataye a kafadarsa,
"Lahh baki mukayi a garin,wa nake gani kaman sameer,ko dai gizone yake min kai?"
Iyah ce ta amshe da cewar,
"Ba gizo bane shine yazo da matarsa gashi nan,wata sabon gani a garin zariyah"
"Toh madallah sannunku da zuwa yah iyalai tunda naga an fara tarawa koh?"
Sunkuyar dakai sameer yayi yana sosa keyah kafin yace,
"Iyalai alhamdulillah,mun sameku lafiya dai ko"
"Lafiyah alhamdulillah,yah iyalinnan ka bata magana ne"
Kunya ce ta kama sameer da halin saleemah na rashi girmama mutane,dan duk abinda ake idonta akan malam din amma gaisuwa ta kasa hadata dashi,shikuwa irin mutannene masu nuna wa mutum kuskurensa sannan bayason raini ko kadan shiyasa ko wasan kaka baya yi.
Jungurarta yayi yana mata alama da ido,saida taga ransa ya baci kafin ta gaisheshi tana wani yah tsina fuska.
Shima dayake baya daukar raini amsawa yayi ciki ciki kafin yayi hanyar dakinsa.
Iyah ce takallesu tareda cewa,
"Zaku kwana mana ne koh kuma akan hanya kuke kaga saimuji mai za'ayi"
Saleemah ce ta washe bakinta dan dama tun dazu take so taji anyi zancen tafiyah,tun kafin ta bude baki sameemah tayi saurin cewa,
"Eh iyah kwana zamuyi mana ba yau zamu tafi ba"
Takaicine da mamaki ya cika saleemah lokacin da taji abinda sameemah tace,shikuwa sameer a bangaren sa bai damuba duk yanda akayi dayane,saidai shima yayi Mamakin sameemah amma yasan da biyu tayi hakan,dan saleemah taji haushine.
Dakin dayake gefen iyah aka gyara musu domin su kwana shikuma sameer ya shiga dakin malam din.
Katifa dayace a dakin ta bunu saikuma tabrmar karauno,a tare suka shiga dakin su biyu kowa yana karewa dakin kallo,saleemah ce ta bude baki tana kallon itacen da akayi rufin dakin dashi ga kuma yayi kasa kaman zai kifo a kanta,hannu ta kai tana taba plastar kasar da akayiwa daki da kuma wanda akayi a kasan dakin.
Bata ga komai ba saida aka zo kwanciya ta dora hannunta akan katifah taji wani tauri kaman buhun siminti,ja tayi da baya tana zare ido tareda cewa,
"Nikam gaskiya bazan kwanta akam wannan abunba ,wannan ai saina tashi da ciwon jiki gobe"
Jin abinda ta fadane yasa sameemah kara matsawa ta baje akan katifar sosai yanda babu wamda zai iyah sake kwanciyah akai idan ba jinjiri bane,wata uwar hamma taja tareda juyawa da alamar bacci zatayi.
Saleemah tafi kusan awa daya a tsaye itah bata kwanta ba itah bata zauna ba,ganin yanda kafafunta suka fara gajiyah ne yasa ta zaunawa dabas akan tabarmar tana karewa sameemah kallo da take kwance a akan gadon cikin takaici.
Kwanciyah tayi akan tabarmar saidai koh minti uku batayi ba ta tashi ta zauna,saboda yanda taji kaman a saka ta a kabari,bubbuga katifar take akan sameemah ta tashi amma tayi shiru kaman dutsi.
Har ta juya zata kwanta kuma sai taji motsin wani abu a dakin,bata kawo komai a ranta ba ta gyara kwanciyarta da niyyar yin baccin kawai.
Wani katon abu taji akanta amma bai kai kuliya ba saidai katone,ihu tasaka tana kakkade jikinta,shikuwa beran tuni ya fice a dakin.
Jijjiga sameemah take tana hawaye amma shiru babu alamar ma zata motsa,da haka tana kukan bata san lokacin da bacci ya dauketa ba.
Da safe da ta bude idonta a kasa ta ganta kayanta sunyi futu futu da kura saboda artabun da sukayi da berayen dakin,sameemah tah kallah wanda ita ma tashinta kenan tana mike hannu babu ko salati,saleemah ce ta kalleta tareda cewa,
"Jiya kika tare katifar ina tashinki amma baki jiba ga kuma wasu abubuwa a dakin koh"
"Ina jinki rass ba bacci nayi ba,dariyah ma nakeyi har kika gama kukan kikayi bacci"
Da sauri Saleemah ta zabura daga inda take zaune kafin tace,
"Dan tsabar iskanci dama kina jina ina tashinki kikayi shiru?"
"Toh uban me zan miki,goyonki kikeso nayi ko me?"
"Amma dai ................."
"Kinga karki dameni da surutu da sassafe nan,ajiyarki aka bani mtsewwww".
Tun daga haka babu wanda yasake magana acikinsu har suka fito karyawa wajen iyah.
Anan ne suka hadu da sameer wanda shima ya fito daga dakin malam.
Gaisuwa aka farayi itah kuwa saleemah sai shagwaba take yiwa sameer ko kunya bata ji.
Kaman mai zargin wani abu sai sameer yace,naga dakinku shiru kunyi bacci mai dadi koh?",iyah ce itama tace,
"Lallai kam dan naji da asuba ma shiru basu fitoba"
Kunyah ce ta kama saleemah amma sameemah koh a jikinta saima kokon da takai bakinta a karo na biyu,fada sameer ya fatayiwa saleemah ta inda yake shiga ba ta nan yake fitaba,wanda yana cikin fadan ya kalli sameemah da niyyar bata itama nata kason,sauke kofin tayi kafin tayi saurin cewa,
"Karka tambayeni komai ,saboda ba'a tambayar mace tayi sallah,yanzu zaakji kunya da jin amsata kuma ba abinda ya dameni ehe,(kiji maman najwa mutumiyar taki koh,dan ma naga su yah kubrah suna yi mata nasiha,da kuma su zuzunmasta,batayi sallar ba kuma fah?🙄😲,gashi kalau take rasss).
Malam ne yayi gyaran muryah ai kuwa kowa yayi shiru aka cigaba da cin abinci.
Bayan sun yi wanka sun shirya saida suka shiga gidan kawunsu wanda suke uwa daya uba daya da inna hajara kuma kaninta.
Surfe sukeyi a tsakar gidan matannasa lokacin dasu sameemah suka shiga,gidane mai fili sosai saidai sun shareshi kall abin sha'awa,iyah matannsa suka gaisar basu sameshi ba ya tafi cikin gari cin kasuwa,kudi sameer ya rabamusu sai godiyah sukeyi da saka albarka.
Shikuwa malam mansur lokacin da suka zo tafiyah kayan gona ya hada musu irin su wake da gyda ,da yake lokacin kaka'a ce,amfanin gona ya dawo gida.itama iyah tayi kokari,dan jarkoki ta cika musu da kindirmo da kuma shima man shanu ciki leda,godiyah sukayi sosai dai kafin suka kamo hanyar dawowa gidan.
Wayar sameemah ceh tayi kara inda tafara magana cikin tsare gida,
"Bance kuyimin shirme ba ina dawowa in anjima dinnan,ka saka wani yah wankemin motar nan kafin na dawo dan akwai aikin da ban kammala ba na shekaran jiyah,sannan ku tabbatar yarinyar nan kun kula da itah yanda ya kamata,idan har nazo naga ba yanda nace ba duk ranku zai baci..................yadai fi muku,ina zuwa yanzunnan"
Tana sauke wayar suka hada ido da sameer tah madubi yana kallonta da alamar tambaya,itama dayake tasan yau kawar da idonta tayi kaman bata san yana kallonta ba.
"Wace yarinya kike magana akai,yar gidan uban waye?"
"Yar Gidan uban wani ce mana"
Tsayar da motar yayi yana huci jijiyiyin jikinsa sun tashi sunyi wani rudu rudu,saleemah ceh ta make a jikin kujerar ta ganin yanayin daya shiga,sake kallon sameemah yayi ta cikin madubi har idonsa sunyi kala,
"Me kike nufi,bayan abinda nakeji na dabanci har kidnap din yara kikeyi ashe?"
"Yanzu idan kidnap dinne ina ruwanka dan farouq na dauke ko me,ni banaso ana min katsalandan a rayuwata,akwai wanda yake daukar dawiniya tane,ko kuma kayanka na taba kake tada jijiyar wuyah,saika bari idan na taba naka sai kamin abinda ka ga dama mtseww"
Tun kafin ta gama tsukar yah kifa mata mari a fuska,abinda ba'a taba yimata na tunda take bayan ta girma,kallonsa take da idonta wanda suka fara canja kala zuwa jawur,saurin rufesu tayi dan tasan a lokacin idonta sun fita daga kalar dasuke,sannan tana koarin saita rawar da jikinta yakeyi.
Shikuwa juyawa yayi ya tashi hanyar suka cigaba da tafiyah,har sannan bai daina masifa da kuma kirafin halayyarta ba na raini da kuma rashin kamun kai.
Tana jinsa duk abinda yake fada saidai a lokacin ba tashi takeba tukunna ta hucin da zuciyarta takeyi take tukunna.

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03

❤23❤


Suna isowa kofar gida tun kafin yah tsayar mota sameemah tayi saurin ficewa daga motar kaman ana harba ta ceàudirect zuwa kan gadonta,ta dade a kwance kafin ta dago saboda ringing da wayarta tayi,saida ta ga mai kiranne kafin ta tuna da cewar ashe tana da wajen zuwa fah.
Cikin yanayin daga mutum yagani yasan tana bukatar hutu amma hakan bai hanata tashi fita wajen ba.
A bakin kofar gidan suka hadu da burgu ya kawo mata motar da ta bayar a wanke,karbar key din tayi ta su ka shiga sai gidan horonta inda ta bayar a ajiyemata yarinyar.
Kofar wajen a bude suka ganta hakan yabawa sameemah mamaki saidai bata ce kkmaiba sai shiga gidan da tayi kawai .
Su mungun dawa ne a zaune sun baje suna karta,saikuma wata yarinya a tsakiyarsu itama da katin wasan a hannunta,wani saurin bugawa tayi tareda tsalle tana murna saboda nasarar da taci a wasan.
Babu dan kwali a kanta sai dogon gashinta madaidaici wanda ya baje saboda rashin daureshi da ribbon,dogon wando ne a jikinta da kuma riga t-shirt bak'a anyi mata adob fari.
Dukkan su surutu suke basu damu da tsayuwar sameemah a wajenba wacce ta kama kunkumi tana kallon ikon allah.
Saida burgu yayi magaana kafin kowa yah nutsu ciki harda yarinyar da take tsalle da murnar cin wasan,mungun dawane yah gyara murya kafin yace,
"Eh wato dama shugaba abinda yafaru shine,itah yarinyar ce wai gwanda da muka daukota kuma zatayi vidion anayimata azaba ma kodan yasaka hannun,wai dama ya takura mata"
Dakatar dashi sameemah tayi tareda cewa,
"Banason wani shashancin zance,ba abinda na daukota dan nayiba kenan,tsakaninta da shi bai dameniba"
Matsawa baya yayi jin mai tace,matsawa kusa da yarinyar tayi tareda cewa,
"Menene sunanki inason jin takaitaccen bayani game da tarihinki"


*true life story ne na yarinyar wanda yah faru da gaske,saidai zan kara wani abu ba kaman yanda aka bani labarinba,amma zan sanja suna saboda yanayin tsaro*



"Sunana Surayyah kuma ni kadaice a gidan mu y'a mace,sannan kuma nice ta karshe a gidan wato y'ar auta,Saida mafi yawan yayuna suka girma har suka zauna da kafarsu kafin aka haifeni,Akwai soja ,yan sanda,morpol custom da sauransu,kuma dukkansu yawanci aikin d'amara sukeyi.
Mahaifiyar mu bata yimin fada dukkan abinda nakeso shi nake,gashi allah yah yini da rawar kai kuma da farin jinin mutane,sanadiyyar rashin mutuncin danake yi a gari ina jawomusu abin magaan yasa suke yimin horo mai tsanani,amma duk a banza ina warkewa zan koma.
Haushinsu nakeji kaman na kashesu,inaso naga suna bani kudi sosai amma babu wanda yake bani komai,dan haka ni koma menene zanyi idan ta kama ma kuce saceni kukayi,suna da kudi sosai kuma nasan su abba zasu tashi hankalinsu har sai an bada kudin.
Nima saiku dan bani nayi harkata"
"Toh naji labarinki saidai ban daukoki dan nayi kudi dake ba,na daukoki ne dan nasa yayanki yayimin saigning akan wata paper game da wani aikina.
Batun kudi kuma zaki iyah yi dakanki,saidai abu daya zanyimiki ,nayi niyyar dan taba lafiyarki dan yasan da gaske nake,amma tunda naga kema da hannunmu ce zaki iyah yin pretend a matsayin mun dakeki saboda abin ya tafi miki a sauki"
"Toh shikenan naji shugaba,amma inaso na zauna a cikin kungiyar nan,saboda nima nayi zama a cikin yan daba a unguwarmu"
"Ahah ban karbekiba ,baki cika abinda nake bukata ga yan kungiyata ba,saboda ke kina da yadda zakiyi wato bin maganar yayunki,amma idan har kika karbo saka hannunsu a paper toh wato sun amince toh zan karbeki,yanzu zan kira creator yah sanja mikk kama irin na wanda yasha duka,zamu fara buga wasa da yayanki tunda naji shima dan taurin kai ne"
Bayan wasu mintina kuwa mai kwalliya yazo,inda surayyah ta zauna aka gama kirkirar ciwo kala kala a jikinta,kai kace dama ciwon gaskene.
Lesson na dramar dazatayi aka fara bata kafin lokaci n action din yah fara.
A can gida kuwa su mahmood in hankalinsa yayi dubu toh ya baci,saboda batan layar zanar da surayyah tayi tun shekaran jiya,babu kuma labarin ta ko kadan,tun abin suna zaton karamine har yazama babba,kuma shi kadaine babba wanda yake garin,sauran dukkansu suna garin aikinsu.
Karin abun ma kuma mahaifiyar su da ko abinci taki ci sosai dole sai an kawo mata yar ta.
Yanzun haka yana tsaye a cikin gidansa itama matarsa tana nata korafin na kudin ankone ya ga kiran waya,da bazai daukaba saboda bakuwar lamba ce,kuma layinsa na gida aka kira ba na aiki ba amma duba da yanayin aikinsu ga kuma dama kanwarsa wanda yakeji kaman yah hura wauta yasaka ta ita ma ta bata.
"Salam wa yake magana"
Muryar wanda yajine yasa shi sauke wayar na yan sakanni,saida ya dan washe da Mamakin kafin yamayar da wayar kan kunnensa,
"Eh nine ,kina magana da mahamood ne"
"Dama nasan dashi nake magana ai,basai nayi maka bayanin waye yake magana ba,dan daga yanda ka sauke waya na wani kankainin lokaci nasan ka ganeni,dama nakira na fada maka ne cewa;kanwarka da kuke ta wahalar nema tana wajena tun shekaranjiya,idan kuma ta cika adadin danake jira banji kayi abinda nakeso ba,toh har Iman(yarsa)da kuma uwarta zan hada na yi gaba dasu,saika zaba koh su kokuma takardar wajenka"
Komawa statue(gunki) yayi kafin yah saita saboda yin magana,
"Uhm naceba amma taya zan san.........."
"Karka damu ga vedion ta nan yana shigo maka,gobe nakeson kayi saigning din,saboda akaita wajen manya da wuri,mukwan lafiya a ci gaba da rarrashin tsohuwa"
Sauke wayar tayi tana kallon surayyah wanda ta daina kukan karya da rausaya jikin lokacin da aka dauke camera daga kanta,saidai kuma akwai alamar bataji dadin maganar da akayi ba,saboda ta so a tambayi kudi masu yawa ko ta samu kasonta,amma ji yadda aka tsaya akan wata paper ta banza,cuna baki tayi tana kukkumbura fuska itah a dole ga sakaliyah.
Tsawa sameemah ta daka mata duk da bawani finta tayi da yawa a haifeba,amma yanda takeyi kai kace itah ta haifeta,
"Banason shashanci,nariga na fadamiki abinda nake da bukata karki sa nayi magana biyu,kodan kinga ina miki gentle,toh wallahi sa'a kika ci,dan koh shi yayannaki banason sakashi dole ta wata hanyar ne da tuni an wuce wajen.
Ki shirya gobe watakila zaki koma gida,dan nasan zai yi signing ko daga jin yanayinsa"
"Amma nace miki inasob shiga kungiyar nan fah"
"Saikin kawo saka hannun yayunki ko iyayenki,idan ba haka ba karki bari musake haduwa dake,bazaki ji da dadi ba kwata kwata "


Tana fita daga gidan horon bata zarce ko ina ba sai club,dan yau yanda yayannata ya bata mata rai tanajin idan dai ba shaye shaye tayi na fitar hankaliba toh akwai matsala babba,dan shedanun kanta babu abin da suke bukata sai jinin wanda yah bata mata rai a lokacin,saidai idan har ba babbban kuskure mutum yayi ba toh bata yimasa irin wannan hukuncin.
A table din dayake karshen club din ta Zauna tayi shiru kaman mai nazari,muryar wani gaye taji yana yi mata magana,amma ko daga kai batayiba har ya gaji ya zauna dan kansa.
Bartender (mai kawo odar)ce ta zo da book list a hannunta,tambayar sameemah ya shigayi akan mai takeso,itadai bata kalleshi ba sai nunawa da tayi da hannunta kan abinda takeso,dayake tasan mai sameemah tace ,wucewa kawai tayi domin isarda bukatar customer dinsu.

"Yan mata ina ta magana amma bakice komai ba,gashi da alama kina cikin damuwa,koh zamu dan yi dance ne ina ganin zakiji kin dan sakko,ko kuma bari nayimana oder wata zazzafar giyah yanzu zakiji kin daina jin abinda kike ji,"
Har yayi surutun yagama sameemah bata dago tackalleshi ba,saima wasa da farcen hannun ta na dama da takeyi,abinne kaman yafara isarsa hakan yasa ya cigaba da magana,
"Beb bakice komaiba,bai kamata ki dunga jin haushiba da irin wannna kyawunnaki ya kamamta kiji dadin rayuwarki gashi kuma......."
"Kai bakone a cikin garinnan?"
"Eh nazo wani aikine meyasa kika tambaya"
"Saboda nasan da kasanni bazaka zauna anan ba,dan haka ka bace ka bani waje tun ban huce a kanka ba gaye"
"Amma beb hakan bai miki kyau ba sam,sunana Tukur ana cemin TK,ke ya sunanki"
"Dama ni na tambayeka sunanka ne ,bare ba fadamaka nawa sunan"
Suna cikin hakanne matar ta dawo da wata yar karamar kwalba an nade samanta da leda said kumu murdaddiyar wiwi suma kusan goma a kan wani plate,tun kafin ta ajiye Tk yake Mamakin wanene yake shan irin wannan giyar mai karfi anan garin.
Saida yaga an ajiye a gaban sameemah kafin hankalinsa yakoma kansa dukka.
Yar karamar kwalba ce amma babu wanda zai iyah shanta haka ba tareda ya sirka ba,idan kuwa ba haka ba mutum zai iyah shiga coma ko kuma yayi akallah sati daya bai tashiba idan yayi sa'a.
Mantawa tayi da wani jarababbe a gefenta saima bude kwalbar da tayi tana zubawa a cikin bakinta har zuwa makogaranta.
Shikuwa gogan kaman television haka ta KO ma masa,koh A bai sake cewa ba har ta sauke kwalbar ta kuma dauki kwarkwaro daya na wiwin tana kyasta masa lighter.
Busawa take hankali kwance saidai duk wanda yake kallon idonta yasan akwai sauran bakin ciki a cikinsu.
Sun dad'e a wajen a zaune har sannan bai gaji ya tafi ba saima kallonta dayake tayi har takusa tashi da wiwin itama,lokacin dare yayi sosai dan a kalla shabiyu zata kusa gotawa,tashi yayi ya bar wajen koh sallma bai mata ba,itama kuwa bata kukashiba har ya fita a cikin club din da Mamakin ganin ko layi bata faraba bare kuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login