Showing 39001 words to 42000 words out of 62773 words
bacci ya dauketa na giyar.
Sameemah bata tashi daga kujerar da takeba har saida ta ga babu ala mar wiwin da gama da su tukunna,fitowa tayi ta nufi motarta tana wani rausaya idonta har wani sanja kala yakeyi.
Figar motar tayi duk da darene amma hakan bai hanata fara rage haushinta akan motar ba.
Wata kwana tayi ta shiga layin gidannasu babu kowa sai filin wajen,a gefen motar sameer ta faka motar kafin ta fito tareda rufeta.
Har takusa shiga cikin gidan said kuma taji kaman alamun mutum a bayan ta,tsayawa tayi domin jin menene zai faru,gyaran muryarsa taji amma duk da haka bata juya ba,shima kuma zo gabanta ba din ,duk da yasan ta gane waye yake bayannnata.
"Daga ina kike da wannan daren,wanda in namijine ma yanzu yah koma gida,tun dazu kowa ya shiga gida har mazan amma ke sai yanzu zaki dawo?"
Juyowa tayi suna kallon kallo itah dashi babu alamar maganar dayayi mata ta shigeta saima haushi da maganar tasa tayi mata,
"Daga club nake,shiyasa kaga nayi dare ko kana da business akan hakan ne"
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤24❤
"Daga club nake ko kana da business kan hakan ne,har yanzuna sai wani ya fadamin abinda zanyi,abinda naga dama nakeyi sannan banason wani yah dunga shiga lamarina,lokacin da wasu zasu fadamin mai zanyi yah wuce yamzu nice da alhakin jan ragamr rayuwata saboda nikadai nasan yadda nake fiye da kowa"
Duk da karamar riga ce a jikinsa amma kana ganin yanda tsokar jikinsa ta murde saboda maganar da sameemah take yimasa,cikin zafin na ma kuwa yasake kifa mata wani marin har saida tayi baya amma ta tirje da kafafunta,
"Ke Wacce irin yarinya ce,har ana cemiki daga inakike kina cewa wai daga club kike,gani kike abinda kike na arzikine,ko kuma rashin hankali,dakike cewa kinada hankali toh ko dabba bazayyi abinda kikeyi ba ,sannan nasake ganin kina mayar min maganar son ranki tana fitowa daga bakinki kina fadamin,idan bakiyi wasaba saina karyaki a gidannan kafin na tafi shashasha kawai"
Saida ta bari yah gama fadar duk abinda yake bakinsa kafin ta dago da idanuwanta wanda farin cikin idon ya koma jawur kaman garwashin wuta,saida ta cije bakinta har fatar bakinta tana fashewa saboda bakin cikin dayake cikin ranta kafin tace,
"Sameeeeeer!
Sameeeeer!!
Sameeeeer!!!
Idan har kanaso ka cigaba da tunanina a matsayin kanwarka da kake da ita guda daya cikin kaunar rai toh kadaina shiga rayuwata ,bare har hannunka yasake taba fuskata,kayi na farko dazu yanzu kayi na biyu toh karka sake na uku,saboda hukuncin dazai biyo baya bazai yiwa kaff yan gidan gandu dadiba,har ummah da take makwancinta bazata yafemin ba.
Dan haka tun ina iyah rike kaina duk da hakan yana cutar dani toh karka kara,kaci albarkacin umma dan haka karka sake shiga sabgata na fada maka,ka dauki matarka ku tafi kuna cikin koshin lafiya. Wannan gargadine idan kaji da kyau idan kuma ba haka ba .....................hmmmmmm"
Dunkule hannunta tayi jikinta har rawa yakeyi ta shige cikin gidan ta barshi a wajen yana wasiwasin abinda tayi.
Gogar kuwa tana zuwa ruwa ta diba tafara tuttulawa a cikin bakin ta tana jijjiga kai,saida ta gama ta fada kam gado tana ritse ido da karfi,dahaka can wani lokaci bacci ya dauketa mai nauyi sosai.
............kallonta take a wata duniya daban mai duhu,sadai daga ganin idonta dama tah saba zuwa wajen ba yau ne na farko ba,kayan jikinta ta kallah jawur da su ,saida ta daga ido taga suma wanda suke wajen haka kayansu yake,saidai itah nata anyi masa hoton wani katon tattoo a tsakiyar rigar irin na jikin kayan shugaban dayake kan kujerar,
"Koyaushe cikin saba doka kike,babu wani ruhi daga cikin mu dayake saba doka saike,kuma kedai ce a tarinhimu kike saba dokar shugaba amma yake kyaleki dan haka ki shiga hankalinki"
"Idan naki fah ,wai me hadina daku ne wai,akan uban me zan dunga bin umarnin naku,shidin yayanane kufurinku shine kusakani kashe duk wanda ya bata min rai ciki harda ahalina,to kun makara dan yanzu na koyi control din hankalina ba kaman shekarun baya na lokacin ina Brazil,sannan ai bance ina cikinku ba ai"
Tana gama fadin hakan ta kama rigar da take jikinta da karfi ta cireta,aikuwa cikin kankanin lokaci hankalinta yah koma iyah cikin bacci kawai,da haka baccin gaske ya dauketa bayan ta bar wajennasu.
Kwana sameer yayi yana tunanin yamda sameemah tayi masa magana,abin haushi ya bashi ganin yamda take taka kowa san ranta.
Tun kafin kowa ya tashi saleemah ta tashi ta gyara danta saboda tafiyah,dan itah gidan ya isheta musamman sameemah da tsoronta takeyi yanzu tun sanda akayi dramar mota a gabanta,kuma ta dau kudurin babu ita ba garin zariyah har abada,musamman wannan yankin nasu da babu komai sai yan daba,ta tashi a cikin sojoji amma bata tashi a cikin mutanen da babu wanda yake ganin mutuncin na gaba dashi ba.
Shima sameer bayan yah karyah fitowa yayi suka gama sallama da mutanen gidan ya kama hanya.
Gogar kuwa sai wajen bayan azahar kafin ta tashi tana mutstsika ido,hada ido sukayi da karen ta bingo yana saki baki,hannu ta mika masa yazo yana shanshanata,
"Oh Baku ci abinci bane,bari na tashi dama akwai wajenda zanje na manta kwatakawata"
Sakkowa tayi ta fito daga dakin tana hamma da kuma mika,da baba umaru suka hadu a tsakar gidan yah dawo daga gona,kallonta yayi tareda jijjiga kai,koh gaisheshi batayi ba kuwa tayi hanyar bandaki,dan dama idan ba yan muyuncinne suke kusa ba koh gaisuwa bata hadasu da yan gidan,
"Ke sameemah ni kun yi sallama da yayannaki ne?"
"Ahah "
"Ya tafifa dazu da hantsi kuma bakuyi sallmaa ba"
"Sallama kuma,saikace wasu yara,yafi masa ma dan wallahi daya ga yanda ake iyah shege,kuma hankalinku yah kwanta"
"Tabbbdi lallai yarinyar nan,yanzu dan uwannaki kiyi shekara da shekaru baki ganshi ba saida ya tafi bakuyi sallama na kike cewa yafi hakan"
"Baba bazaka ganeba ne a bar zancen kawai"
Shiryawa tayi cikin atamfa anyi mata dinki simple na doguwar riga,sai daurin ture ka ga tsiya da kuma gyalen rigar a kafadarta,tayi kyau sosai dan ba karamar kyakykyawa bace (kyan dan macijiba)kuma tafi saka abaya,ko kuma riga da wando,haka in bata ga dama ba sai tayi sati bata daura dan kwaliba sai gyara gashi kawai takeyi ta daureshi.
Hanyar waje tayi su bingo suna biye da itah a baya,kicibis sukayi da manjo yana shigowa,yah saka wata babbar riga wanda takusa ta yadi goma,a ina ya samota oho,dan dama manjo ba dai shigar hauka ba,taba ce a hannunsa tana hayaki ga kuma wani kwalli dayasha kaman dan farauta,
"Yawwa ke dama ina nemanki zamuyi wata magana"
"Wacce maganar ka bari saina dawo akwai wani abu dazanyi manage yanzu"
"Ke ni zakice zakiyi wani mange(manage),maganar muhimmancin nima nake tafe da itah"
Har zatayi magana saikuma ta gyara tsayuwa tareda cewa,
"Ina jinka manene"
"Ehe yawwa zancen soyayyarki keda sule maye,inaga maganar zatayi karfi tunda ni yayanki nashiga ciki,yanzu hak nace yabani sadakinki dubu talatin,kuma yabani duk da ma na dan ci dubu biyar a ciki,kinsan sha'anin rike kudi abinka da mutum mai dan uzuri,hhhhhhh amma tunda naga yana sonki sosai nasan zai karo cikaton kudin.
Kai dole ma ya ce yanason ki duk da irin tantirancin da kikeyi ,akwai kyau ne musamman idan kikidau wanka"
"Toh yanzu dai kagama magana mai muhimmancin ko kuma da saura har yanzu kai"
"Ke kina rainani fah,dama sanda na dawo kulu tacemin kin mata rashin kunya kyaleki kawai nayi saboda sule abokina yana sonki"
"Allah koh,haka akayi kenan,duk zancennan ka barsu idan na dawo sai muyi shi"
Jijjiga kai kawai tayi tana Murmushin mugunta ta shiga mota suka tafi itada karnukannata.
Wajen da ta ajiye surayyah ta tafi domin jin yanda ta kaya,yauma a zaune take saidai dayake su mugun dawa sun tafi aiki daga itah sai C.I.D shikuma bashida magana sai leken asiri koh bera ya sara masa.
Sameemah tana shigowa surayyah ta tashi tana gaisheta duk da a gida koh uwarta sai taga dama take gaisheta.
C.I.D ne ya matso tareda yimata bayanin abinda yah faru dazu,mika mata wata takarda yayi yana cewa,
"Ranki ya dade ga wannan paper burgune ya kawota dazu wai yayan surayyah ne yabayar,yayi signing din yaan neman a sake masa kanwarsa,tun dazu muje jira ki iso gashi kin ce kar wanda yakiraki shiyasa na zauna ko zaki zo"
"Okay shikenan babu matsala,zaku iyah maida ta gida,amma ban yadda tasan wane waje take ba,na gama da wannan shafin"
Saida ta gama kallon signing din ta tabbatar shine kafin ta rufe paper cike da murnar nasarar da ta samu.
"Amma shugaba nafadamiki cewa nima fah a nan wajen zan zauna"
"Eh kuma nima na fadamiki idan baki kawo signing din yan uwankiba bazan daukeki ba ai,koh kin mantane?"
Sunkuyar da kai surayyah tayi cike da jin haushi saidai ta kudiri aniyar karbo izini dan itah taga wajen zama inda yayi dadai da ra'ayinta.
Wani bakin kyalle aka saka mata a idonta har sannan sai cuna baki takeyi wai sameemah bata yadda da itah ba,ita kuwa ko kallonta batayiba har su ka isa kofar gidan yayannata a mota,C.I.D yah fito ya budemata kyallen fuskarta da kuma motar kafin ta fito,cikin gidan yayannata ta shige koh kallon sameemah batayiba.
Suna ganin shigewarta gidan suka bar wajen.
Mahmoud ne a zaune shida matarsa haka ma iyayennasa suna zaune a daya kujerar kowa yayi jugum sun rasa ma me zasuyi,ko sallama surayyah batayiba haka ta shigo tana wani cika,dukkansu tashi sukayi suna kallonta da mamkin ko kwarzana babu a jikinta,bayan hoton da aka turomusu duk jikinta ciwone.
Mahmoud ne yafara cewa,
"Ke ya na ganki kaman babu abinda yasameki baayan jiya video da suka turomin nishi kike yi kaman zaki mutu"
"Ba abinda suka min,duk nice nayi saboda su saka ka bada kudi,dan cewa nayi zan taimakesu,amma wannan shugabar tasu ta ce wai bazata karbi kudiba saka hanunuka kawai take bukata a wannan paper"
Da bakin ciki sir Mahmoud bai san lokacin daya zabga mata mariba da kuma yin boll da itah,kuka ta rusa tana kallon ummahn ta,itama kawar da kai tayi da a wannan fadan babu dama tayi magana dan surayyah ce bata da gaskiya.
Haka ya dak at a saida tayi lis tukunna ya barta.
Cikin sheshshekar kuka tace,
"Kuma an taimakesu din,naga inna ce ka bani kudin hanani kakeyi,ka bawa su yaya Najeeb,kuma koh kasheni zakuyi saidai kuyi,ni yanzuma idan nasamu dama wajenta zan koma aiki.
Dan takaici shigewa daki yayi kaman zai tashi sama,itakuwa mahaifiyar su ce tazata daga kwancen da take tace,
"Gaskiya bakyaji surayyah,duk wuyar dayasha ganin kin fito ashe da hannunki a ciki,saiki tashi mutafi gida ai kafin ya karisa ki"
Da haka uwar ta jata suka tafi nasu gidan,shikuwa uban dama dayajj abinda yafaru tun da farko yabar gidan.
A cikin mota kuwa sameemah ce ta kalli C.I.D,tace,
"Kafadamin inda zan ajiyeka dam akwai wajen da zanje daga nan"
"Ahh KO Ina ma kika ajiyeni duk dayane"
Fakawa tayi gefen hanya ta saukeshi kafin tayi hanyar gidan alhaji bala direct,tun kafin ta kai ga shiga cikin gidan tayi wani murmushin migunta.
Da shirinta tazo dan jiyah C.i.d ya fadamata duk wani shiri da alhaji balan yakeyi akanta,kuma dama tayi tunannin hakan,dan a rashin muyumci irin nasa,da kuma itama irin tsiyar da tayi masa tasan bazasu kare iyah hakaba.
Shi bazai fasa daukar fansaba itama kuma bazata daina yaki ba har sai ta hau kan kijerar shugabar vigilantee tukunna,saboda tarihin da takeso ta kafa bazai tafiba saida wannan kujerar tukunna.
Danna kai tayi cikin ainihin gidansa kuma tasan yanannan. Mai gadine ya bude mata kofa ta shige kafin yamayar da get din yah rude.
...........hmm mm D'an sa ma yadawo yana nan.😂🤣😂
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤25❤
Saida ta gama saitawa kafin ta fito daga cikin motar,hanyar dazata kaita cikin gidan ta nufa tana wani shekar iska.
A bakin kofar tayi sallama wata mata da alama mai aikice ta amsa mata,
"Matar Gidan tana cikine?"
"Eh hajiya tana nan bari nayimiki iso da itah "
A kujera ta zauna kafa daya kan daya,wasu samarine suka shigo guda biyu suna ta magana,har saida sukayi wata hanya kafin daya daga cikinsu ya kula da itah.
"Lah umar wallahi wannan zazzafar yarinyar danake fadamaka na hadu da itah a club toh wannan ce"
Yafada yana nuna sameemah,itama kallonsa tayi sau daya dan taganeshi sarai,shine yace mata sunansa tukur. Cigaba yayi da magana tareda tsayar da ummaruje a waje daya.
"Kai ban gane ba fah ko yar uwarkuce,naga ta sake a falon daga gani ba zuwanta na farko ba kenan"
Da yayi niyyar share abin amma daga kallonta dayake shima dan duniyar ne,cikin sakanni yaji ya fola mata shima.
Komawa falon sukayi suka zauna,ummaruje ne ya daga girar barin dama yana lashe baki kafin yace,
"Yan mata me ne sunanki,abokina yace kun hadu a club daga gani kema yar hannunce wato ta hannun damanmu"
"Like father like son"
Sameemah ta fada a ranta,dayake ta sha kansu iyah rashin mutunci,kara daga kafarta tayi tana wani jijjiga ta irin ta shegun matannan,saida tah ciji lebenta ta gefe da hakoranta kadan kafin tah kashe murya tana cewa,
"Uhm Wai ni sunana sameemah saidai banji sunan gwarazan mazanba kuma?"
Ummaruje ne yah washe baki har kunne kamar gonar auduga kafin yace,
"Sunana umar,ina karatu a abroad sannan nan gidanmune kuma nikadaine a namiji a wajen babana sai kanwata da tayi aure"
Yah karisa magana yana kafafa,shikuwa a bangaren Tk mamaki abin yabashi domin yasan haduwarsu ta baya da itah batayi kama da wannan da take zaune ba,shikansa badan yagane fuskar ba zaice sanja ta akayi,waccer fuskarta banu annuri ga kuma uban shaye shayen da tayi,amma wannan idan ka ganta saika ce ai batasan menene fushi ba,dan fuskarta sai murmushi takeyi da annuri.
Hada ido sukayi da Tk da kuma sameemah,wani kallo tayi masa na alamar gargadi,cikin sauri kuwa yah sauke idon tareda wayancewa yana dariya.
Suna ta tadi dukkansu babu wanda yah kulada zuwan alhaji falon shiga hajiya Mairo,jerowa sukayi ko wannensu kaman zai fashe dan kiba,musamman ma hajiyah mairo sai huci takeyi.
Tsayawa su sameemah sukayi da tadi ita da ummaruje wanda ya zare sai surutu yakeyi kawai dan yaga wannan kyakykyawan Murmushin a fuskar sameemah.
Hajiyah mairoce ta tambayi ummaruje tareda cewa,
"Kai daddy wannan kuma fah a ina kuka samota?"
Sameemah ce ta hada ido da alhaji bala wanda yake feso gumi a akan fuskatarsa ta kyasta masa ido batareda kowa yah kula ba,
"Ahh mommy nima anan na ganta ,nayi zaton fah kin santa,tana jiranki ne ki fito"
"Ahah ni bansantaba kwata kwata"
Tun kafin sameemah ta bude baki zatayi magana alhaji bala yayi sauri ya rigata saboda yaga niyyar ta kenan ta tona masa asiri,
"Ahh hajiyah sai yanzu nagane ta ,ai yar gidan aminina ce,yayi min zancen tana neman kudin makaranta toh shine nace ta zo ta karba"
"Ayyah to ai bazata tsaya anan ba sai tayi magana kuma"
Wani Murmushin sameemah tasake yi masa mai nuna alamun ka ceci kanka,shikuwa ummaruje jin abinda akace gameda sameemah cikin sauri yace,
"Lah Ashe kema student ce,allah ya taimaka,amma da kin bani number ki ko zamu sake gaisawa dan yanzu fita zanyi foot ball ba lallai na dawo na sameki ba "
Yana gama fadan haka yabawa sameemah wayarsa,itakuwa kodan taga yah alhaji bala zayyi cikin innocent smile ta karbi wayar ta saka masa number tah.
Tun wajen yayi tsallen samun nasara kafin yah fita aka bari daga alhaji sai hajiyah,itama hajiyah mairon Murmushin takeyi ganin abinda dannata yayi,
"Yarinya ki saki jikinki kinji,idan da wani abunma kizo kanki tsaye,babu wata matsala"
Sunne kai tayi kaman yar arziki tace,
"Nagode hajiyah allah ya jikan mahaifa,yasaka muku da alkhairi"
"Ameen ameen diyar albarka,menene sunanki"
"Sunana sameemah hajiyah"
"Kai suna kuwa mai dadi,yah dace dake sosai"
Da haka hajiyah ta koma sashenta tabar Alhaji bala a tsaye wanda yayi simmm kamar gunki.
Sameemah ce ta tafa hannunta kafin yadawo hankalinsa,
"Amma seemah menene wannan kikeyi da iyalina,musamman umaruje wanda ba hanunsa a komai kike son ki cutar dashi"
"Ka ga dakata cutarwa kuma bashi numbar ta shine cutarwa,cinyeshi kaga nayi komai,sannan abinda nakeyi sunansa wasa"
Ta gama maganar tana kyalkyalewa da dariyaar mugunta,
Takaicine yakama alhaji bala yarasa ma mai zaice,ganin tsayuwar ta gagareshine yasa ya samu kujera ya zauna wanda take facing din sameemah.
Yanzu dai mudawo zancen gaskiya,duk abinda zakiyi kar ki taba iyalina,kowa yah ajiye iyalai a gefe,idan kuma ba haka ba kinsan kin fi kowa iyalai sama dani,zan iyah daukar mataki"
"Lahhh alhaji bala gwanda da kafadi abinda yake bakinka,toh bari kaji in fadamaka,ba abinda zai shafeni dan ka taba wayannan mutanen,koh zai dameni ma ba sosai,saboda wadda naso a duniyah sama da komai ta tafi ta barni kuma na rayu,dan haka uban kowa ma yah mutu,idan aka jajanta na sati daya kowa ya koma harkarsa.
Bar ganin na fadi hakan kuma,allah yasa naji ko mura wani yayi a cikin gidannan ace da hannunka...........hmmmm danka zan dauke mubar kasar dashi muyi rayuwa,sai yagama makancewa akaina na nuna masa video ka sanda kake kokarin yin lalata dani,idan ciwon zuciyah ya kamashi sai na dawo na barshi a can😎"
Tun daga jin bayanin irin ta'asar da sameemah zatayiwa dansa yasa yasha jinin jikinsa,saidai bai kai ga komawa hankalinsa ba yaji ta cigaba da cewa,
"Kai maganar da kayi ma,ka karawa kanka yanzu bayan na siye zuciyar hajiyah mairo da kuma danka,saina saka yarka taji batada wata kawa mai shirin zama kuma yar uwa a zuciyarta sama dani,saina ga yanda zakayi dani idan sukaji ka illatar dani,kuma kana kokarin keta min haddi a video"
Saurin toshe kunnensa yayi tareda cewa,
"Yah isa haka mai kikeso ne kika zo gidannan iye?"
"Abu kadanne,naji labarin shirin da kakeyi a kaina,Toh ka daina banaso sannan batun bani kujerar vigilantee tana nan babu inda zaraje,dan har na karbi takardar ixini a wajen shugaban yan sanda,dan haka ka shiryah zuwa wani sati,in kuma kak ji baza ka ki ganiba.
Ina nan a kan bakana babu inda zanje"
Saida yasauke ajiyar zuciya na babu yanda zayyi kafin yace,
"Shikenan naji,amma batun d'ana please karkiyi wasa da zuciyarsa kinga baisan komai akanki ba"
"Zai sani a hankali karka damu,ai yanada hankali ba mahaukaci bane shi,dan haka in yayi kuskuren hanya zan saita muku shi,sai kuyimin godiyah na cigaba da aikin da iyayene ya kamata su dinga yi,kun sakaltashi da yawa yana bukatar gyara daga irinmu"
Zaro glass dinta tayi daga cikin jaka ta toshe fuskarta dashi,har ta isa bakin kofah ta dawo tana cewa,
"Ahh alhaji zan tafi amma bakazo kun gaisa da motarka ba,ko ka daina santa ne bansaniba"
Ganin dan bakin ciki bai kulata bane yasa ta fita tana Murmushin mugunta.
A can Gidan su surayyah kuwa yau sati daya