Showing 57001 words to 60000 words out of 62773 words
wannan aikin nasan tabbas babane a harkar"
Wata harara sameemah ta watsa mata kaman idonta zai fita tace,
"Lallai dan adam kayan allah ,wato baki daddara ba koh?,toh wallahi idan kika sakemkn wannan zancen koh kika fadawa wani toh zanjiji sarai,kuma hukuncin bazai miki dadi ba kkh kadan"
Tun kafin tabari ta karisa sameerah ta yunkura da sauri tah fice a dakin har sannan jikinta rawa yakeyi kaman tasha tsimin yan farautan.
Saboda maganar da sukeyi da sameerah har sameemah tah manta davzuwa gidan su surayyah da zasuyi itah da kawun burgun saboda tambayo masa izini,daga wayar tayi domin kiran burgu dan taji koh kawunnnasa yah shiryah dan itah bata son zuwan daren ta fiso ta gama da wannan babin kawai.
Tashi tayi tah fara shiryawa jin zuwannasu yana nan ba'a canja ba.
Dayake Surayyah ta sanar da zuwan su sai aka fara shirin taryarsu tunda wuri,dan haka lokacin da suka shigo kowa yana gidan harda babanta shima yau bai je aiki ba.
Toh wata sabon gani surayyah ta fada a ranta ganin yanda sameemah tasha wani uban hijabi mai alkyabba kaman ba itah ba saboda koh a tairihi babu wanda yah taba ganin tasaka,"gaskiyah koba komai na samu matsayi a ran shugabrtawa alalmu ya nuna ta karbi tayin zamana kanwa a wajenta"
Har suka wuce falon baki inda akayimusu shiri bakin Surayyah bai rufuba dan farincikin ganin su sameemah,koh yaushe suka hada ido sai tayiwa sameemah Murmushi itakuwa koh sau daya bata sau fuska ba bare kuma tayi mata magana,hakan bai damu surayyah ba koh kadan saboda tasan haka take,kuma itah haka kawai sameemah take burgers Kodak bata yimata komaiba.
Maganar abinda yah tarasu suka farayi bayan kowa yah kammala abinda zaiyi.
Babantane yafara magana bayan yah bude taro da addu'a.
"Toh da farko tun banji abinda yah taraku anan wajen ba hankalina a kwance yake,don yanayin da kukazo da kuma yamda kuka sananr damu zuwanku akan wata muhimmiyar magana nasan abin alkhairi ne,dan haka zamuso muji abinda yake tafe daku"
Alhaji isah yayan mahaifin burgu shiya fara jawabi kafin yah fara magana da jawabi duk da bai fito fili ya fadi abinda yake ransaba.
Haushine yakama sameemah ganin yanda suke tah jan magana guda daya ana ta bata lokaci ,dan dama tun sanda shigo bata ce komaiba,katsewa kawun burgun tayi tareda numfasawa tana kallon agogonta tukun kafin tafara cewa,
"A takaice dai a daina wani bata lokaci,ni sunana sameemah nasan kunsan sunan koda fuskata zatayi muku wuyahr sani,sannan kuma nice shugabar kungiyar da yaranku suke ciki kafin yanzu kuma suna karakshi kuwata ta kungiyar vigilantee,kuma dukkanku saida kuka amince kafin na fara aiki dasu,wanda hakan ya nuna kun yarda dani a kusa da yaranku.
Sun zo sun sameni akan nayi magana da ku amatsayin iyayensu saboda su basuda karfin gwiwar tunkararku saboda abubuwan da suka faru,abayah.
Sun ce su na son junansu kuma kuma burunsu shine hakan yakaisu ga aure,shin kun amince???.
Shiru wajen yayi kowa yana nazari,ganin hakanne yasa sameemah cigaba da cewa,
"Ni nazo a matsayi guda hudune,na farko amatsayin shugabrsu na biyu a matsayin yar aikar sako,na uku a matsayin abokiyar Ahamd(burgu)na hudu kuma a matsayin yaya ga Surayyah kuma yar uwa,wanda jiyah ta rokeni akan na zamo tamkar yaya a gareta kuma na amince,dan haka ni na amince da kasancewarsu tare saboda hakan abune mai kyau wanda ake fatan yah dore"
Kowa ma dayaji abinda sameemah ta fada kuma sun san dagaske takeyi sai kawai suka amince har aka fara shirye shiyen yanda abin zai kasance,daga haka taro yah kare kowa yah tafi nasa harkar.
Dadai lokacin da sameemah tazo fita daga zauren gidan taji an rungumeta ta baya,ko bata fada ba tasan mai aikata hakan,muryar surayyah tah tsinkayo tana cewa,
"Nagode sosai da kokarin da kikayimana anty sameemah,ina lekawa duk naji abinda kika fada,hakika ko kowa bazai alfahari dake ba ni ina alfahari dake antyna.
Har cikin ranta sameemah tah ji dadin abinda surayyah ta fada,amma a fuskarta iyah karamin Murmushi tayi tareda cewa "nagode"atakaice kafin ta fice.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤35❤
Wata biyu aka saka biki surayyah da burgu,babu a binda suke sai murna da hakan saboda ganin burinsu zai cika,dan yanzu ko a wajen aikima soyayyar su suke sha,dan ma sameemah tana taka musu burki ganin abinnasu yana nema yah wuce gona da iyahka.
Kwanaki haka ma watanni sun shiga,yanzu sameemah tana neman shekara guda akan kujerarta,inda yazamo cewa burunta na yin suna a garin yah fara cika saboda duk inda ka shiga babu abinda ake labari sai gwarzuwar macen da tayiwa maza zarrah barekuma mata,ta kawo cigaba da kuma gyara da dama,amma idan muguntar tazo ma ana tabata kuwa.
Maganar da baba umaru yayi musu na aure tana cigaba da matsowa,saidai koh kadan hakan bai damu sameemah ba dan tasan zancen bai shafeta ba ta kowacce siga.
Su kuwa wanda zancen yah shafesu wato su inna ramatu ana ta shirin hidimar biki,dan saurayin zainab yah turo akan yah shiryah shima yanzu.
Wata motace a tsaye a bayan gidan su sameemah tah faka a cikin duhu dan kar a gane me suke a wajen,salma ce cikin yatsina fuska tace
,"alhaji yakamata idan sona kake toh ka fito,dan nima tunda naga sa'annina a gida zasuyi aure gaskiya nima auren zanyi,idan kuma kaga bazaka aureni ba toh gaskiyah karka sake zuwa kofar gidannan"
"Haba salma baby meyasa kike haka,yanshe zan bari ki subucemin yanda na sameki dinnan,dudu watam mu biyu amma kin sace zuciyata,ai irinku mutum yasaka a cikin gida yah boye hankalinsa kwance yana sakawa a gaban motah"
Murmushin jin dadi salma tayi jin yadda alhajinnata yana gwadata da kuma yaba kyanta,
"Toh shikenan alhaji,nima kaine a raina ai idan har kaga kana ciki toh ka turo gidanmu,idan kuma ba haak ba na bawa wasu dama"
"Ahah baza'ayi hakaba indai aurene ai abune mai sauki"
Da haka kuma bayan zancen auren suka fara tabe taben su har wajen karfe dayan dare kafin tah fito ta shige gidannasu .
Kulu ce tah kalli manjo wanda zamansa a gida baya zuwa wajen shaye shayen har yayi dan hankali saboda bata gara masa badaidai ba din,
"Yanzu manjo kai baka ga hakan yafi maka ba,ji na lokaci daya har ka dan sanja abinka"
Kara gyagygyara kayan yakeyi yana jijjiga kai shi a dole yayi abinda aka yabeshi,
"Ai nake fadamiki yanzu haka idan na fita neman aiki zanje saboda nima a dunga ganina da kamala,ko yah kikace"
"Eh hakan yayi,toh ni ai gwanda da akyi maka dukan gashi ai ka nutsu kana shirin bin hanya"
Harararta yayi yana cewa,
"Kefah dadina dake kenan ba'a abin arziki dake,toh in fadamiki makasudin kara shiriyahta saboda taron da za'a yi a gidannan ne,dan naji labarin duk yan matan gidan aurensu za'a yi lokaci daya,kinga idan mazajen suka ganni a haka,kuma aka nuna ni akace nine yayansu na karamin kyauta zasuyimin ba koh?"
Dariyha kulu ta kece da itah tareda cewa,
"Lallai manjo har yanzu da saura,kaidin yanzu jira kake ajo auren kannenka mazajensu su tara maka dukiyah ?"
Kai mata duka yayi tah shige daki,sai kimbura fuska yakeyi ganin yanda take masa dariyah dan yayi mata tadi zasu samu abin alkhairi.
Dukka yan matan kowa hidimar aurenta takeyi banda sameemah wanda hankalinta gabadaya akan aikimta yake,tah wani wajen ma dadi takeji zasu tafi subar gidan ta maida dakin iyah itah kadai kawai.
Yanzu sameerah duk wani abu da zai shiga tsakaninta da sameemah gudunsa takeyi tumda ta gano sameemah tafi karfinta,saidai mai hali baya fasawa ,bayan mutuwar tsohon bokanta yamzu ta samu wani,wanda yafi na da yimata aiki,saidai koda wasa bata yarda wani tayi maganar sameemah a wajensa balle kuma yimata asiri.
Ummaruje zaune a falon mahaifiyar tasa bayan isha,shiru yayi baiyyi magana ba ita ma kuma hankalinta bai kai Kansba dan ko dauke kanta batayi daga kan shirin da akeyi a gidan television na bolly wood,ganin bazata kula da sunkuyar da kan dayake yi bane yasashi cewa,
"Ummah! Ummah ummah!"
Saida yakirata wajen sau uku kafin tah juyo ta kalleshi,
Na'am son me ake ciki?"
"Dama Idan abba yana nan inaso zamuyi magana ne daku"
"Ahh wannan ba matsala bace bari na kirashi sai yah shigo".
Suna zaune kuwa sai gashi ya shigo, shima zama yayi akan kujerar tareda daukar wani apple akan pilate yana ci.
"U hmm mahaifiyar ka tace kanason magana damu,ina jinka"
"Eh ......eh damaaaa abbba akwai wacce nakesone a gidan gandu shine nakeson aje nema min ,dan tah cema na turo,gashi babansu yace zuwa nan da karshen shekarar nan kowa a cikinsu tah fito da miji"
"Toh naji dadi da ka fadi haka kuma munyi farin ciki,dan dama shi namiji cikar mutuncinsa shine aure,toh amma yar ina ce waye babanta"
"Eh a Gidan Gandu take sunan babanta umaru,yayar sameemah ce ma"
Hajiyah mairo ce tayi saurin cewa,
"Ayyah Kaga nifi na allah,ni da da farko ma nayi zaton da sameemah za'ayi ashe kuma da yayrta ne ashe,toh allah yasanya alkhairi inshaallah za'a bincika sai ajen tambayowa"
Duk maganar da akeyi alhaji bala bai ce komai ba sai wani shiru da yayi kaman wanda ya tafi wani nazari,maganar da ummaruje yasake yi ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi.
"Amma ummah bazawara ce dan ta taba aure,amma koh shekara batayiba ta fito,dan ko da bata dashi"
"Toh gaskiya my son bazaka auri bazawara ba ban aminceba sai ka nemo budurwa,ga mata nan birjik a gari......"
"Meyasa kake haka alhaji,wannan wane irin zamcene haka,bawani dan zancen bazawara tunda aka fadi yar wacece ka wani hade rai baka ce komaiba,kuma naga annabi ma yana saurayin yah auri bazawarar,ai abin farin cikine dan ka zai dabbaka sunna,ni dai bazan hanashiba duk da banso ba amma tunda yana son shikenan bazan haanshi ba,saidai kuma idan akwai abinda kake boyewa?"
"Ahh ha m.............ahahha babu abinda nake boyewa mai zan boye,shikenan za'a san yamda za'a yi kaje allah yabada sa'a"
Shidai mamakin ubannasa yayi ganin yanda yake wata rawar muryah ta rashin gaskiya.
Manjone a zaune a unguwar su kulu dayake nanne inda yah samu sana'ar had'a bulo,sumyi dan hutune dan kowa yaci abinci yah koma aiki.
Wata kanwar kulu ce take ta fad'a da wata sai zage zage sukeyi an rabasu sunki su daina.
Budar bakin wani a wajen sai cewa yayi,
"Hmm ai wanna yarinyar bata da mutunci,dukkansu yaran gidan haka suke,naga kana ganin itah kanta yayarta wacce tayi aure a gidan gandu,duk da aurenta amma duk sanda tazo gidansu raba dare zasuyi suna hira da tsohon saurayinta har sai sukai dayan dare a wajennan,gashi babu dama a fada sai uwarta tace karya ne"
Wanine shima yah cafke tareda cewa,
"Toh laifinta zaka gani,naga shima mijin shashashane,inba marar hankaliba ka tafi rani har kayi kusan shekara biyu babu labarinka,idan ma ba irin su kulun ba wace matarce zata yadda,ni banga laifinta ba sai nasa laifin gaskiya,ai aure ba hauka bane koh"
Duk maganar da akeyi a kunnen manjo wanda yayi mutuwar tsaye,banda juyawa babu abinda kansa yakeyi,dan jinsa yakeyi kaman a wata duniya yake.
Tun kafim wani yah ganshi ya dauki rigarsa daya cire yah bar wajen siyarda abincin tun kafin wani ma ya ganshi.
Shirye shiye ake tayi dan yau masu kawowa kayan auren su sameerah zasu zo itah da zainab,sai wani rankwada kai sukeyi,za'ayi aure watan gobe.
Dare yafayi dan wasu kanma sun kwanta,alhaji balane ya shigo dakin hajiyah mairo wanda har tasaka kayan bacci,
"Alhaji lafiyah na ganka da darennan babu alamar kwanciyah allah yasa dai lafiyah"
"Eh lafiyar ce tah kawo haka,dama inaso muyi magana da kene saboda in fitah hakkinki"
"Toh wace maganace haka inajinka"
"Dama inasone na kara aure,kuma badan kin gazamin ba kawai ra'ayin hakkanne ya taso"
"Aure! Aure!! Fah kace alhaji?,wacce shigiyar ce zaka auromin ka kawomim cikin gida yau shekarar mu talatin da takwas da aure?"
"Haba hajiyah ki kwantar da hankalin mana,yarinyace ba lallai tah baki matsala ba dan koh kanwar ummaruje bata kaiba"
"Kutumar ubancan,alhaji mai kake nufi,dan kaga kwaanannan nayi sanyi shine har ka samu kwarin gwiwar fadamin wannan maganar?,kuma ma dankayi mungun rainamin hankali hadda wani cemin yar yarinyace,wato ni na gama zama dakai da haifamaka yara,ka gama ragwargwajeni bari ka auro sabuwa dall ku more nikuma na zauna na zuba muku ido koh?"
Hmm .....alhaji dani kake zancen kawai,kuma banson sake jin wata magana daga bakinka ka fice kabarmin dakina tun kafin raina yafi haka baci,hawan jinina ya hau ka kasheni da dalili kayi auren ka hankalin ka kwance"
"Aurene kuma kayi mugani,amma daga kai har amarayar zaku san kun tabo hajiyha mairo hmmmmmm".
Alhaji bala yana ficewa ta daga wayah ta fara dannawa babu ruwanta da yanayin daren da gari yah fara.
"Hello hajiyah Lailah kina jina"
"Eh ina jinki hajiyah mairo,amma lafiyah kika kirani da tsohon darennan ?dan ma nayi sa'a mai gidan baya nan yana dakin shegiyar"
"Hmm kedai bari kawai,dama kina fadamin halin maza nake cemiki alhaji bala dabanne,toh yanzu kam na gano halimsu duk dayane tamkar an cakudasu an raba su"
"Wai meyah farune hajiyah mairo ki kaini ganuwa mana"
"Alhaji ne fah wai zai kara aure nan da wata daya,ke inda irin nakine ma da sauki a auro maka wanda bata wuce sa'arka ba ta yanda babu abinda zata nuna maka,amma bakin cikin shine budurwa zai auromin mai jini a jika koh yusrah bata kai na a haife,ina so ki fadamin abinda za'ayi dan bazan zauna haka ba kam"
Ashar hajiyha lailah ta durah kafin tace,
"Ai bazai yiyuba kam dolene ayi wani abun,kinga irinta koh dama ina fadamiki ai kike wani yabashi gashinana ya zefar miki zani a kasuwa"
D'urum manjo yah buga kofar dakinsu shida kulu yah shiga ,kallonsa takeyi tareda tambayar lafiyah,bai cemata komai ba sai maida kofar dayayi yah rude idonsa yayi jawur da shi dan bakin ciki.
Zare wani tsohon belt a kungunsa yafarayi,yana wani kakkadashi tareda nufar gunda kulu take tsaye a dakin.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤36❤
Matsawa takeyi da baya yana nufarta,bata amkara ba sai jin duka taji a jikinta zuwattt,ihu ta saka tana soshe soshe,tareda da dadare,
"Dan ubanki saboda kin maidani mutum mutumi wawa soko,shine wato inacan na tafi rani kike zagewa wajen kwartonki koh,toh yau allah ya toni asirinki naji komai,kuma mai rabani dake sai Allah"
Kulu tanajin abinda yafada tah daina ihun tareda tike belt din dayake dukan ta dashi da hannunta,
"Ohh dama akan hakane kake dukana,toh bari kaji na fadamaka dama tun ranar dana gane cewa wani yasam abinda yah faru na shiryah wa zuwan hakan,wato sameemah ceh tah fada maka koh,dama nasan sai ta fada ai kuma ......"
"Dallah rufemin baki munafuka,toh ba sameemah bace ta fadamin a unguwarku naji wasu suna fada,ai dama abin duniya baya buya indai anyishi"
"Eh nasan na aikata amma sau dayah nayi kuma daga lokacin ban sake ba,shima kansa na yi masa gargadin kar ya sake kirana tun rananr,kuma koma mai yah faru ai lefinka ne,naga tun ina da cikin mai sunan baba ka tafi ka barni,bakasan halinda nake cikiba har na haifeshi na yayeshi yayi wayo baka nan,sannan daka dawo babu abinda ka bani bakasan mai muka ci ba bare kuma muka saka,komai ma a lokacin ne yah faru,ai nayi kokarima da ban tafi gidanmi na,shidinma jugani yayi akan bazaka dawoba,na kashe aurena na aureshi,nayi nadama nace yadaina kulani"
Zuwa yanzu kuka takeyi amma bana dukan da manjo yayi mata ba,na halin dasuke ciki takeyi,durkusawa tayi akan gwiwarta tareda cewa,
"Duk da nasan banda mutunci a idonka,saidai ina kwadayin muyi zama irin na ma'aurata na gari badan muba saidan yayanmu,banida ilimi na arabi dana boko haka kaima duk dayane dani,sannan dagani har kai munsan hanyar da muke kai bamai kyau bace,mai zai hana mu gyara,ko makarantar yaki da jahilci mushiga domin musamu ilimin bawa y'ay'an mu tarbiyyah,ni dama ina zuwa wajen matar kawu munkaila tana doramum,rayuwarsu tana burgeni,sannan har yanzu manjo ina sonka wallahi,soyayyar ka ita tasa na kasa kashe aurena na bishi badan wai dan ina tsoron Allah ba a lokacin.
Dan allah kadaina shaye shayennan sannan karka sake zuwa cirani dinnan da bashida amfani,ka zauna tareda damu iyalanka mugina rayuwa mai kyau tun kafim lokaci ya kure"
Tana gunjin kuka tana fada iyah karfinta,matsawa tayi tah kamo rigarsa da hannunta ta rike gam kaman wanda zai fita yah barta.
Shima ganin hakanne yasa ya jefar da belt din tareda tsugunnawa yana rungumeta a jikinsa,
"Shikenan kuluna na yafemiki kuma na fahimceki,nima inso ki yafemin,hakika laifinane kam babbba a ciki,inshaallah zan gyara halayya tah,amma ina ga zanje wajen mai gidana nace masa na yarda zan je Kazaure na rike masa aikin bulonsa nacan,inyaso sai mu tafi daku gabadaya na kama mana haya na sakasu a makaranta,dan wannan wajen zayyi wuyar sanja mutum zuwa na gari koda kuwa yayi niyyah"
Kara rungumeshi tayi cike da jin dadi,jim abinda manjon yace ,kuma cikin muryah irin ta mutum mai hankali,fito da kudin dake cikin aljihunsa yayi wanda yake tunanin zuwa siyan kwayah dasu yah mika mata tareda cewa,
"Ka wannan ki sayi abinda babu kiyi abincin rana,kuyi hakuri da rashin ciyarwar dana yi muku a baya"
Da farinciki ta karbi kudin tana yimasa godiyah da kuma fatan neman budin allah.
"Yanzu inna haka za'a kawashe duk wannan ubam kayan kayan akaimata,wanda akayi shekara ana tarawa,saikace wata diyar sarki,naga ko mu ma akwati daya aka kawomana shine ita sai ankaimata har akwati uku,gaskiyah bazai yiyu ba"
Sahura ce take fada yayar Yunusa saurayin zainab,Iyah Larabace mamar su yunusa wadda aka kira da inna itama tace,
"Kema dai kya fada y'ar nan(bata fadan sunan tah na farine)sai wani rawar kafa yakeyi akanta,duk wani dan kudinsa yah kashe a kanta tun kafin tazo,ni wannan tun kafin tazoma na fara zargim inaga farar kaface da itah"
Wata ce a gefe tah jijjiga kai ,saboda kaff garin babu wanda bai san inna laraba da kishi da matan y'ay'an ta ba,ga masifa da kuma saka ido,kuma su kansu yaranta mata halinta suka gado a jaraba.
Kanwar inna larabance tace,
"Gaskiya yaya karkiyi haka,wannan ai sai aji kunyah,ki bari koma menene idan tazo ai sai ayi koh amma ba a nan ba gaskiyah"
Dahaka badan tasoba ta bari amma bahakan yana nufin tana son akai kayanba.
Tun kafin yamma gidan gandu yah fara cika kasancewar za'a kawo kayan yan mata har guda biyu ,na salma kuma sai gobe.
Inna ramatu sai shiga ake ana fita saboda hidimar tarar baki.kasancewar al'adarsu da yamma ake kawowa shiyasa mutanen dazasu karbi kaya daga bangaren amare har sunzo.
Guda aka fara rangadawa tun daga zaure