Showing 30001 words to 33000 words out of 62773 words
ake nice na ke tarewa saina zo gida kafin na cireshi,idan wani yayimana cikas kuwa cizo kawai nake masa kafin bayan sati daya mutanen mafarkina sun zuk'e jininsa,dan dama abinda suke so kenan,su kuma ko yaushe cikin karamin karfin jiki sukeyi idan nakai musu jinin da suke so.
Bayan kwana biyu shiru banji labarin shaheedah ba duk da tacemin zatazo wajennamu,abinne yabani mamaki hakan yasa na shiga cikin gari da b'adda kama,mai gadinsu na tambaya a gefen gidansu nan yake shaida min kanin babanta yah tafi da itah gidansu wai zayyi aurenta a can,da farko nayi bakin cikin bamu sake haduwa ba,,amma nayi mata murna domin hakan shiyafi dacewa da itah,sama da rayuwar damuke,dan irin wannan rayuwar nikadai yakamata da dungayi tunda hakane kaddarata.
Komawa nayi jikina da sanyi jin bata gidansu ta tafi inda rayuwarta zata inganta,tun kafin na isa na watsar da tunanin ta dan yanzu banason saka wani abu a raina har ya dameni.
Maida himma nayi akan aikinmu ba dare ba rana,dan yanzu nice nake kulada da kowanne shiga da fita,saboda ogah Binlad shida Samad sun tafi kasar Brazil,binciken wani sirri,yanayin yanda abun yake tafiyha har yafi in ogah yananan,saboda sun fi tsorona fiye dashi yamzu,dan kowa yasan halina idan yah aikata abinda banceba.
Ina cikin bincikene na gano wani aiki a gidan sarkin malamai,saboda yanada kudi sosai,sannan duk wani kudi a gidansa yake tarawa.
Shirye shirye muke ba kama hannun yaro,kullum muna cikin binciken yanda zamu aiwatar da shirin.
Tun da yamma,na zabi wanda zasu bini da kuma wanda zasu kulada gida kafin mudawo,babu wanda yayi magana bare musun abinda nace,bindigoginmu muka cika da bullet,duhu yana farawa muka shiga motocinmu sai cikin gari,a bayan gidan muka tsaya muna ganin shige da ficen gidan,wasu motocine suka,fara shigowa zasu kai wajen bakwai,har wajen karfe sha daya amma babu motar da ta fito hakan yasa na bada umarnin mushiga kawai.
Wani daga cikin yaranne yace,
"Amma ogah seemah akwai fah mutane a ciki"
"Nasani ai ko makahuwa ce ni,ubanme mutanen zasuyi mana,idan tsoro kake ka zauna acikin mota,banza lusari kawai,idan kuma suka fito da kudin suka tafi fah,mu mai zamu samu"
"Afuwa Ranki ya Dade"
"Dallah yimin shiru,ku mazaje maza a kafta"
Cikin sanda muka fara dosar gudan,har muka shiga babu wanda yah kulada mu,cikin gidan babu kowa sai haske daya gauraye gidan,ina biye suna bina a baya har muka haura stairs din benin,acan wani daki karshen corridor muka jiyo maganar mutane,da alama suna cikin dakin kenan.
Alama nayiwa na baya su tsaya kafin nayiwa nagefena su biyoni,a bakin kofar muka tsaya sai kuma muka banka kofar da sauri.
Falone mai girman gaske an jereshi da kujeru,manyan malamaine a zaune amma shigarmu kowanne ya tashi ya tsaya yana kikkifta ido,jerin malam na bi da kallo inda idona yasauka akan mu'allim,"dank'ari" nace a raina.
Daga bindigar nayi sama kafin nace wa yaran,
"Maza Ku bincikemin sako da lungu na dakinnan,karku bar ko ina"
"Angama ranki yah dade"
Zagawa nayi ina kallon malaman wajen,tsawa na daka musu cikin sauri suka zube a kasa suna karkarwa,tafiyah nake saida nazo saitin mu'allim kafin na tsaya,sunansa na kira inda yah dago da mamaki da alama yasan muryar,dadai lokacin yarana suka dawo da cewar basuga komai ba,.
Cire hular fuskata nayi ina kallon mu'allim din da shima kallona yake da Mamakin.
"Kayi mamaki koh,nicedai sameemah,wannan itace hanyar danake kai ba wacce kake kokarin dorani ba,inayine saboda tsoronka badan ina so ba,tunda kai ka sanni inaso ka fadawa shugabanku yabani kudi na tafi bana bukatar taba kowa a nan wajen,idan kuma ba hakaba,karkayi tunanin,zaka iyah kallon wannan sameemar"
Tun kafin mu'allim yayi magana na nuna masa yayi shiru saboda ina kallon sanda shugaban yah mikawa yarona kudin ta gefen idona.
Tsayawa nayi a gabansa,bayan ya mika kudin nace,
"Mu zamu tafi saika musu bayanin irin kodar yaran daka siyar kafin ka samu wannan kudin,saboda su sanjaka da wuri kafin lokaci yah kuremusu,muma kuma su daina zargin mun sace kudin marayu kamar yanda ka fadamusu"
Ina gama fadamasa na tunkuda keyarsa da karshen bindigata zuwa gaban sauran malaman nayi gaba.
Sai wajen karfe biyun dare 2:00am,muka koma sansanin mu.
Ogah binlad nasamu a kan kujerarsa a zaune har sannan bai kwanta ba yana jiran isowa ta,kallona yayi da alamar tuhuma na fitar aikin danayi bayanan.
Nima banyi masa magana ba sai mika masa jakar kudin danayi,karba yayi yana zugewa dan ganin menene a ciki,
Dagowa yayi da alamar neman karin bayani,nima shiru nayi banyi magana ba ,dannaga alamar da miskilanci yadawo,
"Baki fadamin wane aiki kukayi aka samu wannan kudin ba"
"Toh ogah kaima baka tambayeni ba ai"
"Hmm kina nan da rashin mutuncinki toh yanzu na tambaya"
Labarin inda muka samu kudin na bashi tun daga farko har karshe,jijjiga kai yayi tareda mikamin alamar jinjina da hannunsa,
"Yayi kyau gobe akwai maganar dazamuyi daku,akwai wanda za'a zaba zasu je Brazil wani aiki,amma sai gobe tukunna,kowa tafiyah yayi ya kwanta,kafin muji mai ogah yake tafe dashi bayan tafiyar tasu.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤19❤
Tunda safe ogah Binlad yah taramu domin yanda lavarin yake cinsa kaman arai.
Faraway yayi da cewa,
"Yawwa kaman yanda kukaji nace akwai wani abu,nasan kunga munyi tafiyha nida Samad zuwa kasar Brazil mun hadu da wasu yan uwanmu na can,suke fadamin akwai training daza a yiwa sojojin kasashe na horon hacking,kwarewar harbi da kuma sneaking,(sanda),.
Za'ayi program na tsawon shekara uku,duk wanda yayi nasarar gama wannan horo yah fito da mataki mai kyau toh ba karamin aiki zayyiba,a yanzu haka maganar dananke mun gama yin information na badda kama ga yaranmu guda uku;Na farko Samad ta biyu sameemah sannan kuma da hakeem,saboda shi yayi karatu dama a kan na'ura,sukuma sauran kowa yasan jarumtarsu da kuma boye sirri.
Jin kaman ya gama bayaninsa ne kuma gashi banji gamshashshan bayani ba yasa ni cewa,
"Amma ogah munji abinda kace,saidai munaso kayi mana bayanin a wane irin yanayi zamuje wajenne?"
"Kinyi tambaya mai kyau,ke zakije a matsayin RAUDAH ABDULSALAM,mahaifiyar kice yar najeria babanki kuma dan palastine,zamu baki password akan raudah dakuma fuskar dazaki na sakawa saboda kar a ganeki.
Kai kuma Samad zakaje a matsayin SULAIMAN BIN HUD,sai hakeem kuma a matsayin ABDULHAKEEM BIN MALEEK,na gama bayani kowa za'a bashi information akan sabon sunansa,dakuma training da ogahna zai muku kafin yasaka ku cikin sojoji ta barauniyar hanya,saboda kar a samu matsala ko kadan.
Da farko abinne mukaji shi banbarakwai ,wai zuwa kasar Brazil kuma zama na shekara uku,har mun juya zamu tafi ogah Binlad yakirani,juyowa nayi da alamar ina jinsa,
"Da farko inaso karkiyi wata yarinta a can,tunda har yanzu bakiyi shekara sha bakwai ba,girmanne kawai da kuma zallan kwarewa a harkar teranci,toh kikula sosai karsu gano ke karamace"
Abin mamaki yabani jin yadda ogah Binlad yazageni hankalinsa kuma kwance,nima karkakce kaina nayi kafin nace,
"Toh in hakane shi tsohon yaje mana tunda yana tsoron kar yara suyi shirme idan yah turasu,sannan kuma.........."
Katseni yayi ta hanyar cewa,
"Bana bukatar jin komai,tunda kinji mai na ce kuje allah yah kaimu wani watan"
Tun daga lokacin muka dukufah yin training din yanda zamu boye kamanninmu a cikin ainihin sojoji,ta hanyar sanin abubuwan daya shafesu,lokacin da results wanda zasu tafi yazo kowa mamaki yayi ,domin a cikin wanda zasu tafi candin,a cikin mu dari kowa yah taho daga sansaninsu an zabeshi da kuma wasu sojojin daga wani waje a cikin kasar,dukkan mu iyah mutum goma suka dauka wanda zasu tafi kasar Brazil,abin mamaki babu sunan Samad a ciki.
Bakin cikine kwance a kan fuskarsa ganin zamu tafi nida hakeem banda shi,da farko nayi niyyar hakura nima,amma yanda naga yana bakincikin hakanne yasa nace zanje,dan naga ya zaiyi,kuma *zama waje daya ma ai hatsarine inji kifi*,gwanda muje muga mai duniyah take ciki a dayah bangaren.
Shiri aka gama mana tsabb muka kama hanya cikin taron sojojin palastine,bisa kasada irin tamu na rayuwa.
Lokacin da muka dira a kasar wani iri naji saboda tsawon shekarata shida nafi sabawa da kasar palastine,a air Port suka saukemu mota tazo daukarmu zuwa masauki.
Tun daga washa gari muka fara aiki ba dare ba rana,wanda cikim saka abu a rai da kuma kwazo banyi wata shida ba saida ya zamo ko ina sunan RAUDAH ne yake zagawa har na fara mantawa da Sunana sameemah in ba Hakeem yakirani muna mu kadai ba.
Sukuwa sojojin palastine har murna suke saboda a cikin tawagarsu nake,shikanasa ogahn duk abinda ban saniba shiyake nunamin domin burinsa na fito da tauraro wanda zai daga kasarsa.
Lokacin da muka shiga shekara ta biyu aiki yah fara tsananta,domin har wajen kaiwa a hari ake turamu,ni ina a cikin rukunin yan hacking amma wani lokacin idan naga yannamu zasu kasa yi,bansan lokacin danake shiga cikin filin ba,da haka ta nan ma nafara koyon aikin sojoji na shiga filin yaki,dan idan na bisu mukanyi sati biyu har wata bamu dawo sansaniba.
Wani lokacin wasu su mutu,wasu kuma su dawo a wahale,mune yan basu taimako da kuma cigaba idan wasu sun gaza.
Tunda nake binsu fili ban taba dawo wa da ciwo ko dayah ba,domin a wajen yake warkewa da kansa cikin yan mintuna,duk da babu wanda ya taba yimin magana nasan kowa na mamaki,saidai suka barshi a matsayin kwarewa ta ce kawai.
Bayan mun shiga shekara ta uku sannan kam na kware a ta bangarori da dama ciki harda abubuwan da ban taba tunanni zan gansu ba ,irin tuka egwuwa,da kuma harba bombs.
Kowa hankalinsa ya tafi yanda zaici gasar karshe saboda yakoma kasarsa cikin abin alfahari da yabo.
A cikin wata na takwas kafin shekarar ta kare muka fara shirye shiryen tafiyah wajen gasa tah karshe,wanda zamu shiga cikon wani bakin dajine mai cike da arna duk wanda yah fito da rai cikin kwana goma toh sune wanda za'a bawa tutar yabo.
Mukuma masu hacking wani mission aka bamu wanda zamuyi bayan wata daya,akan wasu gogaggun barayin hacking a kasar Canada,duk wanda yayi nasara shima shine da tutar yabo.
Shiga nayi cikin yan zuwa daji muka tafi,ko ba komai zan kashe kwarkwatar ido,aikuwa naga abin mamaki,nan akayi ta artabu aka kashe mutane da dama,mu wanda muka fito babu fi mu dari ba,dan ma na taimaki wasu da yawa.
A wajen hacking kuwa kwana muke a gaban computer sai bacci ya kama mu muyi,idan mun farka mu cigaba,mun fi sati muna abu dayah kafin wani yaro a cikin mu yagano lagonsu,muka afakamusu.
Idan aka sakawa abu rana toh sai yazo,yau mune a tsaye a fili da kayan sojoji muna kiran karbar sakamako,tun waccen satin aka fara sallamar wanda sukayi nasara,dayake mune Batch C,muna kasar Brazil,yayinda Batch A suke America,sai Batch B a Canada.
Nice na karbi numaber yabo ta uku,bayan wasu guda biyu a kasashe daban daban sun karba.
Daga kyautar nayi a hannuna,ta silver sai sheki take,anyi alamar soja mace a jiki da kuma sunana wato RAUDAH, yayinda a daya bangaren kunnuwa na suke jiyomin karar sauti tafi rafff rafff da kuma harbin bindiga,kuma duk ni akeyiwa.
Kowa murna yakeyi acikinmu zai koma gida da irin nasarar daya samo,wanda suka mutu kuma saidai muce Allah ya jikansu da rahama.
Shugaban tawagar palastine ne ya taramu murna a cikinsa kamar ba gobe,bakinsa yaki rufuwa saboda murnanar nazo tah uku,a cikin kasashe da dama,magana yah faracikin harshen turanci maimakon larabci,wanda yasan kowa yah iyah saboda zamanmu cikinsu.
Kowa zuwa yayi yah kwanta da niyyar gobe za'a fara shirye shiryen komawa gida jibi kuma mu tafi,
Wani duhu nake gani saidai duk da bana gani sosai nasan gidanmune na Nigeria,wutace take cin cikin gidan amma kowa yah ki kaiwa taimako,gani na nayi a tsaye a gefen gidan mutanen cikin gidan suna ta ihuu amma babu wanda ya kulada ni,wani mutum ne naga yazo wucewa na ja rigarsa,tsayawa yayi yana kallona kafin nace,
"Bawa allah baka ganin suna neman taimakonka ne?"
"Nagani amma ke da kike yar gidanma aikin barshi ina kuma yani,ke mai zai hana kidawo ki taimakesu hannunka a baya rubewa kayanke ka zefar,saidai kayi masa magani koda kuwa maganin akwai wahala har ka samu yah warke........kidawo gida,saboda wanda yabar gida ,gida ya barshi.
****
Da sauri na tashi daga kan katifata jikina duk gumi,mafarkin danayi kuwa har sannan yana ta dawomin cikin kaina,babu abinda nakeson gani sai kasata Nigeria,zaman kasar wasun yah isa haka.
Filin jirgi muka iso kowa yasha kayansa yana jan trolly a kasa,tafiyah muke cikim tawagarmu tah yan palastine kowa ka ganshi murna yake saboda nasarar da aka samu.
A waiting room muka zauna muna jiran sunanmu yazo layi zuwa jirgin palastine din,shugabanmu ne yah fita shida wani daga cikinmu zuwa dubo wani abu wanda bamu sani ba.
Sunana ne yake amsa kuwwa a jirgin da zai tafi Nigeria,wato SAMEEMAH UMAR,tashi nayi hankali kwance na maida glass idona tareda jan trollyn na nufi hanyar jirgin,Hakeem ne yah ankare dani tunda dama yasan sunana,hakan yasa sauran ma suka farga da jirgin danake kokarin hawa,saurin riko hannun doguwar rigata yayi tareda cewa,
"Kee sameemah mai kike kokarin yine,wannan fah ba jirgin kasarmu bane"
"Eh ba jirgin kasarku bane,amma ni jirgin kasarmune ai,koh baka ganine"
"Hankalinki d'aya kuwa,kinsan mai kike shirin aikatawa,idan ogah Binlad yagano mai zakice,kinfi kowa sanin ya matsu ki dawo saboda nasarar da kika ciyo"
"Toh so what Ubana ne shidin,kuma ta ina zai hadu dani din,daga yau babu wanda zai sake ganina a cikinku saidai tarihina,dama shine abinda nake barwa duk wanda muka zauna,ni zan tafi kasarmu nasara kuma kai ta shafa bata shafenba,daga nan ma bazan sake maganar ta ba"
Har na fisge hannuna na tafi,sai kuma najuyo,har sannan yana tsaye kaman kungi da Mamakin abinda na aikata,Murmushi nayi masa tareda cewa,
"Ka gaidamin kowa idan ka isa lafiyah,musamman ogah,kace ina yi masa missing😘😘😘"
Karfe biyu na rana dadai na sauka a kasata wato uwa Nigeria,tundaga yanayin mutanen nasan Nigeria ce kam,a garin abuja muka sauka,ana tah hayaniya wai wani dan sanda sai yah caje wata mata a airport din,duk da ba hausa nakeji sosai ba a wajen saboda dadewa da nayi banyiba,amma na cafki wasu kalmomin kuma nasan shine baida gaskiya.
Rike hannunsa nayi wanda yake kokarin dorawa a kugun matar,wanda hakan yasa fadan yah dawo kaina,matsowa kusa dani yake wai nima sai ya cajeni,banyi tsammaniba kawai naji hannunsa a kan kirjina,bansan lokacin dana sauke masa dukkan training din danayi ba na tsawon shekara uku akan fuskarsa ta hanyar zabga masa mari.
Tun kan na sauke hannuna na nemeshi na rasa ashe yah zube kasa sumamme,karfe naji a hannuna saida na duba ashe ankwa ce suka sakamin dan zuwa police station,banyi musu ba na bisu muka tafi inda suka bukata,saboda koda zanyi magana ba zasu gane so sosai ba hausar tawa sai a hankali.
File suka fara cikewa akan nayi attemp din kashe dan sanda ,nidai ban ce musu komai ba har suka gama rubuce rubucensu suka gama,a raina nace mai hali baya fasawa,wato mutanenemu na Nigeria sai a hankali wajen san kai sa kuma yin hukuncin zalunci,wannan kam sun rufe kofah a kai.
Prison a ka turani kasancewa babu wanda zai min beli na tsawon wata shida,banji komai a raina ba,allah na tuba nayi shekara shida ma a prison ai ,menene kuma wata shida ,kaman gobene,kuma wallahi tunda a prison din duke aiki dukkan su,zasu ci ubansu a guna sai sun kwammaci sun sallameni yah fiye musu,bari kawai a dan buga wasan kafin yah kare ......................muje zuwa😀😀😀😀😀😀
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤20❤
Tun daga bakin kofar prison din nake yah mutsa fuska ganin yanda wajen yake duk babu tsari ko kadan,wani daki aka kaini wai shine na mata,babu kowa a ciki sai wasu mata tula tula guda biyu a gefe suna zaune da kayan prison din a jikinsu.
KO magana banyi musu ba na kade wani waje na zauna ina kallon wani gefen daban,muryar dayar naji tana min magana cikin wata hausarta da duk yare ya gauraya da itah.
'Ke baki ganin mutanene da bazaki kulasu ba"
"Toh miye saina kulaku,tare mukazo daku,ko kuma zamanku nakeyi a wajen"
Dayar ce ta matso tana wani hura kirji itah ga yar iska,nima gyara zamana nayi domin naji mai zata ce,cikin rashin sani naji ta kamani da kokuwa mun dungura kasa,matsawa tayi tana huci itah a dole ga karamar yar iska.
Da farko takaici abin yabani ganin yanda tah batamin kayana da datti,dagowa nayi ina kallonta dadai da isowar wani ma'aikacin tsaro wajen,kallona yakeyi tareda dariyah yana cewa,
"Bake yar iska ba hada marin ASP,yanzu zaki fadawa yan garinku a cikin wannan masifaffun matan,dama ba'a saka kowa a cikinsu,saboda karyah mutane sukeyi,yanzu zamuga bakin rashin kunyarki yarinya"
Haushi maganar tasa ta bani,kafin nace masa,
Kana nufin kenan koh karyani sukayi babu wanda zai dau mataki?"
"Kwarai kuwa"
Murmushin jin dadi nayi kafin nace,
"hakan babu matsala ,bari a fara buga wasan"
Tun kafin na gama magana na dauki buleliyar cikinsu na duma tah da kasa,dimmmm saida cell din yah Amanda wani vibrate,koh motsi batayi ba sai wani nishi da tayi na wahala,nufar dayar itah ma nayi fuskata dauke da wani evil murmushi,ihu ta fara tana neman taimako,wanda shima ganin abinda yah faru kaman yah daskare haka yayi shiru.
Labari ne yaje kunnen DPO,inda aka kiramu nida su,tsura mana ido yayi da alamar neman karin bayani.
Cikin sauri kuwa suka zayyane masa,hadda cewa wai ni ce na fara bugata da sumunti,nidai bance komai ba har naji DPO yana cewa a kaini cell din maza,kallonsa suke da mamaki,jin ina mace yace a kaini cell din maza,sannan laifinna ya nunku zuwa shekara guda ciff.
Jana sukayi muka nufi wajen mazan har sannan ko kala banceba.
Wajen mazan yafi girma sosai saboda suna da yawa a wajen,ni hakanma yafimin saboda ba fiye son zama da mata nake ba,sun faye rainin hankali.
Cikin sati biyu muka saba dasu,saboda duk abinda suke tsoron yi ninake aikatawa,zuwa lokacin hausata ta fara dawowa normal saboda yanda nakeyinta akai akai.
Masu shaye shayen cikinsu kuwa in sujjada nace sumin zasuyi,saboda dare nake bi na tsallaka fence cikin sauki (saboda training danayi a Brazil),na sayo musu a cikin gari,yan iska kuwa harka ta bude saboda sun samu jagorancina,kullum dare za'a raba ana hira kafin kowa yah tafi yah kwanta,daki daban na ware nace musu nawane,babu musu kuwa suka barmin shi,wasu yan kusan yankinmu na hadu dasu a wajen,suke bani labarin yanda garinmu yasanja,suma an kamasune bayan sunyi laifi a garin abuja.
Mikewa nayi da sauri,kkwa saida yah kalleni dan ganin mai yah ke faruwa,hade fuska nayi babu alamar wasa nace,
"Wayake son yabini garinmu?"
Kusan mutane ashirinne suka daga hannu,ina ganin haka nace,
"Shikenan an gama ,gobe zamu kama hanyar tafiyah da safe bayan an sallamemu,dan tunda naji labarin gida toh nafasa