Showing 48001 words to 51000 words out of 62773 words

Chapter 17 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4430

yaune farauba.
Kwanciya tayi ta kashe wayoyinta saboda kar a dameta.
Baccine yayi gaba da itah har sai wajen isha kafin ta tashi,domin shirin tafiya dinner da za'ayi na samun kujera da sukayi.
Wanka kawai tayi dan babu batun sallah,kafin aka zo fara shiri,rigar da akayi domin zuwar ranar ta dauko mai masifar kyau,daidai ciff jikinta rigar ta kama,ita kanta saida ta juya tayi Murmushi a gaban madubin kafin ta zauna domin yin hira.
Dadai misalin karfe tara ta gama shiri saiga kiran umaruje,dan dama cewa yace tayi masa izinin ya kaita wajen dinner,da har taki amincewa amma ganin yanda ya damu yasa tace babu komai.
Toh kawai tace kafin ta fita tana tafiya a hankali saboda takalmin da ta saka mai tsayi.
A bakin kofar shigowa ta hadu dasu sameerah zasu shigo,tun safe da suka fita sai yanzu suka dawo,kallon kallo sukeyi da sameemah ganin kayan alfarmar daya ke jikinta.
KO ci kanku bata ceba ta nufi motar umaruje wanda yah ke tsaye a kofar gidan.
Yana ganin tahowarta ya fito tareda bude mata kofa ta shige,shima ya koma ya ja motar suka bar wajen.
Duk abinda yake faruwa akan idon su inna ramatu wanda suka fasa shiga cikin gidan suna kallon Ikon Allah.
Sameerah ce ta hade fuska gameda dunkuke hannu tace,
"Ummah kin Gabi koh,wallahi yau zan fara amfani da maganinnnan basai gobe ba,tunda boka yace matukar tashi tsaye mukayi ba toh abin sai ya fi karfinmu"
Hall din da za'ayi dinner ya dau haske da kida ga dare kaman ba shiba.
Sameemah suna shigowa aka dau ihu da tafi,ita kuwa dan Murmushi kawai tayi na gefen baki alamun ta ji dadin abinda sukayi mata.
Wajen da aka tanada dan zaman ta ta nufa kafin salon kidan ya sauya.
"Kai aboki dan Allah ganemin lady din can,gaskiya duk wanda ya sameta yah more,ga kyau ga kuma zarrah,kai da ganinta kaga zazzafar manyan mata wanda ake shiga taro dasu"
"U hmm saidai ka gani daga nesa,ita cefah aka zo taron dan itah,sabuwar shugabar yan vigilantee ceh toh,kai ma daga gani kasan za'a sha dabi,mace da shugabancin yan kato da gora,ai abin Akwai show billahillazi"
"Hmm Bari kawai,ni ina ga da gangan zanyi laifi dan akaini office din ta na dung a Ganinta kawai"
"Saika DA ur a niyya,idan naga ta wanye lafiya dakai toh nima sai nayi,dan ba a shaidar mutum a fuska,tsaff sai ta baka mamaki ina fada maka"
Hakadai abin yakasance kowa yana fadar albarkacin bakinsa,shikuwa umruje duk yanda yayi da sameemah tazo suyi rawa kin amincewa tayi,iyah yanka cake akayi aka danyi serving abinci kafin kowa yah kama hanyar sa.
Watsewa akayi saura iyayen gayyar wato sameemah da tawagarta,direct gidan kungiya suka wuce za'a fara sabon shagali,dan dama ta ayyana a ranta ita da gida kuma sai gobe.
Da daddare da kyar su sameerah sukayi bacci saboda tunanin mai zai faru,dan maganar boka na cewar indai har ba rabata akayi da maza ba toh bazasu taba auren miji mai maiko ba,hakan sukayi ta jiranta bata dawoba har sukayi bacci.
Zainab ce ta shigo sauri tareda fadawa inna ramatu sameemah tana shigowa cikin gidan.
Cikin gudu gudu sauri sauri suka gama abinda zasuyi kafin ta karaso.
Shigowa tayi amma kayan dayake jikinta ba na jiya bane da alama tah sauya kaya,babu sallama bare bisimillah haka ta zefa kan ta dakinnasu,wani abune taji ya coki tsakar kanta har saida kanta yah sara lokaci guda,sannan idan bata manta ba tah taba jin irinsa lokacin da ummah tana da rai.
Basarwa tayi tareda shigewa cikin dakin kawai,duk da kannata bai bar sarawa ba amma bata kawo komai a ranta ba sam.
Uniform din aikinnata ta dauka tana kallo hade da murmushi ita kadai tasan mai take rayawa a cikin ranta.
Wayar ta ce tayi kara tana dauka taga surayyah ce,kayan hannun nata ta ajiye kafin ta daga kiran.
"Hello Allah ya taimaki ogah"
Aka fada a daya bangaren,
"Dama Bayan an gama shagali munga ogah burgu yah bamu kayan uniform ne na aiki,dama ogah abinda wurine haka"
"Me kike nufi baku shirya bane"
"Ahah min shiryah ogah allah ya bamu sa'a toh"
"Yau Ku tabbatar kun gyara office din da duk wani abu daya kamata,ran monday kowa yasa uniform yah fito aiki,idan kuma naga mutum yasaba lokaci zai fadawa yan garinsu,kafin lokacin zan tsara wa kowa aikinsa da inda yakamata ya yi aiki,sannan zan duba tsofin maikata idan sun cancanta kuma zasuyi aiki dani toh zan barsu amma wasu dole zan sallamesu.
Dafatan kin saka a speaker kowa yana jin abinda nake fada koh"
"Eh kowa yana jinki shugaba,bari muje gida mu shirya saimu tafi gyaran office din,kuma ran Monday da asuba zanje,ai mun fi kowa jin dadin aikinnan"
"Ya is a haka ban as on surutunki nan surayyah,kudai kuyi yanda nace kawai"
Tana jin surayyah tana surutu amma ta shareta ta kashe wayar ta,shiyasa wani lokacin shirinsu da surayyah sai a slow,akwita da surutu da kuma lalaci,kubra da lubna sun fita nesa ba kusaba,saboda koh a maza ma sai an tona a samu kamarsu.
Tun daga bakin kofah umman su surayyah take jiyo feduwarta a zauren gidan har ta iso tsakar gidan. Ummah bata kulata ba sai cigaba da tsinar shikafarta da tayi,shima nazeef dayake zaune suna hira da ummah kallonta kawai yakeyi,
"Gaskiya umma ke yar gata ce fah"
"Da akayimin me mai sunan uwata?"
"Duk yayanki aikin damara sujeyi,nice ma babu wanda yayi zaton zanyi koh goge gogene sai gani da dankareren aikin vigilantee,ran monday dinnan mai zuwa za'a fara kwatance damu a garinnan,kuma wallahi babu mutunci kan ta ko uban waye,tunda shigaba ta bamu lasisi"
"Dallah rufema na baki,a wane aikinnaki da bai taka kara ya karyah ba"
"Kai ji nazeef dinnan,yo ba gwara namu ba da wannan shegen aikin sojojinnaku da mutum bai isah yayi abinda yaga dama ba,kullum hannunsa yana gefen kansa shi a dole ga mai biyayya"
Haushi ne yakama nazeef inda yah tashi zai maketa,ummah ce ta hana tareda cewa,
"Mai kake ci nabaka na zuba,ni bakaga kyaketa nakeyi ba,ai baza'aje ko ina ba zaka jita da ogar tasu,ina wannan yarinyar ce,kyaleta da ita kawai"
Ahah ummah albarka zaki saka mana zamu fara aikin damarar muma muji mai wasu suke ji a ciki,har suke tada mana jijiyoyin wuyah"
"Allah yasaka albarka"
Shine kawai abinda ummah tasu tace,aikuwa daga jin haka surayyah ta hau wani kirkirar doron da da bata dashi,
"Shikenan ai tunda kika saka albarka ummah to kowa ma yah kushe,kuma gyara gariannan sai inda karfin mu ya kare,sai mun kafa namu tarihin"
Tana shiga daki kuwa bata wani dade ba sai gata ta fito da uniform dinanta ta janjame belt dinnan kaman zata miyar shi cikin cikkinta itah a fole tayi damara.
Kallon su nazeef sukeyi suna boye dariyarsu dan karta gani,
"Yawwa ummah kallifa uniform din yanda sukayi min"
"Eh nagani kam,sunfi wannan tsukakkun wandunan naki,yau kam babu cin abinci da sauri ne,ko kuma yau baza'a koma ba ne?"
Zaro ido tayi sai sannan ta tuna ashe zasuje shiryah office,komawa dakin tayi da gudu tana cewa,
"Wayyo na manta Ashe fah ance mukoma,yau inaga tsire shugaba zatayi da nama na idan taji,ummah hada abincin gani nan fitowa yanzu nan"
Jijjiga kai nazeef yayi dan ganin ahirmen kanwar tasa,
"Wai ni ummah yau ban jita da safe ba,ko yau ma bata kwana a gida bane?"
"Eh amma ta fadamin wai dinner zasu je na shugabar tasu ta samu kujera sanann kuma suyi shagali nasu daban,har gari ya waye,kasan shahshancinsu ai,tun wancan satin take lissafin shagalinnan,mudai addu'a zamuyi tunda yanzu ta daina zuwa kwana a wani wajen ma a nemeta a rasa,amma wannan sai da ta fadamin su da sameemah ne da kowa,kaga ba lallai ne ayi badala a wajen ba,saidai sharholiya kam wannan wajibine"
"Toh shikenan Allah yah kara shiryawa ,indai zuwa wajen seemah alkhairi ne ana ganin sanji ai sai aiyi ta yimusu addu'a gaba dayansu"
"Hakane abinda muke fata kam"



*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤30❤


Manjo ne a kwance akan wata katifa wanda da ita da babu ma duk daya ,sai nishi yakeyi yana daddaga ciki,ga fuska tayi suntum kaman yan mata zasuyi kwalliya sai sheki takeyi.
Haushine ya ishi kulu ga wutar da take kokarin hurawa taki kamawa ga kuma dawainiyah da manjo.
"Kulu zo ki gyara min wuyannan nawa yayi tsami"
"Kai Dallah kaima ka rabu da ni,dame zanji wai,da wannan shegiyar wutar ko kuma da kai daka dameni,aikin banza lokacin dakake cin kudin ai bansaniba saida wahala tazo za'a zibgemin yau ga jaka"
"Yanzu kulu ni kike fadawa haka ,ina mijinki"
"Miji ? Muna miji dai,ai nayi kokari ma yini gudan da aka kawoka wane shegen ne ya leko a cikin yan gidannaku ya ga ya jikinka,har uwar da ta haifeka ma bata san me kake cikiba,ta dorawa kanta bakin kishi akan wacce ko yawo take da bakin jaki bata isa da itah ba(sameemah),daga ganinta da mai mota ta kwallafa wa ranta sai y'ay'an ta sun aureshi,sai kace itah nata dan motace dashi ake zaune dashi"
"Yanzu kulu ni kike zagi dan kinga ina kwance kuma harda uwata"
"Eh an zage kam,mai zakayi iyee?,kai ba gwanda kowa ma a cikin gidannan da kai ba,kafi kowa rashin amfani ,dan mugunta aka tashi aka hadani da kai,kuma duk inna ce ta bataka itah a dole ga mai da bata san laifinsa,gashi nan ta cuceka ta cuceni nima da nake ta fama"
"Haba habibiyata share hawayenki wallahi ina sonki sosai,kuma na miki alkawari kodan farin cikinki zan zan shiryu idan na warke na fara sana'a"
"Babu wani dadin baki ne dan nayi jinyarka saika warke ka koma gidan jiyah"
"Bazan komaba kulun majatan uwar gida sannan kuma amaryar manjo"
Murmushi tayi najin dadi kafin tazo ta gyara masa kwanciyar,sai nishi yakeyi babu dauriyah.
Sameerah ce zaune a bakin katifarta sai tadi takeyiwa sameemah wanda take danne danne a waya,
"Uhm naceba yar uwa mai yah farune naga kwanannnan sai zirga zirga kikeyi,koh wani abune yasamu"
Dan tsabar mamaki lokaci daya salma da sameemah suka dago suka kalleta jin yamda ta kira sameemah din,da farko kam ma saida sameemah ta kalli salma dan ta zata da salman take magana,amma sai taga ita take kallo.
"Uhm wani abu nakeyi,na riga ma na kammala sai kuma fara aiwatarwa"
"Ayyah allah yah taimaka,yah saurayinnan naki dana ganku tare kuwa"
Murmushin gefen baki sameemah tayi dan ta dago sameerah din,bare kuma salma wanda itah dama kar tasan kar ce itada sameerah,
"Yana nan kalau shima"
"Uhm amma yaushe zaki hadani dashi mu gaisa kuwa"
"Banida iko da rayuwarsa duk sanda kika ga dama kika nemeshi zaku iyah gaisawa banda business da hakan ni"
Shiru sameerah tayi daga haka dan taga babu alamar samun nasara a zancen.
Zainab ce ta shigo dakin tana rusa ihu kaman ranta zai fice,sameerah mai karfin gwiwar tambayar ta menene,amma sauran mutanen dakin koh kallo bata ishe su ba,
"Ba........ba shine ba wai an zanye yin auren sai ya dawo daga service din aikin dan sanda ,yace wai sai bashida kudi toh sunansa ya fito a cikin masu tafiyah service,kuma dama wai bai gama giniba yana so dama a daga auren"
"Koh so yake yah gudu dama ba"
Salma ta fada tana dariyar mugunta,wani ashar zainab ta nana mata kafin suka rukume da fada kaman karnuka.
Itah kuwa sameerah da dakin mahaifiyar su ta nufah da sauri domin jin tushen bayanin.
Da wuri ta tashi yau babu baccin safe,wanka tayi ta ruwan sanyi amma ba ta sanyin take na burinta kawai taje inda yake ranta.
Kayan uniform ta dauko na vigilant ta saka,dan karamin hijab din kayan ta saka tareda dora hular a kansa,hoda ta shafa kawai sai mai kafin ta feshe jikinta da turare,glass ta saka baki wanda yayi match da wandon jikin ta ga kuma kalar fatarta ta fito a cikin coffee rigar tasu,jakar ta dauka da kuma key din motarta kafin tah fita daga dakin.
Duk abinda takeyi su salma suna kallonta,dukkansu mamaki suka dungayi da ganinta cikin kayan,dan babu wanda tah fadawa zata fara aikin.
A tsakar gida kuwa bata hadu da kowa ba har ta isa wajen motarta ta shiga.
Su surayyah kuwa an fi kowa d'oki dan rana ma acan ta fito ta ganta,dukkan su kame wa sukayi tareda sarawa lokacin da sameemah tah iso wajen,dan labarin sauyin shugaba dama yazo musu,kuma sunyi farincikin da hakan dan dama babu wanda yake somsa,shiyasa da tace wanda yake bukata zai iyah tafiya babu wanda yah tafi,suna fatan dai kar ayi gudun gara a tadda zago.
Fitowa tayi a motar tana gyara zaman glass dinta fuskarta babu alamar fara'a bakinnan a d'ane.
Hanyar office dinta ta nufa koh kallonsu batayi ba,wata bazawara ce wanda anan suka zo suka samesu tah kalli surayyah tareda sauke murya kasa kasa tace,
"Hmm kika ce shugabarku tanada mutunci?,amma yanzu ji yanda tazo ta wucemu koj kallonmu bata yiba bayan wannan shine zuwanta na farko"
"Ke me kike ci na baka na zuba yanzu fah aka fara wasan,ki tsaya ki gani mana"
Itah kuwa sameemah batayiwa kanta a ko ina waijiba sai kan kujerar ta office din,saida ta zuyah ta sake juyahwa kafin ta saki wani dan iskan Murmushi.
Wasu takardu aka kawomata da alama sauran aikine da tsohon shugaban bai gamaba.
Zare glass din idonta tayi ta ajiye a gefe kafin ta daga takarda tah farko,case ne akan yanda karuwai da yan daudu sukayi yawa a gidan kara,yan hisba sun kawo case din akan za'a hadu dasu ayi amma babu wanda yayi magana.
Sai kuma na gaba yanda sane yayi yawa a kasuwa sannan idan an kama su yan sanda basayin komai akai,da kuma wani saurayi dayah kama wani tsoho a unguwarsu yayi masa duka,dan kawai yakaishi kara yah sace masa akuyah.
Dariyah sameemah tah fashe da itah saida mai kawo takardun yah ja da baya,daga ganin dariyahr kasan ta mugunta ce zallah,
"Irin wannan kujerar dama nake nema,inda zan baje tawa baiwar,kai inaso ka kiramin duk wani maikaci yasameni a waje yanzunnan"
"Angama Ranki yah dade"
Da gudu yah fitah kaman zai kifah.
Bayan mintu kadan yadawo tareda shida mata kowa ya hallara.
Fitowa tayi ta tsayah a gabansu,kowa yah kame kaman an daskarar shi,yaranta ta kallah acikin tsofin maikatan dukkan su sun sha kaya kaman ba suba,koba komai taji dadi da ta sama musu sana'a.
"Inaso kijini da kyau,wanda suke wajennan dayawa dama yarana ne nasan halinsu,su kuma sauran na duba bayanansu wanda ina fata muyi aikin daya kawomu banason shashanci.
Abinda yasa na kiraku shine,akwai casr kuda uku wanda sune suka fi girma kuma ina so yau dinnan basai gobe ba a gama dasu"
File din ta Bude tareda kiran suna,saida ta tabbatar ta raba wani rukuni gida uku tukunnan tace sauran su koma aiki.
Su burgu tah nuna da wssu suma biyar tace su je kasuwa,duk wanda yayi sata su kamo mata shi kafin ma yan sanda du sani,sannan wsu ma guda uku tareda surayyah da kuka shamsiyyah(bazawar nan),su kamo mata yaton da yayi duka ga tsohon anguwarsu.
Sai kuma wanda tasaka akan aje gidan kara kamen karuwai,amma kar a tabasu har sai taje tukunnan,kawai suyi kaman ba wajen suka jeba su yi shiru har zuwa yamma.
Nuna lubna tayi da kubra kafin tace su biyota zuwa wani waje.
Direct office din hisba ta nufah,tana isa ta nemi iso zuwa office din shugaban,shiga sukayi ta zauna su kuma su kubra suna tsaye a bayanta sun kame,dan dama matan sun ji karfi da kuka kira,bare suka samu training daga wajen sameemah na salon fada daban daban,shiyasa itama take ji dasu ta wannan fannin.
Dagowa yayi daga rubutun dayakeyi yana kallonsu,ganin sun shigo amma babu wanda tayi magana,
"Eh ina jinku mai ke tafe daku"
"Da baka tambayi mai ke tafe damu ba shiyasa nayi shiru domin baka daMa ka gama,amma yunda yanzu ka taambaya sunana sameemah sabuwar shugabar kungiyar vigilantee. Gameda abinda yakawomu kuma ba kkmai ba ne illah akan zancen case daka rubutah na gidan karuwai ne yakawoni saboda na ganshi a office"
"Eh anyi haka amma wannan case din yace bazasu damar yiba,ku kuma muma muna wani aikin har yanzu gashi bamuda wasu ma'aikata masu yawa,idan muka ce zamuje irin wannan aikin mu kadai,mukan samun barazana,toh shi kuma yace mana wai ogansa ya hanashi irin wannan aikin"
Numfasawa sameemah tayi dan tasan wa yake nufi da ogan,
"Shikenan karma damu dama akan case din nazo,Inaso kasaka hannu akan takardar Ta yajejeniyar ni zan ajiyesu a wajena ba ma kune zakuyi ba, nikuma a yau basai gobeba zan kamasu"
Hankalinsa ne kaman bai dan kwanta da zancneta ba dan da alama bai wani yarda ba,ganin hakanne yasa tace,
"Idan wata matsala ta faru ka dora laifin a kaina sannnan karka sake bani wani hadin kai anan gaba"
Karbar takardar yayi yai mata sign din kaman yanda ta bukata kafin yabata.
Tana fitowa direct gidan karuwan suka shige,acan nesa da wajen suka hadu da sauran yarannata inda itama ta fito daga motar ta suka shige.
Gidane mai fili sai dakuna dayawa,kaman dai gidan haya,da wasu yam daudu suka fara cin karo a tsakar gidan suna wasan karta,aikuwa suna ganinsu suka rufah da gudu kowanne yana zefar da zanin daya rufe kirjinsa dashi.
Dakuna dakuna suke bi suna fito da mutanen ciki,mutane kala wasu da attach wasu saikace fatalwa dan fari.
Duk tarasu akayi a tsakar gidan masu ihu suna yi masu roko sunayi.
Wata kujera sameemah taja ta zauna tanan kare musu kallo,wai yau itah ake roko kartayi rashin mutunci,gashi kuma gangar rashin mutuncin nata ta riga ta kada sauti.
Wani dan daudu ne yakalle ta tareda cewa,
"Haba ke kuwa sister ai andaina zamanin kame tun wancan karnin,ki fadi kawai nawa kike so a baki a wuce wajen"
"Ahah mai kake ci na baka na zuba dama ai za'ayi ciniki,har saikayi cinnki ka kaji,yanzudai bari muje a gyaraka ka koma ainihin siffarka tukunna koh?"
Shiru yayi jikinsa yafara tsima jin abinda tace,wata ce a cikinsu tace,
"In gaskiya ne naga ba'a je chamber su yar sheelah ba idan iskanci ne ma ai sun fimu,kawai dan dai suna lungune"
Tashi sameemah tayi tareda iza ketarta tana cewa,
"Ina ne muje ki nuna min wajen,wayaki k'aari kuma"
Wani lungu suka bi sai gasu a wani gidan irin wanda sukayi kame a cikinsa,dakin dayake farko sameemah ta bankada tah shige,zare ido tayi dan ganin da wanda suka hada ido.
Shima zare idon yayi da yai kulu kulu a duhu,gashi yah hada gumi shirkiff.
Da kyar bakinta ya samu damar tattaro harafin kafin ta furta....
"Kawu sheeeeehu!!!"

Toh lokacinku yah kare sai wani jirgin yazo zai dibeku yanzu dai ku sauka a nan wajen..............


*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login