Showing 21001 words to 24000 words out of 62773 words
sosai,saboda nasan idan mutum yana ciwo sosai mutuwa zayyi kuma in yah mutu bazai dawo ba,har kuka nake idan naga tayi shiru ,sai yah sameer yace min bacci takeyi kafin nayi shiru,dan saina ga kaman tah mutune.
Yauma a kwance nake a gefenta saina ji tana riko hannuna,tashi nayi na rike hannun tareda tambayar tah,
"Ummah mai kikeso na miko miki?"
"Babu komai inaso ki bani hankallin ki ne yanzu"
Jijjiga kai nayi alamun ina sauraronta,Murmushi tayi irinna dauriyah kafin tace,
"Inaso da farko seematu ki kasance mai hakuri,sannan duk rintsi karki watsar da ahalinki duk da sun kasance masuyin san ransu amma ki barsu watarana sai labari,ki kama mutuncinki a matsayinki na y'a mace,ban yadda kibawa wani namiji dama yah yaga mutuncinki ba,saboda kudi,wahala,koh kwadayi,idan kikayi haka bazan yafemikiba,duk wata huduba daza'a doraki a bayana ban yadda kibita ba sai yah kasance huduba mai kyau ce,in abune baki ganeba ko yah shige miki duhu ki tambayi dan uwanki kinji,sannan duk rintsi ki guji abinda za'amiki wanda zai ji miki ciwo,saboda boye yanayin halittarki daga idon mutane.
Allah ya tsare ki daga sharri,yah inganta rayuwarki sannan yah yabaki miji nagari"
Duk abinda take fada ina jinta saidai na gagara bata amsar komai saboda bansan mai zance ba.
Yah sameer ne ya shigo shima idonsa yana hawaye da alama yaji duk abinda take fadamin,shima tana kallomsa ta rike nasa hannun tareda cewa,
"Nasan kai kasan mai kake,Toh inaso kacigaba da bin hanyar dana doraka,sannan ka kulamin da rayuwar seematu domin tata rayuwar zata fi shiga hatsari fiyeda naka,karka bari wani mungun abu yah faru da itah,sai abu na karshe munyi magana da babanku,na bashi wata wassiyyah wanda nakeson yah cika min itah,koda bana duniyha wata rana yah baku wannan wasiyyar inaso ku zama masu cikata,sannan ku kasance masu min addu'a bayana,sann............nan...........uhhh ........uhh
Tarine yah sarketa jini yana fitah ta bakinta,amma duk da haka tana rike da hannunsu,cikin dauriyah ta hada hannunsu waje d'ayah,kafin tace cikin nishi
"Na baku amanar kanku,kar d'ayah yabar d'ayah cikin halin wahala shikadai,kuzama tsintsiyha madauri d'aya"
Tana gama fadan hakan ta sau hannunsu da alama jikinta yasake,suna kallo tana fadan wani abu wanda basajin mai take cewa har kuma suka ga idonta yah rufe.
Kallon yah sameer nayi ganin yanda yayi wani shuri kaman an daskareshi,
"Yah sameer yanzuma ina bacci tayi koh,kace min zata tashi idan anjima,kaji yah sameer"
Kallona yakeyi kawai fuskar sa da alamar tausayawa idonsa yana zubar da hawaye,batareda y ace komai ba yah rungumeni a kirjinsa,nima a sannan babu abinda nake bukata sai naji wanda zai saurari kukana,hannuna nasaka na zagaye bayansa tareda sake kankameshi,mun dad'e a haka kafin ya dago fuskata muna kallon juna,saida yah share fuskata kafin yace,
"Kiyi Shiru haka,ummah batason kina kuka ,sannan muma watarana zamuje inda ta tafi ,kidaina kuka haka bari na kira su baba yanzu "
Saida yaja numfashi tukun cikin yanayi na juriyah da alama yana cikin mawuyacin hali shima,jijjiga masa kai nayi ina jan majina kafin shikuma yah fita ya barni dagani sai gawar ummah nah.
Tsura mata ido nayi ina ayyana abubuwa da yawa a raina,ciki harda maganar da mukayi da ita nida yah sameer mintuna kadan da suka wuce,d'aga kaina nayi ina kallon baba umaru wanda suka shigo shida yah sameer da kuma inna ramatu,wani irin ihu inna ramatu ta rantab'a tana tsugunnawa a wajen,baba umarune ya wuceta tareda zama a gaban gawar inna hajara,
"Ke matace tah gari hajara mai sunan matar annabi ibrahim,kuma kema kin gado mai sunanki wajen yin biyayya ga mijikinki cikin dad'i da rashinsa,indai a lahira shedar mai mijice ke saka mata su shiga aljanna toh na shedeki matata,allah ubangiji yah yafemiki duniya da lahira sannan yayi miki rahama daga cikin rahamarsa😭😭"
Saida yah kare mata kallo yana zubar da kwalla kafi yah ja mayafi yah rufe mata kanta,shiru inna ramatu tayi tana sauraransa daga ji kasan ranta bayason yanda baba umaru yake yaba halayen ummah na kirki.
A zaune muke a tsakar gidan munyi zugum bayan an tafi kaita gidanta na gaskiya,har sannan zuciyata ta kasa gaskatamin cewa na rabu da ummahn tawa farincikin raina.
Mutanene suke ta shigowa wasu na fita wasu na shigowa,har babu inda wasu zasu zauna.
Wasu mutanene suka fara shigowa gidannamu bayan anyi kwana uku da rasuwar ummah,wanda ranar ne yakama ana sadakar uku,tun daga yanayin jikinsu mutum yasan ba y'an garinmu bane,baba umaru aka kira yazo yagansu bayan an kaisu d'akin da ummah take a da.mamaki ne ya isheni ganin yanda baba umaru yake gaisawa dasu kaman yasan su,toh yaushe yaje wajensu har yah sansu haka,oho.
Sum dad'e dan saida suka kai har wajen la'asar kafin suka sauke buhun shinkafa dana sugar dakuma jarkar manja suka tafi.
Mai hali baya fasawa inna ramatu tana cikin kukan munafurcinta,tana ganin wannan kaya ta share idonta tana washe hakora,(Allah yah shirya).
Yanzu ummah tayi wata guda da rasuwa mutane kowa yah manta da itah inka d'auke ni da yah sameer sai kuma baba umaru,nikam ma nice wadda mutuwa tafi bankad'a saboda cin zarafi tun ba'a kai ko'inaba nafara ganinsa a cikin gidan,su kuwa si yah sameer in suka fita aikinsu sai dare nagansu,toh dama shima rashin lafiyar ummah ne yake sakawa yana shigowa gidan,Amma yanzu tunda babu itah dare yake dawowa.
Dakin ummah shiya zama na yan matan gidan,kowa anyi mata shimfid'i,amma nikuwa sai dare yayi na tura kofa na kwanta a wajen,saboda duk sun saka shirginsu su Badariyyah da kuma manyan yan matan gidan irinsu hafsa,shukura,da kuma lami,dukkansu yayan kannen baban mune mata wanda sun kasa zama a gidamsu sunzo suna takura mana,saidai babu wanda zaiyi magana sai an tab'a d'ansa nikuwa wazayyi magana tunda babu tawa uwar.
Tun abin baya damuna saboda yarinta yamzu har ya kai na fara ganewa,sau daya na je wajen yah sameer na fadamasa cewa ba a bani abinci na koshi,yah tsina fuska yayi yana juya kansa,da alamar na takura masa,
"Kee bafa zan yadda kina takuramin ba ,dan kawai ummah tace na dunga kula,fisabilillah kina ganin dawowata kenan fah amma kina cemin wai ba'a baki abinci kin koshiba,nima kina ganin d'an kad'an suka bani amma nayi shiru nake ci haka,kiyi hakuri kawai kisha ruwa ki kwanta"
Kallonsa nake da mamaki kaman wanda aka sanjashi tun daga mutuwar ummah,takaicine yah cika zuciya tah ganin wanda zan ji sanyi a wajensa ma kallon na takura masa yake,yana kallon na takura masa,dole na sanja tunani na tsaya da kafafuna kawai.
Tashi nayi cikin sanyin jiki na koma d'akin na kwanta,
Jeji ne wajen mai cike da duhun dare da kuma ban tsoro,idan walkiyah ta haska babu abinda nake gani sai wasu halittu a tsaye,matswa nakeyi jikina yana rawa had'e da karkarwa,ji nayi na dungura da wani abu kaman bishiya alamun babu inda zan sake matsawa kenan,saidai abubuwan basu fasa matsowa inda nakeba shiru kawai nayi dan na saddakar da sake rayuwa a lokacin.
Rike fuskata daya daga cikinsu yayi yana hada kallona dashi,cikin wata irin murya yake magama mai cike da amo wanda nakejin ta har cikin jikina ba iyah kunnena ba,
"Hakika dole watarana zaki sallama ki dawo inda yah dace dake,kedin mallakinmu ce,duk da busan inda kike ba har yamzu amma dole muna hade dake,dole zaki dawo inda ya dace dake watarana,sakin fuskata yayi wanda saida wajen yah faramin zafi saboda rikon dayayi min,wata kwaryah suka mikomin mai cike da wani abu kaman jini,kin karba nayi ina kallonsu kawai,dannima gwana ce a taurin kai insu suna gadara da iyah shege,yah mutsa fuska nayi tareda kawar da kai,
"Bazan saha ba"
Shine kawai abinda nace,
"Hhhjhh babu dole a harkar musamman ma ke kinada muhimmanci a wajen mu muna jiram amincewarki"
Tun daga lokacin na ga kamar an wayemin wani duhu sai kawai na ganni a dakinmu,toh mafarki nakeyi ?ko kuma gaskiyace ni kadai nayiwa kaina tambaya sannan na kasa bada amsa.
Tashi nayi naje na sha ruwa na dawo,har sannan mafarkin danayi yana tsaye a raina,yau kusan kwana uku kenan kullum sanayi irin mafarkin,duk da ina shakkar daukarsa a matsayin gaskiya amma nasan yanada alaka da wani abun,saidai banida wanda zaikula da halin dana ke ciki bare yatayani yaki da abinda yake shirin tunkaroni,zama nayi akan gadon duk abin duniya yah isheni,da kuma wane irin aiki zan samu na dungayi saboda magance lalurin rayuwata,tunda nagane abinci ma baza'a bani mai yawa ba ina kuma ga sauran abubuwan bukata na rayuwa.
Da safe ina tashi bayan na cinye d'an dumamen da'aka bani nayi wanke wanke sai na fita waje wajen abokaina su wanda yanzu suke zuwa gonaki aikin gona,ina zuwa kuwa na samu suna jirana saboda munyi dasu nace nima zanje.
Gonar da nisa sosai haka muka tafi a kafa,dayake tafiyar yarace bamu damu da nisan ba haka har muka isa.
Gonace mai girma sosai babu komai a ciki sai wake,yah nuna yayi kyau,roro muka fara cikin buhu naira d'ari d'ari,da murna na fara jin zan samu kud'i nima na sai abubuwan danake bukata.
Saida muka kai har lokacin wajen azahar kafin kowa yaje yah faracin dan tuwon daya zo dashi,nikam ban tashiba saboda nasan idan naje wajenma babu abinda zanci tunda banzo da komaiba,su iliya ne sukai takirana nazo muci amma naki,saboda banason a yanzu dogaro da abin wani koyaya yake kuwa. Kafin a tashi saida na cika buhu guda biyu,ko su dasuka saba zuwa buhu daya sukeyi,mamaki na bawa shikansa mai gonar inda yah bani dari biyu da hamsin saboda dagewa danayi,karba nayi tareda godiya muka kamo hanya muka dawo gida.
Ina shigowa gidan naji karar karan dawa a bayana,tun kafin mai dukan yayi magana nasan inna ramatu ce,aikuwa bata gama sauke karan ba tabini da uwar ashar tana fadin,
"Yar kusun uwa shegiyah,gidan uban wa kikaje tun safe sai yanzu kika dawo ina ta neman ki ki iyo markad'e"
Babu alamar kuka na kalleta raina a bace nace,
"Aikin kudi nabi yara wata gona"
"Eh lallai wuyanki yayi kauri nawa kike harkin fara wani neman kudi,ke yanzu har kinkai a barki da kudi?,bani kudinnan naga naira nawane,wuyarki danake sha duk wani kudi kika samu dama ki kawomin su"
Kallonta nake da Mamakin jin furucinta,su kuwa su inna larai suna gefe suna zigata kaman in anamin azabar cetona sukeyi,maida hannuna nayi baya alamun bazan bata kudin ba,wata wawiyar cafka ta kawowa hannuna na yi saurin gocewa saiga ta tashsh a kasa tayi zaman yan bori,daga kai tayi tana kallona da mamaki,saidai babu alamar tsoro a idona saima kallonta nake kaman zan kai mata duka,hakika in idona yagani dadai kaman na ga alamar shakka a idonta,wuceta nayi na nufi d'akinmu,na tona rami na boye naira d'ari,kafin na d'au hamsin na tafi wajen mai shayin unguwarmu domin nasiya.
Daga ranar tunda nagane da aikin gona ko yan anguwarmu bazasu je ba saina je,dan yanzu nagane da zamana babu kudi hatsarine tunda babu wanda zai kula da rayuwata.
Yauma tafiyah mukeyi nida su iliyah kaman kullum,saida mukayi kusan rabin tafiyar,mun bar gari a baya,turus muka tsaya ganin wani maciji a gabanmu,abin yara da tsoron macijj cikin sauri muka koma da baya zamu koma,saikuma cikin rashin sa'a yah sareni saboda nice a gaban tafiyar dan yanzu nazama shugaba,dan a jinina yake koh cikin yara yawanci nike jan ragamar abubuwa.
Kallona sukeyi da Mamaki kaman idonsu zai fito saboda ganin abinda yah faru,saurin kawar da mamkinnasu nayi tareda cewa,
"Kai Karku damu nasha maganin maciji babu abinda zaimin"
Ganin sun yarda da abinda nacene yasa hankalina ya kwanta saboda kullum ina kula da gargadin da ummah tayimin game da halittata,alama nayi musu akan suyi gaba ina zuwa,yarda sukayi da abinda nace kafin sukayi gaba,saida naga sun bace babu alamarsu kafin na bude inda macijin yah sareni.Wajen ciwon ya warke sai wani abu daya fito daga cikin ciwon baki kirin da alama dafin macijinne,irin yanda ya tabayi sanda kunama ta harbeni lokacin ummah tana da rai,rude kafar nayi kafin nabi bayan hanyar da macijin yabi bayan ya sareni.
A kwance naganshi a jikin wata bishiyah,yah murde kaman igiya yayi baki,tsugunnawa nayi ina kare masa kallo tareda Mamakin shin wane irin jini ne dani,duk wani abu inya dandana shi sai yah mutu.
Tunani na tafi lokacin baya,idan na tashi da safe sai ummah ta kade shimfidina saboda duk sauron daya cijeni mutuwa yakeyi,kafin safiyah sun taru a gefen shimfidina,haka kunamar ma itama mutuwa tayi ummah ta zefar da itah ,toh gashi macijin ma ya mutu.
Tun lokacin da ummah tana raye ban taba tunanin tambayar taba saboda yanayin yarinta,amma yanzu na gano cewar nidin dabance da sauran mutane kaman yanda dodannin mafarkina suke fadamin,amma har yanzu zuciyahta taki yardar cewar nidin dabance har yanzuina ji a jikina nima mutumce kaman kowa,tunda yah sameer ma mutumne yaza'ayi kowa na gidan mutum kuma niba mutum ba,hakan ba mai yiwuwa bane .
Da haka na kawar tunanin a raina na tashi daga tsugunne a gaban macijin na kade rigata na bi bayan su iliyah wanda sunyi nisa yanzu.
Ina zaune a tsakar gidan a gefe kowa yana ta harkarsa yau banje ko ina ba saboda an kare amfanin gona saidai muna tunanin tafiya wani gari aiki,saboda yanzu mun kware a wajen aikin kodago sosai musamman ma ni ,wani yarone yah shigo da sallama tareda cewa wai nazo inji yah sameer,gyara dan kwalina na nayi nabi bayan yaron,a zaune na sameshi akan benchi gefen dakinsu,samun waje nayi na zauna banyi magana ba,
"Ke Bali I yah sallama bane bare kuma gaisuwa"
Shiru nayi ina jinsa dan ina akwai wanda nakejin haushinsa toh ya biyo bayan yah sameer saboda su inna ramatu idan basu kulada rsyuwata ba banu komai saboda ni ba dolensu bace,amma yah sameer shi aka bawa alhakin kulawa dani,kobai min komai ba a kallah ya tambayi wane hali nake,amma babu ruwansa saima wata masifa daya dauki yi kaman wani shine uban mutane,
"Duk abinda kika ga dama ma kiyi tayi,kowa a gidan zancen rashin muncinki yakeyi dama ummah ce take daure miki gindi gashi yanzu babu itah"
Katseshi nayi da masifar dayakeyi kafin nace,
"Uhm akwai abinda zanyi idan ka fadi metasa ka kirani"
"Dama ba kiranki nayi na dunga kallonki ba inason na fadamiki gobe zan bar garinnan da asuba zan tafi aikin soja,ogah soja na anguwarnan ya min hanya,saiki fadamin mai kike bukata"
Kallonsa nayi kawai na ya rainamin hankali dan yaga ni yarinya ce ,banda haka yaushe rabon dan ganshi sai yanzu zai cemin wai me nake bukata?
"Babu abinda nake bukata ni,saboda duk abinda nake bukata,ina yiwa kaina dan haka kaje allah yah bada sa'a,idan shikenan nizan tafi cikin gida"
"Eh shikenan dama dan karkiji na tafine baki saniba kice ban fadamiki ba,"
KO magana ban sake yi masaba na bar wajen saboda wani abin bakin ciki daya tasomin dan takaicin halin yayannawa na rashin kulawa.
Dakinmu na shiga da sauri ,ina shiga kuwa na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,saboda duk abinda yakemin ma na halin koh inkula,koba komai in ina ganinsa ko ina tuna cewa yana cikin gidan hakan kan karamin sanyi a zuciyahta,musamman kama da yakeyi da ummah kaman an tsaga kara,irin kyau na anihin fulanin asali,naso ace nima na iyota saboda na dunga kallon fuskata a madubi duk lokacin dana yi kewarta,saidai yanzu shima zai tafi yah barni a cikin wannan halin na kunci ni kadai,wanda kullum cikin kalubalen rayuwa nake.
Saida nayi kukana na koshi kafin na fito daga dakin,ina mitstsika ido.
Yah sameer kuwa kaman yanda ya mafadamin da asubar yabar garin yah nufi jahar porthacourt,domin cikar burinsa dayayi niyyar cikawa,nima kudira nayi a raina saina cika nawa burin na tafiyah babban gari aiki nemam kudi,wanda zamubi irin manyan motocinnan da suke wucewa idan sanyi yazo.
Haka rayuwar take ta garamin da dadi da babu dadi,har muka fara shiga sanyi sannan an gama duk aikin gona,shiri mukryi sosai da wasu tsofaffi wanda suma dasu zamu tafi,inyaso idan lokacin aikin can yakare saimu dawo,dama suna zuwa duk shekara nice dai sai wannan shekarar zan fara zuwa,zancen makaranta kuwa dama ba zuwa nakeyi ba tun daga mutuwar ummah na daina zuwa dama itah ce take korani zuwa makarantar ba a son raina nake zuwaba,dan haka koh hanyar makarantar bana zuwa,idan kanason rawar jikina toh aikin kudine zanyi a biyani toh zakaga aiki har sai ka kama baki.
Tun kafin saura sati dayah da tafiyar nake ta shiri kaman ance zamje makkah,nayi wanki da sabulun dana siyo duk da ma kayan sun tsufah kyakykyawan mutstsika su kayi saidai kaga garinsu a cikin hannunka. Shagon dan anguwarmu naje na sayi garin kwaki rabin kwano dakuma k'arago a wajen a wajen masu tallah,a takaicedai na hada kayana kiciff saboda tafiyah.
Acikin akwatin ummah na karfe na jera kayana a ciki ina kuka ina komai haka na dauko kayan na fito daga dakin,wanda bantaba tunanin zan barshi a kwana kusaba,kkda na kwana dayane bare na watanni.
Dakin inna ramatu na shiga suna zaune ita da baba umarun,tsugunnawa nayi daga gefe tareda gaisheshi,maganar sa ta farkoce tah batamin rai sosai,
"Ahh sameemah dama kina nan yaushe rabon dana ganki a cikin gidan,yanzun wani abune yah faru ?"
Daga masa kai kawai nayi tareda cewa,
"Eh dama inaso zanbi su iyar shehune aikin gona zuwa cikin babban gari"
Shiru yayi yana tunanin maganar tawa,har zai ce wani abu inna ramatu tai caraff tace,
"Ahh Toh ai dakyau kije allah yah tura keyah"
"Ahah ramatu hakan bayyiba tafiyah mace neman kudi hakanma har wani garin?"
"Ahh ba ita tace zatajeba ina ba kai ka tursasa mata ba,ai babu alhakinka koda wani abune yah faru,taje kawai allah yah tsare hanaya"
Daga kai kawai yayi alamar yah ji,nikuwa koh na jira yace wanj abu na kama hanyata na fita a cikin gidan,koh sauran kofofin ban shigaba nayi musu sallama,shima abinda yasa na fada masa dan yah amsa sunan uba ne,badan hakaba saidai yaji labarin tafiyata,dan hakan kamar halin gidannamune in kaga da hanya kawai saidai aji baka nan kayi wata hanyar.
** *tan uwa mukula musamman ma mata,saboda daga majority matan mu na yanzu daga an saki kishiyarki koh kuma ta rasu sai yah zamana duk wani aiki su za'a dinga sakawa ko kuma shikenan sun daina zuwa makaranta saboda dama uwarsu ce take kokarin rakasu makarantar*.
*abinda matanmu basu saniba shine idan yaron yayi karatum watakil ke zai fara amfana saboda ke yatashi yagani ba uwar tasaba,mu kula dan Allah,d'a na kowane idan da hangen nesa*.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤
Kar ku manta da
#comment
#share
#like
#follow.
____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤
Wattpad username:SAKHNA03
❤15❤
Lokacin danaje gidan su iyar shehun ban samesuba sai sallahu suka bari akan na bisu da sauri sun tafi neman motar