Showing 18001 words to 21000 words out of 62773 words

Chapter 7 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4425

tayi sama tai kyass dasu kafin tace,
"Ki kawomin ruwa mai sanyi kawai,su kuma kowa ki kawo masa abinda ransa yake so"
"Sai ogahhhh suka fad'a cikin jin dad'i"
Kafin kowa yah fadi wane irin kayan maye yakeso.
Bayan an kawone kowa yah fara hawa caji,kafin sameemah ta kallesu d'aya bayna d'aya tana wani linshe ido kaman wanda akewa tausa,ajiye kofin ruwan sanyin tayi kafin tace,
"Kusha iyah shanku,daga yau duk kun daina shaye shaye"
Kallonta sukayi a zabure cike da Mamakin abinda ta ce,
"Eh Ai nasan kunjini,shaye shaye is enough from now,do you hear me"
"Kowa kallonta yayi kamar ba itah ba,jin yanda take turanci kaman wata yar gidan mongopark,
"Daga yau duk gyaraku zanyi na d'ora ku a hanyar gaskiya,saboda iyayenku basa son abinda kukeyi,kuma nayi tunanin dan inaso nayi iskancina bai kamata nasaka ku acikiba,bayan wannan shaye shayen dakuke zai iyah tab'a hankalinku dan na kula ni kuke biyewa bayan nidaku ba d'ayah bane.
Saboda haka wani watan zan zama shugabar kungiyar vigilantee na garinan,dukkan ku zan d'aukeku aiki,saidai bazan hana kowa yin muguntar daya ga dama na,amma shaye shaye na hanaku daga yau,ni kadai zan dungayi banda ku,saboda zai iyah yimuku illah.
Dan haka kowa yaje yah shirya kafin zuwa nan da wani watan,zaku tayani fara aikin rashin mutunci a garinnan,dan nakula kowa yah rainani,tun daga kan yan gidanmu har kan yan gari saina saita su na gyarawa kowa zamansa.
Da fari sun ji babu dad'i data hanasu shaye shaye,amma daga baya da sukaji zasu sami aikin vigilantee kuma kowa zai yi tsiyarsa yanda yaga dama ba mai hanashi,ai suka fara ihu,kowa yana tunanin wace irin mugunta zai shuka a garin saboda ya kafa tarihi.(Allah dai yah kaimu lokacin)
Suna cikin ihunsu ne,itakuma sameemah tana zaune kaman wata mai hankali tana jinsu,wasu y'an matane suka zo wajen table dinnasu guda biyu,sunyi shiga irin ta bariki amma daga ganinsu kasan bakaraman gogaggu bane a harka tsiyah,wani rausaya sukayi tareda sauke muryah kafin sukace,
"Uhm idan bazaki damuba seemah jar wuyah muna san muyi magana dake"
"Ku fad'i miye ina jinku"
"Am da mundan fita waje saboda yanayin hayaniyar wajennan da kuma gamu a gaban maza,sannan maganar mai muhimmanci ce"
Har su burgu sun hayyak'o zasu fara masifa ,sameemah tah dakatar dasu tareda cewa,
"Ahah ban as on hayaniyah,ku kuma ina kukeson muje muyi maganar?"
"Akwai wani lungu ta bayan gurinnan inaga muje can,saboda nan babu kowa"
Burgune ya hararesu kafin yace,
"Gaskiya shugaba bai kamata ki bisu ba ,ni kawai daga ganinsi naji ban yadda dasuba gaskiya"
"Kai ne gaba dani koh nice shugaba?"
"Kece shugaba"
"Toh bance kasake shiga maganar nan ba,sannan kar kowa yah biyoni ku gama abinda kuke ku tafi gidanku"
Tana gama fadin hakan ta tashi ta bi bayan matan suka bar wajen.
Saida sukayi tafiya mai nisa amma babu wanda yah ce komai daga itah harsu,dan a yanzu sun bar wajen hasken club d'in sun fara shiga cikin duhu,tsayawa tayi tana karemusu kallo,yayinda suma itah suke kallon ganin ta tsayah,murmushi tayi tareda kama kunkumi ta gyara tsayuwarta,
"Wai har yanzu bamu iso gun wanda suka aiko kun ba,koh suna tsorone basu fitoba,yanzu kam ai munfita a cikin haske,kafar mutane ta d'auke a wajen ,duk abinda zasumin ma babu wanda zaiji su"
Zaro ido matan sukayi da Mamakin yah akayi tasan abinda suke niyyar aikatawa,kallon kanannan yara tsyimusu kafin tak'ara da cewa,
"Lallai Ku yarane,a tunanin ku bansan me kuke nufi ba,toh tun a hanya nakulada ku kuna bibiyata,har na shiga club din kuma kuka kama table,bayan kunyi waya da wanda yasakaku kafin kuka nufo inda nake".
Fezar da iska tayi daga bakinta irin na takaicinnan sannan ta d'ora da cewa,
"Lallai wanda yah aikoku bai sanni ba har yanzu,ku kuma ba laifinku bane,amma idan muka gama da wannan cakwakiyar ku tabbatar kunnemi inda nake kunzo ,domin inason yin magana daku"
Bata gama maganar ba tajiyo karar fed'uwa a bayanta anabin kid'an wakar *naira maley*,koh kuyawa batayiba har me wakar yah zo ta gaban ta,da wata wuk'a a hannunsa ya sak'alata a wuyansa.
"Yau wata tazo hannu babu yaranta,ina dasu kike takama har kika aikatawa shugaba haka(buba jini).Toh yau saidai uwarki ta haifi wata,dan saimun farke cikinki mun cikashi da kasa,mun jefar a hanyar dabbobi"
Duk maganar cikin larabci yakeyi irin na sudan,dan shikansa mutumin baiyi kama da mutanen nijeria ba.
Farine sol yahsha rawani ,amma koh a duhu mutum yah ganshi yasan ba karamin tantiri bane.
Wani ne daga cikin mutanensa yah matso kusa da itah tareda fassara mata abinda ogannasa yace,saidai har yah gama fassarar babu alamar tsoro a fuskar sameemah,dan ko motsawa batayiba daga inda take.
Mutumin ne yah kalli yaronnasa tareda tambayar,
"Ka fassara mata duk abinda nace kuwa?(yah kara fa'da cikin harshen larabcin)"
"Eh shugaba dukka na fassara mata"
Fusata yayi da yanda tah wani tsaya babu alamar tsoronsa,bayan duk kasar dayaje kowa tsoronsa yake,cikin zafin nama yah d'aga wukar hannunsa yah shaftawa sameemah a hannunta na hagun inda rigarta bai rufeba,wanda kuma yayi dadai da isowar su burgu wajen da gudu.
Ihuu suka fasa dukkansu ganin abinda akayiwa shigabar tasu,burgune yah isa wajenta da sauri,saidai tsayawa yayi cakk a gabanta yana karewa wajen da'aka yanketa ido,jijjiga kansa yayi tareda murza idonsa,anya kuwa yah gani dadai,saidai lokacin daya d'ago idonsa yah kalli Mamakin dayake kan fuskar kowa har shikansa wanda yayi aika aikar sai hakan ya tabbatar masa da abinda yah gani gaskiyah ne ba gizo idonsa yayi masa ba.
Wajen da aka yanki sameemah ne yake komawa yana had'ewa dakansa,kaman yankan wuk'a bai tab'a wanzuwa a wajen ba,shikansa jinin daya fito a wajen k'onewa yayi ya b'ace b'atttt.😲😲😲.

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤13❤

Ganin kallon da burgu yake mata yah isheta ne yasa ta tureshi daga kusa da itah kafin tace,
"Kai miye kazo kusadani har haka kaman zan maida ka cikina,wato dana ce karkuzo saida kuka biyoni koh,banzaye taron matsorata,ji idonku kaman kunga aljani da tsakar dare"
Har tagama masifarta bayan ta tureshi bai ko motsaba,saima kallonta yakeyi kaman yah samu hoto.
Wuceshi tayi taje har gaban shugaban,wiwi din da take hannunsa tah karb'a saida tayi masa zuk'a mai kyau kafin ta fesar tah hanci da baki,jefarta tayi take a kasa kafin ta mayar masa da martanin maganar da yayi mata cikin harshen larabcin da babu inda akeyinsa sai ainihin cikin kasashen larabawa.
"Oh da kana tunanin banajinka d'azu koh,hmmm lallai kana cikin duhu a gameda sanin koh ni wacece,saidai yanzu zan nuna maka wani misali"
Tana gama fad'ar hakan tayi masa ruk'o tareda kafa hakoranta a akan wuyansa,babu wanda yasan mai yah faru sai ganin sa sukayi dukka yah fad'i a kasa kaman wanda yah mutu.
Kare masa kallo tayi tana goge jinin dayake bakinta,tana kuma tofar da yawu,
"Ka tursasani yin abinda banida niyyah,ku kaishi asibiti aka ra masa jini yah mori lokacin sa kafin su biyo nemansa kwanan sa yak'are"
Juyawa tayi ta bar wajen,har ta yi nisa amma su burgu basu biyota ba kamar wanda suke jin tsoron ta a yanzu,kallonsu tayi harda matan da aka aikosu gurinta,kafin tace,
"Duk wanda yake wajennan yaga abinda yah faru inason gobe da safe yah sameni a office din kungiyata ,wanda bai san wajenba yah samu yarana su rakashi,kunji ina?"
"Eh munji muka zamu dole"
Kowa a wajen yah amsa jikinsa har rawa yakeyi tun daga kan yarannasa har yarannata.
Tana komawa gida ta shige dakinsu kan gadonta tareda rike kanta wanda yake barazanar fashewa dan azabar ciwo,da haka har bacci barawo yah saceta.
Da safe gidan da shirye shirye aka tashi na zuwan major sameer wanda zasuzo shida matarsa da kuma d'ansa,zuwan gobene amma tun yau ake shiryawa saboda cewar matar tasa yar shugabansu ce.
A bangaren sameemah kuwa da ta tashi ma batasan wace wainar ake toyawa ba saboda wankan ta tayi ta fice babu wanda tayi wa magana.
Motarta ta nufa wanda ta ajiye a kofar gidan,abin mamaki babu yaro ko d'aya a kusa da motar,saboda da wanine koh mashin ya ajiye sai an jefar dashi barekuma sabuwar motah

Direct gidan kungiyar tasu ta nufa inda take kiransa da office dinta,saboda a makare ta zo ,gidan a cike yake kowa yah hallara ana jiran isowarta.
Tana shigowa kowa yayi tsitt kaman ruwa yah cinyeshi saboda ganin fuskarta a murtuke kaman ta boss din y'an indiyah.
Zama tayi akan kujerarta yayin da kowa yah zube akasan wajen yah zauna kaman wanda akayi musu wahayin su zauna a lokaci d'aya,kallonsu tayi da mamaki ganin harda su burgu ake mata kallon dodanniya ko mayyah,wanda ko kadan bata ga laifinsu ba saboda ita kanta tasan ta dace a kirata da dodanniyar,domin tun tashinta lokacin data fara maida martanin abinda ake mata ,yazamana kowane halitta yah rabeta sai yaji tsoronta,"lallai akwai aiki"ta fad'a a ranta.
Gyaran muryah tayi kafin daga baya tace,
"Kowa yah ga abinda yah faru jiya daddare ko?"
"Eh kwarai kuwa mun gani sosai"
"Toh inaso daga nan wajen kar kowa yah tuna cewa yah ga abinda ya faru barekuma yabawa wani labari,idan kuma ba haka ba,............"
"Baza akai ga hakaba babu wanda yah tuna abinda yah faru ,koba haka ba yan uwa"
Burgu yah fad'a yana kallon kowa a wajen,cikin sauri kuwa suma suka amsa da cewa,
"Hakane babu wanda zai tuna da abinda yah faru"
"Shikenan naji abinda kukace,saidai nasan a yanzu kunsan koni wacece,kowa a cikinku zai dunga kallona a matsayin dodanniya,kaman sauran mutanen dana yi rsyuwa dasu a baya,saidai bazan ga lafinkuba saboda nasan dagaske hakan nake"
Sukunyar dakai tayi alamun hakan yah tabata,saidai cikin sauri tamayar da fuskarta wanda babu wanda yasan mai yake cikin zuciyarta.
Burgune yah d'ago kaman zayyi magana sai kuma yayi shiru,kallonsa tayi ganin yanda magana ma yanzu yakasa yi mata,ganin yanda a lokacin baya har kyaleshi take idan yah isheta da surutu,
"Karamin shigaba wace magana kake da itah?
"Eh dama shugaba,mun ji kinyi yaren larabci kaman wata balarabiyah,ga kuma abinda yah faru wanda gaskiya yah shige mana duhu,toh kafin kizo kowa yah ce na taimaka na tambayeki ,idan bazaki damuba munason jin tarihinki"
"Shine bukatarku jin labarina"
"Eh Ranki yah dade"
"Toh shikenan bari naga koh bazai d'auki lokaciba,saidai inaso kusani bawai zan fad'amuku saboda ku kai wa wasu labariba,saidan inason yin aiki daku,kuma naga yakamata kusan ni danjin da wa kuke zaune"
*** *** *** ***

Da farko kaman yanda kukaji sunana SAMEEMAH,saboda tunda nayi wayo haka na tashi naji ana kirana,abinda yha faru kuma kafin nayi hankali toh banida masaniyah akai.
Mahaifiya ta hajara batada lafiyah,kullum tana daki kafafunta suna ciwo,ko yau she nice nake gyara kaya idan tah bat'a sannan na kai mata abinci idan kuma taci na fito dashi,shikuma yayanah wanda shima muke uwa d'aya dashi wato yah sameer,shine yake wanke kaya idan tah b'ata saboda ni sannan ban yi wayon yi mata hakanba.
Watarana da safe na tashi daga bacci da safe lokacin banfi shekara shida ba,saboda tun bankai shekarun yin wasu abubuwan ba nake koyah,duba da halin da muka tsinci kanmu nida ummah tah,shikuma yah sameer namijine kuma yayi girma koyaushe suna gona shida baba umaru ,don su manjo ko me za'ayi bazasu jeba,kuma haka inna ramatu take d'aure music gindi suyi abinda suka ga dama.
Bayan na yi shara da kuma gyarah dakin da muke,inna ramatuce tah shigo d'akin tana ta zage zage wai ummah tah bata iyah aiki kuma ta hanani ni na gunga tayasu aiki,ummah ceh takalleni bayan ta d'auke idonta daga kallon inna ramatu wadda tah kama labulen kofar ta rike tana ta masifa kaman tanayi da y'arta ba kishiyarta ba,
"Seematu tashi kije ki tayasu wanke wanken kinji keda su sameerah kuyi"
Inna ramatuce tayi saurin cewa,
"Su sameerah bazasuyi ba itah kad'ai zatayi ,ai su jiyah su sukayi lokacin da kika aiketa karb'o maganin munafurci,yanzu haka ma na cutar damune mu da y'ay'anmu"
Ummah bata kulataba saini ce,da abin yah k'ona min rai nayi magana,saboda maganin da take magana akai,manjo fah ummah tah aika a wani kauye kusa damu amma yak'i zuwa,saboda yah sameer yah tafi aikin kud'i shida yaran unguwarmu,amma haka inna ramatu tace bazaijeba saini ta aika naje na karb'o duk da aikan yayimin girma,amma ji abinda take cewa kaman batasan mai ake cikiba.
Tun kafin nayi magana ummah tah katseni tareda cewa,
"Seematu maza je kiyi wanke wanken allah yayi miki albarka"
Kallon ummah nayi da takaicin yanda take bin duk abinda sukace kaman wasu iyayenta bayan itah ce duk babba a gidan idan ka d'auke IYAH MAI KALWA(mahaifiyar su baba umaru,matar alhaji babba,kakarmu kenan).
"Amma ummah kince fah nayimiki tausa lafafunki suna ciwo?"
"Eh ba sosai bane kije kiyi inyaso saikimin daga baya"
Dan takaici haka badan nasoba na bi bayan inna ramatu ina zobara baki.
Na dad'e tsaye a gaban wanke wanken ina kallonsa saboda bala'in yawansa kuma wai ni zanyishi,kwallar da ta fito a idona na share kafin na tsugunna na fara shirye shiryen farawa.
Na shafe kusan awa d'ayah inayi duk kayan jikina sun jik'e jarab da ruwa,ban kulaba sai ganin Badariyyahn nayi ta watsomin kwanuka tun daga sama,har saida wani kwanon silver yah bigeni a kan goshina,kallonta nayi amma ko nuna alamar mutum yana wajen batayiba sai kama hanya da tayi tah juya,tana karairaya itah a dole ta fara k'irgen dangi.
Ihun yara na faraji wai ankawo gyad'ar baba shehu ,da gudu nabar wanke wanken na zura da gudu domin nima kar ayi babuni.
Kan gyad'ar muka hau nida su salma da manu muna tah tsina,karar duka naji akaina kaman saukar aradu,ihu nafaryi tareda tashi daga kan gyad'ar dan ganin waye,inna ramatuce take dukana wai ta bani aiki bangamaba kuma na tafi kan gyad'a.
Dakinmu na shiga dasauri na tsugunna a gaban ummah ina kuka,kad'e kurar da take jikina tafayi saboda birgimar danayi a tsakar gida.
"Toh kiyi shiru haka"
Ta fad'a tana duba inda yah tsage a jikina yana had'ewa da kansa,nima kalon wajen nayi har sannan ban daina kukan ba,
"Nasan kuka ne irinnaki amma ina babu zafi?"
Jijjiga kai nayi ban bata amsa ba,
"Ni abinda nake tsoro seematu banason kina lalfi suna dukanki,idan wata rana kikayi laifi suka gane cewa ciwo a jikinki Yana mannewa da kansa bansan mai zance ba,maganganune zasuyi ta fitowa wanda bazasumin dadiba sam"
D'aga mata kai kwai nayi alamar naji,kafin ta bingire a wajen na fara bacci.
Na manta ma da tausar danace zanyi mata itama kuma bata tasheni ba ,saboda dukkan mu tausayin kanmu mukeji.
Abubuwa da dama sun faru a satin ciki harda zafin da rashin lafiyar ummah yah k'ara,yanzu har yah kai koh tashi tah zauna bata iyah yi sai an taimaka mata,shikansa yah sameer ko yaushe yana d'akin,nukuma nakan fitah wasa,wajen yara a waje,saidai in anyimin abune zan dawo gida kokuma in dare yayi ,dama masu iyah magana suna cewa *sai gida wai an doki kare a kayi*.
Fitowa nayi daga dakinnamu aikuwa cikin rashin sani na shambe kalwar IYAH,wacce tah shanyah a Rana tana jiran ta dan sha ta curata dan taci kasuwar gobe,tsayawa nayi nai shiru dannaji ta ganni koh bata ganniba,cikin daga muryah kuwa irin ta masifaffunnan muryarta ta doki dodon kunnena.
"Keeeh dan kusun uwarki uwarkice tace kibimin takan kalwa koh kuma tashen rashin hankalin danaji dama ana shedarki dashi,dazaki zo ki takamin kalwar yanzu idan nace uwarki tazo tayi zata minne,tana nan da itah ba gurguwa ba itah ba mai kafafuba,bata tsinana komai saidai a zuba abinci a kai mata ta cinye.
Cikin yanayin dama na saba da masifarta nayi ficewata wajen wasa,dama ana ta jirana nice nake acting din boss a wasan.
*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤14❤

Tun lokacin dana fita bani na dawoba sai wajen la'asar,muna had'a ido da yah sameer wanda yake gefen ummah a zaune yah watsamin wata uwar harara tareda cewa,
"Ke dan ubanki daga ina kike iyee"
Shiru nayi ina mitsitstsika ido,saboda kogi muka bi malam sule yaje kamo kifi,kuma nasan sarai an hanamu zuwa,kawai rashin ji ne irin nawa,ummah tayi saurin fansata daga amsar dazan bashi,saboda a duniya ta tsani a dunga dukana domin guje tsoron a gano yanayin yanda jikina yake,ni kuwa ko a jikina itah ce take rawanta da kid'anta ita kad'ai.
Saurin rab'ewa nayi na koma gefenta na zauna,can gefe dashi saboda kar yah bugeni dan nasan halinsa sarai,mungun yaro ne shi,kama hannun ummah nayi na rike tareda cewa,
"Ummah ya jikinnaki kinji sauki koh?"
Tun kafin ta bani amsa yah sameer yayi saurin cewa,
"Zaki tambayi yah jikinta mana bayan tun safe kika fitah gidannan bance da rana ba,sai yanzu aka ga k'eyarki,saboda shegen yawo irinnaki"
"Kai kai sameer,nikam banason kana hamtararta kaman ba kanwarka ba,idan batayi wasaba mai kake so tayi,yaro ai dole sai yayi wasa,kayi addu'a ma da ta dawo lafiyah"
Tabb yah sameer dinner zaiyi wata addu'a wai na dawo lafiyah yo na mutu mana,na fad'a a raina,ummah ce tah katseni da tunanin danake musamman da taga ina hararar yah sameer din tagefen idona,tasan sarai yanzu zai bugeni idan yah kula da mai nakeyi masa,
"Ke seematu tashi ki d'auko abincin ki a gefen daki can,har yayi sanyi baki ci ba tun rana"
Toh na amsa dashi kafin na tashi na d'auko ,ina budewa na saka hannu na fara ci,lomar farko dana kai muka had'a ido da yah sameer,ya mutsa fuska yayi tareda cewa,
"K'azamar banza ,ji yadda take ci babu wanke hannu kaman ba yanzu tah dawo daga wasan k'asa ba"
Juyawa nayi na kalli bongon d'akin ina nuna musu k'eyah,dan gaskiya yah sameer din yah takuramin magana ce kawai banyiba.
Tun daga lokacin zama kusada ummah yakemin wuyah saboda Koyaushe yah sameer yana makale da itah,gashi yanzu babu damar tah koreshi ta kirani saboda yanzu babu abinda takeyi da kanta,sai sameer din yayi mata,nikuwa bana shigowa dakin sai kwanciyah ko kuma zuwa neman abinci,duk sanda na je dakin sai ummah tasaka min albarka tareda yimin kashedin zaman duniyah,duk da ina ji amma babu damar aiki dashi a lokacin saboda yarintata nakeci a lokacin babu babbaka.
Bayan wata d'ayah da kwanciyah jinyarta mai tsanani,sai yazamana ciwon dayake kafarta yah fara shiga har cikin jikinta,tashin hankali kam babu irin wanda su baba umaru da yah sameer basu ganiba,idan kaga yah sameer a zaune yah zuba tagumi toh tunanin jinyar yakeyi.
Babu yanda baba umaru baiyi da ummah ta barni na dinga kwana a dakin inna ramatu,amma haka firr taki yarda,komin halin ciwo da ta shiga tana dawowa hayyacinta zata nemeni,nikuwa yanzu tunda naga haka jikina yayi sanyi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login