Showing 6001 words to 9000 words out of 62773 words

Chapter 3 - GIDAN GANDU

09 Oct 2024

4435

ku bata min nawa,saboda so nake naje nayi bacci kuma sai gobe,aga dame zatazo a tareta ana mika wuyah"
Har taje bakin kofar gidannasu batabar surutunba kaman wanda wani ne a kusa da ita yana jin me take cewa.
Alamun kamar mutum tagani a bakin gidannasu kamar mace tana firah,duba agogon hannunta tayi tana murza ido,karfe biyu ta kusa amma ga wata a kofar gidannasu tana hira,
"K'undun ubancan mai yarinyar nan take a waje a wannan Daren,mu manya ma mungama mun dawo gida amma ita tana waje,hmmmmm bari nazo na sameku"
(Toh fah kunji wai itace manya,su manya gatan wasa)
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤05❤

A manne suke a jikin katangar sun lab'e itada dashi har baka gane me ake kullawa a wajen,sameemah ceh ta sharo mashin din da gudu,suna kallonta kuwa sukayi saurin bajewa da sauri,saida taje ta kafe mashin din kafin ta dawo wajenna su tana gyara zaman gyalen dayake wuyanta da kuma wandonta wanda rigar ta tattare saboda hawa mashin.
Kad'a key din tayi a gabansu kafin ta karewa saurayin kallo,
"Kai uban me kakeyi a kofar gidannan,har karfe biyun dare,duk wanda kasamu da ka lallatsa tun karfe goma bai isheka ba saika kai har karfe biyun dare dan zalama,kawuce ka bar wajennan ko saina saka karnuka sun sanja ma kamanni tukunna,da haka kam ai sai kajata ku shiga cikin gidan zuwa kan gadon baba umaru ku karisa tunda har yanzu bai isheka ba(wato ubannata ma bata barshiba kenan)"
Cikin sauri da alamar rashin gaskiya yabar kofar gidan yana sosa keyah,harara ta bishi da shi tareda cewa,
"Heeeege mai siffar mayu kawai"
"Wai miye hakan zakina wani zagin min saurayi kaman wanda yayi miki sata?"
Buge mata baki sameemah tayi cikin sauri kana ta dora da cewa,
"Har kina da abin cewa keda na kamaki dumu dumu da laifi,a kofar gidanmu saboda ki jawo mana abin magana koh?,nasake jin bakinki ,kin shige gida ko saina yi kwallo dake tukunna"
Cikin kunkuni khadija tafara cewa,
"Kuma wallahi saina gayawa ummah abinda kikamin,naga kema daga yawon ta zubar din kika dawo kuma daga gani shaye shaye kika iyo tunda ga nan warin wiwi a jikinki.....,"
"Mekikaceh wai?"
"Babu komai ba abinda nace"
Tana fadin hakan ta shige gidan da gudu dan ba karamin aikinta bane ta biyota ta kara mata wani dukan.
Sassafe masifar a gidan su labiru ta kare dan yanda salame taga rana haka taga dare ita da labiru da kuma mai maganin tofi ,wanda ta daukoshi saboda yayi ma labirun magani,dan batada arzikin kaishi ko chemist ne bare kuma asibiti.
Da safe har ya samu ya yi d'an bacci saboda maganin da aka saka masa,saidai fah su labiru babu saka wando zaman daki yakamashi kenan.
Saida safenne saleh maye yah shigo dakin uwar tasa duba labirun,salame ce takalleshi da takaici kafin tace,
"Yau ganshi bawan mace kawai,tun jiya ake ta maganar abinda akayiwa dan uwanka sai yanzu uwartaka ta biyu ta barka kazo ka dubashi kenan,wanda yarako maza duniya kawai"
"Haba Babar labiru yah kike yawa ne,ni ina can bansan ma me ake yi ba,dan sai yanzu na tashi a bacci,shine nace bari nayi hankali nazo na duba shi da jikinnasa,kuma ma dazakice LUBABATU ceh tahanani zuwa,ai kaunace idan ta hanani ma"
Kuka salame takawo ta kece tana fyace majina ga ciwon labirun ga kuma takaicin babban dannata wanda yanzu shida wanda suke turu babu wata maraba mai yawa,
"Dallah ni tashi kaban waje,yanzunnan ba sai anjima kaje ka dau matakin abinda akayiwa labiru dan bazan yadda ba wallahi"
Mikewa yayi da d'an guntun karfinsa yah ciro wata wuka a wandonsa wanda yafita acikin kalarsa saboda daud'a,
"Wannan dolene yanzunnan zanje na koma waye fad'a minshi saina fard'e masa wuya a yau ba sai gobeba,mu daman ai ta irin wannan harkar muka kware"
"Eh naji ana cewa wani a anguwar yaga yaran sameemah wannan shegiyar yarinyar mai kama da y'ay'an aljanu,wai sun ajiye buhun da aka samu labiru a ciki,ina da itace tayi wannan aika aikar ,dan kowa yasan zata aikata"
Suleh ne yajuyo ya kalli uwar tasa tareda cewa,
"Iyee inna banji mai kika ceba,ai seemah dai tawa kike nufi?,kai ba mai taba wannan cikar na kyaleshi ,yanda nakejinta a kashin raina ai koke banajinki,babar labiru itah ceh fah surukarki wanda za'a daura auran kwanannan,so kike idan naje na yanketa akawomiki suruka mai tabo"
"Inalillahi jama'a kuzo ku tayani bakin ciki,wannan d'a haihuwar banza nayi,yanzu nikake fadawa bawanda kakeso sama da ita a duniya,kuma wai harda ni,bayan irin aika aikar datayiwa dan uwanka?"
Turewa sulen tayi cikin bacin rai yah wancakala gefen labiru wanda yake zaune an saka zani an lullube masa gun da ya kone din,sai zazzare ido yake maganar ma wuyah take masa kaman wanda aka kone masa bakin.
"Dan banza ji yanda ka wani baje a kasa dan kawai na bugeka,dama uwar me zaka iyah idan kajedin duk kwaya ta gama hudaka tun daga baki har hanji,wannan masifah da mai tai kama"
"Inna gaskiya karkije gidanannan kiyi musu wannan masifar taki ,gidan surukanki ne fah "
"Innnnnnaaaa ba ita bace tayimin haka ba,karkije kice itace tayimin haka na rokeki innannnnaaaa"
"Yawwa inna kinji abinda labirun ma yace koh?,in ma itace cikin soyayya zan lallameta ta fad'amin"
Dawowa tayi tana karewa y'ay'an nata kallo,daga wanda yake kwance babu abinda zai iyah an nakasa shi sai wanda shida tab'ab'b'u basuda maraba dashi da su.
Cije baki kawai tayi dan takaici ta rasa ma mai zata ce,
"Shashashu kawai in ma asiri tayi muku yau zai karye dan ubansa,zuwa gidan gandu kuwa ba fashi inyaso idan naje ku hadiyi zuciya ku mutu,yau koni koh su a garinnan wallahi,dan bazan tab'a yarda ba,in ta kamama kotu zan maka su,muje ayi ta shari'ah daga nan har kotun k'oleee.
KO safiyah bata gama waye ba,dan wasu ma ko karyawa basu gama yiba salame ta doko sallama cikin gidan gandun,
"Salamu alaikum gafaranku dai,ko bakowa a gidanne"
Wani yarone ya fito daga kofar su larai din yace,
"Suna nan amma kowa yah kofarsu"
"Inane kofar su sameemah wannan shegiyar yarinyar"
Tun kafin yayi magana larai ta leko domin ganin wace bakuwar da safiyanannan,dan tun a jiya da daddare suka baro asibitin saboda yanayin sha'ani na kudi,
"Kutt dama kece,kin hutasar dani dama ina shirin zuwa gidannanki muyi duk wacce zamuyi dake amma tunda kinzo shikenan sai a fara"
"Mekike nufi da cewa muyi wacce zamuyi ,toh ni ba wajenki nazo ba ,wurin yar dabar gidannan nazo da ta lahantamin d'a yana nan a kwance kaman bazaiyi raiba"
"Ayyyirirri koma wa kike nufi tamin dadai duk da bashi zai hana na fasa abinda nayi niyyah ba"
"Kehh duk abinda yafaruma larai ki bari sai daga baya yanzu ba wajenki nazoba"
"Ohh kina nufin bakiji abinda dannaki la'ananne ya aikata ba,koda yake bazakijiba saboda ba y'arki yayiwa ba,yanzu dayake shi akayiwa aika aika aikin ji har kinzo neman ba'asin labarin.
Toh in ma baki sani ba kisani danki labiru y'ata hanifa ya farkata,kaman yasami fanko saboda tsabar tashanci kuma yayi gado,toh bazan yadda ba,yanzu dakike cewa yana jinya toh yana warkewa zan bawa gardawa sadaka su sake maidashi kwance,dan jinin y'ata billahillazi bazai tafi a banza ba"
"Ke wai dankinga nayi shiru ina jiran ki fadi abinda yake bakinki,aikin banza saboda gadon kwadayi yasa ina kuke lik'a masa ita,dama aka ce ai k'uda wajen kwadayi akan mutu,kuma dazakice wai gado dan ma abin kunyar kowa yana da shi a gidansu ,ko kin manta tsoho wanda baya saka wando sai babbar riga kawai saboda bin bazawaran kauye"
Hayaniyar ce tafara yawa inda matan kofa ko wacce take lekowa dan kashe kwarkwatar idon ta.
Da abin yayi yawa fad'ane ya rukume tsakanin salame da larai kowa yana tsinewa kowa albarka kaman wasu zakaru.
Saida mazajen suka fito kafin aka samu aka rabasu dakyar kowa tana huci kaman shanu.
"Kai kai mai yafarune haka,mu gidannan babu dama mu tashi a ji shru kaman kowane gidan saidai Koyaushe da masifar dazata kunno kai"
Kawu KAMILUNE,mai magana yah fito zai tafi gona,dama shi bai fiye zama a gidanba kl yaushe yana wajen neman kidinsa,matansa ma yahanasu shiga duk wata cakwakiyah da ake a gidan indan yakama wata kuwa da hannunta a ciki toh saidai ta nemi wani gidan badai nasa ba.
Jin muryarsane yasasu salame tsayawa fad'an sauran matan kuma kowa ta koma gefe ta kasa kunne dan taji mai za'a ce,dadai lokacin ne kawu shehu shida baba umaru suma suka shigo daga wajen mai shayi da alama wani yaronne yaje ya kirasu,
"Wannan yar rainin hankalince mana,dan tsabar su dangin marasa kunyane duk abinda danta yayi bai isheta ba hada zuwa tana wani kumfar baki wai an illah ta mata d'a a gidannan,kuma illatawa bata ga komai ba ma saina tashi yanke nawa hukuncin ehhe"
"Hukunci kin dade baki dau hukuncin ba abinda akayi masa ma na yanzu ba shiru zanyi ba barekuma kiyi tunanin daukar wani matakin"
"Kai ya ishemu haka wannan yarintar,kun girma ku ba yara bane amma baku da maraba da yaran kuma abin kunyar ma a gaban yaranku kuke wannan abun,ke salame mai akayiwa dannaki kikazo tada fitina da safennan"
Baba umaru ne yadaka musu tsawar cikin bacin rai da kuma k'osawa da halinnasu na yau da kullum,
Jin an tambayeta ne yasata fashewa da kuka tana shareewa da gefen zaninta kafin tace,
"Dan tsabar rashin imani bakuga aika aikar da akayi masa ba,tun daga kasan cibiyasa har zuwa rabin cinyoyinsa an konesu da man gyada mai zafi,babu komai sai fatarsa a waje kawai,kuma anfadamin wani marar imaninne a cikin gidannan yayi masa dan haka bazan yadda ba wannan ai niyyar kisan kai akayi ,yanacan katon saurayi a kwance sai abinda akayi masa tukunna"
"Allah ya kara baiga komai ba ma,in duninsa halin bunsuru"
Larai ce tayi sauri ta fada tareda d'ane baki kaman ba itah ce ta fad'a ba,
"Keh larai banason shiririta ana kwantar da wuta kina kara mata fetur koh?"
Baba umaru yana rufe baki kawu shehu yadora da cewa ,
"Laifinta Toh kagani yayan umaru,bayan abinda dannata yayiwa yar mutane kuma taxo tana fadan wai wani yah nakasa mata shi,ina ruwanmu toh,in zatayi hakuri tayi in kuma bazatayi ba ta kai kara ,muma saimu kao karar in yaso ayi ta shar'ar tunda ita take so ayi tayi,
"Ahah baza a kai har haka ba,ke salame tunda kinji mai danki yayi sai kije gida kiyi jinyarsa tunda kinga suma jinyar tasu yar suke,kowa sai yayi hakuri yaran zamanine sai hakuri ka haifesu baka haifi halinsu ba,muma kuma iyayen da na mu laifin ta wani wajen ,allah dai kawai yah shiryamu gabaki daya"
Dakyar su kawu kamilu suka kwantar da fitinar salame ta tafi gidanta tana kanana nan maganganu wanda allah ne kadai yasan ranar dazata bari.
Sameemah kuwa duk abinda akayi a gidan bata sani ba,saida wayarta tayi Ring ne kafin ta juya ta kalli screen din ,tareda tsuka saboda tashinta a bacci saboda tasaka wayar a kusa da kunnenta,
"Alhaji bala"
Shine sunan da ta fad'a cikin muryar bacci kasa kasa..........

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤06❤
"Heelloo alhaji bala yah hidima?"
Seemah ta fada cikin muryar barci,wani irin mika alhaji bala yayi jin yanda ta amsa masa cikin sanyin muryah kaman ba sameemah daya saniba,
"Lafiyah kalau madam yah hutu da jin dadi"
"Lafiyah kalau,wani abune yah faru?"
"Ahah babu abinda yah faru gimbiya kawai na kira ne naji lafiyar ki,sannan kuma na sanar dake inkin shirya ko yaushene to kiyi min magana zan aiko mota har kofar gidanku a dauke ,kizo mushakata muji dadin mu,saidai ina rokonki dan allah naji kiran shiryawarki da wuri,dan baki san yanda nake jinki a cikin zuciyah ta bane,akanki babu abinda bazan iyah ba,kawai hadin kanki nake bukata shine kawai cikar burina"
Saida ta tabe baki tukunna tace,
"Naji alhaji yanzu ina kwance banason a takuramin ka bari idan na tashi nayi tunani zaka ji mai na yanke ,kuma karka sake kirana sai na nemeka tukunna"
"An gama gimbiya,ai duk abinda kikace shi za'ayi kawai"
Sauke wayar tayi kafin ta kara danna wani kiran,ring daya aka dauka a d'aya bangaren,
"Allah yah taimaki shugaba me kike da bukata"
"Kai C.I.D(dan leken asiri),ka saurareni da kyau"
"Ina jinki"
"Ina son duk wani bayanai akan alhaji bala wanda muka hadu dashi a gidan alhaji Sama'ila,tun daga kan iyalansa sana'arsa har zuwa kan karfin siyasarsa,in takama inason bayani kaf akan gidan shata warsa,ka kawomin nan da bayan azahar,sannan kuma akwai abinda zakamin bayan hakan"
"Wannan mai saukine an gama shugaba"
Ta shi tayi daga kan gadon kafin tah zuba wata uwar feduwa wanda in kana bakin kofar tasu saika jiyota,
Wasu manyan karnukane guda uku suka shigo dakin suna karkada jelah,suna sakin yawu a bakinsu kaman zasuci babu.
Sameerah ceh wanda take kwance tah buga uwar tsuka tareda cewa,
"Aikin banza wai dan tsabar rashin mutunci kare har dakin mutane,su gasu abu kamar kuraye dan muni wannan ai walakancin yayi yawa"
"Kehh reza yaga mata kayan jinkinta yanzunnan sannan kiyi mata balli balli a cinya"
AI kuwa kaman jira farar karyar take tayi kan sameerah da sauri tana gyara baki,wani uban ihu sameerah ta buga cikin kankanin lokaci sai gata a waje,dakin uwarta ta nufah tana ihu tareda neman taimako.
Dakin inna ramatun ta shige tareda rufo kofah tana rafza ihu a ciki.
Mutanen gidanne hankalinsu yadawo kan abinda ake,dama kowa yana tsaye bayan an yi hayaniya tsakanin salame da larai,
"Wayyo baba umaru ku taimakeni kuna ganin zasu cinyeni da raina wayyyo inna"
Kowa yana jin ihun sameerah ga karnuka a kofar wajen amma babu wanda yayi gigin karisawa kusa dasu,bare su had'a dashi,
Baba umaru ne ya d'aga muryah yah kira sameemah wanda take daki a zaune kaman ba itah ce ta saka su ba,saida akayi kira kusan uku kafin tah fito a dakin tana mitstsika ido kaman ba itaba,
"Gani baba mai yafaru"
"Gaki kaman yah,ki debe wannan karnukannaki kina gani zasu yiwa yar uwarki illah ?,kuma sannan ki debesu a gidannan yanzunnan"
"Bazan Hanasuba har saita bani hakuri in ba haka ba kuwa wallahi sai sun mata balli ballin dana saka suyi mata,gobema ta sake zaginsu a gidannan in zamanta sukeyi"
Sameerah kaman jira take dama tanajin mai ake cewa,
"Kiyi hakuri bazan sakeba dan Allah ki hanasu karsu min fata fata"
"Shikenan allah yah ceceki,kehh reza zo ki tafi yawanki yanzunnan,saidai barin gidannan babu inda zasuje,inda wanda yake bani abincinsu ya daina daga yau,ai sun mafi bil'adaman dasuke gidan mutunci,tunda su basa yin tazubardin da y'an gidan sukeyi"
Tana gama fada tabar wajen ,batare da jira jin mai wani daga cikin wajen zai ce ba.
Kowa shiru yayi yah tafi harkarsa,ita kuma sameerah ta fito tana share hawaye tareda jan zuciyah,fitasari yana bin gefen cinyarta.
Zainab ceh (kanwarta wadda take binta saidai sameemah ta girmeta da kadan),tah kalli sameerah suna hada ido ta tuntsire da dariyah tana nuna fitsarin dayake bin kafar ta,itama sameerah fitsarin dayake bin ta takallah wanda sai a sannan ma ta kula da shi,
"Kuttt keh dan buhun ubanki ni sa'arki ce kikemin dariyah iyee"
"Hehehe niba sa'arki ba ce ina na isa,saidai ga wacce itama ba sa'arki bace ai ta saka ki fitsari a wando😄😄😄"
Sameerah ceh tabi bayan zainab da gudu a zuciye,sai kuma inna ramatu tayi saurin dakatar da itah,
"Keh dakata ina zakije da wannan fitsarin koh mahaukaciyah ta maida ki,bayan tura miki kare?,gashinan ai kin kaso aurenki kinzo yarinya karama tana miki yanda ta ga dama"
"Kai ji inna da wani zance,naga ke kika nace saina aureshi saboda yana kawomiki kayan dad'i,da kika gane yana dukana kuma d'an shaye shaye ne,sai kika shiga kika fita kika raba aurena dashi,kuma yanzu kizo kice na kashe aure na,sameenu ma kullum sai dad'in baki idan nace yah fito aure sai yacemin zai tafi,yoh ya kikeso nayi iyeeh"
"Toh yah isa haka ba tone tone nace kiminba wuce ki cire kayanki,dukkanku baku da wani ishashshen hankali kaman kuna cin k'asa"
Wayah C.I.D yayiwa sameemah akan cewa yana kofar gida hakan yasa ta fita domin karbar abinda yah kawo mata,
A zaune yake akan dakalin kofar gidannasu,yana ganinta ya taso tareda mika mata abinda tasashi yayi mata.
Wani abu tah mika masa baki sannan sukayi kus kus babu wanda yakejin mai suke cewa,
"An gama shugaba ranki yadade "
Baba umaru ne yadawo daga masallaci anyi sallahr azahar ya wuce ta gefensu ita da c.i.d.din,har yawuce kuma ya dawo,
"Kehh sameematu idan kin gama dashi din kizo ina san ganinki"
"Tohhh"
Lokacin da ta karbi abinda take bukata maimakon ta tafi kiran da mahaifinnata yayi mata sai wucewa daki da tayi kaman basuyi yace ta zo ba.
Sai can wajen la'asar ne baba umarun yasake aika yaro ya kira masa itah.
Nan ma saida ta gama sha'anin gabanta kafin ta tafi dakin baba umarun inda yake kirannata,
KO sallama batayiba ta nemi waje ta zauna tana kallon bangon dakin ,
"Baki iyah gaisuwa bane?"
"Na iyah "
"Toh miyasa bazakiyi ba,koh sai ance kiyi?"
"Banayine nasaba kowa gaisheni yake bana gaishe da kowa"
"Toh nima harda ni,ni zan gaisheki kenan,mai yasa kina girmane amma komai yana kara tabarbarewa"
Hade girar sama da kasa tayi da alama an tab'o inda yake mata kaikayi wato fad'a,
"Tun dazu ka kirani ,amma toh kayi hakuri mana wani abu nakeyine,ni kasan banason fadannan,banaso ana min fada kuma ka sani"
"Hmm mm allah yah shiryaki,toh naji kinji labarin alhaji babba(uban gidan gandu kenan,yah tsufah tukuf shine baban su baba umaru) bashi da lafiyah?"
"Eh naji su zainab suna fad'a"
"Toh kinje kin gaisheshi? Kokuma sai yah mutu ki leka gaisuwar sa"
"Haba baba yanzu akan wannan ne dama ka kirani ,kuma fah kunsan mutuwa zaiyi shine kuma za'a fatamin lokaci akansa,habba dan allah,a dinga yimin adalci mana"
"Keee sameematuh gyauton uwaki,nake ganin ki kamar kinada hankali ashe babu komai akanki kema sai wiwi din,ki tashi ki bani waje ,kuma ki tabbatar kinje kin dubashi,dan uwanki ma wani satin zasu taho ,sun samu hutun sati d'aya"
"Tabbb AI wannan mai zubin aranan,hmmm ashe nasake shirin taryarsa kenan,dan rashin mutuncin nawa yayi sanyi,kar naje yah zo ya sameni da wanda ya sanni dashi,gwanda na yi sabo fill"
"Innalillah yanzu koshi d'an uwannaki ma baki barshi ba,ashe ba iyah y'ay'an innarku ramatu kikeyiwa rashin mutuncin ba har shima baki barshiba"
Toh kai ma baba umaru..........."
"Karki sake cewa komai tashi kije yah isheni haka dan Allah,allah ya shirya ku kawai shine addu'a ta a kullum.
Tana shiga daki kuwa taji su zainab suna zancen zuwan yayannata,wanda suke uwa d'aya uba d'aya itada shi,su kadaine y'ay'ayan inna Hajara,wanda tah mutu tun sameemah tana shekara bakwai,shikuwa MAJOR SAMEER tun bayan mutuwarta da kwana bakwai yabar ma garin gabad'aya ,inda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login