Showing 21001 words to 24000 words out of 129540 words

Chapter 8 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6695

bayero ke bawa baki masauki Dan haka masarautar kano su sukabawa su malam imam masauki, inda akabasu katon Gida a unguwar mandawari
Gidansa ya kasance kusa da gidan wani alaramma malam shehu, malam shehu yanada Tarin almajirai dan haka zuwan malam imam kano basu San kowa ba wannan makocinasu shiya zama kamar Dan uwansu
Shi ya kai Imam kasuwa ya hadashi da wani almajiransa ya koya masa san'ar takalma a kofar wambai
Sannan in ya dawo sukan zauna da malam shehu ya koyamasa karatun addini
Imam yasamu Ilimi me tarin yawa a gurin malam shehu wanda ya kaishi ga zama mahadddacin qurani, sannan yana samun alheri a kasuwancinsa yA tsaya akan gaskiyarsa dai? gwargwado,
yana samun rufin asiri a sana'arsa
? ? Haka bangaren matan malam uwar gidansa ta dauki mairo kaman Yar data Haifa yayinda amaryarsa takasance masifaffiya Dan bata shiga shirgin mairo tunda taga uwargidamta ta dauketa kaman ya, uwargidan malam shehu ta iya saka Dan haka ta dinga koyam???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ata sakar kayan sanyi

A zamansu a kano? mairo ta haifi yaronta na farko ya rasu a ranar da ta haifeshi yarasu bayan wani Dan lokaci ta Haifi na biyu
Suka masa sunan Usman wato sunan malam shehu, yatashi da ilimin addini da soyayyar iyayensa gashi malam shehu ya daukeshi kaman jikansa yana matukar kaunarsa da ya isa sakawa a makaranta akakai usman makarantar boko
Seda mairo ta kuma haifan yara biyu suna mutuwa sannan ta haifi Yaronta namiji akasamasa Aliyu
Addu'a Imam yayi tayi Allah ya bar masa Aliyu Usman ya samu Dan uwa,
Usman ya tashi da matukar kaunar Dan uwansa kullum yana tare dashi har Goya masa shi mairo takeyi,
Ba 'a Dade ba
Ta kuma haifar mace itama ta rasu daga nan bata sake haihuwa ba,
Haka suka rungumi yaransu suna kula dasu malam imam be sakasu a harkar kasuwanci ba se dai ya tsaya musu akan Neman Ilimin su, na islama Dana zamani,

A kwana a tashi malam shehu Allah yayi masa rasuwa, sun shiga matukar damuwa da tashin hankali haka akayi zaman makoki kowa ya watse.
Rayuwa tacigaba a haka malam imam be taba tunanin sunemi wani daga danginsu ba, yana ta kula da yaransa , yakuma siyan gidajen kusa dasu ya hade a cikin gidansu.

Usaman da Aliyu suka girma da matukar kaunar junansu, gasu masu matukar biyayya duk da kasancewar su maza amma daga kan shara gyaran gado wanke? bawanda basu iyabaan Usman yafi Aliyu hakuri, shi
? ? Aliyu akwai kafiya da taurin kai sannan yana da zafi, halin babansu ya dakko, gashi shine karami amma in ya dau zafi sedai Usman ya kyaleshi amma duk da wannan halin nasa kaf kayan gidan nan shi yake wankewa ya goge sannan yana matukar son yayannasa amma wataran in kaga yasa Usman a gaba yana masa fada seka dauka shine babba
(Ashe JALILA ba a banza ta dakko ba)

shidai malam imam kullum zancensa be wuce
" Ku rike junanku Ku rike zumunci, kunga bayan imu IMU bamu da wasu dangi duk sun watse wasu sun mutu Ku rike junanku Ku nemi ilimi ko bayan ba raina karku yada zumunci"

Kwanci tashi asarar rai Usman yagama makarantar secondary ya shiga Jami'a yake karantar engineering,
Bayan ya kammalla jami'a ne aiki be samuba ya dawo Gida ya zauna yake dan bin babansa kasuwa, ana haka ya hadu da wata yarinya Zainab da farko dai suna mutuncine kawai kafin daga baya abin yakoma soyayya,
Lokacin daa malam Imam yasamu labarin Usman yana zuwa tadi gurin yarinyar ya kirashi yayi masa nasiha yace tun wuri in yasan ba aurenta zeyi ba ya dena zuwa gurinta

Shidama Aliyu be tsaya iya karatu ba yana taba kasuwanci
In yafita abinda yasamo se yabawa Dan uwansa yace yafara Tara kayan aure tunda ya fuskanci yana matukar son zainab,
Duk randa Aliyu beje makaranta ba haka zewuni Neman kudi ba abunda zeci a ciki haka ze dauka ya bashi,
?? Sannan dayake? mutane dayawa sun San Aliyu saboda yana da baki ba kaman Usman ba salihi ne kaman mairo, Aliyu ya dinga shiga yana fita domin yaga danuwansa yasamu aiki amma abu yafaskara kai kace shine yake nemawa kansa aikin
? Shekarar da Aliyu yasamu admission, babansu ya dauki kudin
Registration ya bashi amma daya tashi se ya hada kudin da Wanda ya dinga Tarawa ya tafi yaje kasuwa Yakama shago aka zuba takalma ya dankawa Dan uwansa yace gashi nan ya dinga juyawa yasamu yayi aure
Dafarko Usman kin amincewa yayi seda yaga Aliyu yadena kulashi, yadena cin abinci tare dashi yayi fushi sosai sannan ya yadda ya karba

Malam imam yace aikuwa badi se dai kanemi naka kudin kashiga makaranta, we da Aliyu yabata shekara biyu be fara makaranta ba saboda yaga kasuwancin da ya kafawa yayansa ya bunkasa

Duk wannan abun baya hana in Usman yayi masa laifi ya zauna ya kare masa masifa, amma beta ba yimasa gori ba.
? Shekara ta zagayo Aliyu sannan ya Shiga Jami'a
Usman ya cigaba da kula da shago yasamu Sana'a yafara core ransa saga batun samun aiki

Ahaka har Allah yasa Usman ya auri Zainab aka ware masa bangarensa a cikin gidan yasata a ciki, tana zaune da mairo lafiya saboda ita Sam bata da hayaniya Dan haka Zainab bama Shiga harkarta take ba balle kyautatawa ko akasin haka ya Shiga tsakaninsu.
Allah ya Albarkaci kasuwancin usman, aciki ya dinga tallafawa karatun Aliyu dakuma iyayensu da girma ya cinmmusu,

?? A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, matar Usman ta haihu ta haifi da namiji, aka sakamasa sunan Aliyu suke cemasa Jawwad, Zainab taji haushi ga mahaifinta memakon ayi mata kara a saka sunanshi se a wani saka sunan Aliyu
Aliyu yayi murna da haihuwar JAWWAD dakuma karar da dan uwansa yayi masa kullum yana tare da Jawwad, yaronma yana matukar kaunar Aliyu Jawwad, soyayyar da Aliyu yakema Usman Yakoma kan Jawwad,
Jawwad yana da shekaru biyar cif, Aka tura Aliyu bautar kasa kwara state yaji babu dadi sakamakon rabuwar dazeyi da gida gakuma dansa JAWWAD dayake matukar kauna

Haka Aliyu yayi shirin tafiya yayi sallama da mutan gida iyayensa sun masa nasiha sosai akan ya kula da Kansa da addininsa, Usman beji dadi ba ya Shiga damuwa sosai, saboda shi lokacin da yayi NASA bautar kasar a kano yayi beyi nisa da Gida ba.

Haka Aliyu ya shirya ya tafi kwara, wani babban kamfani aka turashi kamfanin yakasance mallakin masarautar garin Wanda ya kasance na construction ne na gine? dakuma tituna

Aliyu yaga mutane daban? wanda suke da banbancin addini da al'adu da zaman takewa na rayuwa

Aliyu ya hadu da wani bayerabe a kamfanin me suna Abiola Wanda ya kasance kuma hadimi ne a cikin masarautar garin dukda banbancin addininsu amma tasu tazo daya shiyake zagawa da shi gurare a cikin garin

In Baku manta ba kusan halin Aliyu da shige?
Dan haka yace yana so abiyola ya Shiga dashi gidan sarautar yaga? yanda take, haka akayi ya dauke shi ya Shiga da shi cikin masarautar ya dinga nuna masa abubuwa, haka ya dinga kallonsu wasu iri saboda yanayin saraautarsu? yayi daban da masarautar kano

Wasu abubuwan sun kayatar dashi wasu kuma sun bashi haushi haka abiola ya dinga bashi labarin
masarautar da abubuwan data kunsa? ciki kuwa hada labarin shalelen masarautar wadda akan a batamata rai gara abatawa sarkin saboda tsananin kaunar da sarkin yake mata

Sarki yana matukar kaunar yarinya nan, shikam Aliyu duk surutun nan da abiola yake besan me yake cewa ba saboda ya shagala da kallon abubuwan kayatarwa da suke a masarautar,
Wani part suka karaso kai bakace a Nigeria ne ba ya hadu karshen haduwa an kawata shi da abubuwan zamani da kawatuwa
"Nan kuma inane?"
"Ai nan shine bangaren yarinyar danake gaya maka jikar sarki ce, bangaren shalelen gidan ne"

"Ehenn mushiga inga mene a ciki mana"
Zaro ido abiola yayi "sokake in kwana a kurkuku baza ja min wahala ba iyakacin mu nan"

"To meye a ciki gani fa kawai zanyi"
"Dan Allah kabari ka zo mutafi kaga akwai masu tsaronta Dan haka kazo mu tafi"
Da kyar abiola ya shawo kan Aliyu ya yadda suka tafi.
Abiola ne durkushe a gabanta, ta hakimce tana cin kayan marmari
Tayiwa hadimanta umarnin sutafi subata guri
Sannan ta mike zaune sosai
"Abiola"
Takira sunan shi
Ya Dan kalleta ya maida kansa kasa

"Waye wannan Wanda kuka shigo da shi dazu?"
Gabansa ne yayi mummunar faduwa ya tsorata, nan da nan gumi ya rufe shi ya kama in'ina
"Abiola bafa abu me wahala na tambayeka ba kawai na tambayeka waye shine
Ina kallonku dazu ta saman bene kuna jayayya waye shi? Daga ina yake? Mekuma ya zo yi nan"?

Da kyar abiola ya hadiye wani yawu ya daidaita nutsuwarsa Ya dan suka da Kansa yace
" your royal Highness Dan bautar kasane an turoshi kamfani domin yayi aiki sunanshi Aliyu daga kano state yazo nan"
A kidime ta kalleshi kana nufin musulmine
"Eh bahaushe ne kuma musulmi"
Gigicewa ta danyi tare da bashi umarnin ya tafi seta nemeshi
Nan ta Shiga sintiri a gurin
Da karfi tai shouting
"Impossible!!!!!!"
Wanda ya janyo hankalin masu yi mata hidima ,kafin su an kara........

Wata sabuwa



Share please
More comments more typing...............

Love u all Abdul jalal novel fans








=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 12

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin=د?=د?=د? da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all d'd'd'

I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? Takabbalallahu minna wa minkum eid el Mubarak alaina wa alaikum
Allah ya karbi ibadunmu yasamu a Wanda yYafewa a wannan kwanaki goma na dhul hajj

? ? ? ?? -my first Novel-

Numfasawa yayi ganin yadda yaran gaba daya suke durkushe a gabansa ga maryam da take ta kuka

Ko ba komai Aliyu yaron kirki ne tun tasowarsa ba taba dakko masa magana ba dukda fadansa da shige shigensa baya dakko magana
Kuma ya duba misalin da inna mairo tai masa Suma yadda sukazo basu San kowa ba malam shehu ya daukesu kaman yayansa Dan haka ya numfasa

"To shikenan na amince Allah ya tabbatar mana da Alkhairi yayi muku albarka gaba daya"
Marry ta dago da sauri

"Baba dagaske ka yadda in auri Aliyu"

Ya gyada mata kai
Da gudu marry ta tafi gurin Inna mairo ta rungume ta

"Mama bani da bakin godiya mama kiyimin godiaya gurin baba, kun gama min komai a rayuwa da kuka karbeni nagode sosai.

" ba komai maryam nima nayi diya dama bani da ya mace"
Inna mairo tayi maganar tana sharewa marry hawaye

Aliyu da Dan uwansa haka suka dinga yiwa mahaifinsu godiya tare da adduo'i
Usman yaji dadin yadda baba ya amince ko ba komai shima Dan uwansa ya samu farin ciki

Bayan malam imam ya koma daki ya kira Aliyu yayi masa nasiha? ya ja kunnensa game da rike amana da yi masa gargadin zama jakada nagari na addinin musulinci da kuma kabilar hausawa
?? Haka marry ta karbi musulinci? ta koma maryam Amma aliyu yake kiranta da noorat saboda sunan mahaifiyarsa ne
Abubuwa sunzo mata da sauki saboda tasan addinnin musulinci se Dan abinda ba a rasa ba.
Itakuwa Maman Jawwad tunda taga abunda yafaru gashi kuma mutanen gidan sun karbi maryam.ta fara jin haushi, yadda inna mairo take kula da maryam kamar yarta amma ita dasukayi kusan shekara shida da ita bata wani shiga sabgarta,
Dan haka ta shiga yayatawa a anguwa kanin mijinta Aliyu ze auri kirista dukda tasan ta musulinta, hakanan se yan unguwa su shigo dan aga matar da Aliyu ze aura.

Duk surutun da ake a gari Aliyu da yan gidansu suka toshe kunnensu, dama ba a tunkarar Aliyu da maganar Dan ansan masifaffe ne
Sedai ayiwa Usman ko magulmata in sun shigo suyiwa inna mairo
Aka ware musu bangarensu a cikin gidan, dukda kasancewar maryam kabila kuma wadda tayi girma a gidan sarauta amma tana da matukar biyayya da girmama manya ba ruwanta da hayaniya, mamansu Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama

Malam ya tsaida ranar daurin auren maryam da Aliyu sati biyu
Usman shi ya hadawa Aliyu lefen da aka bawa maryam itakuma tace ai tana da kayan sawa
Inna mairo tace mata wannan itace Al'adarmu ana hadawa mace kayan lafe abata

A lokaci kankani mutan gidan nan suka saki jiki da maryam ta shiga ransu saboda tsabar nutsuwa da biyayya gashi kullum tana tare da Jawwad yaron yana sonta wataran hada JALAL in an kawo shi,
amma banda Zainab wadda ba ruwanta da ita
yan gidansu Zainab musamman sukazo don ganin maryam suka dinga Yar mata da bakaken magana yayarta wadda suke cewa Yaya mairo ta dinga ziga Zainab,
"Ba ruwanki da ita kuma karki kara yadda danki yaje inda take don arna mugayen kazamai ne gasu da asiri na bala'i dan haka ki rike kanki karki bari a mayar miki d'a da irinta dan wannan tuban nata be kai zuci ba mumafuka CE yaudararku kawai takeyi"
Haka sukayi ta zigata sannan da yamma suka fito zasu tafi suka tarar maryam tana wanke? a tsakar Gida

Se Yaya mairo ta waigo ta kalli Zainab
"wai ya sunan ta ne"
Ta tabe baki
"Wai maryam" Zainab ta fada a wilakance

"Kutt dan wulakanci sunana aka samata"
Itakam maryam tana ganinsu ta fara murmushi
"Sister zaki tafi ki gaida gida Allah ya kiyaye hanya mungode"
Tai maganar tana dan durkusawa
"Au dama ta iya hausa, tab wai Allah ya kiyaye Ashe tasan Allah"
Yaya mairo tafada tana wani kebe baki
Da maryam ta fuskanci wulakanci zasuyi mata seta cigaba da aikinta
"Tab an baro iyaye an fake da za a musulinta an ta ho bariki,
Allah dai ya kiyayemun kanwata"
Ido taf hawaye maryam ta dago tana kallonsu
"Meye kuma na kura mana ido to indai kurwarmu ce kwalelenki dangin maita, banda jaraba wannan kanin mijin naki yarasa wadda ze aura se tubabbiya tir"
?? "Nawa ubanki yabani gudunmuwar auren da zanyi?"
Sukaji yo muryar Aliyu dama shi ba sabgar matar wansa yake shiga ba saboda ya fuskanci bata da mutunci ita da yan gidansu
?? "Zainab bari in gaya miki wani abu guda daya tunda iyayena suka karbi maryam banga matar da ta isa tazo tana zaganmin mata ba muddin kika kuma kuskuren zaginta zan baki mamaki munafukan banza kawai marasa tarbiyya"
"Noorat aje wanke? kikoma daki rabu da su jahilai kawai"

Lokaci? maryam kanyi kuka inta tuna da iyayenta tana kewarsu
??
?? Yayinda ya kasance bangaren iyayen maryam ma haka mamanta kullum setayi kukan bakin cikin rabuwa da yarta kullum cikin tunanin Allah yasa kar yarta ta fuskanci kalubalen da ta fuskanta a gurin al ummar hausawa ubangiji yasa tana hannu nagari.

Ranar wata juma'a bayan sallar juma'a aka daura auren Aliyu da kuma maryam
Malam imam shi yayiwa maryam kayan daki yayinda Usman shi yabiya kudin sadakin maryam
Suma aka basu guri a cikin gidan ranar maryam bakinta kasa rufuwa yayi ji take kaman mafarki waita mallaki Aliyunta
? ? Haka rayuwa tacigaba da gudana yayinda maryam ke fuskantar wulakanci daban? daga bangaren Zainab, danginta, kawayenta da kuma? sauran yan unguwa
Ko ruwa maryam ta sha da Kofi Zainab bazata kara taba kofin ba datayi abu zata fara cemata tubabbiya ta baro danginta ta taho yawon ta zubar indai Jawwad yaje inda take har dukansa takeyi amma kullum shida Jalal suna manne da maryam
Maryam bata taba kulata ba, ita soyayyar da Aliyu da iyayensa suke mata yafiye mata komai dayake Allah besa ta samu haihuwa da wuri ba
Aliyu ya maida ita makaranta takuma yin waec bata samu admission ba dan haka se ta shiga poly ta karanta catering
? Rashin haihuwar da batayiba ya dameta matuka Aliyu ke kwantar mata da hankali, yana cemata gasu da Jawwad ga Jalal suma yayan sine
?? yayinda Zainab take cewa tunda an saba zubar da ciki sannan akai aure ya za ayi yanzu asamu haihuwa tunda angama barar da kwayayen a titi sannan aka tsallako aka taho wai an tuba,
Itakam maryam bata tanka mata, se dai in Aliyu yaji yazo ya kare mata tas,
malam imam ya sha Jan kunnen Zainab akan wannan abubuwan data ke wa maryam amma bata fasa ba dan ba kunyace da ita ba.
?? Katsam maryam tasamu ciki ta fara laulayi tayi farinciki sosai da wannan cikin dukda kasancewar cikin na wahalda ita Aliyu shiyake mata komai har cikinta ya fara girma sannan tasamu sassauci
Amma bangaren cin mutinci daga yan uwan Zainab da sauran yan unguwa se abinda yayi gaba yayinda
Zainab ta dinga cewa watakila ma cikin bana Aliyu bane cin zarafi daban?
Babban bakin cikin Zainab maryam bata kulata kome zatayi

Wata tara cif Allah y sauki maryam lafiya ta haifi ya mace me matukar kyau kamanta daya da Yaya mairo kalar Fulani sosai

Tunda aka haifi yarinyar nan JAWWAD da JALAL suka zama yan raino JALAL baya tafiya Gida kullum yana manne da jaririyar nan,
JALAL Ya dinga bin Aliyu yana cewa Abee (yanda JAWWAD take kiransa) yana cewa dan Allah Asama jaririyar JALAL dariya Aliyu ya dinga yi yana cewa JALAL kataba ganin ansawa mece sunan maza
Shidai ya dage asawa babyn sunansa
"Kar ka damu yarona ko dan kaunar da kakewa dana Jawwad zanyima yanda kakeso"
Ranar suna ta zagayo akasawa jaririya suna Jalila
?? Watan Jalila 3 Zainab ta haihu itama ta haifi ya mace lokacin Jawwad yana da shekaru Tara
Ranar suna akasama yarinya Nana Fiddausi sunan Jakarta
? Nana da JALILA suka tashi kamar yan biyu
Jalila ba abinda ta bari bangaren halin mahaifinta na fada da Neman magana in tafita bata da aiki se Neman magana da cin zalin yayan mutane, sukuma iyayensu su kamata su daka? tare da yimata gorin Yar tubabbiya jikar arena
Abin yana bakantawa maryam da shikansa Aliyu maryam ta dauki son duniya ta dorawa Jalila in dai aka taba Jalila ji take har cikin zuciyarta amma se ta kauda kai,
A cikin Gida ma Maman jawwad yimata take ko Yaya Jalila ta kwace Abu a hannun Nana, in dai Nana tayi kuka Zainab ta dinga zage? kenan tana cin mutuncin maryam
? Wata rana hakan ya kuma kasancewa inna mairo bata nan, Jalila tasaka Nana kuka Zainab

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login