Showing 30001 words to 33000 words out of 129540 words

Chapter 11 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6692

shi kije kiyo alwala kiyi salla ki dau Qurani ki karanta Allah yasa kina Azkar"
"Ummi bana salla"
"To jekiyo Alwala kibiya Wanda kika haddace"
Ba musu taje tayo alwala tazo taita bitar Qurani da ka bacci kam gagararta yayi se dai juye?

? Yauma kamar kullum haka ta tashi jikinta kaman Mara lafiya ko abincin kirki takasa ci ga idonta daya kumbura saboda rashin bacci Ummi kallonta kawai take dakinta ta koma ta nemi guri ta kwanta tayi shiru

(Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi!!!)
Tas kalaman da akayi mata a mafarki suke dawo mata kwakwalwarta Wanda yayi dai? da wani mugun bugawa da zuciyarta tayi da karfi, kanta ya Sara
"Nashiga uku ni Jalila wannan wani irin bala'i ne meye hadina da wannan mutumin ake tsoratani akanshi wani tsautsayin ne ya kaini kano wanannan wani irin jarabane ana nema a haukatani why?"
Tafada tareda yin jifa da pillows din kan katifar ta yage bedsheet din kan gadon ta kifa kanta akan katifar

"Dan Allah ji abinda nake kamar mahaukaciya Ta Yaya zan hanashi tafiya ina nan yana can how? Be duba amincinsu da Yaya Jawwad yafasa tafiyar ba se ni da bama shiri to ni ya zanyi?
Kawai shirmen mafarkine kimanta kicigaba da harkokinki
Wani bangare na zuciyarta ya gayamata,
aikam ta yadda da abinda zuciyarta ta gayamata na ta manta shirmen mafarkine
Ga bacci a idonta kanta har ciwo yake amma bazata iya ba saboda fargabar inta kwanta me zata gani
Duk yadda taso ta manta takasa zuciyarta se bugawa take da sauri? hankalinta yaki kwanciya
" Nashiga uku ni Jalila meke shirin faruwa dani haka ya zanyine?
Ko ingaya Ummi me
Karki kuskura hakan be dace ba mussaman intaji abinda yayi miki bazataji dadi ba, wani sashi na zuciyarta ya gargadeta
Siyama ce ta fadomata a rai, dan haka da sauri ta mike taje ta wanke fuskarta tasaka hijjabi ta fito, ta tarar da Ummi tana saka a dakinta
"Ummi inaso zanje gurin siyama"
"Adawo lafiya kigaidamin da ummanta saura ki dade inkika dade kin kori gaba kinsan halina"
Gyada kai Jalila tayi ta fita ta nufi hanyar gidansu siyama

Haka nan take tafiyar kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, haka takarasa gidansu siyama.
? ? makeken Gida ne Wanda yayi matukar haduwa da tsaruwa baban siyama yana da kudi sosai custom ne daga shi har Maman siyama mutane ne masu saukin kai kuma sun yaba da hankalin Jalila shiyasa suka kyale kawancen nasu
Siyama Sam bata da girman kai a makarantar boko suka hadu da Jalila tun primary suke tare makarantar 'yay'an masu kudi ita Jalila takeyi saboda Jajircewa da rikon amana na baban su Jawwad
Kawancensu har tsakanin iyayensu mata Wanda yakai har kasuwanci sukeyi tare, umman Siyama ta San komai game da rayuwar ummin Jalila ta dauketa kaman Yar uwatta ummin Jalila bata fiye shiga harkar mutane ba amma tana mu'amala sosai da umman Siyama

A tangamemen parlour Jalila ta tarar da Umma (mahaifiyar siyama)
"Hajiya Umma brk da rana"
"Anya Jalila zan amsa gaisuwar nan taki, kinyi tafiya ba sallama kin dawoma bakizo mun gaisa ba balle insa ran tsaraba to ni nayi fushi"
Umman tafada cikin zolaya
"Haba Umma tuba nake yau ai gani Nazo"
"Bawani kinzo dai gurin Siyama sekije tana daki,
Nikuma zamu gauraya dake naganki wani iri ko baki laafiya ne"?
"Hajiya Umma kenan, lafiyata kalau, bari inje gurin siyama, Ummi tana gaisheki "
"Ina amsawa"

Jalila ta mike ta haura sama dakin siyama
Siyama ce kwance akan katafaren gadonta tayi rub da ciki tana game a waya,
Sallama Jalila tayi, siyama ta amsamata ba tare data daga kai ta kalleta ba
"Aminiya gurinki nazo akwai matsala"
Banza siyama tayimata tacigaba da abinda take
"Aminiya magana fa nake kika min banza"
Jalila ta maimaita
"Ni a wa zan San matsalarki, ni na isa ko kin manta wulakancin dakika yimin A gidanku"
Siyama ta bata amsa ba tare da ta dago ba
"Ohh God am sorry aminiya lokacin ina cikin tashin hankaline, Dan Allah kimin afuwa ki saurareni, right now ma a cikin wata matsalar nake siyama jinake kaman zanyi hauka, yanzu haka zuciyata bikiji bugun data keyi ba"
? A razane siyama ta mike zaune tana kallon Jalila
"Kaman Yaya? Meyafaru?"
Ajiyar zuciya Jalila tayi sannan ta labarta mata duk halin da ake ciki
"Ni yanzu babban tashin hankalina aminiya ni bansan ta Yaya zan hana shi tafiyar nan ba yana kano ina Kaduna,
Tunda na fara mafarkan nan bana nutsuwa se inji kaman zan haukace"
"Easy, don't said that again please karki kuma batun hauka
Kinga maganata ce fito? dama nagaya miki zaman Kaduna bana kibane inkika temake shi kanki kikayiwa kamar kin temaki Jawwad ne"
"Kinga ni ba wannan surutun ba kigaya min mafita siyama kaina ya kulle"
"Aikuwa dole kibude shi, shi tunanin naki, yaya Jawwad zaki kira ki zigashi akan kar yabarshi ya tafi saboda besan meze faruba in ya tafi zuciyar Yaya Jawwad zzaki karya yadda zaki ingiza shi ya hana shi tafiya"
"Siyama bana tunanin hakan me yiwuwa ne, nasan Yaya Jawwad zeyi iya yinsa kan yahana shi tafiya tunda kika ga ya hakura to abun yafi karfinsa,
Dama da ganin idon nan na Jalal zeyi azababben taurin kai"
"A'a Jalila ki dai gwada kigani, kema ai taurin kan yana damunki"

Mummy ce take ta rusa kuka
"Yanzu Jalal dagaske tsallakewa zakayi kabarni, kai kana ganin hakan shine dai? a rayuwarka bani da kowa se kai zaka Sa k'afa ka tafi, har kana fadin inka tafi bazaka kuma dawowa ba"
"Idan na tafi hutun mune ni dake gaba daya ki huta dasaki bacin rai danakeyi"

Ilham ce tafito tazo gabansa
"Haba Yaya Jalal yanzu in...
" ke!!!!! Kikasake kika Sa min baki sena tattakaki ina ruwanki dani mayya kawai"
Ya fice daga parlour lambar Jeje yakira
"Karka manta fa kazama cikin shiri karfe hudu insha Allah jirginmu ze tashi"
Ya katse wayar ya tafi dakinsa

"To siyama bari in jarraba amma nikam na karaya Allah kabani iko "
"Ameen don't waste time yi sauri"
Siyama ta fada a gaggauce

Lambar Jawwad Jalila ta kira
Aikuwa tayi sa'a ya dauka

"Barka da rana yayana"
"Yawwa autar Ummi ya ummina ya Gida"
"Lafiya kalau, amma yanaji muryarka wani iri ko duk Dan tafiyar Yaya Jalal dinne"

"Kedai bari sisy na Daren Jiya banyi bacci ba Jalal ya kafe wannan karon tun tasaowata tare muke dashi jinsa nake wani bangare na zuciyata amma ze tafi ya barni gani nake Lamar da wasa yake"
Ajiyar zuciya Jalila tayi

"Ya tafinne?"
Jalila ta tambaya
"A'a jirgin karfe hudu zebi yau zetafi"
Cikin Jalila ne yayi wata kara ta kalli agogo karfe daya da rabi
"Yaukuma ?"

Tafada a tsorace
Siyama ce ta kalleta ta girgiza mata kai alamar kwarin gwiwa

"Eh yau sisy haka dai yacemin, yau ban yi tsammanin Dan uwa zetafi ya barni ba"
Jalila ta numfasa tace
"To waime yasa ze tafine?"
"Cewa yayi gara ya tafi mummy ta dena ganinsa, yadena sata bacin rai"

"Allah sarki mummy ko yazataji idan ya tafi, ya daddynsa zeji in ya bude ido yaga baya kusa dashi,
Yaya Jawwad abokinka bashi da tausayi baka tunanin me ze faru Idan ya tafi kasar da babu me Sa shi babu me hanashi,
Baka tunanin wasu abokai ze hadu dasu a can,
Allah sarki nasan dole mummy ta zubda hawaye inya tafi, kuma Kasan hawayenta matsalane a rayuwarsa, Yaya yakamata kahana shi tafiyar nan, ka temakawa rayuwarsa daga masifar hawayen uwa
Yanzun ma karkayi mamaki abokanan banzarsa ne suka ziga shi shine zeyi tafiyar"

Da sauri Jawwad ya tashi zaune tare da furta
"Abokanan banza Jeje"

"Mekace Yaya"
"No bakomai zanyi kokari inkuma jarraba hanashi tafiya nagode sosai da gudunmuwarki kanwata, da na hakura amma kin tunatar dani wani abu me mahimmanci nagode"
Sukayi sallama
Jalila tayi ajiyar zuciya
"Good dear kinyi yadda yakamata sekace Jarumar film"
"Hmm ba wannan ba aminiya Allah yasa ya yadda kar yayi tafiyar nan"
"Ameen insha Allah bazeyiba Addu'a zamuyi tayi"
"Allah ya amsa amma nakaraya saura awa biyu ya tafi fa"
"Ba komai calm down mucigaba da addu'a Allah ya bawa Yaya Jawwad sa'ar hanashi tafiya"
"Ameen"
Jalila ta amsa a sanyaye

Da sauri Jawwad ya tashi ya nufi gidansu Jalal kai tsaye part din Jalal ya nufa yaje ya tarar yashiga wanka
Gefe ga katuwan trolley dinshi ya hada ta tsaf
A hankali Jawwad ya shafa trolley yayi ajiyar zuciya, ya nemi guri ya zauna yana jiran fitowarsa ya shafe akalla mintuna sha biyar yana jiransa sannan ya fito daga wankan

"Kana nan banji shigo warkaba ai"
JALAL ya fada yana goge jikinsa da Dan karamin towel

"Jalal"
Jawwad yakira sunansa da dan sauri Jalal ya kalleshi saboda da wuya ya ambaci sunansa

"Baka saba yimin karya ba yanzun ma bana fatan kayimin kaida wa zaku tafi dubai"?

Jalal ya danyi shiru sannan ya yi magana
" nida Jeje ne"?
Da sauri Jawwad ya kalleshi Jeje fa kace Jalal
"Jalal kasan me kake cewa kuwa yanzu kaida shi zaku tafi,
Ka fifita tafiya kabar iyayenka saboda wannan Dan iskan Mara mutuncin
Kazabi ka tsallake kawai katafi garin da banaka ba, ka zauna,
Dama nasani he is behind all what u are doing"

"No Jawwad don't blame him u know who is behind all this kasani kasan komai karka Dora masa, nan da wani dan lokaci shi? jeje ze dawo nizanyi zamana a can in karatun Yakama in cigaba a can"

"Jalal kasani ba kaunarka yake ba, baze bari kayi kyakykyawa rayuwa ba kullum burinsa ya kuma rusaka"

"Ouhhh don't mind me bros, kabani gudunmuwa a rayuwata bazan mantaba, bana tunanin ko ciki daya muka fito da kai zansamu fiye da haka ,
Amma gara in barka kaima ka huta, kanwarka bata son? mu'amalarka dani banaso mutane sucigaba damin kallon zan bata maka rayuwa kamar yadda tawa tasamu illa,
Banason mutane sucigaba da kyamata da miyagun halayena
Gara inje rayuwar da naga dama Inda ba Wanda yasanni balle ya damu dani"

Cigaba da shirinsa Jal yayi yasaka kananan kaya wando jeans da T-shirt blue, ya taje sumar kansa ya daura agogo sannan ya dakko bakin glass yasaka
Yayi kyau matuka, duk abin nan da ake Jawwad yana zaune yana kallonsa,
"Dan uwana kazama me min addu'a aduk inda kake kaman yadda kake min abaya Jawwad bazan manta da kai a rayuwata ba"
Jalal yafada jikinsa a sanyaye

"Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,
Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,
Da second daya bantaba kyamarka ba amma sekai akan wani dalili naka Mara amfani
Zaka tsallake ka barni,
Akan wannan Mara imanin zaka tafi kabar kasarka ta haihuwa iyayenka yan uwanka ka tafi, wannan shine sakamakon abota wannan shine yan uwantakar dake tsakanina da kai
This is what I deserve from you nagode da kauna Jalal"
Jawwad yayi maganar cikin fada

Jalal ya tako gaban Jawwad ya dafa kafadarsa idonsa dauke da kwalla, muryarsa na rawa yafara masa magana

"Am sorry dan uwana baka cancanci haka daga gareni ba but am sorry ba yadda na iya"

Yaja trolley dinsa yayi waje da sauri

"Siyama nifa wallahi gabana faduwa yake ganinake wallahi seya tafi
Bakisan halin Sa da taurin kai ba"
"No kwantar da hankalinki, kome zezo da sauki insha Allah yanzu kira Yaya Jawwad din muji ya ake ciki"
"Anya zan iya magana kuwa bakiji bugun da zuciyata take ba"
"Calm down kirashi kiji"

Layin Yaya Jawwad takuma kira
Sedata kusa tsinkewa sannan ya daga
"Yaya Jawwad ya ake ciki ne yafasa tafiyar kuwa"
"Jalila ya tafi bashi da niyyar fasawa ya tafi yau ze bar kasar nan"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Share please
More comments more typing......
Love u all my fans


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??

Daga Alkalamin Yar baba
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 16&17

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

Aimin afuwa the page is not edited
? ? ? ?? -my first Novel-

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Jalila ta fada jikinta a sanyaye
A hankali ta sauke wayar daga kunnenta ta kashe wayar
Takalli siyama
"Aminiya ya tafi"
Yasalam shine abinda siyama ta furta

"Kwantar da hankalinki har yanzu da sauran lokaci ai"
"Kwanciyar hankalifa babu shi Aminiya dan bakiji yadda zuciyata take min bane
Bari in tafi Gida uumi tace kar in dade kuma kinga nabata lokaci bari in tafi kawai"
Har gate Siyama ta rakota tana bata kwarin gwiwa, tare da bata shawarar cigaba da addu'oi
Sannan ta mata alkawarin zatazo har gidan taji yadda akayi
Haka Jalila ta tafi Gida jikinta a mace
Yanayin fuskar Ummi ya nuna mata tayi fushi da ita
Dan se basar da ita take Jalila ta rasa meyake mata dadi

Jeje ne a tare da wani mutum a cikin mota me tint glass yasaka wando three quarter da wata Yar Riga Mara hannu suman nan tayi tsage?
Kai daka ganshi ka ga dan iska

"Katabbatar kayi abinda yakamata in kukaje kasan abinda ya dace kayi shima wannan aikin naka akwai kaso me tsoka ka tabattar da aikin nan ya tafi dai? "
Mutumin yayiwa jeje maganar

"Considered it done my boss zan tabbatar da aikin nan ya tabbatat"
Jeje yafada yana dan risinar da kai
"Good"
mutumin yafada cikin Isa
Sannan jeje ya bude kofar motar ya fita ya dauki akwatinsa
Inda sukayi zasu hadu da Jalal yaje ya tsaya ya kirashi a waya yan mintuna kadan sega Jalal ya karaso
Shima
"hmm yau kayi abun arziki ka cika alkawari"
Murmushi Jeje yayi
"ba dole ba my boss ina ciki farin ciki"
"Good yanzu se mu tafi ko"
Gaban Jalal ne yai mummunar faduwa
Meyake damuna ne haka, menake shirin yine"
Jalal yake maganar a zuciyarta

"Yanaga kana tafiya kuma a hankali yanzu ko akwai abunda yake damunka" Jeje ya tambayeshi
Girgiza kai Jalal yayi
Jeje ne yafara mika passport dinsa aka duba aka bashi ya danyi gaba yana jiran a duba na Jalal,
Jiki a sanyaye Jalal ya mika passport dinsa

(Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,
Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,!!!!!)

Maganganun Jawwad ne suke dawo masa dakuma tsantsar damuwa da hawaye da ya gani kwance a idon Jawwad su yake tunowa se yaji zuciyarsa ta cunkushe bakin ciki ya ziyarci zuciyarsa, gaskiya ba karamin kauna Jawwa yake masa ba in ya tafi beyiwa kansa adalci ba Jawwad wani bangarene me mahimmanci a rayuwarsa ga kuma mahaifinsa, anya inyayi tafiyar nan yayiwa kansa adalci
jikinsa ne yayi matukar yin sanyi, hannu yasa ya karbi passport dinsa ya juya dabaya yafara tafiya
"Jalal ya haka lokaci fa inazaka jene"
Jeje ya tambayeshi
Bebashi amsa ba yacigaba da tafiya da gudu Jeje ya taho ya sha gabansa
"Man wai meyafaru ne ?
Ina zakaje yanzu fa jirginmu ze ta shi"
? "Zaka iya tafiya nikam na fasa"
Zaro ido Jeje yayi "why meyasa zaka fasa"
"Saboda haka naga dama nace in zaka ka tafi ni na fasa"
Ya bashi amsa
JALAL yayi maganar a tsawace

Wayarsa ya dakko ya kira Jawwad, amma be daga ba taita ringing
Jawwad yana kallon kiran yaki ya amsa seda takusa katsewa sannan ya daga wayar
"Kazo ka daukeni a airport"
"Kamar ya?"
Jawwad ya tambayeshi
"Ina airport nafasa tafiyar kazo ka daukeni"
"Bazan zo ba dacan ni na kaika"
"Idan bakazoba zan tafi u know I mean what I said"
"Ohh sorry gani nan zuwa"
Wai dagaske ya fasa tafiyar Jawwad ya tambayi kansa da sauri ya mike ya dau mota ya nufi airport

Ummice take lazimi akan dadduma gidan shiru kaman ba me rai a cikinsa
Jalila tana can dakinta tana duniyar tunani
Ummi ce ta dinga kiranta takirata ya kai sau uku sannan taji ta amsa
"Jalila zonan"

"To Ummi gani nan zuwa"
Mikewa tayi ta nufi dakin Ummi taje gabanta ta zauna
"Ummi gani"

"Naganki ai, Jalila wai meyake damunkine kwata? yan kwanakin nan kaman baki da lafiya baki da walwala Sam
Meyake damunkune baki da Wanda zaki gayawa matsalar ki fiye dani baki da aiki se tunani
My dear tell me what's actually wrong with you bana jin dadin ganinki a haka"
Tausayin ummine yakamata taji kaman ta gayamata gaskiya amma seta fasa
"Ummina babu abunda yake damuna kawai surutan danake da daddare ne da mafarkai bana so"
"Eyyah sorry my dear kinji tunani baze hana faruwar komai ba addu'a zaki dingayi nima inayimiki Komene Allah zemiki maganinsa"
Haknan se Jalila taji hankalinta ya Dan kwanta
Zame jikinta tayi a hankali ta kwanta akan cinyar ummi
Tanata ambaton Allah a zuciyarta domin tasamu zuciyarta ta rage bugun da take

Ba a dau dogon lokaci ba Jawwad ya karasa airport Jalal ya hango a zaune jeje yanata lallaba shi
"Tir da wannan dan iskan bawan, mtseeww"
Jawwad yafada a hankali

Jalal yana hango Jawwad ya mike
"Dan uwa dagaske ka fasa tafiya"
"Nafasa Jawwad kona tafi bazan samu nutsuwa ba zuciyarta tana Nigeria tare da Dan uwana"
Rungume juna sukayi kaman zasu shige jikin juna
Wani mugun kallo Jeje yayiwa Jawwad
"Wai dagaske fasawar zakayi?"
Jeje ya tambayeshi a fusace

"Jeje nafasa tafiya bazan juri ganin kwalla da bacin rai a idon Jawwad kamar yadda nafada maka kona tafi dubai zuciyata tana Nigeria"
Jawwad ne yaja trolley Jalal yasaka a boot, ya bude masa motar ya shiga
Jeje ne ya zagayo gaban Jawwad yai masa magana kasa?
"Yadda ka bakantamin yau ka rubuta ka ajiye komai Daren dadewa se na bakanta maka fiye da yadda kayimin"
"Allah ya fika"
Shine amsar da Jawwad ya bashi
Ya shiga ya kunna mortar suka tafi Jeje kaman yayi hauka gaba daya shirunsu ya rushe shi beasan meze gayawa boss dinsa ba
Naushi ya kai cikin iska kamar mahaukaci
"Fuck you Jawwad, indai muna raye sena kuntata maka kamar yadda kayimin "

A hankali wani bacci me dadi ya dauke Jalila akan cinyar Ummi se ajiyar zuciya take kaman wadda ta wuni tana kuka
A hankali Ummi ta shafa kanta Allah yayi miki maganin abunda yake damunki baby na
Duk da yamma tayi Ummi bata tashe ta ba ta kyaleta saboda in tayi wannan farkawar cikin dare bata komawa bacci
Se gefin magariba Jalila ta farka tana farkawa da bugun zuciyar nan ta farka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login