Showing 57001 words to 60000 words out of 129540 words

Chapter 20 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6666

wayarki ba baby"
"Yaya Jawwad Ummi sunyi fushi dani wai se sun dawo dani kano, Dan Allah kabawa Abba hakuri,"
"Kai sisy to meye a ciki kinga seki dawo kusa damu naji dadin hakan"
Cikin shagwaba tace
"Ni wallahi, Yaya bana son zaman kano, ni nafi son zama a gurin Ummi"
"Hmm mune ba kyason zama damu ko"?
"A a Yaya nifa bahaka nake nufi ba, Ummi tace wai in na dawo kano garinsu zata koma"
"No, calm down sisy, dena kuka nan is OK ko so kike nima kisani kukan, bana son kukan nan"
Jalal da haushi ya isheshi Hannu yasaka ya fizge wayar daga hannun Jawwad
"Kana ta shirme da yarinya ko kunya bakaji, se wani shagwaba take kana lallabata"
Jawwad ne ya bishi da kallon mamaki
"To ina ruwanka dani so kake in kyaleta taita kuka in kanta yayi ciwo fa?"
"A'a bindiga kan nata zeyi ba ciwo ba, kukan dadi take da sojoji basu karairayota sun zubowa Abba a boot ba yakawo maka"
"To naji ban wayata"
Kashe wayar Jalal yayi,
"Na hana in munkoma Gida idan nabar gurin seka cigaba, kokuma in baka wayarka in tsaya ka sauka, seka samu gurin zama a titi, ka cigaba da shiriritar"
"Yanzu kiri? bazaka bani wayata ba"?
"Eh bazan bayar ba"
"Allah sarki baby, nasan kukan zata cigaba, Dan Allah kabani in rarrasheta"
"Aiko sedai ta mutu, in seka rarrasheta zata dena"
"Shikenan zan ramane"
Haka suka tafi Gida suna tafe suna fad'a
Memakon? Jalal ya kaisu Gida se ya canza hanya
"Ina kuma zamuje"
Jawwad ya tambayeshi
"Yunwa nakeji ice-cream kawai zan siyo ko fura"
"Kwadayayye kawai"
"Eh naji kwadayayyen ne nasan duk haushina kake ji Dan na hanaka waya, kuma bazan bayarba"
Yasa hannu ya dau wayar Jawwad, ya bar wayoyinsa sabuwa da tsohuwar a cikin mota ya bude motar ya fita

Dan murmushi Jawwad yayi
Jalal kaima ai rigimammen ne
Jawwad ya furta hankali

Jeje tun dazu se trying lambar JALAL yake amma baya shiga
Yanzun ma kuma trying yayi by luck wayar ta shiga
Jawwad dake kashingide a cikin mota yaji wayar Jalal tana ringing da ya duba ba suna ya daga yasa a kunnensa ba sallama ba komai Jeje yafara magana
"Ina ka shigane tun dazu nake kiran wayarka amma yaki shiga"
"Sorry ba shi baneba wayarsa ce ta Dan samu matsala"
Jeje yagane muryar Jawwad amma alamu ya nuna shi Jawwad be gane shiba Dan da ya ganeshi baze daga wayarba ma
"OK Dan Allah yana ina yanzu"
"Mun Dan fita dashi, yanzu muna kabuga ya Dan fita ne yanzu zamu karasa Gida insha Allah"
"OK nagode"
"Wa zance masa?"
"No bakomai zan kuma kira"
"OK"
Jawwad ya katse kiran

Jeje ne ya kira Hannah a waya
Bugu biyu ta dauka
"Ya"?
" ke kin ban wahala gaskiya tun dazu nake kiransa a waya se yanzu na same? shi a waya, shima ba shi ya daga ba mayensa ne ya daga wai wayar Jalal dince ta lalace, sun Dan fita yanzu zasu koma Gida"
"Au nice ma nasaka wahala kamanta aikin naka ne?"
"Hakane fa tuba nake me idon zinari"
Murmusawa Hannah tayi
"Weldon yanzu kuma zanyi nawa aikin, zan Dan jefa masa fargaba a zuciyarsa"
"Meye shirin naki?"
"Ba ruwanka kai dai zuba ido"

Jawwad yafara gajiya da zaman jiran Jalal
"Kome ya tsaya yi oho"
Jawwad yai maganar tareda duba wayar Jalal don ganin lokaci message ne yake shigowa wayar


? "Yau kaki daga wayata, ka jefa Zuciyata cikin matsala, ko Abinci nakasa ci dan haka Kaima zan saka taka zuciyar a damuwa Ina hanyar zuwa gidanku
Zakazo ka sameni a gidanku
Cikin dakinka, kuma komai
Ze iya faruwa in aka ganni a
Dakinka, in baka son hakan
Ya kasance mu hadu a??
Restaurant din damuka hadu
Da farko mintuna goma sha
Biyar kawai kake dashi
? ? ? ? ? From your lovely bae
? ? ? ? ?? (Hannah)

Wannan wace irin jaraba ce, haka Jalal yai maganar hankalinsa a tashe, bayaso sunan Jalal ya kuma baci, da sauri yayi dialing number da aka turo message din da ita amma taki dagawa,
Yasalam Jalal ina ka tafine ana shirin jefaka cikin matsala

Daren ranar ma Jalila batayi ishashen bacci ba ko abinci taki sakin jiki taci, Ummi se rayuwarta take ita kadai ba tare da ta shiga sabgar Jalila ba dukda a cikin zuciyarta bata jin dadin abinda takewa Jalilan amma yazama dole ta nuna mata bacin ranta akan abunda Jalilan takeyi
?? Washe gari da safe Jalila haka Jalila ta shirya ta tafi makaranta, tana zuwa yan ajinsu yan son jin gulma sun so su tambayeta yadda akayi amma ba fuska ta hade rai se muzurai take, suna tsoron su tambayeta suma ta juye musu kwandon bala'i
Mummy Hanan dakanta tare da wasu sojoi Guda biyu suka kawo Hanan makaranta cikin wata CRV me tint glass, sojoji guda biyu na gaban motar, sun dan jima a kofar makarantar koza suga wucewar Jalila amma basu ganta ba daga baya, mummy tace Hanan ta shiga school ita tasan abunyi
Tsakanin Jalila da Hanan ba Wanda ya kula wani, duk yanda yan aji sukaso jin gulma basu samu dama baa

bayan tafiyar Hanan ba dadewa sega malama ramatu an sauketa a napep zata shiga cikin makarantar
Dan sauke glass mummy Hanan tayi
"Sannu dai"
Mummy Hanan tafada cikin ISA da iyayi
Malama ramatu na ganin mota
Ta washe baki da durkusa
"Yawwa sannu madam ina kwana"
A dan wulakance mum Hanan ta amsa
"Yawwa lafiya, if u don't mind please I have an issue to discuss with you"
"A a ba wata damuwa, madam ina jinki"
Alama tayiwa malama ramatu data shigo cikin mota
Ba tayi tunanin komai ba ta shiga
Mummyn Hanan ta numfasa
"Da alama kema staff ce a school din nan ko?"
"Yea of course"
"Good, kinsan case din da akayi a school din nan da akayi fada tsakanin dalibai biyu aka daki yarinya Yar gidan captain rasheed "
Se a lokacin malama ramatu ta kalli suwaye a gaban motar taga sojoji nan take ta sha jinin jikinta
"Emm...e..eh nasani madam amma wallahi bana gurin akay...."
"Inma kina gurin ke kikasani tambayarki zanyi kikamin karya, zaki gane kurenki ne"
"Zanma fadi gaskiya wallahi"
"Wacece Jalila Aliyu Imam Yar uban waye ita?"
Nan take malama ramatu ta karkace ta dinga rattaba bayanin karya da gaskiya
"Ba Yar uban kowa bace ba, a sanina ma bata da uba, amma naji ana wai ya mutu ko karya akema ohoo, daga? ita se uwattta suke zaune baata da wani gata, se tsabar iskanci da Neman rigima"
Haka taita zuba, kaman ruwa ba comma ba full stop
"Ke surutun ya isa haka bani address din gidan su"
Malama ramatu ta bata address
Maman Hanan Tabawa malama ramatu 5k a wulakance sukaja mota sukayi gaba

Kuma trying lambar Hanna Jawwad yayi da wayar Jalal
seda taja aji, azatonta Jalal ne sannan ta daga cikin yanga tafara magana
"Baby lokacinka ya fara karka dauka da wasa nake wallahi dagaske nake in samu haduba gidanku zanje"
"Amm Hanna ba? JALAL bane nine Jawwad dan Allah karkiyiwa Jalal haka, dama yan anguwa sun samasa ido, yanzu in kikayi haka zaki kara bata masa suna kisa akuma tsanarsa dan Allah karkiyi haka duk abun Jalal baya bin mata kuma mahaifinsa yana gari in ya ganki bazeji dadi ba"
Nisawa Hannah tayi
"Jawwad dan uwanka yafiye taurin kai yaki karbar bukata ta, gara in biyo masa ta inda yakamata, mintuna sha biyar ne kacal daku, in bakuzoba wallahi zanyi shigar danaga dama ince karuwarsa ce ni kuma har Gida xanje, ko dayake nasan hakan ba lallai yabata masa ba but at least ze gane da gaske nake, ganinsa kawai nakeso nayi in samu sauki a raina, zabi ya rage naku dan uwa na gari"
Ta kashe wayar
"yasalam wannan wane irin abune, Allah ya fidda kai sharrin wannan yarinyar Jalal, ohhh gara muje mu sameta karta bishi Gida daddy bazeji dadi ba dama ga yan unguwa sunsawa Jalal ido, inaga kuma aga karuwa taje gurinsa "
Jawwad ne Ya bude motar da sauri ya fita Neman Jalal

Ko islamiyya Jalila ba taje ba, kuma Ummi batace ta shirya taje ba, ta kyaleta idonta duk ya kumbura saboda kuka
"Allah sarki baby na banajin dadin ganinki a haka amma kedin ce Zuma seda wuta, gara in horaki" Ummi tayi maganar a zuciyarta
Da yamma likis su Jalila sukaji tsayuwar mota a kofar Gida, Jalila tana tsakar Gida ta zurawa Ummi ido kaman bata Santa ba, Ummi tanaa shan fura,

Cikin izza sukaji sallama
Ummi ce ta amsa sallamar tare da jiran shigowar Wanda yayi sallama
Jalila tana zaune bata amsa sallamar ba balle ta motsa daga inda take,
"Sannu da zuwa shigo"
Ummi tayi maganar tana mikewa tsaye bata gane matar ba tayi zaton irin customers dinta ne
"Ba zamane ya kawoni ba"
"To lafiya meyafaru?"
Ummi ta tambaya
"Nasan baki sanni ba nice Hajiya Safiyya Mrs. Captain Rasheed "
Da sauri Jalila ta daga kai tayi arba da Hanan da mamanta
Maman Hanan ce ta janyo hannun Hanan
"Kalli duba ta'addancin da y"arki tayi kina tunanin kunci bulus ne?"
Gaban ummine ya fadi da taga Hanan

Share please
More comments more typing............
Ina alfahari da masoyana da masu yi min addua ina godiya d'd'd'
Masu bukatar shiga group dina akwai link din group din Asama amma akwai dokoki

=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 26

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

? ? ? ? ?? -MY FIRST NOVEL-

Wani mugun kama Ummi taga Hanan tanayi da Jalila, ciwon goshin Hanan ta kalla
"Eyya kiyi hakuri ai munje makaranta akan case din, mun bada hakuri, babanta yace komai ya wuce kiyi hakuri Dan Allah"
"Keda kinsan da bada hakurin kika haifi Yar da bata da tarbiyya, kika haifi yarinyar Datafi karfinki ni na dauka ma Yar wata hamshakin ce Ashe ba Yar uban kowa bace face Mara galihu?"
"Duk me ya kawo wannan maganar, haba ke kuwa Jalila tana da tarbiyya rashin ji ne kawai na yara, kuma batun gata kowa gatansa Allah,"
Wani abune yakawo wa Jalila iya wuya motsa baki tayi da niyyar rashin mutunci cikin tsiwa sukayi ido hudu da Ummi seta hadiye maganarta tayi shiru
"Da wallahi niyyata ubanta zansa akoyawa hankali in yaso gobe yabawa yarsa tarbiyya ya banbance mata matsayin yayan gata da marasa galihu"
"Kar a kuma sakomin uba, a barshi ya kwanta cikin aminci a kabarinsa, ni nayi laifi ba shiba"
Jalila tayi maganar tana jujjuya idanu
"U see mummy wannan yarinyar bazata yi nadama ba memakon tabaki hakuri rashin kunya zatayi miki, in bakiyi Sa a bama zaginki zatayi, kawai kisa a dauketa a je a horata"
Hanan tayi maganar tana kallon Jalila
Da yarabanci Ummi tayiwa Jalila magana, Jalila ta yamutsa fuska ta Dan kara hade rai
"Naji yata ba Yar uban kowa bace bamu da gata se Allah mu bamu su arziki bane, amma kiyi hakuri batun a dauki Jalila a horata be taso ba, bazata karaba"
"Tsiyar talaka kenan ko ince matsiyaci, ya dakko abunda yafi karfinsa, karshe yazo yana karya murya,"
Ta maida idonta kan Jalila
"Kekuma kinci Sa a da ubanki zan Sa akama, wannan uwataki ce ma tabani tausayi, ba dan haka ba da sena Sa an sauya miki halittu, kibari kitaka wani matsayi kisamu me tsaya miki in kinyi rashin mutunci, a yanzu dabaki da galihun nan wahala zaki sha Mara tarbiyya kawai"
"Nice ma ke saboda rashin tarbiyya kuma kar......
Jalila ce tafara magana ummi ta dakatar da ita
Ummi ta kalli mummy Hanan sannan tace,
" nace kiyi hakuri ko, se magana kike akan gata se dai ko nan gaba amma a yanzu dai banajin kinsamu gatan dana samu a rayuwata, sannan yata ba Mara galihu bace ba, da gatan ta, daliline yasa kiga ganmu a haka, amma bazan gazaba Allah yabaki hakuri"
Tsaki mum Hanan tayi taja Hanan suka fita, ga magana fal abakin Jalila amma Ummi ta hanata magana,
Wata kwallar bakin ciki ce ta taru a idon Jalila, meyasa Ummi ta hanata magana daki ta wuce ta kyale Ummi a tsakar Gida

Jawwad Yana ta duba ta inda Jalal ze taho ya hangoshi yana nufo inda motarsu take da ledoji a hannunsa da sauri Jawwad ya karaso
"Ina ka tsaya daga siyen abu"
"Au fitowa kayi nemana, da nasani kulleka nayi a cikin mortar"
"Bar wannan maganar ban mukullin mota ni zanyi driving dinmu"
"Me yasa?"
Jalal ya tambayi Jawwad da mamaki, be bashi amsaba yasa hannu ya karbi key din daga hannun Jalal, suka shiga suka tada mota
Jalal ne ya kalli Jawwad
"Nifa bangane wannan abun da kakeyiba, ina kuma zamuyi , ba gida zamu tafi ba?"
"No wani guri zaka rakani"
"Ina kenan?"
"Just watch" inda sukayi zasu hadu da Hannah ya kaisu, ya kulle Jalal a motar ya fita da wayar Jalal kaman yadda shima yayi masa dazu lambar Hanna ya kira
"Kina dai? ina gamu munzo restaurant din"
"Nabar nan gurin ina bayan layinku rukunin sababbin gidajen nan"
"Haba Hannah amma ba haka mukayi da farko ba"
"Na canza ra ayine ina daf da zuwa gidansu Jalal in bakuyi Sauri ba" katse kiran yayi ya koma motar da sauri ya kunna ya ja motar ya bar gurin
"Nikam naksa gane ma'anar abunda kakeyi Jawwad wai meye haka?"
"Zaka gane ma'anar abunda nake yanzun nan"
Inda Hanna tayiwa Jawwad kwantace nan Jawwad ya kaisu ya kirata yace gasu sunzo, sannan yacewa Jalal ya fito daga motar, ba musu ya fito daga motar yana kallon Jaww??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ad, daga cikin tata motar Hannah ta fito tana wani taku cike da iyayi da isa wata shedaniyar rigace a jikinta straight found ce amma yadin roba? ya kwanta a jikinta yakamata tsam se Dan kwali data daure kanta dashi ta fito da Wig's dinta ya bazu a gadon bayanta,
Da mamaki Jalal ya kalli Jawwad cike da tuhuma da sauri Hannah ta karaso domin rungume Jalal amma yayi saurin matsawa baya
"Meye haka wannan wane irin shirmene baki da hankali niza ki hugging? Meye ma anar hakan daka kawoni nan gurin Jawwad?
Yai maganar a fusace yana kallon Jawwad, Jawwad bece masa komaiba
" ba laifinsa bane, ni nace yakawomin kai ko in maka ba dai? ba kuma Dan na rungumeka ai ba laifi bane,? Jalal why are you avoiding me? do you thinks am Jocking danace ina sonka, se wulakanci kake min haba Jalal kalleni sama da kasa banyi kama da irin matar daza a wulakanta ba meye aibuna"
Kallon Jawwad yayi
"You see, meye amfanin hakan dakayi, ka dakkoni ka kawoni gurin wannan mahaukaciyar yarinyar, kalleta kalli jikinta, dan ta rainamin hankali kuma tace tana sona, koda nake shan giya nasan abunda ya dace dani"
Jalal se fada yakeyiwa Jawwad duk yadda Jawwad yaso ya kwantar da hankalinsa yayi masa bayani yaki yadda se fada yakeyi, murmushi Hannah tayi sannan tace
"Masoyina naji kana kasan abunda ya dace da kai, ai babu wani abu me kyau da yadace da kai babyna, nidin dai nina dace da kai, kai duba da yanayin taka rayuuwar, da kuma tawa suna kamanceceniya babancin kadanne kawai"
Kurawa Jawwad ido Jalal yayi"kagani ko ka kyauta" shine abunda Jalal yafada Yakama hanyar tafiya, da sauri Jawwad ya bishi "Dan uwa Dan Allah ka saurareni"
"Nika rabu dani babu abinda zaka gayamin, wallahi in kayi wasa sena Sa an batarmin da yarinyar nan, Dan me zaka dinga cusamin ita dolene sena dinga shiga sabgar matan, I hate her"
Ya juya yayi tafiyarsa yabar Jawwad a nan gurin a tsaye Hannah kuwa dariyar farin ciki tayi saboda tayi nasara, so take dama ta Dan janye Jawwad daga jikin Jalal don tasamu damar gudanar da abinda tayi niyya, tayi nasara tunda Jalal har yayi fushi haka
Jawwad ne ya dawo inda yabar Hannah cikin damuwa ya dubeta
"Haba Hannah baki kyautamin ba kalli yadda yayi fushi, ba? haka mukayi dake ba, anya son gaskiya kike masa?"
"Kwarai kuwa son gaskiya nake masa, kayi kokari nagode daka yi dalilin dayasa naganshi at least dukda yaji haushi amma ka faranta min"
"Dan Allah ina rokonki, karki je gidansu Jalal a hakan ma fama ake akan ya canza halayensa, in kika kuma sanadin lalacewarsa biki kyauta ba, Hannah ke mace ce baza kiso ace Jalal danki ne ko yayankine a haka ba"
Yadda Jawwad yai maganar abun tausayi har Hannah taji yana nema ya kashe mata gwiwa Dan haka da sauri tace
"Thank you, ni na tafi semun kuma haduwa"
Ta juya tai shige motarta, bashi dazabin da ya wuce shima ya tafi, Dan haka ya hau motar da sukazo ya tafi

Bayan sallar magariba Jalila durkushe agaban Ummi tana kuka"Ummi Dan Allah kiyi hakuri, najanyo anzo har Gida anci zarafinki nasan laifinane amma insha Allah bazan kuma ba kiyi hakuri Dan Allah "
Hannu Ummi tasaka tana gogewa Jalila hawaye"ya wuce baby amma ki canza halinki ki rike maraicinki ki dena dakko mana magana"
"Ummi na dena insha Allah"" yawwa baby nima ba a son rains name fushi dake ba" rungume Ummi Jalila tayi"nagode Ummina Allah yabaki tsawon rai me amfani"
"Ameen, Allah ya shiryamin me yabaki miji nagari" shiru Jalila tayi tareda kuma gyara kwanciyarta a jikin Ummi
"Ummi amma kinfasa maidani kano ko?
" tafiyarki kano tana nan"
"Ummi meyasa?"
"Haka mahaifinki yace kafin ya rasu" dagowa tayi ta kalli Ummi
"To amma ai yanzu baban nawa baya nan,"
"Zaki kumako ai bazaki canza halinki ba dagani ni"
Mikewa tayi daga jikin Ummi taje ta samu guri ta zauna tana tunani

Duk yadda Jawwad yaso ya shawo kan Jalal ya nuna masa dalilin dayasa ya kaishi gurin Hannah amma Jalal yaki saurarensa
Haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi gida, yaje yayi salla sannan ya shiga cikin Gida bangaren Abba, ya tarar dashi yana kallon labarai
"Sannu da zuwa Abba ya kabarosu ya hanya"
"Lafiya kalau Jawwad, ai tun dazu na dawo naita zuba ido in ganka, amma banganka ba"
"Mun Dan fitane da Jalal, Abba ya akayi da case din, munyi ways da wani Dan ajinmu yacemin ai ita yarinyar kanwarasa CE"
"Eh kam mun hadu yace ya sanka, ajinku data, Ai Allah ya temakemu abun yazo da sauri,"
Abba ya labartawa Jawwad abunda ya faru
Jinjina kai Jawwad yayi"amma Abba Jalila takirani a waya tana kuka, tace kunce nan zata dawo, zama tare damu"
Murmushi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login