Showing 87001 words to 90000 words out of 129540 words

Chapter 30 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6683

ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys d'd'd'd'd'

? ? ? ? ? -MY FIRST NOVEL-

Jalila na zuwa daidai nan a mafarkinta tai firgigit ta tashi zaune tana gumi, Ta juya ta kalli Nana tana ta baccinta, ita kuwa se maida numfashi take kamar wadda tayi dambe, tanata jujjuya mafarkin nan datayi
"Tabbas akwai wani abu a boye amma ta Yaya zan Sani, taya zan gane," gani tayi zaman tunani baze mata magani ba
Mikewa tayi ta dauro Alwala ta koma kan gadon ta zauna tafara karanta Qur'ani a hankali, a haka har bacci yakuma dauketa wayewar garin yau da Nana da Jalila tareda Ilham sunata hada? shirya abinci domin bakin dazasuzo wato su hanan, suna cikin aikinne, Naja'atu tazo Naja kanwar Sa'ada ce wato "ya'yan Yaya mairo, yayar Maama, daka ganta kasan kanwar Sa'ada ce saboda kamar dasukeyi,
Da Halima ta fara clashing a parlour, " ke ina Maama take da sauran mutanen gidan naga bakowa?"
"Sunana Halima"
"Bazance Haliman ba, ke zance, kina Yar karere Yar aiki, zan tambayeki, kicemin wani sunanki Halima, koma wace, matsiyaciya kawai mara galihu" Halima tayi saroro tana kallonta, daga baya kuma tace
"Allah yabki hakuri, hajiya tana bangaren Alhaji, sauran mutan gidan kuma suna dakin girki"
Jalila ce tafito daga kitchen da roba a hannunta
"Ya dai nakejin hayaniya, leemart meya faru"
"Bakomai bakuwa akayi"
Jalila tana kallon Naja, taga kamanin Sa'ada, tasan Yar uwarsu ce seda gaban Jalila ya fadi
"Sannu da zuwa, bari akira maaman"
"Kekuma daga ina, tambayarki nayi ko gurinki nazo"?,
Jalila ta dan murmusa
"ai banyi kalarkiba dama balle kice zakizo gurina"
Halima a ranta tace yawwa uwar dakina shiyasa kike burgeni, Jalila ta kalli Halima
"Leemart ga robar ki debo sugar a cikin"
Daga nan suka watse sukabar Naja a parlour, Naja tai kwafa lallai
"Yan aiki har sun fara samun wannan damar haka a gidan nan"
Dakin Maama Naja taje amma bata ciki, Dan haka tanemi guri ta zauna, bata dadeba Sega Maama tazo
"Naja saukar yaushe,?"
"Tun dazu nazo"
"Amma ban saniba, meyasa Nana bata kirawoniba"?
" oho ni ina na ganta, masu aiki nagani, sukamin rashin kunya a parlour, Maama yaushe yan aikinki suka samu wannan damar,"
" yan aiki kuma? Ai Halima ce kawai Yar aiki "
"A a hadda wata, tanemi tazageni danni bansanta ba, wata Mara mutunci"
" Ke ba Yar aiki bace ba, Yar kanin megidan nan ce Jalila ce fa"
"Wai itace ta girma tazama haka,? Har tanemi ta zageni"
"Ai indai wannan yarinyar ce zatayi fiye da haka"
"To me ta keyi a gidan nan"?
" hmm ta dawo nan da zama"
"Aikuwa zan saita miki ita kafina in tafi, bari inje kitchen din in karemata kallo"
Duk sun maida hankalinsu akan aikin dasukeyi sunayi suna tana hira, Naja ta shigo kitchen din ba ko sallama
"Nana aiki kuke haka"
Waigowa Nana tayi
"Naja yaushe kikazo,"
"Tun dazu nazo, masu aikinku sukayimin rashin mutunci"
"Suwa kenan?"
Nana ta tambayeta, saboda wulakanci seta nuna? Jalila, Jalila a ranta tace "wato hali zanen dutse, yadda mahaifiyarsu Sa'ada ta tsenata har y'ayanta haka suke mata wannan tsanar
Nana ta kalli Naja, lallai ma Naja, Jalila tayi miki kalar masu aiki? To Yar masu gidace me cikakken iko"
"Yar masu Gida kuma?, to ai ya'yan masu Gida mutum biyu nasani, yaushe kuma wannan tazama Yar masu Gida"
Jalila kam tayi kaman bata San da mutum a gurin ba, Nana a hasale tace
"Kai Naja Wai baki gane JALILA bane"?
Saboda iya gulma secewatayi
" ke haba itace tazama haka, tai wannan kilewar, Yar gidan kiristan nan ko?"
"Kekam Naja wallahi keda Yaya Sa'ada ban San wadda tafi wata rashin hankali ba"
Duk yadda Naja taso? Jalila ta tankamata taki, dan ita yanzu bata ita take ba abubuwan dasuka dameta ma sun isheta, sema karatun Qur'ani data fara a fili, cikin
kira arta me dadin sauraro (=??=?? Jalila Yar duniyace wato ta maida Naja shaidan, gara tanemi tsari da ita)
Karfe sha biyu da rabi suka kammala, shirya abincikan dasuka yi,
Sukaje sukayi wanka suka canza kaya
?
Yaseera da Ilham sun kule a daki suna tattaunawa, Ilham fuskarta cike da damuwa take magana
"Wallahi yaseera kaina ya kulle nakasa gane ma meyake faruwa, kullum abu kara hargitsewa yakeyi, babu cigaba, kinga rashin mutuncin da yayimin, wai yayi bakuwa namata rashin mutunci namasa krya, waikuma ranan ankkirashi a waya na daga na zagi wadda takirashi, ni abun tambayar wacece, haka hardayake kumfar baki akanta, iya sanina baya shiga sabgar mata, nakasa gane wace ce, da nayi tunanin ko Jalila ce amma kuma naga itama yana kokarin yimata rashin mutunci da kyar nasamu na gudu, Dan rashin mutuncin da nayi masa jiya daya kamani seya kusa kasheni"
Yaseera ta nisa sannan tace
"Abun da daure kai Ilham, amma fa seta yiwu wani makircin Jalila ta hada"
"Anya kuwa Jalila ce tunanina yafara bani ko wata ce daban"
"Ke bar mutum kawai Ilham yanzu abunda ze faru, kama ta yayi mu bigi cikin Jalila maybe mugane wani abu"
"Ta Yaya? Wannan me mugun wayon"
"Da hikima zamuyi ai bada fadaba, amma sekin boye wannan fushin naki, sannan abu na karshe da zamuyi shine, duk yadda za ayi kawai, ayi Auren nan a wuce gurin"
??
Kiran Hanan Jalila tayi, Dan yaci ace sunzo
"Wai yanaji shirune, har yanzu"?
" hh sarkin mita, semu koma, "
"Ke kin isa kukoma, na kagu in gankune,"
"Yi hakuri munkusa, kara turomin address din namanta, na farkon"
Jawwad ya dawo daga masallaci ze shiga Gida shida Jalal, wata arniyar Mota tayi parking a kofar gidan, Dan tsayawa su Jawwad sukayi, Abdallah ne yafara fitowa ya tunkaro su Jawwad da fara'arsa, yana zuwa Jawwad ya ganeshi rungume juna sukayi, Abdallah ya kalli Jawwad
"Aliyu mazan fama dama ana ganinka, tunda muka rabu a school bamu kuma haduwa ba"
Jawwad yai murmushi
"Aikam dai kazama wani babban mutum"
"Kaima haka ai"
Abdallah ya maida kallonsa kan Jalal, sannan ya mika masa hannu sukayi musabaha
"Aliyu wannan brother dinka ne?"
"Eh kanina ne"
Jalal ya kalli Jawwad, ya Dan harareshi
"Ko kuma dankaba sukayi dariya gaba daya"
Yarinyar data fito daga cikin motarce tasaka Jalal, da Jawwad sukayi saroro, suna kokarin gane wacece
Jalilace ko wata daban, takaraso inda suke, "Abdallah ka barmu a mota daga ganin abokanka, kamanta damu, nima yakamata inga Yar uwata, daddy ma ya matsu yaga 'Yar baba"
Takalli su Jawwad
"Sannunku, ina wuninku"
Jawwad ne ya amsa mata,
A yanayin maganar hanan da Jalila akwai Dan banbanci ita Jalila maganarta dauke take da tsiwa, ita kuma hanan da Izza take magana
Ta kalli Jawwad
"If I guess Kaine Yaya Jawwad din namu ko"?
Abdallah yace
" kin canka dai? shine"
Captain Rasheed ne shima ya fito ya karaso inda suke,
Gaisawa sukayi cikin fara a, sannan JAWWAD yayi musu jagora zuwa cikin gidan, JAWWAD yaje yagayawa Abba ga baki nan sun karaso
Hanan se rarraba ido take taga Jalila
Abba yayi farincikin ganin captain Rasheed suka gaisa cike da girmama juna
Jalila jikinta yabata, kamar sun karaso Dan haka tafito palourn da gudu hanan ta tashi ta rungume Jalila
"Ke in kika karyani fa, matsa inje in gaida Baba"?
Hanan ta harareta
" ni ba kya murnanr ganin se Baba ko"?
Babansu hanan yayi dariya
"Karaso mu gaisa Yar baba"
Jawwad binsu yake da kallo yana kuma jinjina wannan kama ta Jalila da hanan suke kaman yan biyu
Nana ma fitowa tayi domin ganin Hanan, ita kanta Nana abun yabata mamaki,
Abba yacewa Jalila taje ta kira Maama su gaisa, Jalila ta tafi kiran Maama yayinda Nana taja Hanan dakinsu
Jalal ma Jan Abdallah yayi zuwa part dinsa
Nana na shiga daki da hanan Naja ta kallesu,
"Wai hayaniyar me nakeji a gidan nan?"
"Jalila ce tayi baki"Nana tabawa Naja amsa tareda cewa hanan
" bismillah Hanan"
Hanan ta shiga dakin tareda fadin
"Thank you dear"
Kallo daya Hanan tayiwa Naja tafara kokarin tuna inda tasan fuskarta
Mamakine yadan kama Naja
"Wata tsirfa yaushe kuma ta canza suna zuwa Hanan,"
Basu kulataba, Nana takuma fita don kawowa Hanan abun tabawa
Naja se kallon Hanan take, kamar Jalila kamar ba itaba kuma Jalila dai ba wannan kayan tasakaba
Hanan ta kalleta
"Baiwar Allah banason yawan kallo, kalli gabanki Dan Allah"
Naja ta mata wani kallo
"Uban me zan kalla a jikinki, ina cewa akayi kinyi baki, meye kuma na zuwa ki zauna anan, dukda nasan baze wuce danginkune na arnan ba sukazo"
Hanan ta fuskanci Naja ta dauka Jalila ce
"Ba arna bane cocine sukazo da Kansu, ba arna ba, keba gara arna dakuba, nasan abunda baki saniba, kokuma kinsani amma kuke boyewa, ki kiyayeni "
Sallama Nana tayi da tray a hannunta ta doro ruwa da lemo se glass cup, ta ajiye a gaban Hanan
"Sannu da kokari" Hanan tai maganar cikin kasaita,
"Bakomai"
"Nana nakasa ganewa, waiba Jalila ba ce"
"Amma gaskiya Naja ba kya ganewa, to ba ita ba ce, abun mamaki ko, suna kama sosai"
Jalila ce ta shigo dakin, hanan ta kalleta
"Wai ina kika zauna kuka barni"
"Ina gurin Baba, ashema tafiya zeyi"?
" Eh zebi jirgin, Karfe 2 zeyi tafiya"
"Eh Su Yaya Abdallah sun tafi kaishi airport"
Nan suka zauna suka kama hira hada Nana, Hanan akwai saurin sakewa da mutane in taga dama, taita basu labarin yadda tayi missing Jalila, da kuma yadda suka cigaba da kawance ita da siyama, sunayi suna dariya
ita dai Naja kallonsu kawai take tana tabe baki ga mamakin maganganun Hanan sun cikata, to me take nufi? Ga kuma kamanin da taga sunayi da Jalila tanaso ta tambaya, amma tsakanin Jalila da Hanan bata San wadda tafi iya wulakanci ba.
Nana tace musu tana zuwa ta fita, ta Dan basu guri, yayinda Naja ta kame a dakin taki fita
Hanan ta kalli Jalila
"Queen kinsan wani abu kuwa"?
"A a sekin fada"
"Ina ganin Yaya Jawwad nagane shi yanada yawan fara'a"
"Ai Yaya Jawwad duk inda yake tauraro ne haskensa ne kawai yake bayyana shine,"
Murmushi sukayi gaba daya, Hanan takuma kallon Jalila, sannan tace
"Kuma kallo daya nayiwa Jalal nasan shine"
Da sauri Jalila ta kalleta
"Ya akayi kikasan Jalal, har kika ganeshi?"
"Hmm nasan komai,kin manta ranar dazaki taho kano keda Siyama kunyi zancensa, Dan haka Siyama na tambaya ta gayamin,"
"Hmm Siyama ko shine tagaya miki, bayan nace mata amana"
"To meye a ciki Dan ta gayamin, nida naganshi, he's looking so innocent"
"Waye din looking innocent? Amma ba Jalal ba"?
"Shidin Jalila, dukda na gaishesu be amsaba, kuma ban zauna da Shiva, amma yanayinsa miskilanci ma yana matukar damunsa"
Jalila ta tabe baki "tab wannan Jarababben"
"Trust me miskilanci yana damunsa, dakuma kadaici Jalila, yanayin yadda Siyama tabani labarin, akwai wani abu a boye game dashi, amma kafin mutafi zaki gane hakan,"
? "Mtseww gulmar banza, munafuncin yabar kan yan Gida harda ya'yan makota" inji Naja
"Kee!! Naga kanki yana wata rawa, this should be the last warning, har in bar gidan nan, kika kuma shiga harkata akwai matsala, Jalila ki gayamata bana bakunta, zanyi ba dai? ba"
Hannan tayi maganar tata cikin isa
"Hmm manta da ita nima tunda tazo nabawa banza ajiyarta, saboda gaba dayanata suffar karyace, da halin Jakuna,"
Bude baki Naja tayi
"Ni kikewa haka Jalila"?
"Wallahi kina kuma cewa tak, zan keta miki rashin mutunci, ba a shiga sabgata"
Mikewa Naja tayi ta bar dakin tana zage?dan taga inta zauna sesu daketa
Hanan ta dawo da kallonta ga Jalila
"Waike dama haka kike zaune a gidan nan ana miki wulakanci duk bakin naki, Tun dazu take wani zage? ta dauka kece"
"Manta da ita yau tazo, taketa wannan shirmen, abunda yasa ban biye mataba abunda yake damuna daban"
"Jalila wai wannan ba kanwar Sa'ada bace ba"?
"Eh kanwarta ce ina kika Santa"?
"Shedanu karuwan banza kawai"
Zare ido Jalila tayi
"Haba Hanan wannan wace irin maganace"?
"Eh ba karya nayiba, yayarta Sa'ada kawar murjace Yar autar su mommy su ukune, group dinsu
Da murja da Sa'ada da Hannah, school daya sukayi, tun daga makaranta suka lalace, duk ina ganin hotunansu a wayar ta, ba inda basa zuwa a Nigeria club? suke zuwa, gurin manyan masu kudi da yan siyasa, daga bayane sukayi fada da Hannah yanzu saura su biyu,"
"Na shigesu ni Jalila,"
"Karki kara yadda wata jaka tacewa danginku arna suma duk gayyar tsiyane, ita batasan nasantaba ai, ita kanta Sa ada bata sanniba amma ni duk nasansu, a wayar murja, manta dasu mucigaba da hirarmu"
Jalila rasa me zatace tayi, se mamakin abunda Hanan tafada ta keyi, Jalila ta nisa "naso ace hada Siyama kukazo, ina cikin damuwa, bata karasa maganar ba
Nana ta shigo da sallama, tacewa Jalila
"Jalila su Yaya Jawwad sun dawo, yakamata akai musu abinci"
"To bari in kaimusu"
Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi, tareda fadin "muje in rakaki"
Suna zuwa parlour Maama tana zaune, zata ci Abinci, seda ta Dan bude baki tana kallon Hanan da Jalila
Jalila tace "Hanan ga Maama"
Hanan ta danyi murmushi
"Mamansu Yaya Jawwad kenan"?
"Eh itace" daga tsaye Hanan tace Maama ina wuni
"Lafiya kalau ya hanya"
Maama ta amsa mata ba laifi da faraa a fuskarta saboda ta gaisa da baban Hanan, taga babban mutum ne me Iko
Daga nan Hanan tabi su Jalila har kitchen suka dakko kayan Abinci
Hanan ta kalli manyan kulolin sannan ta kalli Nana
"Ta saku wahala ko? Kalli wannan kayan a wani cikin za a zubasu"
"Wane irin wahala, a cikinku zaku zubasu"
Nana tabata amsa, sukayi dariya gaba dayansu
Suka kwashi kaya se part din Jawwad tunda suka shiga, Jalila taga yadda Jalal yake dariya se abun yabata mamaki, dama Jalal yana dariya kamar haka mutum kullum fuska kamar fuskar shanu ba fara a, amma yasamu Jawwad da Abdallah se dariya yake
Sukaje suka ajiye kayan Abincin, Jawwad yana tayi musu sannu
Hanan ta kalli Abdallah
"Yaya kalli wahalar da Queen tasa sukayi, kasan niba wani Abinci nake ciba lemo da biscuit ya isheni, kaikuma zaka iya zama bakaciba, tunda in katashi ci na mutum biyar kakeci lokaci daya"
Zare ido Abdallah yayi
"Ke hanan Dan sharri" Hanan ta kalli Jawwad
"Yaya Jawwad ba a zuwa da abokinka bakunta, kunyata mutane yake"
Dariya sukayi gaba daya ciki harda Jalal
Jawwad yace "kalli ikon Allah kamannin Ku har mamaki yake bani"
Abdallah yace "ba kai kadaiba farkon fara ganina dasu nikaina nayi mamaki, Inaga Allah ne yahadasu saboda kamanin dasu keyi"
"Eh amma nasha wuya ba"
Hanan ta fada tana shafa goshi
Jalila ta Dan girgiza kai "mhmm bari inje in dakko plates" ta juya ta fita, Nana ma guri ta nema ta zauna
Hanan ta Dan gyara zama ta waiga taga Jalila ta fita
"Hmm Yaya Abdallah kana Allah ne ya hadamu da Jalila amma nasha wuya,"
"Wuyar me kuma?" Nana ta tambayeta
hanan ta kwashe haduwarsu ta farko a school ta basu labari, Sannan tace
" Yaya Jawwad wallahi kanwarka kakkarfa ce mari daya nayi mata Dan mugunta tayimin biyu, Wanda kowane mari daya datayimin dai? yake da nawa uku, ai ban gama shiga hankalina ba, seda naga tayi wurgi dani Jini yana bin fuskata, na dago ina dubawa kowanj malaminne yazo rabamu yayimin haka, yai Jifa dani Ashe Queen ce"
Dariya suka kamayi sosai, Yadda Hanan tasaki Miki take zuba kai lace sun Dade tare, kuma tanayi ne Dan monitoring din action din da JALAL ze dingayi
Jalal yai murmushi sannan yace "ko y'ar gidan bullet ce"
Hanan ta danyi murmushi a ranta, tace hasashena yafara zama gaskiya
Abdallah yace "Jalal Ashe kaima kasan zancen"
Jalal ya nuna Jawwad
"a lokacin ya damu sosai, shi yagayamin"
"Nikam ban San labarin nan ba"
Nana tafada cikin dariya, Hanan takuma gyara zama sannan tace
"Yaya Jalal bakasan wani abuba, tacemin Yar gidan bullet, nazo da daddy ina shirin a casa queen, abun haushi wai Ashe yasanta kwana uku kafin hakan tafaru, Bayan anyi hakan ta dinga like min kaman chewngum kullum setazo inda nake muyi fada ina mata rashin mutunci amma batajin haushi"
Duk abun nan da Hanan ta keyi tana monitoring yanayin Jalal ne, Hanan ta danyi murmushi
"Se dai Queen duk inda taje kokuma Wanda yai tarayya da ita seyasamu wani benefits a tareda ita Wanda mutum baze mantaba, kamar daini ta saukemin rashin kunya, Dan tundaga ranar na nutsu Dan tanada luck a rayuwarta"
Jalila ta dawo takawo musu plates, abun yabata mamaki ita kuwa Hanan metake fada yasa hada Jalal a cikin masu dariya, Jalila ta kalli Nana
"Ku tashi mu tafi muci abincin muma"
Hanan ta kalleta, "Tab anan zamuci anayi ana hira, ni bani da yayye ko kanne a gidanmu masu debemin kewa nikadaice, Abdallah in ya fice koyakoma makaranta sena ganshi, yanzu ga dama ta samu nasamu Yayye" Jalila har mamakin wannan zakewa da Hanan tayi take
Jalila ta kalli Nana sannan ta kalli Hanan
"A gabannasu zamuci Abinci?"
"To meye a ciki ba yayyanmu bane, ko Nana"?
"Aikuwa dai Hanan, gaskiyarki"
"Gaskiya yau ranace ta mussaman Dan tayimin dadi"
Abdallah yafada yana murmushi
"Nima haka Abdallah, kobahakaba Jalal?"
Gyada kai Jalal yayi yana murmushi
Nana ta fara serving dinsu Abinci
Fried rice ce, da sos se simple salad ga juice nan na kwali da Wanda aka hada
Abdallah yace "Jalila meyasa Baku girka tuwo ba na masar miyar kuka"
"Kutmelesi wallahi da bazanciba"
Hanan tafada tana hararar Abdallah, JAWWAD yace
"Sha kuruminki Hanan Jalal ma da bazeciba, bayason miyar kuka"
"Hh Ashe makiya tuwon dayawa, me fadarma bayaci"
Nana tai maganar tana kallon Jawwad
Murmushi Jalal yayi, sannan yace "wani abu na tuna, Bros ka tuna lokacin da daddy yake kaimu Maiduguri, abamu biskin shinkafa da miyar kuka, Hajjo tace semunci"
Jawwad yayi dariya
"Allah sarki rayuwa, kokuma ta dumama tuwo tace shi zamuci, ka wuni da yunwa"
"Mu wuni dai, ai kaima bakaci"
Suka kuma kwashewa da dariya,
Hanan ta Dan taba Jalila sannan tai magana a hankali
"Jalila kin yadda da abunda nagaya miki game da Jalal,?"
Abdallah ya jefoma Hanan handkchief dinsa
"Kai Hanan kiji tsoron Allah me kike gayamata haka"
"Ina ruwanka sirrine"
Wayar Hanan ta fara ringing, ta mike zata fita ta amsa wayar, Jalila tace
"Kunyarmu akeji dabaza a amsa a gabanmuba"
"Allah ya kiyaye inji kunyarki, inma kunyarce kunyar Nana zanji itace sirikata"
Abdallah yace "ji Mara kunya to wa Nana zata baki"
"Idan ma Nana bata baniba nasan Yaya Jalal ze bani"
"Wa kikeso in baki"
Nana ta tambayeta
"Rabu dasu sirrine se mun kebe da Nana zan gayamata"
Tayi waje abunta
Tafito tana amsa waya turo gate din gidan akayi, yaseera da Ilham suka shigo
Kai tsaye suka nufi inda Hanan take

Share please
More comments more typing..........................



=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??

? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-?40

PART 1
Share please

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login