Showing 63001 words to 66000 words out of 129540 words

Chapter 22 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6677

daza a cika wasiyyar mahaifinki, zaki koma gurin wan mahaifinki, nima zanje ganawa dangin, munyi magana da Abba sati me zuwa insha Allah zezo ya tafi dake"
Ummi tayi maganar cikin kuka
"Gaskiya ummi ni ba inda zani ina tare dake, bazan iya zuwa wani guri in rayu ba tare da ke ba,"
"Am sorry baby wannan karon dole kiyi hakuri, nima zani inga iyayena, komawarki kano ba yana nufin mun rabu baneba"
"No ummi seda na rayu da soyayyarki for all this years lokaci daya acemin wai sena barki dama dagaske kike, ummi dama uwa zata iya Barin yarta?"
"Baby illa ne ga ratuwarki a matsayin ya mace ace kin girma an ta shi aurenki amma ace babu namiji tsayayye akanki, kiyi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa,
Zankoma ahalina kicigaba da zama a dangin mahaifinki ya aurar dake"
Kuka sosai Jalila ta dingayi ranar da take ta farinciki a gareta ta koma mata ta bakin ciki tayi kuka har ta gaji, haka nan yan kwanakin nan ta dinga yinsu ba kuzari se aikin kuka kawai ummi kuma se rarrashinta take tare dayi mata nasiha
"Baby duk inda kika samu kanki kizama me tsoron Allah, ki rike mutuncinki, kizama me tsoron Allah ki rike amanar tarbiyyar danayi miki, ina kaunarki baby nima ba a son raina hakan zata faru ba"
Ita dai Jalila jin ummi kawai takeyi
Saura kwana biyu tafiyar Jalila taje yiwa Siyama sallama sun sha kuka sosai Maman Siyama tai ta bata hakuri tayiwa Jalila alheri
Siyama ta tafi raka Jalila gidansu Hanan, Hanan rudewa tayi
"Jalila meyasa zaki tafi Zuwanmu Kaduna na kiyi abubuwa da yawa a gurin ki, meyasa zaki tafi bani da wata Yar uwa sama dake"
Duk yadda Jalila taso dakewa kasawa tayi suka dinga kuka Hanan tai musu jagora har gurin daddy, haka nan yaji ba dadi mussaman yadda yaga sunata kuka
Jalila tasoyi masa godiya kan alkhairan da ya dinga yimata amma kuka ya hanata nasiha yayi mata shima sannan yace insha Allah har kano zasu dinga kawo mata ziyara
Haka ta koma Gida ummi ta hada mata kayanta cif, data kalli kayan seta kuma fashewa da kuka
"Baby kukan nan ya isa haka, kirike abubuwan danake gaya miki, kizama me hakuri da rayuwa duk inda kika tsinci kanki, ki zauna da kowa lafiya, ki rikemin amanar kanki da tarbiyyar danayi miki,
Baby duk mijin da Allah yabaki ki masa biyayya, kiyi hakuri dashi"
"Ummi wai ya kikemin magana kamar me wasiyya"
Murmushi kawai ummi tayi tanaji a jikinta akwai wani abu daze faru da Jalila a kano amma ta dake taketa kokarin kwantar da hankalinta

To kome ze kasance in ummi ta koma garinsu?
Wace rayuwa Jalila zatayi a kano?
Ya makomar rayuwar Jalal?
Waye Jalal ?
Meze faru da Jalila zamanta a kano?
Meye alakar Jalila da Hanan da suke kama?
Tskanin Jeje dasu Ilham suwa ke nasara akan Jalal
Dama sauran tarin tambayoyinku Ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun amsoshinku
Daga alkalamin (daddy's girl)

Share please
More comments more typing...................

=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 29

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
Ummu hanif really enjoy u comments and prayers Allah yaraya mana hanif ya bar kauna =?
?=?
?=?
?

? ? ? ? ? ?? -my first Novel-

Tsayawa Jalila tayi daga inda take a tsakanin flowers tana kallon su Jawwad Ilham ce takarasa shigowa gidan
Su Jalal ke kokarin shiga mota Ilham ta danyi sauri ta je gabansu
"Yaya Jalal ina zaka ne?, inason zamuyi magana da kai"
Dama tunda tafara suspecting Jalila ke son Jalal ta dena kula Jawwad, yarasa me yayi mata

"Yaushe kika zama uwata dazaki ce kina son magana dani, kokuma yaushe kikazama ISP da kike tuhumata ina zani"
Jalal ya tamvayeta
Dan tabe baki tayi sannan tafara magana cikin shagwaba "two minutes kawai Dan Allah"
Bude mota yayi ya shige ya batta a gurin kaman gunki
Jawwad ne ya kalleshi, "haba bros Dan Allah fa tace, ka saurareta mana kasan mezata gaya maka"
"Indai wannan yarinyar ce babu wani abu me amfani dazata fada, komai nata daga shirme se hauka, bawani abun hankali a lamuranta"
Ya karasa shigewa motar ya kulle kofa ya batta a tsaye
Jalila daga inda take tana jin abunda suke cewa mamakine yacika Jalila tun wancan lokacin har yanzu Ilham ba ta dena son Jalal ba kuma har yanzu yana wulakanta ta amma tana manne dashi, tirkashi Allah kayi mana tsari da wahalalliyar soyayya dama wani mutumin arzikin ne takeso da da sauki amma Jalal wannan Dan wulakancin uban shaye?
Wayar da Jalila ta tabaji Ilham tayi a wancan zuwan nata ta tuna
"" ZANCIGABA DA HAKURI HAR LOKACIN DA BURINMU ZE CIKA AKAN JALAL DA MOMMYNSA""
Jalila bata manta ba wannan sune abunda taji Ilham tafada shekaru biyu dasuka wuce,
"Lallai akwai wani abu a kasa ba a banza Ilham take jure wannan wahalalliyar soyayya ba"
Ringing din wayarta ne ya fargar da ita daga dogon tunanin data tafi, lambar Siyama ce da sauri ta daga seda suka sha hira, takira Ummi ma suka gaisa sannan ta mike ta koma cikin Gida
Dakinsu ta nufa don aje wayarta tana shiga ta tarar da Ilham da Nana suna hira kuma dai ga dukkan alamu hirar akan Jalal ne, cikin dakin ta shiga tana fadin
"Juliet ta Romeo kokuma ince laila majnun, ya labarin soyayyar takune, domin labarin soyayyar nan akwai kayatarwa"
Jalila ta karasa maganar tana zama a gaban Ilham tareda yimata murmushi
Hade rai Ilham tayi kaman taga mutuwarta tareda tsurawa Jalila ido na wani lokaci, JALILA ma kallonta take kafin daga baya tace
"Manyan yan mata a cikin garin kano wannan kallon fa"
Wani mugun kishine ya tokarewa Ilham ganin Jalila takuma girma ta kara kyau, maganarta ma gwanin burgewa, Nana ce tai farat tace "Ilham Jalila fa ta dawo kano da zama, tabar garin Kaduna, anan zata cigaba da zama damu"
Ras!Ras!!Ra's!!! Ilham taji gabanta ya fadi
"Ta dawo kano da zama?"
"Eh mana munkara yawa"
Dagawa Ilham gira Jalila tayi
"Ko ba kya farinciki da zuwana in koma"
(Mhmm kaman ba Jalila data gama kuka akan zuwa kano ba kunga harta ware tafara sana ar Neman magana =??=? ?)
Wani matsiyacin kallo Ilham takewa Jalila aranta take fadin
"Lallai yarinyar nan muguwar Yar rainin hankali ce ga yadda take pretending kaman ba wani abu a ranta game da Jalal"
A zahiri kuma cewa Nana tayi
"Kinga mubar zancen nan mayi wataran, in mun sake haduwa"
Tai maganar tana yinkurin tashi tsaye riketa Jalila tayi
"No baza ayi hakaba ina lefin kice in baku guri, sha zamanki ai Jalila ba bakuwar zafi bace"
Jalila ta tashi tsaye ta bar musu dakin
Ta koma Kitchen tayi wanke? ta gyara kitchen din ta dawo parlour tana gyarawa, sallama akayi ta amsa wata budurwa ce wadda bata fi Sa arsu ba dauke da bagcco a hannu ta
amsawa Jalila tayi tareda yimata sannu da zuwa, yarinyar
Ta kalli Jalila tace "ina mutan gidan ne?"
"Suna ciki wani abunne?"
Jalila ta tambayeta
"A a dama dawowa nayi"
"Kokece Halima"
"Eh nice"
"Allah sarki sannu da zuwa karasa suna ciki"
"To nagode"
Dakinta halima ta nufa taje ta aje kayanta ta fito domin fara aikace? taga kusan an gama komai
Jalila ta kalleta "kije ki huta mana dagani kinyo tafiya"
"A a kaida ba Hutu kazo ba ina batun Hutu"
"Jikin Dan Adam yana bukatar hutu, ni nagama komai na dauke miki aikin yau"
Suna cikin haka Nana ta fito ita da Ilham, Nana ce ta kalli halima "sarkin biki, suna, ko mutuwa, se yau kinje kinyi zamanki a kauye ko"
"Wallahi bahaka bane Nana ni dince na danyi jinya"
"Haka dai kika iya kin barni aikin Gida kaman ya kasheni"
"Kai Nana Dan Allah wani irin aiki kaman ya kasheki ina aikin anan"
Jalila tafada tana hararan Nana
"Kenima wallahi in Yar aikin mummy ta tafi bana iya wannan wahalan tuni nake sawa a sallamesu a canza wata bana son shirme"
Ilham tayi maganar tanayiwa Halima kallon banza
Jalila kuwa kwashewa tayi da dariya a ranta tace kaga Yar masu Gida hada sawa a kori me aikin a fili kuwa cewa tayi
"Halima kyalesu na dauke miki aikin yau jeki sha zamanki"
? "Mtseww shirme kawai"
Inji Ilham, "nice ma ke, akan shirme" Jalila ta bata amsa
"Enough please narasa wannan rashin jituwa a tsakaninku, Ku indai zaku hadu sekunyi fada, wuce muje"
Nana tafada tana tura Ilham
"Muje zuwa zangane abinda kike kullawa ne Ilham narasa inda kika dosa,"
Jalila tayi maganar a zuciyarta ta nufi dakin maama, da sallama ta shiga Maama ta amsa mata da kyar amma dayake Jalila ta iya siyasa se ta nuna kaman bata San abinda Maama take mata ba, ta karasa kusa da ita ta zauna "Hajiya Maama hutawa kike? Me za a dafa miki yau"
"Kinga ban saki ba balle Abbansu Jawwad yace daga zuwaanki an fara takura miki"
"Haba Maama wani irin takura, aikin Gida ai dolene ga ya mace ba batun takura"
"Kinga ga kitchen din nan jeki abinda kika gadama"
Maama ta karasa maganar cikin kosawa"
Mikewa Jalila tayi ta fito ta bata guri, ta nufi kitchen, ta tarar da halima tana kokarin dora abinci tare sukayi komai da Jalila sukayi girkin suka gama suka gyara kitchen din Jalila tanayiwa Halima gyare? a wasu abubuwan
Yayinda Nana tana daki a kwance tana chatting Jalila ce ta shigo ta sameta "Nana gaskiya mijinki ze sha fama"
Dan kallonta Nana tayi
"Kaman ya?" "Kallifa tunda garin Allah ya waye daga chatting se bacci haba Nanancy gaba fa akeji ba yanzu ba"
"Jalila kenan in Allah ya nufi ka huta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kawai ka huta, kema ke kikasa kanki, wannan wahalar shikenan mutum baze huta ba"
"To naji tashi ki kaiwa Yaya Jawwad Abincinsa, in munyi salla se muci namu"
"Ba inda zani, in yanason ci in sun dawo daga yawon yazo ya dauka"
"Kai Nana Yaya Jawwad din?"
"Eh shidin, ina zuwa ze fara Sani aiki yana min masifa, bakiyi kazaba, wannan ba dai? bane, ga Yaya Jalal ma yaitawa mutum wani gani? mistake kadan seyace bazeci abincin ba, kuma in beciba Yaya Jawwad ma baze Ciba, shiyasa Halima ce take kaimasa itama haliman in basu gadama ba in ta kai bazasu Ciba, Yaya Jalal yafi kowa wannan tsirfan, kokuma yanzu susaki dafa wani abincin, shiyasa ko yazo ya dauka da kansa,ko halima ta kaimusu, bana son wahala"
"Tabdijan indai Yaya Jawwad ne meye a ciki se in masa amma Jalal kam yayikadan"
Dariya sosai Nana tayi,
"Tab cakwakiya Ashe kuwa zakuiyi fada da Yaya Jawwad"
"Ke ni bari in wanka in yazo se ya shigo ya dauka,abincin"
"Kin temaki kanki kema seki huta"
? ? Se bayan sallar la'asar sannan su Jawwad suka dawo ko ina sukaje? Oho nima bansaniba Jalila tana tareda halima sunata hira, Jalila ta sha mamaki da halima tace mata ta taba aure amma tasha wahala gashi auren dole akayi mata, tanata bata labarin kauye
Yaya Jawwad ne ya shigo ya tarar dasu a parlour, cikin grimamawa halima ta gaida Jawwad ya amsa mata a mutunce sannan ya kalli Jalila
"Baby mun dawo, atemaki cikin gayu, munajin yunwa"
"To babban Yaya yanzu kuwa bari in kai"
"God bless you my sister"
"Ameen Yaya Jawwad"
"Bari in shiga in duba Maama"
"To Yaya a fito lafiya"
Ta mike ta nufi kitchen ta shirya kayan abincin akan tray ta dauka tayi hanyar waje
A kashingide ya tarar da Maama tana waya Dan haka yajira ta gama sannan ya Dan dubeta
"Maama mun dawo"
"To sannunku, ina fatan komai lafiya?"
"Komai normal Maama, kayan ma suna boot"
"To shikenan Bari zan tura Nana ta kai musu"
"To shikenan Maama nasa JALILA ta kaimana abinci mun debo yunwa"
Yafada yana mikewa
"Yawwa dawo ka zauna zamuyi magana"
Guri ya nema ya zauna ya bata attention dinsa
"Ba kaga yarinyar nan ta dawo gidan nan ba, bana son shishshige mata daka keyi, wannan rawar kan da kake akanta kana wani janta a jiki duk banaso, ga Yar uwaka nan cikinku daya ta isheka bana son yayime? da cusa kai kanajina ko?"
Mamakine ya cika Jawwad wai Jalila ce yayime? Allah sarki Jalila itama Yar uwassu ce ai suke nan ba yawane dasu ba amma meyasa Maama har yanzu batason alakar my da Jalila, ya numfasa sannan yace
"To Maama za ayi yadda kika ce, insha Allah za a kiyaye"
"Gara dai itama Nana zan mata magana naga zakewar taku tayi yawa, Tashi kabani guri" mikewa yayi ya fito, jikinsa a sanyaye

Jalila ta kai Abinci part din Jawwad kaman dazu yanzuma Jalal yana nan amma bata kulashi ba be kulata ba ta ajiye zata fita, taga wani key holder akan center table da keys na mota a jiki dakuma wasu keys din, key holder din yayi kyau wani Dan Teddy ne a jiki me kyau, kai tsaye Jalila taje ta Sa hannu ta dauka, ta jujjuya shi yayi mata kyau sosai, tafara kokarin cire teddyn jiki, ita a tunaninta na Jawwad ne, Jalal ne yake satar kallonta yaga ikon Allah, seda ta cireshi tsaf daga jiki, tabar keys din haka ta mayar kan center table din ta ajiye, ta dau Dan Teddy zata fito Jawwad ne ya shigo dakin jikinsa a sanyaye sakamakon maganganun da Maama tayi masa
"Kinkawo abincinne"?
"Eh na kawo gashi can"
"Mungode sosai"
Murmushi yayi, hannunta ya kalla, yaga abin key holder din Jalal,
"Baby waya baki wannan"?
"Yaya sonake a jikin keys dinka naganshi"
"To wayace miki nawane?"
"To ai duk abunda yake dakin nan nakane"
"Dagaske"?
" eh mana duk abunda ya shigo cikin dakin nan yazama Naka"
Dariya Jawwad yayi "to na oga ne dafatan kin tambayeshi kafin ki dauka"?
Dan zaro ido Jalila tayi
" waiwa kake nufi"
Da ido ya nuna mata Jalal, Dan bude baki tayi
"Ni cirewa kawai nayi, na dauka nakane"
Kwaikwayonta Jawwad yayi
"Eyya na Yaya Jalal ne a tambaye shi tukuna"
Jalal yana jinsu yayi musu banza ya sakko ya fara kokarin zuba abincinsa salad din data hada ya bude tayi masa wani decoration yayi kyau sosai,, maida hankali yayi yafara zuba abincinsa
"Jeki tambayeshi mana?"
Jawwad ya maimaita, noke kafada tayi,
"Meyasa bazaki tambayeshi ba"
Dan tura baki tayi "ai nakane"
Jawwad ne yadan kalli Jalal yaga shi ta abinci yake, Jalila? ta shammaci Jawwad tayi waje abunta da Dan Teddy a hannunta
A parlour ta tarar da Maama tana lissafawa Nana Atamfofi da less
"Yawwa Jalila zomuje tare, kayan nan zan kaiwa mommy Jalal"
"To shikenan Ku gama kirgawa"
Akagama kirgawa suka zuba a manyan leda suka dauka suka nufi gidansu Jalal
Shigarsu yayi dai? da fitowar Mummy daga part dinta, Dan bude baki mummy tayi, "yan mata saukar yaushe?"
Durkusawa Jalila tayi ta gaisheta ta amsa da fara a "kinzo mana Hutu kenan""
Nana tai farat tace"a a mummy ta dawo nan gaba daya"
"Masha Allah hakan yayi kyau, ya Maman naki?"
"Lafiya kalau ta bata amsa"
"Masha Allah toku shigo ciki mana"
suka shiga cikin parlour shima yasha gyara kaman parlour amarya,
kayan suka zube agabanta, dubawa ta shigayi dayake suna business sosai tsakaninsu da Maama
"Kai amma lesses din nan sunyi kyau, kafin akaisu bari Ilham tazo ta zaba, Jalila Dan kirawo Ilham tana dakin ta "
Ba musu JALILA ta tashi ta tafi dakin Ilham, tayi ruf da ciki tana jin music a wayarta, duk tasaka Bluetooth a kunnenta, tana bin wakar a hankali, tayi ruf da ciki tabada attention dinta akan waya shiyasa bataji shigowar Jalila ba
Bakin gadon Jalila ta karasa ta Dan leka wayar Ilham, hotunan Jalal, takewa wannan kallon kurillan,
Jinjina kai Jalila tayi tareda furta
"Yar wahala, kina nan kina shirme yana can yana shagalinsa"
Hannu Jalila ta kai ta girgizata
"To uwar soyayya kije ana kiranki"
Dan dagowa Ilham tayi ta kalleta a wulakance, jitayi kamar hannun Jalila na kamshin turaren Jalal zumbur ta mike tana kallon Jalila
"Meye haka? Kin shigomin ba sallama"
"Kina can kina ibadar dababu lada taya zakisan nazo"
Hannun Jalila ta kalla taga teddyn jikin key holder din Jalal
Kwalalo ido Ilham tayi ta kai hannu kan abun tareda fadin
"Wayabaki wannan aina Jalal ne"
"Kamarya waya bani? Dan na Jalal ne kuma shi kadai akayiwa? Kinji mace kinga ni cewa akayi kawai nakiraki"
"Inba nasa bane ya akai naji kamshinsa, kamshin turaren Jalal ne a jiki fa, kuma tabbas nasane"
"Au Jalal din har wani kamshi yake na daban, banda warin hayaki meyakeyi, kullum cikin zukar hayakin taba har wani kanshi yake"
Mikewa Ilham tayi tsaye tana kallon Jalila sannan ta nunata da yatsa
"Naga wannan karon kin karo wulakanci, kuma wallahi bazan saurara miki ba koni ko ke, tuntuni nagane take? ki, se yanzu nagane inda kika dosa, am ready for you"

Share please
More comments more typing..........................
Love you all my fans really appreciate your comments and prayers
d'd'd'd'


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-?30

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

? ? ? ? ? -MY FIRST NOVEL-

Yatsan da Ilham ta nuna Jalila dashi, Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Ilham
"Dukda Ban gane inda kalamanki suka dosaba, banga abunda nayi miki kike tada jijiyoyin wuya hakaba, sedai bansaniba ko kema Jalal yafara baki giyar saboda naga alama daga wannan maganganun naki, yanzu dai kije matar gidan tana kiranki"
Jalila na zuwa nan a zancenta tasaki hannun Ilham, tayi waje abunta
"Ina Ilham din?"
Mummy ta tambaya "nagaya mata amma naga kaman batajin dadine amma nagaya mata"
"Bata jin dadi kuma? "Meyasameta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login