Showing 96001 words to 99000 words out of 129540 words

Chapter 33 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6668

yace
"Wannan matar bata da hankaline? Kokuma bataje Islamiyya ba, ita Jaleeelan shashashar inace ta tsaya, aka dinga zagin mahaifiyarta, Uwa tafi Uwane?"
Jalal yai maganar a hasale
"No Jawwad, nasan Jalila kara take mana amma tabbas da a wajene, bazata yaddaba, ni nasan hakan"
"Ba wata kara Jawwad kadinga gayawa yayar mahaifiyarka gaskiya, dan tana zaune a gidanku bekamata a dinga cin zarafinta ba, koni nan"
Ya nuna kirjinsa,
"koni bazan bari wani banza a gari yazagarmin uwaba, dukda abjnda ke tsakanina da mahaifiyata ba, me yasa za a dinga dawo da abunda ya riga ya wuce?"
"Haba Jalal ya kakeso inyine nayi kokarin nusar da ita amma itada Maama sun rufeni da fada"
"Mmm ba yadda zakayi, amma Jawwad mahaifiyar Jalila, Mutum ce, ba abar yarwa bace agurinmu, be kamata a ci zarafinta a gabanmu ba"
"Nasani Jalal, amma ka fahimceni, ba yadda na iya ne, nasani kowaye akayiwa haka baze Ji dadiba, Ina iyajin pain din da Jalila takeji amma ba yadda na iya, da nayi tunanin ko Abba zan gayawa, amma hakan ba mafita bane, ze kuma haddasa fitinane kawai"
"to wai ma tukuna zuwa kayi kace musu kana sonta"
Kallon Jalal yayi
"Jalal koban fada ba shakuwar dake tsakanina da Jalila, bata y'an uwanta bace kawai, Jalal ni son Jalila nakeyi dagaske aurenta nakesonyi"
Wani dogon tsaki Jalal yayi
"Wannan yarinyar mara kunya ita zaka aura, lallai kaci kai,"
"kaman ya naci kai? Meye aibunta?
"Babu kam, bayanma bata da kunya ka aurarwa Ummi yarta, wannan matar tazo tana zagin mata mahaifiya, ni danta wannan yarinyar komeyema akmata ban damu ba, amma cin zarafin Mace kaman Ummi be kamata ba, bekamata a cigaba da wulakanta taba saboda kanason yarta ba" Jawwad ya dan gyara zama sannan yace
"Jalal ina fatan komai ze daidaita insha Allah, amma ina son Jalila, so bana wasa ba"
"to shikenan Allah ya kyauta"
? Cikin gida kuwa Jalila tayi kuka, har ta gaji, Nana taibata hakuri, se ajiyar zuciya Jalila take, Nana ta tashi ta tafi palour domin dakkowa Jalila ruwa, tana zuwa itama Yaya mairo tafara saukemata n????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ata fadan, itakuwa Nana ta hade rai tana kunkuni
Jalila tana Cikin kukanne ummi ta kirata a waya, ta dinga kallon screen din har wayar ta katse, kuma kira ummi tayi amma wannan karon se ta Kai hannu ta daga
Ta tattaro nutsuwarta, suka gaisa da ummi
"lafiya kuwa naji muryarki kaman kina kuka"
"lafiya kalau Ummi banajin dadiine"
"meyasame ki?"
"Ummi ciwon marane fa kawai"
"Hmm Allah ya sawwake" tafada ba dan ta yaddaba"
Kaman an tsikari Jalila tace
"ummi yaushe zakije garin naku dan Allah ummi kije ki dawo, in dawo gurinki"
"akwai matsala kenan?"
"ummi ta tambayeta
" ba wani matsala ni dai kawai sonake kije ki dawo, bazan iya rayuwa ba kya kusadaniba, sannan na kagu inga yan uwanki ummk, "
Jikin Ummi yayi sanyi tasan akwai matsala ne take kokarin boye mata,
" Baby wayace miki idannaje dawowa zanyi? Bazan kuma dawowa ba nima a cikin ahalina zan zauna"
"haba ummi karkiyimin haka mana, wallahi ko ina kika tafi sena biyoki, bazan iya rayuwa babu ke a kusa daniba"
Ta karashe maganar tareda fashewa da Kuka, dama kukan take ta boyene dan kar ummi tagane
"is ok my dear, ina nan zuwa jibi Insha Allah, a satin nan zanje gida Nima kidena kukan haka"
Ummi taita rarrashinta, sukayi sallama
Wunin ranar Jalila a daki tayishi tana kuka, gashi ko abinci bataciba, Nana tayi juyin duniya akan Jalila taci abinci amma taki ci, haka take ma a bangaren Jawwad shi yayi breakfast amma bayan nan beci komai,
Jalal ya kalleshi
"kai nifa yunwa nakeji, kaje kace ta kawo mana abinci"
Jawwad ya kalleshi
"wakenan?"
"kafini sani ai, ni yunwa nakeji"
"haba Jalal nagaya maka halin da take ciki, ya za ayi ta wani dafa abinci"?
"Ina ruwana da halin da take ciki? Halin da cikina yake ciki ne ya dameni,"
Jawwad ya kalleshi
"toni na damu da halin da take ciki, ina ji a jikina har yanzu kuka take"
"Ko? Da gaske ka damu,? Aini ban saniba, tunda banga kana kukan ba kaima, sharokhan sarkin soyayya, kagani ka tashi kasamomin abinci"
Wani mugun kallo Jawwad yayi masa, ya tashi yashige bedroom ya bar Jalal a palour
Jalal yai murmushi ya girgiza kai
? Bayan la'asar Maama ta kira Nana tasata a gaba suka fita, tareda Yaya mairo, sannan ta aiki Halima, akabar Jalila a gida,
Jawwad yaji karar motar Maama ya leka ta window palournsa yaga fitar Maama da Nana da Yaya mairo, Jalal ya uzzurawa Jawwad se ya tashi ya rakashi cin abinci, dan baze bari yjnwa tayi masa illa ba Badan Jawwad yanasoba ya tashi suka fita,
Fitarsu Nana, hakan yabawa Jalila damar yin kukanta yannda take so
Tabbas da watace ta gaya mata abunda aka gayamata yau a cikin gidan nan to da setayiwa Yaya mairo rashin mutuncin da harta mutu baza akuma yimata makamancinsa ba
Amma kash koba komai yakamata tayi al kunya ko dansu Jawwad, ga nasihar umminta data dingayi mata akan tayi hakuri dazaman da zatayi da mutane, gajiya tayi da zaman cikin gidan, zuciyarta na ayyana mata abubuwa, tasan tunda aka fara haka, lallai Maama zata dau shawarar cigaba da cuzgunamata, kuma yau da gobe se Allah dan wataran zata iya marin mace akan taba mata uwa.
Tashi tayi ta fito harabar gidan, zuciyarta na saka mata abubuwa dayawa
Ilham ce ta shigo gidan, ta hangi Jalila tsaye a wajen kofar shiga cikin gidan, ta nade hannuwa tayi shiru alamun tana tunanin wani abune,
Zuwa tayi zata wuce amma Jalila na tsaye a bakin kofar bata fito ba bata shigeba,
Seda su Jalal suka je karshen layi, sannan ya tuna yabar wayarsa, yace Jawwad yayi parking ya jirashi yaje ya dakko baxe dade ba, Jawwad yayi parking, Jalal ya sakko ya tafi.

Ilham ta karasa inda Jalila ke tsaye
"Zan wuce" Ilham ta fada tana kallon Jalila
"basa nan masu gidan, ki koma inda kika fito" Jalila ta fada a takaice
"ke bana son shirme, ba gurinki nazo ba ai"
"Nasan ba gurina kikazoba, bazaki shiga bane kawai tunda ba kya ganewa nace miki ba sa nan"
A tsawace Ilham tace
"Ke dakata Malama, karki gayamin magana mana, da kikemin wannan gadarar, aiba gidan ubanki bane, dan nasan ubanki ko taku daya bashi dashi a gidan nan" aikuwa Jalila tayi niyyar sauke fushinta akan Ilham, takuma kallon Ilham
"Ke daga inda kike gidan naki ubanne ai, saboda tsabar arzkin ubannaki shiyasa naga yabarki kina ragaita tsakanin gidan yan uwa, saboda kwadayi"
"Hmm Aida tuni gidan ubanane, wasu dalilai suka hana faruwar hakan, amma wataran dukiyar da kike magana zatazama mallakina"
Kallonta Jalila tayi baki bude
"A matsayinki nawa, dukiyar uban wani zata zama taki kwadayayyiya, aje ai takama da dukiyar uba, bata uban waniba, malama kijuya inda kika fito,
" Karki gayamin maganar banza malama, kodamene ubana yafi ubanki, tunda nasan kowa kika tambaya ze gaya miki inada Uba, amma ke wayasan naki uban
Wani wawan Mari Jalila ta saukewa Ilham batare data bari Ilham tagama maganar ba
" Karki kuma dukanmin kanwa, inkika kuma sena rama mata"Muryar Jalal ce, suka waiga gaba daya

Share please
More Comments More Typing.............................

Love u all my Fans
Ina me baku hakuri bazan cigaba da posting kullum ba, saboda zankoma online lectures, amma zan cigaba da kokarin cigaba dayi muku posting nagode sosai




=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/13, 10:27 PM] +234 816 830 7871:
? ? _ABDUL? JALAL_

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 43
PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane
Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa

? ? ?? _My first novel_

Jalala ya karaso inda suke, ya kalli Jalila, "kina kuma marinta kema sena mareki, mara kunyar kawai, Ilham sa'arki ce?"
Wani banzan kallo Jalila tayi masa
"Ilham din banza Ilham din wofi, wallahi ta kuma zagina sena kuma wankamata mari dama Jakace kaima kasaba jibgarta, sha3 Karya banza
Mamakine ya cika Ilham wai ita yake tarewa fada, kallon Jalila tayi
" Kece babbar karya baniba"
Jalila tace "kinga karnuka nan" ta nuna Ilham da Jalal,
Ilham tace "Nida yaya Jalal dinne karnuka"
Tsaki Jalila tayi, ta shige ciki, ta hankado kofa, Ilham ta kalli Jalal
Zatayi magana kawai yai tafiyarsa, yabar gurin dama dan ya kuma kunna Jalila yayi, ba nufinsa ya shigarwa Ilham ba, suka batta a tsaye baki bude
"to me suke nufi da hakan?"
Babu me bata amasa dan haka ta juya ta koma gida, se bayan sallar isha'i sannan su Nana suka dawo, Nana tai tabawa Jalila hakuri akan sun tafi sun barta ita kadak, Jalila ta nuna mata bata damu ba, tun ranar da Yaya mairo tazo tayi wannan cin mutuncin Jalila bata kuma bari sun hadu da Jawwad ba, ya damu sosai ko wayarta inya kira bata dagawa, ko palourn ma ta dena fitowa se dai ta zauna a daki,
??
?? Yau ta tashi da murnar ummi zatazo, amma haryanzu ba saki jikinta ba abunda su Yaya mairo sukayi mata yana taba mata zuciya, sannan idan ta tuna ummi tafiya zatayi ta barta a gidan, setaji ba dadi,
Nana da halima ne sukayi wa Jalila kara sukayi girki domin tarbar ummin Jalila, amma ita kam ko san fitowa batayi, seda Abba yasa aka kirata ya tambayeta ko akwai matsala kwana biyu baya ganin gilmawarta, amma tace masa ba komai, Jawwad ma yayi sintiri a cikin gidan amma baya samun ganin ta, gashi yana tsoron yaje dakinsu Jalilan, saboda Maama, in yakira Nana yace tabata wayar se taki karba, Jawwad ya damu sosai
Karfe sha biyun rana ummi ta iso gidan, Jalila kaman ta shige cikin ummi dan farin ciki, tayi murna matuka, Abba yana gidan saboda zuwanta, Maama dai ba yabo ba fallasa ta tarbeta saboda idon Abba, Jawwad ya shigo domin gaida ummi, se lokacin yaga Jalila, ta dan fada idonta yayi zuru2 tana manne? a jikin ummi, tausayinsune yakama shi, suka gaisa da ummi, daga nan ya shantake akayi ta hira, ya tashi ze fita ya waigo ya kalli Jalila yace
"Jalila, dan Allah kawomin coffee"
Abba yace
"Yayana kafiye takura, tana zaune tana jin dumin ummin zaka sakata aiki, murmushi Jawwad yayi yana dan sosa keya, Maama kam wani mugun harara tayi masa, suna hada ido da Maama ya sunkuyar da kansa kasa, ummi kuma tace
" Ai ba wani takura dan yasata aiki, ai kanwarsa ce, tashi ki kaimasa"
Jalila ba dan tasoba ta mike taje ta hado masa, ta fita domin kai masa, Maama a ranta tace "lallai Yaron nan, wato beji maganar da mukayi masa ba kenan?, aikuwa sena saba masa"
Jalila tana kaimasa, ta ajiye ta juyo zata fice Jawwad ya kira sunanta
"Jalila" cak ta tsaya amma taki yadda ta kalleshi,
Tasowa yayi yazo gabanta ya tsaya, suna iya jin numfashin juna, muryarsa a sanyaye yace, "Baby menayi miki na cancanci wannan hukuncin? Kin kauracewa ganina, tsawon kwana biyu, kinki daga wayata, kinsani cikin damuwa, Baby why?"
Dan dagowa tayi ta kalleshi, idonta sun ciko taf da hawaye, ta sunkuyar da kai, kallonta yayi ya kuma sassauta muryarsa
"Ohhh no Baby, nagane, Jalila you are not suffering alone, i also feels what you feel, Baby dan Allah kiyi hakuri akan abunda akayi miki, kar hakan yasa ki kuma, kauracemin kwana biyun nan na shiga damuwa, sannan kidena zubar da hawayen nan, banaso, kuma in Ummi, taganki cikin damuwa bazata ji dadi ba"
Gaba daya jiknta yayi sanyi, duk yabata tausayi, ta gyada masa kai alamun ta gamsu da maganarsa
"Kindena kukan?"
Ta gyada masa kai, ya ciro handkechief a aljihunsa yabata, ta goge hawayen da yake idonta, ta mika masa, sannan ta fito, ta koma cikin gida,
Ta tarar ummi tana cin abinci, spoon ta dauka tazo ta zauna, suna ci da Ummi,
Zuciyar Ummi fal tausayin Jalila, akwai abunda yake damunta, amma taki fada mata,
Nana ta fito taga Jalila da ummi suna cin abinci tare, ta kalli Jalila
"Wato dan ummi tazo shine, yau bazaki ci abinci dani ba?"
Dan murmushi Jalila tayi, wanda iyakacinsa lebenta
"Ni na isa, Nana"
"gashi nan makuwa nagani"
Ummi ta kallesu tana murmushi
"kema dakko spoon dinki, kizo muci"
Haka kuwa akayi, suka zauna suna cin abincin tare
Ummi tagayawa Abba, kwana daya zatayi, ta wuce,
Maama ta shige daki ta kira Naana, ta hanata fiyowa, karshe ma ta aiketa tabar gidan, ta bar Ummi se Jalila da Halima, dakinsu Jalila taja Ummi, ta dinga mata magiya ta tafi da ita, amma Ummi tace mata baze yiwuba, Yanayin yadda taga Maama ta karbeta, tasan akwai matsala amma Jalila tace komai lafiya kalau suke zaune
Haka Jalila sukai ta hira da Ummi wanda hakan ya rage mata bacin ran da take ciki ,
Rabin hirarsu da Ummi, Nasiha ce take mata akan hakuri da karbar kaddara a duk lokacin datazo mata,
Da dare yayi ma Maama cewa tayi Nana ta kwana a dakinta, tabar musu can, dan bazata kwana a gurinsuba bata san me za a koyamata ba.
? Washegari tunda safe Ummi tafara shirin tafiya, tun wayewar garin Jalila take kuka, ko karyawa takiyi, karfe goma na safe, Ummi tagama shirinta tsaf ta fito, Jalila janye da trolley din Ummi tana share hawaye, Nana kuma ta dakko karamin jakar Ummu, hakan yayi dai2? da fitowar Abba wanda shi zeje yasa Ummj a motar garinsu, Abba yace a kirawo Maama suyi sallama da Ummi, Maama ba dan tasoba ta fito, sedan kar Abba yayi mata fada,
Abba ya kalli Jalila yace "Baby muje, asaka kayan a mota" Jalila tayi gaba ita da Nana, ya bisu a baya, suna zuwa harabar Gidan, suka tarar da Jawwad ya kunna motar ya bude kofofin, suna zuwa yaje ya karbi trolley din hannun Jalila yana kokarin bude boot
? Ummi ta kalli Maama da take tayi mata kallon banza, ta danyi murmushi sannan tace
"Zainab har yanzu ina ganin kiyayyata a idonki, bansan dalilin hakan ba, amma ina rokonki ga Jalila nan amana, kar kiyayyata ta shafeta, ki dubi Allah ki dubi maraicinta, in kikaci amana Allah yana kallonki, badan wasiyyar mahaifinta ba Zainab, babu abunda zesa in bar yata a gidanki, tunda nasan ba kya kaunarta, keda danginki, da da ita zan tafi, ko ina ne" Maama ta katseta ta hanyar cewa
"kinga saurara, amanar yarki a hannun dan uwan mijinki take baniba, dan ba muhada dangin komai dake ba, ni ban hada jini da arna ba balle abani amanarsu in karba"
Murmushi Ummi tayi me ciwo sannan tace"shikenan Zainab ki fadi abunda kikeso, kema kin haifa, bazan fasa fada ba Jalila amana ce, zan iya yafe duk abunda zakiyi min amma banda cin amanar gudan jinin Aliyu, wato Jalila " Ummi na zuwa nan a zancenta tayi waje tana share hawaye, tareda tausayin tilon Babyn ta.
Harabar gidan ta fito, suka koma gefe, da Abba suna magana, Jalal ne ya shigo gidan, ya hangi Ummi yana ganinta ya karaso da sauri yana murmushi, yace
" Ummi saukar yaushe"?
"Abdul Jalal haka ka girma, Jalal ka yadani, ka manta dani"
Ya dan girgiza kai
"ummi wane ni in manta dake ni na isa, yanzu kikazo ne?"
"A a tafiya zanyi, tun jiya nazo"
Kallon Jawwad yayi, sannan ya kalli Ummi
"Ummi Jawwad be gayamin ba danazo mun gais, yaushe rabon da naganki"
Abba yace "Lallai Jawwad baka kyauta ba tunda baka gaya masa ba"
Jawwad yace "Abba ba laifina bane jiya throughout ban ganshiba, ban san inda ya tafiba"
"amma lambar wayata ma baka ganta ba itama ta tafi yawon"
Jawwad yayi dariya
"Allah yabaka hakuri"
Jalila mamaki takeyi yadda ya ke girmama Umminta haka, yasan Ummi kenan, amma ranan datayi mata zancen waye JALAL tace mata bata saniba
Ummi tace "Abdul Jalal ina Mummynka?"
"tana nan Ummi, yanzu nan ta fita", daddy kuma baya gari,"
Ummi tace Allah sarki, dan Allah a gaishesu
" zasuji Insha Allah Jmmi"
Jalal ya kalli Abba yace "Abba ka bari, semu rakata"
Abba yace masa "ai ba kano zata koma ba, tasha zasu kaita, zataje garinsu"
"Ba komai Abba, bari mu kaita"
"to shikenan yarona, karbi mukullin"
Jalal yasa hannu ya karba,
Seda Jalila ta zare ido, ko dai Abba besan irin tukin da Jalal yake ba, yabashi mukullin motarsa
Abba suka gama maganar dazasuyi da Ummi, Jalila da Nana suka shiga bayan motar, sannan Ummi ta shiga,
Jawwad kuma ya zauna a gaban mota, sekuma Jalal da zeyi tuki
Suna tafe Jalila tana kuka, Nana, da Jawwad suna rarrashinta yayinda Ummi ta maida hankalinta kan JALAL sunata hirarsu, bawai dan batajin kukan Jalila ba sedai kar garin rarrashinta itama tayi kukan,
Ummi tace "Jalal ya karatu fa?"
Yace"Ummi kicigaba da yimin addu'a, very soon zakiji labari me dadi"
"to Allah ya tabbatar da alkhairi, yabaku mataye nagari kuyi aure"
Dariya Jalal yayi "Aure kuma Ummi"
"Eh mana Jalal, aure ai shine cikat mutum"
"ko ba hakaba Jawwad"
"hakane Ummi"
Jalal yai murmushi, tareda dan girgiza kai,
Haka suka cigaba da tafiya, har suka je tasha, Jalal hira suke da Ummi, aka samawa Ummi mota, suka saimata ticket, Rirriketa Jalila tayi tana kuka,
"Ummi dan Allah kidawo da wuri, karki tafi ki zauna Ummi"
Ummi ta dan goge kwalla tana dan dukan bayan Jalila, alamun rarrashi, sannan ta kalli su Jawwad
"ga sister dinku nan, asaka ido akanta, kuyi hakuri da halayenta, dan Allah,"
Nana tai saurin cewa "Ummi karki damu, Jalila bata da wani damuwa, lafiya kalau muke zaune"
Jawwad ma yace "ummi karki damu shagwaba nsme kawai takeji, shiyasa take kuka, amma ba wani damuwa," murmushi Ummi tayi sannan ta dago Jalila tace
"Baby na is ok, bazan dadeba zan dawo insha Allah, zamu dinga waya, Baby kiyi hakuri da rayuwa, sannan kizama me hakuri da kaddararki, kizama me yafiya da kauda kai, akan al amuran rayuwa, banda tsokana da neman magana duk abunda yasameki kiyi tawwakali ga Allah kinji baby"
Gyada mata kai Jalila tayi
"Yawwa Allah yayi muku albarka, ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login