Showing 48001 words to 51000 words out of 129540 words

Chapter 17 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6681

seda Jalal yafara jin haushi sannan ya dena
"Jalal wayagaya maka mata matsalane, mata ni'ima ne, tabbas akwai daga cikinsu masu matsala, amma akwai na kirki sosai, soyayya akwai dadi mussaman in kayi dace da mosoyi na kwarai, bazaka gane hakan ba seka fada tarkon soyayya"
"Hmm mata duk matsalane indai irinsu Ilham ne duk matsalane"
"Hmm bazaka gane ba Jalal"
"Eh naji bazan ganeba"
"Lokaci ze ganar da kai ai"
"Eh naji mutafi"
Jeje ne yakira Jalal yana son su hadu Jalal
Shikuma yace masa ya fita shida Jawwad bazeyiwu su hadu yanzu ba
Gurin cin abinci suka tafi shida Jawwad
Bayan sungama cin abinci ne suna hira aka kira Jawwad lambar Ummi yagani ya kara nutsuwa ya dau wayar
"Salamau alaikum Ummi barka da rana"
"Yawwa barka Jawwad ya kake ya mutan gidan"
"Kowa lafiya Ummi ya Jalila"
"To lafiya kalau za a ce meyasamu lambar abbanku nakira bata shiga"
"Inaga inda yake ne ba network, amma lafiya Ummi"
Ajiyar zuciya Ummi tayi ta kwashe kaf abunda yafaru tagayawa Jawwad
"Yasalam Ummi kiyi hakuri insha Allah komai zezo da sauki, yanzu bana Gida idan na koma zanwa Abban bayani insha Allah, kiyi hakuri Ummi dan Allah kinsan har yanzu yarinya ce"
"Ba batun yarinta? Jawwad tsabar rashin hankaline kawai
" adai yi hakuri Ummi "
Haka dai sukayi sallama Jawwad ya dafe kai
"Ohhh my God sisy ba dai rigima ba"
"Ya dai meyafarune?"
Jalal ya tambayeshi, Jawwad ya kwashe komai ya gayawa Jalal,
Dariya Jalal ya dinga yi kaman wani tababbe
"Kan bala'i wannan yarinyar Yar bala'ice wallahi, kaga zancena ko Jawwad, nagaya maka mata matsalane, mussaman irin wannan kanwar taka zama da ita seda panadol"
"Hmm haba Jalal kaima kanwarka ce, Jalila bata son raini bata yadda da wulakanci ba nidai fatana Allah yasa kar baban yarinyar yayi mata wani abu"
Wata dariyar Jalal yakumayi
"Kamar ya kar yayi mata wani abu "yarsa fa ta Daka, aigara suko yamata hankali yadda gobe bazata kuma ba,"
Yayi maganar yana dariya
"Haba Jalal Yar gidan Abee c??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e fa, in duniya da gaskiya bekamata kace haka ba"
"Hakane Jawwad kaima kace wani abu amma kasani bataji, in mutum yana rashin kunya in besamu dai? da shiba baze dena ba

? "Wow tauraro a cikin taurari kaina mussaman ne ban taba tunanin kana dariya haka ba, bakaga yadda dariya kemaka kyauba"
Gaba daya suka waiga domin ganin me maganar Hannah ce budurwar dasuka hadu da ita wancan karon, tayi maganar tana karasowa inda suke guri tanema ta zauna
"Jarumin maza meyabaka nishadi kake wannan dariyar haka ka fi ko yaushe kyau ko dan uwan ne yake baka nishadi"
Ta karasa maganar tana kallon Jawwad
"Uban wa yace kizo inda nake, me kike Nema a gurina ne kin uzzuramin kindami rayuwata meye hakane, waima wayagaya miki ina nan da kike bina"?
? Wani kasaitaccen murmushi Hannah tayi
"Call me by my name Hannah, or any special name u choose,
Kasan ita zuciyoyin masoya kaman wireless ne, our hearts and souls are always connected, dan hakazuciyarkace tagayawa tawa zuciyar kana nan shiyasa nazo kuma nayi sa'a nasameka zuciyarka kawai nake bukata Jalal, in har kabani zaka huta da nacina, akasin haka kuwa zan cigaba da hanaka sukuni cikin dare ko rana har sekabani abunda nakeso"
Wani wulakan taccen kallo Jalal yai mata ya watsar da ita bece mata komai ba
Jawwad ne ya danyi gyaran murya
"Kinaji Hannah already Jalal akwai wadda takeson Sa kanwarsa ce kuma kinga.....
Dagawa Jawwad hannu Hannah tayi
" haba dan uwan masoyina meye laifina anan dan ina kokarin cikawa zuciyata burinta, kowa iya allonsa ya wanke, tayi nata kokarin nima inyi nawa wadda tai galaba ta kafa soyayyarta a zuciyarasa shikenan, ni Hanna babu macen data isa tayi takara dani akan soyayya,
Jawwad son danakewa dan uwanka ko matansa hudu sena kori biyu ya aureni saboda space din daya yamin kadan,
Kar ace rashin adalcin nawa yayi yawane da se ince seya kori kowa ya aureni saboda shidin nawane ni kadai"
Saroro Jawwad yayi yana kallonta
"In kagama jin tatsuniyar kazo mutafi inada abunyi" Jalal yafada yana mikewa
Hanna ma mikewa tayi tazo gabansa kaman zata shige jikinsa se wani irin fitinannen kamshi take
"Babyna kabani dama ko sau dayane in gwada maka yadda nake sonka mana, kuskurewa bukatata shizesa incigaba da uzzura maka har gidanku nasani zaka iya ganina a kowani lokaci, karkayi mamaki nasanka farin Sani a yadda kake a haka nake sonka, zan iya komai akanka, kagayawa kanwarka ta janye kudirinta na sonka ta barmin kai in bahakaba"
Ta kashe masa ido daya daga nan tai tafiyarta,p babban abunda yabawa Jalal mamaki dayakasa yimata komai
Jawwad ne ya janyo hannunsa suka hau motarsu suka nufi Gida
"Jawwad ka yadda mata matsalane, abunda zuciyarsu ta raya musu kawai shi sukeyi, yanzu ga haukan da wannan tayi min, amma zan dau mataki akai"
"Kabi komai a hankali Jalal, kasan in mutum yana kan ganiyar so makancewa yake so ba karyane ba, ka dena wulakanta Wanda yace yana sonka kai baka san a ya zaka fara taka soyayya ba,
Amma wannan Hannah ka nemi tsari da sharrinta because Dana kalli cikin idonta ya tabbatar da she mean what she said"
Haka suka cigaba tattaunawa har suka iso gida
Bayan sallar isha'i Jawwad yaje part din Abba ya tarar dashi shi ka dai, yagaya masa abunda ya faru jinjina kai Abba yayi
"Hmm Jalila iya rigima, halin mahaifinta ta dakko bata son raini Allah ya kaimu goben, zan San yadda za ayi"
Da asuba Abba ya taho kano be gayawa maama abunda ya faruba ya dai cemata zeyi fitar asuba zashi wani guri

? Still wannan Daren ma messages din Hannah suka dinga shigowa wayarsa seda yagaji ya kashe wayar

Washe gari da safe Jalila ta shirya ta tafi makaranta, Daren ranar addu a ta kwana? tanayi
Ba wai Allah ya sassauta fitinar da ta dakko ba, se dai Allah yasa kar Ummi ta korata kano
? A hanyar makaranta ta hadu da yayan lubabatu data tsokana ranar akayi Sa a ya ganeta, ta Ganshi sarai amma taki guduwa tacigaba da tafiya a hankali,
Zuwa yayi ya sha gabanta
"Ke karamar Mara mutunci ni kika zaga ranan ko waike Yar iska"
"Wallahi kasake ka tabani sena tara maka jama'a nace zaka lalata ni shekara goma sha hudu ce zakayi a gidan yari bayawa"
"Au tunaninki barazanar ki zata hanani in casaki senaga uban da ya tsaya miki"
"Bari kaji in gaya maka idan kana shan kwayarka tagaya maka karya kayiwa mutane hauka, to karkayi gangancin gwada kwayarka akaina,
Dan wallahi sena kulla maka sharrin dazaka kare rayuwarka a prison"
Kafin kace meye wannan Jalila ta ware murya ta fara ihu iya karfinta hankalin jama'a ne yafara dawowa Kansu ana fara taruwa ta silale ta gudu ta nufi makaranta
Abunda yasa ta guduma gudun kar takuma shiga wata cakwakiyar bata fita daga wadda take ciki ba ga Ummi tace zata maida ita gidan su Jawwad da setasaka anmasa duka
? Tana zuwa ajinsu ta tafi taje gurin zamanta ta hakimce ba tareda ta kula kowaba, "Allah ya biya Queen J Dama tunda yarinyar nan tazo kanta yake hayaki, se wani takama take, malamai ma kaman wani tsoronta sukeji segashi kinyi maganinta"
Haka dai seatmates dinta suka dinga zigata ita dai Jalila hankalinta yana kan batun Ummi
Bayan anfita break an dawo ba dadewa Hanan ta shigo ajin tana kallon kowa a wulakance ga malami a ajin amma Hanan batabi takan malamin ba ta tako
Tazo gaban Jalila
"Sannu uwar rashin kunya, dama na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki,
Yau zakigane kin taba Yar gidan bullet kizo office bullet yazo da kansa"
"Amma kin bani kunya da kikazo da bullet kawai, ai na dauka barikin zaki dakko gaba daya su taho da egwa yadda in sun markadeni baza ageneniba dan dai bullet, ai bullet yayi kadan aga bayana dashi"
Jalila takarasa maganar hade da tsaki"nonsense "
Mikewa Jalila tayi tai gaba ta wuce hanan
Wato Jalila Yar bala'ice babu alamar risina a tare da ita tun tasowar Hanan take taka Wanda taga dama take jefa tsoro a zukatan duk Wanda yai kuskuren shiga hanyarta saboda takamar ubanta wani ne amma yau ta hadu da wadda tafita rashin mutunci
Haka ta bi bayan Jalila suna zuwa harabar ofishin director Jalila sukayi clashing da malama ramatu aikuwa Jalila ta tsaya
"Ita wutar munafiki ko tana karkashin jahannama ne,
Kekam baki dace da malamar makaranta me bada tarbiyya ba kema kina bukatar me baki"
Jalila ta gayawa malama ramatu sannan tai gaba abinta

Tana shiga office din director ta tarar da mutane ba Wanda ta kula kuma bata kalli suwaye a ciki ba ta shige

Share please
More comments more typing.............

=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 20&21

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? ?
? ? ? ? -My First Novel-

"Meyasa kikace kar ya sha"
"Nidai kawai kahana shi sha kar ya sha tea din nan"
Jawwad ji yayi gaba daya ta firgice masa
"Amma meyasa kikace kar ya sha?"
Sekuma tarasa mezata ce masa
"Am...emm.. Idan ya sha ze iya yin amai gara kaimasa tofi na ayoyin Qurani ya sha kafin kabashi abinci in Bahaka ba, ze iya bashi matsala eh..m.. In...nima malaminmu ne yafada mana a Islamiyya"
? Da Jawwad yaji haka da sauri yasa hannu ya karbi cup din tea
Daga hannun Jalal
Jalal ne ya kalleshi
"Meye haka kuma?"
"Kanwarka tace karka sha tukuna, Dan huta ina zuwa"
"Kaga ni bani yunwa fa nakeji yaushe zan tsaya biye maka yarinya Karama tana juya ka"
ya yunkura ze karbi cup din tea daga hannun Jawwad yaji kansa ya kara nauyi dan haka ya koma ya zauna yana jujjuya kan
"Sannu bros"
Jinjina kai kawai Jalal yayi
Kamar yadda Jalila ta gayawa Jawwad yaje fridge ya dakko ruwa ya karanta ayoyin Qurani ya busa masa a ruwan yazo ya tsiyayo a cup ya bashi
Hannu yasa ya karba ya shanye ya ajiye kofin, ko minti biyar beyi da shan ruwan ba ya mike ya tafi bandaki ya dinga wani irin bakin amai
Jawwad ne ya bishi yana masa sannu ya kwashi mintuna yana amayar da wani bakin abu
Seda Jawwad ya Dan tsorata

"Jalal mutafi Asibiti your condition is getting worst jin ciwon nan nake kaman a jikina"
Ture Jawwad yayi ya tafi ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu ga wani mugun Jiri dayakeyi
Jawwad ya biyo bayansa, Dan kura masa ido yayi yaga jijiyoyin kan Jalal duk sun mike fuskarsa tayi Ja
Gefen gadon ya zo ya zauna yasa hannunsa akan Jalal yana masa karatun Qurani a hankali
Wani baccin wahala ne ya kuma awon gaba da Jalal abun mamaki a cikin baccinsa ya dinga Jin sautin karatun Jalila Wanda ya dinga jin nutsuwa tana saukar masa

Jawwad ne ya mike ya nufi gida don tafiya masallaci lokacin salla la'asar yafara gabatowa
Cikin Gida ya shiga ya tarar da Nana tana video game maama kuma ta Dan kwanta a akan kujera tana kallon Nana
Sallama yayi suka amsa gaba daya
"Maama sannu da Gida"
"Yawwa ya jikin Jalal din"?
"Da sauki maama"
"Allah ya sawwake"
"Ameen"
Ya amsa
"Nana babu abunda kika iya se shirme,
Jalila tana can tayi abun arziki ke kam shirirtarki ta fiye miki"
Attention dinta gaba daya Nana ta bashi
"Allah Yaya me Jalilan tayi"
"Gasar karatun Qurani sukaje abuja jiya, tazo na biyu, amma se rikici takewa Ummi wai ita na daya take so"
"Dan Allah Yaya dagaske amma naji dadi, ga fitina ga kwanya Allah sarki Jalila Allah yakara hasken makaranta"
"Ameen kema se ki dage kidena wannan shirmen"
Duk abun nan maama bata ce uffan ba
? "Amma shine ko ta gayamin amma kai ta gaya maka dani take zancen"
Nana tafada tana Dan bata rai
"Aini kullum se munyi waya da ita"
"Ai Yaya dole muje Kaduna we have to celebrate the victory of my great sister bari Abba ya dawo"
Nana tai maganar tana murmushi
?? "Karki fara, kwata? yaushe ta bar gidan nan kike zancen, wani zakuje to babu inda zaku, nasake naji kin tambayi abbanku zakije sena bata miki rai sha? kawai,
Kaikuma naga zakewarka akan yarinyar nan yafara yawa ka kiyayeni? Jawwad in bahakaba daga kai har ita senaci mutuncinku,"
Maama ce tayi wannan maganar cikin fada da fushi gaba daya suka bita da kallo
Ajiyar zuciya Jawwad yayi ya dan girgiza kai
"Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki za a kiyaye insha Allah"
Ya Fita yabar parlour itakuwa Nana zunbura baki tayi itama ta barwa maama parlour
"Lallai in ban dageba maganar Yaya mairo na shirin zama gaskiya zakuci kaniyarku sena raba Ku da yarinyar nan"

Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki
Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa
Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da "ya'yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu
Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya
Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba
Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna
" kina ina ne?"
"Ina Gida mana"
Hanna taba shi amsa
"Muna tare da mutuminki fa yanzu haka"
"Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya"
"Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi"
"I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi"
"Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari"
"Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne"
"That's good seda safe"
Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya
Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha
Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa
Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing
"Maza wayarka fa ake kira"
Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa
"Nagani"
Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa
Messages ne suka dinga shigowa wayarsa
Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din
? ? ?? "Haba fitilar rayuwata? ? ? ?? meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice
I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby
? ? ? ?? From your lovely bae"

Ire? wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad?
Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar
"Jalal kana ina?"
Jawwad ya tambayeshi
"Na dan fitane"
"Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe"
Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice
Jeje ya kalleshi
"Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?"
"Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri"
Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka,
Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace
Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa
Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin

Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane? dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana
A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai
"Naji kaman kinyi bakuwa se anjima"
Jalila tayi maganar
"Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa"
"Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi"
Dariya Nana tayi tare da fadin
"To Ilham kinji dai sakon Jalila"
Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta

"Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali"
Ilham tai maganar tana mikewa
Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar
"Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka"
Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?"
"Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi"
"Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka"
"A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba
Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu"
"Ai nasani"
Ilham tabata amsa
"Ya akayi kika Sani?"
"Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni"
Ta karasa maganar cike da damuwa
Nana ta dafa ta
"Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara"
Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa
"Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?"
"Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane"
"Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba"
"Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa"
"Allah yasa haka Nana"
"Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be"
Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login